Wannan aiki ya mayar da hankali ne kan tasirin biɗa (nema) da tanadi (tattali) ga cigaban tattalin arziƙin Bahaushe. Takardar ta yi bitar ma’anoni da kamanci da kuma wasu bambance-bambancen da ake iya samu tsakanin kalmomin guda biyu. Bayan haka, an nazarci yadda lamarin ya ke ga Bahaushen yau. Bugu da ƙari, an yi bitar gurbin biɗa da tanadi ga bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe. Domin binciken ya kuɓuta daga jin kunyar ilimi da masu ilimi, an bi manyan hanyoyi bincike guda biyu waɗanda da su ne aka yi amfani wajen tattara bayanai yayin binciken. Hanyoyin su ne, bitar ayyukan da suka gabata da kuma tambayoyi. An ɗora aikin kan tunanin Bahaushe na “Mai nema na tare da samu.” Binciken ya gano cewa, biɗa da tanadi ba a matsayin tasiri kawai suka kasance ba, su ne ke tallafe da tattalin arzikin Bahaushe a tarihance. A ɓangare guda kuma, tasirin zamani da sauye-sauyen yanayi ya kawo sauyi ga yadda tsarin yake a baya. Hakan kuwa ya samar da giɓi bayyananne ga tattalin arziƙin Hausawa, duk kuwa da cigaban da aka samu a ɓangare guda. A bisa haka ne takardar ke ba da shawarar cewa, a yi hoɓɓasar nazartar hanyoyin ɗinke wannan ɓaraka a matakin ɗaiɗaikun al’umma da gundumomi da kuma a gwamnatance.
Wanda ya Tuna Bara...: Biɗa
da Tanadi a Tsakanin Hausawa Matasa a Yau
Abu-Ubaida Sani1
Umar Buba2
Ibrahim Mohammad3
1Department
of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria
2 and 3School
of Educational Services, Aminu Saleh College of Education, Azare, Bauchi State,
Nigeria
1.0 Gabatarwa
Duk
da cewa akwai fasahohin rayuwa da ba su zo wa Bahaushe ba sai bayan cuɗanyarsa
da baƙin al’ummu,[1]
abin ba haka yake ba ga falsafar biɗa da tanadi. A wannan ɓangare, sai dai a ce:
“Tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta!” A rayuwar
Hausawa, biɗa da tanadi na da tsohon tarihi. Hasali ma, Hausawa sun shahara ta fuskar
noma da kasuwanci da fatauci da sauran sana’o’i daban-daban. Ficen da Hausawan
suka yi a ɓangaren sana’o’in fatauci da kasuwanci ya taimaka matuƙa wajen
bazuwarsu zuwa wurare daban-daban. Hausawa sun kafu a ire-iren waɗannan wurare
tare da cigaba da gudanar da sana’o’insu.[2]
Wannan
takarda ta dubi yadda lamarin biɗa da tanadi ya ke a Bahaushiyar rayuwa. An
waiwaiyi yadda abin yake a da, tare da nazartar sauye-sauyen da aka samu. Kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Zamani riga
ne.” Wanda bai saka rigar ba, haƙiƙa dole ya bayyana tsirara. Ke nan dai cigaban
tattalin arziƙin Hausawa a yau ba zai samu ba sai Hausawan sun taka nau’in
rawar kiɗan da zamani ke rangaɗawa. Duk kyawun tsarin salo na biɗa da tanadin
Bahaushe na gargajiya, ba dole ne ya dace da zamani ba. Wannan kuwa duk da
cewa, a ɓangare guda bin zamanin na kawo koma baya ta wasu fuskokin zamantakewa.
Hakan ya fi shafar haɗin kai da zaman “ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda” wanda shi
kansa ya kasance wani babban jigo ga bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe.[3]
1.1
Manufar Bincike
Maƙasudin
wannan aiki shi ne bitar gurbin biɗa da tanadi ga bunƙasar tattalin arziƙin
Hausawa. Kai tsaye aikin zai mayar da hankali a kan:
i.
Nazartar tasirin biɗa ga bunƙasar tattalin
arzikin Bahaushe.
ii.
Nazartar tasirin tanadi ga bunƙasar
tattalin arziƙin Bahaushe.
iii.
Nazartar biɗa da tanadi a zamantakewar
Hausawa a yau.
1.2Hasashen
Bincike
Masana
da manazarta al’adun Hausawa sun tabbatar da cewa, Bahaushen asali jarumi ne
kuma jajirtacce mai kaifin basira da dogewa kan gaskiya da riƙon amana.
Azancinsa da dabarunsa sun taimaka masa ainun wajen ƙyallaro hanyoyin biɗa da
tanadin da za su bunƙasa tattalin arziƙinsa. Sai dai kash! Rubuce-rubucen
baya-bayan nan na ƙara tir ga taɓarɓarewar al’amuran Bahaushe a yau. Wannan har
ya kai ga Amfani (2011) yana siffanta Bahaushen yau da cewa:
Hausawan
wannan zamani ba su da wata cikakkiyar manufa ta rayuwa. Babu wata manufa
bayyananniya ta neman duniya ko lahira. Shashanci da shaye-shaye da lalacewa su
matasa suka sa a gaba. Bugu da ƙari kuma, ga ta’addanci da ‘yandabanci. Sata da
lalaci da zamba sun yawaita a cikin al’umma. Yara da manya ba su son gaskiya,
kuma ba su iya riƙe amana. Lalaci irin na kwaɗayi da roƙo da bara ya shigi
mutane sosai. Mutane masu lafiya zuciyarsu ta mutu sai son roƙo da bara.(Amfani, 2011:
4-5)
Shehu
da Sani, (2018: 274-284) sun kawo misalan ɓangarorin rayuwa da suke hasashen Bahaushe
ya samu ci baya. Sun haɗa da zamantakewa tsakanin masu mulki da talakawa da
tsakanin attajirai da koma bayansu da kuma tsakanin malamai da ɗalibai. Lura da
ire-iren waɗannan rubuce-rubuce, wannan takarda na da hasashen cewa, Bahaushe a
yau ya gaza a ɓangaren biɗa da tanadi. Wannan kuwa kan iya samar da naƙasu ga
bunƙasar tattalin arziƙinsa.
1.3 Ra’in Bincike
Kasancewar
wannan bincike ya shafi tattalin arziƙin Hausawa ne, da laluben dalilan da suka
sanya aka wayi gari da sukurkucewar lamari a yau. Wannan ya sa na ɗauki karin
maganar nan da ke cewa: “Karen duk da ya yi cizo da gashinsa ake magani.” Kasancewar
rubutun ya shafi Hausawa ne kai-tsaye, an ga dacewar ra’in binciken ya fito daga
hikimomi da azancin Hausawa waɗanda ake samu a cikin adabinsu da al’adunsu da
kuma harshensu. A yau, babu wanda ke musun ɗimbin hikimomin da ke ƙunshe a cikin
adabin Hausawa, waɗanda kuma su ne ke jagorantar rayuwarsu ta yau da kullum.
Akan sami ire-iren waɗannan ra’o’i kan tsarin rayuwa a cikin karuruwan magana
da azancin Hausawa da kuma ƙudurin imaninsu na camfe-camfen da dangoginsu. A
bisa waɗannan dalilai, aikin bai yi nisan kiyo ba wajen neman ra’in da ya
kamata ya yi masa jagora. An ɗora aikin kan falsafar Hausawa da ke cewa: “Mai
nema yana tare da samu.” A taƙaice ke nan, yayin da aka samu al’umma sun
jajirce kan hanyoyi da matakan biɗa da tanadi, zai kasance tattalin arziƙinsu
ya samu gindin zama. Koma bayan haka kuwa, sai dai a ce: “Allah dai Ya kyauta!
Wai in ji raggo da ya sha kiɗa.”
“Bunƙasar
tattalin arziƙi na da nasaba da hoɓɓasa da ƙoƙarin da akan yi. Zai iya zama a
matakin ɗaiɗaikun mutane, ko kuma al’umma ɗungurungum. A hasashen wannan
bincike, a yau Hausawa, musamman matasa ɗaliban Jami’a, sun saki sana’o’i.
Wannan ya kasance saɓanin rayuwar Bahaushe a da wanda “kowane gida akwai
sana’a” (Gobir, 2019).[4]
1.4
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Domin
ɗaure akuyar binciken a gindin magarya, an yi amfani da wasu manyan dabarun
aiwatar da bincike waɗanda suka ƙunshi bitar ayyukan da suka gabata da kuma
tambayoyi. Domin cimma manofofin aiki na farko da na biyu, an sami nasarar kai
rangadin bincike wasu ɗakunan karatu, inda aka sami damar leƙa wasu littattafai
da kundayen digiri na matakan ilimi daban-daban da kuma wasu muƙalu da
manazarta suka gabatar a tarukan ilimi daban-daban. An sami zarafin bibiyar
ra’ayoyin masana dangane da ma’anar “biɗa” da “tanadi.” Bayan nan, an duba
yadda masana ke kallon biɗa da tanadi ta fuskar tasirinsu kan tattalin arizikin
Hausawa.
A
ɓangare guda kuma, kasancewar mai ɗaki shi ya san wurin da ke masa yoyo, an yi
amfani da tambayoyi domin binciko yadda biɗa da tanadi suka kasance ga Bahaushen
yau. An zabi ɗaliban da suke karatun digirin farko a Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato a matsayin samfurin gudanar da
wannan bincike. An yi la’akari da kasancewarsu matasa yayin gudanar da wannan
zaɓi. Wannan na nuna cewa, ana kyautata zaton amsoshinsu su kasance madogara
yayin magana kan biɗa da tanadi ga Bahaushen yau, musamman wanda ke cikin
tsarin karatun boko.
Ɗaliban
sun haɗa da ‘yan aji huɗu (400L) da aji uku (300L) da aji biyu (200L) da kuma
aji ɗaya (100L). Jimillar adadin ɗaliban su ne 90.[5] A saboda haka, an ɗauki
adadin ɗalibai 87 a matsayin samfuri. Wannan ya yi daidai da ƙa’idar ɗaukar
samfuri na Krejcieda Morgan(1970). A ƙasa an kawo jadawalin ɗaliban:
Jadawali 1:
Samfurin Ɗaliban Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato (2019/2020).
Lamba
|
Aji
|
Jinsi
|
Adadi
|
Samfuri
|
|
1.
|
4 (400L)
|
Maza
|
23
|
26
|
25
|
Mata
|
3
|
||||
2.
|
3 (300L)
|
Maza
|
37
|
38
|
36
|
Mata
|
1
|
||||
3.
|
2 (200L)
|
Maza
|
12
|
13
|
13
|
Mata
|
1
|
||||
4.
|
1 (100L)
|
Maza
|
11
|
13
|
13
|
Mata
|
2
|
||||
Jimilla
|
90
|
87
|
Madogara: UDUS
Web Team, (2019)
Tambayoyin
da aka yi amfani da su, suna da ɓangarori guda uku. A ɓangare na farko an nemi
bayanai ne game da masu amsa tambayoyin. Ɓangare na biyu kuwa na ɗauke da
tambayoyin da ke buƙatar amsar “eh” ko “a’a.” Ɓangare na uku kuwa, ya ƙunshi
tambayoyin da ke buƙatar amsa daga ɗaya daga cikin zaɓuka uku (threeLikert
scale). Zaɓukan sun kasance: “Eh” da “Ina Kokonto” da kuma “A’a.”
Domin
tabbatar da ingancin tambayoyin da aka bayar, an ba da tambayoyin ga wani
masani a Tsangayar Nazarin Harkokin Ilimi, Sashen koyar da dabarun koyar da
darussan fasahohi da hikimomin al’umma/Tushen Karatu (Faculty of Education, Department
of Educational Foundations) na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. An gwada waɗannan
tambayoyi a kan ɗalibai guda biyar a matsayin gwaji.[6] An raba waɗannan tambayoyi
cikin kwanaki uku kacal, sannan an nemi ɗaliban su cika tare da maido da su a
cikin kwanaki biyu ko ƙasa da haka. An nemi agajin shugabannin ɗaliban na kowane
aji domin rabawa tare da karɓo tambayoyin da aka raba musu. Hakan ne kuma ya sa
ba a samu matsalar ɓacewa ko lalacewar ko guda ɗaya daga cikinsu ba.
An
yi amfani dajadawali da kuma hanyar nuna adadin amsoshin da aka tattara domin
fito da bayanan da aka samo daga waɗanda suka amsa tambayoyin. Dabarar (Formulae)
da aka yi amfani da ita ta kasance A/Y×100. “A” na matsayin adadin mutanen da suka zaɓi
wata amsa. “Y” kuwa na matsayin yawan amsoshin da ke wurin gaba ɗaya.
2.0
Tattalin Arziki a Bahaushen Tunani
Tattalin
ariziƙin al’umma abu ne mai faɗi. Ya shafi dukkanin al’amuran da ke haɗuwa su
ba da hoto ko bayani kan arzikin al’umma. Curarren furuci ne da ke da yalwa.
Farfajiyarsa ya haɗe da abubuwan da suka shafi kasuwancin al’umma da sana’o’insu
da dukiyoyinsu da kadarorinsu da kuma yadda suke cuɗanya da gudanar da rayuwa
tare da waɗannan abubuwa da aka zayyano.
Furucin
tattalin arziki hatsin bara ne. Mika’il, (2015: 3) ya bayyana cewa: “Kalmomi guda biyu ne
suka tayar da kalmar tattalin arziki, watau, “tattali” da “arziki.” Wannan na
nuna cewa, sanin ma’anonin kalmomin biyu na da matuƙar amfani. Hakan ne zai ba
da damar fahimtar gundarin ma’anar furucin (tattalin arziki). Kalmar “tattali”
kamar yadda Auta (2006:194) ya bayyana: “... kalma ce mai nuna rainon wani abu
har ya kai ga ya girma.” A ɓangare guda kuwa, ya bayyana ma’anar “arziƙi” da
“... samun dukiya ko wani abin mallaka.”
Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni, ke nan, tattalin
arziƙi na nufin “renon dukiya ko wani abin mallaka mai amfani da tarisi ga cigaban
rayuwa ta hanyar yin amfani da dabarun tattali da adana da killacewa.” Bunƙasar
tattalin arziƙi na faruwa ne yayin da abin mallaka ko dukiya ta haɓaka. Koma bayan
haka kuwa, shi ake kira “daƙushewa ko karayar tattalin arziƙi.” Ƙumshiyar
tattalin arziƙi na shafar abubuwa da dama a zamantakewar al’umma. Daga cikin
abubuwan da ke shafuwa sun haɗa da:
a.
Kasuwanci.
b. Sana’o’i.
c. Fatauci.
d. Adana.
e. Tallafi.
Haɗakar
waɗannan kuwa (da ma wasu makamantansu), a jimlace sun shafi “biɗa” ne da “tanadi.”
Cigaban tattalin arziƙi na iya kasancewa:
(i)
Na matakin mutum.
(ii)
Na matakin al’umma ko ƙasa.
Tattalin
arziƙin matakin mutum ya shafi sukuni ko wadata ko tajircin ɗaiɗaikun jama’a a
cikin al’umma.[7]
Shi kuwa na matakin ƙasa ya haɗa da arziƙi da wadatar ƙasar na gaba ɗaya. Bisa
haka ne ma Ibrahim ya bayyana
ma’anar tattalin arziƙi ta hanyar la’akari da matsayi ko gurbin gwamnati ga sha’anin
tafiyar da tattalin arziƙi. Ya ce:
... tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran
ni’imomin da Allah ya yi wa ɗan’adam domin samar da muhimman abubuwan buƙatu da
rarraba su ga jama’a masu buƙata. Ibrahim
(1981:5).
Kafin a ce tattalin arziƙi ya bunƙasa kuma ya samu gindin
zama, dole sai al’umma (wadda ake magana a kanta) ta kasance mai fasahar
sarrafawa tare da samar da abubuwan buƙata na rayuwar yau da kullum. A bisa
wannan tunanin ne Umar ya gina ma’anar tattalin arziƙi. A ciki ya bayyana
sarrafa abubuwan rayuwa a matsayin ginshiƙin tattalin arziƙi. Ya ce: “Tattalin
Arziƙi tsari ne na sarrafa wasu abubuwa domin samun abubuwan rayuwa.” Umar
(1983:5).Yayin da ake ce an samu bunƙasar tattalin arziƙi, ana
nufin cewa:
a. Akwai
ci gaba a hada-hadar kasuwanci.
b. Akwai
sabbin fikirori da fasahohi a ɓangaren sana’o’i, sannan ana samun riba mai gwaɓi.
c. Arziƙin
al’umma ya kai ga bunƙasar da za su iya dogaro da kansu.
d. Masu
ayyukan yi su suke da rinjaye, yayin da marasa aiki suka kasance ƙalilan.
e. Talauci
ya yi ƙaranci a tsakanin al’umma.
3.1
Biɗa da Bunƙasar Tattalin Arziƙin Bahaushe
Kalmar
“biɗa” na nufin “nema.” Ma’ana dai kalomomi ne guda biyu masu kinin ma’ana. Wani
babba abin lura a nan shi ne, an fi amfani da kalmar “nema” a Hausar gabas. “Biɗa”
kuwa, an fi amfani da ita a Hausar yamma. Sule na da wannan fahimtar inda ya
bayyana cewa:
Hausawan yankin Sakkwato da Kabi da Zamfara da ma wasu da
ke ƙarƙashin Yammacin ƙasar Hausa irin su Katsina da wani yanki na Jamhuriyar
Nijar ne suke cewa biɗa a maimakon nema.[8](Sule, 1986:15).
Wani muhimmin abin lura shi ne, za a iya kallon biɗa ta
fuskoki guda biyu. Da farko dai akwai biɗar “arziƙi.” Wannan kuwa ta shafi duk
wata sana’a ko wani kasuwanci ko fatauci da mutum zai runguma domin inganta
tattalin arziƙinsa. Yana kuma iya kasancewa taron jama’a ne suka haɗa kai ko
kuma ma ƙasa gaba ɗaya, suka duƙufa kan sana’a ko kasuwanci ko fatauci, duk dai
domin inganta tattalin arziƙi. A taƙaice, duk wani yunƙuri na neman kuɗi da
sauran al’amuran da suka shafi wadata da walwalar rayuwa, to ana ce masa “biɗa.”
A bisa wannan, idan aka ambaci biɗa, hankali zai koma kan:
a.
Sana’ar
da za a yi domin biɗar kuɗi.
b.
Kasuwanci
da za a yi domin biɗar riba.
c.
Fatauci
da za a yi domin biɗar riba.
A ɓangare guda kuwa, ana iya samun biɗa a cikin su kansu
“hanyoyin biɗar arziƙi” (sana’o’i da kasuwanci da fatauci). Misali:
i.
Sana’a
a. Biɗar
ilimin gudanar da sana’a.
b. Biɗar
kayan gudanar da sana’a.
c. Biɗar
wurin gudanar da sana’a.
d. Biɗar
masu sayen abubuwan da aka samar (masu ciniki).
e. Biɗar
hanyoyi da matakan yin fice da buwaya kan sana’a.
ii.
Kasuwanci
a. Biɗar
ilimin gudanar da kasuwanci.
b. Biɗar
jarin gudanar da kasuwanci.
c. Biɗar
wuri ko wuraren gudanar da kasuwanci.
d. Biɗar
abokan gudanar da kasuwanci (masu sayen kaya).
e. Biɗar
matakan inganta kasuwanci.
iii.
Fatauci
a. Biɗar
ilimin gudanar da fatauci.
b. Biɗar
abokan fatauci.
c. Biɗar
jarin yin fatauci.
d. Biɗar
abubuwan da ake buƙata yayin fatauci (dangin tafiye-tafiye da kare kai da
sauransu).
La’akari
da waɗannan, za a iya kallon biɗa a matsayin babban ginshiƙin da ke tallafe da
tattalin ariƙin al’umma. Ga al’ummar Hausawa, biɗa ce ta kasance ƙashin bayan
tattalin arziƙinsu.[9]
Kaɗan daga cikin dalilan da suka nuna haka akwai:
i.
Ta hanyar biɗa ne Hausawa suka samu
kasuwanci da sana’o’i da sauran hanyoyin dogaro da kai.
ii.
Ta hanyar biɗa ne Hausawa suka samu dabaru
da magungunan buwaya domin bunƙasa tattalin arzikinsu.
3.2
Gurbin Tanadi a Bunƙasar Tattalin Arziƙin Bahaushe
Kalmar
“tanadi” ta samo asali ne daga “tanada.” Ita kuwa “tanada” kamar yadda ta zo a Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero, Kano tana nufin: “(i) Shirya ko adana. (ii) Ajiye wani
abu saboda ɓacin rana, daidai da tattala.” (Sa’id 2006: 425). Shi ma
tanadi za a iya kallon sa ta manyan fuskoki guda biyu kamar haka:
1. Tanadin
kayan biɗa.
2. Tanadin
arziƙi.
3.2.1
Tanadin Kayan Biɗa
Kamar
yadda aka yi bayanin biɗa a sama (ƙarƙashin 3.1), akwai tanade-tanade da ake
gudanarwa yayin biɗar. A wannan ɓangare, biɗa da tanadi na faruwa lokaci guda.
Ma’ana a nan ita ce, yayin da za a tanadi kayan da ake buƙata domin aiwatar da
sana’a, to biɗo kayan ake yi. Haka ma idan aka ce za a biɗo kayan gudanar da
sana’o’i, to maƙasudin bai wuce tanadinsu domin gudanar da sana’o’in ba. Lura
da wannan, tanadin kayan biɗa ya shafi:
i.
Tanada kayayyakin da ake buƙata yayin
aiwatar da sana’a, misali, a sana’ar ƙira akan tanadi arautaki da uwar maƙera
da gawayi da guduma da sauransu.
ii.
Tanadin kayayyakin da ake buƙata yayin
gudanar da kasuwanci, misali, maisayar da goro zai nemi faifayi da algarara da
sauransu.
iii.
Tanadi domin fatauci: Misali, fatake na
tanadar dabbobin hawa ko na ɗaukar kaya irin su jakai da dawaki da raƙuma da kuma
alfadarai.
3.2.2
Tanadin Arziƙi
Arziƙi
kamar yadda bayanai suka zo a ƙarƙashin 2.0, ya shafi kuɗi da dukiya da kadara
da sauransu. Tanadin arziƙi a nan na nufin tanadin kuɗi ko wani abu da za a iya
sayarwa a samu kuɗi domin amfani da su a lokacin da buƙatar hakan ta taso.
Bahaushe na amfani da wasu hanyoyi da dabaru domin tanadar kuɗin da zai yi
lalurori ko biyan buƙatu na musamman. Ire-iren buƙatun da Bahaushe ke yi wa
tanadi sun haɗa da:
i.
Aure.
ii.
Haihuwa.
iii.
Samun jari.
iv.
Doguwar tafiya (guzuri).
v.
Bukukuwa.
Yayin
gudanar da ɗaya daga cikin waɗannan hidindimu (da ma wasu makamantansu), akwai
buƙatar kuɗi. Hausawa sun ce: “Mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka.” Kamar
haka ne Bahaushe ke fara tanadi tun da wuri yayin da yake fuskantar wani al’amari
da ke da buƙatar kuɗi masu kauri. Daga cikin fitattan hanyoyin da yake bi domin
tanadin akwai:
a. Adashe:
Akan
yi adashe domin gudanar da wani aiki mai muhimmanci yayin da aka kwashi
adashen.
b. Asusu: Akan yi asusu domin wata hidima ta
musamman. Yayin da hidimar ta zo sai a fasa asusu a biya buƙata. Ba don wannan
tanadi ba ta hanyar asusu, to kuwa da wuya a samu adadin kuɗin da ake buƙata
kai tsaye a yi hidimar.
c. Ajo:
Ajo a nan na nufin gudummuwa da ake kaiwa yayin biki. Yayin da mutum ya lizimci
ajo, haƙiƙa shi ma/ita ma zai/za ta samu gudummuwa lokacin da hidima ta taso
masa/mata. Wannan na nuna cewa, kai ajo tamkar ajiya ce.
d. Ajiya: Bahaushe ya gama magana inda ya ce:
“Ajiya maganin wata rana.” Akan ajiye wata kadara ko dukiya domin yin amfani da
ita yayin da wata buƙata ta musamman ta taso. Yayin da ajiya ta shafi kuɗi,
musamman waɗanda ake tarawa sannu a hankali, to ana iya kiran ta asusu.
e. Turke:
Turke a nan na nufin kiwata wata dabba musamman domin sayarwa tare da yin
amfani da kuɗin yayin biyan wata buƙata ta musamman. Ana kuma iya yin turke a
matsayin tanadin abin yanka lokacin salla ko wasu bukukuwa da sauransu.
4.0
Biɗa da Nema a Duniyar Bahaushen Yau
A
yau, duniyar Bahaushe ta samu sauyi matuƙa ta ɓangarori da dama. Cikinsu har da
abin da ya shafi biɗa da tanadi. Daga cikin manyan dalilan da suka samar da waɗannan
sauye-sauye akwai, ƙaruwar ilimi da cuɗanya da baƙin al’ummu da kuma wayewar
zamani. A yau, akwai sabbin hanyoyin biɗa da tanadi da Hausawa suke cin
gajiyarsu. A ɓangare guda kuma, an samu sauye-sauye ga hanyoyin biɗa na gargajiya.
Wasu daga cikinsu sun haɗa da:
1. Amfani
da banki a maimakon asusu.
2. Kasuwanci
ta hanyar intanet (yanar giza-gizan sadarwa).[10]
3. Amfani
da ababen hawa dangin motoci da jirage (da sauransu) yayin kasuwanci da fatauci
koma bayan jaki da doki da alfadari (da sauransu) da ake amfani da su a da.
4. Amfani
da kafafen yaɗa labarai domin tallata haja.
5. Zamanartar
da hanyoyin gudanar da sana’o’i ko kasuwanci, misali sanya kayayyakin da ake
sarrafawa cikin leda ko kwali da makamantansu.
Waɗannan
da aka lissafo (da sauran makamantansu) na daga cikin sauye-sauye da aka samu
dangane da biɗa da tanadi. Waɗannan cigaba sun taimaka matuƙa ga tattalin arziƙin
Bahaushe. A sakamakon cigaban da aka samu, za a iya fahimtar cewa:
a. Bankuna
na taimakawa wajen ajiye kuɗi hankali kwance tare da ɗibar su lokacin da ake buƙata,
sannan a wurin da ake buƙata. Wannan ya taimaka wa tattalin arziƙin Bahaushe ta
fuskar rage haɗari da tsautsayin da ke tattare da tafiya da kuɗaɗe masu yawa,
ko kuma ajiye su a gida ko wurin sana’a.
b. Intanet
ta samar da sauƙin gudanar da kasuwancin da ya shafi kawo kayayyaki daga wurare
masu nisa. Wannan ya sauƙaƙe wa Hausawa tilascin fita fatauci bisa hanyoyin
gargajiya da ka iya ɗaukar kwanaki ko makonni ko ma watanni.
c. Ababen
hawa a yau na taimakawa wajen saurin kaiwa da ɗauko kayayyakin kasuwanci.[11] Tuni wannan ya zama
hanyar cin abincin Hausawa da dama. Hakan kuwa ya kasance cigaba ga tattalin
arziƙin Bahaushe.
d. Dukkanin
waɗannan sauye-sauyen zamani na ɓangaren biɗa da tanadi na zuwa da sabbin
ayyuka waɗanda kuma akan sami Hausawa na cin gajiyarsu.
5.0
Sakamakon Nazari da Sharhi
Tun
tuni Bahaushe ke da dabarun bunƙasa tattalin arzikinsa. Daga cikin manyan
hanyoyin akwai biɗa. Tattalin arziki ba ya iya cigaba ba tare da biɗa ba. Ta
hanyarsa ne ɗaiɗaikun mutane da al’umma ɗungurungum ke samun abin hannusu.
Kamar yadda wannan bincike ya gano, Bahaushen asali ba malalaci ba ne. Yana da
sana’o’i daban-daban da yake aiwatarwa domin biɗar halali. Daga ciki akwai jima
da saƙa da kaɗi da kitso da dukanci da fawa da sassaƙa da wanzanci. Jimillar waɗannan
hanyoyin neman abin kai shi Bahaushe ke kira da “biɗa.”
A
ɓangare guda kuma, binciken ya fahimci cewa, Bahaushe ya riƙi tanadi a matsayin
hanyar bunƙasa tattalin arziƙi. A ƙarƙashin 2.2.2 an ga bayanin cewa, akwai
lalurorin Bahaushe da dama da ba za su gudana yadda ake so ba, ba don dalili na
tanadi ba. Da taimakon dabarun tanadi, sai Hausawa (musamman masu ƙananan ƙarfi)
su samu damar gudanar da lalurorinsu baki alekum. An fahimci cewa, biɗa da
tanadi Ɗanjuma ne da Ɗanjummai a gwagwarmayar Bahaushe ta bunƙasa tattalin arziƙinsa.
Jadawali 2:
S/N
|
Qumshiyar Tambayoyi
|
Eh
|
A’a
|
1.
|
Shin
kina/kana sana’a?
|
65(74.71%)
|
22(25.29%)
|
2.
|
Shin
kana/kina da ra’ayin adashe?
|
65(74.71%)
|
22(25.29%)
|
3.
|
Shin
kana/kina da ra’ayin asusu?
|
63(74.41%)
|
24(27.59%)
|
4.
|
Shin
kana/kina da ra’ayin ajo[12]?
|
34(40.23%)
|
52(59.77%)
|
5.
|
Shin kana/kina
da ra’ayin aikin gayya?
|
63(72.41%)
|
24(27.59%)
|
Madogara: Tsararriyar
Tambayau
A
lamba ta farko na jadawalin da ke sama, za a iya lura da cewa, 65 daga cikin waɗanda
suka amsa wannan tambayar suna da sana’a. Wannan ya yi daidai da kashi 74.71
cikin 100 (74.71%). Waɗanda ba su da sana’a kuwa, sun kai 22, wanda ya yi daida
da 25.29%. Haƙiƙa wannan sakamako ya ci karo da hasashen wannan bincike. A
hasashen binciken, a yanzu Hausawa matasa ɗaliban jami’a sun yi watsi da
nau’o’in wasu sana’o’i kwata-kwata. Duk da haka (kasancewar wannan adadi na
masu sana’a), an kauce wa turbar rayuwar Hausawa ta asali a ɓangaren biɗa da
tanadi.[13]
A
lamba ta 2 na cikin jadawali na 2 da ke sama, mutane 65 (74.71%) sun nuna cewa
suna da ra’ayin adashe. Sauran 22 (25.29%) kuwa ba su da shi. Ba abin mamaki ba
ne a samu raguwar adadin al’ummar da ke da ra’ayin adashe musamman da yake
hanyoyin tanadi na zamani sun yawaita a yau. A lamba ta 3 cikin jadawali na 2
da ke sama kuwa, mutane
63 (74.41%) na da ra’ayin asusu. 24 kuwa, wato kashi 27.5 cikin ɗari ba su da
wannan ra’ayi. Ke nan dai mafi yawan ɗaliban suna da ra’ayin amfani da wannan
tsohuwar dabara ta tanadi har zuwa yau. A bin lura a nan shi ne, asusun na iya
kasancewa a zamanance (misali amfani da banki da sauransu).
Lamba
ta 4 a jadali na 2 da ke sama, na nuna cewa 34 (40.23%) ne kaɗai ke da ra’ayin
ajo. 52 kuwa, wato kashi 59.77 cikin ɗari ba su da wannan ra’ayi. A hasashe, za
a iya tunanin ko wannan ya samu ne sakamakon raguwar danƙon zumunci? Yayin da
aka yi la’akari da lamba ta 5 a jadawali na 2 da ke sama, za a tarar da abin ba
haka yake ba. Dalili kuwa shi ne, 63 daga cikinsu (72.41%) na da ra’ayin aikin
gayya. Waɗanda ba su da wannan ra’ayi 24 (27.59%) ne kawai. Dangane da aikin
gayyar ma, za a iya fahimtar raguwar ra’ayi yayin da aka kwatanta da
zamantakewar Bahaushe a da. A wancan lokaci, aikin gayya na kowa da kowa ne
cikin Hausawa.
Jadawali 3:
S/N
|
Items Statement
|
Eh
|
Ina Kokonto
|
A’a
|
6.
|
Shin kana/kina son sana’a fiye da aikin gwamnati?
|
63 (72.41%)
|
13 (14.15%)
|
11 (12.64%)
|
7.
|
Shin kana/kina ganin darajar masu sana’a sama da
ma’aikatan gwamnati?
|
43 (49.42%)
|
22 (25.29%)
|
22 (25.29%)
|
8.
|
Shin kasancewar mutane sun fi son aikin gwamnati
kan sana’a a yau na da nasaba da kasala?
|
47 (54.02%)
|
21 (24.14%)
|
19 (21.84%)
|
9.
|
Shin kasancewar mutane sun fi son aikin gwamnati
kan sana’a a yau, na da nasaba da ɗagawa/girman kai?
|
34 (39.06%)
|
17 (19.54%)
|
36 (41.38%)
|
10.
|
Shin kasancewar mutane sun fi son aikin gwamnati
kan sana’a a yau, na da nasaba da halayyar mutane na ɗaukar bashi?
|
45 (51.72%)
|
10 (11.49%)
|
32 (36.79%)
|
11.
|
Shin kasancewar mutane sun fi son aikin gwamnati
kan sana’a a yau, na da nasaba da da ƙarancin ilimin kasuwanci?
|
46 (52.87%)
|
15 (17.24%)
|
26 (29.79%)
|
12.
|
Shin kasancewar mutane sun fi son aikin gwamnati
kan sana’a a yau, na da nasaba da rashin jari?
|
63 (72.42%)
|
9 (10.34%)
|
15 (17.24%)
|
13.
|
Shin kana/kina daga cikin masu fahimtar cewa,
tattalin yana raguwa a tsakanin Hausawa?
|
53 (60.92%)
|
21 (24.14%)
|
13 (18.94%)
|
Madogara:
Tsararrun
Tambayoyi
A
lamba ta 6 na jadawali na 3 da ke sama, mutane 63 (72.41%) sun fi son sana’a
sama da aikin gwamnati. 11 (12.64%) kuwa sun fi son aikin gwamnati sama da
sana’a. Su kuwa sauran 13 (14.15) ba su ɗauki matsaya ba. Wannan sakamako ya saɓa
wa hasashen binciken. Ganin cewa matasa Hausawa da dama da suka yi zurfin
karatun boko (har zuwa matakin jami’a) sun fi karkata kan aikin gwamnati. Wannan
ya sa tunanin takardar a farko ya kasance cewa “matasa Hausawa ‘yan jami’a sun
fifita aikin gwamnati kan sana’o’i.” Wannan sakamko na nuna cewa, matasan na
karkata zuwa aikin gwamnati ne bisa wasu dalilai na daban, amma ba don sun fi
son sa sama da sana’a ba. Wannan kuwa ya so ya yi daidai da sakamkon da aka
samu a lamba ta 7 ƙarƙashin jadawali na 3. A nan an fahimci cewa 43 (49.42%) na
ganin girman masu sana’a sama da masu aikin gwamnati. 22 (25.29%) kuwa sun fi
ganin girman masu aikin gwamnati sama da masu sana’a. Su kuwa ragowar 22
(25.29%) ba su da matsaya dangane da lamarin.
Lamba
ta 8 a jadawali na 3 da ke sama na nuna cewa, 47 (54.02) daga cikin mutanen
wasu na da ra’ayin cewa, gujewa sana’a tare da burin sai an yi aikin gwamnati
na da alaƙa da kasala. Wannan kaso kuwa shi ne mafi rinjaye, domin 21 (24.14%)
daga cikinsu ba ɗauke ɓangare ba. A dalilin haka, mutane 17 (21.84%) ne kaɗai
suke da koma bayan wannan ra’ayi.
A
ɓangare guda kuwa, binciken ya nuna cewa son aikin gwamnati da guje wa sana’a
ba a kodayaushe ba ne ke da alaƙa da ɗagawa/girman kai. Za a ga hakan ƙarƙashin
lamba ta 9 cikin jadawali na 3 da ke sama inda mutane 36 (41.38) na ganin babu
wannan alaƙa. Mutane 34 (39.06%) ne suke da saɓananin wannan ra’ayi. Sauran 17
(19.54%) kuwa ba su ɗauki matsaya ba.
A
lamba ta 10 da ke jadawali na 3, mafi yawan mutanen sun nuna cewa, ɗaukar bashi
wurin masu sana’a ko kasuwanci na daga dalilan da suke hana matasa a yau shiga
harkokin sana’o’i da kasuwanci. Masu wannan ra’ayi sun kai 45 (51.72%). Masu saɓanin wannan ra’ayi su 32
(36.79%) ne. Sauran 10 (11.49%) ba su karkata ko’ina ba.
Mutane
46 (52.87%) na da ra’ayin cewa, ƙarancin
ilimin kasuwanci na daga cikin abin da ke tilasta wa matasa gudun harkar. Kamar
yadda yake ƙarƙashin lamba ta 11 da ke jadawali na 3, mutane 26 (29.79%) ne
kacal ba su aminta da wannan hasashe ba. Sauran 15 (17.24%) kuwa, ba su zaɓi
matsaya guda ba.
A lamba ta 12 da ke jadawali na 3, mafi rinjayen
mutanen sun nuna “rashin jari” a matsayin ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke
janyo matasa na guje wa kasuwanci. Masu wannan ra’ayi sun kai 63 (72.42%). Waɗanda
suke da saɓanin ra’ayin su 15 (17.24%) ne kacal. Sauran 9 (10.34%) suna kokonto.
Masana da manazarta sun daɗe suna tattauna wannan batu na rashin jari a
matsayin cikas ga bunƙasar sana’o’i da kasuwanci. Wannan ne ma dalilin da ya sa
a Nijeriya gwamnatoci a matakin ƙasa da jaha da ƙananan hukumomi ke fito da
tsare-tsaren tallafa wa matasa domin fara kasuwanci.
Sakamakon
da ya zo a lamba ta 13 da ke jadawali na 3 ya nuna cewa, mafi yawan waɗanda
suka amsa wannan tambaya na da fahimtar cewa, “tattali” na raguwa tsakanin
al’ummar Hausawa. Masu wannan fahimta sun kai 53 (60.92%). Mutane 13 (18.94%) ne kacal ke da fahimtar da ta saɓa wa
wannan. Ragowar 21 (24.14%) kuwa, ba su ɗauki matsaya ba.
5.0
Kammalawa da Shawarwari
Wanda
ya tuna bara bai ji daɗin bana ba! A baya-bayan nan, rubuce-rubuce na ƙara
yawaita dangane da taɓarɓarewar ɗabi’un Bahaushe. Daga ciki kuwa har da abin da
ya shafi biɗa da tanadinsa. Rubuce-rubucen masana da manazarta daban-daban a
kan wannan batu na ɗaukar salon “Allah wadaran naka ya lalace, in ji ɓauna da ta
ga shanun noma.” Duk da cewa rayuwar Bahaushe ta samu sauye-sauye da dama,
wannan bincike ya fahimci cewa, har yanzu akwai Hausawa da yawa da ke riƙe da
al’adar biɗa da tanadi na bakin-rai-bakin fama. Da ma dai “ba a taru an zama ɗaya
ba!” Sakamakon binciken ya nuna cewa, an samu koma baya dangane da riƙo da sana’o’i
da kasuwanci a tsakanin Hausawa. Dalilan da suka jawo hakan kuwa sun haɗa da
matsalar jari da rashin ilimin kasuwanci tsakanin matasa da kuma yawan karɓar
bashi da masu sayen kaya ke yi. A ƙarshe, sakamakon binciken ya tabbatar da
cewa, al’adun biɗa da tanadi sun yi rauni a tsakanin Hausawa. Wannan kuwa
babban gyambo (miki) ne ga sha’anin tattalin arziƙinsu. A bisa abubuwan da
binciken ya nazarto, an sami damar fito da shawarwarin da ke biye:
1. Bayan
ƙoƙarin da gwamnatoci ke yi dangane da koya wa matasa sana’o’i da kuma ba su
tallafi a matsayin jari, ya kamata a samu sa hannun ɗaiɗaikun jama’a da ƙungiyoyi
a cikin al’umma. A kuma samu ƙarin faɗakarwa da wayar da kai game da
muhimmancin sana’a da kasuwanci. Za a cimma wannan manufa ta hanyar haɗa ƙarfi
tsakanin gwamnatoci da makarantu da malaman addini da ƙungiyoyi da ma ɗaiɗaikun
jama’a, musamman masu faɗa a ji.
2. “Tun
ran gini tun ran zane…” Iyaye su riƙa tarbiyyantar da ‘ya’yansu kan tafarkin
tattali da neman halali. Da haka za su taso da ra’ayi da fasahar biɗa da
tanadi.
[1]Sani da Umar, (2008: 19) sun
rawaito Yahaya, (1988) da Musa, (2013) da kuma ALS, (2015), duk sun nuna cewa,
ana rubutun Ajami ne ta hanyar amfani da harrufan Larabci. Rubutun boko kuwa,
ana amfani da harrufan Romanci ne. A taqaice, an sami waxannan nau’o’in rubutu
bayan cuxanyar Hausawa da baqin Larabawa da kuma Turawa.
[2] Sabo Ibadan babban misali ne na
mazaunin Hausawa da ya kasance ba a qasar Hausa ba.
[3] A tarihance, al’adun da suka shafi
kara da taimakon juna na “mu gudu tare mu tsira tare” na matuqar taimaka wa
tattalin arzikin Hausawa. Al’adun da suka shafi xaure da xauke da aro da
gudummuwa (da makamantansu) sun daxe suna tallafa wa tattalin arzikin Hausawa.
Ta hanyarsu ne ake rufa wa juna asiri.
[4] A hirar da aka yi da shi, ya
tabbatar da cewa: “Kowane gidan Bahaushe a da akwai sana’a. Wasu gidajen ma
akwai sana’o’i sama da guda, sannan kowa na yi. Babu wanda yake zaman banza.”
[5] An samu wannan bayani daga
madogara gamsasshiya wato UDUS Web Team, (2019).
[6] Kalma xaya ce aka tarar da tana da
nauyi musamman ga xalibai ‘yan aji xaya. A bisa wannan dalili aka yi mata xure
da ke xauke da bayanin ma’anar kalmar. Kalmar ita ce “ajo” da ke tambaya mai
lamba ta 4 a jadawali na 3.
[7] Wannan kuwa ya shafi abin da al’ummar
ta riqa a matsayin arziqi. Yana iya kasancewa tsabar kuxi ko kadara ko yawa
‘ya’ya da mata ko kuma tarin amfanin gona.
[8]Faruk,
(2007) na da irin wannan ra’ayi, inda ya bayyana cewa: “... kalmar ta ‘bixa’
kalma ce da Hausawan yankin qasar Sakkwato da Kabi da Zamfara da ma wasu
garuruwa da ke qarqashin Yammacin qasar Hausa irin su Katsina da wani yanki na
Jamhuriyar Nijar.”
[9] A vangare guda kuwa, yana da kyau
kada a mance cewa, ba a fannin tattalin arziqi ba ne kawai ake samun bixa.
Rayuwar Bahaushe gaba xaya (kamar ta sauran al’ummu) na cike da bixa. Wasu daga
cikin misalan bixa a Bahaushiyar zamantakewa su ne:
a.
Bixar
magani.
b.
Bixar
mata.
c.
Bixar
ilimi.
d.
Bixar
mulki/sarauta.
e.
Bixar
buwaya.
[10] A yau ana kasuwanci ba sai
gaba-da-gaba ba. Ana iya yin odar kaya daga wata uwa duniya ta intanet. Poon,
da Swatman, (2005: 7) sun rawaito cewa: “Internet use among small businesses
has recently become a popular topic for researchers in the fields of
Information Systems and Entrepreneurship.” Fassara: “Amafani da intanet ya zama
wani fitaccen lamari (batu) ga manazarta a fannin ilimin kimiyyar intanet da na
kasuwanci.”
[11] Masu sana’ar gwari na xora wa
manyan motoci tumatur da albasa da tattasai da saunsu, daga arewacin Nijeriya
zuwa kudanci. Haka ma masu sana’ar kara (sayar da dabbobi). A taqaice ke nan,
wannan ci gaba na zamani ga bixa da tanadin Bahaushe ya taimaka matuqa ga
bunqasar tattalin arzikinsa.
[12] Wannan ya shafi irin gudummuwa da
ake bayarwa (musamman mata) yayin biki. Wacce aka kawo mata ajo za ta rama wa
waxanda suka kawo mata yayin da buki ya same su.
0 Comments
Rubuta tsokaci.