Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanne Ya Fi?Mata kam ransu bai natsu da ƙarin auren nan ba, duk da cewa ba dukansu ne ba, amma na ga wacce ta yi wa mijinta cinne don ya ce zai ƙara aure. Haka aka yi masa ritaya! Na ga wace ta zazzagi mijinta ta uwa ta uba a gaban 'ya'yansa, ta tottana wasu asiransa a dalilin ƙarin auren...

Wanne Ya Fi?

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Na yi ƙoƙorin jefa wata tambaya a tsakanin dalibaina mata masu neman diploma a harshen Larabci da addinin muslunci, wanda yawansu ya kai 35-40, kuma ba na tsammanin akwai wata budurwa a cikinsu, duk matan aure ne, galibin shekarunsu daga 30-45, na ce: "Wai maigidanki ya yi laifi idan ya nemi aure, aka ba shi, har lokacin daura auren ya yi kafin ya gaya miki?" Wallahi mace daya ce rak, matar aure da shekarunta na ƙimanta da talatin da wani abu ta ce "Haƙƙinsa ne in so ya fadi, in ya ga dama ya boye" na so na san dalilinta a farko tukun kafin na saurari na sauran matan.
Sai ta ce "To ai ba wani haƙƙi nawa a wuyarsa da za a ce sai ya gaya min kafin ya yi, hasali ma na fi ganin ya bar wa cikinsa in ta so in lokacin ya yi ya gaya min, don in ni mai kishi ce abin zai yi ta damuna na tsawon lokacin har sai an daura tukun, na san ba fasawa zai yi ba, wata ma dalilin da za ta san shiga bokaye kenan ta rasa duniya da lahira" nan take wata dake gabanta ta ce "Allah ya sa a yi miki kishiyar!" Maganar ta yi mata zafi har ta yi addu'ar da take ganin mummuna ce ba ta sani ba, na gamsu da hujjarta, ban sani ba ƙila ko don ni namiji ji ne, amma duk da haka na ce bari na saurari sauran matan, nan wata ta ce: Wallahi ko kwana daya ba za ta ƙara a gidan ba don bai dauke ta abokiyar zamansa ba, don me tana tare da shi zai ɓoye mata cewa zai yi aure kawai sai ta tsinci cewa saura 'yan kwanaki ƙalilan a daura?
Wata ta ce: "Ai munafurci ne da rashin gaskiya, in ba munafurci ba an taba ɓoye abin arziki ne? Wallahi ko a muslunce ba inda aka ce namiji ya ɓoye wa mace zai ƙara aure?" Haka na yi shiru ina jin hujjojinsu, ƙarshe maganar ta koma tsakanin wannan dalibar da sauran daliban kan dole sai ya gaya wa matarsa ta ciki ko ba sai ya gaya mata ba, a ƙarshe na yi ƙoƙarin shiga tsakiya don na gamsar da su illar tsayawa a kan sai ya gaya musu din, sun karba amma a fuskokinsu na fahimci cewa ba su yarda ba, na kuma tattauna da wasu mazan a gefe a kan wannan mas'alar, sai na ga mafi yawa suna ganin a gaya mata tunda ana zaune da ita a matsayin rabin gidan gaba daya, kuma kishiyannan kamar ita za a yi wa.
Duk da haka wani abokina, Dr ne ma, ya ce: Ba kuskure kamar ka gaya wa mace za ka ƙara aure tun nesa da ƙofa, kuma da gaske din ne har ka shiga neman, ya kawo hujjojinsa kuma na gamsu da su, sai a ƙarshe nake ganin kamar zai yi wahala ka yi wa mata kudin goro; wace kake ganin ko an gaya mata ba matsala sai ka gaya mata, in kuma ka ga gaya mata din zai mai da gidan filin yaƙin badar sai ka ɓoye abinka, wannan shi ne mafita, amma na ga matan da suka shiga bokaye da yawa a kan mijinsu ya ce zai ƙara aure, wata tana ƙasar waje ta fasa aiwatar da abin da ya kai ta ta dawo tsoron kar rade-radin da ake yi ya zama gaskiya, mace ba ta wasa da maganar kishiya.
Na ga wace take mummunar ɓata wa mijinta da cewa da yunwa suke kwana, don dai kar ya ƙara aure. Ga wata A'isha da na ga rubutunta yau 20/10/2019 a fesbuk tana cewa: "Da a ce maganar Nanono da gaske ne ana ci a ƙoshi a Naira 30, da ka ga ƙarin aure wurin maza, Allah mun yi ma godiya, a tafi a haka" wata malama da na sani mijinta ya ce "Allah kawo kudi mu ƙara mata" ta ce "Allah ka bar mu haka kar ka ba shi" a gabansa ta fada ƙiri-ƙiri, na taba jin wata tana cewa da Allah ya ba mijinki kudi ya ƙaro auro gwara ya bar ku cikin talauci, mazan yanzu wallahi da sun yi kudi aure za su ƙara, wata da mijinta ya sami aiki cewa ta yi "Wallahi ban so ya sami aikinnan ba, gwara Allah ya bar mu da talaucinnan, yana fara samun kudi za ki ji ya ce zai ƙara aure!"
Mata kam ransu bai natsu da ƙarin auren nan ba, duk da cewa ba dukansu ne ba, amma na ga wacce ta yi wa mijinta cinne don ya ce zai ƙara aure. Haka aka yi masa ritaya! Na ga wace ta zazzagi mijinta ta uwa ta uba a gaban 'ya'yansa, ta tottana wasu asiransa a dalilin ƙarin auren. Ka ga irin wadannan matan gaskiya ɓoye musu shi ne zama lafiyar mutum, na ji wace ta dauko wuƙa kuma ta rantse da Allah in har mijinta ya runtsa a wannan gidan sai ta farke shi, shi ma dai haka ya wawuro tasa suka kwana ido bude kowa da wuƙa a hannu, auren ma ya baci, ya auri wace ya ce zai aura.

Post a Comment

0 Comments