Akwai kuma wata Balarabiyar ƙasar Lebanon inda na ga hirarta a talabijin ɗin ƙasar ita da wani baƙin fatan ƙasar Ghana. Ita ma ya je karatu ne ajinsu guda. Ya je bai iya Larabci irin nasu ba amma yana fus'ha, wato gamagarin Larabci wanda shi ne karɓaɓɓe a tsakaninsu. Ta ce wannan shi ne babban dalilin da ya sa...

Kundin Ma'aurata - 15: Ƙwarya ta bi Ƙwarya

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Na jima ina da wannan fahimtar, a gaskiya na gwada sosai kuma na ga amfaninsa, na sa ido a rayuwar wasu da dama don na yi karatu, kuma na fahimci abubuwa da dama, sai dai ba ina ƙoƙarin cewa saurayi ya auri budurwa ko bazawari ya auri bazawara ne ba, sha'awa wace ake mata laƙabi da soyayya ana samunta a ko'ina, kuma tsakanin kowa, tare da bambancin aƙida ta siyasa ko addini, hali na dabi'a ko dukiya, mulki na sarauta ko aikin gwamnati,  matsayi na wurin aiki ko rayuwa, wayewa ta ilimi ko ta duniya, bambancin shekaru ta bangaren mace ko namiji da dai sauransu.

Yawancin maza in suka mace a ƙaunar macen ba sa rabewa tsakanin soyayya ta gaskiya da sha'awar kasantuwa da mutum don dadin bakinsa da salon iya magana, mace a rayuwarta abin da take buƙata kenan a wurin namiji kamar yadda muka karanta a baya, in ta sami wani namiji ya iya kalamai masu dadi za ta ƙaunace shi ba tare da ta duba ko shi waye ba, nazarin ya yi daidai da rayuwarta ko bai yi ba wannan ba lissafinta ba ne, don in ka tambaye ta "Don me kike ƙaunarsa?" Da wahala ta iya ba ka katamaiman dalili guda daya, magana ce kawai mai dadi.

Na taba ganin wata Baturiyar ƙasar Sweden da ta auri wani baƙi dan ƙasar Sudan, ana hira da ita a talabijin ɗin Sudan din, mai gabatarwar ta tambaye ta "Don me kika aure shi tare da bambacin rayuwa kika canja addini, yare, ƙasa, abinci, sutura, kika bar gari mai mugun sanyi kika dawo gari mai mugun zafi?" Na so na ji bayanin da za ta yi masamman kasancewata mai nazari ta fuskar rayuwar dan adam, ƙila na tsinci wani abin da ban sani ba, koda yake in kana neman bankaura ka sami Bature ka gama.

Da bude bakinta ta ce ba ta da wani dalili, ta ce "Kawai dai mun yi karatu tare kuma ajinmu guda, shi mutum ne mai yawan barkwanci da son ba'a, to launin fatarsa ya fita da na kowa don haka hankulan mutane suna yawan komowa kansa, ni ban taba sha'awar zama tare da shi ba, amma in ya zo ta wurina nakan tsaya na saurare shi, da haka dai da yake gidansa yana kusa da namu har muka saba, ni ban san lokacin da ya shiga raina ba, ban ma sani ba wa ya fara neman wani a cikimmu, a ƙarshe dai mun fahimci juna kuma ga ni a Sudan".

Matar ta iya baro ƙasarta ta tare da shi a Sudan, ta haifa masa 'ya'ya 6, amma ta ce gidansu ba wace ta haifi 'ya'ya ƙasa da 12, kuma ita ma in Allah ya sa za ta haife su a shirye take, ta ba ni sha'awa masamman yadda na gan ta musulma, kuma na ga ba ta da wata niyya ta komawa ƙasarta, a maganarta ma sai ta kwashe shekaru kafin ta je gida, in ta je ɗin ma dan lokaci kadan sai ta dawo wurin mijinta, wannan kam zama ya yi dadi, sai dai bambancin launin fata ne, ƙasa, addini, yanayi, cima, sutura da rayuwa, ban san bambancin hali irin na dukiya ba, don in dan Sudan zai je karatu ƙasar Sweden akwai yuwuwar kasancewarsa mai arziƙi, ita kuma a ƙasarta ba dole ba ne, kasancewar tana zuwa Sweden ta dawo ka ga akwai hali.

Akwai kuma wata Balarabiyar ƙasar Lebanon inda na ga hirarta a talabijin ɗin ƙasar ita da wani baƙin fatan ƙasar Ghana. Ita ma ya je karatu ne ajinsu guda. Ya je bai iya Larabci irin nasu ba amma yana fus'ha, wato gamagarin Larabci wanda shi ne karɓaɓɓe a tsakaninsu. Ta ce wannan shi ne babban dalilin da ya sa ƙaunarsa ta kurdada zuciyarta ba tare da ta sani ba, har dai a ƙarshe suka yi aure, koda yake a iya hirar ba a ambato dadewar da suka yi tare ba, bare a yi maganar ko takan je Ghana ɗin ko ba ta zuwa, ba a yi kuma maganar sun sami zuri'a tare ko har yanzu suna nema ba, sai dai an nuno yadda ta riƙe shi tamau, sannan maganganunta da motsinta duk suna nuna irin tsabar ƙaunar da take nuna masa.

Shi ma an nuno cewa ta fara ƙoƙarin koyon harshensa wato Hausa, shi Bahaushen Ghana ne, kayan jikinsa yana nuna cewa ɗiyan masu hali ne, koda yake waɗannan Larabawan mun sani suna da ƙyamar baƙin fata, amma in kana da hali ba matsala, za su iya aurenka kuma su zauna da kai a duk inda kake son ka rayu da su, sai dai dole ka riƙa tunawa cewa tana da 'yan uwa, kuma ita kamar gona ce dole ka riƙa ban ruwa daga lokaci zuwa lokaci, in ba haka ba kuwa in wata rana ta je ganin gida auren ya ƙare kenan, yaranka ma dole ka haƙura ka bar mata, ko kuma ku yi ta shari'a, koda yake in za a yi adalci ba dukansu haka suke ba.

Sai dai na ga aurarrakin da aka yi tsakanin 'yan Nigeria da fararen buzayen Nijer, na ji irin koke-koken da aka riƙa yi wadanda suka so su yi kama da auren diyoyin fulani a yau, haka na zauna da wadanda suka auri Shuwa, su kam ba wani kuka sama da bambancin zamantakewa ta wurin me za a ci, kuma ya za a dafa shi, almuhim, wannan ba zai zama hujja a wurin talaka ya ƙyalla ido kan ɗiyar masu kudi ya kafe kuma sai ya aure ta ba, banda auren akwai rayuwa kamar me za a ci? Me za a sanya a matsayin sutura? Wace iriyar mota za a hau? Wani gida za a zauna? Wa zai yi hidimar gida da dai sauransu.