Ba abin da wata mace take da shi wanda ba ki da shi, kuma ba abin da za ta yi wanda ba ki iya ba. Kowa ta iya allonta ta wanke! In kika ji namiji ya ce zai ƙara aure, kuma da bakinsa ya fada, tabbas wace yake so zai auro. In kika matsa sai kin yaƙe ta dayan abu biyu zai faru, ko dai ki ci nasara ki hana aurenta, ko ita ta ci ta kashe naki
Me Kike Tsoro?

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Zancen ƙarin aure tsakanin miji da mata in ka so ka kira shi da sunan rikici ko wani ƙulli mai wuyar warwara, amma ya danganta daga mutum zuwa wani, ko a matattararmu ta maza in mutum ya ce zai ƙara aure na kusa da shi kan tambaye shi "Shin ka gaya mata?" Ba wai shawara suke ba shi don ya gaya mata ba, ba kuma so suke su ji ya fadin ko bai fadi ba, babban abin da suke tunani shi ne: Gaya mata cewa zai ƙara aure ita ce babbar matsalar da za ta iya rikirkita masa gida, wani daganan ne zai tabbatar in zai iya ƙarawar ko sai ya sallami ta ciki kafin ta waje ta shigo.

A 'yan labarurrukan da muka tattara:-
a) Akwai wanda ya yi wa dakin uwargidan fenti ya sake mata komai don dai ya danne ƙirjinta.
b) Wani ya saya mata mota ga kudin kashewa.
c) Wani ya sake mata kayan daki gaba daya.
d) Wani tafiya da ita ya yi aka sayo kayan nata da na amaryar komai iri daya don dai a zauna lafiya.
e) Mun sami labarin wanda ya tura ta haji kafin ta dawo an yi komai.
f) Wani sakin ta cikin gidan ya yi sai da ya yi amaryar sannan ya dawo da ita, ya ce ba wata hanya ta zaman lafiya in ba wannan ba.
e) Wani ranar bikin ne ma uwargidan ta ga 'yan uwansa take tambayar ko lafiya aka ce mata aure mijinta yake yi.
Wasu abubuwan fa namiji kan yi ne gwargwadon yadda ya ga matarsa take, wata tana da zafin kishi, akan gane haka a maganganunta.
Wata kuwa ba'a kawai take yi, mai lura dai shi yake iya gane dingishin kwado, amma a wannan shirin wata ta yi min kashedin farko na cewa za ta kulle ƙofa da ni a waje don ma ta daina ganin tashin hankali, abin tambaya anan me take tsoro ne? Me amaryar za ta yi wanda ita ba za ta iya ba? Ladabi ko aiki don jin dadin maigida? Me amaryar take da shi wace ita Allah bai ba ta ba? Tarkon dake kama namiji ba wata wahalar danawa ce da shi ba, lura kuma za ki fahimta, "Shin me yake so?" Karuwan dake dauke hankalin mazanku me mazan ke buƙata a wurinsu? Mazan kan yi musu maganganun ƙauna kala-kala.

Sukan kashe maƙudan kudi a kan karuwai, su saya musu mota, su ba su aiki, wata a gina mata gida, a yi mata duk abin da take so, shin ita kuma me take ba namijin? Abu guda ne kawai ba ragi ba ƙari, da za ka ce masa "Wane irin kudin da kake kashe wa wance ka aure ta mana ka huta!" Wallahi cewa zai yi "Allah ya kyauta, wance zan maishe ta uwar 'ya'yana?!" Ashe duk kudin da yake ba ta da yawon da yake yi da ita da maganganun da yake fada mata duk na ƙarya ne, abu guda kawai yake so a wurinta ke ma kina da shi, bai ƙaunar ta zama matarsa ke kuma kina ma da yara tare da shi, riƙe yaranki kawai Allah ya kawo ta lafiya.

Ba abin da wata mace take da shi wanda ba ki da shi, kuma ba abin da za ta yi wanda ba ki iya ba. Kowa ta iya allonta ta wanke! In kika ji namiji ya ce zai ƙara aure, kuma da bakinsa ya fada, tabbas wace yake so zai auro. In kika matsa sai kin yaƙe ta dayan abu biyu zai faru, ko dai ki ci nasara ki hana aurenta, ko ita ta ci ta kashe naki, wanda hakan ya sha faruwa a wurare da yawa, kuma damar da take da ita na cin nasara a kanki tana da yawa, masamman yadda shi alƙalin wasan yana ƙaunar wace kike fada da ita, ga miyar unguwa da zaƙin tsiya, in ba ki yi sa'a ba wallahi wantsalar dake za ta yi, anyi an gama, sai wani jiƙon wai akuya ta zubar da tsamiyar kura, koda kin ci nasara auren ya gagara, yanzu mijin naki zai fahimci da shi kike yi, kina bata masa neman aure don haka zai nemo inda ba ki isa ba.

Wannan a unguwarmu ya faru, uwargidan ke bin wace za a auro har inda ta ci mata mutunci a ƙarshe auren ya gagara, don akwai inda take gaya wa yarinyar ko uwayenta cewa matuƙar yarinyar ta shigo gidanta sai ta kashe ta, sai uwayen ko yarinyar su ji tsoro su canja ra'ayi, wannan ya sa ya ce "Ta ga ina nemo mai sauƙi-sauƙi ne" aka ce ya nemo wata wace tun ba a je ko'ina ba ta nakada wa matar ciki dukan tsiya a dalilin ta bi ta har gidansu kamar yadda ta saba, ƙarshe dai ta dawo wurin maigidan ta ce ta yarda ya auro koma waye amma banda wannan matar, shi kuma ya yi kunnin uwar shegu da ita, amaryar dai ta iza ƙeyar uwargidan, ta kuma gaya mata ƙiri-ƙiri cewa wallahi ta fi ƙarfin mijinta, amma za ta aure shi don kawai ta kore ta ne a gidan, kuma za ta riƙe shi tamau don kar ta dawo masa daga baya, ƙila da gaske take yi, don ta kure ta din, kuma ana fadin irin ladabin da take masa.

A ganina ba wani abin tsoro a ciki, in ma ke ce dalilin ƙara auren nasa yi ƙoƙari kawai ki san me kike yi wanda ba ya so ki dena, an wuce wurin, in kuma dama akwai abin da ba ki yi ne ki koya, na ga wani dan bidiyo da ake yawo da shi wanda wata budurwar Basakkwaciya ta yi, a cikinsa ta nuna cewa an kawo mata amarya wace take wanka sau biyar a wuni, nan da nan ta dauke hankalin maigidan, don haka ita ma ta koya, da zarar amaryar ta dawo bayi ita ma sai ta sabi bokiti ta ruga makewayi ta watsa ruwa, dariya za a yi, amma darasin dake ciki yana da yawa, na kusa-kusa shi ne tana tura saƙo ga mata cewa matuƙar mace za ta zama ƙazama to kuwa amaryarta za ta ƙwace mata miji, na biyu ta yi ƙoƙari ta gano me ya sa hankakin nasa ya karkata wajen amaryarta, shi ya sa ta kwafa.