Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata - 16: Neman Kusanci a Fahimta



Shi ya sa abokan aikinta suke girmamata suna kiranta da malama. Ban san yadda suka haɗu da malamin ba amma dai soyayya ta bayyana a tsakaninsu, kuma kowa ya ji daɗin wannan aure. Abin da zai ba ka mamaki malamin bai yarda ta...

Kundin Ma'aurata - 16: Neman Kusanci a Fahimta

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Daya daga cikin abubuwan da muke fama da su a yau tsakaninmmu da abokan zamammu har da kuskuren da muke yi a wurin zabe, domin za ka sami mutum wayayye dan boko mazaunin birni, in ya ƙyalla ido ya hango wata bafulatanar riga, jar fata, sai ya sha alwashin ko nawa zai kashe sai ya aure ta, zai kashe ɗin ya kuma auro tan, amma ba dole ne a sami komai daidai ba, don shi ya yi Kudu ne ita ta yi Arewa, duk abubuwan da yake so a yi masa ba ta san su ba bare ta sa himmar yi masa, zai yi mata bayanin ga yadda za ta yi a rana guda, ita kuma wayewa karatun shekaru ce da take shiga a hankali, in ba ta yi masa abin da yake so ba sai ya kama fada, yau da kullum sai ta fara maida masa, in ba a yi sa'a ba sai lamarin ya ƙi ƙarko.

Wata da aka auro ta ba shakka an kashe kudi a kanta, koda yake tun farko an canfe su da cewa ba sa zaman aure, amma abin da na karanta a kanta, mutumin yana da mata tun asali, zancen iya kwalliya, tsafta, gyaran kai kamar tsuke da sauransu suna da alaƙa da wayewa, kuma sirri ne na mace, ba kowace mace ce za ta tsaya tana yi wa kishiyarta bayanin cewa ga abin da maigidansu yake so don haka ta yi masa ba, balle uwa uba sirrin dafa abinci da abin-ci, abubuwan suna da yawa, don in ka tabo bangaren tsafta dama makaranta ce guda mai zaman kanta.

Wato dai duk abubuwan da mutumin yake buƙata ba ta iya yi masa, a ƙarshe ya fara yi mata fada yana cewa ta sa ido mana ta riƙa kallon abokiyar zamanta, su mata wannan ƙasƙanci ne da raini, sannan sirrorinsu in ba su suka fada ba ba idon da zai iya kallo maka, a ƙarshe dai ya saki amaryar tasa bayan ta haifa masa yaro kyakkyawa, ban san me ya sa ba, don kyawun da ya aure ta don shi har yanzu akwai shi.

Dayan kuwa malami ne, da yake sauka gidan wani mai hali a duk lokacin da ya zo wa'azi garin, matar Alhajin tana da wata ƙanwa da ta yi karatun digirinta na farko a dayan jami'o'immu, kuma ma'aikaciyar asibiti ce, ƙira ta halitta gami da jin dadin rayuwa duk sun bayyana mata, takan yi kwanaki tana aikin dare kafin ta komo na rana, ba ta cika tsoron maza ba don tun tana nursery school tare da maza ta yi har jami'a, yanzu kuma yanayin aikin nata dai tana tare da mazan ne, har ma a wurin aiki, akwana tare a tashi tare, sai dai duk da wannan mace ce mai kamun kai da son ibada.

Shi ya sa abokan aikinta suke girmamata suna kiranta da malama. Ban san yadda suka haɗu da malamin ba amma dai soyayya ta bayyana a tsakaninsu, kuma kowa ya ji daɗin wannan aure. Abin da zai ba ka mamaki malamin bai yarda ta ci gaba da aikinta ba matuƙar tana matarsa saboda abin da ya kira da zubewar ƙimarsa, ya yi mata alƙawarin daukar duk nauyinta, ita kuma ta yarda, saboda ƙaunarsa tana zucuyarta, masamman kwadayin abin da ta gani tare da shi na ilimi, shuhura da tsoron Allah, abin da take sha'awa kenan a rayuwarta.

Bayan aure da wasu yara ƙanana da ta samu rigingimun dake tsakaninsu tun da jimawa suka fara ƙamari, domin shi ba mai zaman gida ba ne, yakan hada wata ba shi a gari, ga kuma matansa a garuruwa daban-daban, ga wa'azuzzuka wasu har a jahohi masu nisa, bai da lokacin zama da iyalin bare su yi maganar karatu ko wasu abubuwan, yanayin wayewarta da karatunta ko kusa ba su yi kusa da halin da ta sami kanta a ciki ba, a ƙarshe duk ƙoƙarin da uwayen suka yi na ganin an zauna lafiya bai yuwu ba, dole aka haƙure wa juna.

Na ce: Da a ce ya kalli rayuwarta tun farko da yadda ta taso koda za a sami matsala za ta zo da dan sauƙi, ita ma za ta shiga fagen nasa ne na yi wa mata wa'azi, da halartar tarurrukan imani na mata, ga makarantun islamiyu ga na gwamnati da suke da alaƙa da abin da ta karanta waɗannan ma kawai sun ishe ta, rashin duba wannandin ya sa auren ya ƙi dorewa, ta yi ta zarginsa da rashin ba ta haƙƙinta, abubuwan ma da bai dace wani ya sani ba duk ta fada saboda bacin rai, aure dai ya lalace, ma'auratan kuma duk ransu a bace, shi maigidan yana jinjina wa irin kyautatawar da yake wa matar amma sam ba ta ni, ita kuma ta lissafo abubuwa da dama da irin rayuwarta da aikinta da ƙawayenta da duk ta rabu da su a dalilinsa amma kullum cikin baƙin ciki, abin dai ba dadi wai mahaukaci ya ci kashi.

Ita kuwa wannan baiwar Allan kowa yana yaba mata kamunkai da shigar mutunci, ga ta da hardar Ƙur'ani, ta gama sakandarenta kenan tana burin shiga jami'a, ita ma ta ce pharmacy take son ta karanta, fara ce ƙal amma ba kowa ya sani ba don ba inda ake kallo a jikinta, ban sami cikakken bayanin yadda ta hadu da mijinta ba bare yadda aka yi auren, amma kullum cikin fada suke, ta nemi ya sake ta ya ƙi, tana zarginsa da yin sakaci da addini shi kuma yana cewa tana yi masa wasa da gida, sannan bai yarda da koyarwar da take son yi ba, kuma ba ita za ta tsara masa rayuwarsa ba, a taƙaice dai babu kusancin fahimta a tsakanin duk waɗannan ukun, ina ganin shi ne masabbabin samun tasgaro a auren.

Post a Comment

0 Comments