Masamman wannan lokaci na 'social media', wasu matan dalilan da suke sanya su su riƙa hira da wasu mazan kenan. Kuma in suka saki jiki da su to tabbas za su riƙa gaya musu duk matsalolinsu na gida don samun kawar da damuwar da take ƙirazansu. Ba wai suna neman mazan su taimaka musu da wani abu ba ne, kawai so suke a...

Kundin Ma'aurata - 7: Ka San Matsalarka?

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Kana ganin duk abin da ya wuce ya riga ya wuce, dawowa da shi kuma naci ne, tunda an riga an tattauna shi, har ka kawo mafita, kamata kuma ya yi a kalli gaba, to a daidai wannan lokacin da ba ka son a yi maganar abubuwan da suka gabata, da wahala ka kawo batun da za ku tattauna kai da iyalin a cikin gida, kana jira ne ita ta kawo da kanta, ƙila ma ba ka son magana a lokacin, alhali ita kuma ba mai fita ba ce, kullum tana cikin gida, zai yi wahala ta samo wani batu, in ma akwai shi to za ka taras ma'aikaciya ce ko mai fita kasuwanci, ita ma'aikaciya ba za ta so ta riƙa zuwa da zantuttukan wurin aikinta gida ba saboda sanin dabi'ummu na kishi, kar wata rana ta fado abin da zai raba ta da aikin gaba daya, ita kuma 'yar kasuwa a tsakanin mata duk abin da za ta dauko za ka riƙa ganin gulmammakin mata ne, in ma ta fara za ka ce kai ba ka son ƙananan maganganu, kai kuma ba za ka kawo manyan ba.
.
Da za ka bar ta ta fi son ta dauko abubuwan da suka gabata a baya, in ta gama ta fara dauko wadanda take ganin za su iya faruwa, in dai kana sauraronta, kana dan jefa magana daya biyu shi kenan, za ka ga ƙaunarka a zuciyarta ta ƙaru, tana yawan son zama da kai, da yin hira a kowani lokaci, matsalar da za ka iya samu ita ce, in fa ba ka gyara lamuranka ba, to za ta zauna da wani ta kuma yi waɗannan maganganun da shi.
.
Masamman wannan lokaci na 'social media', wasu matan dalilan da suke sanya su su riƙa hira da wasu mazan kenan. Kuma in suka saki jiki da su to tabbas za su riƙa gaya musu duk matsalolinsu na gida don samun kawar da damuwar da take ƙirazansu. Ba wai suna neman mazan su taimaka musu da wani abu ba ne, kawai so suke a saurare su, in dai aka yi rashin sa'a ne sai mazan su fara zaton ko ƙaunarsu matan suke yi, da wannan shedan zai sami wuri, kodai soyayya ta shiga tsakaninsu, ko ta saye zuciyarsa ta fara yi masa kallon mutumin banza yana son ya nemi matar aure.
.
Ko shi ya same ta ya yi ta mamakin yadda matar aure da mutuncinta tana soyayya da wasu a waje, duk dai maigidan ya ba da ƙofa, a irin wannan lokacin in ya nemi sanya mata takunkumin yin amfani da kafofin sadarwar, ya sake dauko hanyar bude wata barakar babba, ba wata hanyar gyara kamar ka sami lokaci kai da iyalinka ku riƙa zama kuna musayar hira, in ba za ka iya surutu ba ka saurare ta, in tana magana, shi ya sa wayar salula ta zama musu kishiya, in dai kana kula su, sai ku dauki dogon lokacin kuna fahimtar juna, in ma shawara ka ba ta za ta dauka, in kuwa ba ka sauraronta da wahala ta yi aiki da maganarka komai amfaninta, a banza wani can zai ba ta kuma ta yi amfani da shi dari bisa dari.
.
A taƙaice bayan dogon lakacin da muka dauka kan wannan matsalar ya kamata duk mu dawo kan wasu 'yan kalmomi guda 2.

1) Namiji ko bai iya ba ya koyi yadda zai riƙa zama da iyalinsa yana jin matsalolinsu, ya dena yanke su in suna magana don ya ba su shawarwarin da yake ganin su suka fi dacewa da su, ya gane cewa shurun da yake yi musu yakan gina matsalar da kudi ko ababan alatu samsam ba za su iya magancewa ba, wannan ga mai zaman gida kenan, bare wanda ba a ganinsa sai da daddare inda zai zo ya nemi buƙatar shimfida, ko wanda yake debe kwanaki yana waje in ya dawo kuma ya shiga wata saugar ta daban.
.
2) Ke kuma Hajia ki yarda ki riƙa yi masa hanzari, wani malami ne, aikinsa kenan surutu, wani wa'azi, in ya dawo gida hutu yake buƙata, to bare mai aikin ƙarfi, wani sana'arsa tare da mata yake, ya saba da waɗannan surutan a waje, ke ma mace ce zai ga matsala daya dai za ki kawo masa, ki koyi yadda za ki tafiyar da gidanki, kar ki yarda wani ya bata miki, ko ya zama shi ne ma maigidan, ba zai iya ba ki farin cikin da kike zato ba sai dai ya bata miki gida, namiji kuma a duk inda yake sunansa kenan, in ma kin rabu da wannan wani namijin kuma za ki aura, da irin fahimtar ake iya magance matsalolimmu, kawo duk abubuwan da gida yake buƙata ba ya sayen zuciyar mace, yin biris da namiji da tayar da rigingimu ba sa karya zuciyar namiji, sai ma ya fara tunanin ƙaro wata matar.
.
Ko Ka Tuna Wannan?
Kalmar ba ka taba yin kaza ba a wurin mace abu ne mai sauƙin fadi, amma fa ba shi ɗin take nufi ba, za ka ji wani sa'in ta ce "Ba ka taba kawo kaza ba" ko "Ba ka taba gaya min kaza ba" galibi takan yi wannan furucin ne don sanya ka ka aikata tunda ba shi a cikin tarihinka, amma har cikin zuciyarta ta san ka yi din, mai yuwuwa ka ji ta ce "Mu dai a gidannan ba mu taba cin dambun kifi ba, kullum sai alƙawari amma ka kasa cikawa" shi kuma sai ya ce "Ka ji zancen banza, ina ce nan na kawo muku nama na ce a yi dambu lokaci kaza..." A ƙarshe ta tsaya kai da fata ba a yi haka ba, don ta sami hanyar da za ta yi hira da shi, shi kuma gogan zuciya ta kai masa maƙogwaro, in mai naci ne ya dunga fada kenan, ita kuma ƙila ta tashi ta ba shi wuri.
.
Masamman ma wasu matan da mutunci ya yi musu yawa, sai sun fadi cewa za su kunna maigidan, sun san hanyar da za su bullo masa ya yi ta fada, amma in za ka tuna takan fadi cewa "Kai sam ba ka zama a yi hira da kai" a maimakon ka fahimce ta sai ka ce "Ka ji wai 'sam!' Yanzu me muke yi?" Ko ta ce "Wai kai yaushe za ka sami lokacin kanka ne ka zauna da iyalinka a gida ku dan yi hira?" Gogan naka sai ya ce "Ka ji maganar banza! So kike ni ma na zama kamarki hala? Duk 'yan kwanakinnan ina nake zuwa? A taƙaice dai ba wata fahimtar juna.