Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 09: Ka Yaudare Ta



Za ka sami wanda zai tausaya wa yarinya da irin halin da take ciki, kamar talauci ko canjin addini da sauransu, sai ya fara nemanta ba tare da ya yi shawara da uwayensa ko abokai ba, kawai sai ta kware masa sai ya ba da haƙuri ya yi tafiyarsa.

Zan Ƙara Aure // 09: Ka Yaudare Ta

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Da za ka bi shawarata ba za ka taɓayunƙurin ƙara aure ba sai ka tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya, tunda ka fara ba abinda zai sa ka janye wannan yunƙuri, in ka yi haka ka yi daidai, zan ba da misali, wani mutum ne ya fara neman aure gadan-gadan, sai matansa suka miƙe tsaye, ta inda suka shiga ba tanan suke fita ba, suka sami abokansa suka marairaice musu gami da rantsuwar cewa ba za su sake bijire masa ba, da ya ji haka sai ya janye ƙudurinsa, tunda sun yi ladabi.
To ita wancan da ka fara nema ta riga ta gaya wa uwa da 'yan uwa cewar kana nemanta, meye laifinta da ka dena? In ka karbi hanzarin ta gida ka janye maganar, ita kuma wannan da ka cusa wa ƙaunarka har ta fara son ka wani abu za ka yi ka saka mata, kudi? An ce ba sa sayen ƙauna, a taƙaice dai ka cutar da rayuwarta sai dai Allah ya isa, daga ranar kuma ka zama mayaudari a wurinta da duk makusancinta, wannan a babin misali na ba ka ba shi kadai ba ne.
Za mu yi bayaninsu a rarrabe amma bari mu kawo su a dunƙule, wani yakan yi sha'awar ƙarin aure ne idan ya ga wace ya taɓanema ta baro gidan miji, nan da nan sai ya tuno tsohuwar soyayya ya bi ta, wani abokansa suke zuga shi, wani damina ce ta yi kyau ya ga yabanya, wani uwayensa ke matsa masa, wani kwalliyarta ya gani ya yi sha'awa, ko ƙoƙarinta a karatu, ko kyakkyawar dabi'arta, wani ita matar da kanta take zawarcinsa, wani bai da dalili kawai cusa kansa ya yi.
To duk irin waɗannan mutum zai kai kansa da zarar ya ga abu bai kai masa ba sai ka ga ya ja da baya ya ce ba ya yi, wani ma sai dai matar ta ga ya dauke ƙafa kawai, kwanaki wani malamin makaranta yake ba mu labarin cewa wani mutum mai ƙima da daraja ya kawo wata yarinya, ya shigar da ita makarantarsu, makarantar unguwar-zoma ce, ya yi alƙawarin zai dauki nauyinta har ta gama, nan take ya fara biya, amma bai kammala ba, wani tudu wani kwari ya sare a kan hanya, lokacin da makaranta ta dan matsa masa ya biya na zango daya ba wanda ya sake ganinsa.
Ita kanta ta yi mamaki don ko musayar yawu ba su taɓayi ba, kawai dauke ƙafa ya yi, ko ta buga masa waya ba ya dagawa, ta bi waɗanda yake shiri da su amma ba wani labari, a ƙarshe ta fara fadin ya yaudare ta, don kawai haka ta dena ganinsa kamar daukewar wutar lantarki, wani kuma shiga ƙarin auren ya yi gadan-gadan, soyayya babu kama hannun yaro, mutane na kallo suna sha'awa, sai da aka zo sa rana sai ya ce a je a yi gwaji, ana gwadawa sai ga duk suna da AS, wato akwai yuwuwar samun cutar Sikila a yaran da za su samu, sai ya ce ya haƙura.
Za ka sami wanda zai tausaya wa yarinya da irin halin da take ciki, kamar talauci ko canjin addini da sauransu, sai ya fara nemanta ba tare da ya yi shawara da uwayensa ko abokai ba, kawai sai ta kware masa sai ya ba da haƙuri ya yi tafiyarsa. Gaskiya wannan yaudara ce, wallahi wata a hannuna ta muslunta saboda wani saurayi da suka dade suna jin mu'ujizar juna tare, yayin da ya tafi Legas, ta muslunta da zammar in ya dawo za ta aure shi, gogan naka na dawowa ya tubure wai bai san maganar ba, ya ce gidansu ba za su yarda ba ko 'ya'yansa da na kishiyar za su riƙa cewa kaza da kaza.
Akwai wata ma da ta zo wurimmu bayan ta muslunta, ta ce; mijinta yana da aure na tsawon lokaci amma ba su taɓahaihuwa ba, sai ya musluntar da ita, ya aure ta, ta haifa masa yara biyu, daganan ya sake ta, ba tare da lefin a zo a gani ba, dama abinda yake nema kenan yara, kuma ya samu, ya zai yi da amincewar data yi masa oho, har maganar da muke cikinnan ta kasa zaman aure saboda irin ƙaunar da take masa, da kuma irin dadin da ta ji a baya, in ta tuno sai kawai ta fashe da kuka, ta yi auren ta sake fitowa.
Wani kuma ya fara neman auren ne bai tuntubi babansa ba, lokacin da abu ya yi nisa aka ce ya fito lokacin ne ya sami babansa, shi kuma baban ya ce bai yarda ba, yaushe ya yi ta farko da zai ce zai ƙara? Ya bari sai ya yi gidansa na kansa ya sami jari mai ƙarfi in ya so sai ya ci gaba, haka dai ya sami uwayen yarinya ya yi magana da su, yarinyar kuma sai daina jin duriyarsa ta yi, a ganinsa ya gama kenan, wani ƙazantar matar ta sa ya fara neman aure, da aka yi mata fada ta ce ta gyara, shikenan wai an daidaita sai ya watsar da wancan.
Wani ya yi ƙudurin ne a dalilin matarsa ba ta haihuwa, Allah cikin ikonsa, shekarar da ya fara neman wata a shekarar ta sami ciki, har ma sun dan sami hayaniya a tsakaninsu matar ta tafi gidansu shi kuma ya ƙi zuwa biko, da ya ji bullar maganar cikin shikenan ya watsar da maganar ƙaro aure ya dawo da matarsa, duk dai maganar da muke yi ita ta biyun da mutum ya dasa mata ƙaunarsa sannan ya watsar da ita me yake tunanin ya yi, yaudara?

Post a Comment

0 Comments