Ticker

6/recent/ticker-posts

Buki Salatin Mata: Rawar Mata A Bukukuwan Garin Tsafe



 Al’adun Hausawa sun samu sauye-sauye da dama a goshin ƙarni na ashirin da ɗaya. Bisa ga haka, za a ga cewa wasu al’adun suna salwanta wasu kuma suna  gurɓata, kai ka ce ba ma na Hausawa ne ba. Kamar irin su al’adun aure da na haihuwa da na zamantakewa, da dai sauran makamantansu. Wannan shi ya ƙarfafa mini guiwar yin wannan bincike a kanrawar mata ke takawa wajen sauya fasalin bukukuwa a garin tsafe.
 ______________________________________________________
NA
SADIYA KABIRU
Sadilawalfug@yahoo.com
08069673875
_______________________________________________________

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan kundin bincike nawa ga mahaifana Alh. Kabiru Bagudu Tsafe da Malama Hussaina Sani Mai Yadi Tsafe.
GODIYA

Ina godiyaga Allah Maɗaukakin Sarki Mai Kowa Mai Komai, wanda ya bani iko na gudanar da wannan aiki cikin nasara.
Haka kuma ina mika godiya ta musamman ga Maigidana da ya ɗauki nauyin ɗawainiyar karatuna har na kammala.
Ina jinjina da ɗimbin godiya ta musamman ga Dr. Yakubu Aliyu Gobir, wanda ya duba wannan aiki tare da yin gyare-gyare da kuma bayar da shawarwari har wannan bincike ya kamala. Ubangijin Allah Ya sa kama sa da gidan Aljanna, ya kuma yi masa jagoranci a cikin ayyukansa. Haka kuma, ba zanyi ƙasa a guiwaba, wajan miƙa jinjina da godiya ta musamman ga Shugaban wannan Sashe, wato Farfesa Aliyu Muhammad Bunza,  Allah ya sa ya gama lafiya. Haka kuma, bazan manta da sauran Malaman Sashe ba, waɗanda sukai ta faɗi tashi da mu, har muka kawo wannan lokaci: wato Mal. Aliyu Rabi’u Ɗangulbi da Mal. Musa Abdullahi da Mal. Isah S/fada da dai sauran Malaman Sashe. Allah Ya sa kamasu da gidan Aljanna maɗaukakiya, kuma ya yi masu jagoranci a cikin ayyukansu.


BABI NA ƊAYA: GABATARWA
1.0     Shimfiɗa
Al’adun Hausawa sun samu sauye-sauye da dama a goshin ƙarni na ashirin da ɗaya. Bisa ga haka, za a ga cewa wasu al’adun suna salwanta wasu kuma suna  gurɓata, kai ka ce ba ma na Hausawa ne ba. Kamar irin su al’adun aure da na haihuwa da na zamantakewa, da dai sauran makamantansu. Wannan shi ya ƙarfafa mini guiwar yin wannan bincike a kanrawar mata ke takawa wajen sauya fasalin bukukuwa a garin tsafe.
Domin cimma nasara a wannan bincike, an karkasa shi zuwa babi- babi har guda biyar, kamar haka: Babina ɗaya, shimfiɗa ce aka yi wa aikin, domin ya samu gindin zama sosai. A cikin shimfiɗar, an yi bayanin dalilin da suka sayin wannan bincike da manufar gudanar da binciken da kuma muhimmancinsa. Har ila yau, babin yana ɗauke da bayanin muhallin da za a gudanar da binciken da kuma hanyoyin da za a bi don gudanar da binciken. A ƙarshe an yi bitar ayyukan da suke da alaƙa da binciken, da kuma hujjojin da za su ba da damar ci gaba da gudanar da  binciken.
A babi na biyu kuwa,an kawo tarihin garin Tsafe kacokam, wato muhallin gudanar da binciken. A cikin wannan babi, an yi bayani a kan asalin sunan garin Tsafe, da kafuwar garin Tsafe da yanayin garin. Hakakuma, babin ya yi bayanin tsarin mulkin sarakunan ƙasar Tsafe da mulkin ’Yandotawa a Tsafe da naɗin sarautar ’Yandoto da kuma sunayen sarakunan Tsafe tun farkon kafa garin har zuwa yau.
Babi na uku,yana ɗauke da bayani a kan bukukuwa a garain Tsafe, a inda aka yi bayaninyadda ake gudanar da wasu bukukuwa da suka haɗa da: bukin aure da na haihuwa, dabukin sallah da na maulidi da na saukar Alƙur’ani da sauransu. Sannan daga ƙarshe a kawo tasirin zamani a kanwaɗannan bukukuwan a garin Tsafe a yau.
Babi na huɗu, shi ne ƙashin bayan aikin, domin shi ke ɗauke da bayanin rawar da mata ke takawa a bukukuwan garin Tsafe. Babin, ya yi ƙoƙarin bayyana yadda mata ke shige da fice a wajen gudanar da bukukuwa, irin su, Gasar kwalliya da gasar liyafa da sata a gidan buki da gudunmuwar ’yan buki da faɗace-faɗace da tsegunguma da tsince da kiɗa da rawa da ƙirjin buki da kuma ajo.
Babi na biyar kuwa yana ɗauke da jawabin kammalawa, a inda aka yi jawabin taƙaitawar aikin, aka bayar dasakamakon aikin, sannan a ƙarshe aka bayar da shawarwari ga manazarta da ɗalibai da malamai da kuma hukumomi gaba ɗaya.


1.1      Dalilin Bincike
Dalilin gudanar da wannan bincike na wannan muhimmiyar al’ada ta bukukuwan Hausawa a garin Tsafe shi ne, domin a zaƙulo wasu muhimman bayanai na al’adun waɗannan fitattun bukukuwa a garin Tsafewaɗanda sun bambanta da sauran bukukuwan gargajiya na wasu garuruwa.
Wani dalilin kuwa shi ne, domin a samar wa ɗalibai wani kundi na bincike, ga masu sha’awar nazarin al’adun Hausawa da kuma waɗanda za su ƙara faɗaɗa bincike a kan waɗannan al’adu na bukukuwa.
Sai kuma wani babban dalilin ko kuma a ce maƙasudin wannan bincike shi ne domin cika ɗaya daga cikin sharuɗɗan samun takardar shaidar digiri na farko a ƙarƙashin Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu na Jami’ar Gwamnatin Tarayya Garin Gusau.
1.2      Manufar Bincike
 Babbar manufar wannan bincike ita ce binciko yadda mata ke taka rawarsu a wasu fitattun bukukuwa  da suka fi yi fice a garin Tsafe, kamar bukin aure da bukin suna da bukin salla da bukin mauludi da bukin  walimar sauka, da kuma yadda ake yin kowane daga cikin waɗannan bukukuwan. Haka kuma, wata manufar ita ce fito da wasu sauye-sauye na zamani da ake samu a cikin al’adun Hausawa. Wasu sauye-sauyen masu amfani ne da ƙarin samun wayewar kai, wasu kuma sun kawowa al’adun cikas, wato ci gaban mai ginar rijiya.
1.3      Muhimmancin Bincike
 Wannan bincike yana da muhimmanci ƙwarai da gaske, domin kuwa za a fito da irin yadda mata ke taka muhimmiyar rawa a wajen gudanar da harkokin bukukuwansu da suka fi yi fice a garin Tsafe. Haka kuma, wannan bincike zai yi ƙoƙarin fito da wasu al’adu na waɗannan bukukuwa waɗanda ba a samun irin su a wasu garuruwan Hausawa. Wasu al’adun ma sukan ba mai karatu mamaki, kamar yadda wasu ƙauyukan garin Tsafe ke gudanar da nasu bukukuwan na maulidi har ma sukan kira bukin da suna Bukin Sallar Mata. Saboda irin yadda mata ke yi wa maza hidima a yayin gudanar da wannan bukin.
Wani muhimmin abu kuma shi ne, za a duba yadda zamani ya yi tasiri ga al’adun bukukuwan Hausawa, musamman waɗanda za a tattauna a kansu. Haka kuma ga masu sha’awar sanin tarihin garin Tsafe, duk za a same shi a ciki.
1.4     Muhallin Bincike
 Wannan bincike an gudanar da shi a cikin farfajiyar al’adun Hausawa ne, kuma ƙarƙashin bukukuwansu. Sannan ko a bukukuwan ma, ya tsaya kan rawar da mata ke takawa a bukukuwan garin Tsafe, wani yanki na ƙasar Zamfara. Kamar dai yadda aka sani, bukukuwa suna suka tara a rayuwar ɗan Adam. Bukukuwan Hausawa akwai bukukuwa daban- daban da ake gudanarwa bisa ga al’adu, kamar irin su: Bukinshan kabewa da bukin buɗar daji da sauransu. Don haka, wannanaiki zai tsaya ne kawai a wasu bukukuwan da suka fi fice a garin Tsafe. Misali: Bukin Aure da bukin maulidi da Bukin Salla da Bukin Haihuwa da kuma Bukin Walimar Sauka.
1.5     Hanyoyin  Gudanar  da Bincike
 Za a bi hanyoyi da dama domin a samo ingantattun bayanai akan yadda mata ke taka rawarsu a waɗannan bukukuwa a garin Tsafe, wato bukin aure da bukin haihuwa da bukin salla da bukin maulidi da bukin walimar sauka. Daga cikin hanyoyin da za a bi akwai: ziyarar ɗakunan karatu na wasu manyan makarantun, domin yin nazarin bugaggaun litattafai da kundayen bincike da ƙasidu da sauransu,domin samun haske a kan hanyar da za a bi wajen gudanar da wannan aiki.
Wata hanya kuma da za a bi ita ce, ziyartar inda ake waɗannan bukukuwa, domin Hausawa na cewa ‘gani ya kori ji’, wato wuraren da ake gudanar bukukuwan domin a ga yadda ake tafiyar da su. Yin hakan, zai sa a samu cikakken bayani. Za a kuma a tattauna da wasu mutane masu ruwa da tsaki a kan waɗannan al’adu. 
1.6     Tambayoyin  Bincike
Tambayoyin binciken za su kasance kamar haka:
·         Me ke sa mata halartar waɗannan bukukuwa?
         Me ke zaburar da mata wajen halartar buki?
         Wane irin matsayi buki yake da  shi a wajen mata?
         Wane alfanu mata ke samu a wajen buki?
         Wace dangantaka ke sa mata halartar buki?
         Me ke sa mata ƙure adaka a yayin zuwa gidajen bukukuwa?
Amsoshin waɗannan tambayoyi su za su kai mu ga samun nasara wajen gudanar da wannan aiki.
1.7     Bitar  Ayyukan  Da  Suka  Gabata
Idan aka yi la’akari da irin ayyukan da suka gabata za ga cewa  masana da wasu ɗalibai su  gudanar da bincike mai yawa a kan al’adun malam Bahaushe musamman abin da ya shafi bukukuwan Hausawa da zamantakewarsu ta hanyoyi daban-daban. Wasu sun yi bayaninsu a bugaggun litattafai wasu kuma a kundayen bincike na matakan digiri daban-daban wasu kuma  muƙalu ne aka gabatar a wajen taron ƙara wa juna sani daban-daban.Kaɗan daga cikin ayyukan da suka gabata da aka samu nasarar kai wa gare su sun  haɗa da:
1.7.1   Bugaggun  Litattafai
Habibu Alhassan da wasu (1982) mai suna Zaman Hausawa, A cikin littafin, sun yi magana a kan aure da haihuwa a al’adance. Don haka wannan littafi ya ƙara haske wajen gudanar da wannan aiki domin ya danganci wani ɓangare na wannan aiki musamman ta inda ya yi bayani a kan aure da haihuwa. Haka kuma aikin nasu ya bambanta da wannan ta inda su sun gina littafin ne a kan zaman Hausawa, wannan kuwa ya ƙunshi bayani ne a kan rawar mata a bukukuwa  a garin Tsafe.
Yahaya da wasu(1992), a littafinsu mai suna Darussan Hausa Don Makarantun Sakandare,sun yi bayani kan ma’anar aure. Don haka wannan aiki yana da alaƙa da nasu ta yadda dukansu sun ƙunshi bayani a kan aure da kuma yadda ake yin sa.
Sadi (1998), ya rubuta littafi mai suna,Tsafe Garin Yandoto, wannan littafi yana ɗauke da tarihin garin Tsafe kaf. Wannan littafi ya taimaki wannan aiki, musamman wajen fito da tarihin garin Tsafe wanda shi ne farfajiyar gudanar da wannan aiki. Bambancin ayyukan kuwa su ne, nasa ya tsaya ne a kan tarihin garin Tsafe, shi kuwa wannan aiki zai kalli irin rawar da mata ke takawa a bukukuwan garin Tsafen.
Falama (2010) ya rubuta wani littafi mai suna Shawarwari 55 Ga Marubuci.Wannan littafi ya taimaka wajen gudanar da wannan bincike. Alaƙarsu kuwa itace ya taimaka ta fuskar gudanar da wannan aiki da shawarwarin da ya kawo a cikin littafin. Bambancinsu kuwa shi ne, wannan aiki zai kawo bayani ne a kan rawar mata a bukukuwan Hausawa a garin Tsafe.
Gusau(2012), ya rubuta littafinsa mai suna:Bukukuwan Hausawa. Wannan aiki nasa yana da alaƙa da wannan, ta yadda duk suna magana ne a kan bukukuwan Hausawa da suka haɗa da bukin aure da bukin haihuwa da bukin salla da bukin maulidi da bukin walimar sauka da sauransu. Bambancin ayyukan kuwa shi ne, nasa littafin ya tsaya ne a kan bukukuwa, wannan kuwa za a kalli rawar da mata ke takawa a cikin bukuwan.
1.7.2   Kundayen  Bincike
Buhari(1983) a kundin digirinsa na biyu mai taken:“Illolin Auren Ƙananan Mata a Gundumar Kebbi”, wanda aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, ya kawo illolin yin auren wuri ga ’ya’ya mata, da kuma shawarwari da za a bi don gyara wannan al’amari. Alaƙar aikinsa da wannan ita ce a nan ma za a kalli al’adar aure a garin Tsafe. Saidai sun bambanta ta yadda a nan za a kalli rawar da mata suke takawa a bukukuwa ba aure kawai ba a garin Tsafe.
Zariya(2000),  yayi kundin digirinsa na farko mai taken:“Ado da Kwalliyar Hausawa”, wanda ya gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello  Zariya. Ya kawo bayanin yadda matan Hausawa suke yin adonsu a wurare daban-daban. Don haka, wannan aiki zai ba da wani haske ga nawa aikin. Sai dai kuma, wannan aikin bai tsaya a kan ado kawai ba ya zarce zuwa ga bayanin fitattun bukukuwan da ake yi a garin Tsafe.
Sulaiman (2002), a kundin digirinsa na farko da ya gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya mai taken:“Tasirin Zamananci a Kan Al’adun Hausawa”,ya kawo irin yadda zamananci ya yi tasiri a kan wasu al’adun Hausawa, wanda hakan, ya alaƙanta aikin nasa da nawa domin a nan ma za a kalli yadda zamani ya yi tasiri a bukukuwan garin Tsafe.
Maryam da wasu (2003), sun gabatar da kundin bincikensu mai taken:“Al’adun Gargajiya A Kan Auren Hausawa” da suka gabatar a Kwalejin Ilimi ta Shehu  Shagari Sakkwato. Wannan aiki nasu ya yi bayanai da dama a kan gyare-gyaren da ake samu a al’adar aure kamar na-gani-ina-so da kayan sa rana da sauransu. Don haka wannan aiki yana da alaƙa da wancan aiki nasu. Sai dai sun yi hannun-riga ta yadda a nan ba a tsaya ga aure kawai ba.
Ɗan'azumi(2004), ya rubuta kundin digirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya mai taken:"Auren Gargajiya  A Ƙasar Kwatarkwashi". Wannan aiki nasaya yi kama da wannan ta yadda a nan ma za a yi nazairin aure amma a garin Tsafe a cikin babi na uku. Alaƙar wannan aikin ya danganci yadda suka yi bayani a kan bukin aure. Sai dai a nasa ya danganci bukin aure ne kawai nan kuwa za a kalli wasu bukukuwa bayan na auren.
Rambo(2007), a kundin digirinsa na biyu mai taken: “Nazari a Kan Wasu Keɓabbun Al’adun Hausawa Da Dakarkari” da aka yi a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, ya yi nazari a kan hikimomin kaka da kakanni wajen aiwatar da wasu al’adu. Sannan kuma ya ɗora bayanai a kan yadda Hausawa ke gudanar da al’adar aurensu da kuma yadda Dakarkari ke gudanar da tasu al’adar ta auratayya.Aikinsa da wannan sun yi tarayya a kan buki, sai dai nasa ya taƙaita a kan bukin aure inda wannan ya tattaro wasu bukukuwan da bana aure kawai ba.
Jahun (2007), ya rubuta kundin dogirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zariyamai taken:"Tasirin Baƙin Al'adu a Auren Hausawa", wannan aiki yana da alaƙa da nawa saboda wannan bincike zai dubi rawar mata a cikin bukukuwan garin Tsafe, tare da nuna tasirin zamananci a cikin bukukuwan. Sai dai a nan ba a bukin aure kawai za a tsaya ba.
Bala (2010), a kundin digirinsa na farko a Jami'ar Usmanu  Ɗanfodiyo Sakkwato mai taken:" Bincike a Kan Baƙin Al'adun Aure a Garin Sakkwato", ya ba ni hasken gudanar da wannan, aiki domin kuwa aikin nasa ya yi kama da wannan ta fuskar wasu al'adu da ake aiwatarwa a loacin bukukuwa kamar cin abincin rana (lunching) da ƙwallon amarya da ango, da anko, da sauransu. Saboda haka, za a ga cewa suna da alaƙa ta fuskar nazari a kan bukukuwa, amma a nan za a kalli yadda mata ke taka rawa wajen bukukuwa a garin Tsafi.
Kanoma (2011), a kundin digirinsa na farko a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato mai taken: "Al'adun Aure da Haihuwa a Garin Kanoma",za a ga yana da makusanciyar alaƙa da wannan bincike ta yadda ya taɓo muhimman al'adu na aure da haihuwa. Saidai a nan an faɗaɗa zuwa wasu bukukuwa kamar su bukin salla da bukin maulidi da bukin sauka.
Ruƙayya (2011), ta rubuta kundin digirinta na farko mai taken: "Kwalliyar Sifa da Nau'o'inta".A cikin aikin ta yi bayanin yadda ake yin kwalliyar sifa (hydrogen) ta hannu da ta ƙafa da ta wuya, ta kuma yi bayanin adon mata kamar su kitso da ƙunshi da sauransu. Don haka, an samu dangantaka tsakanin aikin nata da wannan ta yadda a babi na huɗu na wannan aikin za a kawo bayani a kan irin kwalliyar mata a gidajen bukukuwa har ma da gasar kwalliyar da suke yi a yayin buki.
Saudat (2012), ta rubuta kundin digirinta na farko a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato mai taken "Kayan Adon Hausawa na Zamani" , Wannan aiki yana da matuƙar muhimmanci ga wannan bincike domin ya taɓo wani ɓangare na wannan binciken, don kuwa a babi na uku na wannan aiki, za a yi magana a kan tasirin zamananci a kan bukukuwa.
Asma'u (2012), a kundinta na digiri na farko mai taken "Nazari a Kan Kwalliya a Harshen Hausa" da ta gabatar a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, kundin nata ya yi bayani ne a kan ma'anar kwalliya, da asalin kwalliya, da muhimmancinta da sauran dangin abubuwan da suka shafi kwalliya. Wannan aiki ya taimaka ta wajen samun bayanai musamman a babin da za a yi bayani a kan gasar kwalliya.
1.7.3   Maƙalu  DaMujallu
Umar  (1980),  ya gabatar da wata muƙala mai taken "Al'adar Aure da Nau'o'inta a Ƙasar Hausa" a taron ƙarawa juna sani da aka gabatar a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya inda ya zurfafa bayani a kan yadda al'ummar Hausawa suke gudanar da aurensu ta hanyoyi da dama. Ya kuma fayyace nau'o'in Hausawa, Wannan ya sanya aikin nasa ya taimaka ma wannan bincike ta yadda aka samu wasu bayanai dangane da aure wanda yana daga cikin ɓangaren da za a gudanar da bincike a kansa. To sai dai a  nan za a kalli wasu bukukuwan na daban bayan aure.
Ibrahim (2013)  ya gabatar da wata takarda mai taken "Kwatancin Al'adun Auren Hausawa da na Ɓachama" domin neman amincewa da batun gudanar da bincike a matakin digiri na uku (PhD) a Sashen Harsuna da Al'adun Afrika Tsangayar Fasaha Jami'ar Ahmadu Bello Zariya. A cikin wannan takarda ya yi bayanai da dama a kan al'adun auren Hausawa kamar irin su neman aure jiya da yau da bukin aure da zaman aure jiya da yau da mutuwar aure da sauran abubuwan da suka danganci auren. Don haka wannan takarda ta taimaka wajen tattara bayanai na wannan kundi.
1.8     Hujjar Ci Gaba Da Bincike
Duk da yake cewa waɗannan ayyukan da aka nazarta kaɗan ne daga cikin ayyukan da aka yi kan al'adu waɗanda suka danganci bukukuwa, daga kwalliya da yanayin bukin, amma ba a samu wani bincike ba wanda ya yi daidai da wannan ba sai dai masu kama da shi. Wasu kuma sun yi kama da wani ɓangare na wannan bincike ne. Saboda haka, wannan ya nuna cewa akwai wani giɓi da ya kamata a cike musamman idan aka yi la'akari da cewa al'ada ita ce babban ginshiƙi ta gudanar da rayuwar al'umma, wadda bukukuwa na ciki.Wannan shi ne ya sanya aka ƙudiri niyyar aiwatar da wannan bincike mai taken “Biki Salatin Mata: Rawar Mata a Bukukuwan Garin Tsafe".
1.9     Naɗewa
Manufar dai wannan bincike ita ce gano rawar da mata su ke takawa a bukukuwan garin tsafe.  Sannan kuma an yi bayani akan dalilin bincike, da mahimmancin bincike, da muhallin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike, da tambayoyin bincike, da bitar ayyukan da suka gabata, da kuma hujjar ci gaba da bincike. 




BABI NA BIYU: TARIHIN GARIN TSAFE
2.0     Shimfiɗa
Wannan babin zai yi magana ne a kan taƙaitaccen tarihin garin Tsafe. Kamar dai yada aka sani shi dai tarihin gari abu ne mai matuƙar muhimmanci, musamman ga mai bincike a kan wasu al'adu da suka shafi wannan garin da zai yi bincike a cikinsa. Dalili kuwa shi ne, da dama daga al'adun gari suna da alaƙa da tarihin kafuwar wannan gari ko wasu sarakuna da suka  mulki wannan gari.Bisa ga haka ne ya sanya aka yi ƙoƙarin samo taƙaitaccen tarihin garin Tsafe inda nan ne farfajiyar gudanar da wannan bincike, daga asalin samuwar sunan garin da sarakunan da suka taɓa mulki a garin da kafuwarsa.
2.1  Asalin  Sunan  Garin  Tsafe
Sadi (1998) ya bayyana cewa, akwai mabambantan ra'ayoyi aƙalla guda uku dangane da asalin sunan Tsafe.
Ra'ayi na farko:
            Lokacin da maharba Katsinawa ko kuma zuriyar mayaƙin nan da ake kira "Gemen Dodo" suka zo kusa da dutsen Tsafe, sun iske wasu kayayyakin sihirce-sihirce a wurin, sai suka ce ashe ma wuirin na matsafa ne, tsahe-tsahe suke yi. Daga nan ne wai aka ba wurin suna Tsafe. Wato dai an danganta sunan Tsafe da Tsafi, sai dai wannan ra'ayi bai shahara ba.
Ra'ayi na biyu:
            An danganta wannan ra'ayi da wani maharbi dake zaune a gindin dutsen Tsafe daga Gabas daidai zuwa filin Idi na yanzu, wurin da ake kira da "Magurawa". To wasu sun ce sunan maharbin Tsafa, kuma daga sunansa  ne aka samu sunan Tsafe.
            Wasu kuma sun ce sunansa Idrisu kuma daga Magurawa yakan shigo garin Tsafe don farauta ko saƙi, kuma wurindaji nea wancan lokaci, saboda hatsabibancinsa, wasu kan ce ku dubi yadda ya je ya Tsahe shi kaɗai. Wato ya koma gefe shi kaɗai a nufinsu. Daga nan ne ake jin garin ya samu sunan Tsafe bayan da jama'a suka yi yawa a wurin.
Ra'ayi na uku:
            Ana danganta wannan ra'ayi da wani malami da ake kira da malam Muhammadu Aminu mutumin ƙasar Ɓurmi ta ƙasar Bakura.Shi wannan malami babban almajiri ne kuma mahaddacin Alƙur'ani mai tsarki. An ce yakan tafi neman ilimi a birnin Zariya. An ce daga Zariya yakan kama tIlawar karatu har sai ya isa Burmi. Sai dai yakan tsaya a wasu zanguna idan kuma ya kawo zango yakan dakatar da tilawar har sai ya tashi. To an ce garin Tsafe a yanzu yana daga cikin zangunansa a wancan lokaci, kuma duk lokacin da ya iso a  wannan wurare na tsafe yana daidai da lokacin da yake karatun suratul Ɗhaha. To da yake yana zango ne, kuma yana hulɗa da arnan wurin , sai suka karɓi sunan. Sai dai saboda rashin fahimtar Alƙur'ani da bambancin harshe, sai su gurɓata "Ɗhaha" ɗin ta koma "tsaha". Wai daga nan ne sunan Tsafe ya samu.
2.2     Kafuwar Garin Tsafe
            Sadi (1998), Mutanen Tsafe dai, babu wata tababa haɓen Katsina ne, bisa hujjar tarihi da yankin ƙasar da suke zaune da kuma al'adunsu. To na ba da labarin asalin Tsafe da kuma kafuwarta da wani mashahurin mayaƙin sarkin Katsina wanda ake kira mayaƙi "Gemen Dodo". Wasu sun ce ya yi zamani ne da Sarkin Katsina Gozo. Shi wannan mutum dai asalinsa ya so shiga duhun tarihi. Domin wasu suna cewa wai shi Bukutumɓe ne, wato ɗan zuriyar Bawo da suka mulki Kano, sai ya yo hijira zuwa Katsina.Wasu kuma na ganin cewa shi Bakatsinen Maraɗi ne cikin jahar Katsina, kuma yana cikin sarakunan yaƙi na kusa da sarki. An ce, wannan mutumen shahararren mayaƙi nekuma jarumin gaske. To akwai kuma wani shahararren mayaƙi ɗan samame mutumin Maraɗi wanda ya hana Katsina saƙat da hare-hare a wancan lokacin. Sunan wannan mayaƙin "Kufaya".An cewannan mayaƙi ya raunana katafaren cinikin nan na ƙetaren sahara zuwa ƙasashen Arewa na Larabawa. Kwatsam, rannan ana nan sai ga wani shahararren mayaƙi ya zo fadar sarki yana ce wa fadawa "Da sarki zai ba ni rabin gari ko da sarki zai ba ni doki da takobi, da na kashe masa Kufaya". Sai wani bafade ya zagaya ya faɗa wasarki, sai sarki ya ce a kira masa wannan mutum. Ana kiransa, sai sarki ya tambaye shi, "shin wannan maganar da bafade ya faɗa gaskiya ce?". Sai ya ce "e".
            Sai Sarki ya ce ya je ya zaɓi doki, duk da dai ya san kashe Kufaya ba ƙaramin aiki ba ne. Wannan mayaƙi ya shiga bargar dawakai ya zaɓi doki ya darje ya zaɓi jarumin doki. Ana cikin haka, aka ji ƙugin Kufaya ya shigo gari, sai sarki ya ce wa mayaƙin ga Kufaya can ka je ka tarbe shi. A cewar wasu masana suna tsakanin farfajiyar Mada da Wonaka da Kwatarkwashi ne mayaƙin ya haɗu da Kufaya, sai mayaƙin ya jefa masa baƙar magana, a nan ne fa sukayi ta fafatawa har wannan mayaƙi ya kashe wa Kufaya dakaru bakwai.
            Ko da ganin haka, sai fa yaƙi ya ɓarke tsakanin Kufaya da mayaƙi, daga ƙarshe dai Kufaya ya tunkuyi burji, mayaƙi ya saro kansa ya saka a burgaminsa ya kawo wa sarkin Katsina yana busa yana kirari ya ce, " Ranka ya daɗe, ga kan Kufaya", Sai sarki da mutane suka kama mamaki irin yadda mayaƙin shi kaɗai ya samu wannan nasara. To daga nan ne, sarki ya ba shi sarautar Kwatarkwashi. Kuma ya auri ɗiyar sarkin Kwatarkwashi, wasu kuma suka ce a'a matar tsohon sarkin ce ya aura bayan ya mutu. Wannan mata ita ta haifa masa "ya"ya biyu, wato Umaru da Habu.  Kuma an ce waɗannan ‘ya’ya duk sun sarauci kwatarkwashi. Umaru ya fara, to an ce ba ya jituwa da arnan garin, sai ya kwashe kayansa ya koma Katsina. Wasu kuma sun ce arnan ne suka yi masa bore. Da Umaru ya bar gado sai ƙaninsa Habu ya gaji sarautar Kwatarkwashi.
            Shi kuma Umarun, bayan ya koma Katsina, sai ya yi ta biyayya ga sarki, wadda wannan biyayya tasa, ta samo masa tukuici da sarautar ‘Yandoto wadda a ƙarƙashin mulkin Katsina take.To ko bayan mutuwarsa, ‘ya’yansa ne suka ci gaba da mulki a ’Yandoto. Masu bayar da tarihin duk a wannan lokaci ba a kafa garin Tsafe sai bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, lokacin da ɗansa Muhammadu Bello ya ci garin ’Yandoto a shekara ta 1221H (1806AD). A cewar Malam Isiya Tsafe, wai ’Yandoto Bawa (1801-1818) ya kafa garin Tsafe bayan Banaga Ɗanbature ya zo ya ci ’Yandoto da yaƙi a 1816.
            Wani ƙaulin kuma, ana nuna kai tsaye aka naɗo Umaru sarkin Tsafe daga Katsina, a matsayin tukuicin da sarki ya yi masa na hidimar da ya yi. Kuma wannan ra'ayi ya fi shahara, kuma an ce lokacin da ya zo Tsafe, an ce da shi da zuriyarsa sun sauke zango ne a gindin dutsen Tsafe kafin su  dawo ainihin inda Tsafe take a yanzu. Don haka ake cewa sarautun Tsafe da Kwatarkwashi 'wa" da "ƙani" ne.

2.3  Farfajiyar Tsafe Da Yanayinta
            Yankin Tsafe gunduma ne kuma tana cikin Afirika ta yamma ne a ƙasar Zamfara. Sadi (1998), ya ceTsafe tana da iyakokin ƙasa kamar yadda Turawa suka ƙiyasta a 1911. Cibiyar mulki ta Tsafe tana daga Gabas kilomita 48 daga garin Gusau a kan hanyar zuwa Zariya daga Gusau. A 1911 mataimakin (D.O) wani Bature cikin Turawan mulkin mallaka wai shi kaftin Black ya Zagaya yawo don tantance yankin gundumar Tsafe ya kuma ayyana cewa tana da iyakoki samammu da yanayi fitacce.
            Bisa ƙiyasin Turawa, ƙasar Tsafe tana kan faɗin ƙasa 110inch 57 arewa da tsawan ƙasa 60'55 gabas. Wato ta yi iyaka da Gulbin Gagare dagas gabas(in ban da wajensu hayin alhaji da ‘yar talata da unguwar sarki da sauransu waɗanda ke gabas da shi kaɗan).Watodaga wannan yanki ta yi iyaka da ƙoramar Jauri. Daga yamma kuwa ta yi iyaka da gulbin Sakkwato da ƙoramar Marra, wato mil 3 arewa da Raƙyaba ko mil ɗaya da garin ’Yandoto. Bisa ga waɗannan iyakoki Eric Saɗon ya ce garin Tsafe yana da murabbi'in faɗin ƙasa na mil 400.
            Amma a ra'ayi wasu sun nuna cewa ƙasar Tsafe ta fi wannan faɗin da aka nuna.
             Dangane da nau'in ƙasar Tsafe kuwa, kamar na mafi yawan dogon faƙon arewa (high plains of Hausa land), ƙasar Tsafe ma jigawa ce shimfiɗaɗɗiya mai "yan tuddai jefi-jefi (mai hawa da sauka mita 500-1000 daurin teku). Ƙasar Tsafe ƙasace da ke da manyan duwarwatsu (Precambrian basement) masu ƙwari da gurunguntsi kuma sandararru.A ƙalla bisa ga ƙiyasi shekarun waɗannan duwatsu ya kai miliyan 150.Kusan duk nisan kilomita goma akwai dutse a faɗin ƙasar Tsafe, musamman daga gabas. Tsiron nasu kuma ya fi bayyana a Tsafe da Kurku.
2.4  Tsarin Mulki A Ƙasar Tsafe
            Sadi (1998), Tsarin mulki a ƙasar Tsafe kamar dai yadda tarihin garin Tsafe ya shiga duhu haka shi ma ya shiga, sai dai da yake ita sarauta tana ginuwa ne a bisa tsarin rayuwa ta al'umma da kuma irin cigabanta, to ba wuya za a iya gano abubuwa da yawa ta fuskar nazarin fannonin rayuwar wannan al'umma waɗanda suka bayyana. Misali, an san ba a samun sarkin yanka ko uban ƙasa a ƙauye, sai dai mai unguwa.Don haka, da an san sana'o'i da al'adu da nau'in rayuwar al'umma, to ba wuya za a iya hasashen irin tsarin sarautarsu.
            To idan gari da mai gari suka bunƙasa sai hakan ya sa garin ya zama birni. Birni shi ne babban gari mai ganuwa kewaye da wasu gonaki da kasuwa da masallatai da fada, sannan kuma ya zama cibiyar kasuwanci da mulkin wannan yanki da yake. To a birni ne ake da sarki, wato uban ƙasa, wanda ake kira da Sarkin yanka. Saboda yana da ikon sawa a kashe ko kada a kashe. Wannan shi ne tsari na farko a tsarin sarautar Tsafe.(Uban Ƙasa).
            Tsari na biyu kuma shi ne ake kira da yan majalisar sarki, su ne masu  taimaka wa sarki wajen sha'anin mulki da inganta harkar tafiyar da hidimomin mulki na wannan al'umma. Daga cikinsu akwai:
Galadima
Magajin Gari
Waziri
Madawaki
Ma'aji ko Ajiya
Turaki ko Sarkin yaƙi
Sarkin Dogarai da Dagattai
Hakimai, masu kula da ƙauyukan gari, da dai sauransu.
2.5     Mulkin ’Yandotawa A Tsafe
            Sadi (1998), Kamar dai yadda bayani ya gabata, dutsen Kurku wanda yake gabas da garin Tsafe, shi ne mazaunin mutanen Tsafe na farko. Iyali da jama'a daban-daban sun zo suka zazzauna wurare da yawa a kewayen dutsin Kurkun da kwarin Dagazau. To sai dai kuma yawan mazaunan da keɓantuwarsu daga juna ya nuna asalinsu da kuma nau’ikan sana'arsu ya bambanta. Haka kuma, yanayin zuwansu da zama wurin ya bambanta dangane da lokaci,wasunsu sun haɗa da Tsanga da ’Yanza da Sakiya da Asaula da sauransu, za a fahimci cewa kowa a cikinsu gashin kansa yake ci wajen gudanar da mulki. To bisa haka, za a fahimci cewa, waɗannan mutanen, sun gudanar da mulkin su ne a matsayin masu unguwanni a wancan lokaci, shi ya sa ake wa mulkinsu take da cewa "Mulkin mai unguwa a kurkui."
            Kamar yadda bayani ya gabata a tarihin kafuwar Tsafe, an nuna  cewa duk yadda aka yi mayaƙi ko zuriyarsa sun iske wasu mutane(Arna) a dutsin kurku ko kuma a Tsafen. Don haka, bayyanar mayaƙin a Tsafe kamar ƙaurar Ummaru da jikokinsa kamar Anne da Bawa da Ɗangarba da kuma Gangi da Kadaura wata gaɓa ce mai muhimmanci a tarihin Tsafe musamman ta fuskar mulki.
            Kasancewa Mayaƙi da ɗansa Ummaru da jikokinsa suna da alaƙa da Katsina da Kwatarkwashi, wannan ya sanya suka zo da wata gogewa da wayewa a kan sha'anin mulki ta haɗa jama'a wuri guda. To a nan ra'ayin da ya shahara shi ne daga Katsina aka naɗo Ummaru sarautar ’Yandoton Tsafe, amma wasu na ganin jarumtaka da hikima ta haɗa kan mutane sun sanya Ummaru ya samu nasarar mulkin ’Yandoton Tsafe. Wai saboda Katsina ba ta da hannu wajen naɗin sarauta a yankin, sai dai idan mutane sun zaɓa sarkin Katsina ya tabbatar.
            Haka kuma, an nuna cewa Kuku ne asalin sarautar ’Yandoto domin a can dutsen Doto yake, kuma can mutanen Tsafe suka fara zama kafin su dawo gindin dutsen Tsafe. Shi kuma ’Yandoton yana zaune ne a ’yan sarki gindin dutsen Kurkun. Idan aka zaɓi sarki a wancan lokacin akan zo a yi buki a kan wannan dutsen na "Doto" shi wannan dutsin an yi imani yana da kwarjini da wani asiri. Shi ya sa ake yi wa sarki ko sarautar nasaba da wannan dutse (’Yandoto). Kuma sarki ba ya tabbatuwa sai an yi wannan buki a kan wannan dutse na "Doto". Kuma akan ɗauki tsawon lokaci ana wannan buki in aka zaɓi sarki.
2.6  Zaɓe Da Naɗin Sarautar ’Yandoto
Sadi (1998), Kamar yadda yake a tarihi, jarumta da siddabaru da hikima da ƙarfin tsafi sukan sa mutun ya cancantar da zama sarki. Kuma dattijan gari da masu unguwanni suke zaɓen wanda za a naɗa sarki. Kuma duk sarkin da aka zaɓa dole ya kai caffa (gaisuwar ban girma) zuwa Katsina bayan an gama bukin naɗin nasa da ake yi a kan dutsen "Doton". Gaisuwar da sabon sarkin zai kai ta ƙunshi kayan alatu haɗe da doki da bayi da kuɗi waɗanda zai kai Katsina. Sai sarkin ya tambayi jakadun ko jama'a na zaune lafiya?  Ko ana kawo hari, kuma jama'arsu na iya kare harin/? Daga nan zai gane cancantar sabon ‘Yandoton. To sai sarki ya karɓi kyautar da aka kawo masa, shi kuma ai ya ba ‘Yandoton kyautar wanduna da kyankyandi da dawakai da sauran ƙasaitattun kyauta na mulki. Idan kuwa bai karɓa ba, to ba zai karɓi kyautar ba ko ya ƙi yi masa kyauta ko ma ya hana ai masa iso.
To da lokacin da tafiya ta fara nisa, musamman da garin Tsafe ta dawo inda take yanzu, sai ya zama daga ’yan sarki sai ‘yan majalisar sarki kawai ke shiga sha'anin zaɓen sabon ‘Yandoto. Misali, wani ƙasaitaccen ɗan sarki Ɗangaladima, Ɗanmagajiya (babban ɗan ‘Yandoto Usman) shi yai tsaye aka naɗa ‘Yandoto Muhammadu. Sauran yan majalisar sarki masu naɗi kuwa, sun haɗa da Galadima da Madawaki da Magayaƙin Tsafe da Wambai da Zarummai da Majikira da Shantali da manyan masu unguwanni; kuma har a wannan lokaci idan an naɗa sabon ‘Yandoto sai ya kai gaisuwa ga sarkin Katsina.
To daga lokacin da mulki ya koma Sakkwato, bayan jahadi, daga naɗin ‘Yandoto Labaran sai hanyar zaɓen ta canja. A wannan lokacin akan kira ‘yan sarkin su duka su je Sakkwato, ko da kuwa mutum bai so. Amma kafin lokacin da za a kira su, ‘yan majalisar sarkin sun riga sun yanke shawarar wanda ya kamata a bai wa sarautar. To da an je, sai majalisar sarkin Musulmai ta yi nata nazarin, tana iya tabbatar da zaɓen ko ta canja. Daga nan sai a tara "yan sarkin a yi masu jawabi, a kuma bayyana wanda ya yi nasara. Sannan a neme su da su yi masa mubayi'a tare da yi masa naɗi su rako shi zuwa gida.
2.7 Sunayen Sarakunan Tsafe Tun Farkon Kafa Garin  HarZuwa Yau:
’Yandoto Ummaru (1771-1791)
’Yandoto  Ɗanfatu (1844-1867)
’Yandoto  Usman (1873-1897)
’Yandoto  Muhammadu (1897-1924)
’Yandoto  Abdullahi Mazawaje (1928-1948)
’Yandoto  Aliyu Ɗanladi  (1960-1991)
’Yandoto  Habibu  (1991-2017)
’Yandoto  Mamman  (2017-?)

2.8     Naɗewa
         Tirƙashi! lallai garin Tsafe gari ne da ya tara tarihi mai ɗimbin yawa, domin kuwa, wannan babi ya feɗe muna biri har wutsiya dangane da tarihin garin Tsafe. A cikin wannan babi, an yi bayanai dangane da garin Tsafe. Waɗanda suka shafi asalin sunan garin Tsafe, da Kafuwar Garin Tsafe, da Farfajiyar Tsafe, da Tsarin Mulki a ƙasar Tsafe, da Mulkin ‘Yandotawa a Tsafe, da Zaɓe da naɗin sarautar ’Yandoto da kuma sunayen Sarakuna Tsafe tun farkon kafa garin har zuwa yau.    



BABI NA UKU: BUKUKUWA A GARIN TSAFE 
3.0     Shimfiɗa
    A babi da ya gabataan yi bayanin taƙaitaccen tarihin garin Tsafe kamar asalin sunan garin da kafuwarsa da sarakunansa tun farko zuwa yau. A wannan babi kuwa za akawo bayanin wasu fitattun bukukuwa a garin Tsafe ne da kuma yadda ake yin su, kamar irin su bukin aure da bukin haihuwa da bukin salla da bukin maulidi da bukin saukar karatun Alƙur'ani. Haka kuma za a kawo yadda zamananci ya yi tasiri a cikinsu.
3.1     Ma’anar Buki
Buki dai wani taro ne da mutane kan shirya kuma su gabatar domin su nuna farin cikinsu ga faruwar wani abu na jin daɗi kamar Aure ko Haihuwa ko Salla da sauransu daga wani lokaci zuwa wani.
3.1.1   Salatin  Mata
Salati wata hanyace da Musulmi suke ambaton wasu keɓaɓɓun kalmomin domin yabon Annabi Muhammad (S.A.W) Kuma umurni ne daga Allah (S.W.A). Duk Musulmin da ya yi wa Annabi Salati, yana da lada ta musamman. Domin muhimmacin Salati ga Musulmi da yadda mata suka ba buki muhimmaci, sai Hausawa suka danganta buki da salati ga mata, tamkar mata basu da abun girmamawa sai yin buki. Wannan shi ne dalilin da yasa wasu Hausawa suke yiwa buki kirari da “Buki Salatin Mata”. 
3.1.2  Asalin  Buki
Gusau (2012), ya nuna cewa daga taron mutane ne waɗanda suke halartar wani wuri da aka samu wani abu mai faranta rai. Irin wannan taron ne na mutane ke sanya a gudanar da wani shagali na nuna farin ciki. Irin wannan shagali shi ke maimaita kansa a duk lokacin da ya sake zagayowa.
3.2 Bukin Aure Da Yadda Ake Yin Sa
Wannan ɓangaren zai ƙunshi abubuwa muhimmai kamar haka:
3.2.1   Ma’anar Aure
A taƙaice dai idan aka faɗi kalmar aure ta na nufin shigar da wani abu cikin wani domin samar da wata muhimmiyar fa’ida. Don haka za mu duba muga yadda wasu masana suka bada ra’ayoyinsu game da ma’anar aure.
Habib Alhassan ya bada ma’anar Aure da cewa:
Aure alaƙace ta halaccin zama tare tsakanin namiji da mace. Ana yin sa ne sabo da abin da aka haifa ya sami asali, da mutunci, da ɗaukaka, da kiwon iyaye kuma shi ne maganin zina da ’ya’ya marasa iyaye. (Alhassan da Wasu 1992).

Gusau da ‘Yar Aduwa (1992) sun ba da tasu ma’anar da cewa:
Aure wata hanya ce ta ƙulla zaman tare tsakanin Namiji da Macce ba tare da iyakancewa ba sai in mutuwa ta raba.
Kwantagora (2010) ya na cewa:
Aure hanya ce ta rayuwa mai ɗorewa tsakanin Namiji da Macce. Wadda aka gina ta hanyar shimfiɗaɗɗun ƙa’idoji.

Bashir Sa’id Gusau (2002) yana cewa:
Aure hanya ce da ke haifar da zama mai ɗorewa tsakanin Mace da Namiji bisa ga amincewar al’adar al’ummar da ma’aurata suka fito.

Ta la’akari da ra’ayoyin masana a kan ma’anar aure. Ni ina iya tofa albarkacin baki na da cewa: “Aure shi ne haɗuwar abubuwa masu rai mabanbanta jinsi, wato Mace da Namiji domin a samu ƙaruwar hauhuwa ko iyali.
3.1.2   Bukin Aure
               Wani taro ne da mutane kan gudanar domin taya murnar aure daga lokaci zuwa lokaci.A al'adar garin Tsafe, bukin aure ba ya tabbatuwa sai an gabatar da abubuwa kamar haka:
i.        Nema- Idan saurayi ya ga ‘yar budurwa yana son ta da aure, zai ɗan fara tsokanarta ne da wasa daga nan sai ‘yan kyaututtuka su biyo baya. Sannan daga baya ya bayyana mata manufarsa. Idan ta amince za ta tura shi gidansu domin ya nemi izinin fara ganawa da ita. Shi kuma sai ya tura magabatansa a tambayo masa izini.
ii.      Amincewa- Waliyyan yarinya za su binciki halayyar yaron dake neman ‘yarsu da kuma asalinsa. Idan sun gamsu da sakamakon binciken, sai su aika a shaida ma waliyyan yaron cewa sun ba shi dama.Su kuma waliyyan yaro za su sayi goro da minti da biskit a kai gidan su yarinyar domin a raba wa danginta a bai wa danginta don shaidawar ‘wane’(a ambata sunanasa) ke nemanta.
iii.    Kayan Na Gani Ina So/Shiga Gida/Gaida Iyaye- Bayan an bai wa yara damar ganawa da junansu, za su ci gaba da mu'amula ta saurayi da budurwa. Idan sun gama fahimtar junansu zuwa ɗan lokaci kuma sun aminta da junansu, sai yaro ya sayi dangin goro da alawa da sauran su a kai gidan su yarinya domin shaida masu cewa yaro na nem, an "yarsu kuma har ta aminta da auren sa.
iv.    Sa Rana- Bayan wata uku ko huɗu da kai kayan na gani ina so, sai waliyyan yaro su je ga waliyyan yarinya domin a sa masu ranar da za a ɗaura auren yaran. Daga nan sai waliyyan yarinya su nemi a ba su dama domin su yanke shawarar ranar da ta dace. Bayan haka sai su aika wa waliyyan yaro da crewa ga ranar da suka sanya.
v.      Kayan Sa Rana- Iyayen yaro za su sayi minti da goro da biskit da sauransu su kai gidansu yarinya domin a rarraba wa "yan uwa da abokan arziki a shaida masu an sa ranar Auren yaran.
vi.    Sadaki- Bayan duk an gabatar da waɗancan abubuwa da aka ambata a baya, sai waliyyan yaro su dawo domin a saka masu sadaki. Su kuma waliyyan yarinya sai su saka sadakin daga dubu talatin zuwa sama, amma yawanci ko an saka sadakin, iyayen yarinyar ba su cika karɓa ba sai ranar ɗaurin aure ko cikin makon bukin.
vii.    Kayan Lefe- Kayan lefe kuwa iyayen yaro mata ne kan kawo su yawanci ana sauran wata ɗaya ɗaurin aure ko kuma mako biyu koma ana sauran kwana uku ake kai su Kuma idan za a kawo lefe ana la'akari da gidan da yarinya ta fito ko kyawunta ko kuma iliminta da wayewarta. Su kuwa iyayen yarinyar sukan yi la'akari da ƙoƙarin da yaro ya yi ga kayan lefen, sannan zu zuba mata kayan ɗaki. Misali, za a yi wa mace saiti da kujeru da sauran kayan ɗaki daidai da kayan lefe. Wato dai kamar kumbo kamar kayanta.
3.1.3      Yadda Ake Bukin Aure A Garin Tsafe
               A al'adar bukin aure a Tsafe a wannan lokaci, haƙiƙa zamananci ya yi yawa a cikinta, saboda irin yadda Hausawa ke gudanar da wasu al'adu kai ka ce ba na Hausawa ba ne. Abin mamaki, za a ga hidimar bikin yarinya ‘yar Hausawa, amma da wuya ka ga an aikata wasu abubuwa muhimmai guda biyu na al'adar Hausawa.Sai dai a yi ta aro wasu al'adu kamar su Arabian Night,Yuroba Day, Fulani Day da Picnic da sauransu duk da yake ba kowa ne ke yi ba, amma wasu kan gudanar da su.
              Yawanci mata kan fara hidimomin bukin tun ana saura kwana huɗu kafin ranar ɗaurin aure. Domin sukan tsara abubuwa kamar haka:
a.       Zaman Lalle- Wannan rana ita ce wadda ake nuna wa mutane wance ta shiga lalle. Ma'ana bukinta ya zo daf, Amarya takan gayyato ƙawayenta don a zo a taru gidan wata uwar ɗakinta, a yi ta hirace-hirace da wasa da dariya. Daga nan sai wata abokiyar wasan amarya ta lallaɓo ta zo ta shafa wa amarya lalle ko turare, daga nan sai su ci gaba da tsara yadda suke tsammanin hidimar za ta, kasance, kamar dafa abincin ƙawaye da fati, da sauransu. Daga nan sai su gayyato abokan ango don karɓar wasu kuɗaɗe daga wurinsu na wasu hidimomi kamar kunshin Amarya da na ƙawayenta da abincin buki da sauran kayayyakin da zasu siya domin rabawa ƙawayensu.
b.      Zaman Cin Fara Ko Shan Rake Ko Shan Kankana Ko Cin Ɓula- Wannan wata al'ada ce dake faruwa kashegarin ranar sa lalle. Kuma wannan na daga cikin baƙin al'adu a cikin bukin aure. Yawanɓci amarya kan tara ƙawayenta don yin wannan ciye-ciye wanda yakan zama abin gori ma in ba ta yi hakan ba. Kuma akan ware gida guda ne don wannan ciye-ciye. Yawanci wanda aka yi zaman a gidansa shi ke ɗaukar nauyin duk abinda za’a ci a ranar. Don haka idan za a yi irin wannan zaman sai an sanar da mutun cewa za a yi zaman cin abu kaza a gidansa.
c.       Zaman Laushi Da Ƙunshi-A ranar ta uku kuwa, ana yi wa amarya ƙunshin zamani na hydrogen/Sifa. A nan ma amarya da ƙawayenta za su sam u wani gida sai su kira mai yin ƙunshi ta zana wa amarya da ƙawayen amarya, bayan ta gama sai a biya ta. Wadda akai wannan zama a gidanta ita ke haɗa wa amarya da ƙawayenta liyafa.
d.      Gyaran Kai Da Kamu.- Amarya kan je wajen gyaran kai na zamani (saloon) domin a gyara mata gashin kanta ta yadda zai yi kyau da sheƙi da haske. Bayan sun dawo sai a kira m,ai yin kwalliya don ta caɓa wa amarya ado saboda daga wannan rana za ta fara kwalliyar bukinta. Bayan an gama wannan , sai ta sanya kayan da iyayenta suka ɗinka mata, domin a wannan lokacin a Tsafe, amarya ba ta sanya kayan lefenta sai waɗanda iyayenta suka ɗinka mata don yin kwalliyar bukinta. Bayan amarya ta shirya, sai abokan ango su zo da motoci a ɗauki amarya da ƙawayenta a kai ta wurin kamu zuwa yamma. A wurin kamu, akan sanya kaset na waƙoƙi ko kuma a kira makaɗi na zamani ko na gargajiya domin a waƙe amarya da ango da ƙawayenta da iyayensu da sauran abokan arziki a yi rawa da liƙi da liyafar abin ci da abin sha har zuwa tsawon lokaci, kamar ƙarfe bakwai ko takwas na dare. 
e.       Walima- Wannan na faruwa ana gobe ɗaurin aure. A wannan rana amarya ko iyayenta kan gayyato malaman addini dominsu yi wa'azi tare da yiwa amarya nasiha da jan hankali da shawarwari dangane da zamantakewar aure. Yawanci an fi yin walimar aure ranar Juma'a a nan garin Tsafe, Amarya takan caɓa ado ta sa alkyabba ko kuma gyale mai ƙayatarwa. Su kuma ƙawayen amaryayawanci  sukan sanya jallabiya ne, wasu kuma sukan sa gyaluluwa ko hijabai a lokacin gudanar da walimar. Bayan an gama wa'azi, sai ƙawayen amarya su fito da abinci da abin sha a bai wa jama'a.
f.        Yinin Buki- Amarya da iyayenta da na ango da ango da sauran abokan arziki sukan gudanar da yinin bukinsu a ranar da aka ɗaura aure, kuma a gidan iyayen amarya ake yin sa. Bayan an ɗaura aure, za a ga mutane sun caɓa ado da kwalliya suna ta shigeda fice a gidan iyayen amarya da ango. A wannan ranar, amarya kan caɓa ado ta saka kaya na alfarma, har ya zuwa yamma inda za a kai ta gidan wanka.
g.      Wankan Amarya Da Kai Ta Gidan Ango-Yawanci wankan amarya an fi yinsa ne a gidan ƙanin uban amarya, ko wani babban abokin uban amarya. Tun kafin a kai amaryar, matan gidan wankan sun riga sun dafa ruwan lalle sai a ba amarya ta je ta yi wanka da su. Idan ta gama wankan, sai a fesa mata turare iri-iri, sannan ta canza kaya. Zuwa yamma, sai iyayen ango mata su zo biko a ba su amarya su wuce da ita gidan mijinta. Yawanci a ƙasa ake kai amarya gidan miji idan cikin gari ne ba’a mota ba.  Su kuma abokan ango su ɗauko ƙawayen amarya zuwa gidan amarya domin rakkiya.
h.      Sayen Baki- Bayan "yan biko sun kawo amarya ɗakinta , sai su yi mata nasihohi kafin su tafi su bar ta. Daga nan sai ƙawayen amarya da abokan ango su shigo domin a yi raha da annashuwa, ita kuwa amarya ta lulluɓe kanta da mayafi. Daga na sai babban abokin ango ya dakatar da surutun mutane, sai ya umurci mutane da gabatar da addu'o'in nema wa amarya da ango zaman lafiya. Sannan ƙawaye da abokan ango su ba su shawarwari nagari dangane da zaman aure. Sai abokan ango su ba ƙawayen amarya kuɗin sallama da biskit da minti da sauransu. Sai kowa ya kama hanyar gidansu. Amma a sauran garuruwan ƙasar Hausa, kamar irinsu Katsina da Zariya, ƙawayen amarya sukan kwana a gidan amarya ne, bayan an gama sayen baki.


3.2     Bukin Haihuwa Da Yadda Ake Yin Sa.
            Wannan ɓangare na bukin haihuwa da yadda ake yin sa ya ƙunshi abubuwa ne kamar haka: Ma’anar Haihuwa, da bukin Haihuwa, da yadda ake yin bukin haihuwa.
3.2.1      Ma'anar Haihuwa:
 Haihuwa na nufin samun ƙaruwa daga kowane irin jinsi na abu. To a taƙaice dai, haihuwa na nufin samun ‘ya’ya daga kowane ko kowace halitta mai rai , sannan kuma macen mutum ba ta haihuwa sai bayan ta samu ciki kuma ta rene shi tsawon wasu watanni daga shida zuwa tara ko fiye da haka.
3.2.2      Bukin Haihuwa:
Taro ne na cuncurundon mutane musamman mata da akan gudanar a duk lokacin da aka samu ƙaruwa, wato haihuwa a gidan wani mutum. Ana gudanar da bukin ne bayan kwana bakwai da samun ɗa ko ɗiya. Mutane kan halarci bukin daga ɓangaren mahaifiyar jariri ko jaririya da kuma ɓangaren mahaifinsa da sauran abokan arziki. Sukan zo domin taya iyayen yaro murna da samun ƙaruwa.
Kafin ranar bukin haihuwa, akwai wasu al'adu da akan gudanar tun daga ranar da aka haihu har ya zuwa ranar da da za a sanya suna. Waɗannan abubuwa sun haɗa da:
         Faɗin Haihuwa: Ana fara faɗin haihuwa ne daga lokacin da aka ce mace ta haihu lafiya, idan kuma ta sami matsalar haihuwar akan ɗan jira zuwa wani ɗan lokaci kana a fara sanar da mutane haihuwar. Wasu shaƙiƙan yaron kan fara sanar da mutane ta hanyoyi da dama, kama daga baki har ya zuwa ga wayoyi ga waɗanda suke nisa.Wani lokaci kuma akan tura yara domin sanarwar.
         Huɗuba    Ranar da aka haihu wani daga cikin "yan uwan uban yaron zai zo ya ɗauki jaririn ya yi masa kiran sallah a kunnensa na dama ya kuma tada iƙama ana hagu, sannan ya faɗi sunan da mahaifansa suka sanya masa a kunnensa.wannan Al’ada ce wadda aka koya daga Musulinci. 
         Wankan Jego:Hausawa na masa kirari da “wankan jego maganin sumɓuita, yarinya daure ki yi shi ki huta,. In kin kuskure shi sai buzunki.” To! Idan aka ce wanka ga mai haihuwa to ana nufin wankan jego, wanda akan yi wa mace bayan ta haihu, musamman a haihuwar farko. Kuma wakan kan cigaba har zuwa bayan suna ko ma tsawon kwana arba'in da haihuwa. Shi wannan wanka ana yin sa ne da tafasassun ruwan zafi bayan sun ɗan sha iska, sai a yi amfani da ganyen bedi(dalbejiya) ana sanya su cikin ruwa ana bugawa ga jiki. Ana yin wankan ne domin mai jego ta samu cikakkiyar lafiya da ƙarfin jiki, kuma wannan wanka ana yin sa ne a kowace haihuwa, sabuwa ko tsohuwa. Jariri kuwa, ana samun unguwarzoma ta rinƙa yi masa wankan har a fita bakwai, sai mahaifiyarsa ta cigaba da yi masa.
         Barka:Barka na nufin zuwan da mutane ke yi na yi wa mai jego murnar an sauka lafiya da fatan Allah ya raya. Barka na farawa daga ranar da aka ce mace ta haihu lafiya, za a ga mutane musamman mata na ta shige da fice a gidan mai jego. Wasu yan barkan kan ɗauki jaririn su yi masa addu'a wasu kuwa sai dai su ɗauka su gani su yaba da kyansa da sauransu.
         Kunu: A  al'adar garin Tsafe , idan mai jego ta haihu za a fara dama kunun gero ne da tsamiya domin mutanen dake zuwa barka su sha, sannan kuma ana zuba shi a kai wa mutanen da ake da alaƙa ta zumunci ko mutunci da su. Da kuma maƙwabta domin tofa albarkacin bakinsu; wato su ce Allah Ya raya  da abin da aka samu. Za a cigaba da dama kunun ana kai wa tun daga washegarin haihuwa har zuwa kwana huɗu da haihuwa.
          ShanƘauri:  Idan namiji a ka haifaana shan ƙauri bayan kwana uku da haihuwa, in kuwa mace ce sai bayan kwana huɗu. Mahaifin jariri zai sayo kan sa da ƙafafu ko kawunan raguna da ƙafafunsu wasu kuma akuya suke sayo wa adafe a raba wa mutanen arziki bayan an cire wa dangin mai jego da na uban jego nasu. Sai a cire wa mai jego nata. Kuma yawanci dangin miji ke dafawa.
         Kayan Barka- Kayan barka wasu turamen zannuwa ne da kayan jarirai da sauran kayayyakin kwalliya da na aiki da sauransu, waɗanda miji ke saye domin tarbon haihuwa. waɗanda mai jego da jariri za su sanya a lokacin suna.Waɗannan kaya daga gidan iyayen miji ake kawo su, kuma akan sanya ɗinkakku kamar kala biyar ko sama sai a sanya a akwati ɗaya ko sama da haka daidai da ƙarfin miji dai. Amma a wasu garuruwan Hausawa Miji kan saye Kayan Barka yakaiwa mai jego kai tsaye ba sai ya kai gidan iyayensa an kawo wa mai jego ba.   
         Aikin Gobe Suna (Ranar Barokaci)-- A wannan ranar ne ake wa mai jego kitso ta kuma yi ƙunshi, kuma a wanan ranar ne dangin mai jego da na miji za su zo domin yin shirye-shiryen abincin suna da na kayan liyafa. Kamar: Ɗaɗɗaura lemun leda ko soɓo ko kunun Aya da Tace ƙullun kunu / koko ‘yan zanen suna da kuma haɗa miyar tuwon ‘yan zanen suna. Kasancewar ƙarfe bakwai na safe ake zanen suna. 
         Zanen Suna- Yawanci akan zana suna ne a ƙofar gida ko a masallaci bayan mutane sun taru,sai a yi addu'o'i a raɗa wa yaro suna. Sai a raba wa yan zanen suna goro tare da yi wa yaro aski da cire hakin wuya. Sai a sallami mai aski da kuɗi da abinci sai a  maida jariri wajen uwarsa.  Yawanci kakanni ko iyaye maza ke zaɓen sunan da za a raɗa wa yaro. Kuma yawanci akan zaɓi sunayen iyaye ko kakanni ko sunayen Annabawa da Sahabbai domin Girmamawa. 
3.2.3  Yadda Ake Yin Bukin Haihuwa
A Tsafe ana fara bukin haihuwa bayan an zana sunan jariri. Kuma mata na fara halarta bukin ne tun ƙarfe sha biyu na rana har zuwa shida ko bakwai na yamma.Amma su tsofaffi suna tashi na su bukin ne bayan sun ci sun sha, sai su kai tasu gudummawar ga mai jego su kama hanyarsu sai kuma a bar matasan mata da sauran budurin buki.
Daga ƙarfe sha biyu ne mai jego za ta fara caɓa kwalliya da ado iri-iri , kuma yawanci za ta yi kwalliyar da za ta fita daban da sauran "yan bukin da suka zo taya ta murna. Kai wata ma sai ka ga kamar amarya, musamman ma idan haihuwar fari ce. Wasu ma kan yi shiga sama da ɗaya ko biyu. Kuma takan zagaya ko'ina cikin gidan saɓanin daga ɗaka sai ɗaka a wancen lokacin.
               Mai jego kan shirya wa ƙawayenta abinci na musamman kuma ba ta haɗa su da sauran yan bukin, sai dai ta keɓe su a wani wuri na daban. Kuma kafin halartar ƙawayen nata ,babbar ƙawarta kan fara zuwa don shirya masu komai. Sauran "yan buki ma da sun ci abinci sai su fara kai wa mai jego gudummawarsu suna kama gabansu. Su ma ƙawaye daga baya sai su fara bayar da tasu gudummawar suna tafiya. Akasari kayan da ake kawowa sun haɗa da , kayan jarirai da kuɗi da atamfofi da sauransu.
3.3 Bukin Salla  Da Yadda Ake Yin Sa
              A wannan ɓangare za a kalli salloli guda biyu da ake gudanarwa, wato babbar sallah da ƙaramar sallah.Wasu kuma sukan kira su da sallar layya da sallar azumi.Amma a nan Tsafe ana kiransu da ƙarama da babbar sallah. Ga bayanan yadda ake yin bukin kowace daga cikin sallolin:
3.3.1 Bukin Ƙaramar Sallah
            Wannan bukin ana gudanar da shi ne ranar ɗaya ga watan Shawwal na shekarar Musulunci. Mutane kan yi dafe-dafen abinci kala-kala musamman ma tuwan masara, da miyar Taushe, da saka sababbin kaya tare da isar da zumunci. Kuma akan kira ta da ƙaramar Salla ne domin mutane kan halarci masallacin Idi domin yin sallar nafila raka'a biyu kamar yadda addini ya wajabta. Kuma a wannan salla mutane ba su cika yanka raguna ba kamar ta babba sallah ba, sai dai mutane kan shiga rarrabar naman sa, wasu kuma sukan yanka dabbar da ta sawwaƙa  kuma yawanci ana soya nama ne ana gobe sallah.
   Mata sukan maida ranar salla tamkar wani babban bukina musamman.Kuma sukan yi ɗinkuna da ƙunshi da kitso domin caɓa kwalliya wanda  hakan kan canza sifar wasu. Don haka ma samari kan ce " kar ka zaɓi budurwa ranar salla kowace kucaka ta cake".
3.3.2 Yadda Ake Bukin Ƙaramar Salla
                Salla ƙarama salla ce da mutane ke fito-na fito wajen gasar sanya sutura da shirya liyafa a gidajensu.Sannan kuma wannan salla bata bar kowa ba wajen bukinta, tun daga maza har mata da manya da ƙanana har ma da Tsofaffi mata. Kowa zai caɓa ado ne ya wuce masallacin Idi.Sannan kuma yadda ake yin wannan buki ya sha bamban da sauran bukukuwa. Domin kuwa da an taso daga masallacin idi bukin sallar ya fara wucewa a wurin maza, don kuwa da ya dawo zai ci abinci daga nan zai kwanta daga nan sai ya wuce wajen abokai ai ta fira. Su kuwa mata bayan an taso kuma an yi hotuna da kamarori ko kuma wayoyi , sai a koma gida a sake caɓa kwalliya a runtuma gari domin yawon salla musamman ƙananan yara.
                Yawanci masu sarauta sukan yi amfani da motocin alfarma ko dawakai wajen zuwa filin salla. Matansu kuwa sukan sanya alkyabbu tare da masu rakiyarsu a nufin filin sallar, shi ma limami zai zo da tasa ƙungiyar. Yawanci ana yin sallar Idin ne da safe.Bayan an sallame yawanci akan tsaya sauraren huɗuba wasu kuwa ba su tsayawa.
             Abincin da ya fi shahara a wannan rana shi ne tuwon masara, ko na shinkafa ko shinkafa da miya ko sinasir ko masa da sauransu, kuma akan zuba wa yara su kai gidajen yan uwa da abokan arziki. Wasu kuwa sai kashe gari suke kai nasu abincin sallar.
Da yammacin wannan rana "yan mata za su caɓa kwalliya su shiga gari yawon salla, amma fa ba irin yawon yara ba shiga gidaje suna samun kuɗi ba. Su irin wannan yawon na "yan mata sukan ziyarci ƙawaye ne da dangin samarinsu da samarin da kuma abokan samarin. Kashe gari kuwa yawanci samarin ke ziyartar "yan matansu a gidajensu domin su bayar da barka da salla. Samarin kan bayar da kuɗi ko wasu abubuwa da suka zo wa da "yan matansu. Yawanci a wannan rana "yan mata kan caɓa kwalliyar haɗuwa da sahibansu.Su kuwa "yan matan kan shirya wa samarin liyafar girma.
Akwai waɗanda sukan keɓance wani wuri n musamman domin shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bukin nuna farin ciki da wannan rana.A wuri bukin ana sanya waƙoƙi domin taya annashuwa ga samari da ‘yan mata.
3.3.3  Bukin Babbar Salla
              Babbar Salla:Sallace da ake gudanarwa a ranar goma ga watan Zulhijja, wato watan ƙarshe na shekarar Musulunci.A garin Tsafe yawanci ana gudanar da wannan buki washegarin ranar Idi ko ma kwana biyu da yin Idin musamman "yan mata da matan aure. Wai sukan yi haka ne, saboda a ranar salla da kashegarin salla ana yin soye-soyen naman layya, don haka mata ba su yin wanka sosai ko kwalliya a waɗannan ranaku. Babbar salla sallace mata ke taka muhimmiyar rawarsu wajen gudanar da shagulgula daban-daban. Kamar su soye-soye da kwaliya da ziyarar gidajen ‘yan uwa da abokan arziki da sauransu.
       Bukin sallah babba, kamar yadda masana suka bayyana kamar su “Gusau 2012” yace, ana yin sa ne domin taya waɗanda suka je aikin Hajji murnar sun sauke farali lafiya.
3.3.4   Yadda Ake Yin Bukin  Babbar Salla
                   A ranar goma ga watan ƙarshe na shekarar Musulunci mutanen Tsafe za su yi wanka su halarci salla a wani katafaren fili dake wajen gari, bayan Sarki da liman sun sami isowa sai a gabatar da sallar idi raka'a biyu kamar yadda addini ya tanada.Sarakuna kan yi shiga ta alfarma da kuma sauran al';umma a wannan rana. A wannan rana sarakuna kan yanka raguna da hawa dawakai da yin wasu wasanni a wannan fili na idi da an gama yin salla.
                Da zarar an dawo, kuma an tabbata sarki da liman sun yanka ragunansu, sai magidanta su shiga yanka nasu ragunan layya. Mutane kan yanka ragunansu da kansu sannan akira rundawa su feɗe su kuma gyara.Daganan kuma sai mata su hau suya ka ji gaba ɗaya gari ya gauraye da ƙamshi. Idan kuma gari ya waye, to za a ga ana ta rarraba naman zuwa ga maƙwabta da "yan uwa da sauran aminai , ya Allah soyayye ko ɗanye.Saura kuma a ajiye domin amfanin gaba.
         Yawanci a wannan sallar, a garin Tsafe ba a cika dafa abincin rarraba wa ba kamar na ƙaramar salla ba. Sai dai a dafa wanda masu ziyara da mutanen gida za su ci.Kuma ba acika yin sababbin ɗinkuna ba ko wata shahararrar kwalliya, hasali ma, an fi amfani da kayan ƙaramar sallah a wannan sallah. Dalili kuwa shi ne, mutane sun fi maida hankali wurin sayen dabbobin layya, musamman magidanta da matan aure har ma da ‘yan mata.Yawancin wasu samarin su kan yi ƙoƙarin saya wa ‘yan matansu ragunan layyar ne koda kuwa su ba su yi ba. Babban buki dai a wannan sallah, layya ce. Wannan ala’ada, wata al’ada ce da a ke hasashen mazan tsafe sun ɗauko ta ne daga mazan sokoto. Sabo da yawan hurɗa tsakaninsu da mutanen sokoto.
        Idan aka kwana biyu da hawan Idi, matan aure kan shirya ziyara zuwa gidajen surukansu su da yaransu su yi masu yini, kashegari kuwa su nufi gidajen iyayensu domin wannan ziyara. Su kuwa ‘yan mata kan yi tasu kwalliyar a ranar da samarinsu za su kawo masu ziyara.
‘Yan asalin Tsafe kuwa waɗanda suke zaune a wasu garuruwa, kan kawo ziyara gidajensu ko na iyayensu su da iyalansu domin gudanar da shagulgulan salla a mahaifarsu. Da salla ta wuce sai su koma wuraren ayyukansu ko kasuwancinsu.
3.4  Bukin Maulidi Da Yadda Ake Yin Sa
           Bukin maulidi ya sha bamban dangane da masu gudanar da shi, duk kuwa da cewa masu yin sa sun keɓanci wasu aƙidu ne na addinin Musulunci. Kuma ba Hausawa kaɗai ba ne ke yin bukin maulidi, har da ma wasu ƙabilu, kamar Fulani da Yarbawa da Igbo da sauransu.Dukkan waɗanna ƙabilu sukan gudanar da bukin maulidi. Amma a wannan bincike za a duba yadda bukin na maulidi yake agarin Tsafe. Kuma za a fi maida hankali a kan rawar mata a  cikin wannan buki.
3.4.1  Maulidi
               Maulidi na nufin murnar zagayowar ranar haihuwar shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W). Ana yin maulidi ne a ranar 12 ga watan uku na shekarar Musulunci, wato Rabiyul Auwal. Domin a daidai wannan rana aka haifi Manzon Allah (S.A.W).
3.4.2 Bukin Maulidi
                 Bukin Maulidi buki ne da wasu daga cikin masu aƙidu na addini Musulunci ke gudanarwa. Kamar aƙidar shi'a da masu aƙidar ɗariƙu, wato tijjaniyako ƙadiriyya .A garin Tsafe, masu waɗannan aƙidu ke gudanar da bukin maulidi. Kuma suna fara gudanar da shi ne tun farkon watan uku zuwa watan huɗu na shekarar Musulunci.
3.4.3  Yadda Ake Yin Sa
            Ana fara gudanar da wannan buki ne a sha biyu ga watan uku na shekarar Musulunci musamman ga masu aƙidar Shi’a, kuma mata sukan taka muhimmiyar rawa wajen yin sa. Kafin wannan rana ta zo, iyaye za su yi ƙoƙarin ƙawata ‘ya’yansu musamman mata wajen yi masu ɗinke-ɗinke da yi wa ‘ya’ya kyaututtuka daban-daban saboda murnar wannan rana.Mata sukan yi kitso da ƙunshi da ɗinkuna da hijabai da sauran kayan kwalliya. Haka kuma samari kan haɗa wa ‘yan matansu kayan kwalliya da sauran abubuwa har ma da dabbar da za ta yanka a ranar. Matan aure ma kan yi wasu abubuwa kamar yi wa mazajensu kyautuka na dabbobin yanka da ɗinkuna da sauransu. Kuma sukan rarraba kyautuka ga yaran gari.
           A ranar 19 ko 20 ga watan, sukan samu keɓaɓɓan wuri su ƙawata shi da tutoci da ganguna da furanni sai su shigo gari suan bi layi-layi suna waƙe-waƙe da tirenin kala daba-daban. Kuma har baƙi daga wasu garuruwa sukan halarci wannan zagaye wanda suke gamawa idan dare ya far shigowa. Kashegari kuwa su gayyato malamai a kwana karatu da wa'azi da sira da sauran nasihohi.
       A ɓangaren ‘yan ɗariƙu kuwa, nasu ya bambanta da na‘yan shi'a. Kuma su ma tsakanin 'yan ɗariƙun akwai bambancin yadda ake yin bukin na maulidi. Misali ‘yan ƙadiriyya sukan shiga masallatai ne su yi ta wa'azi ko karatun Al'ƙur'ani  da zikirai tun daga farkon watan har ƙarshensa.
Su kuwa ‘yan Tijjaniya, su ma sukan fara tun daga farkon watan har zuwa ƙarshensa, har ma wani watan ya shigo. Amma a ranar 12 ga watan, an fi yin kwalliya da dafe-dafen abinci da sauran hidimomin maulidin. Kuma a wannan rana sukan gayyato malamansu na gari da wajen gari domin jan hankali gamr da bukin na maulidi da tarihin Annabi da sauran faɗakarwa. Kuma makarantunsu nan ne dandalin maulidinsu. A cikin wannan wata, sukan samu ƙofar gidan shehun ɗariƙarsu su kafa sifiku a sanya kaset na yab on Annabi su yi ta rawa  suna bugun ƙirjinsu. Amma fa maza ne ke yin haka ban da mata.
3.5  Bukin Walimar Sauka Da Yadda Ake Yin Sa
Asalin Kalmar walima Hausawa sun arota ne daga larabci.A Harshen Larabci walima na nufin liyafa ko shirya abinci daban-daban na musamman ga mutanen da aka gayyato a wajen wani sha'ani. A Hausa kuma yawanci Hausawa na amfani da kalmar ne domin shirya wani taro da zaa wa’azantar da mutane tare da jawo hankulansu zuwa ga wasu muhimman abubuwa na shari’a. Yawanci Hausawa sukan shirya walima ne domin nuna farincikinsu ga samuwar wani abun alkhairi.Misali a wajen aure ko suna ko Saukar Alƙur’ani da dai sauransu. A taƙaice dai, ana shirya walima ne ‘yan uwa da abokan arziki su taya wani murnar wani abu da ya same shi. to a nan za a yi bayani ne a kan walimar saukar Alƙur'ani ne.
3.5.1 Bukin Walimar Sauka
              Bukin walimar sauka buki ne da malaman Islamiyu kan shirya wa ɗalibansu domin taya su murnar sauke Al'ƙur'ani mai girma. Ana shirya wannan buki ne domin zaburar da ɗalibai na ƙasa masu tasowa, don su dage wajen ƙoƙarin karatu da kuma haddar Al'ƙur'ani mai girma. Bukin walima ya ƙunshi kowa da kowa, manya da ƙanana mata da maza. Wato dai, kowa ana yi masa wannan walima madamar ya sauke Al'ƙur'ani mai girma.
3.5.2  Yadda Ake Yin Sa
                 Ana yin wannan buki ne bayan malaman Islamiya sun yi shawara , sai su yanke ranar da ta dace sannan su sanar wa ɗaliban da abin ya shafa don su sanar da iyayensu saboda afara shirye-shirye. Su kuwa malamai za su buga takardun sanarwa su bai wa manyan malamai da masu faɗa a ji na wannan gari. Malamai sukan shirya wasu kyautuka ga ɗaliban da suka sauka kamar su Alƙur'anai da turame da hijabai da sauransu.
       Iyaye kuwa za su fara shiri ne daga lokacin da aka sanar da su domin su faranta wa‘ya’yansu rai.Kowane ɗalibi iayayensa kan yi masa hidima ne daidai ƙarfinsu. Wasu kan yanka raguna ko kaji ko a siyo kifi tare da dafa abincin alfarma da abubuwan sha da sauransu. Dukkan wannan hidima ana yin ta ne saboda waɗanda za su halarci bukin.‘Yan mata kan yi ado su sanya manyan hijabai, maza kuwa kan sanya manyan kaya da babbar riga. Yawanci akan yi walimar ne a ranar Juma'a ko Asabar, kuma an fi gudanar da bukin ne da safe ko da yamma. Akan ƙawata muhallin walimar da kujeru da fulawowi da rumfuna da tabarmi domin mahalarta su sami wurin zama. Manyan kujeru kuwa an tanade su domin  manyan baƙi.
        Ɗaya daga cikin malaman zai yi jawabi a madadin saura na maraba da zuwa da kuma bayyana maƙasudin taron, sannan za a kira ɗaliban su karanta abin da ya sauwaƙa daga ayoyin Ƙur'ani mai girma. A wasu lokuta sukan gudanar da wasan kwaikwayo na larabci domin ƙara ƙayatar da taron. Daga nan sai a ba manyan gari dama su yi jawabai tare da bayar da kyaututtuka ga makaranta da kuma ɗaliban. Akan samu ma masu ɗaukar nauyin yi wa makaranta wasu manyan ayyuka daga cikin baƙin. Bayan jawabai sai a fara rarraba abinci kala-kala ga mahalarta, sai kuma a damƙa kyautuka ga ɗalibai sai addu'ar rufe taro ta biyo baya.
3.6 Tasirin Zamani A Kan Waɗannan Bukukuwa
Shi zamani abu ne mai tafiya da lokaci kamar yadda shekaru ke sauyawa haka shi ma zamani ke sauyawa. Bisa ga haka, za a yi tsokaci game da tasirin zamani a kan bukukuwan da aka bayani a baya.
                Haƙiƙa idan aka yi la'akari da bukukuwan da aka kawo bayaninsu a baya, za a ga cewa akwai tasirin zamani sosai a cikinsu saboda an yi bayanin yadda ake yin su a yau.Idan aka dubi bukukuwan za a ga wasu sabbin abubuwa waɗanda ake gudanarwa a wurin hidimar aure saɓanin a zamanin da, misali; zaman laushi da kamu da dai sauransu. Akwai abubuwa guda biyu muhimmai da suka yi fice wajen kawo zamananci a wannan lokacin kamar irin su gudummawar fina-finai, da kuma gudummawar na’urorin zamani.
3.6.1 Gudunmuwar Fina-Finai Wajen Gudanar Da Bukukuwan Hausawa
    Fina-finai na bayar da gudummawa matuƙa gaya wajen gudanar da bukukuwan Hausawa daban-daban. Misali:
         Kamu- Kalmar kamu na nufin kamun amarya. Idan aka dubi yadda ake kamun amarya a wannan lokaci za a ga cewa ya bambanta da yadda ake yin sa a lokutan baya. Masu fina-finan Hausa na ɗaya daga cikin mutanen da suka sauya wa kamun amarya sifa daga yadda yake. Kamar yadda aka ambata a babin baya, shi kamu a garin Tsafe ba dole ba ne a wannan lokaci, amma a zamanin da, dole ne ga kowace amarya. Domin a wancan lokaci amarya kan ɓuya yan bukisu yi ta nemanta lunguna da saƙuna har su gano ta su sanya mata lalle, daga nan a rako ta a yi mata wanka sai ɗakin miji.
         Cin Abincin Dare (Dinner)- Shakka babu an koyi wannan abu ne daga wurin masu shirya fina-finai. Wannan al'ada ta cin abincin dare ana yin ta ne daga misalin ƙaarfe 8 zuwa 12 na dare. Akan kuma cakuɗu tsakanin maza da "yan mata a yi kaɗe-kaɗe da raye-raye da ciye-ciye da shaye-shayen kayan sha a tsakaninsu. Kuma ana ganin yin hakan shi ne wayewa kuma burgewa a wurin bukin auren kowace amarya.
         Ɗauko Makaɗa da Mawaƙan Zamani- A kan ɗauko makaɗa da mawaƙa na zamani musamman daga wasu garuruwa, waɗanda yawansu "yan wasan fina-finai ɗin ne, kamar su Nura M. Inuwa da M. Sharif da Asnanic da Gwanja da sauransu. Wai idan buki ya kai buki to ana tsammanin a ga ɗaya daga cikin makaɗan zamanin nan ya halarci bukin. Domin a shagala a shaƙata.
         Ƙunshin Sifa Na Amarya Da Ƙawayenta- Bincike ya nuna cewa mata sun samu wannan ɗabi'ar ƙunshin sifa ne daga wajen masu shirya fina-finan Indiya. Don haka ne yasa matan mu na Hausawa suka koyi wannan ɗabi'a ta ƙunshin sifa, domin kwalliya a gare su musamman wajen gudanar da hidimar bukukuwa daban-daban.
         Ƙunshi amarya daban yake da na sauran ‘yan buki, domin akan cika wa amarya ƙafa da hannuwa ne da zanen sifa kai wata ma har a ƙirjinta ana zana mata, kuma a tsara shi ya yi matuƙar kyau. Akan ɗauko masu sana'ar masu sana'ar sifa ɗin ne idana sun yi a biya su.
         Ankon Buki Da Yi Matsattsun Ɗinkuna- Anko na nufin ɗinkin sutura iri ɗaya a kuma sakata a rana ɗaya ga mutane daga biyu ko fiye da haka. Ankon buki na aure ko haihuwa ko ma dai wani buki na daban, abu ne wanda mutane suka samo ɗabi'ar yin sa a wajen masu shirya fina-finai. Shi dai anko na nufin ɗinka kaya iri ɗaya, wato atamfa ko leshi ko shadda ga wasu mutane da za su gudanar da wata hidima. Kuma akasari ango ko amarya ko masu ruwa da tsaki a bukin kan fitar da kalar kayan da za a ɗinka. Kuma akasari yanayin ɗinkuna sun saɓa wa al'adar Hausawa.
         Canje-Canjen Sa Tufafin Amarya Ranar Buki- Tabbas a wannan zamani shi ne cikakkiyar wayewa ga amarya a ranar bukinta, ta dinga sa sutura kala-kala tana canzawa, tana bayyana adonta ga ‘yan buki. Kuma wannan wayewar ma ta samo asali ne daga masu fina-finai. A yayin da amarya ke wannan canje-canje za ka ji mutane kowa na tofa albarkacin bakinsa. Misali, za ka ga wasu na cewa ashe haka wance take da kyau. Kuma hakan na nuna yanayin lefen da aka yi wa amarya.
3.6.2 Gudummawar Na'urorin Zamani Ga Bukukuwa
                 Tabbas ko shakka babu na'urorin zamani na sadarwa na ba da muhimmiyar gudummawa wajen gudanar da bukukuwan Hausawa  a yau.
         Telebishin - Talebishin na'ura ce ta sadarwa da mutane ke amfani da ita wajen sanarwar ranar bukukuwansu. Sannan kuma masu gudanar da wasu bukukuwa kamar na aure da haihuwa da salla da maulidi da sauka da sauransu kan gayyato ma'aikatan gidan talabishin domin su ɗauki hotunan hidimomin bukin a je a saka ga gidan telebishin domin a nuna wa duniya yadda bukin su wane ko wance ya gudana a wani gari.
         Rediyo- Gidajen rediyo kan taka muhimmiyar rawa wajen ba da sanarwar ɗaurin aure da sauran hidimomin buki na haihuwa ne ko na aure da sauransu. Akan bayar da sanarwar buki a gidan rediyo domin gayyatar al'umma zuwa wajen wannan hidima.
         Wayar Salula- Wayar salula na taka muhimmiyar rawa wajen ba da gudummawar hidimomin na yau ta ɓangarori da dama kamar haka:
i.        Hotuna- Waya na ba da gudummawa da dama wajen yin hotunan buki na aure ko haihuwa ko salla da dai sauran bukukuwa, Hotunan wayar salula tana taimakawa wajen yaɗa irin kwalliya da hidimomin da aka gudanar a wajen harkokin buki musamman a yanar gizo. Yin hoton wayar salula a wurin bukukuwan na yau, ya zama ruwan dare musamman ga mata.
ii.      Bidiyo- Ɗaukar hotuna na bidiyo a wayar salula ya zama ruwan dare a wajen gudanar da bukukuwa a wannan zamani. Kuma bidiyon da aka ɗauka a wajen buki yana taimakawa wajen yaɗawa da adana hidimomin da aka yi a wurin buki.Kuma yana yaɗuwa a yanar gizo kamar wutar dare.
iii.    Katin Gayyata- Wayar salula na taimakawa wajen yaɗa katin buki na wata hidima. Akan rubuta katin buki a tutturawa‘yan uwa da abokan arziki ta hanyar yanar gizo.Kuma, katunan kan isa wurare da dama. A cikin ƙanƙanin lokaci katin gayyatar kan isa a duk inda ake buƙata.
3.7     Naɗewa
            Wannan babi ya tattara muhimman bayanai dangane da wasu fitattun bukukuwan Hausawa a garin Tsafe a yau. A wannan babi an gano yadda wasu al’adun bukukuwan aure da haihuwa da sallah da walimar Sauka da bikin Maulidi suke gudana a garin Tsafe. Sannan kuma an yi bayanin yadda zamani yayi tasiri akansu ta hanyar gudummawar wasu na’urorin zamani kamar Talabijin, gidan Rediyo da wayar Salula da sauransu.



BABI NA HUƊU
RAWAR MATA A WAJEN BUKUKUWA A GARIN TSAFE
4.0 Shimfiɗa
Babi na huɗu zai yi bayani ne a kan irin rawar da mata suke takawa a wajen fitattun bukukuwan garin Tsafe, wato bukin aure da na haihuwa da na sallah da maulidi da kuma walimar sauka. A cikin wannan babi, za a ga yadda mata suke aiwatar da hidimomi domin burgewa a wajen tarurrukan bukukuwa. Abubuwan sun haɗa da gasar kwalliya da ta abinci, da kuma bayar da gudunmuwa wato ajo. Haka kuma, babin zai yi bayanin wasu miyagun halaye da mata ke aiwatarwa a jen taro buki, da suka haɗa da faɗace-faɗace da ɗanhali da tsegumi da sauransu.
4.1 Gasar Kwalliya
Gasa na nufin kwaikwaiyon abin da wani ya yi, ko son yin abin da ya yi ko ta halin yaya. Kwalliya kuwa na nufin yin ado ta hanyar yin wanka da sanya kyawawan tufafi. Kwalliya abu ce muhimmiya ga mata musamman a wuri tarukan bukukuwa.Wannan ya haifar da gasar kwalliya a wuraren bukukuwa. Mata kan ƙure adaka, ko su yi sababbin ɗinkuna idan za a gudanar da buki. Kowace mace tana fatan ɗara tsara a wajen buki. Irin wannan gasar tana haddasa wata illaga mata ta yadda wasun su kan kasa haƙura da abin hannunsu, har ta kai su ga yin munanan abubuwa,don kawai a samu kuɗin yin “anko”.
Idan aka ce an yiwa wani abu kwalliya to ana nufin an ƙawata  shi. Yi wa abu kwalliya na nufin saka masa wasu abubuwa da za su ƙawata siffarsa a idon masu kallo. Hakan zai sa ya birge. Kwalliya kuwa ga mata na nufin saka wasu ƙyale-ƙyale da za su fito da kyawun jikinta. Nau'o'in kwalliya sun haɗa da:
4.1.1 Kwalliyar Sutura
Sutura na nufin duk wani nau'in tufafi da zai sirranta tsiraicin jikin mutum. Sutura na cikin kayan adon Hausawa, domin sukan yi musu ɗinkin da zai yi kyau a jiki. Daga cikin irin suturun da aka fi son yin kwalliya da su akwai leshi da atamfa da shadda da sari da fashon hijab da ɗankwali da sauransu.
Mata sukan sanya ɗunkunan sutura iri daban-daban kamar haka: Riga da Sicket Pieces, Riga da Sicket wrapper, Doguwar Riga pieces, Doguwar Riga Bubu, Riga da Zani Pieaces,  Karkace Ƙirji, Riga mai uwan sama (High neck), Stone work, da sauransu.
Riga da Siket Pieces


Riga da Siket rapper

Doguwar Riga pieces


Doguwar Riga Bubu


Riga da Zani Pieces

Karkace Ƙirji da sauransu


Riga mai wuyan sama (High neck)

Stone work,






4.1.2      Kwalliyar Fuska:
Kwalliyar fuska na nufin amfani da duk wani abu domin ƙawata fuska.Daga cikin nau'o'in abubuwan kwalliyar fuska akwai; hoda da kwalli da jambaki da gazar da ƙyalƙyalin ido da man baki da sarƙa da "yan kunne da sauransu. Ita hoda ana shafa ta ne a fuska domin ƙara wa mace haske. Kwalli kuwa a ido ake shafawa. Gazar kuma a gira ake shafa shi. Man baki da jambaki kuwa duk kayan adon leɓɓa ne.
4.1.3 Kwalliyar Kai:
Kitso ne ake yi wa mace don ta yi kyau da sheƙi. Wasu kuwa ba a yin kitson sai dai a yi famin a shafa man gashi mai ƙamshi, domin gashin ya yi kyau sai kuma a yi mai wani salo da zai birge tare da fito da kyawun mace.Kayan gyaran kai sun haɗa da man gashi da na kitso da na wankin kai da turaren gashi da sauransu. Ga hotunan ire-iren wannan gyaran kai kamar haka:



4.1.4 Kwalliyar  Hannu Da Ƙafa:
Ire-iren kayan da matan Hausawa kan yi amfani da su wurin yi wa hannu da ƙafa kwalliya sun haɗa da lalle da sauransu. Mata da dama sukan yi wa hannuwansu da ƙafafunsu kwalliya a yayin da za su yi wani buki. kuma suna da nau'o'in ƙunshi guda biyu kamar haka:
i.        Lallen Gargajiya: Ganyen iccen lalle ne ake dakawa ya zama gari sannan a kwaɓa shi da ruwa a shafa ma ƙafa ko hannu sai ya zama jajir. Bayan an wanke wasu kan sanya gishiri ko kuma su bar shi haka. Wannan ƙunshi na sanya hannu ko ƙafar mace ta yi kyau. Sai dai a wannan zamani mata sun yi watsi da wannan nau'i na ƙunshi, suna ma kallon masu yi a matsayin ‘yan ƙauye ko tsofaffi.
ii.      Lallen Zamani:   Irin wannan lalle ana zana sa ne a hannu da ƙafa , kuma shi wannan lalle yawanci an fi sayar da shi a kantuna. Domin kuwa lalle ne na ƙasar Indiya. Daga cikin ire-iren wannan lalle akwai bejin da sajan da rani da sauransu. Wannan ƙunshi yana ƙawata mace idan aka yi mata shi a ƙafa da hannu. Kuma kwalliyar ƙunshi ta zama ruwan dare ga matan Hausawa musamman a lokacin gudanar da bukukuwa. Ga ƙalolin ƙunshin siffa, kasancewar shi ne baƙon abu a ƙasar Hausa, saɓanin lallen gargajiya da aka saba da shi. Ga hotunan kamar haka:



4.2 Gasar Liyafa
        Gasar Liyafa gasa ce da kowace mace kan yi lokacin da take da hidima, saboda abin kunya ne gare ta a ce a bikinta ba a ci an sha ba an yi hani’an. Wato sukan so a ce a bukin wance an ci abincin da ba a taɓa ci ba, wannan kan haddasa gasa a tsakanin mata dangane da abincin. A ranar yinin aure ko suna, mai bukin za ta tanadar wa 'yan buki da abinci da abin sha matuƙar iyawarta, don kawai a ce wance ta kashe maƙudan kuɗaɗe a wurin bukinta. Ana dafa abinci iri-iri da suka haɗa da:
         Masa(waina) da miya
         Dambun shikafa ko na masara
         Alalar leda da yaji
         Dafa-dukar taliya
         Shinkafa da miya ko dafa-duka
     Su kuwa matan dake son a ce bukin su ya burge bayan dafa ɗayan waɗancan ko fiye da ɗaya, sukan yi ƙari da ɗayan waɗannan:
         Ɓula da miya
         Doya da ƙwai
         Burabisko
         Ɗanwake da sauransu.
Yawancin irin waɗannan abinci mai bukin kan bayar da kuɗi ne ko kayan yin su a kai wani gida a yo mata. Ranar bukin sai a kawo domin buƙatar 'yan buki.Wasu 'yan bukin ma har guzuri suke yi zuwa gidajensu. Irin wannan liyafa ke sa wasu mata zuwa buki ko da ba a gayyace su ba.
4.3  Gudummawa
Gudummawa abu ce mai matuƙar muhimmanci ga uwar buki, domin kuwa takan taimaka wa uwar bukin wajen rage kuɗin da ta kashe a hidimar. 'Yan uwa da abokan arziki ke kawo wa uwar buki kyautuka daban-daban. Matan kan kawo gudummawarsu domin su ma in tasu hidimar ta tashi ta samu gudummawar daga waɗanda ta yi wa. Ire-iren gudummawar da akan bayar sun haɗa da:
         Gudummawar Sutura- Gudummawar sutura na nufin zannuwan turame da kayan jarirai da 'yan buki ke kawo wa mai jego, ko kuma ɗinkakkun kaya da ƙawaye ke kawo wa amarya ko mai jego.Kuma yawanci da waɗannan kayan ne amarya ko mai jego ke cin buki.
         Gudummawar Kuɗi- Yawanci 'yan uwa da abokan arziki kan kawo wa uwar buki gudunmuwar kuɗi domin ta rage wata ɗawainiyar kuɗin hidimar da su. Amma yawanci manyan ƙawaye ba su cika yin bukin kuɗi ba.
         Gudummawar Abinci- A irin wannan gudummawa yawanci ƙawaye da yayye kan yi ta. Sukan ɗauki nauyin dafa abincin da za a ci a wajen buki. Sukan yi matuƙar ƙoƙari wajen ganin asirin 'yar uwarsu ya rufu. Kama daga kayan ci ko na sha ko na lashe-lashe da sauransu. Hakan na taimaka wa uwar buki samun sauƙin kashe kuɗi.
4.4  Ƙirjin Buki
Ƙirjin buki itace aminiyar babbar ƙawar amarya /maijego. Wato wadda uwar biki ta aminta da ita ta hannunta mata komai na hidimar bukin.
Ƙirjin buki mace ce wadda take taka mahimmiyar rawa wajan bukin, domin kuwa, idan haihuwace, to tun randa aka haihu kullun zata rinƙa zuwa gidan mai jegon domin tarbar jama’ar da ke zuwa wajan barka, musamman in haihuwar farko ce. Idan kuwa bukin aure ne to wannan ƙirjin buki kakarta ta yanke saƙa wajen fita kullun zuwa gidan su amarya domin shirye-shiryen bukin kokuma amarya takan rinƙa zuwa ta iske ƙirjin buki a gidansu domin shirye-shirye idan ana sauran sati daya a ɗaura aure amarya da ƙirjin biki tare suke zuwa wajan rarrabama sauran ƙawaye katin gayyata. Sannan kuma wata ƙirjin bukinma ita ke zaɓawa amarya kayan da zata sa a ranar yinin buki sabo da yarda da amincin da ke tsakaninta da amarya  kuma ranar bukin duk ƙawayen amarya da suka halarci bukin itace zata zuzzuba masu abincin da zasu ci sannan kuma ta kakkai wa kowa abun sha kamar su soɓo, lemu, da ruwa. Sannan kuma ita ke rabawa kowa kayan biki irinsu robobi da cincin da sauransu. Haka kuma idan biki na haihuwa ne wata ƙirjin bukin, har ɗinkin tsadaddiyar sutura takan yi ma maijego domin taci kwalliyar biki da ita a matsayin gudummuwarta.Ƙirjin buki ba kowanne buki ne take da tasiri ba illa waɗannan bukukuwa guda biyu wato bukin aure da na haihuwa.
4.5  Ajo
Ajo na nufin haɗin guiwa na ƙawaye da maijego ko amarya su ka yi zama aji  ɗaya da su a makarantar boko. Haka kuma ko ba aji ɗaya a ka yi ba, akan haɗa ƙungiya ne ga duk wanda ke so, sai a sa sunan sa, sannan kuma a faɗa wa mutun kuɗin da za a rinƙa bayarwa idan hidimar ɗaya daga cikin ‘yar ƙungiyar ta tashi. Amma dai an fi yin na ‘yan aji ɗaya wato (mate).
4.6  Yadda Ake Yin Ajo
Shidai wannan ajo kamar zubin adashe yake, idan ka zuba wa mutun ga hidimar sa, shi ma zai zuba maka ga hidimarka. Idan ko baka zuba masa ba, to shi ma ba zai zuba maka ba. Kowa da kowa na yin ajo idan ya so, wato maza da mata, tsofaffi da yara amma mata sun fi yin shi. Wannan ajo yawan kuɗin da ka zuba wa mutun, su zai zuba maka, babu ragi, kuma babu ƙari. Idan aka zuba wa mutuin bai mayar ba to za a bi mutun bashi har sai ya biya. Idan a kai ta bi biyar mutun bai bayar ba, to sai a cire shi daga ƙungiyar, ko da mutun na son a maidashi, to sai ya biya bashin da ke kansa.
A cikin ƙungiyar ajo akan zaɓi wani mutun ɗaya, domin ansar kuɗin ajo. (Idan ajon maza ne, za a zaɓi namiji guda me karɓar kuɗin ajo). Idan kuwa ajon mata ne, to za a zaɓi mace da aka san batada nasiha ta  rinƙa ansar kuɗin ajo. Irin waɗannan shuwagabanni na ajo su ne ake kira (na ajon maza”uban ajo” na ajon mata kuma) “uwar ajo”.
Yawancin mutane sukanyi ajonsu dai-dai ƙarfin ‘yan ƙungiya. Amma saidai da wuya a ƙungiyar ajo a yi ƙasa da ɗari biyar (500). Duk wani ɗan ƙungiyar ajo yakan kawo ma uwar/uban ajo ƙuɗin ajonsa ne a ranar yinin buki, wato na aure ko haihuwa.
Uwar ajo tana ɗauke da wani littafi na musamman a ranar buki, wanda ke ɗauke da sunayen duk wadda ke cikin ƙungiya. Idan ‘yan ƙungiya sun fara shigowa, kowa zai nemi uwar ajo ya ba ta kuɗin da aka tsara za a rinƙa bayarwa ga hidima. Ita kuwa uwar ajo da littafin ta da biro a hannunta, duk wanda ya bayar a yi masa sheda a wurin sunanasa. Wanda kuma bai bayar ba a bar sunansa hakanan babu wata sheda. Amma kuma za a bi sa bashi , idan bai bayar ba a cire sunansa a ƙungiya.
Bayan uwar ajo ta gama tattara ƙudaden ‘yan ƙungiya, sai ta hannanta wa uwar buki/me hidima. Sannan kuma ‘yan ƙungiyar ajo, uwar buki kan shirya masu  liyafa (Abincinsu na daban). Za a ji uwar ajo na faɗin ‘yan ajo ku je ga abincinku can a ɗaki. Haka kuma kayan bukin su ma na daban ne.   
4.7 Aikata Miyagun Halaye
4.7.1   Sata A Gidan Buki
      Sata a gidan buki ta zama ruwan dare a wannan zamani. Wasu mata da dama idan suka je gidan buki suna zuwa ne da niyyar yin sata.Wato da zuciya biyu suke zuwa. Wasu kuwa ko ba a gayyace su ba za su je don kawai su yi sata, da zarar sun ga kayan wata a arha , sai kawai su sace. Ire-iren satar da ake yi a gidajen bukukuwa sun haɗa da:
         Satar kuɗi da waya-Idan 'yan buki sun ajiye jakunansu sai ɓarauniya ta saɗaɗa ta kwashe masu kuɗi ko wayoyi. Wata ɓarauniyar kuwa in ta shahara sai ta laɓaɓa ta sace 'yar gudunmuwar mai mai jego gaba ɗaya.
         Satar takalmi - Ɓarayi mata kan saci takalma a gidajen buki da zarar an aje saboda sun fi sauƙin sata. Da zarar sun tarar da takalma masu tsada sai su saka a ƙafarsu su fice da su. Wasu kan yi satar ne saboda rashi wasu kuwa saboda hangen na sama da su ne ke haddasa su yi sata.
         Satar zannuwan turame ko sarƙoƙi- Wasu ɓarayin sukan saci turame ko kayn jarirai da 'yan buki ke kawo wa mai jego a matsayin gudunmuwa. Ita kuwa amarya an fi yi mata satar zannuwa ko sarƙa ko 'yan kunne. Don haka an fi yin sata a bukukuwan aure da haihuwa.
4.7.2   Faɗace-Faɗace A Wajen Buki
            Faɗa a wajen buki abu ne da ya zama ruwan dare a gidajen buki a yau. Yana da matuƙar wahala a fara hidimar buki har a gama ba tare da an samu saɓanin da ke haddasa faɗa ba. Kuma akasari faɗan na faruwa ne sanadiyar ɗan abu kaɗan, kama daga abincin buki ko kayan buki ko naman buki ko 'ya'yan 'yan bukin. Irin wannan faɗan yana faruwa a tsakanin dangin miji da na mata ko dangin amarya da na ango.
      Mawuyacin abu ne a fara hidimar buki har a gama ba tare da an samu matsala tsakanin dangin miji da na mata ba. Irin wannan faɗan na faruwa ne a tsakanin ƙawayen amarya saboda kuɗin da ango kan bayar domin hidindimun 'yan mata, sai babbar ƙawa ta riƙe.Yin hakan kan harzuƙa sauran ƙawaye su fara habaice-habaice gare ta. Nan take in ba akai zuciya nesa ba sai faɗa ya kaure.


4.7.3   Tsegumi Da Gulma 
         Gulma na nufin ɗauko abin da wani ya yi ko yake aikatawa a faɗa ma wani. Tsegumi kuwa na nufin a ɗauko sirrin wani mutum a je cikin wasu jama'a a fallasa. Tsegumi da gulma abu ne da su ka yi fice a wurin buki, kuma kusan kowa da kowa na yin su, tun daga tsofin mata da yaran mata. Da zarar taron buki ya fara cika, za a ga mutane sun yi ƙungiya -ƙungiya a na firarraki. Awannan lokaci duk macen da ta shigo kota gifta sai a yi maganarta.Yawanci waɗanda ake gulmar da su kan hassala idan suka ji a wasu lokuta wannan yake zama faɗa.
Abubuwan da sukan haddasa gulma da tsegumi a gidan buki sun haɗa da kisisinar wasu matan, da yawan cin abincin wasu, da kallon raini daga wasu, da sauransu.
4.7.4  Kiɗa Da Rawa A Wajen Buki
      A gidajen bukukuwa a yanzu akan ɗauko makaɗa da mawaƙa ko kuma akunna kaset na waƙoƙi domin a ɗan cashe da raye-raye. Hakan na faruwa ne a gidajen aure ko suna ko kuma da salla. Wasu ma kan samu wani keɓaɓɓen wuri domin wannan shagali. Wasu kuwa sukan ɗauko masu kiɗan ƙwarya (amada).
          Hakan na faruwa ne a gidajen bukukuwa domin samun ingantaccen nishaɗi da annashuwa a tsakanin al'umma. Kiɗe-kiɗe da raye-raye na ƙara jawo hankalin mutane da yawa su halarci bukin don su kashe ƙayar idanunsu.
4.8 Naɗewa
            Wannan shi ne babi na kusa dana ƙarshe. A wannan babi an ga yadda mata ke taka muhimmiyar rawarsu a bukukuwan garin Tsafe, wannan rawa da mata suke takawa ta shafi abubuwa guda biyu ne kamar yadda aka yi bayani a cikin babin, rawa ta farko ita ce aikata ayukkan alkhairi kamar gasar bada gudummawa, gasar kwalliya, gasar sa sutura da kuma ajo. Sai kuma rawa ta biyu da suke takawa tana ɗauke ne da miyagun ayukka kamar sata a gidan buki, faɗace – faɗace, tsegumi da gulma da sauransu.



BABI NA BIYAR: TAƘAITAWA

5.0  Kammalawa
Alhamdulillahi, Hausawa dai na cewa, komai ya yi farko, to dole zai yi ƙarshe. Don haka a nan ne na zo ƙarshen wannan aiki da na gudanar a kan “Rawar Mata a Bukukuwan Garin Tsafe.
            Tun da farko dai wannan aiki an rarraba shi ne zuwa babuka guda biyar, kuma kowane babi da abin da ya ƙunsa, kamar haka:

Babi na ɗaya ya ƙunshi muhimman bayanai, waɗanda suka haɗa da, dalilin bincike da manufar bincike, da muhimmancin bincike da muhallin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike da tambayoyin bincike da kuma bitar ayyukan da suka gabata, sa’a nan kuma da hujjar ci gaba da bincike.
            A babi na biyu kuwa, an yi bayani taƙaitacen tarihin garin Tsafe, a inda aka yi bayanin abubuwa kamar haka; Asalin sunan garin Tsafe da farfajiyar Tsafe da yanayinta, da tsarin mulki a ƙasar Tsafe, da mulkin ‘Yandotawa, sannan kuma da sunayen sarakunan Tsafe tun farkon kafa garin har zuwa yau.
            Shi kuwa babi na uku, ya ƙunshi bukukuwan da aka yi bincike a kansu, wato bukin aure da yadda ake yinsa, da bukin suna/haihuwa da yadda ake yin sa, da bukin sallah da yadda ake yin sa, sai kuma bukin Maulidi da yadda ake yin sa, sannan kuma bukin sauka da yadda ake yin sa, sai kuma tasirin zamani a kan waɗannan bukukuwa.
            Sai kuma babi na huɗu, wanda shi ne ƙashin bayan wannan aiki, a inda aka yi bayani ire-iren rawar da mata suke takawa a yayin da ake gudanar da waɗancan bukukuwa. Waɗannan raye-raye da mata suke takawa sun haɗa da gasar kwalliya da gasar liyafa da sata a gidan buki, da gudummawar buki da faɗace-faɗace a wajen buki da tsegunguma da tsince a wajen buki da kuma kiɗa da rawa/ cassu, sai kuma ƙirjin buki sannan kuma ajo.           
            Sai kuma babi na biyar inda aka kamala aikin. Yana ɗauke da jawaban taƙaitawa, da na sakamakon bincike. Sai kuma shawarwari da aka bayar ga ɗalibai da hukumomi da iyaye ko mazajen matan da ke halartar tarurrukan buki.
            A ƙarshe, ina fatar wannan ɗan ƙaramin kundi nawa ya kasance mai alfanu ga duk wanda ya ɗauke shi da niyyar karantawa ko kuma bincike. Sannan kuma ina fatar wannan kundi ya zamo mai amfani ga masana da manazartan al’adun Hausawa musamman akan bukukuwa.

5.1 Sakamakon Bincike
Sakamakon da ya bayyana a wannan bincike shi ne cewar, rayuwar mata ba ta gudana sai da sha’anin buki, wato dai buki ya yi sansani a cikin zuciyar matan Hausawa. Haka kuma, nazarin ya fahimci cewa mata na kashe dukiyarsu ga sha’anin buki fiye da rashin lafiya ko wata matsalar rayuwa. Haka kuma, buki na haifar da fitunnun rayuwa da ke haddasa kashe-kashe da sace-sace da faɗace - faɗace a cikin al’umma. Ko dai su matan su yi satar da kansu ko su saka mazansu su yi satar, don su kawo musu kuɗi, su biya bukatar buki.
Bugu da ƙari, an samu nasara ziyara wurin masu sana’ar ɗunkunan mata da kuma wurin masu gyaran kai da kuma masu sana’ar ƙunshin sifa/ lallen zane na hannu da ƙafa domin samo hutunan salailai na ɗunkunan, da gyaran kai da kuma ƙunshin sifa/lallen zane. Wani abun burgewa kuma shi ne an sanya hotunan ɗunkunan da hotunan gyaran kai da kuma hotunan hannu da ƙafa na ƙunshin sifa a cikin shafukkan da aka yi bayani game da su. Domin mai bincike ya yi saurin fahimtar bayanin yadda ya kamata.

5.2 Shawarwari
            To! Hausawa dai na cewa “Gadon Gida alali a raggo ko wabbar gida, gida ya barshi” a nan ina so in ba al’ummar Hausawa shawarwari akan yadda za su watsar da baƙin al’adun bukukuwa da suka aro daga mutane barkatai. Ina ba mutanen Hausawa shawara da su farfaɗo da al’adunmu na gargajiya wajen gudanar da bukukuwansu. A yau al’ummar Hausawa sun tsinci kansu cikin wasu al’adu barkatai, musamman a wajen hidimomin buki har ma da harkokin su na yau da kullum, abin baƙin ciki za a ga Hausawa na gudanar da wasu ababe a yayin bukukuwansu, waɗanda suke ba al’adu ne na Hausawa ba, wasu al’adun na Yarbawa ne, wasu na Fulani ne, wasu kuma na Indiyawa ne, kai wasu ma ka rasa wai shin daga ina su ka samo waɗannan al’adu, kuma ma wata al’adar da za a tambayesu shin wai wannan abu da aka gudanar a wannan buki, al’adar su waye? To a nan fa za a ga an fara ‘yan kame-kame, sai a ji mutum ya ce, To! Nima dai na ga wane ko wance ta yi abin a bukinta kuma ya yi kyau, shi ya sa ni ma na yi shi a bukina. Da wahala kaji an bada ƙwaƙƙwarrar amsa.
            To! don haka wallahi Hausawa garemu, mu tashi tsaye domin farfaɗo da al’adunmu musamman a wurin bukukuwa.Shin wai idan ba mu farfaɗo da al’adunmu, mu ka ƙafa gina su ba, su waye muke so su haɓɓaka mana su? Al’adun Hausawa al’adu ne na burgewa, al’adu ne na nishaɗantarwa, haka kuma al’adu ne masu muhimmancin gaske. Domin kuwa idan muka guji al’adunmu, to ta ya ya wasu al’umma za su san ko su gane al’adunmu har su yi sha’awarsu?
            Wallahi! ƙalubale gare mu mutanen Hausawa. Idan muka tsaya muka yi tunani za mu ga cewa, da yawa fa mutanen da muke sha’awar al’adunsu, har muke aro su, su zama namu, mawuyacin abu ne a ga su, suna aron namu al’adun, saboda kishin al’adunsu. Sannan kuma, wasunsu ma da yawa maƙiyanmu ne, basu son mu ballantana ma su so al’adunmu.
            Sannan kuma yawancin su ma, sukan girmama tare da fifita al’adunsu fiye da addininsu. To amma ni a nan bance mu fifita al’adunmu fiye da addini ba. Amma dai ya kamata mu gyara. Domin kuwa, idan bamu gyara ba, wallahi babuwanda zai gyara mana. Mun ɗauki al’adunmu ƙauyanci, ko rashin wayewa, musamman a wajen bukukuwanmu na Hausawa, saboda a yau al’adunmu, musamman na aure, duk sun salwanta, saboda idan aka yi la’akari da sa lallen amarya a wannan lokaci, wai sai ka ga amarya Bahaushiyar asali uwa da uba ana shafa mata nonon shanu, ko kuma a fesa mata turare a matsayin sa lallen da ake yi wa amarya. Saboda yanzu wasu Hausawa na ganin ma wai shafa wa amarya lalle ƙauyanci ne. Daga ƙarshe ina kira ga malamanmu musamman masana al’adu, da su ƙara tashi tsaye wajen jawo hankalin al’ummar Hausawa a kan muhimmancin al’adunsu da kuma hanyoyin da za a bi domin farfaɗo da su, sannan kuma da hanyoyin rayasu.

Manzarta


Post a Comment

0 Comments