A’ISHA ADAMU
ZALIHA MUHAMMAD GAMBO
KUNDIN BINCIKE WANDA AKA GABATAR A SAHEN HAUSA NA TSANGAYAR HARSUNA A KWALEGIN ILMI DA K’ERE-K’ERE TA GARIN GUSAU, JIHAR ZAMFARA
Sadaukarwa
Mun sadaukar da wannan bincike ga iyayenmu bisa ga kyakkyawar tarbiya da suka ba mu tun daga farkon rayuwa zuwa yau. Haka kuma mun sadaukar da wannan aiki ga iyayenmu mata da kuma mazanmu da duk wani wanda yake sha’awar wannan sashe na Hausa.
Jinjina
Muna masu jinjinawa babban malaminmu kuma jagoran wannan bincike wanda ya kula da mu wato malam Ibrahim Ahmad ‘Dan’amarya na tsangayar harsuna sashen Hausa. Saboda nuna k’wazonsa wajen duba wannan kundi tare da mayar da hankalinsa wajen wannan aiki tun farkon lokacin da aka fara har Allah ya kawo mu a wannan lokaci. Allah ya saka masa da mafificin alheri. Amin.
Godiya.
Muna godiya ga tabbataccen Sarkin wanda bai haifa ba, ba a haife Shi ba. Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittu annabi Muhammad (SAW).
Haka kuma muna mik’a kyakkyawar godiyarmu zuwa ga iyayenmu, mazanmu da sauran ‘yan’uwanmu da suka taimaka a cikin wannan karatu namu, don bamu tarbiyya da suka yi tun tasowarmu har zuwa yau da kuma ba mu gudunmuwa da suka yi wajen ci gaba da karatunmu.
Haka kuma muna mik’a kyakkyawar godiyarmu zuwa ga mal. Dr. Haruna Umar Bungud’u( H.O.D) na sashen Hausa a Tsangayar Harsuna Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau Jihar Zamfara, kuma muna mik’a godiyarmu ga dukkan malaman wannan sashe, mun gode ga baki d’aya Allah ya bar zumunci ya sa ma karatun da muka yi albarka ya sa abin da za mu taimaki wannan jiha da k’asa baki d’aya.
K’umshiya
- Shedantarwa - - - - - - ii
- Sadaukarwa - - - - - - iii
- Jinjina - - - - - - - iv
- Godiya - - - - - - - v
- K’umshiya - - - - - - vi
- Babi Na ‘Daya
1.0. Gabatarwa - - - - - - - - 1
1.0.1 Manufar Bincike - - - - - - - 2
1.0.2 Muhallin Bincike - - - - - - - 3
1.0.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike - - - - - 3
1.0.4 Matsalolin Da Suka Taso - - - - - 4
1.0.5 Matsalolin Da Aka Fuskanta - - - - 5
2.0 Babi Na Biyu
2.0.1 Waiwaye (Ayyukan Da suka Gabata) - - - - 8
2.0.2 Salo, Zubi Da Tsarin Bincike - - - - - 13
3.0 Babi Na Uku
3.0.1 Ma’anar wak’a - - - - - - 15
3.0.2 Samuwar Wak’ok’in Gargajiya - - - - 16
3.0.3 Rabe-Raben Wak’ok’in Gargajiya - - - - 20
3.0.3.1 Wak’ok’in Yara maza - - - - - 20
3.0.3.2 Wak’ok’in Yara Mata - - - - - 21
3.0.3.3 Wak’ok’in Tashe - - - - - - 22
3.0.3.4 Wak’ok’in Daka - - - - - - 23
3.0.3.5 Wak’ok’in Raino - - - - - - 25
3.0.3.6 Wak’ok’in Da’be - - - - - - 26
3.0.3.7 Wak’ok’in Nik’a - - - - - - 27
3.0.3.8 Wak’ok’in Fada - - - - - - 29
3.0.4 Samuwar Wak’ok’in Zamani - - - - 30
3.0.5 Rabe-Raben Wak’ok’in Zamani - - - - 33
3.0.5.1 Gwauruwa/Mai K’war ‘Daya - - - - 33
3.0.5.2 ‘Yar Tagwai/Mai K’war Biyu - - - - 34
3.0.5.3 Wak’a Mai K’war Uku - - - - - 35
3.0.5.4 Wak’a Mai K’war Hud’u - - - - - 35
3.0.5.5 Wak’a Mai K’war Biyar/Muhammasa - - - 36
3.0.5.6 Tarbi’i - - - - - - - 36
3.0.5.7 Tahamisi - - - - - - - 37
3.0.6 Amfani Da Muhimmancin Wak’a - - - 37
Babi Na Hud’u
4.0.1 Mawak’an gargajiya - - - - - - 40
4.0.2 Marubuta Wak’ok’in Zamani - - - - 41
4.0.3 Mawak’an Zamani Wad’anda Suke had’awa da Kid’a - 43
4.0.4 Dangantakar Wak’ok’in gargajiya Da na Zamani - 44
4.0.5 Kamancin wak’ok’in gargajiya Da Na Zamani - - 45
4.0.6 Bambancin Wak’ok’in Gargajiya Da Na Zamani - 46
Babi Na Biyar
5.01 Jawabin Kammalawa - - - - - 48
5.0.2 Shawarwari - - - - - - - 50
Manazarta - - - - - - - - 51
Babi Na ‘Daya
1.0.1. Gabatarwa
Kamar dai yadda aka sani cewa duk wanda ya kammala wannan karatu ya zama wajibi ya gudanar da wani bincike da zai cika wani ‘bangare daga cikin sharud’d’an wannan makaranta. Haka muma ya zama wajibi da mu gudanar da binciken kamar yadda hukumar makaranta ta tanada muna, yin hakan zai taimaka wajen kar’bar takardarmu ta shedar kammala karatu a wannan Kwalejin.
Domin samun damar gudanar da wannan aikin mun karkasa wannan kundin kamar yadda hukumar makaranta ta tanada wato bisa ga tsari na babi-babi, yayin da muka fito da babi biyar.
A babi na farko dai za mu kawo bayanai ne bayan mun yi gabatarwa ta gaba d’aya sai mu kawoYanayin Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar da Bincike tare da Matsalolin da Suka Taso da kuma Matsalolin da Aka Fuskanta,
Yayin da a babi na biyu kuwa, kamar yadda aka saba za mu waiwayi baya don ganin ayyukan magabata tare da yin tsokaci a kan wad’anda suka samu. Salo da zubi da tsarin wannan bincike zai biyo baya duk a cikin wannan babin.
Babi na uku kuwa, zai k’unshi bayanai a kan samuwar wak’ok’in gargajiya da rabe-raben wak’ok’in gargajiya da muhimmanci wak’ok’in gargajiya da da samuwar wak’ok’in zamani da rabe-raben wak’ok’in zamani da muhimmancin wak’ok’in zamani.
Shi kuma babi na hud’u, zai k’unshi dangantakar wak’ok’in gargajiya da na zamani, kamancinsu da kuma bambancin da ke tsakaninsu, kamar ta fuskar jigo da zubi da tsari da salo da haka kuma za mu yi tsokaci a kan mawak’an gargajiya da mawak’an zamani.
Babi na biyar kamar yadda aka sani a nan ne za mu kammala wannan bincike ta hanyar yin jawabin kammalawa da shawarwari.
1.0.2. Yanayin Bincike
Wannan aikin yana da zimmar yi wa wak’ok’in gargajiya da na zamani nazarin k’wak’waf domin fito da wasu muhimman abubuwa da wak’ok’in suka k’unsa, wad’anda ba kasafai mutum zai yi farat ya fito ya ce ga su ba.
Haka kuma aikin namu yana da manufar zak’ulo wasu bayanai sahihai dangane da su wak’ok’in kansu da kuma irin bambanci da ke tsakaninsu
1.0.3. Muhallin Bincike
Wannan aikin za a gudanar da shi a kanadabi wanda ya k’unshi adabin gargajiya da na zamani na Hausa. Sannan kuma a tak’aita shi a kan wak’ok’i na gargajiya da na zamani ba tare da zube ko wasan kwaikwayo ba. Saboda haka muhallin wannan bincike namu zai ke’banta ne kawai a kan wak’ok’in gargajiya da na zamani na Hausa.
1.0.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike.
Domin samun nasarar gudanar da wannan aiki namu cikin sauk’i za mu bi hanyoyi da dama da suka had’a da:
Karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da muk’alu da Mujallu domin zak’ulo wasu bayanai masu nasaba da aikinmu. Mun kai ziyara a d’akunan karatu da suka had’a da nan cikin makarantarmu wato Kwalejin Ilimi da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya da ke Garin Gusau, (FCET) Gusau, da Kwalejin Fasaha da Kimiyya (ZACAS) Gusau, da Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara da ke Maru (C.O.E.) Maru, da sauransu domin tattara bayanai masu nasaba da aikinmu.
Haka kuma mun yi amfani da tuntu’bar malamai masana da manazarta wak’ok’in Hausa. Har ila wa yau za mu shiga kasuwanni wajen masu sayar da kaset-kaset na wak’ok’in domin k’arin haske ga wannan aiki da muke gabatarwa.
1.05. Matsalolin Da Suka Taso.
A wannan bincike mun fahimci cewa akwai wani gi’bi da aka manta ba a cika ba a cikin fannonin da ake bincike a kansu duk da cewa an yi ayyuka da dama ko da yake a iya binciken da muka sami ba mu ci karu da wani mai kama da wannan ba. Ba zai yiwu mu ce ba a ta’ba yi ba amma saboda ba mu gani ba ya sa muke ganin cewa an manta da wannan ‘bangare. A al’ada akwai abubuwa da yawa wad’anda suka shafi al’amurran jama’a na wannan zamani amma sai aka yi fatali da su ba wanda ya kula. Tuni wasu mashahuran malamai suka yi iya k’ok’arin su don ganin cewa sun samar wa jama’a abin karatu da kuma abinda za su nazarta. Wannan ya nuna kenan har ko yaushe ba a rasa wasu da suka yi k’ok’ari wajen samar da abin da za a iya dogaro da shi na abin da ake nazari.
Saboda a namu gani wannan fanni da muka d’auka, na nazarin bambancin da ke akwai a tsakanin wak’ok’in gargajiya da na zamani ba a yi wani aiki mai yawa ba a wannan fanni. Wannan na d’aya daga cikin manyan dalilan da suka ja hankalinmu muka fantsama cikin yin nazari a kan wannan fanni.
Wasu da suka taso a wannan lokaci ba su san, wak’a tana da matuk’ar rawar da take takawa ba wajen jan hankalin mai sauararo ba. Haka kuma ba su iya bambance tsakanin ‘bangarorin biyu.
1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta
Kamar yadda ma’anar ke nuni “matsala” na nufin irin cikas d’in da aka ci karo da shi a yayin da ake gudan da wannan bincike. A duk lokacin da mutun ya samu kansa a cikin irin wannan aiki na bincike to lallai wajibi ne ya ci karo da wasu matsaloli da za su iya kawo tarnak’i ga aikinsa na bincike kafin ya kai ga cin nasara. A lokacin gudanar da wannan kundi muna samun barazana ta wasu matsaloli da suka had’a da:
Matsalar littafan karatu. Wannan matsala matsala ce babba saboda wannan makaranta ba ta da isassun littafai da za mu duba, wannan wa ya sa sai da muka lek’a wasu makarantu don samun wasu bayanai da za su taimaka mu gina namu kundin. Wannan walaha ta ziyarce-ziyarcen wasu makarantu ta kawo muna tafiyar hawainiya ga gudanar da wannan bincike.
Matsalar kud’i: wannan matsala tana d’aya daga cikin manyan matsaloli da suke tauye komai da ake yunk’urin yi har dai in ya zama abu ne mai buk’atar a inganta shi. Matsalar kud’i babbar matsala ce har dai garemu mata da yake d’auke ake da nauyinmu kuma ba kasafai za mu nemi a bamu kud’i a gidajenmu a bamu ba sai an samo kuma sai an gani in babu wani abu da ya fi buk’atarmu muhimmanci sannan a bamu, idan kuwa aka samu wani abu da ya fi tamu buk’atar muhimmanci to, lallai mu ba zamu samu ba sai har an samu wasu gaba sannan wata kila mu samu. Rashin kud’in dai ya kawo muna matsala, amma yanzu mun shawo kan matsalar.
Matsalar wutar lantarki: wannan matsala ta taka rawa sosai wajen yi wa wannan aiki namu tarnak’i wato matsalar ta kawo tafiyar hawainiya wajen gudanar da wannan binciken. Ana kuma iya gane cewa wannan zancen namu na matsalar wutar lantarki gaskiya ne idan aka dubi yanayin garin na Gusau za a ga cewa babu isasshiyar wutar lantarki wadda da ita ne kawai za a iya buga muna rubutunmu a cikin Kwamfuta (Computer). Wannan ya sa muka saka wannan matsala ta rashin wuta a cikin matsalolin da suka taso suka dabaibaye gudanar wannan kundi.
Babi na Biyu
2.01. Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.
Kamar yadda muka riga muka sani cewa waiwaye shi ne adon tafiya, to ko a wannan aiki waiwayen zai taimaka muna, don haka za mu waiwayi baya mu ga irin ayyukan da suka gabata wad’anda suke da dangantaka da namu aikin..
Domin yi wa aikin mu kwalliya za mu binciki littattafai da kundaye da muk’alu da dai sauran wasu ayyuka da suka shafi namu.
Gusau S.M (1996), a wani littafinsa mai suna “Makad’a da Mawak’an Hausa” a wannan karon masanin ya zuba littafansa ne a tsarin kashi-kashi kamar haka: Kashi na d’aya ya kawo makad’an yak’i, a kashi na biyu kuma ya kawo makad’an sarakuna rukuni na I, a kashi na uku kuwa ya kawo makad’an sarakuna runi na II. Kashi na hud’u makad’an jama’a kashi na biyar kuma makad’an sana’a, daga nan sai ya kammala.
Wannan kundin yana da alak’a da namu aikin yayin da shi Gusau ya kalli wak’ok’in ya karkasa su, mu kuma muka d’auki wasu wak’ok’i mun nazarce su domin ganin irin bambancin da ke tsakanin wak’ok’in.
Gusau S.M (2008), a wani littafi nasa mai suna “Wak’ok’in Baka A K’asar Hausa, Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu” har wa yau dai masanin ya zuba littafinsa a tsarin babi-babi, inda a babi na d’aya ya kawo tarihin k’asar Hausa da yanaye-yanayenta, a babi na biyu kuwa ya kawo kid’a da kayan yinsa. Sai a babi na uku inda ya kawo makad’an baka na Hausa. A babi na hud’u kuwa ya kawo halayya da nau’o’in wak’ok’in baka, daga nan dai sai ya shiga babin kammalawa inda ya gudanar da jawabinsa na kammalawa.
Wannan littafi yana da rawar da zai taka matuk’a wajen gudanar da namu aikin domin kuwa ya nazarci wasu wak’ok’i kuma mun ga yadda ake nazarin wak’a. Don haka za mu bi wannan salo da ya yi amfani da shi mu tsara namu kundin a kan wak’ok’in gargajiya da na zamani don mu ga yadda bambanci ya ke tsakanin wak’ok’in wato na gargajiya da na zamani.
Shi kuwa Mustapha Abba da Balarabe Zulyadaini (2000) a cikin wani aiki da suka yi mai suna “Nazari Kan Wak’ar Baka Ta Hausa” wad’annan masana sun gudanar da aikinsu ne a kan tsarin na babi-babi, inda suka kawo tarihin samuwar wak’ar baka a k’asar Hausa da rabe-raben makad’an baka a k’asar Hausa, dangane da rukunoninsu da jigogin wak’ok’in baka na Hausa.
Wad’annan masana sun gudanar da aikin su a fannin adabin baka kuma wak’a mu kuma daman aikin da muke da k’uduri an adabi ne sai dai yana da bambanci saboda namu aikin akwai wak’ok’in zamani a ciki. Wannan ya nuna cewa aikinmu yana da alak’a da nasu, sai dai su suna kallon dukkannin makad’a na k’asar Hausa ne yayin da mu mawak’an ba na baka kawai muke kallo ba har da na zamani.
Sar’bi (2007), ya rubuta littafi mai suna “Nazarin Wak’ar Hausa” wannan marubuci ya rubuta littafin ne domin masu nazarin wak’ok’in Hausa musamman rubutattu. A cikin wannan littafi nasa ya yi magana a kan jigo, salo zubi da tsari, nau’o’in rubutacciyar wak’a da dai sauransu.
Wannan aiki na Sar’bi yana da alak’a da namu aikin saboda ya yitsokaci a kan wak’ar zamani yayin da muma namu aikin yana magana a kan wak’ok’in zamani. Inda kuma muka sha bamban da shi shi ne, shi Sar’bi wak’ok’in zamani kawai ya mayar da hankali, bai ce komai ba game da wak’ok’in gargajiya.
Bunza (2009), ya rubuta wani littafi mai suna “Narambad’a” wannan littafi da wannan masani Al’dar Hausa ya rubuta littafi ne wanda ya tsara shi bisa ga tsari na babi-babi har babi goma sha biyu. A babi na d’aya masanin ya kawo jigogin wak’ok’in Narambad’a, a k’ark’ashi wannan babin ya fara da gabatarwa da da asalin kalmar jogo da rabe-raben jigo da babban jigo da k’aramin jigo da yadda ake neman sarauta da yadda sarauta take da nad’in sarauta.
A cikin babi na biyu akwai masarauta da a wak’ok’in Narambad’a, a babi na uku ya kawo sarki a wak’ok’in Narambad’a, a babin na hud’u ya kawo fada a wak’ok’in Narambad’a, a babi na biyar kuwa ya kawo k’ananan jigogin wak’ok’in Sarauta. A babi da shidda akwai ke’ba’b’bun k’ananan jigogin sarauta, a babi na bakwai nan ne ya kawo salon wak’ok’in Ibrahim Narambad’a, a babi na takwas ya ba da falsafar wak’ok’in Ibrahim Narambad’a, a babi na tara ya zo da Tussan wak’ok’in Narambad’a, a babi na goma ya yi bayanin fashin bak’in Bakamdamiya, a babi na gaba sai ya rufe da kammalawa.
Wannan littafi da wannan masani ya rubuta ya haskaka muna sosai wajen samu dubarar da za mu gina namu aikin ya k’ayatar. Alak’arsa da namu aikin ita ce, shi yana kallon wak’ok’in Narambad’a kuma yana nazarinsu mu kuma muna nazarin wak’ok’in ne gaba d’aya wato na gargajiya da na zamani. Haka kuma Bunza bai ce komai ba game da bambanci da ke tsakanin wak’ar baka da ta zamani.
Gatari (2010), a kundinsa na kammala digiri na d’aya da ya rubuta mai taken “Jigon yabo a wak’ok’in Mahammadu Shata” wannan d’alibi ya kasa aikinsa zuwa babi biyar, a babi na d’aya ya yi gabatarwa ta aikinsa a babi na biyu ya kawo tak’aitaccen tarihin Muhammadu Shata, ya kayan aikinsa da yawace-yawacensa. A babi na uku ya kawo ma’anar jogo da ire-iren jogo, ya kuma kawo jigon yabo a wak’ok’in na Muhammadu Shata, manazarcin ya kawo yabo da asali, yabo kan addini, sannan da jigon zuga. A babi na hud’u ya kawo ire-iren yabo inda ya kawo yabo da kyauta, yabo da jarunta, da dai sauransu. A babi na biyar kuwa a nan ne ya kammala aikinsa ya zuba manazarta tare da ratayen wak’ok’in da ya yi aiki a kansu.
Wannan kundin yana da alak’a da namu aikin saboda dukansu suna nazarin wak’ok’i ne, sai da inda muka bambanta da shi shi yana kallon yabo a cikin wak’ar baka ne na Mamman Shata mu kuma muna nazarin kamanci da bambancin da ke akwai a tsakanin wak’ok’in gargajiya da na zamani.
2.0.2 Salon Nazari Da zubi Da Tsarinsa.
Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin mutum. Salo muhimmin abu ne a cikin labari ko jawabi, haka kuma duk aikin da aka gudanar ba cikin tsari ba to, ba zai cimma nasara ba. Don haka domin samun nasarar gudanar da wannan aikin cikin sauk’i, mun yi amfani da salo mai sauk’i, mai jan hankalin mai karatu. Mun kuma yi amfani da za’ba’b’bun kalmomi masu sauk’in ma’ana saboda mai karatu ya ji sauk’in karantawa.
Haka kuma mun yi amfani da gajeru da matsakaitan jimloli, sannan muka gudanar da bayananmu d’aya bayan d’aya a cikin sakin layi mai sauk’in fahimta.
Aikin kamar yadda aka sani mun zuba shi ne a kan babi-babi har zuwa babi biyar saboda mu samar wa mai karatu sauk’i wajen nazari.
Babi Na Uku.
3.0.1 Ma’anar Wak’a
Masana da yawa sun ba da gudunmuwa wajen samar da ma’anar wak’a,. Ga wasu daga cikinsu:
Yahya ya ba da tasa ma’anar wak’a da cewa:
“Magana ce da ake shisshirya kalmominta cikin azanci, ta yadda wajen furta su ana iya amfani da kayan kid’a”. Yahya (1997).
Shi kuma ‘Dangambo (2007:) cewa ya yi:
“Muna iya cewa, wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti, d’ango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (k’afiya), da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.
A wani aikin kuma Gusau cewa ya yi:
“Wak’ar baka fage ce wadda ake shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre, wad’anda za su zaburar da al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwa da za su ba da damar a cim ma ganga mai inganci. Wak’a bisa jimla, takan zama fitila wadda take haskaka rayuwar jama’a kuma take kare rayuwar al’umma daga sallacewa” Gusau (2011).
Bungud’u (2014) kuma ya bayar da ma’anar wak’a kamar haka:
“Wak’a ta k’unshi wasu jerin hikimomi ne da a kan tsara domin su dad’ad’a zukatan masu saurare, inda a kan yi amfani da wata za’ba’b’biyar murya don rerawa, ana kuma yin amfani da za’ba’b’bun kalmomi domin fizgar hankalin jama’a ya dawo gare su da zimmar bin diddigin ma’anoni da manufofinsu.
3.0.2 Samuwar Wak’ok’in Gargajiya
Wak’ar gargajiya dai ita ce wak’ar baka. Wak’ar baka kuwa abu ce da wadda ta dad’e a k’asar Hausa tun lokaci mai nisa.
Wak’ar baka dai ta samu ne tun lokacin da d’an Adam ya fara neman abinci ta hanyar farauta. Daga nan kuma wak’ar baka ta dad’a bunk’asa a sakamakon noma da yak’e-yak’e da sana’o’i da wasanni da sauran al’adun gargajiya.
Akwai sa’banin ra’ayi dangane da samuwar wak’ar baka. Wasu daga cikin masana sun ce, “Samuwar wak’ar baka ta samo asali ne ta hanyar bauta ta gargajiya, ta dad’a bayar da haske wajen kyautata sha’anin wak’a duk daga cikin ra’ayoyin da ke bayarwa dangane da samuwar wak’ar a k’asar Hausa. Wasu kuma suna ganin cewa wak’ar ta samo asali ne daga wani marok’i (Sasana). Da wannan ne ra’ayin wasu ya karkata ga makad’an Hausa da cewa, su jikokin Sasana ne wato wancan marok’i, wanda ya rayu a ‘bangaren Asiya daga baya wasu daga cikin ‘ya’yansa suka yo k’aura zuwa k’asar Hausa. A wannan ma’anar kalmar Sasana tana nufin marok’i da harshen Faransanci. Haka kuma har wa yau wannan ra’ayi yana k’arfafa cewa, Sasana rok’o ya fara bud’e baki da shi da nufin ya yabi wani mutum ya bashi samu. Sasana shi ne marok’i na farko da aka yi tun lokacin jahiliyar duniya.
Ibrahim (1983) “Sasana” ana nufi dashi wai wani mawak’in Balaraben wata k’abila ta Madina mai suna Hassanud’an Thabitu wanda ya yi rayuwarsa tun lokacin jahiliyar Larabawa har zuwa lokacin bayyanar Annabin Muhammad (SAW). Daga nan ya musulunta ya koma yana yi wa Annabi Muhammad (SAW) wak’a har ya zama babban mawak’i. Wai jikokinsa ne suka fantsama cikin uwa duniya har suka bayyana a cikin k’asar Hausa.
Gusau (1983), wannan ra’ayi na Gusau game da wak’ar baka ya nuna cewa, “Cikin zato Hausawa sun samu wak’a ne daga tsofaffin daulolin Afirka ta Yamma, wato Ghana da Mali da Songhai. Wannan ra’ayi yana gani lokacin daular Mali akwai su da makad’an fada, kuma suna da alk’a ta kusa da makad’an Hausa musamman ma makad’an fada. Da daular Mali ta shud’e sai daular Songhai ta maye gurbinta, sai ta gaje irin wad’annan kad’e-kad’e. A lokacin mulkin sarki Askiya Muhammadu ya kwarara da rik’onsa har cikin wasu k’asashen Hausa. Saboda haka ta nan ne wasu sarakunan Hausawa suka ga tsarin makad’an suka koya.
Har ila wa yau a wannan k’auli na uku Ibrahim (1983) ya bayyana muna samuwar wak’a da cewa, “samuwar wak’ar ta samo hasken faruwa ne daga bautar iskoki ko dodanni. Hausawa a lokacin maguzanci suka yi wa iskoki ko dodanni bukin cika shekara, ko kuma idan wani abu ya faru sukan taru wajen abin bautar nan, su yi masa yanke-yanke da shaye-shaye. A wajen abin bautar nan sukan yi bukukuwa da wak’e-wak’e da zuga da kambamawa da hawar da su ta hanyar kirari ko kod’asu (take). Dangane da wannan ra’ayi ana jin ta hasken kirari da kad’a taken wad’annan iskoki ko dodanni aka samu wanzuwar wak’ar baka. Kuma ana jin daga nan ne aka samu makad’an gargajiya na ‘yan bori.
Amma duk da wad’annan ra’ayoyi da suka gabata ana kyautatazaton cewa, Hausawa sun k’agi wak’a ne ta hanyar farauta da kirare-kirarenta, daga nan kuma sai ta dad’a bunk’asa ta hanyar noma da yak’e-yak’e. Idan muka yi la’akari da wannan za mu ga cewa, wak’ar baka ta dad’e da samuwa a k’asar Hausa. Kuma tana da dad’ad’d’en tarihi wanda ba za a iya cewa ga rana ko lokacin da aka fara ta ba.
3.0.3 Rabe-Raben Wak’ok’in Gargajiya
Akwai wak’ok’i da dama da aka yi na gargajiya a wannan k’asa ta Hausa. Ga dai wasu daga cikinsu: Wak’ok’in Yara Maza, Wak’ok’in Yara Mata, Wak’ok’in Tashe, Wak’ok’in Daka, Wak’ok’in Raino, Wak’ok’in Da’be, Wak’ok’in Nik’a, Wak’ok’in Fadar Sarakuna. Domin samun warware zare da abawa za mu d’an yi tsokacinsu d’aya bayan d’aya kamar yadda za a gani.
3.0.3.1 Wak’ok’in Yara Maza
Wak’ok’in yara maza wak’ok’i ne da yara maza ke yinsu a lokacin da suke gudanar da wasanninsu na motsa jiki, da hana masu yawon banza, wak’ok’in sun k’unshi abubuwa da dama da suka had’a da: fad’akarwa, ilimantarwa, nishad’antarwa, da sauran abubuwa da suka shafi kiyon lafiya. A wak’ok’in akan samu jagora mai bayarwa da kuma yara da suke amsawa. Ga dai misalin irin wak’ar da Yara suke yi a filin wasa. A duba misali daga wak’ar “‘Dan Akuya”.
Jagoya: ‘Yan Amshi
‘Dan’akuyana Damushere ko Takushere
Ya shiga rumbu Damushere ko Takushere
Za ku kashe shi Damushere ko Takushere
Har da su adda Damushere ko Takushere
Hadda wuk’ak’e Damushere ko Takushere
Hadda takobi Damushere ko Takushere
(Gusau, 1979)
Irn wannan wak’a da yara maza ke yi tana da motsa jiki a ciki kuma sukan taru su yi da’ira su dinga yin wak’ar jujjuyawa suna rera wak’a jagora ya fad’a sauran ‘yan amshi su kar’ba.
3.0.3.2 Wak’ok’in Yara Mata
Su kuma wad’annan wak’ok’i na yara mata wak’ok’i ne wad’anda yara mata ne kad’ai suke aiwatar da su a dandali. Wad’annan wak’ok’i da yara matan ke yi kamar da na maza suma suna fad’akarwa da nishad’antarwa da ilimantarwa da motsa jiki da dai sauransu. Ga dai misalin wak’ok’in da suke yi. Ana samun jagora da take fad’a sauran yara suna amsawa. Misali “Wak’ar Badau”
Jagora: ‘Yan Amshi:
Badau Badauri Badau
‘Yar sauri ce Badau
Wanda ya fad’i Badau
Ai masa sowa Badau
Masussuki ne Badau
Ayye ta cika tumbula Badau
Ayye ta cika tumbula Badau
(Gusau, 1979)
3.0.3.3 Wak’ok’in Tashe
Wad’annan wak’ok’i yara maza na yi yara mata na yi kuma manyan mutane maza na yi lokacin azumi na Ramadana. Akan fara tashe ne idan azumi ya kai kimanin kwana goma, sannan wata ya soma fari sosai ba a k’arewa sai wata ya kai kwana ashirin. A cikin wannan lokaci ne yara da manya maza da mata sukan ‘barje guminsu su gudanar da wasu wak’e-wak’e domin samun wani abu da kuma karantarwa da nishad’antarwa da dai sauransu. Ga misalin wata wak’a da ake yi a lokacin tashe, “Wak’ar Tsoho da Gemu”:
Jagora: ‘Yan Amshi:
‘Dan tsoho da gemu Ya tsufa
A tallaba mashi Ya tsufa
A ba shi sadaka Ya tsufa
A ba shi na Allah Ya tsufa
A ba shi na annabi Ya tsufa
A taimake shi da dawa Ya tsufa
A taimake shi da gero Ya tsufa
A taimake shi da rogo Ya tsufa
(Ummar, 1980)
3.0.3.4 Wak’ok’in Daka
Wak’ok’in daka wak’ok’i ne da mata ke yin su a lokacin da ake yin daka, inda za su rik’a gwama ta’barya da turmi sai su ba da sautin da ake kira, ingude ko mama, su ko (matan) suna yin wak’ok’i. Ga dai misali daga “wak’ar mama”:
Ana lugude ana mama,
Cikin shigifa, cikin soro,
Mama ba habaici ce ba,
Salon daka ah, haka nan,
Ga maccen da ba a so ta haihu,
Ta haifi k’wandamin d’a namiji,
Shugaban daka shi ka daka,
‘yan tanyo kissa sukai,
Sukus-sukus sai su aje,
Gidan marafa kaji ka daka,
Tarmani na izon wuta,
Angulu na kir’ba dawo.
Idan muka natsu muka dubi wannan wak’ar za mu ga cewa, wak’a ce da mata suke yi a lokacin da suke yin daka, kuma wannan ya rataya ne ga mata su kad’an ba da namiji ba.
3.0.3.5 Wak’ok’in Raino
Wad’annan wak’ok’i su ma mata ne suka fi yin su a lokacin da suke raino yara k’anana, suna yi masu tawai domin su yi shiru su daina kuka, sukan yi wak’ok’in ne domin su kwantar wa yaran da hankalinsu su sanyaya masu rai. A lokacin wak’ok’in akan fad’i nasabar yaro da ayyukan da ake yi a gidansu da da yabon masoya da zambo da habaici ga magabta (in akwai su). Ga dai misalin wata wak’ar tawan Sa’idu da aka yi a shekarar (1952).
Yi shiru bari kuka Sa’idu,
Me kake wa kuka Sa’idu?
Mai kud’i, Sa’idu,
Ku taho ku gane shi,
Ku yo ziyara,
‘Dan yaro shi ya buwaya,
‘Dan yaro sai dai a bika,
Amma ba ka bi su ba,
‘Dan malamai Sa’idu,
‘Dan alk’alai Sa’idu,
Gidan ku an yi gadon karatu,
Ga kuma kud’d’i barkatai,
Kuma ga shi kun gadi hank’uri,
Kai yi shiru d’an yaro Sa’idu,
Yi shiru bari kuka Sa’idu.
3.0.3.6 Wak’ok’in Da’be
Wak’ok’in da’be su ne wad’anda manyan mata suke yi musamman a lokacin da suke yin da’be a d’akin da za a kawo wata sabuwar amarya ko sabon gida da za a shiga, ana yin wannan ne tun lokacin dauri kafin a samu wannan nau’i na da’be da ake amfani da shi a yau na siminti. A wancan lokacin idan za a yi da’be akan rera wak’ok’i da suka k’unshi, bagen wasu mutane da da zambo da habaici ga wasu mutane da ake kisantaka da su. (Kishiya), da kalmomin batsa har ma da na zage-zage da na raha da na annushuwa. Ga dai misali daga wata wak’ar da’be.
Ina lumu shege,
Mai malmala ga munta,
Kare bak’in bahwade,
Ya hana mu walawa,
Mata ku yo anniya,
Bana lumu k’wace yakai,
Ta masussuki ya biya,
Yat tada gindi, tsaye,
Wanga d’a bak’in mugu,
Ya hana mu walwala,
Kare, bak’in bahwade,
Mai malmala ga munta.
Wannan ita ce wak’ar da mata ke yi a lokacin da suke gudanar da da’be.
3.0.3.7 Wak’ok’in Nik’a
Wak’ok’in nik’a wak’ok’i ne da ake yin su a lokacin da ake yin nik’a kuma mat ne suka fi yin su. Mata sukan zuba tsaba a dutsen yin nik’a suna gurzawa har su samar da gari. Wannan dutse Hausawa suna amfani da shi tun lokaci mai tsawo kafin a samu injimin nik’a da muke amfani da shi a yau. Suna yin nik’a suna gudanar da wannan wak’e-wak’e na yabo ga wanda suke so da zambo da habaici ga wanda ake zaman d’ar-d’ar da shi, misali kamar kishiyoyi ko matan sauri da dai sauransu. Misali wak’ar “Nak’uda”:
Wayyo nak’uda ta tashi,
Ciyon nak’uda ya tashi,
Kuma ciyon nak’uda ya motsa,
Yau kan babu zaman zaure,
Wayyo inna ki ceceni,
Ciyon nak’uda ya tashi,
Da kis sha dad’in ki,
Ke tuna inna ta ceceki?
Wayyo nak’uda ‘yar ziza,
Ciyon nak’uda bori ne,
Koko nak’uda hauka ne?
Wayyo nak’uda ta tashi,
Wayyo nak’uda ta motsa.
Wannan ita ce misalin wak’ar nik’a da mata ke yi a lokacin da suke nik’an gari.
3.0.3.8 Wak’ok’in Fada
Kamar dai yadda aka sani su wad’annan makad’a ba su yi wa kowa wak’a sai jinin sarauta ko wanda yake rik’e da sarauta a lokacin da suke gudanar da wak’arsu, musamman wad’anda suke rik’e da sarautun gargajiya kamar su Sarki, hakimi , daghaci ko wani babban Bafade. Misalan irin wad’annan makad’an sun had’a da: Salihu Jan Kid’i da Ibrahim Narambad’a da Sarkin Taushin Katsina da Malam Sa’idu Faru da Alh. Musa ‘Dank’wairo da sauransu da dama.
ga dai wata wak’a ta fada a matsayin misali. Wak’ar Buda ‘Dantanoma Argungu.
Makad’i: Buda ‘Dantanoma Argungu
Ubangida: Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama
Gindin Wak’a: Gagara k’arya Sadauki
Jan gwarzon Alk’ali.
Jagora: Bahago ya biya na sha,
Y/Amshi: Bak’in dogo ba d’an yaro ba ne.
Jagora: Ba matsuwa sai tuba,
Y/Amshi: Ba sake hwad’in an yi.
Jagora: Sama ba yaro ba aboki nai,
Y/Amshi: ba warin yaro barwa
Jagora: Kanta Ubangiji Jibo as Sarki,
Y/Amshi: Ba Sarki kake ba.
Jagora: Mamman mai wada yas so,
Y/Amshi: Sarki d’ibah haushi.
Jagora: Daga illon kare-kare,
Y/Amshi: huk sun zo jid’ag gwamnan hwarko.
3.0.4 Samuwar Wak’ok’in Zamani
Wak’ok’in zamani su ne ake kira da rubutattun wak’ok’i, rubutattun wak’ok’i kuwa sun samu ne a k’asar Hausa bayan da aka samu rubutun ajami wanda ya samu daga haruffa Larabci. Tarihin samuwar ajami yana da alak’a ta k’ud-da-k’ud da zuwan addinin musulunci a k’asar Hausa. Bayan Hausawa sun samu ilimin addinin musulunci ne suka kuma ari adabin Larabawa na wak’a suka rik’a yin kwaikwayo suna gina nasu da shi. A tsarin rubutun wak’ar larabci akwai tsarin tafiyar da kari da kuma wasu k’afofi da ake gina wak’a da su wato Aruli (ma’aunin wak’a) wanda da arolin ne ake auna wak’a a kuma tsara ta bisa ga wani tsari da zai k’ara mata armashi.
Hausawa sun ari wannan ne suka kuma daidaita shi da nasu tsarin wanda zai k’ara wa tasu wak’ar dad’i, kamar dai ta Larabawa. Sun kasance masu amfani da wannan tsari ta hanyar rubutawa da ajami.
Abu ne mai wuya a iya cewa ga lokacin da aka fara rubuta wak’a da Hausa, amma kuma ana sa ran an rubuta wasu wak’ok’i tun kafin jihadin Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Dan Fodiyo. Wad’annan wak’ok’i da ake sa ran a rubuta sun had’a da wak’ar Jiddul-Azizi wadda malam Shi’itu ‘Dan Abdurra’uf ya rubuta, mai magana a kan Fik’ihu da kuma wak’ar yak’in Badar wadda Wali ‘Dan Masani ya rubuta.
Amma masana sun bayyana cewa, rubutattun wak’ok’i sun samu bunk’asa da yawa a lokacin jihadin Mujaddadi Shehu Usmanu. Haka kuma a wannan lokaci ne suka samu ingantaccen tsari (wato k’afiya). An bayyana cewa Mujaddadi ya rubuta wak’ok’i da yawa da suka kai kimanin 480, kuma daga ciki ya rubuta guda 25 da kansa 13 ukun ya rubuta su da harsunan Larabci da kuma Fulatanci 12 kuma ya rubuta su da harshen Hausa. Wad’annan ayyuka da Mujaddadi da almajiransa suka yi duk sun yi shi ne cikin k’arni na sha tara (K’19).
Bayan wucewar Mujaddadi da almajiransa rubutacciyar wak’a ba ta gushe ba ta kuma k’ara samun gindin zama a cikin k’asar Hausa musamman a nan gida Nijeriya. a k’arni na ashirin (K’20) ne aka samu wasu marubuta wak’ok’in Hausa suka rubuta wak’ok’i da dama dangane da jigogi daban-daban. Jigogin da aka rubuta wak’ok’i a kansu a wannan k’arni sun had’a da Jigon addini, siyasa, soyayya, ilimi da sauransu. Wad’annan marubuta da suka yi gagarumin aiki a wannan k’arni sun had’a da: Ak’ilu Aliyu, Aliyu Namangi, Mudi Spikin, Mu’azu Had’ejia, Yusuf Kantu, Bawa Sha’iri Durbawa, Sarkin Gwandu Haruna, Shehu Alkanci da dai sauransu.
Bayan an samu wasu da suka yi rubuce-rubucen wak’ok’i a k’arni na ashirin (K’20) sai kuma bayan shud’ewar su aka samu wasu da suka yi rubuce-rubucen wak’ok’i a wannan k’arni na ashirin da d’aya (K’21). Wannan k’arnin ma an samu wak’ok’i da suka isar da wasu sak’una daidai da k’udurin marubuta wad’annan wak’ok’i. Kuma sun mayar da hankali ga siyasar rayuwa da ilimi da zamantakewa da soyayya da addini da dai sauransu.
3.0.5. Rabe-Raben Wak’ok’in Zamani
Masana da manazrata da yawa sun rarraba wak’ok’in Hausa rubutattu daidai da yawan zubin d’angayen baitukan wak’ar da kuma wasu yanaye-yanaye na wasu wak’ok’i. Kuma sun fito da su kamar haka: Gwauruwa, ‘Yar Tagwai, K’war Uku, K’war Hud’u, K’war Biyar, Tarbi’i da Tahamisi.
Yanzu ga bayanin kowane a tak’aice da kuma misalai domin mai nazari ya ga yadda abin yake gudana.
Misalai
3.0.5.1 Gwauruwa/Maik’war ‘Daya
Gwauruwar wak’a dai kamar yadda aka fad’a cewa, gwauruwa ita ce wak’ar da take da baiti d’aya, kuma d’ango d’aya, babbar k’afiya. Wato amsa amo guda d’aya tak. Misali.
“Alhamdu lillahi mun samu fita had’uri.
Wancana jan zamani, wanda ka sa maza wad’ari.
Jama’a musulmi, ku ce amin mu zan shukuri.
Mu samu sarkin musulmi wanda yayi fari.
Kun san ga dauri kiran mu kai babu mai kifri.
Balle shi yaye duhu jama’a su san sarari.
wannan ita ce wak’a mai k’war d’aya wato gwauruwa.
3.0.5.2 ‘Yar Tagwai/Mai K’war Biyu.
Wak’ar ‘yar tagwai wato mai k’war biyu wak’a ce da take d’auke da d’angaye guda biyu, wato k’arami da babba. Wannan galibi k’aramin d’ango na ciki shi ne wanda yake canzawa, babba kuma baya canzawa. Misali.
“ ‘Yan yara ku zo a fad’a maku,
Ku ji labarin Nijeriya.”
“In an Tambayaiku Ku Ce masu,
Mu tamu k’asa Nijeriya,”
“Don kam da yawa aka tambaya,
Shin wai mi an Nijeriya,”
“To wagga k’asa ce ba wata,
Ita anka sani Nijeriya.”
Wannan iata ce wak’a mai k’war biyu kamar yadda ak gani.
3.0.5.3 Wak’a Mai K’war Uku.
Ita wannan wak’a kamar saura wak’a ce da take d’auke da d’angaye guda uku, k’anana biyu babba guda. Misali
“farkon wak’ata Ubangiji naka sawa,
Sarki Mahalicci Ilahu ba shi gazawa,
Alkawarin Allah mai haka bai ta’bewa”.
3.0.5.4 Wak’a Mai K’war Hud’u
Wak’a mai k’war hud’u dai ita ce wadda take d’auke da d’angaye guda hud’u, kuma wad’annan d’angayen k’anana uku a ciki babba guda a waje. Misali.
“Duk masu zargi sui ta yi na d’auka,
Ko za ta kai a tu’be ni ai mani duka,
A rididdige da wuk’a a kai ni a girka,
Ba za ni saurara don son ki ba Dije”.
3.0.5.5 Mai K’war Biyar/Muhammasa
Wannan wak’a, wak’a ce da take d’auke da d’angaye guda biyar, kuma ita wannan wak’a, tana da d’angaye hud’u a ciki wato k’anana, kuma tana da d’ango babba guda a waje. Misali
“Ba ruwan mutuwa da mulki,
Ko na mai d’amara da kaki,
Ko na mai rawani ga sarki,
In ta zo tilas ta d’auki,
Ransu mulkin bai hana ba.”
3.0.5.6 Tarbi’i.
Wannan tsarin wak’ar wak’a ce wadda wani ya rubuta ya rubuta mai d’auke da k’war biyu sai wani ya k’ara mata biyu su zama hud’u. Misali.
“’Yan Musulmi kui mana hanzari,
A mu zan ka yabo gun Gafiri,
A mu gode badini zahiri,
Jama’ag ga Karimi K’adiri.”
3.0.5.7 Tahamisi
Tahamisi dai wak’a ce da wani ya rubuta mai k’war biyu ko uku, wani marubucin wak’ar daban ya d’auka ya yi mata k’arin biyu idan uku ce ko uku idan biyu ce ya cika ta biyar. Misali.
“jan aiki ne a gabnmu duk,
Jawur yake ko mun san shi duk,
Jama’a sai gamu a rabke duk,
Jahilci ya ci lakarmu duk,
Ya sa mana ankwa har wuya.”
3.0.6 Amfani Da Muhimmancin Wak’a.
Masu iya magna kan ce “Ko kare yana da ranarsa” to in haka ne ballantana wannan al’amari da muka saka a gba wato fagen ilimi. Idan muka dubi irin rawar da wak’a take takawa a fagen yad’a addinin musulunci kawai sai mu fahimci cewa wak’a tana da gagarumin amfaniga al’ummar Hausawa musamman ta wajen adanawa da bunk’asa rumbunsu na kalmomi da al’adunsu. Misali manyan mashahuran malamai irin su Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Danfodiyo da k’anensa Abdullahin Gwandu da d’ansa Muhammadu Bello da ‘Yarsa Nana Asma’u da almajiransa dukansu sun yi amfani da wak’a wajen yad’a addinin Musulunci. Ko bayan su kuma muna ittifak’in cewa, kad’an daga cikin muhimmancin wak’a sun had’a da:
- Sauk’in jawo hanakali: wato ta hanyar wak’a ne akan samu sauk’in jawo hankalin mai saurare ko mai son ya koyi wani abu.
- Akwai Samar da nishad’i: Ta hanyar wak’a mutum ko mutane sukan samu walwala su ji nishad’i a kuma ji an kawar masu da damuwa.
- Samun Sauk’in shiga kai: Idan mutum yana buk’atar sak’onsa ya yi saurin kar’buwa ga jama’a yakan yi amfani da wak’a saboda ta fi saurin shiga kai. Misali dubi yara ‘yan makaranta za ka ga sun fi rik’e duk wani abu da aka koya masu da wak’a.
- Wak’a tana d’ebe kewa: Wak’a kan taimaka ainun wajen cire kewar wani abu, musamman na ‘bacin rai. Da zarar mutum ya nishad’antu da jin wak’a sai ‘bacin ran da yake fama da shi ya gushe.
Wad’annan kad’an ne daga cikin muhimmancin da wak’a take da shi.
Babi Na Hud’u
4.0.1 Mawak’an Gargajiya.
Kamar dai yadda aka sani ba kowa ne zai iya yin wak’ok’in gargajiya ba sai wanda ya gada ko ya gada sai in yana da zalak’ar yin wak’ar. Wasu tuni suka samu zalak’ar yin wak’a kuma suna iya aiwatar da ita a ko’ina ta tare da sun d’auki wani tsawon lokaci ba. A k’asar Hausa dai muna da mawak’an gargajiya da suke yin wak’a iri daban-daban kamar dai su:
- Alhaji Musa ‘Dank’wairo.
- Ibrahin Narambad’a
- Mamman Shata.
- Alhaji Aliyu ‘Dandawo da d’ansa Sani Aliyu ‘Dandawo.
- Garba Maitandu.
- Alhaji Salihu Jankid’i.
- Mamman Bawa ‘Dantanoma.
- Kassu Zurmi.
- Abu ‘Dankurma.
- Bawa Jatau Kamba.
- Sani Sabulu Kanoma
- Musa ‘Dan Ba’u
- Rabo Ango Yabo.
- Garba Hore.
- Muhammadu Bawa ‘Dan’anace. Da dai sauarnsu.
4.0.2 Marubuta wak’ok’in Zamani
Da yake akwai makad’a da mawak’a na gargajiya kuma sun bambanta da na zamani, haka suma marubutan zamani suna da bambanci da na gargajiya. Ba kowa ne zai iya rubuta wak’ok’in zamani ba ko da ya gada, haka kuma wannan nau’in yana buk’atar ilimi mai yawa da kuma iya tsara wak’ar da iya jera kalmomi su samar da ma’ana da amfani da salo domin isar da sak’o a cikin sauk’i. A k’asar Hausa muna da marubuta wak’ok’in zamani da suka had’a da:
- Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Dan Fodiyo.
- Abdullahin Gwandu
- Muhammadu Bello
- Nana Asma’u
- Isah Mai Kware,
- Abdullahi Mai Bod’inga.
- Mu’azu Had’ejia
- Gambo Hawaja
- Aliyu Namangi
- Ak’ilu Aliyu
- Shehu Alkanci Sarkin Gwandu Haruna
- Bawa Sha’iri Durbawa
- Yusuf Kantu
- Mudi Spikin
- Bello Wurno
- Ummaru Nasarawa
- Aliyu Bunzu
- Zainu Zubairu
- Kaftin Suru
- Abubakar Ladan Zariya da sauransu.
4.0.3 Mawak’an Zamani Wad’anda Suke Had’awa Da Kid’a.
A wannan zamani akwai wasu mawak’a da ba na gargajiya ba kamar wad’anda muka sani, kuma ba a kiransu rubutattun wak’ok’i, saboda galibi kafin a kira wak’a rubutacciya sai ta kasance tana d’auke da wasu sharud’d’a na zama rubutacciya. Kafin a kira wak’a rubutacciya dole ne ya zan ba ta da kid’a kamar yadda Gusau ya fad’a a wani aiki nasa. Kuma ana kiran wak’a rubutacciya idan tana da tsarin aruli a tattare da ita, ko da kuma ba ta da to lallai ta kasance ba mai amshi ba ce, ba mai kid’a ba, kuma ba wadda ake sakawa a yi ta rawa ba a dandali. Wannan nau’in wak’a ta zamani, ana shirya wak’a a kaita a d’akin tace wak’a a saka a yi mata kwaskwarima da kid’a daidai da yadda ake buk’ata, sai a tace ta daidai da yadda ake buk’ata a fitar a je a rik’a sakawa a inda ake buk’atarta. Marubuta wak’ok’in siyasa da na aure da na soyayya a wannan lokaci su ne suka fi yin wannan.
Akwai nau’ain marubuta wak’ok’i irin wad’annan da suka had’a da:
- Auwalu Isah Bungud’u
- Kabir Yahaya Kilasik
- Ibrahim Aminu ‘Dandago
- Abubakar Hikima
- Sadi Sidi Shariffai
- Adamu Nagudu
- Adam A Zango
- Nura M. Inuwa
- Fati Nijar
- Zuwaira Isma’il
- Dahiru S.K
- Dauda kahutu Rarara
- Misbahu M Ahamad
- Abubakar Sani
- Abubakar M. Sharif da dai sauransu.
4.0.4 Dangantakar Wak’ok’in Gargajiya Da Na Zamani
Wak’ok’in Hausa na gargajiya da na zamani suna da dangantaka musamman idan aka lura da wad’annan abubuwa:
- Saboda sun kasance duk Hausawa ke rubuta su kuma su ke rera wak’ok’in.
- Fassara: Fassara wasu kalmomi musamman na fannin adabin Hausa zuwa adabin zamani.
- Fiyano: wata algaita ce ta yin kid’an Turawa wadda Hausawa, wadda Hausawa suka same ta daga Turawa.
- Jihadin Shehu Usmanu da mabiyansa, yawace-yawacensa na yad’a addinin musulunci ya samu kar’bar wasu wak’ok’i daga malaman zaure yana mayar da su a rubuce.
- Wak’ok’in jama’a da wak’ok’in fada da wak’ok’in sha’awa da wak’ok’in bandariya, duk wak’ok’i ne na adabin Hausa, shigowar zamani duk suka had’u suka zama d’aya.
4.0.5 Kamancin Wak’ok’in Gargajiya Da Na Zamanni
Wak’ok’in gargajiya da na zamani suna da kamanci da juna kamar dai yadda za a gani nan, kamancin kuwa shi ne:
- Dukkansu suna isar da sak’o.
- Ana amfani da su wajen nishad’antarwa.
- Sukan zo da tarihi
- Dukkansu suna da hawa da saukar murya.
- Akan samu yabo a cikinsu
- Suna ilimantarwa
- Dukkansu ana rera su.
- Dukkansu ana kiransu wak’a.
- Dukkansu ana tsara su bisa ga tsarin da ya dace da su.
- Dukkansu suna da sauk’in isar da sak’o.
- Ana iya samun salo da sarrafa harshe a kowace daga cikinsu.
- Dukkaninsu suna iya tarayya a jigogi d’aya.
4.0.6 Bambancin Wak’ok’in Gargajiya Da Na Zamani
Duk da cewa wak’ok’in gargajiya da na zamani suna da kamanci, haka kuma akwai inda suka bamb anta kamar dai yadda za a gani a nan:
- Wak’ar gargajiya tana da kid’a, amma rubutacciya ba ta da kid’a.
- Wak’ar gargajiya tana da ‘yan amshi, yayin da rubutacciya ba ta buk’atar ‘yan amshi.
- Mawak’an gargajiya ana iya gadonta, amma rubutacciya sai wanda yake da ilimin yinta.
- Wak’ar gargajiya tana tafiya da sauti, rubutacciya kuma k’afiya ne take tafiya da shi.
- Wak’ar gargajiya d’iya gareta, amma rubutacciya baiti ne take da shi.
- Wak’ar gargajiya tana da yawan maimaici don amfanin abin da aka fad’a, yayin da a rubutacciya ba a maimaita abin da aka fad’a komai fa’idarsa.
- Wak’ar gargajiya ana amfani da ita don a samu kud’i, yayin da rubutacciya sak’o ne kawai aka fi mayar da hankali a kansa.
- Wak’ar gargajiya ana yinta a dandali, amma rubutacciya ba a yinta a dandali.
- Zubi da tsarin wak’ok’in yana bambanta da juna.
Wad’annan su ne bambance-bambancen da ke tsakanin wak’ar gargajiya da ta zamani.
https://www.amsoshi.com/contact-us/
Babi Na Biyar
5.0.1 Jawabin Kammalawa
Babu shakka wannan bincike ya zo k’arshe kuma a cikin wannan babi ne za mu gabatar da jawabinmu domin kammala wannan bincike. Wannan aiki, aiki ne da muka ba taken “Nazari A Kan Bambance-Bambancen Da Ke Tsakanin Wak’ok’in Gargajiya Da Na Zamani” Kuma mun kasa wannan kundin bisa ga tsari na babi-babi in muka zuba shi bisa ga babi biyar.
Baya ga babi na d’aya da babi na biyu wad’anda suka su abin da ake gudanarwa a ciki bai shafi gundarin aiki ba.
A babi na uku mun kawo bayanai game da ma’anar wak’a inda muka tsamo ra’ayoyi daga masana daban-daban. Haka kuma mun kawo samuwar wak’ok’in baka da ire-irensu inda muka zo da wak’ok’in yara maza da yara mata da wak’ok’in nik’a da wak’ok’in raino da na da’be da na nik’a da dai sauransu. Mun kuma kawo wasu wak’ok’in don ganin misalin yadda wak’ok’in suke. Mun kawo samuwar wak’ok’in zamani wato rubutacci da ire-irensu da inda muka dube su ta hanyar d’angayensu da yanayinsu. Bincike ya kawo amfani da muhimmancin wak’a ga al’umma.
A babi na hud’u kuma nan ne muka zo da bayanai da suka danganci, mawak’an baka inda muka kawo su Alh. Musa ‘Dank’wairo da Alh. Aliyu ‘Dandawo da Ibrahim Narambad’a da Mamman Shata. Haka kuma bincike ya kawo marubutan wak’ok’in zamani inda muka kawo Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Dan Fodiyo da almajiransa. Da kuma wasu da suka yi lokaci a k’arni na 20 da na 21 kamar su Mu’azu had’ejia da Gambo Hawaja da Yusuf Kantu da dai sauransu. Wasu mawak’a da muka kawo na zamani masu had’a wak’ok’insu da kid’a na zamani suma mun kawo su Kabiru Yahaya Kilasik da Alh. Ibrahim ‘Dandago da Dahiru S.K da dai sauransu. Bincike ya kawo kamancin wak’ar gargajiya da ta zamani da kuma bambancin da ke tsakaninsu, inda kuma ce suna da bambanci ta hanyar amshi da kid’a da aiwatarwa a dandali. Kuma suna da kamanci ta hanyar isar da sak’o da sauransu.
A babi na biyar kuma nan ne muka nad’e tabarmar wannan bincike da jawabinmu na kammalawa da kuma shawarwari.
5.0.2. Shawarwari
A matsayinmu na masu nazarin harshen Hausa muna ba duk wanda zai yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da kundin mu kuma in har binciken nasu yana da alak’a da namu da su yi k’ok’arin d’orawa daga inda muka tsaya kar su kwashe d’ai, don wannan ba ya taimaka wa nazari. Kamar yadda muka za’bo taken da wani bai ta’ba yi ba muka yi shige –shige har muka tattaro bayanan da suka gina muna wannan kundin ya zama abin karatu ga wasu to lallai suma ya zama wajebi su dage don su samar da wani abu mai amfani, ba wai su kwashe abin da wasu suka yi ba.
Haka kuma muna ba duk wad’anda suka ci karo da wannan kundi hak’uri da su yi muna uzuri dangane da wannan aiki da muka gudanar. Muna ba da shawara ga makad’a da marubuta da su dage matuk’a su samar da wani abu da d’alibai za su nazarta a wannan fanni na adabi.
MANAZARTA
https://www.amsoshi.com/contact-us/
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.