Harshe
abu ne mai rai da masanansa suka tabbatar da cewa, yana rayuwa yana mutuwa.
Yadda duk rayuwar ɗan Adam ke
fuskantar barazanar haɗurra daban-daban
haka harshe ke fuskantar su.[1]
Harsunan mutanen duniya makaman yaƙi uku suke da su:
(a) harshe da (b) adabi da kuma (c) al’ada. A ɗan nawa nazari, al’ada ta haifi
harshe domin a cikinta yake farautar kalmomin da za a yi magana mai ma’ana.
Haka kuma, da babu al’ada, kasuwar adabi ta gama ciniki, domin da bazarta adabi
ke rawa. Idan aka ce harshe na masassara, dukkanin waɗannan abubawa uku
zazzaɓin ya shafe su.
Don haka, ƙoƙarin tantance ‘Bori’ da ‘Ruƙiyya’ a matsayin
addini ko al’ada wata alama ce ta nuna cewa, kasuwar ‘Bori’ ta fara ban kwana a
alƙaryu
da birane…
Mene Ne Bori?: Fashin
Baƙin Ma’anarsa Cikin Taskar Harshe, Adabi Da Al’ada
Aliyu Muhammadu
Bunza
Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
Waya: 08034316508
Takardar da aka gabatar a taro na musamman da Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya da Mutuntar ɗan Adam (CSNLF) Jami’ar Bayero Kano ta shirya mai taken
BORI ADDINI KO AL’ADA ranar Talata 16 ga watan Yuni 2015 a harabar Cibiyar,
mazaunin dindindin.
Tsakure
Daga cikin daɗaɗɗun al’adun
gargajiyar Bahaushe, babu wadda ta kai ‘bori’ tagomashin bincike ga masana
al’adu na duniya. Masana al’adun Hausa na cikin ƙasar Hausa, da
wajen ƙasar Hausa, sun ce wani abu a kan bori. Aikin da ya fi
daɗewa shi ne
(Tremeane, 1915). Bayansa an samu ayyuka masu ma’ana sosai na fitattun muƙalu. An yi
fitattun kundayen PhD huɗu musamman kan
bori; (Greenberg, 1946) da (Conant, 1960) da (Constantini, 1972) da (Gobir,
2012). Babu marena ga waɗannan ayyuka, amma
ma’anar bori ta kasa fitowa ƙarara a ciki. Bori ya samu taron
dangi na masanan duniya a Ingila, wanda (Lewis, 1991) ya wallafa da taken Women
Medicine: The Zar-Bori Cult in Africa and Beyond. A tsanakin nazari,
masanan sun yi takin saƙa ga kai ga tsayayyar ma’anar ‘bori’. Wannan ɗan bincike, ya yi
kakkaɓan gara ga
ayyukkan da suka gabata, kana ya yi dabarar kallon ‘bori’ a ƙarƙashin gurabu uku
na nazarin Hausa; harshe da adabi da al’ada. Bayan an jinjini nauyin bori a ƙarƙashin kowane
gurbi, aka yi tankaɗe da rairayar
tsayar da ma’ana ɗaya gawurtacciya.
Bori dai a nahawun ma’ana, kalmar ta ci sunanta. A farfajiyar adabi ba ta tsallake ma’anar ‘wasa’ ba. A kadadar
al’ada, ta kasa yin canjanras da ‘addini’ ta yi taho-mu-gama da ‘aƙida’ ta ‘yan
tsirarrun Hausawa. Babu shakka, yarda da samuwar Iskoki, da yi musu hidima,
al’ada ce da ta game duniyar mutane farfarunsu da babbaƙunsu. Duk da haka,
hulɗa da Iskoki da
sunan ‘bori’ Bahaushe ya kaɗaita da ita a farfajiyar duniyar mutane. Ba don
gudunmuwar addinin Musulunci da Larabawa ba, da borin Bahaushe bai tsallake
bukukuwan matankan rayuwar Bahaushe ba (aure, haihuwa da mutuwa).
Gabatarwa:
Harshe abu ne mai
rai da masanansa suka tabbatar da cewa, yana rayuwa yana mutuwa. Yadda duk
rayuwar ɗan Adam ke
fuskantar barazanar haɗurra daban-daban
haka harshe ke fuskantar su.[2]
Harsunan mutanen duniya makaman yaƙi uku suke da su:
(a) harshe da (b) adabi da kuma (c) al’ada. A ɗan nawa nazari, al’ada ta haifi
harshe domin a cikinta yake farautar kalmomin da za a yi magana mai ma’ana.
Haka kuma, da babu al’ada, kasuwar adabi ta gama ciniki, domin da bazarta adabi
ke rawa. Idan aka ce harshe na masassara, dukkanin waɗannan abubawa uku
zazzaɓin ya shafe su.
Don haka, ƙoƙarin tantance ‘Bori’ da ‘Ruƙiyya’ a matsayin
addini ko al’ada wata alama ce ta nuna cewa, kasuwar ‘Bori’ ta fara ban kwana a
alƙaryu
da birane, a ƙauyuka an yi mata riƙon sakainar kashi,
ana cikin jinya ‘Ruƙiyya’ ta bayyana aka raba wa Hausawa hankali biyu.
Wasu na ganin ‘ya’yan tsatso ɗaya ne, wasu su ce, zumuntar daga gefen uwa ne, wasu
su ce a’a ha - babu kare bin damo, masu sharhin bayin fage na ganin abin duk
dai sabon salon ra’ayi ne cin burodi da aidin. A nawa hasashe, ‘Bori’ zan saka
gaba domin tantance haƙiƙanin ma’anarsa a idon masu bori da
duniyar harshe da adabi da al’adar Bahaushe.
Dabarun Bincike:
A duniyar ilmin
zamaninmu, sai an san nauyin kaya ake jingar ɗaukar su. hankalin wannan ɗan bincike zai
tattara a kan gano mene ne haƙiƙanin bori a idon
Bahaushe da manazarta al’adunsa? Don
haka, makamin bincike na farko shi ne tattaunawa ta musamman da masu bori da
wakilansu da masu sha’awar su da masu kushe su da ‘yan ba-ruwanmu. Ƙofa ta biyu ita
ce, farauto fitattun sassan adabin Bahaushe da kalmar ‘bori’ ta bayyana, a yi
tarken su da sakamakon tattaunawar da aka yi domin rarrabe zare da abawa.
Mataki na uku shi ne, a lalubo fitattun ayyukan ilmi da duniyar nazarin al’adun
‘yan Adam suka tabbatar an yi a kan bori a ga irin shiga da fitar da kalmar
‘bori’ ta yi a ciki da yadda aka lugude ta. Mataki na huɗu shi ne, ga wuta
ga masara, watau a kalli wasan bori a aikace daga masu shi, da masu wasan
kwaikwayo da shi, domin a tanka zaren tunanin abubuwan da suka gabata a kan
abin da ya bayyana a zahiri. Cikin waɗannan matakan, an harari jinsin da bori ya
rinjaya, da shekarun masu shi, da wayewarsu da zurfin karatunsu (na addini da
na zamani), da irin matsayinsu ga al’ummarsu. Bincike ba ya buƙatar keɓe wasu shekaru ko
biyar wata ƙididdigen adadi ko hawa wani ra’i daga ra’o’in al’ada
ko adabi ko harshe, domin kalmar ‘bori’ kaɗai ce ake son a tantance ma’anarta, a gano
shin bori al’ada ne ko addini? Duk da yake an yi ɗan rangadi na can da nan, wannan
bincike dabarun aiwatar da shi, shi ne biyar diddigin masu bin diddigin diddigi
domin diddigance diddigaggen diddigi a kan ma’anar bori a Hausance.
Ƙila-Wa-Ƙala:
A kan komai ake
yin muhawara da sa-in-sa da ɗaɗa juna sani, akwai turken da dole kowa a kan sa zai
dinga mafaka wajen kai hari da garkuwa da shi idan aka darkako shi. Tunanin
masana da manazarta da mu ɗalibai ya bambanta a kan ainihin ma’anar ‘bori’. Wasu
sun kalle shi a matsayin wasan kwaikwayon gargajiya, wai domin iskoki ne ake
kwaikwayo. A ganin wasu, addini ne mai cin gashin kansa domin hidimomin da ke
cikinsa irin na bauta ne da za a yi da sunan addini. Wasu na hangen bori a
matsayin ‘tsafi’, domin matakan neman biyan buƙata da ke ciki
maguzantattu ne. Wasu na kallon bori a matsayin ‘bokanci’ domin ganin masu bonkanci suka fi kowa cin gajiyarsa.
Wannan ba ta hana wasu su kalli bori a matsayin ‘wasannin nishaɗi’ na Bahaushe da
ke da keɓaɓɓun lokutan aiwatarwa. A hangen wasu, bori wata gwamnati ce da mata suka
kafa domin ƙwato haƙƙoƙinsu da bayar da tasu gudummuwa ga al'umma. A ra’ayi na bakwai, wasu na
ganin bori a matsayin ƙullin zumunci tsakanin mutane da mutantani
domin neman agajin juna. Waɗannan ra’ayoyi bakwai su ne ra’ayoyin da
masu bori da manazarta da masu kushewa da na bayan fage suke kai da kawo a kai.
Tuƙe tunanin kowace irin muhawara shi ne gano ma'anar abin jayayya.
Fashin Baƙin Kalmar “Bori”:
Tsarin ginin kalmar 'bori' gaɓa biyu ce, /bo/
/ri/. Furucin sautin gaɓoɓin kuwa dogaye ne,
/boo/ /rii/. Idan aka duba hawa da saukar muryar furucin kalmar, gaɓar farko sama take
/boo/, gaɓa ta biyu ƙasa take /rii/. Ga alama, turken
kalmar bori shi ne /bor/. A biyar diddigin ginin kalmomin Hausa ‘yan gaɓa biyu masu
doguwar gaɓa da hawa da
saukar murya su ne mafi rinjaye a harshen Hausa. Wannan ɗan hasashe na iya
zama wata ‘yar hujja ta cewa[3]
kalmar ‘bori’ Bahaushiya ce a gininta da zubi da tsarinta. A li’irabin suna,
kalmar ‘bori’ ɓoyayyen suna ne
(abstract noun) kuma tsayayye ne (dynamic noun), yakan shiga rigar aikatau idan
kalmar ‘nake’ ta gabace shi.
A tsarin nahawun
ma’ana, ‘bori’ suna ne kuma suna gama gari.[4]
Ta fuskar yawa, kalmar ‘bori’ takan ɗauki awon tilo da jam’i, a mahangar jinsi,
‘bori ’ namiji ne duk da yake ya fi tagomashi ga mata. Kalmar ‘bori’ taƙadara ce wajen karɓar ɗofanen goshi da ƙeya, face a fagen
jinjina jinsi da yawa na masu bori kamar: ‘yan, ɗan, ‘yar da masu, da mai. Misali:
·
‘Yan
bori - jam’i
·
Ɗan bori -
tilo/namiji
·
‘Yar
bori - tilo/mace
·
Masu
bori - jam’i/ maza da mata
·
Mai
bori - tilo/ namiji
Ba abin mamaki ba
ne a ga, a harshen Hausa kalmomin da ke da gaɓoɓin /bo/ da turken /bor/ ‘yan
tsiraru ne ƙwarai. Ga ɗan binciken da na yi, akwai:
·
Bori
·
Bore
·
Bororo
·
Borewa
·
Bobbowa
·
Bobbotai
·
Bobboce
·
Boce
·
Borkono
A harshen Hausa,
‘bore’ wani aiki ne da mai shi ke aikatawa bayan ya fita a hayyacinsa ta kamala
da tunani. Da yawa, za a ga ‘yan bore sun shafe fuskokinsu da baƙin tukunya ko
shuni ko bula, a saka tsumma, a ɗaɗɗaure jiki da igiyoyi a ciro kayan faɗa da artabu ana
rera waƙoƙin fito-na-fito na fitar da
hankali. Da haka za a aikata duk wata ta’asa da ake son a aikata ba tare da jin
wani tsoro ba. A wata fassara wanna boren shi ne zanga-zanga. Abin da za mu
tsinta a nan shi ne, sai dukkan waɗannan abubuwa da muka ambata sun kammala
sannan bore ke zama bore na gaskiya. A fassarar bori ta haƙiƙa, waɗannan abubuwa su
ne ‘bori’.
Idan aka nazarci
kalmar ‘bororo’. Ma’anar ‘bori’ na iya bayyana a ciki. ‘Bororo’ shi ne wani
mikin wuta na girshi ko na ƙwaron ‘Bobo’ (shadare) da zai sauka
a jiki wurin ya tsirar da ƙurji babba zama ɗaya ya kumbure ya ɗuri ruwa ya ƙabure, da an soka
masa wani tsinke kamar allura sai ruwan da ke ciki su yi waje da ƙarfi. Ko ƙurjin maruru ko
bar-ni-da-mugu, ruwa suka ɗuru ciki, suka kumbure, akan ce, a yi sakiya a fitar
da ruwan da suka ja. Kumburin na girshi shi ne irin na ‘bore’ don haka ake cewa
ƙurji
ya ‘bore’, ko zama ɗaya sai ‘borewa’.
Irin ɗibar iska da ruwa
da suke ja, haka nan ɗan bori yake
kasancewa zama ɗaya ya rikice sai
hawan ‘bori’.[5]
‘Bobbowa’ da
‘bobbotai’ wata halayya ce ta fito da ma’anonin bori a sarari. Bobbowa ana samunta
ga raƙumi yayin da yake fitar da ƙoƙiyarsa in yana jin
nishaɗa ko ana artabu da
shi. Za a ga ya zazzago harshensa waje cikin kumfa yana ƙabure shi wata
irin cida mai ban tsoro tana fita bakinsa. Da ya shiga wannan halin masana na
cewa, ya fusata, ko ya firgita ya hau ‘bori’. Idan mutum ne ya shiga irin
wannan hali, rai ya ɓaci, baki na
kumfa, murya ta yi kauri ta shaƙe, magana na fita saɓanin al’adar mai
ita, za a ce, an ji shi yana ‘bobotai’ irin na fitar hankali, watau an shiga
yanayin bori ke nan.[6]
Da kurma ne, za a ce, an ji shi yana cida kamar hadari ko a ce, yana ‘bololloƙai’ kamar an cushe
makwararar ruwan gebe.[7]
A nahawu, kalmar ‘bori’ ita ce wani
abu da ya saɓa wa al’adarsa da
aka saba da ita. Kalmar na wakiltar wani aiki ko wani furuci na fitar hankali
mai motsa rayuwa. A nahawun ma’ana, kalmar ta yi kusa ga kalmar ‘hauka’ sai dai
kalmar ‘hauka’ ta fi ta dogon zamani ga jikin mai ita. A zurfin ma’ana, kalmar
bori da kalmomin bororo da bore da botso da bauri da bocewa da borowa wasu
fassarori ne na faɗaɗa ma’anar kalmar
‘bori’.
Harshen Bori:
Cikin yunƙurin ƙyallaro
daidaitaccen ma’auni na awon ma’anar ‘bori’ dole sai an sa ido ga ‘harshen
bori’. Idan ‘yan bori suna cikin giyar bori sosai, zantukan da ke fita bakinsu
ana ganin ba nasu ba ne, na iskokinsu ne, don haka ake yi wa zantukan suna da:
·
Saɓari
·
Sabbatu
·
Soki-burutsu
·
Batutuwa
·
Maganganu
·
Shirɓace
Saɓari - magana ce maras
ma’ana da ke fita a baki bayan da hankalin mai ita ya fita daga gare shi.[8]
Mai sauraronsa ba ya iya fahimtar ma’anar ta, kuma ko an saurare shi da kyau,
ba a kama haƙiƙanin kalmomin bale a tantance
ma’anarsu.[9]
Ana samun irinsu daga bakunan masu ciwon farfaɗiya bayan sun ɗan tashi kaɗan daga magagin
farfaɗowa.
Sabbatu - kuwa maganganu ne da ake yi
cikin ruɗewa babu tsayayyar
ma’ana da za a kama ciki. Idan ja-in-ja ta tsananta, abokanin husuma na amayo
kalmomi ba da shiri ba cikin zafin raɗaɗin duka ko wata wuya da aka sha, ana ce da
waɗannan lafuza
‘sabbatu’ a harshen bori.[10]
Soki-burutsu - magana ce da za
a ji komai nata ƙarara amma a kasa fitar da ma’anarta nan take saboda
shirmen da ke ciki.[11]
A fagen bori,
maganganu irin na yi wa iskoki kirari da zuga su ana ce da su ‘batutuwa’ domin
ga su da yawa amma kowace magana fuskar da ta dosa daban.[12]
Haka kuma, maganganu ne masu sarƙeƙeniya da juna,
ma’anoninsu na yi wa juna shigar
gizagizai, mai sauraro ya rasa tsayayyar ma’ana. A wata fassara, batutuwa
maganganu ne da sai wanda abin ya shafa zai iya hango ruhin ma’anarsu kai
tsaye. Saɓanin batutuwa,
‘maganganu’ kuwa magana ce da ba ta da kai ba ta da gindi. Ba a fara ta da wani
tushe ba, kuma ba a kai ƙarshen da za a dasa aya ba. Maganganu ne daban-daban
aka tattara wuri ɗaya hahhautsine
babbarkace, shisshirɓace, don haka ake
yi musu suna da ‘shirɓace’.[13]
Idan za a nazarci
harshen bori sosai, musamman a bakin ‘Boboniya’ matar da suka sarƙu da iska na
tsawon kwanaki ba su fice ta ba, za a ji surutan da take suna kai da kawo cikin
waɗannan abubuwa
shida da aka lisafa.[14]
Harshen borin Bahaushe wata fassara ce ta ma’anar bori domin ma’anar harshen
bori ita ce:
Gutsattsarin maganganu da ke fita a bakin
mai bori marasa ma’ana da ba su hau kan kowane irin tsari na magana ba. Da jin
su, za a fahinci, ba a cikin cikakken hankali aka furta su ba. A cikin kowane
harshe aka yi su, ba su da tsrin da za a fahimce su. A koyaushe, ba su tare da
hankali, don haka, hankali ba ya iya kamo ma’anarsu. Mai sauraro da ya ji su,
zai ce; ai wannan magana saɓari ce ko sabbatu ko batutuwa ko soki-burutsu ko
maganganun banza na shirme irin batutuwan gyaran garaya.
Buƙatar bincike gano
ma’anar ‘Bori’ ba yadda ake bori ba. Idan za a saurari maganganun masu bori
lokacin da suka hau bori ko bori ya shige su, za a ga:
1. Shirɓatattun maganganun
da suke yi shi ne bori.
2. Abubuwan da za a
sarɓa cikin batutuwan
da suke yi, su za a fassara da cewa; “bori ya ce, abu kaza”.
3. Da sun daina
soki-burutsun, sun fara maganar da ake fahimta, za a ce; ‘bori ya sake su’.
4. Da sun fara rawa
na faɗuwa a ƙasa, suna birkaɗa jiki irin na
jaki, idan ba su fara ire-iren maganganun ba, borin bai bayyana ba.
5. Ko babu rawa, babu
kiɗan garaya, babu
kuwwa, aka ji ɗaya daga cikin waɗannan maganganu na
kai da kawo, za a zargi bori daga bakin mai yin su, ko da ba a san shi da bori
ba.
Baƙon Harshe:
Cikin ƙoƙarin tantance
‘harshen bori’, dole a kula da shigar baƙon harshe wanda ba
Hausa ba. A iya saninmu, borin Bahaushe, Bahaushe ne, dole da harshen Hausa za
a gudanar da shi. Idan wani baƙon harshe ya shigo ciki ba za ya ɗauki Bahaushen ma’auni ba irin ma’aunan da
ya gabata. Idan mai harshen na asali ya saurare shi, yana da damar kallonsa a
matakai shida na Bahaushen bori. Kowane ɗaya suka hau bori ne. Idan ma sun kama
daidaitaccen nahawun harshen, kuma aka tabbatar da shi mai borin bai taɓa sanin harshen ba
gabanin borin, to yana shiga cikin wata fassarar bori.
A tsarin borin
Bahaushe, shigar iskoki na ƙabilu iri-iri kamar Bafulatani,
Badakkare, Ba’azbine, Balarabe, Bature, da sauran ƙananan harsuna na
cikin gida da wasu ƙabilu da Bahaushe ya sadu da su ko suka sadu da
Bahaushe abin kulawa ne da nazari. Abin ban sha’awa, daga cikin harsunan, ba a
samun harsunan al’ummomin da Bahaushe ke takin saƙa da su na adawar
yaƙi
da ƙabilanci
irin su Igbo (Inyamuri) da Yoruba (Bayarbe) da ire-iren su. Harsuna irin su
Ingilishi da Faransanci da Larabci, siyasar addini da zamantakewa ta kawo
iskokinsu cikin ƙasar Hausa har a samu harshensu a borin Bahaushe. A
koyaushe mutum ya shiga wani mawuyacin hali ko tsoro da fargabar wani abu, aka
ji yana magana da harshen da bai taɓa magana da shi ba a duniya, kuma bisa
tsarin nahawun harshen, za a ce; “Ba shi ke maganar ba, Iskoki/iska ne ke
maganar ta bakinsa”. Idan haka ne kuwa, Iska ba a cikin bakinsa yake magana ba,
cikin jikinsa yake magana, ya sa magana da baƙon harshe. Idan
haka ta faru, masu ruƙiyya kan ce; “Shigar Iska ne” wanda a nazarin Hausa ba
ya da wani suna face ‘bori’.
A al’adance, ba za
a ga mai bori na rawa ko yana daka tsalle yana direwa a ƙasa a ce; “Borin
Bature ne ko Balarabe ko Bafulatani ko Babarbare ba.” Dole harshe zai iya
tabbatar da wane/wace Iska ce ta shige shi? Idan za mu ƙyallaro ma’anar
bori a nan, za mu iya cewa:
Magana da wani harshe da maras lafiya ko
wanda ya shiga cikin wata matsala zai yi, kuma masu harshen su fahimci abin da
yake faɗa kai tsaye babu
wata tangarɗa. A haƙiƙance cewa, mai
maganar bai san harshen ba, bai iya magana da shi ba, bai da hulɗa da masu shi
gabanin haka. To! A cikin wannan hali da yake ciki shi ne bori a nazarin
al’ada. Maganganun su ne bori. Don haka za a ce; mai yin su “bori ya kama shi”
ko “ya hau bori”, ko “bori yake yi”. Da da harshensa na gado yake magana shi kaɗai sai dai a ce:
“ya haukace”, ba “ya hau bori” ba.
Ma’anar Bori A
Taskar Adabi:
Adabi babbar
fitila ce ta hasko rayuwar al’umma da yadda take tafiyar da ita.[15]
Duk wata al’ada da ake nazari kan al’umma dole a a lalubo adabi a ji yadda ya
harare ta. Ma’anar bori shi ne abin da muke so mu fayyace. A ɗan bincikena, tatsuniyoyi da kirari da salon
magana da tarihihi da waƙe-waƙen yara maza da mata, da sauran
sassan adabi irinsu ba su kamo bori da yawa a cikin ƙunshiyar ba.[16]
Da yawa za a tsinci sunan bori kawai zai bayyana a ciki wanda ko an so a yi
doguwar fassara ma’anar ya ɗan kakkamo kalmar a sarari abin zai ci tura. Karin magana
bai ambaci bori da yawa ba face wurare ‘yan tsirarru da ba su ɗaukar bincike mai
nauyi ƙwarai.[17]
A dubi waɗannan karuruwan
magana don a tantance abin da nake ƙoƙarin fayyacewa;
1. Bori ya ci boka.
2. Ba a bori
da sanyin guiwa.
3. Duk bori
guda muke wa tsafi.
4. Gyara garaya.
Bayyanar kalmar “bori”
a karuruwan magana (na 1-3) ba su ba da wani haske da za a lalubo ma’anar bori
ba. Sun dai tabbatar da samuwar bori da tabbatar cewa, aikin ƙarfi ne da kama
jiki, kuma shi borin wani abu ne da ake yi wa hidimar ‘tsafi’ ba tsafi ne ke yi
wa bori hidima ba. Haka kuma, mun amfana
da ganin cewa, bori wani nau’in warkarwa ne da ya ƙunshi kaɗe-kaɗe da raye-raye. A
taƙaice,
karuruwan magana tabbatar da samuwar bori suke yi, da yin imani da shi, amma
sun kasa fito muna da mene ne “bori” a Hausa? Wannan giɓin da aka samu ga
karin magana ya tilasta mu leƙo:
Bori A Riwayar
Mawaƙan Baka:
Mawaƙan baka adabin
Bahaushe suke ƙara faɗaɗa wa ma’ana, da ƙara masa tsawo
wurin da tasawonsa bai kai ba, da rage masa tsawo idan an ga ya zure, da ƙara kumbura shi,
domin samun nishaɗi. An samu mawaƙa sun yi wa bori
waƙa
kamar Alhaji Muhammadu Shata Katsina ya yi wa Sule Sarkin Bori. Wani makaɗin zamani na Nijar
mai suna Halilu Bori ya yi wa bori waƙa. Idan aka rairaye
kayan cikin waƙoƙin sarai ba za a ga ma’anar bori ta
fito ɓaro-ɓaro ba. Ganin
haka, na ga tilas a yawata cikin ɗiyan waƙoƙin ɗaiɗaikun mawaƙa a ga yadda suka
fassara bori a nasu gani.
Alhaji Muhammadu Shata Katsina da ya
yi wa Sule Sarkin Bori waƙa, abubuwa biyu kawai za mu tsinta na ma’anar bori a
riwayarsa:
Jagora: Akwai mu da borin ƙwarai
:Akwai
mu da borin giri
Gindi: Sarkin bori na Kande
:Uban ‘yan bori Suke.
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ce)
A fafitikar tantance ma’anar bori Shata na ganin dole a
kiyaye cewa, akwai ‘borin ƙwarai” (na gaske) kuma akwai ‘borin
giri” (na ƙarya). Makaɗa Narambaɗa ya mara wa Alhaji Muhammadu Shata
Katsina da ƙara masa sunan bori ɗaya a bakandamiyarsa:
Yara: Ai bana shi za mu yi ruwa sun canye
gero
Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa
:Babban Dodo ba a tamma da
batun banza.
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ce)
Yanayin Bori:
Makaɗa sun ƙara lurar da mu
cewa, bori abu ne da ya shafi hulɗa da mutanen ɓoye, waɗanda ke shigar
mutum idan ya fita hayyacinsa, a ce:
‘ya hau bori”.
Makaɗa Bawa Ɗan’anace a waƙar Shago yana
cewa:
Jagora: Ɗan Abdu ya hau bori
:Borin da ba shi da girka
:Arne ba a gyara maka iskoki
ba.
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ce)
Mun ƙara da cewa, bori
hawansa ake yi kuma dole a yi wa mai bori girka domin a gyara masa iskoki. Idan
ba a gyara su ba, sai su haukatar da mai su, shi ne dalilin danganta rashin
natsuwa ga ‘yan bori kamar yadda Narambaɗa ya zargi wani wagili a masarautar Isa
yana cewa:
Jagora: In ɗan tauri ka ke duk ɗai na
:In ɗan bori kake duk ɗaina
:In mahaukaci kake
duk ɗai na
Yara: In kat taɓa sarki ka gane(?)
:Ya gwada nake bai san tauri
ba.
Gindi: Bai ɗau wargi ba na Jekada
:Na Majikira baban ‘yan kwana
(Ƙarfafawa ta
marubucin muƙala ne).
Da tauri da bori, abubuwa ne da ake
dangantawa da fitar hankali, da rashin natsuwa, wanda ya kai ga ake yanke musu
hukuncin rashin hankali. Ashe a cikin tantance ma’nar ‘bori’ idan rashin hankali
bai shigo ciki ba, ba a yi daidaitacciyar fassara ba.
Don Me Ake Bori?
Fayyace ma’anar bori na buƙatar a cikin fashi
baƙin,
a nuna, da me ake yin bori? Mawaƙan baka sun
tabbatar da cewa, ana bori da Iskoki, su kuwa Iskoki a lokacin ana yi musu kiɗa na goge ko
garaya. Makaɗa Bala Ambursa na
cewa;
Jagora: Kiɗin duma farauta
:Goge ka kiɗin bori
:Duk mai salati
:Garkan Malam shi ka komawa
Gindi: Ba a gane manya
:Sai ci ya samu
(Ƙarfafawa ta
marubucin muƙala ce)
Makaɗa Ɗan’anace a waƙar Shago ya
bayyana bori da Iskoki ake yin sa bayan an girke su. Makaɗa Bala Mai Gumbe
yana zagin karuwai da cewa ‘yan bori suke so, a cikin zargin ya fito da kayan
haɗin bori yana cewa:
:Wai ba a son mu ‘yan bori aka
so
:To, ba ni girka ba ni zondo
:Sai dai kak ki za ka
:Amma ƙanen Alu ya sake
shiri
:Zan samo goro ɗa hamsin da bakwai
:Gidan turuwa in watsa bakwai
:Hanyar mararraba in jefa
bakwai
:Murnar masussuki in jefa
bakwai
:Mange-Mange ko in ba ta takwas
:Jama’a ku gafara Ifiritu zuwa!
Gindi: Rabbani
ahadun
:Mai gudunmuwa lillahi
:Ka ba mu komi
(Ƙarfafawa ta
marubucin muƙala ce)
A cikin ma’anar bori kada a manta da
kalmar ‘zando’, mazaunin Iskoki, da guzurin hidima irin su goro da taba da
makamantansu. Tabbas! Dole a yi nesa-da-nesa da wanda ya hau bori domin Iskoki
irin su Ifiritu na tare da shi.
Taciya:
‘Yan misalan da suka gabata sun ba da
hasken yadda za a iya kallon fassaar “bori”. A taciyar ƙwalailaice yadda
mawaƙa ke fassara kalmar ita ce, bori sana’ar bokanci ce.
Yayin da wani ƙwaro daga cikin ƙwarin Gambo mai waƙar ɓarayi ke neman
sa’a a kashe masa Tsoho Tudu cewa ya yi:
Jagora: An yi bori, an yi bori, an yi bori
:Na yanka awakina da kaji
:An ce sa’a ta samu babba
:Yac ce “Dogon zango nab biyo Tudu”
:Wai shi ya biyo Tsoho dag Gyalange.
Wani ɗan sarauta da ya
shiga takara makaɗa Narambaɗa na gaya muna
cewa:
Jagora: Ga wani ya kunna ya ga ba ƙafa
:’Yan bori sun kai shi sun baro
:Saruru ya baddala abinai
Yara: Ya koma biɗan kwabon hura
Gindi: Ibrahim na Guraguri
:Maishinkahi bajinin zagi
:Mu dai Allah Ya bar muna
kaya.
(Ƙarfafawa ta
marubucin maƙala ce)
Idan aka ba bori matsayin bokanci irin
na maguzanci bisa ga fassarar waɗannan fitattun adibbai ba a yi kure ba.
Abin da ba bayar da magani ba a cikin bori, wasa ce kawai ta motsa jiki, da
kece raini tare da mata masu dandi a faɗar makaɗa Narambaɗa:
Jagora: Duk ɗan sarkin da kag ga ya lalace
:Ya shiga wasan bori
:Ba shi da niyyar sarki (?)
:… … … … … … … … …
Gindi: Koma
shirin daga
:Gwarzon bahago ɗan Iro
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ce)
Makaɗa Narambaɗa na da tunanin
cewa, bori wasa ce kawai, domin ko Iskokin da ake riya cewa, sun hau kan mai bori, da mai borin, da masu girka borin,
da makaɗan bori, da ‘yan
kallo, babu wanda ya taɓa ganin su, balle
ya yi magana da su. Don haka ne Makaɗa Bawa Ɗan’anace ya yanke
wannan hukunci a waƙar Shago yana cewa:
:Ban hana tsahi a yanke ‘yan
kaji ba
:Amma kowag ga aljani bai
kwana.
A iya tunanin ‘yan abubuwan da
hannayenmu suka kai gare su na mawaƙan baka da saura
sassan adabi, za mu iya kirdadon tace ma’anar “bori” da:
Wata wasa ce ta musamman da ta haɗa mata da maza
(manya) da kiɗa da rawa da ‘yan
waƙe-waƙe. A kiɗan ana riya Iskoki
ake yi wa shi don haka ake tanada musu wasu ‘yan kayan marmari da ake ajiye
musu a wuraren da ake riya suke. Wasar babu mai shiga sai yardadde da ya shigo
ta hanyar girka. A cikin wannan wasar bokanci ya tsira. Ga fahimtar adibbai
masu wasan bori hankalinsu gaban goshi yake saboda hawa kansu da Iskoki ke yi.
Rukunan bori a hasashen Bahaushe su ne, cewa: “Allah gaskiya, Iska gaskiya,
bori ƙarya”.
Ma’anar Bori A
Tunanin Al’ada:
Fahimtocin masana harshe da adabi a
kan ma’anar bori daga cikin al’ada aka tsamo su domin babu wanda zai yi tunani
wajen al’darsa. Ma’ilmanta nahawun harshe kallon da suka yi wa kalmar “bori”
bai fita wajen Bahaushen tunani ba. Adibbai na baka da rubutattu ayyukansu
cikin taskar al’ada ce suka gutsuro abubuwan da suke yi wa sharhi daki-daki. A
al’adance, za mu kalli fassarar bori da muhalli tantance bori cikin waɗannan ‘yan bayanan
kamar yadda al’ada ta waiwaye shi:
Muhallin Bori A
Jikin Mai Bori:
Matuƙar an yarda da
sanin amsa shi ne gane tambaya, a al’adance, sai an ga abu, za a iya ba da
labarinsa mai gamsarwa. Al’adar Bahaushe ita ce, gani ya kori ji. A ganin
Bahaushe, wurare shida ake iya ganin bori a jikin mai bori a halin da ya hau
bori ko borin ya shige shi;
·
Baki Suna da kafar
·
Ido
shigar
Iska
·
Hanci
·
Kai Idan Iska ya shiga su za
·
Hannuwa su yi fizge-fizge su
·
Ƙafafu bayyana
akwai baƙo a jiki
Kogon baki ta nan Iska ke bayyana a yi
magana da shi, a gane shi, da dalilin shigan sa. Idanu kuwa, sauya launinsu
zuwa ja ko fari fes kamar ba baƙi ciki, da zubar da hawaye, su ne
alamar ana tare da baƙo. A kowane bori ta hanci ake tare shi (fyace shi)
idan an gama shi. Wurin da Iska ya shiga ba ta nan zai fita ba, don haka, zai
dinga yawo yana wahalar da doki a dinga rawa da kai ana daka tsalle da ƙafafu hannaye na
fizge-fizge. Da an ga haka, an tabbata shigar Iska, kuma ba a nesa ga hawa
bori. Ke nan, fassarar harshe da adabi, ba ta ba da wadatacciyar ma’ana sai an
lalubo muhallin bori a jikin mai bori. A wannan ganin bori zai kasance:
Shigar Iskoki a ɗayan gaɓoɓin hanci ko baki
ko kunne tare da haƙiƙance bayyanar su a idon mai bori.
Yawo da ake yi da kai da rawar da ake yi da fizge-fizgen hannaye da gaɓoɓi na fitar hankali
su ne ‘bori”. Matuƙar ba a ga haka ba bori bai hau kai ba.
Tantance Bori Ta Fuskar
Rabe-rabensa:
Ka-ce-na-ce da aka sha yi kan bori bai
gushe ba amma idan aka harari rabe-raben da masu daɗa juna sani kan
bori suka yi ittifaƙi a kan su, akwai abubuwan cewa da yawa. Idan aka
kakkaɓe taskar adabi
sosai, aka rairaye ma’anonin bori na ƙamus da na
manazarta za a ga rabe-raben bori zai kasance:
·
Borin
girka
·
Borin
fage
·
Borin
giri
·
Borin
ƙwarai
·
Borin
botso
Kowane irin Iska
aka ce ya shiga mutum, ya hau bori, dole borin ya kasance ɗaya daga cikin su.
Borin girka na shiga bori ne, wanda ya nuna ana shiga bori kamar yadda ake
shiga addinai da sauran ƙungiyoyi. Don haka, girka ba hujja ce ta kasancewar
bori addini ba. Borin fage ya ƙara tona wa girka asiri, domin shi
ne haƙiƙanin bori da Narambaɗa ya ambata. Idan
aka waiwayi Borin giri, abin zai ƙara dagule wa
domin ya tabbatar da cewa, an haƙiƙance akwai borin ƙarya a al’adance.
Borin botso wajen roƙon ruwa ake yin sa idan fari ya tsananta,[20]
wanda ya tabbatar da kasancewarsa wata wasar al’ada. Borin ƙwarai a nan gizo
ke saƙa. Ga alama, shi ne wanda aka tabbatar da Iskoki suka
shiga jikin mai shi, suka taɓi hankalinsa, suka sa shi wani hali da aikata wasu
ayyukka da suka saɓa wa hankalin
tuwo. Irin wannan shi ne shigan Iska na haƙiƙa da ba ya buƙatar garaya da
goge bale girka da rawa da waƙe-waƙe da ihe-ihe, ko
akwai su, ko babu su, Iska ya riga ya shiga fitarsa kuwa sai yadda Allah Ya yi.
A gaskiyar wannan hasashen, rabe-raben bori ta kowace fuska aka yi taliyon
fassara ƙunshiyarsa za a ce:
Bori dai wata wasa ce ta gargajiyar
Bahaushe da ta keɓanta ga wasu ‘yan
tsirarru da ke da sha’awar kwaikwayar ɗab’un Iskoki da hulɗa da su. Shigan
Iskoki na haƙiƙa, ya wuce bori, ya zama wata
lalura ta daban. Don haka bori ba haƙiƙa ba ne kwaikwayon
shigan Iska na haƙiƙa ne. Ina laifin Hausawa da suka
ce: “Kama da wane, ba wane ba ne.”
Kalmar Bori A
Fassarar Al’ada:
A farfajiyar al’ada, kalmar “bori”
takan bayyana wurare da dama da ma’ana ɗaya. Ma’anar da take fitowa da ita ta
al’ada ta yi kusa da ta harshe sosai. A al’adance, Bahaushe na da:
·
Borin
gyaɗa
·
Borin
tukunya
·
Borin
yaro
·
Borin
kariya (a wata fassara shi ne borin giri)
Wata cuta kan
shiga gyaɗa ta kumbura ta ta
lalata mata ɗanɗano. Za a ga ta
cika kwalfanta amma cutar ta cire daɗin sai a kira shi “borin gyaɗa”. Idan aka ɗora tukunya a kan
murhu domin yin abinci. Idan ruwa kaɗai ke ciki, suka ji wuta sosai, suka
zaburo, suna zaɓarɓaka za a ce: “ruwa
sun tafasa”. Idan an saka gari cikin ruwan, suka tafasa, suka ture abin da aka
rufe tukunya da shi, kumfan tafasasshen gari ya gangaro ta bakin tukunya sai a
ce: “girki/tukunya na bori”. Yaro ƙarami idan an saɓa masa ya faɗi ƙasa yana kuka,
yana birkiɗa a ƙasa, akan ce “bori
yake yi”. Babu wai, idan takaici ya ci mace kan wani laifin da ta aikata ko
wani abin kunya da aka riske ta tana aikatawa ko aka zarge ta da shi, nan take takan
hau bori don kare kanta. A wannan fassara za mu ce:
Bori
shi ne wani abu ya fita yanayinsa da aka san shi da shi, ko yanayin da ya
kamata ya kasance. Idan mutum ne faɗuwa ƙasa wata babbar
alama ce ta bori. Dabarar naɗe tabarmar kunya da hauka ana yi mata suna bori a
al’adance.
Jinsin Masu Bori:
Al’ada takan kalli rinjayen jinsi ga
aikata wata al’ada domin yanke mata hukuncin masu yin ta. Za mu ga wasan dambe
maza ne, wasan kokuwa maza ne, wasan tauri maza ne, wasan sharo maza ne, wasan
dagajirau maza ne, wasan Ɗankamanci da gambara da zari da makamantansu duk
mazaje aka sani da su. A wasan bori ko mu ce, bori mata aka sani da shi. A
ko’ina ake aiwatar da bori Magajiya da uwar bori da Boboniya da Uwar girka da
‘yan rawa da makaɗa ƙwarya, mata ne.
Wajen kiɗan garaya da goge
kawai maza ke da hannu. Manazarta bori da yawa suna zargin cewa, matan da ke
gudanar da bori mafi yawan su karuwai ne da gwagware waɗanda mazansu suka
mutu ba su samu maza ba, da waɗanda suka wuce budurcinsu ba su yi aure ba, da waɗanda suka yi abin
kunya suka ƙaurace wa garuruwansu, da waɗanda ba a san
wurin da suka fito ba.[21]
A ko’ina za a nazarci borin Bahaushe
dole a ce, gwamnatin borin Bahaushe ta mata ce. Yadda mazaje suka mamaye sauran
wasannin nishaɗi haka mata suka
mamaye bori. Idan aka kula, da borin fage da borin giri, da borin botso, da
borin girka duk mata ke cin karensu ba babbaka. In an ga namiji ciki daga Ɗandaudu sai kawali
da karma ko ashararu. Waɗannan su ne bori a
ƙasar
Hausa domin “borin ƙwarai” ya saɓa wa dukkaninsu kuma ba ya da kama da su.
Ga alama, neman ƙwato ‘yanci daga duniyar maza, da buƙatar fito da
matsayin mata a al’umma, da neman wata makafa ta walwala ga mata shi ya haifar
da bori.[22]
Idan mun yi tarkakken nazarin wannan fasali dole a fitar da zancen addini a
cikin wannan fasali, dole a fitar da zancen addini a cikin a cikin fassara
ma’anar ‘bori’. A wannan matashiyar za mu ga:
Bori wata babbar mafaka ce da mata suka
kafa domin ƙwato ‘yancinsu na zamantakewa da mutuntaka ga hannun
maza tare da ba da tasu gudunmuwa ga al’umma. Matan da ke bori ba su kai shi
matsayin addini ba domin ba su yi iƙirarin barin addinin
da bori ya riske su da shi ba. Addini bai taɓa zama na jinsi ɗaya ba.
Musabbabin Hawan
Bori A Kimiyyar Al’ada:
Ƙoƙarin gano ma’anar
bori ba zai kammala sai an gano abubuwan da ke sa a hau bori. A zuzzurtan
nazarin bori mun san shigan baƙon Iska, da buƙatar girke shi ko
fitar da shi, na sa a hau bori. Duk da haka, a ko’ina za a hau bori, dole a
dubi abubuwa da ke wakana gabanin a ce, Iska ya bayyana dokinsa ya hau borinsa.
A nan, abubuwa uku za a yi nazari:
·
Kiɗan bori na kiran
Iskoki
·
Kirarin
Iskokin bori
·
Waƙoƙin Iskokin bori
Duk wata al’adar
Bahaushe da ta shafi zaburar da maza su harzuƙa, su fita
hayyacinsu, su ɗebe tsoro, su yi
gaba da gaba da abin da ya gabato su, dole sai an sa kiɗa. Ɗan tauri ba ya
kuwwa sai kiɗi ya ratsa shi.
Mayaƙa ba su faɗa fagen artabu sai an tsima su da kiɗa. Idan garaya da
goge suka ratsi zuciyar doki sai a biyo da kirarin Iskansa ko Iskoki
daban-daban. Ba a bari kirari ya lafa sai a saka waƙa a ciki. A
al’adance, ko wanda ba ɗan bori ba, kiɗa da kirari da waƙa na na sa ya yi ƙarfin halin da ɗan bori ba ya iya
yi. A waiwayi waƙar Shata ta Garba Jikan Garba[23]
da waƙar Tudu Tsoho da Ɗanmaɗacci[24]
da tayar da tuban Nazaƙi duk a waƙoƙin Gambo mijin
Kulu[25].
Kai! Hatta da sojoji aka sa su harbe wanda aka yanke wa hukuncin kisa, sai an
girgiza su da waƙar atisaye, da kirari da busa bigala, su gigice, su ɗebe idon sani su
san a mugunta.[26]
Babu wai, ba a taɓa hawan bori
hankali kwance ba. Ba a hawa, sai abubuwan nan uku sun yi turnuƙu, hankali ya
kawa, a shiga ɗabi’a irin ta
Iskoki. Babu kure idan muka ce:
Musabbabin hawan bori shi ne, tsakanin
amon garaya da turnuƙun kirarin Iskoki da waƙoƙinsu, su ke
tafiyar da hankalin mai bori ya shiga halayyar marasa hankali. Hankali ya riga
ya tashi, da kunya da tsoro sun fita zuciya, sai Iska ya bayyana, a hau bori. A
nan, da bori da wasan tauri sun yi tarayya. Ke nan bori aikin fitar hankali ne
da marasa hankali ke aikatawa.
Kimiyyar Tsimin
Girka Da Borin Fage:
Wata gawurtacciyar maɓoyar sirrin gano
mene ne bori? Ita ce, tantance saiwowi da tsirrai da ganyaye da sauran tarkacen
da ake haɗa tsimin girka da
na borin fage. ‘Yan bori na cewa, suna jiƙa saiwowi da ganye
da ɓawon itacen magani
kimanin tis’in da tara (99) su ne wanda za a yi wa girka zai riƙa sha yayin girka.
Haka kuma, tsimin idan ana borin fage,
shi za a saka a randa, a girke tsakar fage, duk wanda zai taka bori ya sha.
Sirrin da ke ciki shi ne, daga cikin itacen da aka haɗa tsimin akwai zaƙami (Babba jijji)
da sayen tumfafiya da ganyen taba da na kaɗe. Kowane daga cikinsu ɗan kaɗan ake saka shi
domin an san yana sa maye da juyar da hankali na matuƙa. Idan ba a
daidaita su da jar kanwa sosai ba har kisa suke yi kai tsaye. Wanda ya sha
tsimin zai ji jikinsa ba nauyi ko kaɗan, yana ganin kanun mutane bibbirkice.
Don haka, da ya sha tsimin yana kama shi zai daka tsalle ya yi ihu a gaban kowa
domin ruwan Iblis ne ya sha wanda ya fi tabar Iblis kawar da hankali.[27]
A borin fage, ko mutum bai taɓa bori ba ya sha su sai ya kuwwata, an yi rawa da shi.
Wannan shi ne dalilin da ko ɗan bori bai san sirrin abubuwan da ya sha ba sai dai
ya ga ya noce cikin duniyar Iblis kai tsaye. Wa zai musanta abin da ya ji a
jikinsa, ya gani da idanunsa? Na yarda da Bawa Ɗan’anace a faɗarsa:
Jagora: Mai bori ba ya ce wa bori ƙarya ne
Gindi: Maza na tsoron Karo da Ado ɗan Garba
Wannan kimiyyar ita ce tushen kowane
irin hatsabibin abu da aka ga mai bori na aikatawa. Idan za a yi wa tsimin bori
adalci, dole a saka shi cikin ma’anonin bori domin shi ne kanwa uwar gami:
Bori wasar wartske jiki ce da holewa tare
da tsimin maye da zai tsananta nishaɗantarwa da kawar da kowace irin fargaba da
za a fuskanta. Saduwar mayen tsimin da hankalin mai bori shi ke sa ayyukkan
rashin hankali ga mai bori a yayin da yake bori. Mayen babba jijji shi ne bori
ba garaya da goge da kiɗan ƙwarya ba.
Bori A Ma’aunin
Addini:
Fassarorin da suka
gabata, na ji tsoron saka kalmar addini a fashin baƙin ma’anar ‘bori’.
Fassarar addini faɗi gare ta, don
haka wasu masana al’ada suka ɗora bori a ma’aunin ‘cult’, wato ƙungiyar asiri ko ƙungiyar sa kai.
Daga cikin masanan da ke da wannan ra’ayi akwai: Besmar, 1977; da Lewis, 1960;
da Lombard, 1969; da Onwejeogwu, 1969; da Tremeane, 1915; da Echard, 1991; da
Greenberg, 1946. La’akari da ‘yan tsirarun da ke yin bori da dalilan yin bori,
ya sa suka kira shi ‘cult’. Sun san da kalmar ‘religion’ amma suka kauce mata.
Fitattun masana al’adun Afirka wasu sun ɗora ‘bori’ a kan kalmar ‘belief’ wato
yarda ko imani da abu wanda Bahaushe ke kira miƙa wuya.
Faulkinham, 1975 da Tremeane, 1915 sun fito da wannan ra’ayin. Ga alama, aikin
Greenberg, 1946 da aikin Connant, 1960 su suka fara bijiro da kalmar addini a
nazarin ‘bori’. Idan muka kwatanta aikin Greenberg, 1946 da na 1941, za mu ga,
ba matsayin addini ya ɗauki bori ba, ya
dai kalli cuɗeɗeniyar al’adun
gargajiya da na addinin Musulunci a harkar bori, tare da ba da ƙarfi ga irin
tasirin da addinin Musulunci ya yi cikin borin Bahaushe. ‘Yan bori a cikin
hidimominsu na Iskoki, ba su taɓa yi wa bori suna da ‘addini’ ba. Babu nassin adabin
Hausa da ya kawo sunan bori a matsayin ‘addini’. Masu sha’awar bori, ba mu ji
wurin da suka kira shi ‘addini’ ba. Tubabben ɗan bori ba mu taɓa ganin wurin da
ya jaddada kalmar shahadarsa ba, bale sauya sunansa na addinin bori zuwa sabon
addini. Ashe ba mu yi kure ba idan muka ce:
Bori wata daɗaɗɗiyar aƙida ce daga cikin
aƙidojin
gargajiya na Bahaushe da suka makaro a farfajiyar tunanin mata. Da bori da
tsafi da camfi da kwari da ƙofi da fatalwa da dodo da jihilma
babban tsuntsu (Roch) yadda aka ji su, ba dole sai an gan su haka nan ba. Don
haka, aƙidoji ne masu zamani da wayewar mutanen zamaninsu.
Taho-Mu-Gaman Bori
Da Addini:
Kallon da wasu ɗalibai da masana
ke yi wa bori na ƙarnukan da Musulunci ya riga ya shigo, su manta da
cewa, gabanin ya shigo akwai ƙasar Hausa da Hausawa. Idan aka
nazarci adadin kwanakin girka, da yadda ake shiga bori, da sutarar girka, da
yadda ake fita girka, da hidimomin da ake yi da kayayyakin da aka tara wurin
girka (sadaka) za a ga biri ya yi kama da mutum suna da alaƙa da addinin
Musulunci. Sunayen fitattun Iskokin bori irin su Malam Alhaji, Nana A’isha,
Abdu, Hassatu, Adiza, Ali, Aljana, kamar yadda (Nicole, 1999) ya ambace su a ƙasar Adar. Za mu
ga sunayen cike suke da Balaraben naso da tasirin addinin Musulunci.
Yanke-yanken da ake yi wa Iskoki, da ranakun yanka, da siffofin
dabbobi/tsuntsayen da za a yanka, kamar yadda (Greenberg, 1946) ya ambace su,
Musulunci na da hannu a ciki. Binciken masana bori ya nuna, manyan biranen
Iskoki biyu ne “Jangarai” da “Kwankwanɓilo”. Wasu ‘yan bori sun fi yarda da “Jangarai”,
domin har borin ‘Jangarai’ akwai. A binciken da na yi 2002, ‘Jangarai’ wani
babban wurin tsafe-tsafe da borin Larabawa ne a Tunis, yanzu haka babban
Masallacin ƙasar a wurin aka gina shi da sunan Jangere wato
“Masajidil Jangere”. Kayan kiɗan bori su garaya da goge da kuntugi, in ban da ƙwarya duk daga ƙasashen Larabawan
Tunis da Maroko da Aljeriya suka shigo ƙasar Hausa. Da za
a cire tasire-tasiren da addinin Musulunci ya yi cikin bori duka, ɗan abin da ya rage
zai tabbata muna cewa,bori wata aƙida ce ta wasu
‘yan tsararru da ba su taka kara suka karya ba. Gabanin zuwan Musulunci, aƙidar bori ba ta
kai camfi da mafarki ƙarfi ba. Ina da fahintar cewa, bori ba addini ba ne. A
cikin wannan farfajiyar tunani muna iya cewa:
Bori wata dabarar warkarwa ce da bokaye
suka yi fice da ita. Da Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa ya
tarar da ‘yan bori ne jagororin al’umma. Da aka rinjaye su, suka miƙa wuya karkace.
Kasancewarsu cikin summa kafaru summa amanu sai bori da Musulunci suka
cakuɗe wuri ɗaya Musuluncin ‘yan
bori ya koma barbaran yanyawa. Taho-mu-gaman aƙidojin addinin
Musulunci da aƙidojin bori ya sa da wuya a tantance kama da wane ba
wane ba ne. Bori ba addini ba ne, wata hidima ce da wasu ‘yan tsirarru ke yi wa
Iskoki tsakanin ƙarya da gaskiya, har abin ya bi jikinsu da hankalinsu
suka ɗabi’antu da ɗabi’a ɗaya da ake iya
rarrabe su da sauran wasu ba su ba.
Cika Da Batsewar
Bori:
Binciken da aka yi ya gano cewa, bori
ya yi lokacinsa na tashe, yanzu batsewarsa ta zo. Dalilan da suka haifar da
haka su ne: Bori aikin manya ne ba a sa yara ciki. Da zamanin manya ya wuce ko
sun mutu sun tafi da abinsu. Na biyu, bori wata jahiliyya ce da ta gabaci
bayyanar saukakkin addininai a ƙasar Hausa. Da addinai suka bayyana
haskensa (bori) ya dushe batsewarsa ta tabbata. Masu bori na da mata ne marasa
kowane irin ilmi na addini da na zamani. Da ilmin addini ya tabbata, tauhidi ya
zauni ƙirjin masu bori, dole a yi ban kwana da shirka. Bugu da ƙari, ilmin zamani
ba zai zauni ƙirjin mutum ba ya sha wa kansa guba da mayen da zai
zama sanadiyyar halakarsa. Wayewar zamani ta tsafta da siyasar zamantakewa ta
kasance wata annoba ga bori ƙasar Hausa. A hasashen da na yi kashi 95% na Hausawa
matasa mata na zamaninmu sun fi da son zama ‘yan wasan kwaikwayo ko ‘yan rawan
zamani na shaye-shaye da sharholiya, da a ce musu ‘yan bori. Yau da za a ce,
mace ‘yar bori ce, ko saurayi ɗan bori ne, abu mai ne mai wuya su samu mai son su
aure. A ƙarnin da muke ciki, tabar Iblis da ƙwayoyin zamani sun
karɓe wa Iskoki tutar
hawa kan mutanen zamani. Idan don bokanci bori zai ci kasuwa, guguwar jihadi da
wa’azojin da ke gudana ƙasar Hausa sun hana shi shanya garinsa ya miƙe ƙafafu yadda yake
so. Da malaman duba da ‘yan bori duk jifa cikin duhu ne in ji Wazirin Gwandu
Malam Umaru:
Wanda bai wuce shi yi kwana na
Bai wuce shi mance abinai ba
Wanda bai sana ma rabonai ba
Yaushe za shi gane min nawa?
(Wazirin Gwandu: Gargaɗi ga Abokai)
Sakamakon Bincike:
Yawace-yawacen da aka yi cikin
farfajiyar nazarin harshe da adabi da al’ada an samu fassarori takwas
mabambanta a kan bori. Fassarorin kowace ta kama ruhinn fannin da aka kalla.
Nazarin fassarorin bai nuna bori addini ba ne. ‘Yan bori cikin Hausawa ‘yan
tsirarru ne, da addini ne da ya game ƙasa gaba ɗaya. A cikin ‘yan
tsirarrun jinsi mata ke da rinjaye. A fassara, al’ada faɗi ke gare ta, don
haka, idan aka kira bori “al’ada” ba za ta kasance ta ‘yan tsirarun mata
ashararu ba, a yi wa ƙasar Hausa bugun goro. Babbar al’adar Bahaushe da ta
yi naso cikin bori ita ce “bokanci”. Kutsen bokanci cikin bori dole ne, domin
mutanen bokaye da ake yi wa bokanci (mata) ke da kasuwar bori. Bokancin bori ga
masu borin ya fi tasiri ba ga tarsashin al’ummar Hausa ba gaba ɗaya. Kasancewar
“borin ƙwarai” wani suna ne da ake fassarar shigan Iskoki a
jikin mutum na haƙiƙa ya sa ni ban ɗauke shi bori ba,
ya fi adalci a kira shi “shafar Iska” ko “shigan Iska” a jikin ɗan Adam. A kan
wannan tankaɗe da rairaya za mu
fahimci bori shi ne:
Wata wasa ce ta musamman da ta keɓantu ga wasu ‘yan
tsirarrun mata da ‘yan kanzaginsu makaɗa garaya da goge da ake gudanarwa a
lokacin hunturu da bazara. Karɓaɓɓun ‘yan wasan, sai an girke su a kan Iska da suka zaɓa wa kansu ko aka
zaɓa musu. Maganaɗison wasar shi ne
tsimin bori wanda da shi ake hawa bori kuma sai ya sake jiki ake tara (fita)
bori. Wasan bori manyan tubalanta su ne, rawa da faɗuwa ƙasa na fitar
hankali, da fitar da yawu ko kumfa a baki, da furta zantukan saɓari da
hannunka-mai-sanda ga halin da mai borin yake ciki. Wannan shi ya nuna bori naɗe tabarmar kunya
ce cikin fitar hankali da ake laɓawa ga Iskoki ana fizge-fizge da
kuwwa-kuwwace. Lallai bori aikin ƙarfi ne don haka
Hausawa ke cewa: “Ba a bori ba sha dawo (fura) ba”, su kuma masu bori su ce:
“Ba a bori da sanyin guiwa”. Kasancewa sai an kakance damina sosai ake bori ya
sa na kira shi wasan cikan shekara na korar yunwa.
Naɗewa:
Tantance ma’anar bori wani jan aiki ne
mai buƙatar taron dangi. A ɗan yunƙurin da ya gabata,
an yi garkuwa da nazarin harshe da adabi da al’ada domin a yi tara-tara kama da
kamun zakaran yara daren babbar sallah. Babu addinin da bai yarda da samuwar
Iskoki ba da shigar su a jikin ɗan Adam. Babu al’adar da ba ta san da zaman Iskoki ba
da irin dangantakar su da mutanen duniya. Shigar Iska a jikin mutane sananne ne
a duniyar ilmi, sai dai fitar da shi da sunan “bori” ko tsayar da shi da sunan
“girka” Bahaushe ya kaɗaitu da shi a
duniyar mutane (a iya bincikena). Rabe-raben borin Bahaushe, da jinsin da suka
fi rinjaya ciki, da yadda ake aiwatar da shi, da maganaɗison haɗinsa (tsimi) su
suka tabbatar da kasancewar bori wasa daga cikin wasannin gargajiya na ƙasar Hausa. Sunan
“al’ada” ya yi masa faɗi da yawa, ko kusa
ba su haɗa hannu da wasan
kwaikwayo ba. A dai fassara shi da: wasan sagarci na tsirarrun fanɗararrun mata da
‘yan kazaginsu ‘yan Daudu da kawalai da ‘yan korensu ‘yan hamsin da ‘yan dandi
da duniya ta sa wa ido da halinsu. Ga dai irin bulaliyar da Zabiyar ‘yantaru ta
fyaɗa ga ‘yan bori da
‘yan kallo cikin waƙarta ta bege:
Jagora: Masu bori da goge da dundufa
:Masu kallonsu sun fi su dambala
Amshi: Mai gari Makka farin Balarabe
:Mai Safa Marwa mai bi da
Zanzama
(Ƙarfafawa ta
marubucin ce)
MANAZARTA
Abdalla, Isma’il H. 1991. “Neither Friend Nor Foe:
The Malam Practitionaer - ‘Yan Bori Relationship in Hausaland”. In Lewis, I. M.
et al Women Medicine: The Zaar - Bori Cult
in Africa and Beyond. Edinburgh Uniɓersity Press for
International African Institute.
Abdallah,
Isma’ila. 1997. “Islam, Medicine, and Practioners in Northern Nigeria” in Studies
in African Health and Medicine Ɓol. 6, The Edwin Mellen Press, Greenston,
Ontario, Canada.
Abubakar, S. Y. 1997. “Bori A Zariya” kundin digirin MA, Kano: Jami’ar
Bayero.
Al-Shashi, Ahmed. 1986. “Spirit Possession and
Healing in the Zaar among Shaƙƙiyya of the Northern Sudan”, in Ahmad al-Shashi,
Theme from Northern Sudan, London.
Ashkannani, Z. 1988. Middle-aged Women in Kuwait “Ɓictims
of Change” PhD thesis, Durham Uniɓersity.
Bargery,
G. P. 1933. A Hausa-English Dictionary and
English Hausa Ɓocabulary.
Zaria: ABU Press.
Bawa,
A’ishatu Balarabe. 2011. “A History of Bori in Yeldu and Yauri in the 20th
Century”, MA thesis, Sokoto: Usman Danfodiyo Uniɓersity.
Besmer,
Firemount E. 1973. Aɓoidance and Joking Relationships Between Hausa Supernatural
Spirits, in Studies in Nigerian Culture 1, 1, 1973.
Besmer,
Firemount E. 1977. “Initiation Into The Bori Cult: A Case Study In Ningi Town”,
in Africa 47, 1, 1977.
Besmer,
Firemount E. 1983. “Horses, Musicians and Gods: The Hausa Cult of Possession -
Trance, South Hadley, Massachusestts.
Bunza,
A. M. 2014. In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka:
Muryar Nazari Cikin Tafashe Gambo. Cairo, Egypt:
Elkods Printing House.
Conant, Francis P. 1960. “Dodo of Dass: A Study of
a Pagan Religion in Northern Nigeria”, PhD Dissertation, Colombia Uniɓersity.
Constantini
des, P. M. 1972. “Sickness and the Spirits: A Study of the Zaar Spirit-Possession
Cult in the Northern Sudan”. Unpublished PhD thesis, London: Uniɓersity of
London.
Constantini
des, P. M. 1985. “Women Heal Women: Spirit Possession and Seɗual Segregation in
a Muslim Society” in Social Science and Medicine 21, 6, 1985.
Constantini des, Pamela. 1977. “Ill at Ease and
Sick at Heart: Symbolic Behaɓiuor in a Sudanese Healing Cult.” In I. M. Lewis
(ed), Symbols and Sentiments
Cross-Cultural Studies in Symbolism. London.
Dutse,
Y. A. 1989. “Yadda ake Hawan Bori da Ire-iren Iskokin da aka Kira”. Kundin
digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗangambo, A. 2007. Rabe-raben Adabin Hausa. Kaduna,
Nigeria: Amana Press.Besmer, Firemount E. 1973. “Praise-epithets And Songs: Teɗts for
Some Important Bori Spirits In Kano, in Harsunan Nijeriya, 3, 1973,
CSNL, Kano: Bayero Uniɓersity.
Echard, Nicole. 1991. “The Hausa Bori Possession
Cult in the Ader Region of Niger: Its Origins and Present-day Function”. In
Lewis, I. M. et al Women Medicine the Zaar-Bori Cult in
Africa and Beyond, Edinburgh Uniɓersity Press for
International African Institute.
Faulkingham,
Ralph H. 1975. The Spirits And Their Causins: Some Aspects of Belief Ritual,
And Social Organization in a Rural Hausa Ɓillage in Niger, Research report
Number 15, Department of Anthropology Amberts; Uniɓersity of Massachusets.
Gobir, Yakubu Aliyu. 2002. Iskoki Idon ‘Yan Bori Da Masu Ruƙiyya” kundin digirin MA,
Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gobir, Yakubu Aliyu. 2012.
“Tasirin Iskoki Ga Cutuka Da Magungunan Hausawa”, kundin digirin PhD, Sokoto:
Jami’ar Usman Ɗanfidiyo.
Gomrawala,
Mu’izz. 1977. “Maguzawa: The Influence of the Hausa Muslims on the Beliefs and
Practices of the Maguzawa Traditional Religionists of Kano and Katsina. In Orita.
Ibadan Journal of Religious Studies.
4, 2, 1977.
Greenberg, Joseph H. 1941. “Some Aspects of
Negro-Muhammadn Culture Contant Among the Hausa”, in American Anthropologist, NS 3.
Greenberg, Joseph. 1946. The Influence of Islam on
a Sudanese Religion, Monographs
of the American Ethnological Society, 10, New
York, Seatle, and London.
Gulbi, Abdullahi
S. 2014. “Magani a Ma’aunin Karin Magana” Kundin Digirin PhD, Sokoto: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Harold, B. Bardy, 1964. Buurii al Lamaad: a Suburban Ɓillage in the Sudan. Ithaca, New York.
Harris, P. G. 1930. Notes on Yauri (Sokoto Proɓince),
Nigeria in The Journal of
the Royal Antropolocigal Instititute 60.
King, A. Ɓ. 1966. Boorii Liturgy from Katsina
(Introduction and Kirari Teɗts) in African
Languages Studies 7.
King, A. Ɓ. 1967. “Boorii Liturgy from Katsina” in African Languages Studies 7.
Krieger, Kurt. 1967. “Notizen zur Religion der
Hausa” in Paidenna 13.
Krusins,
Paul 1915. The Maguzawa Translated by Gisela Seidenstiker-Brikay, Zaria 1982,
in Archiɓ fur Antholologie, NF Ɓol. ƊIƁ
Last, Murray. 1967. “A Note on Attitudes to the
Supernatural in the Sokoto Jihad.” JHSN, 4, 1.
Last, Murray. 1991. “Spirit Possession As Therapy:
Bori among Non-Muslims in Nigeria” in Lewis, I. M. et al Women Medicine the Zaar Bori Cult in
Africa and Beyond. Edingburgh Uniɓersity Press for
International African Institute.
Lerour, H. 1948. “Animisme et Islam dans la Subdiɓision
de Maradi.” Bull
de IFAN. 10.
Lewis,
I. M. et al 1991. “Women Medicine: The Zaar-Bori Cult in Africa and Beyond” in International
African Seminars New Series, No. 5 Edinburgh Uniɓersity Press.
Lewis, L. M. 1966. “Spirit Possession and Depriɓation
Cults” in Man (n.s.) 1.
Lewis, Walla. 1988. Hausa Medicine: Illness and Well-being in a West African Culture. Durham: Duke Uniɓersity Press.
Lombard, J. 1967. “Les Cultes de Possession en Afriƙue
Noire et le Bori Hausa” in Psychopathologie
Africaine 3, 3, 1967.
Lombard, J. 1969. “Possession Cults in Black Africa
and the Hausa Bori”, Transcultural Psychiatric Research Reɓiew 6.
Montana, Ismael M. 2009. “The Bori Colonies of
Tunis.” In Bchnaz, A. Mirzai et al, Slaɓery,
Islam and Diaspora. Africa World Press, Inc. Asmara,
Eriteria.
Natɓig,
Richard. 1988. “Liminal Rites and Female Symbolism in the Eguptian Zar
Possession Cult.” Numen 35,
Nelson,
Cynthia. 1971 “Self, Spirit Possession and World Ɓiew: An Illustration from
Egypt.” In International Journal of Social Psychiatry 17.
Newman, P. 2000. Hausa language: An Encyclopedic Reference Grammar. Yale Uniɓersity Press.
Nicolas, Jacƙueline. 1970. Culpabilite,
Somatisation et Catharsis au Sein d’un culte de Possession “Le Bori Hausa” in Psychopathologie Africaine 6, 2.
Onwuejeogwu, Michael. 1969. “The Cult of the Bori
Spirit among the Hausa” in M. Douglas and P. M. Kaberry (eds.), Man in Africa. London
Philips,
Abu Ameenat Bilal. 1997. The Eɗorcist Tradition in Islam. UAE: Dar
Al-Fatah.
Price, J. H. 1957. “A Bori Dance in Accra” in West African Reɓiew 28, no. 352.
Tanimu,
Y. 1999. “The Hausa Ritual Theatre: Bori Performance in Zaria”, MA thesis,
Sokoto: Usmanu Danfodiyo Uniɓersity.
Tremeane, A. J. M. 1915. “Bori Beliefs and
Ceremonies” in Journal
of the Royal Anthropological Institute 45.
Tremearne,
Major A.J.N. 1914. The Ban of the Bori: Demons And Demon: Dancing in West
and North Africa. London.
Wall, Lewis L. 1981. “Traditional Medicne and the Ɓalues
of Life in a Rural Hausa Ɓillage”, D.Phil., Oɗford.
Wason,
Peter J. 1967. “Status Ambiguity and Spirit Possession.” In Man. (n.s.)
2.
William,
G. G. da Robert, L. S. 2000. What Science Can Say and Can’t Say About Spirit.
In The theatre of religion and Physical Research, USA.
‘Yar’adua,
Tanimu Musa. 2001.”Wasan Kwaikwayo: Sigoginsa da Jigoginsa.” A cikin Algaita Journal of Current Research.
Maiden Issue Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Zaria,
M. A. Z. 2013. Gamayyar Tasarifi da Tsarin Sautukan
Hausa. Zaria: ABU Press.
Zenkoɓsky,
S. 1950. “Zaar and Tambura as Practiced by the Women of Omdurman.” In Sudan
Notes and Records. 31, 1, 65 - 81.
[1] Cuɗanyar Hausawa da wasu ƙabilu makusanta da manisanta ta hulɗar siyasa da kasuwanci da yaƙe-yaƙe ya haifar da wasu kalmomin Hausa su salwanta. Irin illar da harshen
Ingilishi da Faransanci da Larabci da Indiyanci suka yi wa harshen Hausa ba ƙarama ba ce. A yau, kalmomin wasan bori irin su girka
da saɓani da sabu
da botso da goho da dursuna sun fara salwanta.
[2] Cuɗanyar Hausawa da wasu ƙabilu makusanta da manisanta ta hulɗar siyasa da kasuwanci da yaƙe-yaƙe ya haifar da wasu kalmomin Hausa su salwanta. Irin illar da harshen
Ingilishi da Faransanci da Larabci da Indiyanci suka yi wa harshen Hausa ba ƙarama ba ce. A yau, kalmomin wasan bori irin su girka
da saɓani da sabu
da botso da goho da dursuna sun fara salwanta.
[3] Ana samun
gamsasshen bayanin tsarin sautukan Hausa cikin ayyukan M. A. Z. Sani, musamman
littafinsa Maraka Yanki A
Tsarin Sautukan Hausa. Zaria, 2013 da
Gamayyar Tasarifi da Tsarin Sautukan
Hausa. Zaria, 2011.
[4] Domin fayyace
suna a nahawun Hausa da ire-iren sauye-sauyen da suna yake samu, a dubi,
Newman, P. The Hausa
Language: An Encyclopedic Reference Grammar. London, 2000, shafi na 5 – 15.
[5] Ƙunsar ruwan da ƙurji ke yi idan aka yi sakiya ruwan za su fito kamar
turo su ake yi haukace, haka ɗan bori yake yi
kamar jikinsa ya ɗebi iska irin na tayar mota ta yi babban faci.
[6] Makaɗa
Garba Ɗanwasa Gummi
(makaɗin ‘yan tauri) yana bayanin wani
tauraro nasa da ya yi ta’adi aka kira shi rabon faɗa. Da ya zo rabon faɗa
ya ce; ya tarar da tauraronsa:
Jagora: Kasko nak kai gare shi
:Sannan
nar rungumai
:Shina
bobbotai kama da mato mai injimi
:…
… … … … … … … … … …
Gindi: Mai sharanin biɗan
faɗa ko ba nashi ba
:Na sarkin Kabi Kaɗo masu motsattsen hankali
(ƙarfawa ta marubucin muƙala ne)
A kowane lokaci ‘bobbotai’ shi ne ɗagar da murya baki na kumfa kalmomi wasu su fita
babbarkace wasu su ƙagale.
[7] Makaɗa
Sani Ɗanbalɗo
Warama ya yi amfani da kalmar bololloƙai a waƙarsa ta ‘Zaura’, da kurma ya neme ta aure shi ta nuna
ta aminta, aka je aka ɗaura aure da wani ba shi ba. Yana
cewa:
Jagora:
An kasa kurma ga biɗar zaura
:Ni
rannan na ji bololloƙai
:Han
na tashi biɗo gora
:Don
na aza gebe na yad daɗe.
(ƙarfafawa ta marubucin muƙala ne)
[8] Malam Mamaki (Head Master na Saran
Dosa Primary School, 1989/90) wani fitaccen sha’iri ne da aka yi a ƙasar Jega garin Saran Dosa ya yi
amfani da kalmar ‘saɓari’ a waƙarsa ta yabon masu zikiri, yana
nuna cikin ƙaunar
Shehensa idan magagin zikiri ya ja shi, sai ya ce:
Sai
in faɗi ina ta saɓari
Mis
same shi? A ce: ‘hailala’
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ne)
[9] Makaɗa
Ɗan’anace a waƙar karon Shago da Buzu na Waila mai
taɓa yaggwai ya ce: da Buzu ya sha ƙullin Shago nan take bori ya shige
shi ya yi saɓari da faɗar:
Jagora:
Galik ka mamma shif-shif
:Gamas
garin da ba ni kowa
:An
kai ni an daka mini kashi
(Ɗan’anace: Waƙar Shago)
Kalmomin da Buzu ya furta saɓari ne ba su da wata ma’ana.
[10] Wata shekara, 1978, kunama ta harbi
wani ɗan dako mai suna Onti a tashar
Bunza. Ana yi masa kamu ‘yan tasha na yaba shi da juriya don bai yi kuwwa ba
kuma bai yi kuka ba, amma fa bakinsa faɗar yake:
“Wayyo regede! Wayyo regede! Wayyo regede!”
Wannan shi ne sabbatu, bai san abin da yake faɗa ba.
[11] Soki-burutsu, ko dai a gina zance
gaba ɗaya kan kure misali: “muna cikin
tuwo muna cin zaure, ko da anka yi kura ga walƙiya tsugunne.” Abin nufi a nan shi ne: “Muna
cikin zaure muna cin tuwo, ko da anka yi walƙiya ga kura tsugunne.” Haka kuma, soki-burutsu yakan ɗauki maganar shirme ta hauka. Misali, wani taɓaɓɓen mutum a ƙasar Aljannare ta Jihar Kabi a
koyaushe maganganunsa su ne:
A
san da wakko mori guɗɗa
Ba
ta gai da kowa da gona
Da
gona! Da gona! Da gona!”
Na
ce: da gona, da gona da gona!
Me za a tsinta a nan? Haka ne soki-burutsu.
[12] A tsarin al’ada, kirari batutuwa ne
domin maganganu ne aka tattaro barkatai. Sarkin Gwandu Halilu ya yi amfani da
kalmar “batutuwa” a waƙar
yabon sojan hayansa Garba Gande Janborodo, wadda Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa ya yi wa tahamisi yana cewa:
Da
sunan Ta’ala za ni fara batutuwa
Tunawa
da manya masu kari da garkuwa
Fito-na-fito
ka yi ta ba su ƙidayuwa
Yabon
bajini ad dole don ba shi gasuwa
Zaman ba
a … … … … … ba ta faruwa
(Waƙar Janborodo)
[13] Shirɓace
ita ce maganar da ba ta da tsari kuma ta ɓata tsari. Malam Muhammadu Sambo
Wali Giɗaɗawa
Sakkwato ya kawo kalmar a waƙarsa
mai suna “Waƙar Zaman
Banza” yayin da yake yi wa ‘yan Izala habaici yana cewa:
Akwai wasu na nan da ba ni son in
duba su
Suna
aikin Jalla ba ya karɓar aikinsu
Sabili
da baƙin nuhi da mugun niyyarsu
Akwai
muni mai yawa cikin maƙasudinsu
Suna son
sa shirɓace cikin addininmu.
(Sambo
Wali: Waƙar Zaman
Banza)
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ce)
[14] Boboniya ita ce matar da iskoki
suka aura suka lalata mata magana, komai za ta faɗi
a birkice take faɗarsa. Misali:
Daidai: Boboniyanci:
Barka
da asuba Basua da
kabar
Ina
za ku je? Je
ku za na’i?
A
ba ni ruwa in sha Sha in
waru ni ba a
Ko
kuma ƙago wani harshe na musamman da
sunan harshen Iskoki kamar:
Si gara ta mantasa buba.
A ba ni sigari in sha.
[15] Don ƙara tantance adabi da rabe-rabensa da tsarinsa a rayuwa a dubi, Ɗangambo, A. Rabe-raben
Adabin Hausa Da Tasirinsa Ga Rayuwar Hausawa Ta Gargajiya. Kano, 1999.
[16] Rashin samun kai da kawon bori ciki ya tabbatar da
cewa, bori na wasu ‘yan tsiraru ne daga cikin Hausawa. Da babbar haraka ce gama
gari, dole a same ta daɓa-daɓa cikin
taskokin adabin baka na asali irinsu Tatsuniya da Kirari da Karin Magana da
sauransu.
[17] Don ƙara samun wadataccen bayani a kan haka a dubi, Gulbi, A. S. “Magani A
Ma’aunin Karin Magana” kundin digirin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, 2014.
[18] Borin botso – shi ne wanda mata ke
yi da zane ɗaya kawai, idan ana kiɗa a dafi ƙasa
da hannuwa biyu a ɗaga kwankwaso suma a kware zanen
tsiraici ya bayyana. A da, idan farin ruwa ya tsananta shi ake yi wa kirari da:
Komi
taka zama ta zama
Komi taka zama ta daɗe!
A
ƙasar Gobir da Zamfara ana ce da shi
‘Taburtsetse-burtse’. Malam Ummaru Kwaren Gamba ya kawo kalmar a waƙarsa ta roƙon ruwa da kakansa ya yi, shi ko ya
yi mata tahamisi yana cewa:
…
… … … ……… … … … .. ….
Taburtsetse da siffar mahaukata
Irin
haka ma na sa a ƙi ruwa
(Ƙarfafawa ta marubucin muƙala ce)
[19] Makaɗa Narambaɗa a nan yana kwaikwayon kiɗin bori ne da ake yi wa ɗan sarkin. Faɗar “Zakara” yana bayyana ƙaunarsa ga matan banza, “Yaɗɗamna” ita ce matar da ta fara karuwanci a garin Isa.
Idan an ce mutum ‘Zakaran Yaɗɗamna’ ne, an
dai gane ba sai da sharhi ba.
[20] Wai! Dalilin yin sa ga ‘yan bori shi ne, sun san
Allah ba Ya son bayyanar da tsiraicin mata. Allah zai ji kunyar aikin da suke
yi, ya sako ruwa, ya sallame su, su daina fasadi ban ƙasa.
[21] Wannan hasashe ya fito a cikin aikin Faulkingham, R.
H. “The Spirit And Their Cousins: Some Aspects Of Belief, Ritual,
And Social Organization In A Rural Hausa Ɓillage In Niger.” Research Report
15, Amherst 1975, p. 11.
[22] A ƙasar da Hausawa suka baje kolin al’adunsu irin
Nijeriya da Nijar da Ghana da Togo da Benin da Mali da Senegal da Sudan da
Libiya da sauransu shugabannin bori mata ne. A ganin wasu masana al’ada maza
suka yi wa mata juyin mulki a sarautun ƙasar Hausa da sarautun bori a yau. Hira da Dr. Bube
Gado, fitaccen masani al’ada a Jami’ar Abdul Mumini, Niamey, Jamhuriyar Nijar,
wajajen 1999 a ofishinsa na CELTHO, Niamey.
[23] A cikin waƙar an sa Garba jikan Garba ya sha giya cikin watan
azumi da rana kata. Bayan an ingiza shi ya yi ta’asa, Makaɗa Shata ya ce, “Ba ruwansa da shi”.
[24] Don samun cikakken bayanin artabun a dubi, Bunza, A.
M. In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka:
Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo.
Egypt, 2014.
Jagora:
Yaf fasa kuwwa yay yi yaya
:Yac ce;
“Ayyururui! Gambo mijin Kulu
:Ai
tuba ta tashi Gambo
:Mallami
da zagin doka ga kai nai
:Ya
baza hoda ya yi gazal
:Ba batun tuba akai ba!
[26] A al’adance, ɗan
tauri ba zai daka wa kansa wuƙa ko ƙarfe ba
sai kiɗa ya tsima shi jikinsa ya ɗauki mazari ya yi kuwwa ya ce: “Jarƙaniya! Jarƙaniya !Jarƙaniya!” Da ya furta haka ko sau ɗaya ne, yanzu Shaiɗan
zai zo ya taimaka masa. Ɗanbashirwa
(mazawayin kasuwa) ko ya tuba ya ji kiɗin
bashirwanci sai an rirriƙe shi in
ba a son ya yi tsirara a ko’ina yake. Kiɗa wata
babbar allura ce a al’adun gargajiyar Bahaushe.
[27] A zamanance, ‘yan borin ƙarninmu giya suke sha mai ƙarfi domin su samu damar yin
wasanninsu. Sau nawa ana hukunta fitattun ‘yan wasan ƙwallon duniya da safarar miyagun ƙwayoyi da shan su gabanin shiga
fagen wasa? Babba Jijjin da ‘yan bori ke sha ya fi ko hodar Ibilis kawar da
hankalin mai hankali. Irin wannan halayyar ce tsagerun matasa ke shiga idan
suna son su ci idon gabaci. Alhaji Muhammadu Sambo Wali Giɗaɗawa a ‘Waƙar Zaman Banza” ya ce:
Ga jin daɗin rayuwa samari ka bicewa
Suna wasu ‘yan ƙwange-ƙwange don nuna ɓacewa
Su sa takalmin da ba wuya za a karewa
Su shawo tabar da hankali zai
juyewa
Su gigice
don su samu damar ɓacinmu.
(Ƙarafafa ta marubucin muƙala ce)
Muna godiya.
ReplyDelete