Yanayin
da zuciya take ciki ko kamar yadda Hausawa kan ce; Labarin zuciya, shi ne ake
kira Haliyya. Haliyoyin zuciya kuwa suna da yawa. Akwai fara’a, bacin rai, fushi,
bakin ciki, murna, nadama, da-na-sani, bege, kauna, kiyayya, da dai sauransu. Dan
haka idan aka ce salon tsattsafin haliyya a na nufin barbada daya ko fiye daga wadannan
haliyoyi cikin waka.
Tsattsafin
Haliyya: Nazari Daga Amon Aminu Ladan Abubakar
Na
Musa Suleiman Kofar Mazugal
08061256096
DAGA
KEBANTACCIYAR CIBIYAR NAZARIN
WAKOKIN AMINU LADAN ABUBAKAR ALAN WAKA
GABATARWA
Salo a fagen adabi ba fage ne da ya shafi waka
kurum ba. Wani makeken kogi ne wanda duk inda mutum ya kai ga iya ruwa ko iyo
ba zai iya kure shi ba. Yana da kyau ga mai nazarin waka ya kalli salailainta
da dama da ke cikinta, ba wasu kebantattu bad a aka sani yau da gobe ba. Domin
a fage na nazarin salo kullum sai ido ya kai ga wasu sababbin salailai da ba a
san su ba. A takaice dai, wannan wannan makala zata mai da hankali ne akan
salon tattsafin haliyya da amon Aminu Abubakar Ladan Alan Waka. Wannan salon na
tsattsafi ya fito ne daga wani nazari da shehin malamin mu Ferfesa Abdullahi
Bayero Yahya ya gudanar mai taken “TSATTSAFI:Wani Digo Cikin Gulbin Nazarin
Salon Wakokin Hausa”.
SALON
TSATTSAFI
Salon
tsattsafi salo ne da ke nufin kawo kumshiyar tunani ko cusa wata haliyya a
wurare daban daban cikin waka. Ko kuma amfani da wani salo a kai akai (wato a
yayyafa ko barbada) cikin waka ko kuma mafi yawan wakokin marubuci idan gaba
dayansu ne ake nazari. Tsattsafi a waka haka yake kamar kyallin taurari cikin
sararin samaniya ko diyan rana (kawalwalniya) cikin yashi ko kuma kyallin
kwalli wanda ya barbada akan dabe. (A. B. Yahaya, 2013).
Ta la’akari da wannan ma’anar da aka bayyana
za a fahimci cewa Salon tsattsafi yana da rassa da dama wadanda suka hada da
tsattsafin haliyya da na harshe da kuma na al’ada da dai sauransu da dama. Suma
wadannan rassa su na iya kasancewa da nasu rassan daban. Wato kenan idan aka
dauki wadannan rassan guda uku da aka ambata, a na iya raba su kamar haka:
SALON
TSATTSAFI
-Tsattsafin
Haliyya
-Tsattsafin
Harshe
-Tsattsafin
Al’ada
Haka kuma daga cikin wadannan rassa na salon
tsattsafi su ma akan iya karkasa su zuwa wasu kananan salailai da dama kamar
haka:
TSATTSAFIN
HALIYA
-Tsattsafin
Raha
-Tsattsafin
Bacin rai
-Tsattsafin
Fushi
-Tsattsafin
Murna
-Tsattsafin
Bege
-Tsattsafin
Tausayi
TSATTSAFIN
HARSHE
-
Tsattsafin Ingilishi
-
Tsattsafin Fulfude
-
Tsattsafin Larabci
-
Tsattsafin Kanuri
-
Tsattsafi Yaruba
-
Tsattsafin Igbo
Da dai
sauran harsuna da dama.
TSATTSAFIN AL’ADA
-Tsattsafi Fada
-Tsattsafin Noma
-Tsattsafin Dambe
-Tsattsafin Wasanni
Da dai
sauransu da dama.
Kamar yadda aka bayyana a baya wannan makala za
ta fi maid a hankali ne akan tsattsafin haliyya musamman ma a cikin wakokin
Aminu Abubakar Ladan Alan Waka.
TSATTSAFIN HALIYYA
Yanayin da zuciya take ciki ko kamar yadda
Hausawa kan ce; Labarin zuciya, shi ne ake kira Haliyya. Haliyoyin zuciya kuwa
suna da yawa. Akwai fara’a, bacin rai, fushi, bakin ciki, murna, nadama, da-na-sani,
bege, kauna, kiyayya, da dai sauransu. Dan haka idan aka ce salon tsattsafin
haliyya a na nufin barbada daya ko fiye daga wadannan haliyoyi cikin waka. Wato
kenan ga misali muna iya cewa salon tsattsafin raha ko fishi ko bege.
Fahimtar cewa akwai salon tsattsafin haliyya ya
dogara ne a mafi yawan lokacinkan alakar zuciya da kalmomin waka. Zuciyar
mawaki ko ta manazarci ita ce za ta ji ko ta dandani ko ta ga ta jinjina kalma
ko kalmomi masu haliyya cikinsu. A wani lokaci kuma mawaki kan yi amfani da
salailai domin ya cusa haliyyar cikin wakokinsa. Misali, yana iya amfani da
kalmomi masu kaifin ma’ana domin yin haka, kamar yadda Sambo Waliyyi Gidadawa
ya yi amfani da kalmomin “injoyin” da “yo-ni-kai-na” domin ya cusa haliyyar
nishadi da raha a inda yake gargadin ‘yan matan zamani da ke jinkirta yin aure
da wuri da hujjar cewa wai sai suna son shakatawa ne tukunna;Inda yake cewa:
“ Iliminki babu amre sharri na,
Shaidan ka dunguza ki cikin barna,
Ki yo ta baki dubin aibi na,
Kullun fadi ki kai injoyin na. ’’
‘’Sai radda kig ga kin rasa mai sanki,
Duw wanda kin nuhwa bai dubinki,
Mai son dauri ya bar shawarki,
Sannan ki sa kira yo ni kai na. ’’
(Sambo
Waliyyi Gidadawa:Wakar Amre).
Idan mu ka kalli wakar zuciya ta Aminu Ala ya
bayyana haliyyar zuciya a cikinta. Inda ya bayyana haliyoyin da zuciyarsa ta ke
kullawa. Amma dai bari mu ji daga bakinsa:
‘’In
na shi zan je birget sai ta mai da ni Tarauni,
In na durkusa nai zaune yanzu ka ga ta tada ni,
In na yunkura na mike take ka gata zaune ni,
Nai gabas a na madalla baya za ta zo maida ni,
Na yunkura hannun dama sai dawayar ni hauni,
Bari zuciya bar ja na kar ki mai da ni
majanuni. ’’
(Aminu
Ala:wakar zuciya)
Idan aka
kalli wadannan baituka za a ga cewa Aminu Ala ya bayyana irin haliyoyin da
zuciyarsa ke kulla masa, wanda idan ya yi niyyar shuka abin alkhairi sai ta so
ta cusa masa akasin haka.
TSATTSAFIN RAHA:Salo ne da mawaki ke nuna farin
cikinsa da nishadi a cikin wakokinsa. A nan mawaki yak an bayyana haliyoyin raha
da amfani da kalmomin na haliyoyin raha ya yi tsattsafinsu a cikin baitukan wakarsa.
Aminu Ala ya yiamfani da wannan salo a cikin wakarsa ta “Dan Birni”. Inda ya yi
tsattsafin raha cikin wasu baitukan wakar. Ida yake cewa:
-Ni
ma da lafiya na ka waka har na yi ‘yar rawa nai tsalle
-Kuma
ku rausaya fa ku risa in kun ga sarari kui tsalle,
-Mata
a rausaya fa a risa in an ga sarari ai tsalle.
(Aminu
Ala:Wakar Dan Birni).
TSATTSAFIN BACIN RAI:Salo ne da mawaki ke amfani
da shi inda zai nuna irin haliyyar da zuciyarsa ta shiga a yayin da yake cikin
bacin rai. Wannan ne yasa idan ya yi da waka a irin wannan yanayi dole sai ya
yi tsattsafi na haliypyin bacin rai a cikin baitukan wakarsa. Aminu Ala ya nuna
irin wannan haliyoyi a cikin wakarsa ta ‘’Wayyo kaico’’. Inda ya nuna bacin
ransa ta hanyar yin zambo a cikin baitukan wakarsa. Idan yake cewa:
‘’Wai gyartai ka baiwa kirar mota,
Mai kira ka bas hi sakar mata,
Ya zama ‘yar burum-burum dan wauta,
An yi fagabniya ya mai tatata waayyo kaico. ’’
(Aminu
Ala:Wakar wayyo kaico).
Ba a yi
wannan ya nuna haliyyar bacin rai ba. Idan ka dubi wakar “Garin Gumel”. Za a ga
yadda ya nuna mutukar bacin ransa. Bari mu ji daga bakinsa:
“Bana
an yi gumi nai sharkafya jika ni,
Na taho nai murna gun sarkinmu sani,
Mahara mafasa kwauri kawai suka hana ni,
Sai na dawo gida bacin rai ya kume ni. ”
(Aminu
Ala:wakar Garin Gumel).
TSATTSAFIN
TAUSAYI:Salo ne da mawaki ke amfani da shi domin ya nuna haliyyar tausayi, wanda
zuciyarsa ta tsinci kanta a ciki. Irin wannan haliyoyi su ne makaman da za su
nuna wa mai sauraro ko mai nazari irin tausayawar da mawaki ya yi da kuma
yanayin da zuciyarsa ta shiga ciki. Aminu Ala ya yi amfani da irin wannan salon
a cikin wakar “Marainiya”, amma bari mu ji da bakinsa:
Abin ban tausai gidan marayun yara,
Abin ai kaico hawaye su ta darara,
Abin su marayu dagwai-dagwai ‘yan yara,
Wasu hadarin mota akai suka zamo maraya,
Wasu ko tsinto ake a cikin shara,
Wasu masu tabin hankali ka Haifa yara,
Sababi na hadakarsu ba shi kirgo yara,
Wasu ‘yan jarira akan gadonsu na yara,
Wasu na tatata da rarrafe ‘yan yara,
Wasu na makarantar karatun ta mora,
Wasu an kakkai su sakandare da kara,
Ba uwa babu uba hadin gamayyar yara,
Ga gida daya amma kamarsu bamban yara,
Wani na zaluntar na kas da shi dan kwara,
Wani jarumta wani shagwaba ‘yan yara,
Wani ba koshin lafiya cikin ‘yan yara,
Wasu ko koshi lafiya kamar tantabara,
Abinci idan za a as u tamkar fara,
Jerin gwano suke kamar masu bara,
Gidansu matsattse sai ka ce tantabara,
Gidansu guda daya jal ku je kui duba
TSATTSAFIN
FUSHI:Shi ne salon da mawaki ke fitar da haliyoyin zuciyarsa ta hanyar amfani
dad a haliyoyin fushi ko wasu mizanai da ke iya nuna fushi a yayin gudanar da
waka. Aminu Ala ya yi amfani da iri wannan salon a cikin wakarsa ta “Garin
Gumel”. Inda yake cewa:
“Bana na ga daren kure nab a da baya,
Sukuwa da makahon doki na kidaya,
A bikin sallar gani na hangi
shirinya,
Ba na ga abin al’ajabi ya suke ni. ”
Ba a iya nan ya tsaya bay a kara da
cewa;
“Taro irin na gani tushensa maulidi
ne,
Taro irin na gani tushensa al’ada ne,
Taro irin na gani tushensa zumunci ne,
Mahara mafasa kwauri kawai suka hana ni.
(Aminu Ala:Wakar Gari Gumel),
TSATTSAFIN
MURNA:Shi ma yana daya daga cikin rassan tsattsafin haliyya, inda akan samu
mawaki dauke da murna da farin ciki wanda hakan ne zai sa sai ya gudanar da
wakarsa a cikin wannan yanayin na murna da farin ciki. To a nan dole za a samu
ya yi yayyafi ko barbada tsattsafin haliyya na murna da farin ciki ta hanyar
amfani dad a wasu mizanai da za su nuna irin farin cikin da yake ciki.
Aminu Ala ya yi amfani da irin wannan salo a
cikin wasu baituka a wakarsa ta “Komai ya yi kyau”wadda ya yi wa mai martaba
sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero. Inda yake cewa:
‘’Lale lale duk jama’ar kano suna ma
lale da alfahharo,
Ran sauka ‘yan tahafizu na oyoyo gad an Bayero,
Gatan kumbo ka dawo gare sai madalla
mui ayyiraro,
Matan birni sai guda suke suna yin
nishi sana ta asayyaro,
Tamkar baba in na rufe ido na na bude Ado
Bayero. ”
Ba a iya nan ba, ya bayyana farin
cikinsa inda yake cewa:
“Birni kauye sai guda ake a na ga
Ado sak dan Bayero,
Har kaikawon nan fa da kas sani ga fararen
kaya jikan Bayero,
Na tsinkaya na a za mai kano ne ashe mai Bichi
ne Dan Bayero,
Sai nag a kwalla na ta ciko ido tunani na can
baya ya warwaro,
Kan takawa marigayi mai kano madubin milki ba
siddadaro”.
TSATTSAFIN
BEGE:Shi ma yana daya daga cikin rassan tsattsafin haliyya wanda mawaki ke yin
begen abin day a ke so, yak e kauna. A nan mawaki kan yi amfani da haliyoyin
kauna domin ya bayyana irin son abin da yake bege ta hanyar amfani da mizanan
haliyoyin bege.
Aminu
Ala ya yi amfani da irin wannan salo a cikin wakarsa ta “Miftahul-futuhati”inda
ya kira ma’aiki da “Linzamin rayawarsa” Saboda tsananin so da kaunarsa wanda
haka ya nuna mana cewa shi ne ya juya duk wasu al’amura na rayuwarsa. Da jin
irin wannan kalamai na Aminu Ala ka san so da kauna c eta sa shi ya yi haka. Amma
bari mu ji daga bakinsa:
Na yunkura in yi yabon masoyi,
Annabi ne babban masoyi.
Mai darajar da ta zarce shayi,
Mai hali na yabo da koyi.
Mai nasaba ciki babu shayi,
Rabbu hane ni ni da in yi sanyi.
Kan lamarin da na tsara zan yi,
In yabi Annabi babu shayi.
Babu kure ciki ba bulayi,
Sai madarar kaunar masoyi.
In fadi tarihin masoyi,
Kuj ji busharorin masoyi.
Babu kasala babu sanyi,
Ba nukusani babu shayi.
Ku ji abin da yahudu kan yi,
Daga busharorin masoyi.
Duk a cikin wakar da zan yi,
Nutso a cikin bahari f azan yi.
Hujjoji na zuwan masoyi,
Har ahlil kitabi sun yi.
(Aminu
Ala:Wakar Miftahul-futuhati).
KAMMALAWA
A
wannan fage za a ga cewa wannan makala ta yi cikakken bayani ne akan haliyoyin
zuciya. Wanda ta dauki bangare daya daga cikin manyan rassa na salon tsattsafi wato
salon tsattsafi na haliyya ta yi daka har ma da tankada. Inda ta kalli
tsattsafin haliyya da rassansa da dama ta fito da irin hikimomin da ke salailan
musamman a cikin wakokin Aminu Ladan Abubakar (Alan Waka). Wanda shi ma yak an
yi amfani da irin wadannan salailai da dama a cikin wakokinsa.
MANAZARTA
Dangambo, A (2007) Daurayar Gadon
Fede Waka, Kano:Amana publishers.
Magaji, B. (2009) “Nazarin aron
Kalmomi a Wakokin Muhammadu Sambo Wali Gidadawa”, Kundin Digiri na farko, Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Muhammad, D. (1980) “Waka
Bahaushiya” Cikin studies in Hausa Language, Literature and culture. Kano:Bayero
University.
Muhammad, D. (1980)”Zumunta tsakanin
marubuta wakokin Hausa da makada”cikin Harsunan Nijeriya na 4, kano:Bayero
University.
Yahya, A. B. (1988) “Hikima A Cikin
Wakokin Hausa”Sakkwato:Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Yahya, A. B. (1997) “Jigon Nazarin
Waka”, Kaduna, Fisbas Media service.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.