Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 08: Kafin Ka Fara Tunanin



Na taɓazama da 'yan ƙasar Ethiopia, ni ne ma wakilin angon, ɗan Nigeria ne, ya musluntar da ita ya aure ta. Soyayya ba kama hannun yaro. Kullum tana jikinsa. Ba ta yarda ta yi nesa da shi. Kai ko titi za a tsallaka ba za ta yarda ya tsallaka ya bar ta ba, sai dai su tafi tare.

Zan Ƙara Aure // 08: Kafin Ka Fara Tunanin

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Auren fari abu ne mai sauƙi, haka ma in mutum ya rasa matarsa a dalilin rasuwa ko rabuwa, duka dai zai zauna da mace guda ne, in za ka iya ba ta haƙƙoƙinta na ci da ciyarwa kamar yadda ake fadi a dunƙule, kuma ka ba ta sutura da matsuguni shikenan ka gama komai, sabanin a ce akwai wata matar da za ka ƙaro, galibinmu maza ba mu san wannan ba, gaskiya ga namiji mai son ƙara aure ba kawai in yana da abincin da zai ba su da sutura da za su saka, da matsuguni shikenan ya gama komai ba.
Dole sai yana da zarafin da zai iya daidaita su a zauna lafiya, da yawan maza na ƙara aure bayan ba su da ƙudurar da za su iya daidaita zamantakewar matansu, masamman waɗanda fitinar ta farkon  ta sa ya yi tunanin ƙarin auren, rarrabuwar kan mata kan haifar da rugujewar gida gaba daya, ya bata tarbiyyar yaran, a sami tabkekiyar baraka tsakanin maigida da 'yan uwansa masamman uwayensa, in ba a yi dace ba matan duk su shiga bokaye, in har hakan ta faru, to 'ya'yanka sai a hankali, sai dai a nemi kariyar Allah kawai amma an riga an yi nisa.
Wata rana na ji wasu mata suna hira kan wani gida yadda maigidan ya kasa riƙe gidansa, nan da nan wata a cikinsu take cewa "Ragon maza ne wallahi, da a ce maigidammu ne wallahi kulle ƙofar zai yi ya yi mana dukan tsiya, tabbas da gaske ne, don an taɓacewa ta yi wani abinda bai so ba ya mare ta, ta zage shi, yana miƙewa ta bazama cikin daki ta leƙo ta taga tana cewa in ya san ya isa ya shigo ya tabe ta, ta hada da cewa "Ban yafe ba mugu kawai Allah zai saka min marin da ka yi min, kuma wallahi ba ka daki banza ba, a jikin yaranka zan rama ai za su dawo makaranta!".
Irin waɗannan matan kamar zuma ce, shanta sai da wuta, in ya yi lagwas gidan sai ya gagare shi, wallahi akwai matan da suka shafe shekara 15 ba wace ta taɓataka dakin wata, koda mutuwa aka yi bare haihuwa, hadin-kan yara kuma kai ka sani, kenan samun abinda za ka ba matan ba shi ne kadai ba, dole ka tabbatar kana da ƙarfin zuciyar da za ka iya tafiyar da gidanka, ka zaunar da su lafiya, in babu to ka kalli abinda tashin hankalin zai haifar.
Na zauna da wasu 'yan ƙasar Somalia in da suke mamakin yadda mutum yake ƙara aure kuma ya bar sabuwar matar a gari guda, har ya ce ya ji ana yin haka a Nigeria, na ce tabbas hakan na faruwa na ja bakina, ya ce wallahi a ƙasarsu sai wata ta kashe wata, abinda ya zo raina mu a Nigeria ai kusan a daki daya ma zan ce, don wasu matan sukan hadu a ne falo ne, wato "two bedroom flat" akwai masu madafa daya, ban-daki daya, komai tare suke yi in ba uwar-daka da kowa ke da nata daban ba.
Na taɓajin wata Bamisriya a BBC Arabic tana hira da Nuruddeen Zurgiy da jin muryarta za ta kai shekara 48-53, take cewa amaryarta ba ta san ta ba , ba su taɓahaduwa da juna ba, kuma ba ta fatar Allah ya hada su, da ya tambaye ta dalili sai ta ce "Gaskiya ni kyakkyawa ce! In muka hadu dole ta ji zafin hakan a zuciyarta!" Na yi dariya na ce to an gaya mata cewa kishiyar tata mummuna ce ko tsabar yarda da kai ce? Sannan ya maigidansu zai hada kan 'ya'yansa? Kuma ba a sha'ani a babban gidan ne da ba sa haduwa? Ko ba rashin lafiya ba a rasuwa ne? Akwai dai abubuwan tambaya da dama.
Na taɓazama da 'yan ƙasar Ethiopia, ni ne ma wakilin angon, ɗan Nigeria ne, ya musluntar da ita ya aure ta. Soyayya ba kama hannun yaro. Kullum tana jikinsa. Ba ta yarda ta yi nesa da shi. Kai ko titi za a tsallaka ba za ta yarda ya tsallaka ya bar ta ba, sai dai su tafi tare. An kai yadda wurin aikinsa ma tare suke tafiya, malami ne, duk ajin da zai shiga sai dai su shiga tare, irin alaƙar malami da dalibannan sam ba ta yarda ba kuma ba ta daga masa ƙafa ko kadan, na raba fada har na gaji, a ƙarshe na yi watsi da su, to kai a jinka ta ina zai sami sarari bare har ya yi tunanin zai ƙara mata? Ita kadai din ma ya aka ƙare bare ya auro wata? In dai zai ƙara auren to dole ya yi tunanin yadda za su rayu tare a ƙasa daya ma ba gari daya ko gida daya ba.
Rauni kan bayyana ƙarara a wurin wasu mazan, wanda kai da kanka ka san ba su shirya zama da mata biyu ba tsakani da Allah, wata matar take fadi da kanta cewa "Mu wallahi in shedan ya buga mana tambari dambacewa muke yi, ko maigidan yananan ba abinda yake iya yi, sai ma ya kulle mana ƙofa ya yi zamansa, haka za mu kekketa kayanmu, mu tottana wa kawunanmu asiri wallahi ko ƙala ba ya cewa bare mu sa rai zai shiga tsakanimmu, sai dai in mun gaji mu bari don kammu" abin takaici suna da yara kuma yaran suna ganin abinda yake faruwa, su ma babu cikakken hadin kai a tsakaninsu.

Post a Comment

0 Comments