Ticker

6/recent/ticker-posts

Bako Ra’ba Dan Gari Kaba: Nazari A Kan Tasirin Bak’o A Cikin Karin Maganar Hausawa

DAGA

SADIYA IBRAHIM MAIGANDI

SHAFA’ATU UMAR MORIKI

SAMIRA ABDULLAHI

www.amsoshi.com

SADAUKARWA


Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta k’asa (NCE) a Sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere da ke Gusau a jihar Zamfara ga mahaimafanmu da kuma ‘yan ‘uwanmu. Allah ya saka masu da Alheri. Amin.

GODIYA

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.

Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun farko har ya zuwa ranar k’arshe.

Dunk’ulalliyar godiya cikin girmamawa zuwa ga mahaifanmu: Alhaji Ibrahim Maigandi K’aura da Rabi’atu Ibrahim Maigandi da Muktar Ibrahim Maigandi da Alhaji Umar Moriki da Alhaji Abdullahi da Bashar Yusuf Usman da Alhaji Ahmad Muhammad Bagu (sauran naku)da ‘yan uwanmu yayyenmu, k’annenmu, k’awanyenmu da masoyanmu tareda da abokan arziki, domin su suka ba mu dukan taimako da goyon baya da ya kamata musamman a wannan karatu namu.

Haka kuma muna mika kyakyawar  godiyarmu ta musamman ga malamanmu kamarsu; Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Malam Haruna Umar Bungud’u, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba, Mal. Ibrahim ‘Dan’amarya, Mal. Aminu Saleh, Mal. Husaaini Aliyu da sauran su.

Godiya ta musamman ga Malam Hamisu tare da ‘yan uwa da abokan arziki baki d’aya, dafatan Allah ya saka masu da mafificin alhrinSa. Amin.

 

 

JINJINA


Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu jinjina ma malaman mu musamman Mal. Habibu Lauwali K’aura da ma wasu daga cikin mutanen da suka taimake muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan dalibai da ma duk masu neman k’arin haske dangane da nazari da muka gudanar a kan “Bak’o Ra’ba ‘Dan Gari Kaba: Nazari A Kan Tasirin Bak’o A Cikin Karin Maganar Hausawa” muna masu rok’on Allah ya saka masu da maifificin alheri. Amin.

 

K’UNSHIYA


Shaidantarwa -      -        -        -        -        -        -        -        ii

Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        -        -        iii

Godiya        -        -        -        -        -        -        -        -        iv

Jinjina         -        -        -        -        -        -        -        -        vi

K’unshiya    -        -        -        -        -        -        -        -        vii

BABI NA ‘DAYA

1.0    Gabatarwa    -        -        -        -        -        -        -        1

1.0.1Yanayin Bincike -   -        -        -        -        -        -        2

1.0.2Muhallin Bincike     -        -        -        -        -        -        3

1.0.3Hanyoyin Gudanar da Bincike     -        -        -        -        4

1.0.4Manufar Bincike      -        -        -        -        -        -        5

1.0.5Matsalolin Da Suka  Taso -         -        -        -        -        6

1.0.6Matsalolin Da Aka Fusakanta -    -        -        -        -        8

BABI NA BIYU

2.0 Gabatarwa       -        -        -        -        -        -        -        10

2.0.1  Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata   -        -        10

2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -        -        -        -        -        16

2.0.3 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        17

BABI NA UKU

3.0 Gabatarwa       -        -        -        -        -        -        -        18

3.0.1 Ma’anar Karin Magana -            -        -        -        -        18

3.0.2 Kashe-Kashen Karin Maganar Hausa   -        -        -        20

3.0.2.1 Karin Maganar Jiya (Na Gargajiya)   -        -        -        21

3.0.2.2 Karin Maganar Yau (Na Zamani)      -        -        -        22

3.0.3 Tasirin Karin Magana A Rayuwar Bahaushe  -        -        23

3.0.4 Illolin Karin Magana -      -        -        -        -        -        26

3.0.5 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        27

BABI NA H U’DU

4.0    Gabatarwa     -        -        -        -        -        -        -        29

4.0.1 Ma’anar Bak’o-      -        -        -        -        -        -        29

4.0.2 Ire-Iren Bak’o-       -        -        -        -        -        -        30

4.0.2.1 Bak’on Mutum    -        -        -        -        -        -        31

4.0.2.2 Bak’on Lamari Ko Yanayi      -        -        -        -        33

4.0.3 Matsayin Bak’o A Al’ummar Hausawa          -        -        -        33

4.0.4 Matsayin Bak’o A Addinin Musulunci -        -        -        35

4.0.5 Karin Magangannun Da Suka Danganci Bak’o A Hausa    36

4.0.6 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        42

BABI NA BIYAR

5.0 Gabatarwa       -        -        -        -        -        -        -        43

5.0.1 Jawabi Kammalawa         -        -        -        -        -        43

5.0.2 Shawarwari   -        -        -        -        -        -        -        46

5.0.3 Ta’arifin Wasu Kalmomi  -        -        -        -        -        46

Manazarta    -        -        -        -        -        -        -        -        49

 

Babi Na ‘Daya


Gabatarwa


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mahaliccin kowa da komai, wanda a cikin ikonSa ne da iyawarSa da kuma baiwarSa Ya ba mu ikon rubuta wannan kundi.

Wannan aiki namu mai taken “Bak’o Ra’ba ‘Dan Gari Kaba: Nazari A Kan Tasirin Bak’o A Cikin Karin Maganar Hausawa”  aiki ne wanda za mu gudanar a fagen adabi kuma wanda ya shafi karin magana kamar yadda sunan kundin ya nuna.

Kamar yadda dokar gudanar da aikin kundi ta tanada za mu yi wannan bincike namu ta hanyar amfani da babi- babi, kamar haka:

Babi na d’aya: Za mu yi Gabatarwa da Yanayin Bincike, Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Da Suka Taso da Matsalolin Da Aka Fuskanta.

A babi na biyu: za mu yi tsokaci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata, da kuma Salon Nazari Da Tsarin Bincike.

A babi na uku kuwa za mu yi bayanin Ma’anar Karin Magana da Kashe-Kashen Karin Magana Tasirin  Karin Magana Ga Al’ummar Hausawa da Illolin Karin Magana.

Sai babi na Hud’u inda za mu yi bayanin Ma’anar Bak’o da Ire-Iren Bak’o, Matsayin Bak’o A Al’adar Bahaushe, Matsayin Bak’o A Addinin Musulunci, da kuma Karin Magangannun Da Suka Danganci Bak’o A Na Hausawa.

Babi na biyar kuwa: nan ne mu ka yi Jawabin Kamalawa, tare da  Shawarwari, da  Ta’arfin Wasu Kalmomi.

Yanayin Bincike


Kamar yadda aka sani mun gano cewar akwai buk’atar mu yi nazari a kan wasu bayyanai da marubuta suka yi a kan wannan binciken  kuma mun gano cewa, Hausawa suna amfani da karuruwan magana masu d’auke da darussa wad’anda idan muka tsaya muka kwantar da hankali za mu ga cewa, akwai abin da ya dace mutane su sani game da abin da suke amfani da shi a cikin karin maganar da suke amfani da shi na yau da kullum. don haka muka ga ya kamata mu gudanar da wannan binciken domin  zuwa  gaba ko kuma mu ce domin masu tasowa yanzu da su san cewa wannan fanni na zube yana da muhimmanci.

Haka kuma a yunk’urinmu na gudanar da wannan aikin Binciken mun sha wahala sosai saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi Magana a kan wannan aiki namu. Bayan  shi kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala matuk’a.

Muhallin Bincike


Wannan bincike mun gudanar da shi ne a ‘bangaren d’abi’un Hausawa, wad’anda suke gudanarwa a cikin magangannunsu na yau da kullum. Domin  samun sauk’in gudannarwa mun ke’bance aikin namu a kan Karin Maganar nan da ake cewa, “Bak’o ra’ba d’an gari kaba”. Wannan aikin zai yi tsokaci a kan yadda Tasirin Bak’o yake a cikin al’ummar Hausawa.

 Hanyoyin Gudanar da Bincike


Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na marubucin littafin ko manazarta masu bincike wad’anda suka gabata domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi daban-daban don k’arin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan Ilimi.

Kamar yadda bayani ya gabata mun  lura da cewa, dukkan mai aikin bincike dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantatttu da kuma cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar da wannan bincike namu domin kuwa har d’akunan  karatun wasu manyan makarantu mun lek’a. Mun kuma ziyarci d’ukunan karatu, don yin bincike ga kad’an daga cikinsu Jami’ar Usman Danfodio inda muka shiga d’akunan karatunsu wato (library).

Haka ma binciken namu bai tsaya a Jami’ar Usman Danfodio kawai ba a’a har Jami’ar Bayero da ke kano mun leka a d’akin karatun dalibai duk a wannan Jami’ar.

Binciken namu bai  tsaya a wad’annan Jami’o’in ba kurum. Domin kuwa ziyarar binciken ta kai mu ga dad’ad’d’iyar Jami’ar Ahmadu Bello mai tarihi ita ma mun shiga lunguna- lunguna domin gudanar da wannan bincike namu. Daga nan sai muka cirata zuwa Jami’ar Katsina, inda a can muka samu ziyarar sauran makarantu ne kuma yanayin binciken d’aya ne.

Manufar Bincike


Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano cikakkiyar k’warewar dalibai da fahimtarsu da hazak’arsu. Ta wannan hanyar karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya k’ara tabbatar da abin da aka riga aka sani a fagen ilimi.

Binciken yana fitar da bayanai domin amfani al’umma, wani babban muhimancin bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.

Mun yi wannan bincike ne, domin mu bayyana irin yadda bak’o yake ga al’ummar Hausawa ta hanyar amfani da karin maganar Hausawa.. Don haka muka ga cewar ya kamata mu binciko ainifin ita wannan lamari mu yi bayani ga Jama’a domin su samu abin dogaro da shi. Wata manufar kuma ita ce domin ‘ya’yanmu da jikokinmu su yi alfahari da wannan bincike namu a nan gaba.

Matsalolin da Suka Taso


Wannan bincike namu mun gudanar da shi ne a kan hanyoyin da suka dace, na irin hanyoyin da ake bi wajen samun bayanan da suka dace ta hanyoyi da dama. Mun ci karo da matsaloli da dama wajen binciken mu kamar haka.

Rashin isassun kud’in mota, da matsalar iska wad’ansu masana da muke tuntuba wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kud’in mota domin zuwa wajen  wad’ansu mutane da abin ya shafa, sai mu iske ba su nan. Haka ma kowa yasan irin halin da ake ciki a k’asar nan na rashin tsaro, a inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole sai da taka tsantsan.

Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu d’alibai mata masu rauni da kuma k’arancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama  sun sha kanmu. Daga cikinsu akwai

Matsalar kar’bar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji da ta k’arshen zangon karatu.

Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka had’a da girke-girken abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk wad’annan matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo  da su .

Akwai matsalar tuntu’bar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu suna ganin kamar za mu d’aukin sirrinsu ne mu watsa wa duniya.

Haka ma akwai matsalar yawan d’aukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta d’auke. Kad’an kenan  daga irin matsalolin da muka ci karo da su.

Matsalolin da aka Fuskanta


Kamar yadda aka sani ne a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka, wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kud’i da za mu buga wannan aiki namu. Haka kuma akwai matsalar haduwarmu idan mun yi alk’awali, kuma idan za mu tafi wajen  ganawa da wad’anda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne a same su ba. Haka ma akwai matsalar kayan aiki kamar su rikoda, saboda d’aukar bayanan masana a kan wannan bincike.

Haka akwai sha’anin rashin lafiya yakan kama magidanci , ko kuma halin tafiya wajen k’aro ilimi wato a ‘bangaren su masana.

Ba nan kad’ai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar k’aramcin lokaci. Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a cikin shekara d’aya ko ma fiye ba wai wannan k’ank’anin lokaci ba.

 

Babi Na Biyu


2.0 Gabatarwa.


A wannan babi na biyu nan ne za mu yi bitar ayyukan da suka gabata, wannan kuma shi ne ake kira waiwaye. Wato ana nufin mai nazari ya yi binciken ayyukan da suka gabata kama daga littattafai da kundaye da mujallu da muk’alu da ma jaridu in akwai wani abu da yake da dangantaka da nasa. Bayan waiwaye kuwa za mu yi tsokaci dangane da salon nazari da zubi da tsarinsa.

2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata


An gabatar da ayyuka da dama a kan wannan fanni na adabin baka, saboda haka ya zama wajibi a gare mu da mu waiwayi wasu ayyuka da aka riga aka gabatar a wannan fanni, domin sanin alak’arsu da namu aikin tare da ganin bambancin da ke tsakaninsu.

A cikin jerin ayyukan da suka gabata a wannan fage akwai bugaggun littattafai da masana suka rubuta, da kundayen bincike da manazarta suka rubuta da mujallu da muk’alu da masana da manazarta daban-daban suka rubuta a kan fannoni daban-daban na adabin Hausa. Ga dai wasu daga cikinsu kamar haka:

Madauci I. Da Wasu (1968), A littafinsu mai suna “Hausa Custom” sun yi tsokaci a kan haihuwa zuwa mutuwa da addini da sana’o’i da Chamfi da karin maganar Hausawa.

Wannan gagarumin aiki da wad’annan maruta suka yi yana da alak’a da namu, idan aka duba za a ga cewa sun yi tsokaci a kan karin magana, wanda a namu kundin mu ma muna za mu yi tsokaci a kan karin magana. Duk da cewa wannan littafi yana da alak’a da aikinmu, sai ga shi kuma a wani gefen yana da bambanci da kundin nan da muke da k’udurin yi, saboda su marubutan suna bayani ne a kan karin magana gaba d’ayanta tare da wasu abubuwa da suka shafi al’ada wato haihuwa da mutuwa da addini da sana’a da Chamfi. Yayin da mu namu aikin ba sai mun yi tsokaci a kan wad’annan ba.

Skinner N. (1980), a Littafinsa mai suna “Anthology Of Hausa Literature). Marubucin ya yi bayanin nau’o’in adabi da suka had’a da take da kirari da labaru da wasanni da karin magana da wak’ok’i da littattafan hira da zube da tatsuniyoyi da kacici- kacici.

Wannan aiki na Skinner yana da alak’a da namu ta wani fanni musamman idan aka duba inda ya yi bayani a kan karin magana, wannan ya sa muke da alak’a saboda karin maganar da ya yi tsokaci a kai. Bambancinmu da shi kuwa shi ne ya yi bayanin wasu abubuwa da mu ba sai mun yi bayani a kan su ba. Mu namu aikin ya fi mayar da hankali ne a kan karin magana ne kawai.

Zarruk R. M. da Wasu (1988), a nasu littafin mai suna “Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa; Don K’ananan Makarantun Sakandare, littafi na I da na II da na III, a cikin littafan sun yi bayani a kan harshe da adabi da al’ada, to a cikin abin da ya shafi adabi sun yi magana a kan karin magana wannan ya sa aikinsu yake da akak’a da namu, inda aikinsu ya samu bambanci da namu kuma shi ne su suna Kallon harshe da al’ada da adabi duka a cikin aikinsu, mu kuma namu aikin yana bayani ne a kan tasirin bak’o a karin maganar Hausawa.

Junaidu I. Da Wasu (2007), sun rubuta littafi mai suna “Harshe da Adabin Hausa A Kammale; Don Manyan Makarantu Sakandare”  Marubutan sun rubuta littafin ta fuskoki guda biyu, sun kuma yi shi a kan tsarin babi-babi har babi biyu, inda babi na farko ya k’unshi harshe, yayin da babi na biyu ya k’unshi Adabi. A rabo na biyu kashi na farko ya kawo hanyoyin gwanintar sarrafa harshe kamar su Zaurance, Karin Magana Kirari da dai sauransu.

Wannan aiki yana da alak’a da namu aikin saboda ya ta’bo karin magana a cikin aikinsa yayin da mu ma a namu aikin mun ta’bo karin magana. Sai dai inda muka bambanta da nasa aikin shi ne mu mun ke’bance aikin namu a kan tasirin bak’o a cikin karin karin magana wato ba karin magana gabad’ayanta za mu nazarta ba.

‘Dangambo A (2008), a nasa littafi mai suna “Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari)”. Masani ya yi tsokaci a kan yadda adabin Hausa ya rabu dalla-dalla, a cikin aikinsa ya kawo magangannu irin na hikima wad’anda suka had’a da Ba’a Sara, da Karin magana da Zaurance da dai sauransu. Wannan aikin nasa yana da alak’a da namu aikin saboda ya yi bayanin karin magana wanda yake daman muma namu aikin yana magana ne a kan karin magana, sai da inda suka bambanta shi yana bayanin wasu sassa da dama daga cikin adabin Hausa.

Gusau S. M. (2008), ya rubuta littafi mai suna, “Dabarun Nazarin Adabin Hausa” inda ya yi tsokaci a kan makarantu da makarantun nazarin adabin Larabci da na Ingilishi. Marubucin ya k’ara da kawo tarihi da ginuwar nazarin da fed’e adabin Hausa ciki kuwa har da magangannun hikima da suka had’a da take, kirari, karin magana da salon magana da bak’ar magana.

Wannan aiki na Gusau yana da alak’a da namu aikin saboda ya ta’bo karin magana, wanda muma namu aikin yana da alak’a da karin magana sai da inda muka samu bambanci da nasa aikin shi ne mu mun tak’aita namu aikin a kan Tasirin bak’o a cikin karin maganar Hausa.

‘Dan Hausa E.M (2012) A Littafinsa mai suna “Hausa Mai Dubun Hikima” Marubucin ya tsara littafinsa ne a kan tsarin babi-babi, inda a babi na d’aya ya yi bayani a ne a kan Hausawa da hikimominsu na zantuta. A babi na biyu kuwa ya yi tsokaci a kan karin magana da kirari, a babi na uku ya yi bayanin habaici a wajen Hausawa.

Idan muka lura da wannan aikin za mu ga cewa yana da alak’a da namu aikin wannan kuwa haka yake musamman idan muka duba a babi na biyu inda ya yi bayanin karin magana. Wannan yasa namu aikin yake da alak’a da nasa. Inda kuma suka bambanta shi ne shi marubucin yana bayani ne a kan karin magana gaba d’ayanta inda mu kuma mun ke’bance aikin namu a kan nazarin tasirin bak’o a cikin karin maganar Hausa.

Dukkan wad’annan ayyuka da muka duba suna da alak’a wa wannan aiki namu da muke da k’udurin yi ta wasu fuskokin sai da kuma idan muka dubi wasu fuskokin kuma za mu ga cewa ayyukan suna da bambanci da namu.

 

 

2.0.2 Salon Nazari Da zubi Da Tsarinsa.


Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin mutum. Salo muhimmin abu ne a cikin labari ko jawabi, haka kuma duk aikin da aka gudanar ba cikin tsari ba to, ba zai cimma nasara ba. Don haka domin samun nasarar gudanar da wannan aikin cikin sauk’i, mun yi amfani da salo mai sauk’i, mai jan hankalin mai karatu. Mun kuma yi amfani da za’ba’b’bun kalmomi masu sauk’in ma’ana saboda mai karatu ya ji sauk’in karantawa.

Haka kuma mun yi amfani da gajeru da matsakaitan jimloli, sannan muka gudanar da bayananmu d’aya bayan d’aya a cikin sakin layi mai sauk’in fahimta.

Aikin kamar yadda aka sani mun zuba shi ne a kan babi-babi har zuwa babi biyar saboda mu samar wa mai karatu sauk’i wajen nazari, kuma kowane babi da zamu gabatar sai mun yi masa shimfid’a kana idan muka kai k’arshe sai mu nad’e mu shiga babi na gaba.

 

 

2.0.3 Kammalawar Babi


Kamar dai yadda aka gani a wannan babi mun yi gabatarwa inda muka fad’i cewa a ciki ne za mu yi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, sai muka kawo wasu ayyuka da magabata suka rubuta, masu alak’a da namu kuma muka fad’i inda suka samu bambanci da aikinmu. Mun kuma kawo salo da zubi da tsarin wannan kundin inda har muka fad’a cewa za mu zuba wannan aikin bisa ga tsari na babi-babi kuma zai k’unshi babi biyar.

 

Babi Na Uku





A wannan babi na uku kuwa za mu yi bayanin Ma’anar Karin Magana da Tasirin Karin Magana A Rayuwar Bahaushe da Kashe-Kashen Karin Magana da Muhimmancin Karin Magana da Illolin Karin Magana. Don haka ba tare da ‘bata lokaci ba za mu shiga cikin aikin kai tsaye saboda ganin yadda abin zai kasance.

3.0.1 Ma’anar Karin Magana


Masana da manazarta da dama sun ba da gudunmuwarsu dangane da abin da ya shafi karin magana. Ga dai wasu daga cikinsu.

Zarruk da Wasu (1986), sun bayyana cewa “Karin magana gajeren zance ne wanda yake k’unshe da hikima”

Yahaya I. Y. Da Wasu (2003) sun ce, “Karin magna tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajerce na hikima da zalak’a tare da bayar da ma’ana gamsasshiya mai fad’i mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi daki-daki.

Junaidu I. Da wani (2007) sun bayyana karin magana da cewa, “Karin magana shi ne wata ‘yar jimla gajeriya da mai magana zai fad’a ta hikima wadda ta k’unshi magana mai yawa idan an tashi yin sharhinta”.

Umar, (1980) cewa ya yi, “ Karin magana dunk’ulalliyar jimla ce mai sassa biyu, da ta k’unshi zunzurutun ma’ana lokacin da ake yin bayani. Idan har karin magana ya amsa sunansa karin magana da an ambaci sashensa d’aya za ka ji abokin magana ko wani daban ya cika d’ayan sashen

Shi kuma ‘Dangambo (1984), ya bayyana karin magana da cewa, dabara ce ta dunk’ule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kad’an cikin hikima.

Bisa ga la’akari da wad’annan ma’anoni da masana da manazarta suka bayar za mu iya cewa, “Karin magana wani gajeren zance ne wanda aka shirya shi domin wa wakilci zance mai yawa tare da ma’ana.

Idan muka dubi wad’annan ma’anonin za mu ga cewa kusan duk suna da makusanciyar dangantaka, saboda duk sun yarda cewa zance ne kuma gajere mai k’unshe da hikima. Wato a karin magana za a ga cewa in har zancen yana buk’atar ciko to tilas ne ya k’unshi ‘bangare biyu. Shi dai ‘bangare na farko yana k’unshe ne da jimlataccen bayani na furuci da aka yi wato manufa. Shi kuma ‘bangare na biyu yana k’unshe da k’arin bayani a kan ‘bangare na farko.

3.0.2 Kashe-Kashen Karin Maganar Hausa


Masana da manazarta daban-daban sun yi ruwa sun yi tsaki wajen karkasa karin magana. Misali

Umar (1980), a littafinsa mai suna “Adabin Baka” ya karkasa karin magana zuwa rukuni-rukuni. A cikin “Hausa Ba Dabo Ba Ne”, Kirk Greene (1996) ya bi salon tsara k’amus ne ya karkasa karin magana dangane da haruffa na farko, wato ya jefa su a tsarin abajada tun daga ‘a’ zuwa ‘z’. Shi kuwa Ibrahim Yaro Yahaya a Littafinsa mai suna “Labarun Gargajiya” sai ya yi amfani da hikimomin da ke cikin lamarin ya ware karin magana, ma’ana, hak’uri da arziki.

Haka kuma akwai wata hanya ta rarraba karin magana wato ta bin tsarin gininsu. Ana iya yin la’akari da sigar jimlolin karin magana. Wannan ya nuna cewa kenan abu ne mawuyaci a iya cewa ga iya kashe-kashen da karin magana ya kasu.

A wannan kundin a d’an namu nazari dangane da wannan batu za mu karkasa karin magana zuwa gida biyu, wato za mu dube ta ta fuska biyu, ma’ana karin magana jiya da kuma yau.

3.0.2.1 Karin Maganar Jiya (Na Gargajiya)


A wannan kashi na karin magana wato karin maganar jiya, kamar yadda sunan ya nuna cewa jiya wato lokacin da ya riga ya shud’e ko tsintsar gargajiya to yana nuna duk wani rukuni na karin magana da ya kasance gargajiya ne zalla shi zai shiga a wannan rukuni. misali

  1. Za mu hau inji baran mai doki.

  2. Na duk’e Tsohon Ciniki.


iii. Ba ni na kashe ba rataya aka bani

  1. Allah suturubuk’ui inji kishiyar mai doro.

  2. Sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga.


Da sauran su.

Idan muka kwantar da hankali muka dubi wad’annan karuruwan magangannun za mu ga cewa, dukkannin su suna d’auke ne da lafuzza irin na dauri, wato babu wata kalma da ta danganci zamani a cikinsu.

 3.0.2.2 Karin Maganar Yau (Na Zamani)


Shi kuma wannan kashi na karin maganar yau, akasi ne na karin maganar gargajitya wato shi kamar yadda kalmar nan ta yau ke nuna cewa, abin da bai dad’ad’d’e ba ne yana daidai lokacin da ake gudanar da shi wato dai a tak’aice na zamani ne.

A wannan rukuni nan ne duk wani karin magana da ke da lafuzza da suka danganci zamani zai shiga, muna iya lura da cewa, wasu karuruwan magangannu suna d’auke da lafuzza da suke da ka ji su za ka gano cewa na zamani ne. Misali

  1. Rigakafi ya fi magani.

  2. In mutum ya ce zai baka riga, dubi ta wuyansa


iii. Mai kaza a aljihu, ba ya jimirin as

  1. Ban sa a ka ba, inji ‘barawon hula


Idan muka lura da wad’annan karuruwan magana da muka kawo a sama za mu ga cewa, wasu daga cikin lafuzzan da aka yi amfani da su aka gina karin maganar na zamani ne. Misali kalmomi kamar Rigakafi, riga, aljihu, da kuma hula.

Wannan aiki namu zai fi mayar da hankali ainun dangane da abin da ya shafi tasirin Bak’o a cikin karin maganar Hausawa.

3.0.3 Tasirin Karin Magana A Rayuwar Bahaushe.


Kasancewar karin magana dad’ad’d’iyar magana ce ta hikima wadda take d’auke da sak’o, ta yi tasiri sosai a rayuwar Bahaushe ta fuskoki da dama. Ga dai wasu daga cikin su.

  1. Adon Harshe


Karin magana ado ne na harshe da Bahaushe ke amfani da shi a cikin zancensa na yau da kullum, domin k’awata maganarsa da burgewa ga mai sauraro. Misali.

“zancen kuke so an ce da gwauro ya iyali?”

“Sai ka yi, wai karuwa ta ji mai wa’azi”

“Duk dai ga Baba, inji agola”

  1. Tak’aita Zance Da Saurin Isar Da Sak’o.


Ana amfani da karin magana wajen isar da sak’o a cikin sauk’i ba tare da an yi wani dogon sharhi ba, wato a cikin tak’aitattun kalmomi. Misali.

“Komai nisan jifa, k’asa za ta.”

“Komai nisan dare, gari zai waye”

“Ko an ci goro, an sha barci”

“Kwac ce ya iya wuri aka ba shi”

  1. Yin Sirri A Cikin Zance


Kasancewar ba kowane Bahaushe ne ya san karin magana ba, don haka yakan yi amfani da karin magana don ya ‘boye sirrinsa. Misali

“Na san a rina, an sace wa mahaukaciya zane”

“Laifin ba na bara ba ne, an daki biri ga rani”

“A dai ci gaba da gashi, suya sai ran salla”

“Da ruwan ciki, akan ja na rijiya”

  1. Gargad’i


Ana amfani da karin magana wajen yi wa wani mutum ko wasu mutane don su guji aikata wasu abubuwa mara sa kyau. Misali

“In zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere”

“Zuwa da kai, ya fi sak’o”

  1. Shawara


Shawara tana da muhimmaci a rayuwar Bahaushe, wannan ya sa ya ke amfanai da karin magana wajen ba d’an’uwansa shawara a kan gyara kayanka ko ko aikata wani abu mai muhimmanci. Misali

“Zomo ba ya kamuwa daga kwance”

“In an bi ta ‘barawo, a bi ta mai kaya”

“Fakon kaya ya fi ban cigiya”

 

 

  1. Mayar Da Martani


Bahaushe yana amfani da karin magana wajen mayar da martani a kan wani abu da aka aikata masa da ba daidai ba. Misali

“Kowa ya yi zagi a kasuwa ya san ko da wa yake”

“Kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha”

“Ko ba a gwada ba, linzami ya fi k’arfin bakin kaza”

Tasiran na karin magana da yawa suke ba wad’annan kad’ai ba ne, amma mun d’an bayar da wad’annan ne domin mu d’aure akuyarmu a kan magarya, ma’ana mu bayyana wa mai nazari cewa karin magana yana da tasiri ga rayuwar Bahaushe.

3.0.4. Illolin Karin Magana


Duk da cewa karin magana ya yi tasiri a rayuwar malam Bahaushe to kuma yana da illoli a tattare da shi. Ga dai wasu daga cikin illolin da karin magana ya k’unsa.

  • Karin magana na karya k’a’idar nahawu.

  • Karin magana tana kawo gaba da d’an’uwa.

  • Karin magana tana juyar da ma’anar harshe.

  • Karin magana tana hardasa rashin fahimtar harshe ga bami.

  • Karin magana tana wahalar da mai koyon harshe.

  • A kam yi amfani da karin magana a cutar da wanda ba ya jin harshen sosai.

  • Karin magana wani makami ne na fad’a tsakanin mazauna wuri d’aya.

  • Ana tafka sa’bo wani lokaci a cikin amfani da karin magana.


Wad’annan su ne illolin da karin magana take tattare da su. Ba wai su kad’ai ba ne sai dai su kawai muke iya bayarwa kar mu wuce gona da iri.

3.0.5 Kammalawar Babi


A wannan babin mun bayyana ma’anar karin magana inda muka kawo ra’ayoyi daga masana da manazarta daban-daban saboda aikin namu ya samu kar’buwa inda har muka ce zance ne gajere mai d’auke da ma’ana a cikin hikima. Mun kuma kawo kashe-kashen karin magana inda shi ma har muka kawo yadda wasu masana da manazarta daban-daban suka karkasa shi. Mun kuma kasa shi daidai da fahimtarmu inda muka kasa shi a kan na gargajiya da na zamani kuma muka bayar da misalai da za su yi k’arin haske. Tasirin karin magana ga rayuwar Bahaushe ya biyo baya kuma mun kawo wasu bayanai da za su tabbatar da haka. Sai illolin karin magana duk a cikin wannan babi.

 

Babi Na Hud’u



  • Gabatarwa


Wannan babi wato babi na hud’u zai k’unshi Ma’anar Bak’o da Ire-Iren Bak’o, Matsayin Bak’o A Al’adar Bahaushe da kuma Matsayinsa a Addinin Musulunci. Za mu kuma yi tsokaci a kan Karin maganannun da suka danganci Bak’o na Hausawa.

4.0.1 Ma’anar Bak’o


Akwai ra’ayoyi da yawa mabambanta dangane da kalmar bak’o. Ko wane ne bak’o? Tambayar kenan da ya dace mu dubi yadda wasu suke ganinta.

Wasu suna ganin cewa bak’o shi ne wanda ya zo daga wani wuri mai nisa. Wasu suna ganin cewa bak’o shi ne wanda ba a sani ba.

Amma su masana musamman Farfesa Aliyu Muhammad Bunza cewa ya yi “Bak’o da Bak’unci shi ne shigar wani abu a cikin wani da ba nasa ba ko ba a saba da shi ba. Abin nan da ya shiga wurin da ba a saba da shi ba shi ne bak’o. Haka kuma masanin ya ci gaba da cewa, akan zama bak’o kai har a cikin gida guda. Misali tsakanin d’an d’aki da d’an d’aki.

Idan muka kalli wad’annan bayanai da suka gabata na wasu masana za mu ga cewa, bak’o dai shi ne shigar wani abu ko zuwansa a wani wuri wanda ba nasa ba. Hak’ik’a Aliyu Bunza ya bayyana muna ma’anar bak’o musamman da ya yalwata wannan ma’ana. Wato ba mutum kawai zai iya zama bak’o ba. Lokaci da yanayi da shigar ciki da aukuwar wani abu duk suna iya zama bak’i a cikin wannan ma’ana da ya bayar. Sanin jama’a ne wasu wurare ana kiran Azumi wato (Ramadan) da bak’o a lokacin da yake farkon shiga. Haka idan mutum ya zo daga wani wuri akan kira shi bak’o. Idan wani bak’on al’amari ya auku akan d’auke shi a matsayin bak’o.

4.0.2 Ire-Iren Bak’o


Kamar yadda aka yi bayanin abin da ake kira bak’o za mu ga cewa, bak’on ya kasu kashi biyu.

  1. Bak’on Mutum

  2. Bak’on Lamari/Yanayi


Kamar yadda muka gani dai za mu d’an yi tsokaci ko da kad’an ne dangane da wad’annan ire-iren bak’o da muka bayar.

4.0.2.1 Bak’on Mutum.


Wannan nau’in bak’o dai nau’i ne da ya k’unshi mutane wato ba wani lamari ba.

A wannan nau’in dai mutum ne zai je wani gari ko wata unguwa ko wani wuri wanda tun asali ba nasa ba ne, kuma takan d’auro ya je da kaya ko ba tare da su ba, takan d’auro ya je ya kwana ko wuni ko kuma ya d’an je na d’an wani lokaci. Yana iya zama kasuwanci ko ziyarar ‘yan’uwa ko abokan arziki ko neman aure ko dai wata lalura. A nan idan mutum ya samu kansa a cikin wannan yanayi to shi ne bak’o.

A al’adar Hausawa mutum yakan ziyarci ‘yan’uwansa don sadar da zumunci kuma galibi idan ya je yakan iya yin wasu kwanaki a can ko wuni, su kuma wad’anda aka iske a can su ne ‘yan gida kuma su ne za su yi tarbo bak’o su ba shi ruwa su ba shi abinci da sauran abin da ya dace. Bayan bak’o ya sha ruwa ya ci abinci sai a shiga gaisawa da shi ana tambayar shi mutanen da ya baro gida da kuma hanya da ya biyo kafin ya iso gare su. Daga nan ne shi wanda ya zo wato bak’o sai ya fara bayanin yadda ya baro gida da kuma yadda ya iso a wurinsu. Hausawa sukan yi wa bak’onsu hidimomi kafin ya koma, idan kuma ya tashi komawa sukan yi masa goma sha ta arziki wato su ba shi duk abin da ya sauwak’a gare su. Kamar hatsi ko kud’i ko dabbobi ko tsuntsayen gida kamar kaji, kutatta (Kuti-Kuti) tantabaru da dai sauransu.

Shi kuma bak’o na kasuwanci wato wanda kasuwanci ya kai shi a wani gari ko unguwa ko ma inda ake gudanar da kasuwanci to, shi malam Bahaushe yakan gudanar da huld’a ta mutunci a tsakaninsa da abokin kasuwancin galibai shima yakan bashi ruwa ko abinci tare da tarbonsa cikin mutunci da kuma kyautatawa saboda shima idan Allah ya kai shi wajensa abin da zai tsammani kenan ya samu. Ta fannin kasuwanci da ke tsakaninsu kuma zai yi masa duk abin da ya dace.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

4.0.2.2 Bak’on Lamari Ko Yanayi.


Wannan nau’in bak’o na yanayi ko lamari dai bai shafi zuwan wani mutum ba sai dai zuwan wani abu daban wanda ba mutum ba. Misali idan watan Sha’aban ya k’are aka ga watan Ramadan wato watan Azumi lokacin da yake farko wasu suna kiransa da bak’o, wannan ma ke sa idan aka kwana d’aya ko fiye duk lokacin da wani yana abokin gaisawarsa yakan ce masa “Ina Kwana Ko Ina Wuni ya bak’o?” shi kuma abokin magana yakan amsa “Lafiya lau Ko k’alau bak’o da godiya” wannan ya nuna cewa kenan bak’on yanayi ko lamari shi ma bak’o ne. Haka kuma idan aka samu ‘barkewar wata cuta wadda ba a sani ba ta shiga jama’a wanda ba a fata shi ma wannan lamari ana kiransa bak’o.

4.0.3 Matsayin Bak’o A Al’ummar Bahaushe


Hausawa suna d’aukar bak’o da muhimmancin gaske kuma shi wannan bak’on ko da ba su san halinsa ba. Hausawa suna tarbon bak’o da ruwan sha da abinci da kyawawan magangannu da duk irin abin da su ke da shi sukan taimaka masa da shi.

Wannan zancen haka yake idan muka yi la’akari da karin maganar nan mai cewa, tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta. Wato tu kafin addinin musulunci ya zo ga Bahaushe Hausawa suke gani kimar bak’o suke taimaka masa. Wannan ko ba a fad’i ba idan mutum ya dubi yanayin tsarin gidan malam Bahaushe zai ga cewa ko bayan d’akin da maigida yake da shi yana da d’akin da bak’i ke sauka idan ya samu bak’in. Haka kuma idan aka dubi tsarin Hausawa a can da za a ga cewa, a kowane gare indai har akwai sarki to sai ka ga akwai gidan bak’i, wannan gida an yi shi ne domin bak’i kawai duk inda aka samu bako to a gidan ne zai kwana.

Wannan tsari na kyautata wa bak’i ya sa al’ummar Hausawa sun samu ci gaba musamman had’uwarsa da wasu al’ummu kamar dai Larabawa da Turawa da sauran wasu k’abilu mak’wabta. Saboda irin wannan kyautatawa da Hausawa ke yi ya sa sun samu had’uwa da jama’a da yawa da suka shigo cikin k’asar Hausa kuma suna k’aruwa da Hausawan su ma Hausawan suna k’aruwa da bak’in al’ummun.

Harshen Hausa ya samu ci gaba inda har ya ari wasu kalmomi da al’adu na wasu al’ummu daban-daban kuma sun samu addinin musulunci sakamakon had’uwarsu da larabawa.

 4.0.4 Matsayin Bak’o A Addinin Musulunci


Addinin musulunci ya k’ara sa wannan lamari na kyautatawa bak’o da malam Bahaushe ke yi k’warin guiwa. Addinin musulunci shi ne addinin da Allah Mad’aukakin Sarki Ya aiko Annabi Muhammad tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi tare da Iyalansa da Sahabbansa da duk wanda ya yarda da shi tun daga farko har k’arshe.

Mafi yawan Hausawa sun yarda da addinin musulunci kuma duk abin da annabin Allah ya zo masu da shi, sai su kar’be shi da hannu biyu-biyu. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fad’i cewa, “Duk abin da Allah ya aiko mini gareku na isar”, kenan wannan magana na nuna cewa duk abin da Allah ya aiko ga mutane ta hanyar yin wahayi ga annabinSa, to annabi ya isar ga al’umma. Akwai wani Hadisi ingantacce wanda ke cewa, “Wanda ya yi imani da Allah da ranar tashin alk’iyama ya girmama Bak’onsa”.

Ta la’akari da wannan ne za a ce, addinin musulunci addini ne da ya samar da hurumin kyautata wa bak’o da karrama shi da kyautata masa. Baya ga kimar da malam Bahaushe ke gani na bak’o tun asali, sai ga shi addinin musulunci ya k’ara masa k’warin guiwa.

4.0.5 Karin Magangannun Da Suka Danganci Bak’o A Hausa.


Karin magana ya ta’ba kowane fanni na rayuwar d’an Adam musamman Bahaushe. Don haka ana samun ire-iren karin magana wanda ya shafi abubuwa daban-daban na rayuwa, halayya, da mu’amula da sauransu. A k’ark’ashin mu’amula za a samu kare-karen magangannu da dama wad’anda suke magana a kan bak’o. Misali irin wad’annan su ne kamar haka:

  1. Bak’o ra’ba ne, d’an gari kaba

  2. Bak’o d’an tafiya ne

  3. Shashanci gaba da bak’o

  4. Bak’on Nasara mai wuyar saukewa

  5. Mai jimirin rakiya, shi yake ganin kashin bak’o

  6. Bak’onka la’arinka

  7. Ba bak’o ruwa ka sha labari

  8. Gindin bak’o ba na zama ba ne

  9. Bak’on k’warai ake yankawa zakara

  10. Ragin bak’o na ‘yan masu gida

  11. Dare mak’urar yawon bak’o

  12. Bak’o babu sallama mugu ne

  13. Bak’on safe shi yake saukar da na yamma

  14. Da bak’o ya yi mantuwa, gwara ya k’ara da kayan masu gida

  15. Idon bak’o ba na ganin gari ba ne

  16. Lokaci bak’o ne

  17. Ni ba bak’on tsanani nake ba, ko tsakanin miji da mata ina iya kwana

  18. Yau garinmu inji mak’i bak’o

  19. Nauyi bak’on mai doki

  20. Sauki mutuwar bak’o a gari

  21. Kwantar da hankalinka makar ka yi bak’o ya mutu

  22. Karanbanin bak’o cud’anyar matar gida

  23. Shi ake gudu a raka bak’o ya dawo

  24. Gado ba bak’on tsirara ba ne

  25. Arha kayan bak’o

  26. Na ga bak’in ido

  27. Sallama mutuncin bak’o

  28. Arashin sani, bak’o rowan wanka

  29. Bak’in ciki ba bak’on uwar ‘barawo ba ne

  30. Bak’o ruwan gebe ne


Ire-iren wad’annan suna da yawa, kuma k’unshe suke da sak’wanni daban-daban a kan dalilai daban-daban.

Domin samun k’arin bayani dangane da wannan lamari za mu d’auki wasu daga cikin wad’annan karuruwan magana mu yi bayaninsu don a ga yadda lamarin ke gudana.

  1. Bak’o ra’ba d’an gari kaba:


Bahaushe yana kamanta bak’o da ra’ba saboda ra’ba takan sauka da sanyin yamma har zuwa wayewar safiya idan rana ta fara d’aukakowa sai ra’bar ta gushe kuma sai yamma. To shi ma bak’o yakan zo idan lokacin tafiyarsa ya yi sai ya koma. Saboda haka yadda ra’ba take zuwa ta koma, haka shi ma bak’o yake zuwa ya koma. Ta yiwu wani ya samu damuwa da wasu d’abi’un bak’o ko halayensa sai ya nuna wasu kuma su gaya masa cewa, ai bak’o ra’ba ne, waton idan ya yi hankuri wata rana ba zai ga bak’on ba.

  1. Bak’o d’an tafiya ne.


Shi mai tafiya idan bai kai ga inda zai je ba, dare ya yi masa, sai ya samu wani wuri ya la’ba idan safiya ta waye sai ya kama hanya. Wannan ke sa a ce bak’o d’an tafiya ne.

  1. Shashanci gaba da bak’o:


Gaba dai ita ce rashin shiri da wani ko rashin gaisawa da wani. Idan mutum yana da bak’o sai wani abu ya had’a su an fi son shi mai bak’o ya kasance mai hank’uri, idan kuma ya ce, ya yi gaba da bak’o to wata rana za a wayi gari bai ga bak’on ba, to da wa zai yi gaba, don haka wannan ya zama shashanci kenan.

 

  1. Bak’on Nazara mai wuyar saukewa;


Nasara dai su ne suka yi wa k’asar nan ta Hausa mulkin mallaka, kuma su ba Hausawa ba ne, don haka irin abincin da suka ci a wani yanki na Hausawa babu shi. Shi kuma Malam Bahaushe yana son ya kyautata wa bak’onsa.

  1. Mai jimirin rakiya shi yake ganin kashin bak’o:


Sau da yawa bak’o ba zai so ya yi amfani da bayin masu gida ba saboda kunya, kuma ga girki ko liyafa yana kwasa, wannan ya sa idan yana da lalura ta kashi galibi yakan bari sai duhu ya sauka ko kuma tun da safe ya yi sallama da masu gida ya kma hanya, saboda a dauri k’asa ake tafiya, idan ya samu d’an rakiya da zai masa rakiya mai yawa to lallai yana iya ganin inda bak’o zai kewaya don yin lalurarsa. A wata ma’ana kuwa ana cewa, duk wanda ya yi jimirin hira da bak’o yana samun sirrukansa.

  1. Bak’onka La’arinka:


Duk wanda ya yi bak’o zai yi k’ok’arin ya ga ya kyautta masa, ba ya son ya ji wani abin assha ya faru ga bak’on.

  1. Ba Bak’o ruwa ka sha labari:


A al’adar malam Bahaushe, idan ya samu sakewa to lallai yakan bayyana duk abin da yake damunsa. Wannan ya sa idan bak’o ya zo sai a tarbe shi da ruwa shi kuma da ya samu sakewa sai ya bayyana wasu labarai da suke a cikin ransa.

  1. Bak’on k’warai ake yanka wa zakara:


Zakara yana daga cikin tsuntsaye masu daraja na gida. Idan mutum ya samu bak’on da yake jin kunya sosai yakan yanka masa zakara ya yi masa liyafa da zai ci. Wannan ya sa Hausawa suka mayar da hankali wajen kyautta wa bak’onsu da suke jin nauyinsa.

  1. Ragin Bak’o na ‘yan masu gida ne:


Kasancewar bak’o mutum ne mai girma a wajen malam Bahaushe shi ya sa har kullum akwai inda ake ke’be shi ya ci abinci, idan ya raga to lallai ‘yan gidan ko barori sukan d’auke bayan ya k’are amfani da su.

 

  1. Bak’o babu sallama mugu ne:


Ga al’ada idan mutum ya bak’unci wuri ko wani gida yakan yi sallama, kuma ya nemi mai gida sannan ya samu izinin shiga gidan ko wurin ga mai gidan. To duk bak’on da bai yi sallama ba za a ga cewa mugu ne ba ya son a san shigarsa. (wato ‘barawo ne, sata ya zo ba ya son a san da shigarsa).

Wad’annan kad’an kenan daga cikin wad’annan karuruwan magana da muka kawo wad’anda suka danganci wannan aiki namu.

4.0.6. Kammalawar Babi


A wannan babin mun yi bayanin ma’anar bak’o inda har muka kawo ra’ayoyin masana game da Bak’o, wasu ma sun fad’a cewa shi ne wanda ya zo daga wani wuri mai nisa. Wasu kuma suke ganinsa a matsayin wanda ba a sani ba. Mun kawo ire-iren bak’o inda muka ce ya kasu kashi biyu wato bak’on mutum da kuma bak’on lamari/yanayi. Mun kuma yi bayanin matsayin bak’o a al’ummar Bahaushe, da matsayinsa a addinin musulunci. Mun kawo wasu karuruwan magana da suka danganci bak’o kana muna yi baynin wasu dag cikinsu.

 

Babi Na Biyar



  • Gabatarwa


A wannan babi na biyar nan ne za mu nad’e tabarmar wannan bincike, inda za mu yi tsokaci a kan Jawabin Kammalawa, Shawarwari da kuma Ta’arifin wasu Kalamomi.

5.0.1 Jawabin Kammalawa.


Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah Mad’aukakin Sarki Mai Kowa Mai komai, Mahaliccin sammai da k’assai da ya bamu ikon kammala wannan aikin Bincike. Yabo da jinjina ga AnnabinSa Muhammadu (SAW) Imamin Manzanni Cika makin Annabawa Muhammadu d’an Abdullah, da iyalan gidansa da Sahabbansa da magoya bayansa tun daga farko har k’arshe.

Hausawa kan ce, “Komai nisan dare gari zai waye” wannan ko shakka babu haka yake. Saboda a nan ne za mu nad’e tabarmar wannan bincike mai taken “Bak’o Ra’ba ‘Dan Gari Kaba: Nazari A Kan Tasirin Bak’o A Cikin Karin Maganra Hausawa”.

Kamar yadda aka gani a baya mun raba aikin nan namu gida biyar bisa ga tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko ya k’unshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da aka fuskanta.

A babi na biyu kuwa kamar yadda doka ta tanadar mun kawo Gabatarwar wannan babi, sannan muka biyo da Waiwaye A Kan Ayyukan da Suka Gabata kana muka yi byanin Salon Nazari da Tsarinsa.

A wannan babi na uku mun bayyana ma’anar karin magana inda muka kawo ra’ayoyi daga masana da manazarta daban-daban saboda aikin namu ya samu kar’buwa inda har muka ce zance ne gajere mai d’auke da ma’ana a cikin hikima. Mun kuma kawo kashe-kashen karin magana inda shi ma har muka kawo yadda wasu masana da manazarta daban-daban suka karkasa shi. Mun kuma kasa shi daidai da fahimtarmu inda muka kasa shi a kan na gargajiya da na zamani kuma muka bayar da misalai da za su yi k’arin haske. Tasirin karin magana ga rayuwar Bahaushe ya biyo baya kuma mun kawo wasu bayanai da za su tabbatar da haka. Sai illolin karin magana duk a cikin wannan babi.

Babi na biyar kuwa, mun yi bayanin ma’anar bak’o inda har muka kawo ra’ayoyin masana game da Bak’o, wasu ma sun fad’a cewa shi ne wanda ya zo daga wani wuri mai nisa. Wasu kuma suke ganinsa a matsayin wanda ba a sani ba. Mun kawo ire-iren bak’o inda muka ce ya kasu kashi biyu wato bak’on mutum da kuma bak’on lamari/yanayi. Mun kuma yi bayanin matsayin bak’o a al’ummar Bahaushe, da matsayinsa a addinin musulunci. Mun kawo wasu karuruwan magana da suka danganci bak’o kana muna yi baynin wasu dag cikinsu.

Shi kuwa wannan babi na biyar shi ne muka kammala aikinmu a cikinsa kamar yadda aka gani yana k’unshe da Jawabin Kammalawa da Shawarwari da kuma Ta’arifin wasu kalmomi.

 

 

5.0.2 Shawarwari


Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu d’alibai shawara su mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin k’ok’ari gwargwadon hali, su kasance masu gwazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to su yi k’ok’ari su d’ora daga inda muka tsaya na wannan bincike.

Muna kira ga wasu wad’anda ba nazarin wannan kundi sukai ba da su yi k’ok’ari su koyi darussan da ke cikin wannan kundi kar su yi k’asa a guiwa su kasance masu kyautatawa ga bak’insu kar su bari wannan abin alheri na kyautatawa ga bak’o ya wuce su.

5.0.3 Ta’arifin Wasu Kalmomi


        A cikin wannan kundin da yake yana da alak’a da adabin Hausa kuma abin da ya danganci karin magana mun yi amfani da wasu kalmomi da za su iya shige ma mai nazari duhu don haka za mu tsamo wasu daga cikinsu mu d’an yi fassara ga mai karatun wannan kundin don ya samu k’arin fahimta.

 

Bak’o -        -        - Matafiyi/Abin da ya zo.

Ra’ba -        -        - Wani yanayi mai alamun ruwa da yake sauka da                      yamma

‘Dan gari     -        - wanda aka iske a gidansu.

Kaba -        -        - Wani Haki da ake yin sak’ar tabarma ko tunk’ar                      igiya

Nasara         -        - Turawan Mulkin Mallaka

Saukewa     -        - Ajewa/ ba bak’on wurin zama.

Jimiri -        -        - Jajircewa/ Dagewa

La’ari -        -        - Matsala/Illa

Ragin          -        - Saura

Mugu -        -        - Mai cuta/ ‘barawo

Mak’ura      -        - Tuk’ewa/Dakatarwa Ko Karshe

Nauyi -        -        - Matsawa/takurawa

Karambani  -        - Salo

Mak’i Bak’o -        - wanda ba ya son ya yi Bak’o

Arha  -        -        - Sauk’i

Tsakani       -        - Tsakiya

 

Manazarta


https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments