Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 26: Yau Da Kullum



A ƙarshe ta ce "Gaskiya mijina yana gida. Da ma a ce ita ma ta yi lallen ne ko da bai kai wannan kyau ba, ko kuma tana da miji da da sauƙi. Amma yadda hannayena suke fararen nan nata kuma sun sha lalle, cab! Wallahi ba za ta...

Zan Ƙara Aure // 26: Yau Da Kullum

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wani abinda zai ba ka dariya shi ne sakacin da mata ke yi har sai abinda ba sa so ya faru sannan su dawo suna "Da na sani" duk abinda ba ki yi tsammani zai iya zama dalilin ƙara aure ba wallahi yakan zama, koda kuwa a irin salon adon mace ne, kamar irin lallen da take yi mai daukar hankali wanda ko mata kan yi sha'awarsa bare namiji, irinsa ne maigidanki zai riƙa satar kallo, macen da take neman miji shi kenan abin nema kuma ya samu, ba lalle ba har da salon gyara gashin kai, koda yake matammu ba sa barin gashinsu ya leƙo  waje amma wasu na yi, wani bonono da matanmu ke yi sai boye kitsattsen gashi su bar ƙafar da ta sha lalle mai daukar hankali a waje ba safa.
.
Wasu matanmu sun san cewa mazansu na bala'in son ganin lallen, amma ba su damu da su yi ba saboda mazan ba su ba su kudin lallen, da kuma wata macen za ta yi mai daukar hankali in ta ga mijinta na satar kallo nan take za ta nemi ba'asi, ko ta ce ba ta yarda ba, akwai lokacin da na ga wata malamar Islamiya ta tsaya kai da fata kan cewa ƙawarta ba za ta bi ta gidanta ba, alhali wani abu kawai za ta amsa ta wuce, nan dai abokan aikinta suka sa baki lokacin da suka ga cewa da gaske take.
.
A ƙarshe ta ce "Gaskiya mijina yana gida. Da ma a ce ita ma ta yi lallen ne ko da bai kai wannan kyau ba, ko kuma tana da miji da da sauƙi. Amma yadda hannayena suke fararen nan nata kuma sun sha lalle, cab! Wallahi ba za ta bi ni ba ko alama!" kamar da wasa, amma a ƙarshe dole haka suka yi ittifaƙi kan cewa su hadu gobe.
.
Ni ban ga laifinta ba, na fi ganin kuskuren wace za ta ce a kawo mata 'yar aiki, kuma ba ta son ganin tsohuwa, yarinya ƙarama take so, wace za ta ci ado ta riƙa shiga tsakaninsu, koda ta yi baƙi ba za ta ji kunya ba, tana sane cewa mijinta ba mala'ika ba ne, kullum ƙaramar yarinya da ado na ƙarshe tana tsole masa idanu, wata rana ido zai raina fata, don ba shawara dake zai yi zai yi ba, sai dai ki ji labari ya canja salo.
.
Wata take gaya min cewa wata yarinya ta riƙa shigowa gidanta har suka saba, ba irin maganganun da ba sa yi tare, kusan kullum tana gidansu, har abinci take dafa musu, suka zama kamar 'yan uwa, kwana ne kawai ba ta yi, a zahiri ba wani abu sabo da take gani wanda zai iya jan hankalin maigidanta, koda kuwa gaisuwa bare hira, amma haka kawai ƙawarta ta dauke ƙafa, ta yi ta bin sawunta kan dawo kamar yadda suka saba amma abin ya ci turi, haka dai ta saduda ta fita harkarta.
.
Cikin makwanni biyu maigidanta ya gaya mata cewa zai yi aure, kamar da wasa, ya fara gyaran ɗaki haiƙan, aka daura aure kuma aka kawo amarya, ba ta dai sami damar ganin amaryar a ranar ba, maigida ya tafi ɗakin amarya ya kwana, kashegari tana zaton amaryar za ta zo su gaisa shiru kake ji kamar an shuka dusa, sai ta yanke cewa durƙusa wa wada ba gajiyawa ba ce, ta bi ta ɗakinta, tana shiga sai ga ƙawarta, na taƙaita muku labari a ƙarshe ta ƙara gaba da bar wa amaryar gidan.
.
Ba abinda wata mace za ta yi don burge namiji wanda ke ba za ki iya ba, lura da duk abinda yake so ki dauki mataki, Ramla take cewa "Zan iya bari wa maigidana kwanakin al'adana duka ya je wajen amaryar" za a yi mata dariya amma ita zuciyarsa take farauta, macen da take son namiji ba ya son ta, in ka ga ta dage tana ta kashe kudi zuciyar kawai take so, in ta mallaka ka dawo ka gani in za ta ci gaba, duk macen da ta san mijinta na son abu amma ta yi biris da shi, to fa ta san cewa zai iya zama babban dalilin ƙara aure.

Post a Comment

0 Comments