Kirsimeti suna ne na wani biki da gungun mabiya addinin Kiristanci suke yin sa a watan ƙarshe na kowace shekara tun bayan da Ubangiji ya ɗauke Isah Ɗan Maryam (A.S) izuwa sama. Bisa tafarki na imaninsu, wannan gagarumin biki suna yin sa ne a matsayin ibada. A bisa nazari kan yadda lamuran gudanar da bikin yake wakana ne, marubucin wannan waka ya yi ƙoƙarin fito da wasu ababe muhimmai da ake gudanarwa a yayin shagalin wannan bikin Kirsimeti na ibada. Waƙar ainihi an rubuta ta ne a shekarar 2018 kuma akwai yiwuwar ita ce waƙa ta farko da wani ɗan Arewa Musulmi ya yi a kan shi wannan biki na Kirsimeti don nuna yadda ake yin sa da kuma girman matsayinsa ga mabiya addinin Kirista.
KIRSIMETI
Musaddam Idriss Musa
07067132948/09063064582
Yau ake yin kirsimeti,
Duk gari ya ɗauki sauti,
Na bugun ganga a coci,
Rabbana kai ke da bawa.
Taro, murna da ihu,
Na bikin saukar Masihu,
Wanda Rabbi ya ba wa ruhu,
Da yake iya ta da gawa.
Yau coci rawa da juyi,
Fara'a kowansu ke yi,
Ga rawarsu nutse a layi,
Bakunansu suna ta sowa.
Gaba can za ka hangi fasto,
Ɗan fari tas ga shi ƙato,
Tumbinsa yana ta reto,
Na rawar da yake ta yowa.
Kirsimeti bikin Kirista,
Gasu new year har da Easter,
Duk sukan yi su babu mita,
A duk sanda su kai isowa.
Musulmi kuwa na su Idi,
Ran hawa doki da sirdi,
Sarki kan fito rangadi,
Jama'ar sa yai zagawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.