Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata - 8: Shashantar da Magana


Akwai misalai da dama waɗanda maza sau tari ba sa sakin jiki da matansu su yi musu bayani. A ƙarshe kuma in abin bai yi kyau ba macen ita ce abar zargi. Misali
Miji: "Baƙina za su zo ki tabbatar an gama komai kafin lokacin."  
Mata: "In sha Allah, amma ka kawo kayan hadin da wuri, mutum nawa kake jin za su zo?"
Miji: "Ban sani ba, amma ki yi yadda zai isa"
Mata: "Kana ganin za su kai 10-15?"
Miji: "Na ce miki ban sani ba, ki yi yadda zai isa kawai, kar kuma a banzatar da abinci, ba wanda bai san halin da ake ciki a yau ba".


Kundin Ma'aurata - 8: Shashantar da Magana

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Ɗaya daga cikin abubuwan da suke baƙanta wa mace rai shi ne lokacin da za ta riƙa jin an mai da ita kamar saniyar ware a kan abin da take jin cewa tana da rinjaye, misali ɗiyarta da take auren wani yaro dan kasuwa, tana jin cewa ana cutar mata da yarinyar gwargwadon yadda bincikenta ya nuna a wurin yarinyar, tabbas za ta iya gasgata yarinyarta saboda abu biyu, na farko dai ita ta raini yarinyarta ta san halinta, na biyu kuma duk alamomin damuwa da rashin jin dadi suna bayyana a fuskarta da jikinta, don haka ta yi wa mijinta, wato uban yarinyar, maganar cewa ya je ya binciko abin dake faruwa, ta fahimci cewa yaronnan so yake ya yi wa ɗiyarsu yankar ƙauna, da maigidan ya dawo matarsa tana zaton zai yi mata magana bai ce komai ba, shi ya sa ta ƙyale shi har zuwa lokacin cin abincin darensa, sannan ranta ma ya gama baci.
.
Yana dab da kammalawa ta tambaye shi ko zai sha shayi, ya ce bai da buƙata, sai ta ce "Ina zaton za ka gaya min yadda kuka ƙare da wancan yaron ba ka ce komai ba! Ka gan shi kuwa" ya ce "I na gan shi, kuma mun dan tattauna na tsawon lokaci" a maimakon ya yi mata bayani sai ya yi shuru, ƙila shi yana ganin cewa lamarin abu ne da ya shafi maza zalla, ita kuma ba abin da ya fi mata zancen ɗiyarta, za ta so ta ji yadda lamarin ya kaya, ta ce "Ban gane kun tattauna ba, wai me ke faruwa ne?" Ya ce "Mts! Wasu 'yan abubuwa ne ƙanana, in da za su zauna su tattauna ba ma sai wani ya shiga tsakaninsu ba"
.
Shi yana sauƙaƙa abin ne yadda mahaifiyar ba za ta shiga cikin maganar ta tada zaune tsaye ba, a ganinsa ya riga ya magance matsalar, ta ce "To ai kai ba haka ake yi ba" tana ƙoƙarin ta san hanyar da ya bi ne wurin magance matsalar "Kamata ya yi ka tara su a gabanka, ka ji ta bakin kowa, ba ka kira shi shi kadai ka saurare shi ba" anan ransa zai baci, saboda tunanin cewa ta raina hankalinsa, don ita ce ma take ƙoƙarin gaya masa me ya kamata ya yi, in ba sa'a aka yi ba sai ya bar asalin maganar da suke yi, wace inda zai ce haka na yi shi kenan ya gama, amma sai ya kama ta da fada "Wai ke me yasa ba ki da haƙuri ne? In kina ganin kin fi ni sanin yadda za a daidaita su bismillah! Sai ki je ki tanƙwara shi ya tafiyar da yarinyarki yadda kike so" a wannan misalin ma an sami sabani, wanda zahirinsa shurun namijin ya kawo shi, mace tana son a kawo mata komai a fassale, tana son a riƙa tattaunawa da ita, namiji kuma bai cika son lugwigwita magana ba.
.
Ba fa dole ya zamto 'yarsu ce da gaskiya ba, kamar yadda zai iya kasancewa mijin 'yar yake da gaskiyar, a duk biyun uban yarinyar yana ganin za su iya daidaita kansu masamman yadda ya ja kunnensu dukansu, ya kuma nuna musu hatsarin kasantuwarsu a irin wannan yanayin na rashin fahimtar juna, tunda sun nuna sun ji abin da ya ce shi kenan magana ta ƙare, ita kuma uwar ba ta san hanyar da aka bi ba, ta san maza da rashin kula halin diyoyinsu mata, sai a yi ta cutar da su ba tare da sun nuna kulawarsu ba.
.
Akwai misalai da dama waɗanda maza sau tari ba sa sakin jiki da matansu su yi musu bayani. A ƙarshe kuma in abin bai yi kyau ba macen ita ce abar zargi. Misali
Miji: "Baƙina za su zo ki tabbatar an gama komai kafin lokacin."  
Mata: "In sha Allah, amma ka kawo kayan hadin da wuri, mutum nawa kake jin za su zo?"
Miji: "Ban sani ba, amma ki yi yadda zai isa"
Mata: "Kana ganin za su kai 10-15?"
Miji: "Na ce miki ban sani ba, ki yi yadda zai isa kawai, kar kuma a banzatar da abinci, ba wanda bai san halin da ake ciki a yau ba".
.
Nan ma a dunƙule aka ba ta ba tare da bayani ba, in bai kai ba a ce ta yi ƙoro, in ya rage kuma a ce ta yi almubazziranci, rashin yi wa mata magana yakan dagula abubuwa da daman gaske, koda yake wani sa'in suna da zaulaya, ba abin da suke nufi kenan ba, amma maigidan sai ya fusata, misali za su yi baƙi ne, kuma 'yar shinkafar da suke ci ta kusa ƙarewa, ƙila da safe ma sun tattauna ƙarewar tata da rashin kudin sayo wata, dan sauran duk ba ta wuce mudu 6 ba, kenan ba za ta kai su kwana 10 ba za ta ƙare, lokacin da ya yi maganar dafa wa baƙi abinci sai ta ce "Kamar mudu nawa zai isa, kana ganin 7 ya yi?"
.
Tana sane ko ta gidan ba ta kai 7 ɗin ba, in haushi ya cika shi sai ya gaya mata magana, ko ya jefa mata kudin hannunsa ya yi waje, ba tare da ya gaya mata yadda za a yi ba, kamata ya yi ta gama sauraronsa tukun, in ma zaulayar za ta yi sai ta yi masa a ƙarshe, kamar kuma lokacin da suka gama tattauna matsalar gida, da rashin kudi, ga kayan abinci duk sun ƙare, a ƙarshe-ƙarshen hirar sai ta dauko wata magana "Ni da ma za ka dan biya ni bashin da nake binka da na ji dadi, ga shi ma salla ta matso, wallahi ban da ko sisi a ɗakinnan, dan jarin da nake dan juyawa ma duk ka gama amshewa, don Allah zan dan sami ko rabi ne albashi sauran in ka samu sai ka cika min?"
.
Shi ma wannan in ba sa'ar aka ci ba zai iya zama laifi, don kuwa da ita aka tattauna rashin kudinnan amma ta juya baya kamar ba ta san komai ba, sai ka ga maigida ya yi kinini da fuska ya bata rai ya ƙi cewa komai, ko ta yi masa magana kuma ba zai ba ta amsa ba, wannan zai sa ko ta canja batun ba dole ba ne ya sake tanka mata, ba wai don ta yi masa maganar kudi ba, a tunaninsa baƙanta masa rai take son yi, mun yarda maza suna da saurin fushi, kuma sun dauki hanyar ƙin yi wa mace magana ita ce zababbiyar hanyar da za su huce fushinsu, ko kuma su nuna mata cewa ba su ji dadi ba, wanda hakan a wajen mace kuskure ne, sau da yawa ba ta ba wa abu mahimmanci, namiji kuma yakan dauke shi da zafi, to amma ita ma ya dace ta riƙa zaben lokutan da za ta yi wasa da lokutan da take kallon abubuwa a haƙiƙaninsu.

Post a Comment

0 Comments