Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata - 11: Abin da Kowa Yake Gani



Abubuwan da suka bayyana a irin wannan matakan da ake ɗauka su ne ake kira kishi. In dai haka ne to ba dole ne ya bayyana ga namiji ba. Sau ɗaya na ga wani mutum da matarsa take koyarwa a wata makarantar firamare wanda suka kwashe shekaru da dama suna tare, sai dai duk daɗewar nan suna ɗan samun wasu 'yan matsaloli a tsakaninsu. In kuma an samu ɗin wani abokin aikinta ne yake shiga tsakaninsu, domin mijin har...

Kundin Ma'aurata - 11: Abin da Kowa Yake Gani

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Suna maganar dalilan dake sanya mace hauka ne a lokacin da kishi ya taso mata, sai suka ce: Mace kan miƙa kanta ne kacokan ga namijin da zarar zuciyarta ta natsu da shi, wannan mutumin shi zai yi jagorancin rayuwarta gaba daya, ta yi hukuncin rayuwa da shi daga duniya har lahira, sai ya zamo yana da wani matsayi na yarda wanda ko mahaifinta bai samun irinsa, don akwai maganganun da in ba mijin ba ba za ta taba yi da wani ba, ita kenan, amma shi namijin da mace ta nuna tana ƙaunarsa kuma bai yi wani kokwanto ba wurin yarda da ci gaba da soyayya da ita ƙila don ya hango wani abu ne da ya burge shi wanda ido zai iya gani, shi ya sa in wasu abubuwa daga baya sun taso zai iya rabuwa da ita cikin sauƙi ba tare da cutuwar zuciya sosai kamar macen ba, don tun farko bai ba da zuciyarsa gaba daya ba, gaskiya wannan nazari ne kawai.

Mace in namiji ya nuna ƙaunarta takan dan dakata ta lugwigwita maganar tukun na dan wani lokaci, ta sanya lamarin a cikin mizani ta gani anya wannan ba zai ci amanata ba? Matsalar kuma ba wasu hanyoyi take da su na gano cewa ba zai ci amanar tata ba sama da mu'amalarta da shi, wai tanan ne za ta fahimce shi, in ma uwarta ta nemi jin wasu 'yan abubuwa na sirri a tsakaninsu ba dole ne ta gaya mata ba, saboda tana ganin cewa wannan abu ne da ya shafi rayuwarta.

To in aka sami akasi sai ya yi mata mummunan tasiri, ya hana ta kwanciyar hankali, ta riƙa ganin kanta tsirara a gaban mutane, ta tuna irin maganganun da aka gaya mata na ta bi da lura amma ta watsar, sai ta ji cewa a shirye take ta yi komai don rayuwarta ta riga ta lalace, to namiji a irin wannan matsayin ba kowa ba ne, duk lafazin da ba ka taba zato ba za ta ambato shi, ba ta damu da abin da zai biyo baya ba, wadanda za su iya magance lamarin su ne uwayenta, yadda za su jawo ta a jiki, su dauke hankalinta wajen nuna ƙaunarsu gareta gami da fada mata maganganu masu dadi, wadanda za su mantar da ita halin da ta shiga.

Sai dai kuma uwaye ba su cika yin hakan a irin wannan lokacin ba, kodai don barinta ta dandani abin da ta janyo da hannunta, ko kuma saurarawa har lamarin ya dan yi sauƙi, ita kuwa a daidai wannan lokacin za ta fara neman mafita, wata za ta yanke hukuncin cin mutuncin mijin ne ta kowace hanya, albashi duk abin da zai faru ya faru, wata kuma sai ta daura kaifukan gaba daya a kan wace za a auro, ta ga cewa ita ce take nema ta ƙwace mata jin dadinta don haka sai dai Allah ya raba su, za ta fuskance ta da duk abin da take da shi.

Abubuwan da suka bayyana a irin wannan matakan da ake ɗauka su ne ake kira kishi. In dai haka ne to ba dole ne ya bayyana ga namiji ba. Sau ɗaya na ga wani mutum da matarsa take koyarwa a wata makarantar firamare wanda suka kwashe shekaru da dama suna tare, sai dai duk daɗewar nan suna ɗan samun wasu 'yan matsaloli a tsakaninsu. In kuma an samu ɗin wani abokin aikinta ne yake shiga tsakaninsu, domin mijin har makarantar yake biyo ta, da wannan sai abokin aikin ya zama cikakken alƙalin da su biyun duka suka yarda da shi, don yakan kebe da kowa ya gaya masa laifinsa, ya kuma ja hankalinsa, ya gaya masa maganganu masu dadi yadda zai haƙura ya ci gaba da zama da masoyinsa cikin kwanciyar hankali.

To bayan wasu shekaru sai zaman ya gagara gaba daya, har dai aka haƙura da auren kowa ya kama gabansa, amma abin da zai daure kai shi ne, alƙalin da yake shiga tsakani kuma shi ne ya fito a matsayin manemi, da bincike ya yi nisa an gano cewa tsohuwar matarsa ce ta nuna ƙaunar abokin aikin nata a sakamakon irin ban bakin da yake mata, da irin ƙoƙarin da yake yi na ganin sun zauna lafiya, tanan ne ƙaunarsa ta kurdada zuciyarta, wancen auren na ƙarewa kuma ta ga ba wanda ya dace ta zauna da shi in ba abokin aikin ba, shi kuma tsohon mijin ya maka su a kotu kan cewa bai tarda ba, yana ganin dan tsakiyannan shi ne ya fitar masa da mata don ya sami damar aure masa ita.

A ƙarshe dai ya fadi a gaban alƙali cewa bai damu ba kowa ya aure ta amma ba wannan dan tsakiyan ba, shi kuwa abokin aiki tunda ya ga mata fara sal kyakkyawa wace bai taba zaton zai iya neman irinta ba ta nuna tana son shi sai kawai ya miƙa wuya, a dalilin rashin samun abin da zai hana shi nemanta, alƙalima ya tambayi tsohon mijin in shi ne ya rabu da matar ya ce "I", ya sake tambayarsa in yana da haƙƙin sai ya yarda da mutum kafin tsohuwar matar tasa ta aure shi, ya ce "A'a" daganan aka watsar da ƙarar saboda rashin hujjar yinta.

Post a Comment

0 Comments