Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata - 11: Kishin Ƙauna



Idan kuwa ya kasance ba ta ƙaunar wata ta shugo gidan don kar su ci arziƙi tare, ko tsoron abin da zai same ta in ta bari aka ɗaura auren a hangenta, wannan ba kishin namiji ba ne. Kanta kawai ta sani. Bar batun kare mutuncin mijin, a irin wannan yanayin ita ce da kanta za ta ci masa mutuncin a gaban kowaye, kuma a ko'ina ne ma. Za ta iya zaginsa a gabansa ko a bayan idonsa. Bar batun kare rayuwarsa yadda zai kasance da iyalinsa cikin kwanciyar hankali wanda haka ya dace ta yi, za ta ma iya neman rayuwarsa ta...

Kundin Ma'aurata - 11: Kishin Ƙauna

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Waɗannan kalmomi abubuwa ne mabambanta, amma ana ganin cewa inda ƙauna take ne kishi yake samun wuri ya maƙale, sai dai yadda ake fassara kishin nan ne ake samun sabani ko a gaza ganewa ma gaba daya, mace wai in tana son namiji shi ne za ta riƙa  kishinsa, wannan ita ce fassarar da kowa ya sani, amma in kishin ya yi yawa sai ya zamo kanta kawai take so, ba wani abu na kusa ko na nesa da ya hada ta da mijin ko misƙala zarratin, in ma abu ya yi ƙamari tana iya raba shi da duniyar kacokan don yana neman ya shiga tsakaninta da jin dadinta! In da za ka fadi wannan a wani wuri kusan ba wanda zai yarda haka lamarin yake.

Amma abin baƙin ciki haka maganar take a zahiri dari bisa dari, idan ya kasance mace ba ta son namiji ya ƙara mata saboda tsoronta da halin wace yake ƙoƙarin auren, tana ganin in ya aure ta zai sha wahala ba zai ji dadin rayuwarsa ba, a nan tana kishin mijinta saboda ƙaunar da take masa, ba za ta bari wani abu ya shafi rayuwarsa ko dukiyarsa ko mutuncinsa ba, wannan kishi ne na gaskiya, haka ake son kowace mace ta zama.

Duk macen da ta ji cewa mijinta ya kalli wata mace amma saboda saninta da cewa bai da ƙarfin da zai iya riƙe su duka tare da yaranta, lura da irin halin da ake ciki a yanzu na rashi da halin ni-'yasu a wasu wuraren, sai ta nuna ƙiyayyarta da auren ba da wace za a aura ba, anan za a iya cewa tabbas kishinsa take yi da gaske, saboda ta san in wata ta shugo ƙila ba za ta iya jure abin da ita take jurewa ba, za ta riƙa watsa shi a duniya cewa gidansa ba komai, matansa suna cikin yunwa da sauransu, sai ta yi ƙoƙarin kare sunansa, wannan tabbas kishi ne amma mai kyau.

Idan kuwa ya kasance ba ta ƙaunar wata ta shugo gidan don kar su ci arziƙi tare, ko tsoron abin da zai same ta in ta bari aka ɗaura auren a hangenta, wannan ba kishin namiji ba ne. Kanta kawai ta sani. Bar batun kare mutuncin mijin, a irin wannan yanayin ita ce da kanta za ta ci masa mutuncin a gaban kowaye, kuma a ko'ina ne ma. Za ta iya zaginsa a gabansa ko a bayan idonsa. Bar batun kare rayuwarsa yadda zai kasance da iyalinsa cikin kwanciyar hankali wanda haka ya dace ta yi, za ta ma iya neman rayuwarsa ta raba shi da duniyar gaba daya, abin da kake matuƙar ƙauna kare shi kake yi ba kashe shi za ka yi ba, macen da ta ci wa mijinta mutunci a gaban jama'a saboda wata macen, ta ina za ka iya gamsar da mutane cewa tana yin duk abin da za ta iya don kare mutuncinsa?

Macen da ta nemi rayuwar mijinta a dalilin zai ƙara aure, ta ina za a yarda da cewa saboda kare rayuwar mijin ne kar amaryar da kashe shi shi ya sa ita za ta fara kashe shi? Kishi daban son kai daban, matan yanzu (wasu) suna yin duk abin da za su yi ne don ganin sun zauna su kadai, wata in ta ji cewa mijinta zai ƙara aure takan yi ƙowari ta san matar da za a aura don ta ja kunnenta, ko ta tsoratar da ita cewa ita fa muguwa ce in ta ga za ta iya zama da ita to bismilla, wata in ta ga ta wajen amaryar babu wata riba takan kwano kan maigidan ta ja masa kunne.

Za ta nuna masa ne cewa in fa yana neman zaman lafiya ne da kwanciyar hankali to ya bar ta ita kadai, in kuma tashin hankali yake nema to ya ƙaro wata matar, mun ga wadanda suka kashe mazajen a dalilin wannan haukar, a cikinsu wata ta ce gwara duk su mutu da dai mijin ya yi mata kishiya, na ga wace ta kashe kanta a ranar auren, wannan kam ta fi gasgata kanta a kan abin da take fada.

Na ga wace ta sa aka kori mijin a aikinsa, wanda hakan ta kai ga kamuwarsa da cuta har ya rasa ransa, na ga wace ta nemi ran mijin kai tsaye, waɗannan zai yi wahala ka fassara maganar da cewa tsabar ƙaunarsa kawai ta sa ta ga cewa gwara ma  ta raba shi da duniya don ƙaunar ta ƙara danƙo, a waɗannan hujjoji muke so a gane cewa kishin da mata suke yi yanzu bai da alaƙa da tsaftataccen kishin da matan Annabawa da sahabbai suka yi, duk wata mace mai nuna masifar kishi a yau kanta kawai take so, kuma za ta iya yin komai don ganin ta isa wurin da take hari, sauran dabara kuma ta rage wa mai shiga rijiya.

Shi maigidan ya dace ya dauki wani ƙwaƙƙwaran matakin da zai yi maganin gidansa, ko don ba wa kansa da iyalinsa kariyar da ake buƙata, daga cikin dalilan da suke sa namiji ya yi sha'awar ƙara aure akwai fitina irin na mace, wani yana ganin in ya ƙaro wata matar zai sami kwanciyar hankali, a maimakon in zai yi auren a wannan dalilin ya samo tsohon hannu, wato wace idonta a bude ne kan lamarin, sai ya dauko yarinyar da ba ta san komai ba, a ƙarshe kuma a yi ta zaluntarta.

Kishin mata kala-kala ne, mai sauƙin a ciki shi ne wanda mace za ta yi ta bala'i da fada da kowa a cikin gida, ina nufin wanda ƙiyayya da gabar mace suka fito sarari, irin wannan ko ba a taimaki yarinyar da aka shugo da ita ba yau da gobe yakan koya mata ilimi, a ƙarshe takan iya kare kanta, wani sa'in ma in ya zo da rikici reshe yakan juya da mujiya, ka ga uwar gidan ta komo abar tausayi.

Mummunan kuma mai mugun wuyar sha'ani shi ne wanda uwargidan take boye ƙiyayya da ƙeta a cikin zuciyarta, take bayyana ƙauna da soyayya ga kishiyar, amma ta riƙa yi mata wasu ƙulle-ƙulle ta ƙasa wadanda yarinya sabuwar aure da wahala ta san abin da ake ciki, yana da kyau maza su riƙa bincike, irin wannan kishin shi yake yaduwa a 'yan shekarunnan, sai ka ga an auro yarinya ƙarama amma ita take shan baƙar wahala a hannun mijinta da kishiyarta, in da za ka yi bincike sama-sama za ka taras tabbas yarinyar dabi'unta ba su da kyau, wanda zahiri ba haka abin yake ba, tura ta aka yi ta hau ba ta sani ba.

Post a Comment

0 Comments