Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Kara Aure 04: A Wa Aka Taimaka?



Ban sani ba in namiji yana da karatun da zai iya gamsar da mace kan cewa auren mata fiye da ɗaya yana da amfani a zaman-takewa ko zai iya amfanar da ita, galibi ƙetar da suke magana a kai

Zan Ƙara Aure // 04: A Wa Aka Taimaka?

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

A zahiri in mutum ya ce yana son ya yi aure kuma aka ba shi to shi aka taimaka mawa, wannan aka sani kowa a kan haka ya tafi, shi ya sa muke ganin cewa in mace ta fara cewa tana son mutum kamar ta tallata kanta ne, wasu ma suna ganin zubar da ƙima ne, sai dai akwai wata falsafa ta daban, misali namiji don ya makara bai dawo gida ba da wahala ka ga an rikice, sai dai tsoron abubuwan dake faru a yau na garkuwa da sauransu, amma mace dole a san ina za ta? Me za ta yi? Yaushe za ta dawo? Ina ta tsaya? Da wa ta fita?

Duk wata uwa da take rainon yara mata ba ta da kwanciyar hankali, akwai wace ko gida ba ta iya fita saboda tsaro, an kai lokacin da uwa take ƙoƙarin tsare 'ya'yanta mata daga 'yan uwansu a cikin gida don kar su la'anta mata su, na taba jin wata na cewa hatta uban ba abin yarda ba ne a wannan zamanin da muke ciki, abu ya kai abu kenan, to in aka sami wasu za su dauke miki wannan zullumin da rashin barcin dare saboda wa'azi da jan kunnen da kike yi wa aka taimaka mawa kenan? Ana auren biyu, uku, hudu har yanzu ga matannan, to in kuma kowani namiji mace daya kacal zai aura ya za a yi kenan? Ko su 'yan bokon da suka ƙi auren mata biyu sun fara dari-dari da ra'ayin cewa 'ya'yansu sai mai mata daya, don in suka tsaya kan haka ƙarshe a bar musu 'ya'yansu.
Wani abin dariya da na taba kawowa a wani dan shiri nawa mai taken "KA JI MUNAFUKI" wannan gani na yi, yadda uwa ta saka diyarta a gaba tana zagi don diyar tata ta ce ba za ta zauna ba, wai maigidanta ya dage sai ya ƙara aure, uwar ta zage ta kab, inda ta shiga ba tanan take fitowa ba, a ƙarshe diyar ta nuna mata cewa babanta yana neman ƙawarta, nan take lamarin ya canja, uwar ta bar fadan ta koma zagin maigidanta wato uban yarinyar, duk da cewa da tana gaya mata mahimmancin auren mata biyu ne ko fiye.
Ban sani ba in namiji yana da karatun da zai iya gamsar da mace kan cewa auren mata fiye da ɗaya yana da amfani a zaman-takewa ko zai iya amfanar da ita, galibi ƙetar da suke magana a kai in ka dubi hujjojinsu za ka fahimci cewa suna nufin namiji yana cikin talauci da rashin kudi mace na ta haƙuri tana tafiya da shi a haka, lokacin da ya sami sarari a maimakon ta huta cikin arziƙinsa sai kuma ya je ya dauko mata kishiyar da in ba ta dage ba za ta kore ta, ƙetar namiji kenan, akwai wata mata da na ga zaman lafiyan da take yi da kishiyarta na tambaye ta ta fada min cewa ita ta ba wa mijin shawarar ya aure ta, don ƙawarta ce, da dai na matsa sai na ji dalili sai ta ce to ai ita ma tana da yara mata a gabanta, kuma tana da kyakkyawar sha'awar ta ga ta aurar da su, in kowani namiji zai auri mace guda ta ina yaranta za su sami shiga?
Gaskiya tana da hankali, don ba duka aka zama daya ba, yau dinnan muka yi wa wata yarinya fada, kamar yadda babarta ta nema, uwayenta su hudu ne a wajen ubanta, amma ma'aunin da take auna kowane namiji da shi shi ne ba za ta auri mai mata ba, kuma dole a yi sharadi da mijin kan cewa in ta aure shi ba zai sake auro wata ba, ko ada lokacin da matan suke ƙaranci wannan alƙawarin yana da matuƙar wahala, bare yanzu da matan suka ninka mazan ko dai wajen haihuwa ko yawan mace-mace dake aukawa a matattarar mazan gaba daya, Larabawa masu hankali a cikinsu sun koma auren zumunci, yadda uwayen za su tattauna a tsakankaninsu sannan su hada yaran don dai a sami sauƙi.
Abin takaici mu yanzu sai muka fara fahimtar ƙalu-balen a kaikaice, muna ganin auren shi ne matsala, mai mata ba dole ne ba ya ƙara, ƙarin ma rashin hankali ne ko rashin adalci, sauƙaƙa sadaki yadda za a yi auren kuma zubar da ƙimar mace ne, auren hadaka da kwamitin Hisba a Kano suka faro ba komai ba ne illa saukar da darajar 'ya mace, yadda za a hada su kamar tumaki a rana guda a tura su, idan ka lura da mai wannan maganar sai ka ga kodai mace ce da auren ya yi mata hijira ta komo yaƙinsa, ko wace take zaune lafiya da mijinta ba ta son wata macen ta sami irin abin da take samu, duka dai kuskure ne, yaushe za ki tara yara a gabanki kuma ki ce kar maza su ƙara aure?

Post a Comment

0 Comments