Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 03: Me ya Kamata su Gane?



Wanda ya zauna a ƙasashen Larabawa ya zo kuma ya ga 'yammatammu a Nigeria waɗanda suke neman miji zai ce Alhamdu lillah,  abu ne da ba sai an gaya maka ba, mata sun yi yawa yanzu a duniya, makarantu, kasuwanni, motocin sufuri da sauran wurare duk mata ne ...  
         
Zan Ƙara Aure // 03: Me ya Kamata su Gane?

Daga:
Baban Manar Alƙasim

Gaskiya ko shago mutum ya samu yana sayar da kaya shi kadai in wani ya ce zai bude kusa da shi dole ya ji wani iri, don komai yanzu za a raba 2, dole ya fara ƙoƙarin kawo duk abin da ake nema, ya iyakance farashin kayan, ya sami wani salo na magana da masu sayensu, ya gyara ma'amallarsa da kowa, in ma ba ya  jawo hankalin mutane kusa da shi dole ya fara, in aka dauki gidan aure a matsayin wurin samun abubuwan more rayuwa ko mallake namiji to mace ba za ta so kishiya ba don za su fara sanya gasa a tsakaninsu, in ta so wace ta fi iya abin da ake so ta riƙe gida, idan kuwa mutum ya zama mai taimakon jama'a ta wurin hidimar da yake yi musu, kuma bai neman komai a hannunsu, tabbas zai buƙaci mai taimako a lokacin da aka ce za a kawo masa wani.

A bisa wannan fahimtar in mace ta fahimci aure a matsayin ibada,  tana neman dacewa a wurin Allah ba ta damu da wani abu na duniya ba tunaninta zai koma can wajen ladar ne, mace ba ka raba ta da kishi, matan Annabi SAW sun yi kishi, amma ba don zai auro wata ba, ko don ƙwace wa wata gida, kowa so take ta sami ladar hahira, wannan kuwa dabi'a ce, sai dai in wata ta tsaya kan ba za a auro mata kishiya ba, kuma ta ce matan Annabi SAW ma sun yi kishi gaskiya ba su yi adalci ba, don ba a kan haka suka yi ba.

Wanda ya zauna a ƙasashen Larabawa ya zo kuma ya ga 'yammatammu a Nigeria waɗanda suke neman miji zai ce Alhamdu lillah,  abu ne da ba sai an gaya maka ba, mata sun yi yawa yanzu a duniya, makarantu, kasuwanni, motocin sufuri da sauran wurare duk mata ne, ga kashe-kashen da muke fama da su na maza, yaƙoƙi, bama-bamai, ko a tara su ma a bindige, hatta hatsarin mota yanzu maza sun fi mutuwa a ciki, kenan banda ƙaruwar hayayyafar mata, akwai mutuwar maza, yawan mata na rubanya ta maza in har ba za a ci gaba da auren mata biyu zuwa hudu ba, wasu matan za a haramta musu aure har abada,  ba wai ba sa son yi ba ne, saboda mazan ne ba sa son su aure su.

Na taba miƙo tambayata inda na ce macen da ta wuce shekara 35 ba miji meye sunanta? Gaskiya babu wani suna sananne wanda mutane suka saba aiki da shi, da wannan za a ce babu jinkirin aure har zuwa rabin rayuwa a al'adarmu, in ma akwai to yanzu ne yake faruwa, dole masana su natsu su samar da sunan macen da ta tsufa ba ta sami miji ba, a hirar da muka yi da wata Balarabiya ta tambaye ni sunan macen da mijinta ya mutu, da wace aka sake ta, na ce sunansu Bazawara , tana ta jin dadi, ta ce "Kun yi sa'a" su a wajensu in dai aka saki mace ƙila sai dai a nemo wani dan uwa a hada ta da shi, amma samun miji na wahala.

Na taɓa jin wani ɗan ajimmu yana magana da wata Balarabiya tana gaya masa cewa damar da ta samu ke nan na aure, matar ta shafe shekara 45 ba miji, tana roƙonsa da cewa in dai ya tsaya a kan wani mutuminsa har aka yi auren za ta ba shi wani kaso mai yawan gaske daga cikin sadakinta, ni kaina lokacin da  nake da shekar 35 wani likita ya taba cewa zai tsaya min na auri wata 'yar shekara 45, ya kuranta cewa yarinya ce ƙarama kuma ko auren fari ba ta taba yi ba, kai har an kai ga cewa a yi auren ni ina Nigeria ita kuma tana ƙasarta, in na sami kudi na kawo mata ziyara, ita ma in ta samu ta zo ta yi 'yan shekaru ta koma, duk da wannan matsalar ta wahalar samun miji mata sun kasa fahimtar cewa su suke haifar wa kansu da matsalar, mace na da 'ya'ya mata har 6 a gabanta amma tana cewa ba shegiyar da ita isa ta aure mata miji.

ZAUREN MARKAZUS SUNNAH

Post a Comment

0 Comments