Jiyan nan da za mu yi magana a kai tsawo gare ta. Akwai jiya ta kusa, akwai kuma jiya ta nesa. Amma magana ta gaskiya ita ce, duk jiya, jiya ce. Jiyan nan ita ce dâ ko dauri. Bari mu fara da harshen Hausa. Shekaru masu yawa da suka shuɗe, harshen Hausa cike yake da azanci da hikima, kuma ana iya ganin hakan a waƙoƙin Hausawa da maganganunsu na azanci da karin magana. Hausawa a dâ sun damu da harshensu ƙwarai da gaske har ma ya zama abin burgewa ga jama’a idan mutum ya iya sarrafa Hausa ta hanyar amfani da karin magana ko habaici ko zambo ko zuga ko maganganun azanci ko luguden kalmomi. Don haka a dâ, Hausa ta yi martaba a idon Hausawa. Amma a yau, abin ba haka yake ba. Nan gaba za mu ji labarin Hausa a yau.

Hausa da Hausawa: Jiya da Yau da Gobe
Prof. Ahmed Halliru Amfani

0.    GABATARWA
Maƙasudin wannan lacca shi ne a yi tsokaci a kan Hausa da Hausawa. Yaya Hausa da Hausawa suke a dâ? Yaya suke yanzu? Mece ce makomarsu nan gaba? Ta yaya za mu hudowa wannan batu ta yadda zai yi ma’ana, ya kuma yi armashi?
Abubuwan da za mu tattauna sun kasu gida uku:
.     Tarihi ko labarin abin da ya wuce.
.     Abubuwan da suke faruwa yanzu, kowa yana gani, ana kuma ji.
.     Abubuwan da za su faru gaba, wato makomar  al’umma.
Za mu fara da tambaya: Mece ce Hausa? Su wane ne Hausawa?

1.    MECE CE HAUSA?
Hausa harshe ne, kuma Hausa tana ɗaya daga cikin harsunan ƊanAdam waɗanda ake samu a nahiyar Afirka. A lissafi ko ƙididdiga irin ta masana ilmin kimiyyar harshe (linguists), harshen Hausa yana cikin wani babban rukuni na kason harsunan duniya wanda ake kira Afroasiatic. Shi ma wannan babban rukuni yana da ‘ya’ya, kuma kowane ɗa, shi ma ƙaramin rukuni ne mai ɗauke da harsuna. Ƙaramin rukunin da Hausa ke cikinsa shi ake kira gidan harsunan Chadi. Wasu harsunan ‘yan gidan Chadi, waɗanda ‘yan’uwan Hausa ne, su ne Angas da Bole da Ngizim. A ƙididdigar masana, akwai mutane kimanin miliyan hamsin Hausawa da waɗanda suke jin Hausa. Hausa tana da gidanta na gado a arewacin Nijeriya da kudancin Jamhuriyar Nijar. Wannan gida na gado na Hausa shi ne mazaunin Hausawa waɗanda harshensu na gado, na uwa, shi ne Hausa. Hausawa sun kai Hausa wurare daban-daban irin su ƙasashen Ghana da Togo  da Benin  da Cameroun da Chad da Sudan da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A cikin Nijeriya, kusan ba jihar da Hausawa ba su kai Hausa ba. (An Index of Nigerian Languages (1992), Ethnolologue (2009)).
Harshen Hausa harshe ne daɗaɗɗe, kammalalle kuma yalwatacce wanda yake biya wa Hausawa bukatarsu ta sadarwa da sauran bukatoci na yau da kullum. Harshen Hausa harshe ne isasshe wanda kuma babu irin nazarin da masana ba su yi ba a kansa. Harshen Hausa harshe ne mai farin jini wanda a yau akwai mutane fiye da miliyan ashirin waɗanda suka iya shi, kuma suna amfani da shi. Harshen Hausa fitaccen harshe ne domin kuwa ya watsu a duniya, kuma babu nahiyar da ba a san Hausa ba.

2.    ƘASAR HAUSA
An ce gidan Hausa na gado shi ne arewacin Nijeriya da kudancin Jamhuriyar Nijar. ‘’An tabbatar da cewa a can cikin tarihi akwai wani lokaci da mutane suka yi ta yin ƙaurace-ƙaurace daga yankin Tafkin Chadi suna yin yamma. Babban dalilin yin waɗannan ƙaurace-ƙaurace shi ne ƙeƙashewar Tafkin Chadi. Gulbin Kebbi shi ne maƙurar wannan ƙaura a sashin yamma. Tsakanin Gulbin Kebbi da Tafkin Chadi akwai nisa ƙwarai kuma akwai makekiyar ƙasa. A lokacin ƙaurace-ƙauracen, waɗansu mutane sun ƙarasa har Gulbin Kebbi, waɗansu kuwa iyakarsu tsaunukan ƙasar Bornu. Mafiya yawan mutanen sun watsu ne a wurare daban-daban cikin wannan makekiyar ƙasa. Waɗannan mutane sun daɗe ƙwarai a wannan makekiyar ƙasa yadda har ma ba a san tun lokacin da suka zo ba. Ba a san su sosai ba sai a ƙarshen ƙarni na sha biyar. Mutanen ƙabilu ne daban-daban. Hausawa da Bolawa da Ngizim da Manga da Margi da Buduma da Kotoko su ne manya daga cikin ƙabilun. Daga cikin manyan ƙabilun, Hausawa sun fi yawa, kuma sun fi warwatsuwa cikin wannan makekiyar ƙasa...Ƙasar Hausa tana da girma ƙwarai da gaske. A miƙe, daga arewa zuwa kudu, ƙasar Hausa ta fara daga Azben har i zuwa ƙusurwar arewa maso gabas ta tsaunukan ƙasar Jos. Daga nan sai ta kwasa ta yi yamma har i zuwa inda kogin Kaduna ya yi babban doro. Daga nan kuma sai ta buga ta yi arewa maso yamma sai da ta dangana da wani ƙaton kwari na Gulbin Kebbi. Daga wannan wuri sai ta karkata ta nufi arewa maso gabas har Azben. Wannan zagaye shi ya nuna iyakokin ƙasar Hausa a gabas da yamma da kudu da arewa. ƙasar  da waɗannan iyakoki suka iyakance, ita ce Ƙasar Hausa. Har i zuwa yau, wannan ƙasa, wato ƙasar Hausa, ita ce mazaunin Hausawa. Hausawa sun zauna a wannan makekiyar ƙasa fiye da shakaru dubu ashirin.
 Duk da haka, waɗansu abubuwa sun faru  waɗanda suka kawo faɗaɗuwar Ƙasar Hausa. Ire-iren abubuwan sun haɗa har da nashe waɗansu al’ummai waɗanda asalinsu ba Hausawa ba ne. Faɗaɗuwar Ƙasar Hausa ta faru ne a ƙarni na 15, da na 16 da na 17.’’ (Amfani (1980)).
Tsarin zaman Hausawa yana da ban sha’awa domin kuwa suna zaune ne a garuruwa da birane da ƙauyuka. Hausawa tun fil azal suna da tsarin mulki na zaman gida da zaman gari da zaman karkara. Don haka a tsarin zaman Bahaushe, akwai rukunin shugabanni (sarakuna da hakimai da dagatai da masu unguwanni). Zuwan Musulunci ya sa aka sami ƙarin alƙalai a rukunin masu mulki. Baya ga rukunin masu mulki, sauran jama’a duka talakawa ne. To, amma ko su talakawan sun kasu kashi-kashi. Akwai rukunin malamai. Akwai rukunin attajirai. Akwai rukunin masu sana’a da sarakunansu. Wani rukunin kuma wanda ya jiɓinci masu sarauta shi ne rukunin masu tsaron ƙasa (mayaƙa da dogarai da yaran sarki). Idan aka kalli wannan tsari na zaman Bahaushe  da kyau, za a ga cewa babu wani rukuni na mutane waɗanda suke zauna gari banza. Ko maroƙa da ɓarayi duk suna cikin ajin masu sana’a! Rayuwar Bahaushe daga haihuwa zuwa mutuwa ta ƙunshi a haifi ɗa, idan aka yaye shi, ya shiga makaranta. Idan ya samu ilmi, ya ɗan data , sai ya shiga koyon sana’a. Idan ya iya sana’a, sai ya samu wuri ya gina ɗaki ko gida inda zai saka matarsa. Daga nan sai aure, sai haihuwa da hayayyafa kamar yadda shi ma aka haife shi. Wannan tsari, idan aka kula, bai bayar da dama ba ko kaɗan na yin lalaci da shantakewa da zama cima kwance. Yin watsi da wannan kyakkyawan tsari yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka gurɓata rayuwar Hausawa a zamaninmu na yau.

3.    HAUSAWA
Abin da ya takalo wannan batu na wannan takarda shi ne irin damuwar da mahankalta suke bayyanawa dangane da makomar Hausa da Hausawa. Mahankalta na ganin cewa a dâ Hausa da Hausawa sun yi rawar gani, kuma Hausawa sun yi rayuwa mai ma’ana. To, amma a yau, abubuwa sun taƙarƙare, kuma a irin ma’aunin da waɗannan mahankalta suke auna abubuwa, sun ga lalle Hausa da Hausawa sun yi ƙasa a gwiwa. Don haka sai tsoro ya kama waɗannan mahankalta game da makomar Hausa da Hausawa nan gaba.Mahankaltan sun kwatanta jiya da yau, sannan suka yi hasashen abin da zai auku a gaba. Yaya duniyar Hausa da Hausawa take a dâ? Yaya Hausa da Hausawa suke a yanzu? Yaya gaba za ta kasance?
Kafin mu tsunduma cikin bayani, lalle ne mu jawo hankali da cewa addinin Hausawa shi ne Musulunci, kuma sun daɗe cikinsa, kuma ya yi tasiri sosai a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.

4.    HAUSA DA HAUSAWA  A  JIYA
Jiyan nan da za mu yi magana a kai tsawo gare ta. Akwai jiya ta kusa, akwai kuma jiya ta nesa. Amma magana ta gaskiya ita ce, duk jiya, jiya ce. Jiyan nan ita ce dâ ko dauri. Bari mu fara da harshen Hausa. Shekaru masu yawa da suka shuɗe, harshen Hausa cike yake da azanci da hikima, kuma ana iya ganin hakan a waƙoƙin Hausawa da maganganunsu na azanci da karin magana. Hausawa a dâ sun damu da harshensu ƙwarai da gaske har ma ya zama abin burgewa ga jama’a idan mutum ya iya sarrafa Hausa ta hanyar amfani da karin magana ko habaici ko zambo ko zuga ko maganganun azanci ko luguden kalmomi. Don haka a dâ, Hausa ta yi martaba a idon Hausawa. Amma a yau, abin ba haka yake ba. Nan gaba za mu ji labarin Hausa a yau.
Hausawan dâ ko Hausawan dauri ko Hausawan jiya, mutane ne waɗanda suka san kansu. Mutane ne waɗanda suka fahimci zamaninsu. Mutane ne waɗanda suka riƙi addininsu da gaskiya. Akwai waɗansu fitattun abubuwa waɗanda Hausawan dâ suka riƙe, waɗanda kuma su ne suka ba Hausawan girma da ɗaukaka.
Manufar rayuwa ga Bahaushen dâ ita ce a yi rayuwa ingantacciya, a mutu kuma a samu aljannar Allah.Bahaushen dâ ya riƙe waɗansu abubuwa muhimmai waɗanda su ne gishirin rayuwa, waɗanda kuma su ne ke sanya rayuwa ta yi inganci. Bahaushen dâ yana da tattali da tsantseni da kulawa a al’amuransa na yau da kullum. Waɗannan abubuwa su ne suke sa a samu gida ko iyali na gari. Don haka Bahaushen dâ yake da tsantseni (takatsantsan) wajen aure; yake da tattali don gudun kada ya shiga tsaka mai wuya; yake da kulawa wajen harkar iyalinsa da aikinsa da addininsa.
Bahaushen dâ yana tsare gaskiya da amana a dukkan al’amari. Bahaushen dâ yana da zumunci, sannan ga kana’a (ko dangana) da haƙuri game da duk halin da rayuwa ta kasance.
Bahaushen dâ yana kiyaye shari’a, sannan yana da ɗa’a. Akwai shi da ɗa’a ga shugabanni da sauran jama’a. Bahaushen dâ yana da ƙoƙarin neman ilmi, musamman ilmi na addini. Wannan shi ya kawo almajirci da zuwa gabas neman karatun ƙur’ani. Bahaushen dâ ya yi imani da cewa, ‘’a san mutum, a san cinikinsa.’’ Don haka duk Bahaushen dâ za a tarar da shi ƙwararre ne a fannin sana’arsa.
Wani shahararren abu game da Bahaushen dâ shi ne jaruntaka. Bahaushen dâ jarumi ne, kuma yana yaba jaruntaka. Bahaushen dâ bai san ragwanci ba. Labaru da tatsuniyoyin Hausawa sun tabbatar da hakan. Baya ga jaruntaka, Bahaushen dâ  mutum ne mai ƙwazo. Da yake Bahaushen dâ ya san kansa, shi ya sa ba ya son wulakanci na rainin wayo ko na rainin arziki. Wannan shi ya tilasta Bahaushen dâ  ya zama jarumi kuma mai ƙwazo.
 Bahaushen dâ akwai shi da kirki da halin girma. Bahaushen dâ yakan yi halin girma ga ‘yan’uwa da baƙi da sauran jama’a. Wannan hali na girma shi ya ba Bahaushe daraja a idon wasu har ma sukan yarda da shugabancinsa a baƙon wuri. Halin girma a kullum suna tafiya ne tare da kirki. Bahaushen dâ ya yarda da kirki, har ma yakan yaba wa mai kirki, ya kuma ƙyamaci maras kirki.  (A duba takardar A. H. M. Kirk-Greene mai taken ‘Mutumin Kirki’ wadda ya rubuta a kan kirki a idon Bahaushe).
Waɗannan abubuwa da muka ambata ba su kenan ba game da halaye na gari na Bahaushen dâ waɗanda su ne suka shi ya yi martaba da ƙima a idon duniya. A yau, da alama cewa da dama daga cikin waɗannan halaye na gari an zubar da su an rungumi sababbi, marasa inganci. Inda kuma ake aiwatar da su har yanzu, sai a tarar an sa wata tsirfa a ciki.

5.    HAUSA DA HAUSAWA A YAU
Hausa da Hausawa a yau sun shiga cikin matsaloli iri daban-daban. Idan muka waiwayi tarihi, sai mu ga cewa Hausawa sun daɗe suna yawace-yawace cikin ƙasashe waɗanda ba na Hausa ba. Ta wannan hanya ce suka kai harshen Hausa wurare daban-daban. A duk inda Hausawa suka je, sukan yi gari ne ko unguwa tasu ta kansu. Hakan ya taimake su wajen rage gurɓacewar harshensu da addininsu. A yau, a duniya akwai wata babbar matsala da ke son ta shafe mafi yawan harsunan ɗanAdam a doron ƙasa. Wannan matsala ita ce ta globalization ko ƙoƙarin tsukanta duniya ta zama kowa da kome an zama kusa da juna. Samuwar wannan kusanci zai yiwu ne kawai ta hanyar internet.  Internet  shi ne jirgen da ke ɗauke da duk al’amuran globalization. Masu gudanar da hidimar globalization sun zaɓi harshen Ingilishi ya zama shi ne harshen yaɗa manufofin globalization da aiwatar da shi. Don haka a irin wannan tsari, ɗanAdam ba ya buƙatar harsuna da yawa a doron ƙasa. Tuni harsuna har sun fara mutuwa. Kodayake ana ganin Hausa tana da masu amfani da ita da yawa kuma ana amfani da ita ɗin, duk da haka idan aka kula sosai za a ga Hausa tana gurɓacewa kuma ba mamaki zuwa gaba ita ma ta ɓace. Tilas ne a halin da ake ciki yanzu a ƙara matsa ƙaimi wajen ganin ana amfani da Hausa sosai da sosai, a kuma duk inda ya dace a yi amfani da ita. Tilas ne Hausawa su yi kishin Hausa in har suna so ta ƙara tsawon rai, ta kuma tsira daga sharrin globalization.
Idan muka juya ga Hausawa da tadodinsu a yau, sannan muka nemi mu kwatanta jiya da yau, sai mu ga cewa Hausawa sun yi ƙasa a gwiwa. Zamani ya yi wa Hausawa illa sosai. Kusan dukkan ɗabi’u da al’adu na kirki da muka ambata na Hausawan jiya, duk sun kau, an maye gurbinsu da baƙin tadodi, kuma marasa kyau. Abu na farko shi ne da alama Hausawan wannan zamani ba su da wata cikakkiyar manufa ta rayuwa. Babu wata manufa bayyananniya ta neman duniya ko lahira. Shashanci da shaye-shaye da lalacewa su matasa suka sa a gaba. Bugu da ƙari kuma ga ta’addanci da ‘yandabanci. Sata da lalaci da zamba sun yawaita a cikin al’umma. Yara da manya ba su son gaskiya, kuma ba su iya riƙe amana. Lalaci irin na kwaɗayi da roƙo da bara ya shigi mutane sosai. Mutane masu lafiya zuciyarsu ta mutu sai son roƙo da bara. Masu ‘yar ƙaramar naƙasa sun mayar da bara sana’a. Hakan ya sa mutuncin Bahaushe ya zube a idon sauran mutanen ƙasa. A yau ta kai ga cewa harshen Hausa shi ne harshen bara a Nijeriya. Yara da matasa suna yi wa ilmi ɗaukar sakainar kashi. An ƙi a yi karatu tsakani da Allah don a ƙware sosai a duk fannin da ake koyo. Lalaci da zalunci da son banza sun sa masu neman ilmi ba su tsayawa su sami sahihin ilmi, ingantacce.
Neman duniya ido rufe a yau, ya sa  Hausawa sun shiga bin waɗansu hanyoyi na ƙasƙanci.  A yau mutane suna tsafe-tsafe don neman duniya. Karuwanci irin na zamani shi ma babbar illa ce ga Bahaushen wannan zamani. Mata da yawa sun yi watsi da mutunci, sun shiga harkar karuwanci. A lura a nan cewa irin wannan karuwanci na zamani ba ana yinsa ba ne don huce fushin auren dole ko tsananin talauci. Aure a wannan zamani  da muke ciki lalle yana tattare da irin nasa matsalolin. Wata babbar matsala ita ce ta rashin haƙuri. Wannan ya sa aurarraki a yanzu ba su daɗewa sai su mutu. Bahaushen dâ an san shi da riƙe aure, kuma kusan duk aure a dâ ‘sai mutu ka raba’. Wani muhimmin abu kuma da ya gurɓata rayuwar Bahaushen yau shi ne zalunci a shugabanci. Da dama daga cikin matsalolin da muka ambata ana iya shawo kansu idan akwai shugabanci na adalci.
Akwai abubuwa gama-gari na lalacewa cikin kowace al’umma  ta duniya. Bayanin da akan yi game da su shi ne alamu ne na ƙarshen duniya. Amma wannan ba hujja ba ce da za ta sa a yi shiru, a zura ido, a bar al’umma ta lalace. Sa’au Zungur, cikin waƙarsa ta Arewa, Jamhuriya ko Mulukiya?, ya yi hasashen lalacewar al’ummar Hausawa:
                  Matuƙar a Arewa da karuwai,
                              Wallah za mu yi kunyar duniya.

                  Matuƙar ‘yan iska na gari,
                              ɗan Daudu da shi da Magajiya.

                  Da samari masu ruwan kuɗi,
                              Ga maroƙa can a gidan giya.

                  Babu shakka ‘Yan kudu za su hau,
                              Dokin mulkin Nijeriya.

                  Su yi ta kau sukuwa bisa kanmu ko,
                              Mun roƙi zumuntar duniya.

                  Matuƙar yaranmu suna bara,
                              ‘’Allah ba ku mu samu abin miya’’.

                  A gidan birni da na ƙauyuka,
                              Da cikin makarantun tsangaya.

                  Sun yafu da fatar bunsuru,
                              Babu shakka sai mun sha wuya.

                  Matuƙar da musakai barkatai,
                              Da makaho ko da makauniya.

                  Ba muhalli nasu a Hausa duk,
                              Ba mai tonyon su da dukiya.

                  Birni, ƙauye da garuruwa,
                              Duk suna yawo Najeriya.

                  Kai Bahaushe ba shi da zuciya,
                              Za ya sha kunya nan duniya.     

Matsalolin zamani da suke addabar Hausa da Hausawa suna da yawa. Kaɗan ne daga cikinsu muka ambata a nan. Tilas ne a yi maganinsu in har ana so wannan al’umma ta ci nasara cikin harkokin rayuwa.

6.    HASASHEN GABA GAME DA HAUSA DA HAUSAWA
Idan taɓarɓarewar  al’amura da muke gani a yau suka ci gaba, to, goben Hausawa ba za ta yi kyau ba. Tunda abin ya zama haka, to, tambaya a nan ita ce, ‘’ina mafita?’’ Akwai mafita aƙalla iri biyu. Akwai mafita wadda kowa da kowa sai  ya sa hannu, sannan ne za a iya yin nasara. Akwai kuma mafitar da masana da masu mulki ne kawai za su iya samar da ita. 
Bari mu fara da ci-gaba. Me Bahaushe ya fahimta da ci-gaba? Da alama a irin tsarin zamani, Bahaushe ya so ya yi wa ci-gaba mummunar fahimta. Ci-gaban al’umma ba ya tabbata sai an shimfiɗa shi bisa wasu halaye da falsafa na ƙwarai. Falsafar Bahaushe tana ƙunshe ne cikin karin magana da maganganun azanci. Misali, duk halayen ƙwarai da aka san Hausawa da su, tilas ne a koma musu don a samu ci-gaba. Ana iya inganta waɗannan halaye na ƙwarai don su dace da zamani. Alal misali, juriya da ƙwazo da gaskiya da riƙon amana da mutunta sana’a da ladabi da biyayya, abubuwa ne waɗanda a kowane zamani, ci-gaba ba shi yiwuwa sai da su. Idan wata al’umma ta yi watsi da waɗannan kyawawan halaye, waɗanda su ne gishirin tafiya a kowace tafiya ta ci-gaba, to, babu shakka babu inda wannan al’umma za ta je a cikin zarafofin duniya. Wani ginshiƙin ci-gaba kuma shi ne ilmi na addini da na sana’a.
Idan muka koma ga masana a cikin al’ummar Hausawa, sai mu ga lalle suna da haƙƙi na su sake duba al’amarin al’umma, su daidaita mata sahu, su jagorance ta. Ba lalle sai masana sun kafa gwamnati ba kafin su sake juya al’amuran al’umma. Haƙƙin masana ne su kafa ƙugiyoyi irin na zamani (NGO’’s) masu ƙarfi na daidaita tunanin al’umma. Waɗannan ƙungiyoyi su ne za su riƙa wayar da kan jama’a a kan harkoki daban-daban.

Ta ɓangaren masu mulki kuwa, tilas ne hukuma ta yi wa al’umma jagoranci don samun rayuwa mai ma’ana. Mahukuntanmu sun jahilci abin da ake kira jagoranci na ƙwarai. A duniyar mutanen ƙwarai, mutum ba ya zama shugaba sai ya san mutanen da yake shugabanta. Tilas ne ya san asalinsu; ya san inda suka fito da inda za su; ya san matsalolinsu da buƙatunsu; ya san falsafarsu ta rayuwa; ya taya su hangen nesa don cimma burinsu na rayuwa. A yau shugabanni sun jahilci al’ummomin da suke shugabanta. Don haka zai yi wuya shugabanni su burge waɗanda suke shugabanta.

Wata mafita da ake ganin za ta taimaka wajen ciyar da Hausawa gaba ita ce a yi ƙoƙarin kafa Gidauniyar Hausa (Hausa Project). Manufar  wannan gidauniya ita ce a samu waɗansu mutane masu kishin Hausa da komai nata, su tashi tsaye su taimaka wajen yaƙi da gurɓacewar kyawawan al’adun Hausawa da kuma hana mutuwar harshen Hausa. Wannan gidauniya mutane ne za su kafa ta a dukkan wuraren da Hausa da Hausawa suke, da nufin kare martabar harshen da tadodin masu harshen. Akwai mutane da yawa da za su so su kafa wannan gidauniya a inda suke. Manyan ma’aikata da ‘yan kasuwa da sauran masu sana’a da matasa da malamai duk suna iya haɗa kansu, su kafa irin wannan gidauniya ta Hausa. Babban aikinsu shi ne su sa ido, su kuma tsawata ta hanyar faɗakarwa a kan dukkan lamurran da suka shafi Hausa da Hausawa. Alal misali, irin wannan gidauniya tana iya shirya tarurruka da laccoci da nuna finafinai don jawo hankalin al’umma, musamman matasa, ga wasu kyawawan halaye ko ɗabi’u na Bahaushe. Yin hakan lokaci lokaci zai yi tasiri ƙwarai da gaske. Kada a manta cewa akwai hukuma mai kula da harshen Hausa (Hausa Language Board) wadda aka kafa a shekarar 1955. Ita wannan hukuma har yanzu akwai ta, sai dai ba a ganin tasirinta sosai da sosai kamar yadda ake so a gani. Yawanci tasirin ayyukan hukumar an fi jin shi a da’irar malaman Hausa.

Don tabbatar da ci-gaban harshen Hausa, tilas ne Hausawa su matsa ƙwarai wajen nazarin harshen da kuma amfani da shi. A halin da ake ciki yanzu, Hausa tana gurɓata a hankali. Zuwa gaba, ba mamaki gurɓacewar ta wuce gona da iri. Ana nazarin Hausa a  ƙanana da manyan makarantu, amma yawan almajiran da ake yayewa a manyan makarantu bai kawo kallo ba.
7.    NAƊEWA
Magana a kan Hausa da Hausawa ba ƙaramar magana ba ce tunda Hausa babban harshe ne kuma Hausawa mutane ne masu yawan gaske. Akwai masu ruwa da tsaki a al’amuran Hausawa, kamar Hausawan da kansu. Hakkin hukumomi ne su tabbatar da ci-gaban al’ummar Hausawa da shi harshen Hausa. Dukkan masu ilmi suna da haƙƙi wajen ciyar da al’umma gaba da kuma kare harshen Hausa ta yadda ba zai mutu ba. Aikin babba ne, kuma yana da wuya, amma kuma dole ne a yi shi in har ana so harshen Hausa da al’ummar Hausawa su kai labari.
8.    ZAƁAƁƁUN LITTATTAFAN DA AKA DUBA
Abubakar, I. 1969. Auren Zobe – Abutar Nijeriya  Da Ingila. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
Amfani, A.H. 1980. Nazari A Kan Bambance-Bambance Tsakanin Zazzaganci Da Daidaitacciyar Hausa. B.A. Dissertation, Ahmadu Bello University, Zaria.
Austin, P. K. 2008. 1000 Languages – The Worldwide History of Living and Lost Tongues. London: Thames & Hudson.
Bargery, G. P. 1934. A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.
Crozier, D. H. and Blench, R. M. (eds). 1976. An Index of Nigerian Languages. Dallas, Texas: Summer Institue of Linguistics.
Lewis, M P. (ed.). 2009. Ethnologue – Languages of the World (16th Edition). Dallas, Texas: SIL International.
Smith, A. 1977. Early States of Central Sudan. In Ajayi, A. & Crowder, M (eds). History of West Africa (2nd edition) Volume I. London: Longman.   
Yakubu, A. M. 1999. Sa’adu Zungur – An Anthology of the Social and Political Writings of a Nigerian Nationalist. Kaduna: Nigerian Defence Academy Press.