Wannan aiki na ƙunshe da jerin wasu
zaɓaɓɓun Karin
Maganganu waɗanda suke ɗauke da
hoton mata, abisa tsarin baƙaƙen
abajada, da aka zaƙulo daga
manazartu da wuraren samo bayanai daban-daban. Wannan
gudummuwata ce zuwa ga harshen Hausa. Ina sa ran su taimaka wa manazarta da ɗaliban ilimi, har ma da malamai.
__________________________________________
HOTON MATA A KARIN MAGANA
(THE IMAGE OF WOMEN IN HAUSA PROVERBS)
Shafa’atu Salihu Labbo
Mail: shafasalisulabbo@gmail.com
Phone No.: 07069252226
____________________________________________
A.
1.
Abin da kamar wuya, gurguwa da aure nesa
2.
Abin Allah, budurwa da jika
3.
Abin tsana, amarya a kan kare
4.
Abin wani abi ne, mayya da ta ci ɗanjariri
5.
Abin daga Allah ne, tsohuwa ta sami autan
‘ya’ya
6.
Abin nema ya samu, matar falke ta haifi
jaki
7.
Abin na yi ne, an biya wa bazawara Hajji
8.
Abin da ke ga amarya, shi take ba ango
9.
Abin ya zo, tsohuwa ta ji ƙarar
jirgin sama
10. Abin ya yi
daɗi, an bai
wa mayya jiran gawa
11. Abin da
kunya! Uwar ‘ya ta cinye suriki ranar aure
12. Abin nema
ya samu, matar malami da cikin allo
13. Abin nema
ya samu, matar ɗansanda ta
haifi ɓarawo
14. Abin daga
Allah ne, mai takaba ta yi ciki kafin arba’in
15. Abin da
mace ta yi, ta ce ta ji kunya, namiji in ya yi shi sai ya bar gari
16. Abu namu
uwargijiyar kyanwa da ƙuliƙuli
17. Adashen
Balaraba, ba riba
18. Adashen
Uwar nuhu
19. Aiki in da
kishiya ba ya gudu
20. A ja mu a
kai mu an ba uwar makaho kashi
21. A jiya
magani, tsohuwa ta yi tari
22. Akwai abu ƙasan
danga, baubauniya da cikin ɗan sarki
23. Allah ka
fidda A’i ga rogo
24. Allah ka
ci da mu, inji matar ɗan cirani
25. Allah ya
gani, an tura wata jinyar mayya
26. Allah
suture buƙui, inji kishiyar mai doro
27. Allah
maganin ‘yar sadaka, ‘yar kuɗi ubanta ɓarawo
28. Allah ya
sawaƙe wahala! Tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa
29. Amarya ba
kya laifi, ko kin karya ƙafar ɗan masu
gida
30. Amarya ba
ki laifi, ko kin kashe ɗan masu gida
31. An yi ba a
yi ba, mace ta haifi mace
32. Ana
tsorommu ni da iya, inji ɗiyar mayya
33. A rashin
sani Karen gwabro ya kori bazawara
34. A rashin
uwa akan yi uwar ɗaki
35. Asiri
rufe, an kama uwar amarya da ango
36. Asiri
rufe, batu da kishiya
37. A taɓa ni, aji
ni, mummuna ta je gidan biki
38. Auren
karuwa, auren banza
39. Auren
karuwa auren wofi ne
40. Auren
baya, shi ne sadakin na gaba
41. Aure yaƙin
‘yammata
42. Azarangaɗi,
mugunyar kishiya.
B.
43. Ba faɗa da
tsohuwa ba, jinini
44. Bazawara
uwar son banza
45. Bara
gurbi, kazar ‘yammata
46. Ban gane
ba, an daki ɗan kishiya
47. Babu dole,
ga goyon ɗan kishiya
48. Ba kuka na
ba, uwar kishiya ta mutu
49. Ba zafi,
barkonon tarau ga idon kishiya
50. Ba ni kafa
wa ɗan kishiya
gado ya hau
51. Bita da
kulli, dukar ƙabarin kishiya
52. Batu ya
mutu, mai hassada ta kwana baraya
53. Ba kai na
farau ba, mace ta yi cikin shege
54. Ba kullum
guɗa ba, inji
matar ɓarawo
55. Bance a
mutu ba, ban ce a warke ba, ciwon kishiya ayi ta lalacewa a kan gado
56. Babbar
Macce, wadda ba a sai mata gishiri
57. Bari mu taɓa mu ji,
nayya ta je barkar haihuwa
58. Bana
tsoron amarya da ango, balle ‘yan zaman ɗaki
Ɓ
59. Ɓatan
kai shawara da uwar kishiya
60. Ɓalangandi,
bukin dangin miji
C
61. Cab! an
ce da budurwa ta auri tsoho
62. Cas!
surhen dawar lami
63. Ciwon mace
na mace ne
64. Cin tuwon
kishiya, ranko
65. Cin ƙwan
makauniya, ba a ci ba, a bari ba
D.
66. Da alheri
kishiya ta hau kura
67. Da alamar
zane, an ba Baro ajiyar angurya
68. Daga baya
ke nan, sadakin bazawara
69. Da auren
karuwa, gara kiwon zakara
70. Dabara
kafa inji kishiyar gurguwa
71. Daddage,
kashin cinnakan tsohuwa
72. Da niyya,
karuwa ta taka matar aure
73. Daɗin aure,
shi ke sa a cewa miji baba
74. Da rashin
uwa akan yi uwar ɗaki
75. Da wane
zan ji? Da mutuwar uwa ko kishiya
76. Darajar
Mace miji
77. Da motsi,
farautar mata
78. Darajar
mace ɗakin aure
79. Da zaman
banza gara aikin kishiya
80. Dole a ba ɗan mata
fura
81. Dole a zo,
ɗaki ya faɗa wa
gurguwa da ɗan masu
gida
82. Da ka zama
ƙanen Alhaji gara ka zama ƙanen
Hajiya
83. Duniya
budurwar wawa
84. Duniya
rawar ‘yammata
Ɗ
85. Ɗan
kishiya riƙon mai haƙuri
86. Ɗoki!
Kurma ta ga miji
F
87. Faɗan gwaggo
a Ƙofa
88. Farar uwa
mai sanya alfarma ga ‘ya’yaye
89. Farar mata
abar shiga tsumma
90. Farawa da
iyawa, amarya da raga
91. Fatari
suturar mata
92. Farin
shiga, unguzomar Wasai
93. Funtuwa ta
yi zane biyar gari ya tashi
G.
94. Gaba ta
kai ni, gobarar Titi
95. Gadauniya,
makauniya da yekuwar wuta
96. Gadon ari
sai fanna
97. Ga mu ga
Allah mata ginar damo
98. Ga mu ga
Allah mai takaba ta taka gawa
99. Gara kowa
da ni, inji matar Bebe
100.
Gaɗa sarewar mata
101.
Gwamma ku da gwammar ku ɗaka
102.
Gwatsine aikin mata
H
103.
Haihuwa maganin mutuwa
104.
Haihuwa mai rana
105.
Haihuwa asusun uwa, randa ta fasa ta ga
riba
106.
Haihuwar tsakar dare, munafukai na barci
107.
Haka ratata, inji kishiyar mai ɗiya tara
mata
108.
Haka tara, inji kishiyar mai mageduwa
109.
Hankali ka rabon dawo, har a manta uwar
miji
110.
Halin uwa ɗiya kan ɗauka
I.
111.
Idan ba ki yi gashin wance ba, ba ki kitson
wance
112.
Ida ana dara fidda uwa ake
113.
Idan budurwar bana tana da kyau, ta baɗi ta fita
114.
Idan mayya ta manta, uwar ‘Ya ba ta
mantawa
115.
Ina laifin abokiyar faɗa, da ta
bar ki kika ɗaura zane
116.
Ina wayau, budurwa ta yi ciki
117.
Ina dalili gadon tsohuwa zai karye
118.
Ina tsoron kai na da gari, inji matar mai
kureci
119.
Ina ruwan mai jego da guru da tsakiya
120.
Ina gwari da miji ta ce baba ya isa
121.
Ina wayau karuwa ba zane
122.
In amarya ba ta hau doki ba, ba a aza mata
kaya
123.
Inji batu an kai ‘yar Tanko alƙali
124.
Ikon gwatse, kishiya hana kishiya amsa waƙar
miji
125.
Ilin, amarya ta ci ƙanen miji
126.
Isa da mallaka, biyan bashi da ɗan kishiya
127.
In til, in ƙwal, rinin
zanen mahaukaciya
128.
Iyakar dillanci, an saci zanen matar sarki
an kai an sayar
129.
Ina ruwan wani da wani, mahaukaciya ta yi
baƙuwa
130.
Iya yi sa sarakkuwa boko
131.
Iya yi karuwa da yawon dare
132.
Iya yi sa sarakkuwa NCE
J
133.
Jakin maginiya, sai ka ga dama akan ci
kasuwa
134.
Jinkirin jin kira, bazawara jiran karsa
135.
Jiya ba yau ba, tsohuwa ta ga kuɗin zance
136.
Jiya ba yau ba, tsohuwa ta tuna tsarince
137.
Jiya ba yau ba, tsohuwa ta tuna kwana
turaka
138.
Jiya ba yau ba, tsohuwa da tuna kwanan
gida
K.
139.
Kallabi tsakanin rawunna
140.
Kai ma nan, mace ta rena miji
141.
Kamar gaske, karuwa ta ga noman ɗan koli
142.
Kamar kumbu, kamar kayanta
143.
Komai wayon amarya, sai an sha manta
144.
Komai son rai ne, ƙawo da
makauniya
145.
Komai daɗin ki da
miji, kishin uwargida ya tashi
146.
Komai daɗin ki da
kishiya, inji babbar ƙawar amarya
147.
Kai waye kenan, bazawara da jaka
148.
Karuwa ba matar aure ba ce
149.
Karuwa ba ta kiwon kaza
150.
Karuwa kafirar dangi
151.
Karuwa matar kowa
152.
Karuwa kwata ce, ba ta tarar nagari da
jaki da kare da doki duk nata ne
153.
Katane ciwon masu haihuwa
154.
Kishi kumallon mata
155.
Koshin kishiya ba zai hana miji aure ba
156.
Kishiya sai naki, mai gida duba min
157.
Kishiya mai ban haushi, ana ganin ki akan
zagi miji
158.
Kilin kiso da balan ƙwaima,
kiran miji da akaifa
159.
Kowa ce bai iya kuka ba, uwarsa ce bata
mutu ba
160.
Kowa ya so uwa, ya so ‘yarta
161.
Kowa da kiyon da ya karɓe shi,
kishiyar mai akuya da kiwon kura
162.
Kukan rashin dalili, mutuwar uwar kishiya
163.
Kwasar karan mahaukaciya
164.
Kyanwar lami ba ta cizo ba ta yakushe
165.
Kyanwar lami ba ta miyan ba ta kamo ɓera
166.
Ku kuka sha ta furar Naito
167.
Kwarton uwa mai wuyar ganewa
168.
Kissar mata gomiya tara da tara ce, guda
ta cikon ɗarin
ibilis bai santa ba.
Ƙ
169.
Ƙafar mace
laya, kowa sai ya rataya
170.
Ƙaiƙayi
ya koma kan masheƙiya
171.
Ƙaƙalen
gulama’i gaida uwar saurayi a kasuwa
172.
Ƙaƙa
zan yi da abin da ya gagari wuta, inji kishiyar ƙonanniya
173.
Ƙarfin mata
yawan magana
174.
Ƙarya ba ta
sa amarya lalle
175.
Ƙoƙari
yana tura uwa a rame
176.
Ƙurasa
dangin sheɗan! In ba
ku ba gida, in kunyi yawa gida ya ɓaci
177.
Ƙodon
gwafiyo, roƙon miji gun kishiya
L.
178.
Lallaf ka bi da mace
179.
Lalata dake da goyon farin
180.
Lallenku ya fara kamu
181.
Lalura auren namiji da ‘ya’ya
M
182.
Mai uwa a bakin murhu, ba ya kukan yunwa
183.
Mai uwa a bakin murhu ba ya cin tuwonsa
gaya
184.
Mai uwa a bakin murhu ba zai ci tuwonsa ba
miya ba
185.
Mai ci da uwa, ba ya kukan suɗi
186.
Mai uwa sarki ne, mai uba Lamiɗo
187.
Mai kuda ba ta son mai koda
188.
Mai zane ɗaya ba ta
ba da aro
189.
Mace mai kamar maza
190.
Mace mai ƙoƙari,
,ko ba miji ta haihu
191.
Mai kishiya ba ta mutuwar Allah
192.
Mata mance su yi maka gayya
193.
Mata tarkon shaiɗan, in ya
haƙa kamawa yake
194.
Mata suna suka tara
195.
Mata haja ne, kowa da tayin da ya karɓeta
196.
Matar wani ba ta wani ba
197.
Mata ba ku haihuwa ku lashe abinku
198.
Mata mugun abu, nama ya kashe ɗan mowa
199.
Mata ba tukwane ba ne, balle a ƙwanƙwasa
a ji wadda ta fi ƙwari
200.
Matar mutum ƙabarinsa.
201.
Matar na tuba ba ta rasa miji
202.
Matar bari in tashi ba ta ƙwadda
mijin ta
203.
Mai zane gamin baki ba ta wa miji yanga
204.
Ma ji ma gani an rufe tsohuwa da ranta
205.
Maso uwa ya so ‘yar ta
206.
Magana ta ƙare, mata
ta ce wa mijin ta “shege”
207.
Muna ga rasulu ɗiyar boka
ta rasa miji
208.
Mace darajar namiji ce
209.
Me ya fi raina? Cin tsiren mata
210.
Me zan ce? Zanen aro ya ƙone
211.
Muraran muraran ganin annabin tsohuwa
212.
Mu ‘yammantan gara ne, in ance mu ɗauka mu ɗauka
213.
Mhm! Inji matar Ɓarawo.
N
214.
Na ba ki nawa domin naki, in babu naki
nawa ya komo
215.
Na gaji mai hana wa mata lada
216.
Na ga abin da ya ishe ni, kishiya tara
rana ɗaya
217.
Na iya rawa ta a gaban masheƙiya,
ban taɓa fasa
mata kwarya ba
218.
Na san a rina, an Saci zanen mahaukaciya
219.
Na shiga zunɗe, kishi
da maras hankali
220.
Na taɓa ki da
alheri, kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta
221.
Namiji tabarmar ƙashi, inji
wadda mijinta ya ɓata wa rai
222.
Ni ba tagari ba, yaƙi ya ci
karuwa
223.
Ni na sani, sautun mahaukaciya.
R.
224.
Rashin uwa hasara ne
225.
Rashin uwa kasa a yi uwar ɗaki
226.
Rashin kunya, mace, ta auri mace
227.
Rashin haƙuri shi ke
sa budurwa farka
228.
Rashin haƙuri ya sa
budurwa ta yi ciki
229.
Rashin sani yasa aka yi wa uwar miji
kishiya
230.
Rabo, aure da ciki
231.
Rana bata ƙarya sai
dai uwar ɗiya ta yi
kunya
232.
Rabiɗin leɓo, shawara
da uwar kishiya
233.
Riƙon gida
sai mata
234.
Rufin kan uwar daɗi, gabanta
babu kariya
235.
Rumumui-rumumui, taunar ƙashin
tsohuwa
S
236.
Sai uwa ta ƙosh ɗan ta ke
malolo
237.
Sai ka yi sababbe, karuwa taji mai wa’azi
238.
Saki jikinka, barawo a hannun mata
239.
Salula shawara da uwar kishiya
240.
Samun wuri, zuwa bariki da uwa
241.
Sallallahu sanyi ƙalau, mai
takaba ta ba da waƙa, an amsa
242.
Saurin Tagumbi
243.
Son kira kamar bazawara
244.
Son a sani, yaji da kwarin miji har da ɗan masu
gida
245.
Sauna matar ‘yan cirani
246.
Somin aure tsarince
T
247.
Ta fi babu kakar wajen uba
248.
Ta jefa ta cafe, matar talaka ta ga matar
mai arziki
249.
Takaici zalla, haihuwa da maƙiyi
250.
Takaicin tausai, budurwa da auren karsa
251.
Tambaɗa sayen
kandu ba zane
252.
Tamɓele zuwa bikin
dangin miji
253.
Tambaɗar zamani,
mata biɗar maza
254.
Ta-ta-ta kuturwa zuwa baraya
255.
Tantarakwai, mata ta turke miji
256.
Ta mice ce? An ba tsohuwa fataka
257.
Tilas a gyara wa amarya ɗaki
258.
To, inji mai tallar tuwo-tuwo
259.
Tsautsayin takaba, aure da majinyaci
260.
Tsohuwar gida hana walwalar iyali
U
261.
Uwa gandun daɗi
262.
Uwa maba ɗa mama
263.
Uwar gida ran gida
264.
Uwar gida sarautar mata
265.
Uwar raggo ake wa barka
266.
Uwar raggo ake yi wa jaje
267.
Uwar maza daka ke kashe ki
268.
Uwar wani kakar wani
269.
Uwa ma ta mutu balle kaka
270.
Uwa mafi uba koda uban sarki ne
W
271.
Wada da waɗaƙa,
tada kai da kishiya
272.
Wa ka faɗi? Uwar
Sarki da maƙoƙo
273.
Wahala na ga mai ɗiya tara
mata, ya sai da biyar ya yiwa huɗu aure
274.
Wanda uwarsa ta faɗa rijiya
baya ganin tsadar igiya
275.
Wannan shi ne tsegumi, an ce da mai ciki
ta haihu
276.
Wargi wuri ya kai, ban da tsikarar uwar
–miji da taɓarya
277.
Wa ya isa ya faɗa? Gyambon
uwar sarki na ɗoyi
278.
Wasan kokawa ba na gurguwa ba ne
279.
Wayayyen hauka, goyon ɗan kishiya
ga naki
280.
Wayyo Allah na, Inji ‘yar wawa
281.
Wuce ni, karuwa ta ga maras kwabo
Y
282.
Yabanya Allah ya fisshe ki fari
283.
Ya da guda ɗauki guda,
inji budurwa ƙauye
284.
Ya kamata auren na gida, yarinya da ta ga
wanta da kuɗi
285.
Yarinya farkon ki maɗaci, ƙarshenki
zuma
286.
Yanga ga ‘yar talaka hasara
287.
Yaya aka yi uwa ta gujewa ɗanta
288.
Yaya na iya da abin da ya gagari wuta,
inji kishiyar ƙonanna
289.
Ya yi auki! Uwar miji ta ƙi
cin tuwo
290.
Yau na ga abin da ya ishe ni, kishiya tara
ɗai rana
291.
Yin kunnen uwar shegu, shiru!
‘Y
292.
‘Ya mace ‘yar kasha gida
Z
293.
Zance ya ƙare, sai ɗaurin aure
294.
Zanen aje sai ranar gaɗa
295.
Zanen aro bas hi rufe katara
296.
Zama da kishiya tilas ne, ba don uwargida na
so ba
297.
Zama da kishiya tilas ne, ba don dukansu
sun so ba
298.
Zugurnugu, kishi da masu iyaye
299.
Zungure aikin mata
300.
Zunguru abin ƙunshin
mata, ba a saka a yi yawo
301.
Zuƙui, doron
kishiya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.