Tsakure:
Karin magana a matsayin
nau’i na adabin baka na Hausa ɗamfare yake da tunani da tsarin rayuwar al’umma
tattare da alƙiblarsu a kowane lamari na rayuwa. Shi ya sa
ya zama tamkar rumbu ne na adana falsafa da al’adun al’umma. Da yake rayuwar kowace
al’umma tana tattare da lafiya da cututtuka da kuma naƙasa, shi ya sa wannan maƙala ta dubi ɓurɓushin
nakasa a karin maganar Hausa. An kalli nakasa da nau’o’inta, sa’annan aka nazarci
kare-karen magana masu ɗauke da hoton nakasa a kowane nau’i. Sakamakon
nazarin ya gano cewa, a zahirance, irin waɗannan karin magana suna fito da irin ƙalubalen da naƙasa ke zamo wa mai ɗauke
da ita wajen gudanar da al’amuransu na rayuwar yau da kullum. Haka kuma karin maganar
na fito da irin tunanin al’umma a kan ɗabi’u da halayyar mai ɗauke
da kowane irin naƙasa. An ɗora
nazarin ne bisa ma’ana ta zahiri a tsarin karin maganar da aka yi amfani da su.
Ɓurɓushin Naƙasa a Adabin Hausa: Tsokaci
Daga Karin Magana
Na
Abdullahi Mujaheed
Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
Waya: +2348069299109, +2348156747550
i-mel:mujaheedabdullahi@gmail. com
1.0 Gabatarwa
Naƙasa na nufin tawaya ko gaza
ko raunana, (CNHN, 2006: 356). Saboda haka,
nazarin naƙasa fage ne da ke ƙoƙarin bayyana batutuwan da suke ɗamfare
da zamantakewa da al’adu da siyasa waɗanda suka jiɓanci
yadda ake kallon nakasa da nakasassu[1].
Ita kuwa karin magana
ɗaya
ne daga cikin sassan adabin baka da Hausawa ke amfani da ita domin ƙawata
zance ya yi armashi. Kenan, karin magana zance ne a dunƙule
mai faffaɗar ma’ana, ƙunshe da sharhi kan rayuwar al`umma cikin hikima
da fasaha. Shi ya sa karin magana ya zama rumbun ajiye al`adu da tunani da ɗabi’u da kuma tarihin al`umma. Saboda haka,
karin magana nazari ne na rayuwa a dunƙule, cikin gajerun maganganu
da misalai irin na hikima, Zarruk da Alhassan (1982:3). Masana da manazarta (Edgar,
1919 da Rattery, 1913 da Greene, 1966 da Skinner, 1966 da Yunusa, 1977 da Furniss,
1966 da Bunza, 2013 da Bada, 1995 da Malumfashi da Ibrahim, 2014 da Amin, 2013 da
Koko, 2011 da sauransu da dama) bisa mabambantan manufofi sun sha rubdugu a kan
karin magana da ma’ana da nau’o’i da kuma ƙumshiyarsa. Don haka, wannan maƙala ta ta’allaƙa kan nazarin nakasa da nau’o’inta a
ƙumshiyar karin maganar Hausa.
2.0 Naƙasa Bisa Faifai
Naƙasa kalmar Larabci ce da Hausawa
suka aro suke amfani da ita. A Larabce, kalmar tana nufin rangwamen wani abu, wato
rashin cikar wani abu. Wannan kalmar Hausawa sun aro lafazi da ma’anarta suke amfani
da ita kamar yadda take a Larabci. Sai Bahaushe ya dubi kalmar ta fuskar kalmomin
fannu waɗanda suka danganci
jikin ɗan Adam, da ma’anar
rangwamen ɗaya daga cikin gaɓuɓuwan
jikin mutum kamar ido ko yatsu ko hannu ko ƙafa ko hankali a sanadiyyar
wata cuta ko haɗari
ko shaye-shaye, (Sarkin Gulbi, 2007:37).
A ma’ana ta zahiri kuwa, nakasa na nufin
tawaya ko gaza ko raunana, (CNHN, 2006: 356).
Saboda haka, naƙasa ita ce wata tawaya a cikin
ayyukan jiki ko kuma wahalhalun da ake samu wajen wani sanannen aikin da mutum kan
samu wajen gudanar da hidima ko aiki[2]. Shi ya sa Bunguɗu, (2015:90) ya ce, duk wata tawaya da aka samu a
wata gaɓa ta jikin mutum ana
kiran ta nakasa, wannan kuwa har da taɓin
hankali, (Bunguɗu,
2015:90).
3.0 Karin Magana Masu Ɓurɓushin Naƙasa
Da yake adabin Bahaushe bai bar komai
ba dangane da rayuwarsa ta yau da kullum. An lura cewa mutanen da suka sami kansu
cikin wata halayyar rashin lafiya na naƙasa, rayuwarsu ta bambanta da ɗabi’un
rayuwar sauran masu cikakkiyar lafiya, (Bunza, 2006: 191). Wannan shi yake gina
irin tunanin da ake ɗora karin maganar Hausa mai ɓurɓushin
naƙasa bisa kai, shi ya sa akan
sami karin magana da Bahaushe ke ambaton wasu masu nakasa ga jiki don a tausaya
masu, ko domin a nuna halinsu, ko wautarsu, ko alaƙarsu, (Koko, 2011: 24). A nan, za a taƙaita ga ɓurbushin
makanta da kuturta da gurgunta da kurumta ne a karin maganar Hausa.
3.
1 Makanta
Makanta
na nufin rashin gani, (CNHN, 2006:322). Saboda haka makaho shi ne wanda ba ya gani,
mace ana ce da ita makauniya, jam’i makafi, (CNHN, 2006: 321). Makanta naƙasa ce da ta shafi rasa idanuwa
biyu saboda kamuwa da ciwon ido ko haɗari
a lokacin yaranta ko bayan girma, (Sarkin
Gulbi, 2007: 37). A cewar Bunza (2006:192), makanta ba wata naƙasa da ke taɓa
hankali ba ce, ko ta raunana tunanin masu ita. Makaho a kallon Bahaushe mutum ne
mai yawan musu, da wayo da son jayayya. Watakila saboda rashin ganin da ba ya yi,
yana ganin kamar ana fakewa gare shi ana raina masa wayo. Don haka, duk wani abu
masu idanu suka faɗa
sai ya yi musu don a san ba a fi shi ba,
(Bunza, 2006:192).
Saboda haka, wasu karin maganar masu ɓurɓushin
makanta suna ƙunshe
ne da hoton irin wannan wayo da musu da son jayayya na makafi ko makaho kamar yadda
aka san su a zahirance. Misali:
Ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa.
Hannu da hannu cinikin makaho.
In ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka
dutse.
Makaho na da ido amma ba na ganin gari ba.
Sau ɗaya
gyaɗar makaho ke ƙonewa.
Da
zarar ka ji batun ‘ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa’,
to akwai batun tsananin wayo da rashin yarda. Domin makaho ba ido ne da shi ba,
don haka ɗinyarsa ta nuna a hannunsa
kawai. Haka batun yake in an ce ‘hannu da
hannu cinikin makaho’. Haka nan, wayon makaho ya sa shi takalar wasan jifa idan
ya taka dutse, wayon nasa kuma shi ya sa bai yarda gyaɗarsa
ta ƙone
sau biyu ba. Abin lura a nan shi ne, ire-iren waɗannan
karin magana suna jaddada cewa nakasa ba kasawa ba ce, don kuwa ko da makaho ya
rasa ido, sai aka same shi da wayo wanda wani mai idon ma bai da shi. Ga shi kuma
da tsayin daka, shi ya sa ma yake da musu da son jayayya.
Har ila yau, akwai kuma wasu karin maganar
da ke bayyana hoton rashin gani ga makaho da kuma yadda rashin ganin ya zame masa
ƙalubale.
Misali:
Allah na gani ake cutar makaho.
Allah shi ke gyara tuwon makauniya ya yi daɗi.
Babu ruwan makaho da madubi ko an sawo daga Turabulus.
Bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne.
Na raina damben makaho ko ya shirya.
Rashin sani, makaho ya taka sarki.
Waɗannan
misalan karin magana sun nuna cewa duk da irin wayo da musu na makaho amma haka
nan ake cutarsa saboda ba shi da idon da zai gani a lokacin da ake shirin cutarsa
ko ake cutar da shi. Shi ya sa ma dogaro ga Allah shi ke sanya har makauniya ta
tuƙa
tuwo ya yi daɗi, ba don tana gani
ba, kamar yadda makaho ba shi da idon da zai iya duba fuskarsa a madubi ko daga
ina aka ƙera
madubin kuwa. Hakan ya sa bakin rijiya bai
zama wurin wasan makahon ba, gudun kada ya faɗa.
Kazalika, in ba a rashin sani ba, me zai kai makaho taka sarki?
Abin lura a nan shi ne, ire-iren waɗannan
karin magana ana amfani da su a zantukan yau da kullum domin yi wa al’umma hannunka-mai-sanda
domin su tsinkayi wasu darussa na rayuwa, amma a ma’ana ta zahiri, maganganun suna
fito da ɓurɓushin
nakasa cikinsu ta hanyar bayyana rangwamen gani da abin da ya haifar ga makafi.
Duk da dai Allah da ya yi makaho shi ke masa
ɗan jagora.
3. 2 Kuturta
Kuturta wata irin cuta ce da ake ɗauka
daga iska wadda take ɓata
fuska da sauran jiki, tana riƙe
jijiya ta guntule yatsu. Saboda haka kuturu shi ne mutumin da cutar kuturta ta kama
shi har yatsunsa suka gutsure, mace kuma ana ce da ita kuturwa, jam’insu kuma kutare,
(CNHN, 2006:258). Kuturu a al’adar Bahaushe mutum ne mai saurin suƙewa, da fushi da baƙar magana. A ganin Bahaushe,
wannan ba ta rasa alaƙa
da yanayin cutar da ke damun sa ba. A mizanin zuciyar kuturu ta wuce min sharrin
domin ko da kansa yana fushi balle da wani can da ba shi ba. Duk wata magana, ko
aiki, na kutare Bahaushe na ɗora
shi a kan sanin da ya yi wa kuturu na saurin fushi da zuciya, (Bunza, 2006:192). Saboda haka, karin magana mai
ɓurɓushin
kuturta ana gina su ne bisa wannan tunani na sanin da aka yi wa kuturu na saurin
fushi da zuciya da kuma baƙar
magana. Misali:
An
ce da kuturu ga yatsu, ya ce ; “Me zan yi da su?”
“Da
haka muka fara”; kuturu ya ga mai ƙyasfi.
Kowa
ya ci ladar kuturu ya masa aski.
Naci,
damben kuturu.
“Yaushe
kuma?”; an ce da kuturu ka gama lafiya.
In
ba a kwaɗo da kuturu, a ba shi daddawarsa.
Waɗannan
misalai sun nuna ƙarara
yadda kuturu ke da saurin fushi a zahiri, shi ya sa ma a ganinsa ba abin da zai
yi da yatsu, tun da bai da su. Ƙyasfi
wata cuta ce da take haifar da tamuƙewar
fata da sauya mata launi wanda ya bambanta da nata na asali. Da yake ita ma cutar
kuturta tana da alaƙa
da tamuƙewar
fata kafin daddatsewar gaɓoɓi,
Shi ya sa da ‘kuturu ya ga mai ƙyasfi, ya ce su ma kutaren
da haka suka fara’. Bugu da ƙari, lura da naci da fushin
kuturu ya sa aka ƙirƙiri ‘naci damben kuturu’, haka nan ko da ‘aka ce wa kuturu ka gama lafiya; baƙar magana ya mayar cewa; ‘yaushe kuma?’. Shi a ganinsa, tun da ya
kuturce, batun gamawa lafiya bai ma taso ba! Saboda haka, sanin hali ne ya sa karin
maganar Hausa ya nuna in har ‘ba a kwaɗo da kuturu, to
a ba shi daddawarsa’ shi ne mafi a’ala.
Wani abin lura kuma shi ne wasu karin
maganar ana gina su ne ta dubi da irin larurar da kuturun ke ɗauke
da ita ta rashin yatsu, sai karin maganar ya bayyana gazawarsa kan wani al’amari.
Misali:
Allah
da ikonsa kuturu ya hau giwa.
Ba
zai yiwu ba, wankan kuturu da sabulu.
Komi
da mazauninsa, an sa wa kuturu ankwa ta saɓule.
Ƙwace
goruba hannun kuturu ba wani abu ba ne.
Yau
da kallo, an sa kuturu murzar barkono.
Kuturu
ya so dambe babu yatsu.
Ba
a yabon ɗan kuturu, sai ya girma da
yatsu.
Waɗannan
misalai duk sun nuna a zahirance yadda kuturta a matsayin nakasa ta zama ƙalubale ga rayuwar masu fama
da ita (kutare), ta yadda nakasar take hana su gudanar da wasu al’amuran da masu
yatsu ke gudanarwa. Alalmisali, in dai ba ikon Allah ba, ta yaya kuturu zai hau
giwa tun da ba yatsu ne gare shi ba? Haka kuma, sabulu yana da santsi shi ya sa
ba zai yiwu kuturu ya yi wanka da shi ba don ba shi da yatsun da zai riƙe sabulun. Duk dai cikin rashin
yatsun; idan aka sa wa kuturu ankwa saɓulewa
za ta yi, cikin sauƙi
za a ƙwace
masa goruba, ba kuwa zai iya murzar barkono ba; kamar yadda ko ya so dambe ba ya
iyawa tun da duk ayyuka ne da ake gudanar da su da taimakon yatsu. Da yake ma ita
cutar kuturta ana gadonta, shi ya sa ‘ba a
yabon ɗan kuturu, sai ya girma da
yatsu’. A dunƙule, waɗannan
misalai na karin magana, sun bayyana yadda kuturta (nakasa) ta zama barazana ko
ƙalubale
ko kuma tasku ga masu nakasar kuturta wajen gudanar da wasu al’amura na rayuwa.
3.
3 Gurgunta
Gurgunta
naƙasa
ce wadda kan hana wa mutum tafiya daidai, wannan daidai yake da gurguntaka ko gurgunci
ko ɗingishi. Kenan gurgu shi ne
wanda yake tafiya ba kamar yadda jama’a ke yi ba, saboda illar da ta sami ƙafa ko ƙafafunsa. Idan mace ce kuma
ana ce da ita gurguwa, jam’i guragu, (CNHN,
2006:176). A al’adance kuwa, gurgu shi ne wanda ya rasa ƙafafunsa biyu, ko ya rasa
ɗaya ita kawai. Ta karye ne,
ko ta shanye, ko tsawonta bai kai ba, duk gurgu ne a al’ada. Al’adar Bahaushe na
kallon gurgu wani irin shaƙiyyi
na musamman, kuma ɗan
fitina da jidali. Duk wata faɗa
aka ce wa Bahaushe da gurgu ciki, ba ya musu balle ya yi jayayya don kare gurgu, (Bunza, 2006:192). Irin wannan tunani ya haifar
da karin magana kamar, ‘Maƙetaci mijin gurguwa, wanda
ya sayar da jaki ranar tafiya. ’
Bugu da ƙari, duk wani lamari na tafiya
ko amfani da ƙafa
ba ya zuwa da sauƙi
ga gurgu, shi ya sa galibi karin magana mai ɓurɓushin
gurgunta take bayyanawa ƙarara
yadda lamarin yake ga gurgu. Misali;
Da
kamar wuya, gurguwa da auren nesa.
Gurgu
ba ya koya wa gurgu tafiya.
Gurguwar tsanya da wuri take fara ɓula/tiƙa.
Gurgu bai canza tafiya.
Kaɗan kenan, an wa gurgu ƙafar laka.
A
waɗannan misalai an nuna a fili
yadda auren nesa ya zamar wa gurguwa jidali musamman a zamanin da, zamanin da ake
tafiyar ƙasa.
Idan kuwa har gurgu bai iya tafiya ba ko kuma yana tafiyar ba kamar yadda lafiyayye
ke yi ba, to ta yaya zai koya wa wani gurgun tafiya? Kai hatta tsanya, in dai gurguwa
ce, to da wuri take fara tiƙa.
Kuma duk yadda ya so, gurgu ba ya canza tafiya, wannan ya jaddada yadda tafiya ko
duk wani amfani da ƙafa
ke yi yana zama babban ƙalubale
ne ga gurgu sakamakon nakasar da yake tare da ita (gurgunta).
3.4 Kurumta
Kurumta naƙasa ce da take da alaƙa da lalacewar kunne ta yadda
zai daina jin motsi ko maganar wani. Saboda haka kurma shi ne mutumin da ba ya jin
magana sam, ko sai an yi magana da ƙarfi
kafin ya ji, kuma ba ya iya magana sosai yadda za a fahimta, (CNHN, 2006:256). A wasu lokutan, akan kira mutumin
da ba ya ji sosai kuma ba a gane maganarsa bebe, mace kuwa bebiya, yayin da jam’insu
ke zama bebaye (CNHN, 2006:43). Kenan, wanda bai ji gaba ɗaya
shi ne kurma, mai ji kaɗan-kaɗan
kuma shi ne bebe. Da kurma, da bebe, duka al’ada gurbin mahaukata ta aje su. Ba
mahaukata ne tuburan ba, amma dai ana yi masu uzuri ga ayyukansu idan sun ɗan
aro na mahaukata. Idan aka ga mutum kurma ne al’ada na yi masa uzuri, domin rashin
ji na taɓa hankali, (Bunza, 2006:192).
Irin wannan tunani da kallon da ake yi
wa kurame da bebaye, suna fitowa ƙarara
a zubin wasu karin magana masu ɓurɓushin
nakasa. Misali:
“Gara
kowa da ni”, in ji matar bebe.
Muƙami, bebe da rediyo.
Ruguduma, an kama kurma da kwartanci.
Duk waɗannan
misalai sun nuna irin wannan ‘kallon mahaukata’ da ake yi wa kurame da bebaye. Shi
ya sa ma matar bebe take ganin gara kowa da ita, tun da ta san wane ne mijinta.
Yayin da ake kallon sabon salo ne ko wani ‘muƙami bebe da rediyo’.
Ga kuma wauta ƙarara
inda aka kama kurma da kwartanci.
Bugu da ƙari, kuturta kamar sauran
nau’o’in naƙasa,
ana samun karin magana da suka nuna irin tasku da masu fama da ita suke fuskanta
yayin gudanar da lamurran rayuwar yau da kullum. Misali:
Abin
faɗa na mai baki ne, bebe sai
ka dangana.
Allah kaɗai
ya san karatun kurma.
Da
magana bakin kurma sai ranar da ya sami baki.
Goron magana ga mai baki, kurma sai shi dangana.
Babu shakka waɗannan
misalai sun nuna hoton naƙasa
da kuma gazawar da naƙasar
ta haifar wa masu fama da ita (wato kutare), a misali na farko mun ga yadda aka
nuna in dai abin faɗa
ne shi bebe sai dai ya haƙura,
kamar yadda shi ma kurma a misali na huɗu
aka nuna dangana ce tasa, domin goron magana na mai baki ne. A misali na biyu kuwa,
an nuna cewa Allah ne kaɗai
ya san karatun kurma ba mutum ba, tun da mutum ba ya jin sa, don ba furta karatun
yake ba. Kenan, sanin abin da ke zuciyarsa sai dai Allah (SWT). Ko da kuwa da magana bakin kurma sai ranar da
ya sami baki, kamar yadda aka nuna a misali na uku.
4. 0 Kammalawa
Kamar
yadda takenta ya nuna, wannan maƙala
ta tattauna ɓurɓushin
naƙasa
ne a adabin Hausa inda aka yi tsokaci a kan karin magana. An fi mayar da hankali
ne wajen kallon tsarin misalan karin maganar da aka kawo, aka fayyace yadda aka
sami ɓurɓushin
naƙasa
a zahiri cikinsu. Sa’annan kuma an kalli yadda karin maganar ta fito da ɗabi’u
da halayyar masu ɗauke
da nau’o’in naƙasa
kamar yadda al’adar Bahaushe ta bayyana su. An taƙaita ga nau’o’in nakasa huɗu
ne wato gurgunta da makanta da kurumta da kuma kuturta, duk da ba su kenan ba. Su
ma karin maganar da aka buga misalai da su ba su kenan ba, domin kuwa ba a rasa
ruwa a ƙasa
sai in ba a tona ba. A ƙarshe
an rattaɓo karin magana masu
ɓurɓushin
naƙasa
a matsayin rataye. Hakan ya sake bayyana yadda ire-iren waɗannan
karin magana suke yin tasiri wajen bunƙasa
adabin Hausa baya ga nuni ga ɓurɓushin
naƙasa
da suke yi.
8. 0 Rataye: Wasu Karin Magana Masu Ɓurɓushin Nakasa
1.
“Abin ana so dai?”; an ba
makaho hanjin jimina.
2.
Abin banza hanci babu ƙafa.
3.
Abin faɗa
na mai baki ne, bebe sai ka dangana.
4.
Abin wani abu ne, faɗar
makaho da daddare.
5.
“A ja mu a kai”, an ba uwar
makaho kashi.
6.
“A ja mu a ba mu kashi”, in ji uwar makaho.
7.
Allah kaɗai
ya san karatun kurma.
8.
Allah da ikonsa kuturu ya
hau giwa.
9.
Allah da ya yi makaho shi
ke masa ɗan jagora.
10. Allah na gani ake cutar makaho.
11. Allah shi ke gyara tuwon makauniya ya yi daɗi.
12. Allah ke gyara tuwon makauniya ba don tana ganin
sa ba.
13. An ce da kuturu ga yatsu, ya ce ; “Me zan yi da
su?”
14. Ba a bambance baccin makaho da idonsa buɗe.
15. Babu ruwan makaho da madubi ko an sawo daga Turabulus.
16. Bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne.
17. Ba zai yiwu ba, wankan kuturu da sabulu.
18. Ba a yabon ɗan
kuturu, sai ya girma da yatsu.
19. Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.
20. “Da wari”; “An ce “makaho ga ido”.
21. “Da haka muka fara”; kuturu ya ga mai ƙyasfi.
22. Da magana bakin kurma sai ranar da ya sami baki.
23. Ɗinyar
makaho ta nuna a hannunsa.
24. “Duk ɗaya”;
makaho ya yi dare.
25. “Gara kowa da ni”, in ji matar bebe.
26. Garin gyaran gira an rasa ido.
27. Ga wake ya yi damo na neman ya makance.
28. Gadauniya, makauniya da yekuwa wuta.
29. “Gane min hanya”; makaho ya so gulma.
30. Ganin hadarin makaho, baƙi ƙirin, fari fat, ja wur.
31. Gurgu ba ya koya wa gurgu tafiya.
32. Gurguwar tsanya da wuri take fara ɓula/tiƙa.
33. Gurgu ba ya koya wa gurgu tafiya.
34. Goron magana ga mai baki, kurma sai shi dangana.
35. Hannu ɗaya
ba ya ɗaukar jinka.
36. Hannu da hannu cinikin makaho.
37. In ba a ƙwado da kuturu, a ba shi daddawarsa.
38. In ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa, to ya taka
dutse.
39. Ido in ya mutu kwalli ba ya tayar da shi.
40. Ido ba ya mutuwa tozali ya tashe shi.
41. Kadan ba ƙarya ba, kuturu ya yi dambe
da mai yatsu.
42. Kadan ba rigimar makaho ba, ya yi kokawa da mai
ido.
43. “Kallon ka nake”, makauniya ta yi faɗa
da mijinta har kaikainiyar ka na rawa.
44. Keke ba hawan kuturu ba.
45. Komi da mazauninsa, an sa wa kuturu ankwa ta saɓule.
46. Kowa ya ci ladar kuturu ya masa aski.
47. Kuturu da kuɗinsa,
alkaki sai na ƙasan
kwano.
48. Kuturu ake wa gayya ba mai yatsu ba.
49. Kuturu ya so dambe babu yatsu.
50. Kuturun kutare mai bara da jaka.
51. Ƙafar
kuturu mutuncinta takalmi.
52. Ƙwace
goruba hannun kuturu ba wani abu ba ne.
53. Ƙaramin
kuturu ka dajine, manya sai gwalo.
54. Magaza gani, ido ya rufe.
55. Makaho ba ya shaida.
56. Makaho na da ido amma ba na ganin gari ba.
57. Makaho yana da iko ya ja wa makaho gora?
58. Makahon doki sha kasuwa, dillali ya gaji shi ma
dokin ya gaji.
59. Mai ido ɗaya
a garin makafi sarki ne.
60. Mai ido ba ya gode wa Allah har sai ya ga makaho.
61. Mai ido ɗaya
ba ya leƙa
rami.
62. Mai ido ɗaya
ba shi hawan bisa.
63. Mai ido ɗaya
kiyayi gauɗe.
64. Maƙetaci
mijin gurguwa, wanda ya sayar da jaki ranar tafiya.
65. Me amfanin farin ido ba gani.
66. Muƙami,
bebe da rediyo.
67. Mutanen kirki, damo ya ga makaho.
68. Mutuwar jiki nakasa ce.
69. Nakasa ba kasawa ba ce.
70. Na raina damben makaho ko ya shirya.
71. Na raina damben makaho ko da ya naɗe
hannu.
72. Nan yini nan kwana, an ba kuturu tallar jaki.
73. Naci, damben kuturu.
74. Rashin sani, makaho ya taka sarki.
75. Rashin sani ke sa makaho taka sarki.
76. Ruguduma, an kama kurma da kwartanci.
77. Rintse ido ba makanta ba ce.
78. Sabo da yi, makaho da waiwaye.
79. Sau ɗaya
gyaɗar makaho ke ƙonewa.
80. Tura makaho cikin rami ba wuya ne ba.
81. Tufkar makaho ta gaba ta baya tana warwarewa.
82. Wa zai ba makaho ido?
83. Yau da kallo, an sa kuturu saƙar lauje.
84. Yau da kallo, an sa kuturu murzar barkono.
85. “Yaushe kuma?”; an ce da kuturu ka gama lafiya.
[2] Wannan
ma’ana ce da Hukumar Lafiya ta Duniya, wato World Health Organization (WHO) a Turance
suka bayar a shekarar 2012.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.