Majority of the Hausawa are situated in the Northern Nigeria and the Southern Niger. Nevertheless, there are Hausa speakers in other parts of the world like Benin, Burkina Faso, Cameroon, Central African Republic, Chad, Congo, Eritrea, Ghana, Sudan, and Togo among others. The global population of Hausa speakers (as L1) is estimated to be above 45 million. However, other millions of people, perhaps more than 20 million, speak the language as L2. More so, the language is believed to be fast growing. This is indeed the positive effect of the richness in its lexicon, morphology, syntax and semantics as well as the simplicity of same. Another factor that contributes to the rapid spread of Hausa is the impressive mannerism, personality and the culture of its speakers. As one of the major Nigerian indigenous languages, others being Yoruba and Igbo, it is worth preserving and documenting. This would serve as campaign towards the development of the language. However, this is in line with the phenomenon that emerged national question, thus the need to reframe national language policy in order to have one or more indigenous language(s) as the official language(s) in Nigeria. Before that could be achieved, the indigenous languages must be developed in various domains of life such as; educational, scientific, social as well as political. However, this paper delves into the global growth of Hausa and the need to preserve the language. The preservative measures for the documentation of Hausa might include; recording and mobilization among others.
Waƙar Ranar Hausa

Hassan Abdu Blouse
hassanblouse1@gmail.com
08066303359


1.Ban ce ka dena ba ko ko ka fasa
Kai mai rarraina harshen Hausa

2.Amma ka san kowa ya bar fa gidansa   
To babu shakka ma gidan ya bar sa

3.Yau ga shi Hausar ta riga ta nusa
Ta keta har can Saudiyya da Faransa

4.Ta zam kamar nama cikan kaskonsa
 Ƙanshi yana tashi ana mararinsa

5.Ko ko kamar lemo da ɗan sanyinsa
     Kullun ana ƙaunarsa don daɗinsa

6.Ka ji har da VOA da dangoginsa
   Haka ma su BBC suna ta shirinsa

7.Har jami'o'in duniya sun san sa
      Sun tashi haiƙan ayyukan nazarin sa

8.Ɗan marmatso ka ji ma abin sha'awarsa
 Zai ja ka can sama sai a gan ka a nesa

10.A ƙasa gaba ɗaya duk ku san matsayinsa
 Shi ne fa liman sauran suna mamunsa

11.Yau ga shi ranar tasa har tai rassa
 Ogasta ne ashirin da ma fa shidansa

12.Ake ta biki buduri na harshen Hausa
A cikin gari har fesibuk da waninsa

13.Ni dai ina kishi ga harshen Hausa
 Har ma ina koyon dukan darasinsa

14.Zan dakata Hassaninku ne mai wasa
Kuma ɗalibi da yake nazartar Hausa

15.Ƙaro salati gwargwadon matsayinSa
Sannan ka sanyo dukkanin ahalinSa

16.Da sahabu ma, ni ban cire matansa
Dukkan rawata ma inai da bazarsa.