Bayanan da muka yi a baya sun keɓu ne da abin da mutum yake ji a zuciya, ko dai soyayya, ko ƙiyayya, ko kishi da dai sauransu. Yanzu bari mu shiga maganar auren kai tsaye, wanda a dalilinsa ne muka yi niyyar karanta wannan dan littafi na KUNDIN MA'AURATA. Da farko tambayi kanka "Wai ni don me zan yi wannan auren?"...

Kundin Ma'aurata - 13: Maza na da Kishi

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Koyaushe maza suka tashi magana sai ka ji sun ce kishi kamar mace, a wannan maganar kamar ana nuna cewa maza ba su da kishi ne, ko kuma kishin nasu bai kai wanda mata suke yi ba, alhali na ga wata da aka harbe da bindiga, aka ce ba ita aka yi niyya ba, saurayin ne, kuskure aka samu, wani kuma ya sa sandar fulani ya yi wa wani na kusa da ni rotsi, da ƙyar aka ceto ransa, an sha samun gayu suna narka wa samari dukan tsiya a kan mace, zan iya tuna wani maƙwabcinmu da ogansa ya ga budurwarsa sai ya kira shi ya ce ya rabu da yarinyar zai yi masa goma ta arziƙi, ya fada masa duk abubuwan da zai ba shi amma yaron ya ƙi.

Nan ne ogan ya yi masa kashedin kora, gami da riƙe masa kudinsa da yake hannunsa, yaron dai ya yi tsayayya, tabbas ya auri yarinyar amma ya ci baƙar wahala, don sai da ya zama abin tausayi, wannan kam shi ne kishi na gaskiya, domin ogan nasa bisa wasu bincike bai da niyyar auren yarinyar, sha'awa kawai ta ba shi, don haka zai yi lalata da ita ya watsar, amma wancan bige-bigen da sare-sare da samari suke yi a kawunansu shi ma ba abu ne mai kyau ba, sai dai ba za a hada shi da wanda mata suke yi ba, duk da mun fadi wasu ayyukan hauka da mata suke yi, wanda sun yi daidai da wanda mazan suke yi, kamar raba mutum da ransa, wanda girman laifin a wurin Allah guda ne.

Sai dai ni maganar da nake yi kamar ƙiyastawa ce ta wurin hankali, mace tana ƙoƙarin ta hana 'yar uwanta ne cin arziƙi tare da ita, amma mijinta nanan a matsayin mijinta, kuma zai ba ta haƙƙoƙinta a matsayin mai ɗakinsa, amma  namiji bai da wannan damar, ko dai ya sami matar ne ko ya rasa gaba daya, to shi a har kullum rashin yake kallo, masamman ma in ya kasance shi ya fara nema, ka ga mace rabawa za a yi, shi kuwa namiji rasawa zai yi.

Duk da haka shi ma wannan tsabar hauka ne kawai, akwai dai kishi da muslunci ya yi umurni da shi ga namiji, kamar ka killace iyalinka, ka hana wasu su kusance ta ta kowace hanya, matuƙar hakan bai fita da'irar halasci ba, duk dai shari'a ƙoƙari take yi ta hana alfahasha da abin ƙi, mace mumina ta tsaya ga mutun guda, yadda za a yi maganin alfahasha, shi kuma zai iya hana mata 4 lalata da wasu mazan a waje, sai shari'a ta matsa matuƙa a kan dole namiji ya zama mai kishi, dole ya tsaya ƙyam wajen ganin iyalinsa ta zama kamammiya, ta kuma taimaka masa ta wurin nuna wa matan irin suturan da za su iya sawa a waje, da irin adon da za su iya bayyanawa, hatta ƙamshinnan sai da aka kebe shi da gida, domin abubuwa uku suka fi ta da sha'awar maza a adon mace.

Za ka taras magabata sun riƙa janyo hankulan 'ya'yansu mata da waɗannan abubuwan, da cewa kar su dena yin su a gidajen aurensu, wato "Tozali, turare da lalle", na zauna a wata ƙasa ta Larabawa na ga da lalle ne ake gane matar aure, don ita za ta yi wa mijinta, mace mai sanya turare ta fita kuwa muslunci ya yi kakkausar magana a kanta, inda ya sufanta ta da mazinaciya, sannan ya hana ta cakuduwa da maza, ba wai don ba ta da imani ba, don gaba dayanta ƙawa ce, in wani ba ya sha'awarta wani ya ga abin da ya gani, a taƙaice dole maza su yi kishi don haka shari'a ta tsara.

Bayan Muƙaddima
Bayanan da muka yi a baya sun keɓu ne da abin da mutum yake ji a zuciya, ko dai soyayya, ko ƙiyayya, ko kishi da dai sauransu. Yanzu bari mu shiga maganar auren kai tsaye, wanda a dalilinsa ne muka yi niyyar karanta wannan dan littafi na KUNDIN MA'AURATA. Da farko tambayi kanka "Wai ni don me zan yi wannan auren?" Tabbas akwai dalilai masu dama da suke sa mutum ya yi sha'awar aure, in ka ce za ka lissafo wani zai ce maka ba ka ambato dalilin da ya sa ya yi nasa auren ba.

1) Akwai wanda sha'awar macen ta lullube shi, wace ita ce babban dalilin da ya sa yake sha'awar ganin ya yi aure.

2) Wani haihuwa ke janyo hankalinsa, masamman idan ya ga sa'o'insa wannan yana da 'ya'ya biyu wancan 3 shi bai da kowa.

3) Wani kuwa in  ya kalli yadda mu'amular ma'auratan take ne, sai ya ji ta burge shi, shi ma sai ya yi ƙoƙarin ganin ya sami tasa.

4) Wani tsokanar da abokansa suke masa take sawa ya yi zuciya ya fara nema.

5) Akwai wanda zai yi tunanin yana buƙatar magaji, ba kuma hanyar da zai samu sai ta aure.

6) Wani tausayin yarinya kawai yake ji, masamman in ya ga halin da take ciki.

7) Wani yarinyar ta ce tana son sa shi kuma ya miƙa wuya.

8) Wani sha'awar yarinyar ya yi, a dalilin wani abu na ƙwazo da ta yi, ko fice a wani fanni, ko danganen mahaifinta na kudi ko sarauta ko shuhura da dai sauransu.

9) Wani mahaifansa ko 'yan uwansa ko abokai suka zabo masa suka ce ya je ya nema, sai kuwa ya jarraba.

10) Wani mummunar gaba ce take rikidewa ta koma soyayya ta ƙare da aure.

11) Wani zama wuri guda ne soyayyar take shiga, kamar karatu ko aiki ko mu'amalar kudi.

12) Wani hanyoyin sadarwa ne na zamani suka hada su, a ƙarshe aka ƙare da aure.

13) Wani natsuwar macen da kamun kanta da addini ya sa aka yi sha'awarta.

14) Wani don tarbiyar 'ya'yansa yake aurowa. Haka dai abin yake.