Larabawa sun riƙa yi wa ɗiyoyinsu nasiha da cewa su guji wasu mata. Ban sani ba ko mu a nan ba su da matsala. Sukan ce "Mata 6 ka guje su: Mai yawan ƙunci da kai ƙara, mai gori, mai yawan tuno tsohon mijinta, mai kallon mijin wata, mai son kanta a komai da mai shegen surutu." Mu a nan ka ga mai...

Kundin Ma'aurata - 14: Don Me Ake Auren Mace?
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

A lissafin da muka yi a baya ana auren mace don abubuwa ne da dama, amma wace za a aure ta don addininta ita ce mace, ko a hadisin da Annabi SAW ya fado dalilan da ake auren mace ya yi umurni da auren mai addini, ita mai addini lahirar take kallo ba duniya ba, in kana da kishi dama ta san illar shigar banza da tsayuwa da mazan da ba nata ba, in ayyukan ibada ne kafin ka yi mata umurni tsoron Allanta ya sa ta aikata, kuma shi ɗin zai hana ta kusantar mummunan abu, ko ta yi niyyar wani aika-aika in ta tuna lahira da ƙuncin dakecan sai ta ja baya, in fushi da kai ta yi, da ta yi tunanin ni'imar dake aljanna, da matsayinka a wurinta sai ta aikata ba don kai ba, wannan ita ce ta ƙwarai ga mai idon basira.

Shi ya sa zaƙulo irin waɗannan matan ba abu ne mai sauƙi ba, don ba a fuska abin yake ba bare ka ce za ka riƙa kallonsu, ko ka ce in ka ga mai sa niƙabi shi kenan, kashi 89% cikin dari suna zabo matan aure ne a daya daga cikin wadancan da muka lissafa a baya, da ƙyar za ka ji wani ya ce "Irin tarbiyar da uwar su wance take ba su ta sa na ga inda zan dauko mata, don na tabbata ita ma haka za ta koya wa diyoyinta" galibin masu neman aure cewa suke yi ta yi musu, ba wai ta dace da 'ya'yansu ko za ta iya yi wa uwayensu hidima da kyautatawa ba.

A wani hadisi na Hakim da Baihaƙi wanda Albani ya inganta, Annabi SAW yana cewa "Abubuwa 4 suke nuna jin dadin mutum: Mace ta ƙwarai, yalwataccen wurin zama, maƙwabci na ƙwarai da lafiyayyen abin hawa, akwai kuma munanan abubuwa guda 4: muguwar mace, mugun maƙwabci, mummunan abin hawa da ƙuntataccen wuri" matan da kansu sun san ba mu damu da kyawun halinsu kamar kyawun fuskokinsu ba, don haka kowa a yau fara ce, koda kuwa tana da baƙar zuciya.

Wani hadisi na Ibn Hibban da Albani ya inganta Annabi SAW yana cewa "Idan mace ta yi sallolinta 5, ta azumci watanta (Wato Ramadan), ta kare gabanta (Ba ta zina bare mutu'a), ta bi mijinta, za a ce mata "Shiga aljanna ta ƙofar da kika ga dama" an ma tambayi A'isha RA "Wace mace ta fi?" Ta ce "Wace ta san illar magana, ta guji makircin maza, ta tsaya wa ƙawata kanta don maigidanta, ta kare mutuncin uwayenta".

Larabawa sun riƙa yi wa ɗiyoyinsu nasiha da cewa su guji wasu mata. Ban sani ba ko mu a nan ba su da matsala. Sukan ce "Mata 6 ka guje su: Mai yawan ƙunci da kai ƙara, mai gori, mai yawan tuno tsohon mijinta, mai kallon mijin wata, mai son kanta a komai da mai shegen surutu." Mu a nan ka ga mai shegen surutu, mafadaciya, mai dogon hannu, magulmaciya, da mai shegen yawo da ƙazamiya su ne matan da ya kamata ka guda, ciki har da wace take ji a jikinta cewa nauyin uwayenta yana kanta ne, ta dauki rigar maza ta sanya tun kafin ta yi aure.

Gaskiya ka guje su, sai dai mu a nan in dai mace fara ce to gaskiya ko ya take ba ta rasa mijin aure, koda kuwa za ta yi cikin shege sau barkatai, mai dabi'u na ƙwarai kuwa in dai ba fara ba ce ba ta cika samun shiga ba, na taba jin wasu matasa suna zagin junansu sai wani ya ce wa guda "Allah ya ba ka 'yar musabaƙa" sai na ce "Kamar ya? Ita ɗin ba ta da hali ne?" Suka bushe da dariya, sai a ƙarshe wani yake ce min "Ai ustaz galibin 'yan musabaƙannan kamar fenti kawai ake musu" ya fado abubuwa da dama wadanda ban yarda da su ba.

Wasu mazan sukan ga mace da mummunan hali amma su ce za ta gyara in suka aure ta, su manta da yadda ta ginu tun farko, wasu ma ba wani shirin da suka yi na gyara barnar, in dai ta yi musu a ido shi kenan, akwai wani da ya je wajen wata mata yana son ya neme ta, ta ce masa "Ka yi haƙuri, ni matar aure ce" da kada bakinsa sai ya ce "Ai na sani, kawai dama nake so ki ba ni, shi wancan ai namiji ne shi ma irina" ka ga irin wannan me za ka ce masa? Kallonta fa kawai ya yi sau daya.

Akwai mata biyu da suka yi min waya, daya ta ce "Don Allah malam ya zan yi? Gaskiya ina da cutar HIV, na kashe maza 3 a kan haka, amma wallahi ko an gwada ba a gani, sai dai ni na san ina da shi, ga wani ya fito min, na gaya masa komai amma ya nace sai ya aure ni, kana ganin na amince?" Na hana ta, don da bakinta ta ce ta yi kisa, wata kuma ta ce "Wallahi ba abin da ban gaya masa ba na cewa ina da HIV amma ya ce sai mu yi ƙaryar cewa mun guda, kawai sona yake yi!" Abin takaici duk wadancan mazan suna da mata da yara.

Kenan dukansu ba wanda ya duba addini ko diyoyinsa dake gabansa, bare ya yi tunanin sauran matansa da yadda rayuwa za ta kasance bayan aure, idonsu rufe auren kawai suke so, jiki kuwa in ba lafiya hatta saduwar auren ba za su ji dadinsa ba to bare sauran ma'amalla, a sanina ƙyamar masu waɗannan cutar ma ake yi, amma kalli irin yadda suka mace musu, don Allah za ka sa rai da adalci bayan aure? Ba boka ba tsafi amma namiji ya susuce kamar wani zautacce? Dole in mutum yana son zaman lafiya ya san wa zai aura kuma don me? Ya yi tunanin cewa aure fa tafiya ce mai tsawo ga zanguna da yawa, waye za ta jure har ƙarshensa?