Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata – 5: Maza Ba Su Da Alkawari


Kenan dole ya samo muku duk abin da kuke buƙata, tun daga abinci, matsuguni, sutura, da sauran ababan biyan buƙata. Waɗannan bai san su ba a baya don bai da mata, ko kuma rabin haka yake yi don matarsa guda. Yanzu kin...

Kundin Ma'aurata – 5: Maza Ba Su Da Alkawari
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Sukan ce, kafin ya aure ki, ko gyaran murya kika yi sai ya tambaye ki "Lafiya kuwa?", to bare ya tabbatar cewa da gaske ne ba ki da lafiyar, duk wata kula zai ba ki, in wata damuwa kike da ita masamman wace ta shafi kudi, sai ya tambaye ki nawa zai ishe ki? To bare 'yan kayan kwalliya da turare, yana son ganinki fesfes koda yaushe, ga maganganu masu dadi, wani sa'in ma har da santi, kullum burinsa ya zauna kusa da ke.
.
In ma ba ki cika damuwa ba sai ya nemi ya riƙa daƙuna ki, duk abin da kika fadi kamar doka ne, in ma yana da mata sai ki riƙa ganin kamar ke kike seta gidan nasa yadda kike so, don har shawarwari za ki riƙa ba shi ga yadda zai yi, amma ba a nan gizo yake saƙar ba, da zarar kin shugo hannu, ya samu ya kawar da duk abubuwan da yake hange daga nesa sai ki ga kamar wani mutum kika aura ba shi ba.
.
Wani sa'in ma sai ki riƙa gani kamar tun da Allah ya yi ki ba ki taba saninsa ba, komai nasa ya canja, dauwamammiyar fara'ar da kika saba gani a fuskannan tasa ta bace bat, da ya shugo gida ya ci abinci sai ya ce hutu yake so, ma'ana kar a dame shi da surutu, in ya farka ya yi wanka kuma sai ki ga yana ƙoƙarin fita, ke ba ki canja komai ba, amma shi ya zama wani abu daban, wani lokacin ki riƙa tambayarsa ko kin yi masa wani abu ne?
.
Don kamar haushinki ma yake ji, wani ya ce ba komai wani kuma kallonki kawai zai yi, to ba ki ma ga fuska ba bare ki ce kina son abu kaza, ke da kullum ake rarrashinki yanzu ke ce za ki koma kina ba da baki, dan abu kadan a cikin gida fada, mace kam a irin wannan yanayi, masamman budurwar da ba ta taba yin aure ba, koda kuwa ta yi ta tambadewarta da maza a waje na tsawon shekaru dole abin ya rikice mata.
.
Wace ta taba aure kuwa koda na tsawon shekara daya ne tal, ta san kayanta kuma ta san yadda za ta tafi da shi, zahirin gaskiya ba sauyawa ya yi ba, ba kuma ƙinki yake yi ba, ƙila a rayuwarsa ma ba wanda yake so kamarki, kawai dai kowa ne a tsakaninku yana da hanyar da yake nuna tasa soyayyar, namiji kafin aure ƙoƙarinsa kawai ya shugo dake, kina shiga kuma sai tunaninsa ya koma yadda zai iya gudanar da sha'anin gidansa, ƙila a da abinci ba shi ake yi, yanzu ba kansa ba hatta ke kina ƙarƙashinsa ne, a zuciya irin tasa kuwa bai son wani ya san halin da yake ciki a gidansa.
.
Kenan dole ya samo muku duk abin da kuke buƙata, tun daga abinci, matsuguni, sutura, da sauran ababan biyan buƙata. Waɗannan bai san su ba a baya don bai da mata, ko kuma rabin haka yake yi don matarsa guda. Yanzu kin shugo abu ya ninku, dole ki rasa samun lokacinsa, in ma zai shugo ne a gajiye zai shugo, a tunaninsa ke ba yarinya ba ce za ki jinjina wa wahalar da ya debo a waje, ki bar shi ya huta, in hakan ya yi karo da ke kuma kina jira ya dawo ku sha soyayya kamar yadda kika saba a baya sai ki ga an fara tunanin canjawa ya yi.
.
Alhali a zahirin gaskiya rayuwar ce ta sauya zane ba shi kansa ba, in kuma ana neman zaman lafiya sai a dube ta yadda take a yi wa juna hanzari, in kuma maganar son kusanta ne yanzu ai an gama da wannan, zahiri kawai za a fuskanta, sai dai kuma ke kanki ba ki rasa abin da za a iya dubawa ba, in kin tuna ba kya fito masa sai kin yi goge-goge kin shafa ababan shafawa, ga turare mai ƙamshi yana tasowa a hankali, murya kuwa ki ƙyale ta da gangan yadda za ta jawo hankali.
.
Wato dai kin gama cika shika-shikan sha'awa, yanzu kuwa yana ganinki a kowa ce sifa, wani sa'in ma kina cikin kicin ko ƙoƙarin tsabtace ban-ɗaki, kin ga akwai bambanci, sannan uwa uba kun saba da juna, ba wani zancen bege don kuna wuri guda, dole a dan sami 'yan canje-canje, wanda yake son ya mallaki abu dole ya matsa don kar ya subuce masa, hakan ba ya nufin cewa ya fi wanda yake hannunsa ƙima da daraja, abin da muka kasa ganewa kenan.
.
Namiji fa a dabi'arsa ko wajen mu'amalar cikin gida in abubuwa suka kicime masa yakan zabo wadanda suka fi damunsa ne, ko masu wahalar warwarewa ya fara da su, kin ga kuwa yana da buƙatar aiki da ƙwaƙwalwa sosai matuƙa, wani sa'in ma yakan tara matsalolin ya yi kamar bai damu da su ba, sai ya dawo gida ya fara sassaƙa yadda zai yi da su, kenan in mai-ɗakinsa ta zo da hirarrakinta za ki ga hankalinsa 5% ne kadai yake tare da shi, kusan 95% duk yana can inda yake ƙoƙarin nemo mafita, in mace za ta yi wa kanta adalci sai ta rabu da shi sai ta ga sararin tattauna wasu lamuran kuma, don in ta matsa masa ms yana iya fada ta da fada, ko ya yi ƙoƙarin fita ba a lokacin da ya yi niyya ba don ya nemo wa kansa mafita.
.
Yana samun abin da yake so nan take za ki ga ya warware, sai fara'arsa ta dawo, ya nemi yin magana da uwargidan, ita kuma ƙila ta riga ta fusata a sakamakon watsi da ya yi da ita a baya, yanzu ne ya ga lokacin da zai yi magana da ita, in ba a yi sa'a ba sai ta tashi ta ba shi wuri, ko kuma ita ma ta yi watsi da shi, shi ma ya ji in da dadi, in kuwa bai sami yadda zai warware matsalarsa ba sai ya koma ga waya, ko talabijin, ko ma ya fuskanci 'yan diyoyinsa ƙanana, ta yadda za su wanke masa ƙwaƙwalwarsa don ta komo sabuwa, in kika ga ba ki da lokacinsa a wannan sa'in turo masa yaransa a tsakankani sai ki shugo.

Post a Comment

0 Comments