1.0 Gabatarwa
Aminu ALA mawaƙi ne da ya taɓo kusan kowane ɓangare na rayuwa a waƙoƙinsa. Shi
ya sa a lokaci guda za a iya kiran sa mawaƙin sarauta ko mawaƙin siyasa
ko na jama’a ko ma mawaƙin sha’awa (Rogo 2013:61-67). A
yawancin lokuta an fi danganta saƙonnin waƙoƙin Aminu
ALA da faɗakarwa ko
sa-kai da kuma yabo na sarakuna ko wasu shahararrun mutane. Shi kuwa salo kamar
yadda masana irinsu Mukhtar (2004) da Yahya (2001) suka bayyana, ba komai ba ne
illa dabara ta isar da saƙo cikin sauƙi da
burgewa. Ke nan, salo shi ke bayyana saƙo kuma shi ke ɗaukar saƙon ya dasa shi a zukatan da
ake buƙatar dasawa. Shi ya sa Yahya (2001) da Garba (2012) suka raja’a cewa muhimmancin salo a
waƙa abu ne
da ba ya misaltuwa, domin kuwa salon ne ke kwarzanta mawaƙin da waƙar, kuma
shi ne yake rayar da harshe, ya kuma kaifafa tunanin mai ji ko mai sauraro kuma
ya sarrafa shi tare da bayyana shi cikin irin fahimtar da ake buƙata. Wato
dai, salo dokin jigo ne.
Wani muhimmin salo da ya ratsa galibi waƙoƙin Ala da
ba a faye lura da shi ba, shi ne bugun gaba. Shi ya sa a wannan nazari aka yi ƙoƙarin zaƙulo tare da tsettsefe wannan salo na bugun gaba a wasu baituka na
waƙoƙinsa guda
goma sha biyu.
2. 0 Aminu Ala a Fagen Waƙoƙi
Hanyoyi biyu ne suka zama silar shigar ALA
harkar waƙa. Na farko tun lokacin da malamansa na Islamiyya suke koya masu
karatu ta hanyar waƙa. Sai yawon mandiri da ya yi tasiri sosai kansa ga son waƙa, sai
kuma waƙe-waƙen maulidi wanda ake yi duk shekara (Rogo 2013:61-67). Kenan, ALA
bai gaji waƙa ba ta kowane ɓangare dangin uwa da uba,
haye ya yi wa harkar waƙa kuma Allah ya haskaka
tauraronsa, har ya ɗaukaka. Shi ya sa ya ce:
“Ɗan gado nake kan aure,
Ba gado a sana’una.
Taka kai sama sunana,
Harkar zayyana waƙena.
Na gode wa majiƙan bayi
Allahu maƙagina. ”
(Aminu ALA: Waƙar Sardaunan Kano)
ALA mawaƙi ne da ya kunno kai cikin
harkar waƙe-waƙen zamani kuma a ƙanƙanin
lokaci Allah ya haska tauraruwarsa, tamkar dai lamarin nan da akan ce “dare ɗaya Allah kan yi Bature”. Ya tabbatar da haka a waƙar Lu’u lu’u A Juji:
“Ni Aminu ba ɗan sarki ba ba basarake ba,
Ni Aminu ba ɗan gwamna ba ba mai muƙami ba,
Ni Aminu ba ɗan masu kuɗi ba ba mai kuɗi ne ba,
Ni Aminu ba ɗan malam ba ba fa mu’allimu
ba,
Ni Aminu ba fa ma’aikacin rediyo da tibi ba,
Rabbana ka yalwata harshena ba da baɗala ba,
Ga shi na zamanto lu’ulu’un juji ku yo duba.
(Barista, 2011)
ALA mawaƙi ne da kowace waƙarsa
akwai manufar yin ta, bisa kulawa ga halin da al’umma ke ciki. Shi ya sa duk waƙar da zai
tsara yana gudanar da bincike game da batun, kamar yadda yake cewa:
“Wayyo ni wayyo ni,
Ni Ala za ni tona ajalina.
Yawan karatu da bincike-bincike,
Za ni kai ga ajalina.
(Aminu ALA: Waƙar Bayi).
3. 0 Bugun Gaba Da Yadda Yake a Waƙa
Bunza (2012), ya fito da wannan salo inda ya yi
amfani da fagen al’adu wajen ƙyallaro fannin adabi, ya
fayyace cewa a fagen al’ada bugun gaba shi ne, mutum ya doki ƙirjinsa
da tafin hannunsa na dama ya furta magana ga mai son raina masa wayo ko asali.
Saboda haka idan mutum ya sami karɓuwa ga wani abu, kamar ya samu shiga ga hukuma ko wani shugaba ko
fice a sana’a, idan ana furta wannan baiwar a gabansa zai ɗauki sigar kirari. Idan shi
da kansa yake faɗar su ba da wata shigar washi ko alfahari ba, ya zama “mamakar da
kai”. Idan kuwa ya ji ana faɗar su ya sharɓe maganar, ya tabbatar da su, to ya yi bugun gaba.
Tun farko sai da Bunza (2012) ya rabe aya da
tsakuwa tsakanin kirari da bugun gaba inda ya bayyana cewa idan aka zaburar da
mutum ga abin da ya saba yi ko ya shahara ko ya buwaya ko ya ƙware,
kalmomin suka shiga jikinsa, suka tsima shi, to an yi masa kirari. Idan ya
furta wasu kalmomi domin tabbatar da abin da ake gaya masa, nan ma kirari ya
yi. Idan ma wani dabba ko icce ko gari ko ƙasa aka
yi wa wannan washin duk da yake ba sa ji, ba sa mayar da martani, duk dai
kirari aka yi. [1] Shi kuwa bugun gaba abu ne da mutum zai
yi wa kansa. Mutum kaɗai ke bugun gaba; baya ga shi babu wani mai yi masa. Wato mutum
shi zai yi bugun gaba da kansa, idan wani ya yi masa, ya zama kirari. Misali a
Bakandamiyar Alhaji Mamman Shata Katsina inda ya nuna ya yarda cewa ba a samo
canjin sa ba ballantana ya huta, ya sarara. Iƙirarin wannan ɗaukaka tasa ta furucin bakinsa salon bugun gaba ne:
“Jagora: Ba a samo canji na ba
:Balle in huta
:Balle in ce in sarara
:Yardar Allah ta fi ta kowa
:Na Abu ɗan Ibrahim
:Shata ne…
G/Waƙa :Alo alo mai ganga ya
gode
:Yaran mai ganga sun gode” Bunza (2012).
Har ila yau, Bunza (2012) ya fayyace turaku
bakwai na feɗe wannan
salo, su ne;
- Tushe: Bugun gaba da iyaye da kakanni
- Asali: Bugun gaba da harshe da ƙabila
- Baiwa: Bugun gaba da fasaha da fahimta da
sani
- Koyo: Bugun gaba da ƙwarewa da gogewa da iyawa
- Togiya: Bugun gaba da hawa da nuna wuraren
da aka fi wani
- Suna: Bugun gaba da ficen suna da zarta
tsara
- Turke: Za a iya turke ga abin nan da ake
zance a kansa
A dunƙule Bunza (2012) ya bayyana ma’anar salon bugun gaba shi
ne:
“Furucin da wani mutum zai yi a cikin zancensa
ko waƙarsa ko rubutunsa yana ƙoƙarin fito da irin
martabarsa ko ƙwazonsa. Galibi idan fagen fasaha ne, mai bugun gaban zai yi bugun
gaban ne da fasaharsa da ya yi fice da ita. Idan fagen awon mutunci ne da
sauran sassan da gidajen shida za a yi iƙirari. ” Bunza (2012).
Karɓar wannan tayi na Bunza (2012) ya haifar da wannan nazari na salon
bugun gaba a waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa. Saboda haka, ana iya
cewa bugun gaba a waƙa shi ne furucin mawaƙi na alfahari ta hanyar
cika baki musamman ta fuskar ƙwarewa da
hikima da baiwa ko asali ko gogewa ko kuma bayyana ficensa da zarta tsara don
nuna fifikon da mawaƙin ke da shi kan saura.
4. 0 Bugun Gaba a Waƙoƙin Aminu Ala
Saƙonnin da suka ratsa galibi
waƙoƙin Ala faɗakarwa ne, sai yabo da
siyasa da na sa-kai da sauransu. Saboda haka cikin ƙoƙarin
sadar da waɗannan saƙonni ga
masu sauraro, mawaƙin yake bugun gaba. An bi tubalan da Alan ya gina bugun gaba cikin
wasu waƙoƙinsa, aka tsettsefe su domin kafa hujja.
4. 1 Tushe
Tushe yana nufin farko ko asalin mutum ko magana
ko wani abu (CNHN, 2006:447). A nan, ana gabatar da bugun gaban ne
da iyaye da kakanni ta yadda mutum zai furta da bakinsa domin fito da
tushensa ta fuskar iyaye da kakanni. Alan waƙa ya yi amfani da irin
wannan bugun gaba da tushensa inda yake cewa:
Ɗan Malam Sani Ala,
Ladan Baba a guna.
Sani Ladan Abu ne,
Bakari Kaka a guna.
Shi ko Bakari ko ɗa ne,
Ga Mijinyawa Bincikena.
Mijinyawa Kura Jarmai,
Baba a gurin Kakana.
Dan Sarki Dambuwa ne,
Gobir Tsibiri garina.
Dambuwa ɗa ne ga Gwamki,
Gwamukawa assalina.
Masarautar Bawa Gwarzo,
Ku ji salsalar ubana.
(Aminu Ala: Waƙar Shahara ta 1)
A nan, Alan waƙa ya yi bugun gaba da
tushensa inda ya bayyana tsatsonsa daga masarautar Gobir inda nan ne aka yi
Bawa Jangwarzo. Domin jaddada wannan iƙirarin, mawaƙin ya
jero nasabarsa tun daga mahaifinsa zuwa kakanninsa da kuma inda suka fito wato
gidan sarkin Dambuwa a ƙasar
Gobir. Ƙasar Gobir dai ta shahara
matuƙa a tarihin ƙasar
Hausa, musamman ta fuskar jarumai da mawaƙa da sauran abubuwa na
bajinta da tarihi ya taskace. Saboda haka, wannan iƙirari na
tushe da salsalar iyaye da kakannin Ala da ya yi da bakinsa, bugun gaba ne.
4. 2 Asali
Asali shi ne mafari ko tushe ko salsala (CNHN,
2006:20). Idan mawaƙi ya yi bugun gaba da harshe ko ƙabila, to
ya yi amfani da salon bugun gaba na asali. A wurare da dama ALA ya yi bugun
gaba da asalinsa na Bahaushe, Bagobiri mai amsa sunan Hausa-Fulani. Alal
misali, a waƙar Kyauta, ya ce:
Waƙa ba gado na yo ba a gane,
Ni asalina ɗan gidan ilimi ne,
Yarena Hausa Bagobiri ne,
Ruwa biyu Hausa-Fulani in an gane.
Kyauta gun Allah fa ba ya zobe,
Kyauta gun Allah fa ba ya zobe.
(Aminu Ala: Waƙar Kyauta)
Asalin mutum abin tutiyarsa ne, shi ya sa kowane
mutum yake alfahari da harshensa da kuma ƙabilarsa. Kwatankwacin haka
Ala ya yi a wannan waƙar domin bugun gaba da
asalinsa musamman harshensa da ƙabilarsa.
4. 3 Baiwa
Baiwa ita ce kyauta musamman daga
Ubangiji (CNHN, 2006:30). Kowane ɗan Adam yana da baiwar da Allah (SWT) ya yi masa wadda ta bambanta
shi da waninsa, walau ya sani ko bai sani ba. Ta fuskar baiwa, mawaƙi kan yi
bugun gaba ne da fasaha ko fahimta ko sani na wani abu. Fasaha na nufin
gwaninta ko ƙwarewa
(CNHN, 2006:136) yayin da fahimta ke nufin gane abu (CNHN, 2006:130) Shi kuwa
sani na nufin fahimta ko ganewa ko ilmanta ko ƙaru da
ilimi, (CNHN, 2006:389). Ala yi amfani da bugun gaba ya bayyana baiwarsa ta
fuskoki da dama, misali a waƙar Hikima Taguwa, mawaƙin ya yi
amfani da salon bugun gaba ne wajen bayyana baiwar hankali da ilimi da tunani
da Allah (SWT) ya hore masa:
“Hankali mizanin awona,
Sai tunani akalar batuna,
Illimi jagorar jikina,
Hujja sanda ta kare kaina.
(Aminu
Ala: Waƙar Hikima Taguwa).
Haƙiƙa ilimi
baiwa ne, domin kuwa ilimi ne jagora cikin dukkan al’amura na ƙwarai da ɗan’Adam ke gudanarwa a
rayuwarsa. Shi ya sa ma ake yi masa kirari da ‘ilimi gishirin zaman duniya’. A
nan, Aminu Alan Waƙa ya nuna cewa ya sami ɗanɗano wannan gishiri a
rayuwarsa gwargwado, wanda ilimin ne ya zame masa jagora cikin dukkan
al’amuransa, shi ya sa a kodayaushe yake amfani da iliminsa wajen samun hujjar
kare kansa a cikin duk al’amuran da yake gudanarwa. Haka kuma ya nuna cewa
tunani ne akalarsa batutuwansa, yayin da hankali kuma ke kasancewa mizanin
awonsa a rayuwa! Wannan bugun gaba ne da baiwar da Allah maɗaukakin sarki ya hore masa.
Bugu da ƙari, a waƙar Agajere ma Ala ya yi
irin wannan bugun gaba inda yake cewa:
Allah ka huwace ilhama,
Ka yo min ado da fussaha.
In nai baituka da bakina,
Sai ka ji malamai suna saha.
Sannan kattsaren tunanina,
Kad da na kauce goddaben ɗaha.
Annabi shugaban dukkan alam,
Wanda ya zarce dukka mai fasaha.
(Aminu
Ala:Waƙar Agajere)
Abin lura a nan shi ne Ala ya yi iƙirarin
cewa yana da baiwa ta ilhama da fasaha, shi ya sa malamai ke nazarin
baitukansa, sannan kuma kasancewar Allah ya tsare tunaninsa bai kauce wa
tafarkin Annabi Muhammad (SAW) ba, wannan abin bugun gaba da toƙabo ne
gare shi.
4. 4 Koyo
Kalmar koyo ta samo asali daga kalmar aikatau
‘koya’ mai nufin karantar ko nuna yadda ake yin abu (CNHN, 2006:250) wato koya
darasi ga wani. A nan, mawaƙi na bugun gaba da ƙwarewa ne ko gogewa ko iyawa don saura su koya daga gare shi.
Misalin inda Aminu Ala ya yi irin wannan bugun gaba shi ne a waƙar Sarkin
Zazzau mai taken ‘Atafa’ inda ya bugi gaba da cewa saboda gogewa da ƙwarewarsa ne ya sa:
Ka ji waƙa hannun riga,
Ta bara daban ta bana daban.
Baitoci babu harigido,
Sanka-sanka ka ji su daban.
Don babu kwata a harshena,
Kalmomina ka ji su daban.
(Aminu
Ala:Waƙar Atafa)
Wannan ya nuna ƙarara
irin gogewar Ala da ƙwarewarsa
a waƙa, shi ya sa babu harigido a waƙoƙinsa,
kalmominsa ana jin su raɗau duk da waƙoƙin nasa
suna da yawa birjik, amma a cewarsa godiya yake yi wa Allah (SWT), ba alfahari
yake ba. Kenan, bugun gaba ce yake yi da ƙwarewarsa a waƙa.
4. 5 Togiya
A nan, mawaƙi yana bugun gaba da hawa
da nuna wuraren da ya fi wani ne. Alan Waƙa ya yi irin wannan bugun
gaba a waƙar Atafa, inda ya ce:
Ku lura da baitukan ALA,
Kar ku yi tsuru ina ta zuba.
Tsuntsu sunansu ne fa guda,
Kukansu daban ku dudduba.
Idan wani ya kasa a saya,
Idan wani ya yi ba haka ba.
Kai mai tallar maɗi kauce,
Ga mai tallar zuma a gaba.
(Aminu
Ala: Waƙar Atafa)
Bugun gaba a nan ita ce faɗin cewa a fagen waƙa, shi
Ala yana gaba ne sauran mawaƙa suna biye da shi. Shi ya
sa ma ya kira kansa mai tallar zuma, sauran mawaƙa kuma masu tallar maɗi, domin kuwa a cewarsa duk
da zuma da maɗi abubuwa ne biyu masu zaƙi amma akwai fifiko
tsakanin su kamar yadda kowane tsuntsu da irin kukan da yake yi wanda ya
bambanta shi da waninsa. Kenan, idan mai sauraro ya lura da baitukansa, zai
gane fifiko tsakaninsa da sauran mawaƙa, kamar dai yadda ya sake
jaddadawa a waƙar Matawallen Zazzau:
Ka ji waƙa da bamban da ta shewar
dila,
Baitukana kuna jin su fa dalla-dalla,
Godiyata da ba kwata a harshen ALA,
Na yaba wa Ubangiji Maƙagin ALA,
(Aminu
Ala: Waƙar Matawallen Zazzau)
A nan, mawaƙin ya nuna fifiko ne
tsakaninsa da sauran mawaƙa ta hanyar nunawa ƙarara cewa waƙarsa ta sha bamban da ta
shewar dila (wato ta sauran mawaƙan), shi ya sa ake jin sa
dalla-dalla kuma babu kwata a harshensa. Ya dire bayanin nasa da yi wa Allah
(SWT) godiya, amma a bayyane take wannan bugun gaba ne!
4. 6 Suna
Idan mutum ya yi suna wato ya shahara, ya sanu a
wani fage cikin rayuwar al’umma ta yau da kullum. Shi ya sa a waƙa da ma
rayuwar yau da kullum ake yin bugun gaba da ficen suna ko zarta
tsara. An sami wuraren da irin wannan bugun gaba da suna ya wanzu a waƙoƙin Aminu
Ala, misali:
Wanda ya san ALA silar waƙa ne,
Ga matsayin daraja silar waƙa ne,
Ga dubban jama’a silar waƙar ne,
Ko ilimin ALA silar waƙar ne.
(Aminu
Ala:Waƙar Kyauta)
A wannan baitin, Ala ya bayyana ƙarara
irin suna da shahararsa, har da irin matsayi da daraja da ɗimbin jama’a masoya da kuma ilimin da ya samu duk a dalilin waƙa. Duk da
haka abin yake a zahiri, amma faɗin da mawaƙin ya yi da bakinsa, ya sa
ya zama bugun gaba. Har ila yau, mawaƙin ya sake fito da iƙirarinsa
fili inda yake cewa:
Idan aka ce ALA Mawaƙi ni ne,
In aka ce alkatibi ma ni ne,
In manazarci anka ce maku ni ne,
Fulani ki san wannan ko farilla ne.
(Aminu
Ala:Waƙar Kyauta)
A cewarsa, in dai ana batun suna ne, to Ala fa
ya zarta tsara domin kuwa ya yi fice a fannoni daban-daban; ya sanu a matsayin
mawaƙi, marubuci kuma manazarci. Shi ya sa ma ya kira kansa gantamau na
masu rera waƙar Hausa kuma jakadan harshen Hausa domin kuwa da zarar ya tsara
baitukansa yanzu-yanzu za su kai kusfa-kusfa da garuruwan Hausa.
Gantamau na masu rera waƙa a ji,
Ga jakada na harsuna na Hausa ku ji,
Yanzu in tsara baituka gobe a ji,
Kusfa-kusfa, gari-gari dukka a ji.
(Aminu
Ala:Waƙar Ummu Muhammadu)
4. 7 Turke
Da yake a bugun gaba za a iya turke ga abin da
ake zance a kansa, Aminu Alan Waƙa yana yawan yin turke da
waƙa don
bayyana yadda ya ɗauki waƙa da kuma
inda waƙa ta kai shi da tunaninsa game da waƙa. A waƙar ‘Tadaƙura uban
Shuraim’ Aminu Ala ya yi turke da waƙa ya yi bugun gaba da cewa
shi fa a gare shi waƙa:
Ita ce sulken faɗa,
Ita ce mabugin mai nuna darga.
Ita ce suturar ado,
Da akan ji ana ALA da yanga.
Ita ce fa jakadiya,
Da yawan aike bai gundurarwa.
Can ta zama bindiga,
Tai difendin ko kashe ‘yan adawa.
Nan ko takwarar zama,
Aurenmu da ke ba mai rabawa.
Ko ba ni da rai tana nan,
Za ta wakilci Aminu gawa.
Maza tashi ki sada saƙon,
Soyayya ga Aminu nawa.
(Aminu
Ala:Waƙar Tadaƙura)
A nan, Alan Waƙa ya nuna yadda waƙa ta yi
masa komai; shi ya sa ma ya ɗauke ta a matsayin sulke da
yake amfani da ita wajen faɗa da ƙalubalen rayuwa, ya sanya
ta a matsayin suturar da yake caɓa ado da ita. Ita ce ma jakadiyarsa wadda ba ta yi masa ƙyuya
wajen aika saƙonsa cikin al’umma. Har ila yau waƙar ce bindigar da yake
amfani wajen harbe ‘yan adawansa, tun da ita ce takwarar zama a gare shi don sun yi
auren zobe, mutu ka raba. In ma ya mutun, to waƙar za ta cigaba da
wakiltarsa wajen aika saƙonninsa! Abin tambaya a nan
shi ne, waɗanne saƙonni Alan
Waƙa ya fi
ba muhimmanci? Waɗannan baitukan sun turke su kamar haka:
Jigon waƙar Aminu kamar
Kullum bai zarce ƙauna.
Na faɗi a cikin Zagga,
Agajere da Illela ta ƙauna.
Na faɗi a ta Maitama,
Safiyanu Makaho Sahibina.
Na faɗi a Tiga gari,
Usman edisin nan na gwamna.
Har da Isa Bello Ja,
Da su Yakasai ga Aminu guna. (Waƙar Tadaƙura: Aminu Ala)
Wannan bugun gaba ce Ala ya turke a waƙe cikin
waƙar tasa
domin ya yi iƙirarin yadda ya ɗauki waƙa a
tunaninsa da tsarin rayuwarsa da kuma irin saƙonnin da ya fi ba
muhimmanci a waƙarsa (wato ƙauna da
sada zumunci kamar yadda ya faɗa a waɗannan baituka na sama).
5. 0 Kammalawa
Nazarin salo wani tafkeken fage ne da yake da faɗi, shi ya sa in dai an haƙa, to ba
a rasa ruwa a ƙasa.
Saboda haka, wannan takarda ta mayar da hankali ne wajen jaddada samuwar salon
bugun gaba a adabin waƙa kamar yadda Bunza (2012)
ya ayyana. Domin rabe aya da tsakuwa, sai aka ɗora nazarin bisa waƙoƙin Aminu
Ladan Abubakar (Alan Waƙa); bayan an yi sharer fage
game da salo da kuma waƙa a bakin Aminu Ala, aka
kuma yi tsokaci game da ainihin ma’ana da asali da tubalan gina wannan salo na bugun gaba, an kawo
misalai daga wasu baitoci na waƙoƙin Ala
guda goma sha biyu, aka tabbatar da cewa Alan yana amfani da salon bugun gaba
wajen ƙawata saƙonninsa a
cikin waƙoƙinsa. An fahimci cewa a yawancin lokuta yakan yi bugun gaban ne da ƙwarewarsa ko da asalinsa ko da iliminsa ko kuma shahararsa a fagen
waƙa, tamkar
dai batun nan da akan ce magori wasa kanka da kanka.
Manazarta
Barista,
M. L. (2011). Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa: Littafi na ɗaya. Iya Ruwa Publishers.
Bunza, A. M. (2012). Bugun gaba: Salon
a
san ni, a ji ni, a gane ni ne wane. In H. A. Amfani et al. (Eds.), Champion
of Hausa cikin Hausa: A festschrift in honour of Dalhatu Muhammad.
ABU Press Limited.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.
(2006). Ƙamusun
Hausa. Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya.
Dikko, S. S. (2010). Uwa
a Bahaushiyar al’ada: Nazarin mu’amalar uwa da ɗa cikin waƙar Ummina ta Aminu Ala (Kundin digiri na ɗaya). Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.
Garba, S. (2012). Salo dokin jigo:
Tsokaci a kan waƙar Ƙalubale ta Aƙilu Aliyu. In H. A. Amfani et al. (Eds.), Champion
of Hausa cikin Hausa: A festschrift in honour of Dalhatu Muhammad.
ABU Press Limited.
Giɗaɗo,
H. A. (2012). Tasirin
zamananci kan al’adun Hausawa: Nazarin mu’amalar aure tsakanin mata da miji
cikin waƙar
Gizo-gizo ta Ala da Fati Nijar
(Kundin digiri na ɗaya).
Jami’ar Jihar
Kaduna.
Mukhtar, I. (2004). Introduction
to stylistics: Theories, practice and criticism (Vol. 1). Country
Side Publishers.
Rogo, M. S. (2013). Kiɗa da waƙar Hausa jiya da yau: Kamanci da
bambanci tsakanin waƙar
Jami’ar
Ahmadu Bello Zariya ta Alhaji Mamman Shata Katsina da ta Aminu Ladan Abubakar
Ala (Kundin digirin
farko). Jami’ar Jihar Kaduna.
Yahya, A. B. (2001). Salo
asirin waƙa. FISBAS Media Services.
Yakasai, S. A. (2012). Some
major themes of Hausa responsorial songs in Aminu ALA’s performance
(Conference paper). Bayero University Kano.
[1] Mutum na iya yi wa kansa kirari, wani na iya yi masa kirari kuma ana iya yi wa wani abu ko wasu abubuwa kirari.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.