Ta’addaci kamar yadda al’umma ke kallon abin wani mugun hali ne da matasa kan aiwatar a cikin al’umma. Ire-iren waɗannan munanan halayen sun haɗa da yin fashi da makami ko yin sara-suka ko yin bangar siyasa, ta yin yanke-yanke da wuƙaƙe ko amfani da miyagun makamai don cutar da wasu.
Ta’addanci A Tsakanin Matasa Ina Mafita?: Nazari Daga Cikin
Littafin Zaɓi Naka Na Manir Mamman Katsina
NA
HADIZA ISAH IDRIS
8283
FARIDA ALIYU USMAN 8318
SADAUKARWA
Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta ƙasa
(NCE) a Sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da Ƙere-Ƙere da ke Gusau a jihar Zamfara
ga mahaimafanmu kamar su Alhaji Isah Idris da Alhaji Aliyu Usman da Hajiya
Amina Muhammad da Hajiya Zainab Sani Hussaini. Allah ya saka masu da Alheri.
Amin.
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba
mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.
Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi
Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun
farko har ya zuwa ranar ƙarshe.
Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka muna domin ganin haƙarmu
ta cimma ruwa, musamman ga iyayenmu da suka jure da yin haƙuri da mu har muka
cimma wannan lokaci, kamar su Alhaji Isah Idris da Alhaji Aliyu Usman
Keɓantacceyar godiya zuwa ga Maryam Aminu ɗan Gusau, da Shafa’atu Isah Idris da
Babangida Isah Idris da Zulaiha Isah Idris da kuma Sumayya Adamu Sardauna.
Haka kuma muna miƙa kyakyawar godiyarmu ta musamman ga malamanmu Na
wannan sashe kamarsu; Malama Ibrahim Ahmad Ɗan’amarya wanda ya ɗauki tsawon
lokacinsa yana kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo ƙarshe Allah ya saka
masa da mafificin alherinSa amin. sai Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Malam
Haruna Umar Bunguɗu, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba,
Mal. Habibu Lawali Ƙaura, Mal. Aminu Saleh, Mal. Husaaini Aliyu da sauran su.
Godiya ta musamman ga Malam Hamisu tare da ‘yan uwa da abokan arziki baki ɗaya,
dafatan Allah ya saka masu da mafificin alhrinSa. Amin.
JINJINA
Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu
jinjina ma malaman mu musamman Mal. Ibrahim Ahmad Ɗan’amarya da ma wasu daga
cikin mutanen da suka taimake muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon
baya da suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan ɗalibai
da ma duk masu neman ƙarin haske dangane da nazari da muka gudanar a kan
“Ta’addanci A Tsakanin Matasa Ina Mafita?: Nazari Daga Cikin Littafin Zaɓi Naka
Na Munnir Mamman Katsina” muna masu roƙon Allah ya saka masu da maifificin
alheri. Amin.
Babi Na Ɗaya
1.0.1Gabatarwa
Ta’addaci kamar yadda al’umma ke kallon abin wani mugun hali ne da matasa kan
aiwatar a cikin al’umma. Ire-iren waɗannan munanan
halayen sun haɗa da yin fashi da makami ko yin sara-suka ko yin bangar siyasa,
ta yin yanke-yanke da wuƙaƙe ko amfani da miyagun makamai don cutar da wasu.
Kamar dai yadda aka saba wannan kundin zai ƙunshi babi-babi har babi biyar,
wannan babi na farko zai Ƙunshi Manufar Bincike da Farfajiyar Bincike da
Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Bincike.
Babi na biyu kuwa zai ƙunshi Waiwaye A Kan Bitar Ayyukan Da Suka Gabata da kuma
Salo Da Zubi Da Tsarin Nazari.
A babi na uku nan ne za mu kawo, Samuwar Rubutun Zube da Samuwar Gasar Rubutun Ƙagaggun
Labarai da Jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo da Ma’anar Ta’addanci da Dalilan Da
Kan Haifar Da Ta’addamci.
Babi na hudu zai Ƙunshi Nau’o’in Ta’addanci Kamar su Fashi da makami da sata da
Ƙungiyar Sara –suka da bangar siyasa. Sai kuma mu tsunduma a cikin nazarin
littafin inda za mu ga Na-Muduka a Matsayin Ɗan Ta’adda da da yadda ya su
kansa a gidan yari da shigar Na-muduka a soja, da shigarsa a cikin Ƙungiyar ɓarayi
da dai sauran abin da ya sauwaƘa.
Sai kuma babi na biyar inda a nan ne za mu kammala wannan bincike wato jawabin
kammalawa ne zai biyo baya tare da shawarwari.
1.0.2 Manufar Bincike
Manufar wannan bincike ba ta wuce abin nan da Hausawa ke ce ma “in mutum ya san
farkonsa bai san ƙashensa ba” ko kuma ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. Abin
nufi a nan shi ne sau da yawa a cikin al’umma akan samu lalacewar tarbiyya ko
daga gida ko dai daga wajen abokai, wato dai rashin kulawa ga iyaye kan sa
‘ya’yansu su shiga wani hali maras kyau.
Dangane da wannan ne muke son mu ɗora alƙalaminmu a kan irin lalacewar matasa a
yau ta yadda suke shiga hanyoyi daban-daban na ta’addanci a tsakaninsu wanda
daga bisani yana iya kai ga sauran jama’ar gari.
Don haka wannan kundin bincike yana da ƙudurin yin tsokaci a kan wannan
ta’addanci da ake yi a wannan zamani sakamakon siyasa. Haka zalika wannan
binciken zai yi bayanin hanyoyin da suka dace iyaye da ‘yansiyasa da hukuma su
bi su shawo kan waɗannan matsaloli.
1.0.3 Farfajiyar Bincike
Idan aka ce farfajiya ana nufin da’ira ko yankin wani al’amari ko muhalli ko
kuma bakin iyaka na wani abu.
Wannan bincike mun gudanar da shi ne a ɓangaren adabin Hausawa, sai dai domin
samun sauƙin gudannarwa mun keɓance aikin namu a kan littafin Zaɓi Naka wanda
Munnir Mamman Katsina ya rubuta.
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na
marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka waɗanda suka gabata
domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi
daban-daban.
Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi
daban-daban don ƙarin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta
hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.
Kamar yadda bayani ya gabata mun lura da cewa, dukkan mai aikin bincike
dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma
cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar
da wannan bincike namu domin kuwa har ɗakunan karatun wasu manyan
makarantu mun leƙa, inda muka binciki wasu ayyuka na magabata kamar littafai da
kundaye da muƙalu da mujallu da jaridu. Hala kuma za mu yi ƙoƙarin zantawa da
wasu daga cikin masana a kan irin yadda wannan lamari na ta’addanci ke faruwa.
Matsalolin Bincike
Wannan bincike namu mun gudanar da shi ne a kan hanyoyin da suka dace, na irin
hanyoyin da ake bi wajen samun bayanan da suka dace ta hanyoyi da dama. Mun ci
karo da matsaloli da dama wajen binciken mu kamar haka.
Rashin isassun kuɗin mota, da matsalar haɗuwa da waɗansu masana da muke tuntuɓa
wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kuɗin
mota domin zuwa wajen waɗansu mutane da suke da masanniya game da wannan
lamari na ta’addanci, sai mu iske ba su nan. Haka ma kowa ya san irin halin da
ake ciki a ƙasar nan na rashin tsaro, a inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole
sai da taka tsantsan.
Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu ɗalibai mata
masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da
wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama sun sha kanmu. Daga cikinsu
akwai
Matsalar karɓar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji
da ta ƙarshen zangon karatu.
Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka haɗa da girke-girken
abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk waɗannan
matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo da su .
Akwai matsalar tuntuɓar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu suna ganin
kamar za mu ɗauki sirrinsu ne mu watsa wa duniya.
Haka ma akwai matsalar yawan ɗaukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro
bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta ɗauke. Kaɗan kenan daga
irin matsalolin da muka ci karo da su.
Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka,
wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun
fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kuɗi da za mu buga wannan aiki namu.
Haka kuma akwai matsalar haɗuwarmu idan mun yi alƙawali, kuma idan za mu tafi
wajen ganawa da waɗanda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne
a same su ba.
Haka akwai sha’anin rashin lafiya yakan kama magidanci , ko kuma halin tafiya
wajen ƙaro ilimi wato a bangaren su masana.
Ba nan kaɗai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar karamcin lokaci.
Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a
cikin shekara ɗaya.
Kammalawar Babi.
Wannan babi na ɗaya shi ne babin da aka yi shimfiɗa a kansa dangane da wannan
bincike, kuma shi wannan babi ya ƙunshi dukkan abin da za a yi a cikin wannan
bincike da kuma yadda za a yi shi. Misali a cikin babin an yi gabatarwa inda
aka ce, za a karkasa kundin nan kamar yadda doka ta tanadar wato babi-babi har
babi biyar, an kuma faɗi duk abin da za a yi a kowane babi. Haka kuma an yi
bayanin hanyoyin bincike da Farfajiyar bincike da manufar bincike da kuma
matsalolin bincike.
Babi Na Biyu
Wannan babi zai ƙunshi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, tare da Salon
Nazari da tsarinsa.
2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.
Ayyuka da suka gabata fage na adabin Hausawa suna da yawa, saboda haka wannan
aiki namu ba shi ne na farko ba a wannan fage. Don haka ya zama wajibi a garemu
da mu waiwayi wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa da wannan aiki domin mu ga
inda suka zo daidai da kuma inda suka sha bambam, ko kuma suke da dangantaka da
namu.
Daga cikin ayyukan da suka gabata a wannan fage akwai; bugaggun littafai da
kundaye daban-daban, da suka gabata a kan fannoni daban-daban na adabin Hausawa
ga wasu daga cikinsu;
Yahaya I.Y (1988), “Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubucen Hausa” a cikin
wannan littafi marubucin ya kawo tarihin samuwar rubutun boko, da shigowar
addinin musulunci da shigowar Turawa a ƙasar Hausa. Marubucin ba a nan kaɗai ya
tsaya ba ya taɓo har yadda aka samu rubutun zube a ƙasar Hausa kamar dai ƙagaggun
Labarai da kuma yadda aka shirya yin gasar samar da su.
Wannan aikin na Yayaha I.Y yana da dangantaka da namu aikin saboda ya bayyana
yadda aka samu ƙagaggun labarai da kuma rubutun Hausa kansa. Amma kuma inda
muka samu bambanci da shi shi ne, shi ya yi bayanai da yawa a cikin littafin da
suka haɗa da zube, waƙa, tarihi, samuwar rubutu da shigowar addinin musulunci
da dai sauransu.
Sarkin Sudan (2000) ya rubuta kundi mai taken “Magani Da Siddabaru A Cikin Ƙagaggun
Labarai Na Hausa” Sarkin Sudan ya rubuta wannan kundin ne domin samun digiri na
biyu a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, marubucin ya tsara kundinsa
bisa ga tsarin babi-babi kuma ya yi bayanin yadda ake yin siddabaru da yadda
ake samun magani. Ya kuma bayar da ma’anarsu tare da yin bayani dalla-dalla.
Wannan aikin na Sarkin Sudan yana da alaƙa da namu aikin, saboda shi yana
magana a kan magani da siddabaru a cikin ƙagaggun labarai na Hausa, waɗannan ƙagaggun
labarai su ne suka ja hankalinmu muka dubi ta’addanci a ciki. Inda kuma muka
sha bamban da shi shi ne, shi yana bayani ne a kan magani da siddabaru mu kuma
muna magana ne a kan ta’addancin da matasa suke yi amma kuma sai muka taƙaita
lamarin ga littafin Zaɓi Naka.
Datsimma (2002), ya rubuta kundi mai taken “Tarbiyya A Littattafan Ƙagaggun
Labarai Na Hausa” wannan kundin ya rubuta shi ne domin samun digiri na biyu a
Jami’ar Bayero da ke garin Kano, Dutsimma ya kawo bayanai da dama da suka shafi
yadda tarbiyya take a cikin ƙagaggun littattafai, a bisa ga wannan ne ma yake
ittifaƙin cewa kusan dukkan littattafan zube suna da ƙagaggun labaran da suka
shafi tarbiyya.
Dangane da aikin da Dutsimma ya yi muna ganin cewa, aikinmu yana da alaƙa da
nasa aikin saboda ya taɓo ƙagaggun labarai sai dai shi aiki nasa ya taɓo mafi
yawan littafai amma mu kuma namu aikin mun keɓance shi ne ga liiatfin Zaɓi
Naka.
Muktar (2004), “Nazarin Ƙagaggun Labarai” a wannan littafin marubucin ya yi
tsokaci a kan asalin rubutun zube da rubutun boko da hanyoyin da ake bi wajen
yin nazarin ƙagaggun labarai. Wannan aikin da Muktar ya yi ya taimaka muna
sosai yayin da muke gudanar da namu aikin saboda mun ga irin yadda ake yin
nazarin littafin ƙagaggen labari.
Gusau S.M (2008), ya rubuta wani lttafi mai suna, “Dubarun nazarin adabin
Hausa” a wannan littafi ya kawo dubarun da marubuta ke amfani da su. Gusau ya
kawo hanyoyi daban-daban da ake iya bi domin nazarin adabin larabci da na
Hausa, ba nan kaɗai ya tsaya ba sai da ya yi tsokaci a kan wasu shaihunnan
malamai da suka yi aiki a kan nazarin rubutun zube.
Wannan littafi na Gusau ya taimaka ainun wajen gudanar da wannan aiki namu,
saboda da bazar sa ne muka taka rawa, yayin da muke nazarin littafin Zaɓi Naka
muna aza shi saman mizanin abin da yake faruwa a yau.
Ɗan’amarya (2012), ya rubuta kundin digirinsa na biyu a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato mai taken “Tarihin Gasa Da Gudummuwarta Ga Cigaban Adabin Hausa”
manazarcin ya kawo tarihin samar da gasar ƙagaggun labarai da kuma tarihin
kyautukan da suka samar da yadda marubutan suka samr da littattafai tare da
Gudummuwar da suka bayar ga cigaban adabin Hausa.
Da wannan ne muke ganin cewa, aikin Ɗan’amarya yana da dangantaka ta ƙut da ƙut,
saboda kamancin shi da namu ta fuskar rubutattun labaran Hausa, musamman waɗanda
suka taka rawar gani daga cikin gasar da aka gudanar. Inda kuma muka samu
bambanci shi ne, shi yana kallon tarihin gasa da gudummuwarta wajen samar da ƙagaggun
labarai
2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa
Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin
mutum.
Salon nazari wata hanya ce ta isar da saƙo da bayyana tunanin mutum. Haka kuma
salo ya na nufin hanyoyin da marubuci ko mawallafi kan bi domin yi wa harshe
kwalliya ko kuma yi wa rubutun sa ado, haka kuma wata dabara ce da marubuci kan
yi amfani da ita domin samun sauƙin isar da saƙonsa a cikin rubutunsa. A
dalilin haka ne mu ka yi amfani da hanyoyin guda uku na nazarin salo.
Na farko dai irin kalmomin da muka yi amfani da su, kalmomi masu sauƙi ne. Sai
kuma muka saka su a inda ya dace.
To anan za mu yi amfani da salo mai jan hankali, domin mu ja hankalin mai
karatu ya karanci wannan kundi, ba tare da wata wahala ba ko ya ƙagara da
karatun wannan bincike ba.
Idan mai karatun wannan aiki ya kwantar da hankalinsa ya biyo mu cikin natsuwa
to zai ga irin matakan salon da muka yi amfani da shi wajen rubata wannan kundi
saboda mun yi amfani da littatafai masu saukin fahimta.
An kuma yi amfani da nuna ƙwarewar harshe sosai a cikin wannan kundi saboda an
yi amfani da kalmomi masu burgewa da kuma armashi waɗanda ke sa mai karatu ya
ji daɗi a zuciyarsa, wannan shi zai sa binciken namu ya yi kwarjini da farin
jinni ga makaranta.
2.0.3 Kamalawar Babi
A cikin wannan babi na biyu mun yi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata inda
har muka ci karo da wallafaffun littattafai da kundaye, kuma duka mun kawo
gwargwadon abin da muka samu, sannan muka faɗi inda suke da alaƙa da namu da
Kuma inda muka sha bamban da su. Haka kuma mun ɗan yi tsokaci a kan salon
nazari da tsarinsa duk a wannan babi.
Babi Na Uku
- Gabaratwa
A wannan babin za mu ya magana a kan ma’anar Rubutu da kuma ma’anar Rubutun
Zube. Za mu kuma duba Gasar Ƙagaggun Labarai na Hausa da aka yi daga ciki kuwa
har da Tarihin Samuwar Ƙagaggun Rubutattun Labarai sai mu naɗe babin.
3.01 Ma’anar Rubutu
Kamar yadda aka riga aka sani cewa, rubutu wasu alamomi ne da suke wakiltar
zance ko magana. Wannan ya sa masu ilimi na rubutu sukan samu lokaci su tsaya
su tsara waɗannan alamomi wato rubutu don su bayyanar da abin da ke cikin
zuciyarsu ko su isar da wani saƙo.
Wasu masana tuni sun tofa albarkacin bakinsu game da ma’anar rubutu. Kuma
dukkansu sun tafi kan cewa, alamomi ne masu wakiltar magana, kuma duk sun yarda
cewa, alamomin suna isar da wani saƙo.
3.0.2 Ma’anar Rubutun Zube
Masana da manazarta da dama sun yi tsokaci a kan ma’anar rubutun zube, kuma ga
wasu daga cikinsu:
Yahaya I. Y. (1988) ya ce, “Rubutun zebe, labari ne ƙagagge kuma shiryayye, a
cikin hikima da fasaha da aka gudanar don ƙwarewa.
Shi kuwa Ahmad Magaji (1982) ya bayyana rubutun zube da cewa, “Rubutun Zube
labari ne da mawallafa suke shiryawa da ka, sannan suka rattaba a zube.”
Rubutun zube dai shi ne duk wata wallafa da aka ƙago aka rubuta kara zube ba a
shirin waƙa ba ko wasan kwaikwayo
Wannan shi ne rubutun zube.
3.0.3 Gasar Ƙagaggun labarai
Gasar ƙagaggun labarai
ta samo asali ne tun lokaci mai tsawo, a kan sanya kyaututtuka ko lada ko wani
abu a matsayin goro ga wanda ya fi nuna bajinta ko ya zama gwani a cikin
gwanaye.
Misali, a shekarun da suka gabata hukumar da aka kafa a ƙasar Ingila domin ta
kula da harsunan mutanen Afirka, ta tsara yadda zata rinƙa gudanar da gasa tare
da cin kyautar kuɗi duk shekara, tsakanin al’ummun Afirka ta hanyar shiga gasar
rubuta ƙagaggun Labarai cikin harsunansu. An fara shirya wannan gasar ta
harsunan mutanen Afirka, a shekarar 1930.
Jami’an da ke kula da harkokin ba da ilimin a ƙasashen Afirka, su ke wakilta waɗanda
suka shiga gasar ta hanyar taimaka masu da sanin dokokin da hukumar ta tsara
domin shiga gasar, tare da ɗaukar Labaran da ‘yan Afirkan suka rubuta na shiga
gasar, su kai wa jami’an hukumar da ke shirya gasar a can Ingila domin nazari
da bayar da shawarwari kan yadda za a inganta hanyar rubutun adabin harsunan da
suka shiga gasar.
Shiryawa da gudanar da irin wannan gasa na daga cikin hanyoyin da aka bi domin
samar da ingantaccen adabin harsunan Afirka. Har ila yau, bayan an gama nazarin
Labaran da aka aiko domin shiga gasar, ana aikawa da ladan kuɗi daga hannun
gwamnati da jami’an da suka wakilci masu shiga gasar, domin a raba wa waɗanda
suka shiga gasar, kusan muna iya cewa wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da ya
assasa shirya gasa a rubutun ƙagaggen labari ƙarƙashin adabin Hausa. (Afrika,
1933:102-103 vol.vi No.1).
3.0.4 Samuwar Gasar Rubutattun Ƙagaggun Labarai
Tarihi ya nuna cewa, ƙagaggun labaran Hausa ba su daɗe da samuwa ba, musamman
idan aka kwatanta shi da rubutacciyar waƙa wadda ta soma wanzuwa tun farkon
shigowar addinin musulunci a cikin ƙasar Hausa, duk da ire-iren rubuce-rubucen
da Turawa ‘yan mishan da na mulkin mallaka suka yi a cikin harshen Hausa, kuma
babu wanda aka kira ƙagaggen labari saboda babu wanda ya ƙunshi ƙaguwa kai
tsaye. Dukkan rubuce-rubuce nasu (Turawa) a cikin Hausa sun tsara su ne don
koyarwa a can ƙasashensu.
An fara tunanin samar da litattafai a cikin Hausa ne kuma waɗanda za a yi
amfani da su domin koyar da Hausa, bayan da aka kafa makarantun ilimin zamani a
garuruwa daban- daban na Arewacin Nijeriya.
Makaranta ta farko da aka fara buɗewa ta gwamnati ita ce, makarantar Hans
Vischer (ɗan Hausa) a Shekarar (1909) a garin Kano. Tun daga lokacin da aka
kafa wannan makarata sai aka lura akwai ƙaranci litattafan koyarwa, wannan
matsala ta ƙarancin litattafan koyarwa a makaranta ita ta jawo aka kafa hukumar
fasara wato (Translation Bureau) a ƙarƙashin shugabancin Mr. C.E.J Withing a
cikin shekarar 1929.
An fara zaunar da hukumar ne a garin Kano a unguwar Nasarawa gidan ɗan Hausa
(Hans Vischer) a cikin shekarar 1931 aka mayar da ita a mazauninta na dindindin
a Birnin Zariya. Kuma a shekarar 1932 aka mayar da shugabancin ta ga hannun
wani Bature mai sauna R.M East.
Kamar yadda suna hukumar ya nuna, aikin da ya rataya a wuyan hukumar shi ne,
fassara labarai daga wasu harsuna zuwa harshen Hausa, haka kuma ita ke da
alhaki wallafa litattafai a cikin harshen Hausa da kuma shirya litattafai manya
da ƙanana don karantarwa a makarantu da kuma taimakawa ‘yan ƙasa su riƙa
wallafa litattafai da kansu. Hukumar ta fassara littattafai da yawa kamar:
- Dare Dubu Da Ɗaya
- Labarun Hausawa Da MaƘwabtansu
- Labaru Na Da Da Na Yanzu
- Saiful Muluki
- AbdulƘadir Tanimud Dari
- Al’amurran Duniya Da na Mutane da sauransu
Wani yunƙuri wanda kuma shi ne ya haifar da samuwar tsintsar ƙagaggun labaran
Hausa shi ne, na canza sunan hukumar fassara zuwa hukumar Talifi da aka yi a
shekarar 1932. saboda haka sai nauyin da ke kan hukumar bai tsaya a kan fassara
kawai ba, har ma da wallafe-wallafen litattafai na fannoni daban-daban a cikin
harshen Hausa.
A daidai wannan shekara ne ta 1933 Daraktan ilimi na Arewacin Nijeriya Hans
Vicher ya ƙaddamar da shirin gasar rubuta ƙagaggun labarai, don samar da ƙarin
litattafan karatu a cikin rubutun zube. Saboda haka aka miƙa ragamar gudanar da
gasar ga wannan hukuma ta talifi kai tsaye, sai shugabanta Dr. R. M East ya
zagaya manyan garuruwan Arewacin Nijeriya ya sanar da malamai masu ilimin
zamani da na arbiyya bayani gasar da kuma irin labarin da ake so ga duk mai
sha’awa. Malamai da yawa sun rubuta labarai sun aika sai dai guda biyar ne
kawai suka yi nasarar cin gasar. Waɗannan su ne:
LITTAFAI
MAWALLAFI
Ruwan Bagaja
Mal. Abubakar Imam
Ganɗoki
Mal. Bello Kagara
Shehu
Umar
Alhaji Abubakar Tafawa ɓalewa
Jiki
Gagayi
John Tafida Umar da Dr. R.M East
Idon
Matambayi
Mal. Muhammadu Gwarzo
Waɗannan littattafan su ne littattafan ƙagaggun Labaran Hausa da aka fara
samarwa bisa shawarar Turawan mulkin mallaka.
Tun daga shekarar 1933 ba a ƙara samun wata fitacciyar gasar ƙirƙira ba sai a
shekarar 1971, inda kamfanin Wallafa Littafai na Zariya wato NNPC ya fito da
wata gasar ta ƙirƘira rubutun zube, domin samar da sababbin litattafai na
karatu da nishaɗi. Kamar dai yadda waɗancan suka gabata, ita ma wannan gasar ta
jawo hankalin marubuta da dama. Da ƙarshe an tankaɗe kuma an rairaye daga cikin
litattafan da aka samu, an tace litattafai guda takwas waɗanda suka tsallake
siraɗin ƙa’idojin da aka shimfiɗa wa gasar, amma daga waɗannan litattafai guda
uku kawai kamfanin ya sami damar wallafawa.
Litattafan da suka yi dace suka yi nasara a ƙarshe aka wallafa litattafan su
ne:
‘So Aljannar Duniya; Na hafsat Abdulwahid wanda ita ce mace ta farko da ta fara
yin fice a rubuta littafin ƙirƙira a adabin Hausa, kuma ta zama na ɗaya a
gasar.
Amadi na Malam Ama; Na Magaji Ɗanbatta shi ya zo na biyu a gasar. A ƙarshe sai,
Mamallakin Zuciyata wanda wani ɗan jarida ya rubuta wato, Suleman Ibrahim
Katsina.
Wannan al’amari na gudanar da gasa fagen ƙirƙira yana bayar da gagarumar
gudunmuwa ta fanni da dama musamman samar da litattafan karantawa a makarantu
da nishaɗi.
Bayan kammala waccan
gasa, sai shekarar da ta gabata, sai a cikin shekarar 1982, aka sami wata
sabuwar gasar wadda hukumar yaɗa Labarai ta Tarayya da ke Ikko ta sanya gasar ƙirƙirar
rubutun zube cikin harsunan ƙasa wato Hausa, Yarbanci da kuma Ibo. A wannan
karon ma littatafai da dama sun shiga gasar wasu sun yi nasara wasu kuma
akashin hakan. A harshen Hausa littafin da ɗan jaridar nan Suleman Ibrahim
Katsina ya rubuta mai taken, ‘Turmin Danya’ shi ya zo na ɗaya. Sai waɗanda suka
rufa masa baya kamar haka:
‘Tsumingiyar kan Hanya’, na Musa M. Bello
Ƙarshen Alewa Ƙasa, na Bature Gagare
‘Zaɓi Naka’, na Malam Mannir Katsina
‘Soyayya tafi kuɗi’ na Habib A. Alƙalanci
Ɗausayin Soyayya’ na MuhƊ B. Yahuza.
Bayan kammala gasar an bayar da kyaututtuka, kuma kamfanin NNPC da ke Zariya ya
ɗauki nauyin buga waɗannan litattafai, kuma daga nan aka ci gaba da samun
gasanni nan da can amma ba su yi wani cikakken tasiri ba, saboda waɗanda suka ɗauki
nauyin shirya gasar suna da ƙarancin ƙarfin ɗaukar gasar, ta yadda za ta karae
ko’ina.
3.0.5 Kammalawar Babi
Wannan babin ya ƙunshi ma’anar rubutu da ma’anar rubutun zube da Gasar ƙagaggun
labarai na Hausa da kuma samuwar ƙagaggun labaran Hausa, a cikin mun yi bayanin
ƙagaggun labarai na Hausa waɗanda muka ce sun samo asali ne tu zamanin Turawan
mulkin mallaka, kuma wannan lokaci ne ya yi daidai da shekarar 1933, sai dai
kuma ko bayan wannan lokaci an yi ta yin gasa makamanciyar wannan kuma ana
samar da littattafai, misali idan aka duba shekarar 1982, ai an samar da wasu
litattafai da da suka haɗa da ma littafin da za mu yi nazari a cikinsa.
Babi Na Huɗu
- Gabatarwa
Wannan babi zai ƙunshi ma’anar ta’addanci da dalilan da ke haifar da ta’addanci
da nau’o’in ta’addanci kamar su fashi da makami da sata da kara-suka da bangar
siyasa. Za mu kuma yi nazarin littafin Zaɓi Naka kuma mu danganta shi da wannan
take na kundinmu saboda mu ga yadda rayuwar matasanmu take a yau.
4.0.1 Ma’anar Ta’addanci
Ta’addanci dai kamar yadda aka sani wata mummunar ɗabi’a ce, da wasu mutane
suke aikatawa kuma wannan ɗabi’a sam ba ta dace da kasancewa a cikin jama’a ba.
Wasu mutane da suke ba su da wata takamaimiyar sana’a su ne suke gudanar da
ta’addanci, kuma suka yi shaye-shaye su kawar da hankalinsu kafin su fara
aikata wannan lamari na ta’addanci. Yayin gudanar da ta’addanci akan yi amfani
da wasu makamai da suka haɗa da; takobi, adda, gariyo, hanwagi, wuƙa, mashi,
tsini reza, aska, da dai sauransu.
‘Yan ta’addan sukan sara ko su yanka duk wanda suka tarar a lokacin da suke
gudanar da wannan tabi’ar. Ta’addanci ba sabon al’amari ba ne saboda su ‘yan
ta’addan tuni sun jima suna cin karensu babu babbaka, kuma hukuma ta yi biris,
ba ta ɗauki wani mataki da zai hana wannan ɓarna ba.
4.0.2 Dalilan Da Kan Haifar Da Ta’addanci
Akwai daililai da yawa suke hardasa wannan baƙar ɗabi’a ta ta’addanci daga ciki
kuwa har da:
4.0.2.1 Lalacewar Tarbiyya
Wannan kusan ana iya cewa duk daga cikin dalilan da suka hardasa wannan baƙar
tabi’a shi ne babban dalili da ke saka matasa a cikin sha’anin harkar
ta’addanci. Sau da yawa yaro zai taso a gaban iyayensa sai su saka masa ido ba
su kula da tarbiyyarsa ko don gudun ɓacin ransa ko don nuna soyayya ga yaran.
Wannan lamari na rashin kula da tarbiyyar yara yana sa idan suka girma suka
zama matasa ba su tsoro ko shakkun kowa, kuma sai su aikata abin da suka ga
dama.
Irin wannan lamari iyaye ne suke yin ko-oho ga lamarin kula da yaransu, wato ba
su aikasu makarantu kamar na addini da na zamani kuma ba su tsawatawa idan
yaran suka aikata abin da ba daidai ba. Idan kuwa iyaye ba su tsawata ma yaro
ba ai ko wani ya tsawata masa ba wani jin tsoro za su yi ba, kuma ba su ganin
girman kowa idan suka tashi aikata wani abu ko da ba mai kyau ba ne. Saboda
haka da wannan muke ganin cewa, wannan lamari na rashin tarbiyya yana daga
cikin dalilan da suke hardasa wannan lamari na ta’addanci.
4.0.2.2 Shaye-Shayen Miyagun Ƙwayoyi
Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi yana daga cikin dalilan da suke hardasa
ta’addanci. Saboda idan muka lura za mu ga cewa, ba kowa ne zai iya aikata wani
aiki na ta’addanci a bainar jama’a ba, ba tare da ya kawar da hankalinsa ba.
Shaye-shaye wani lamari ne na shan kayan barasa (Maye) don kawar da hankalin
wanda yasha. Haka kuma shaye-shaye yana iya zama wani yanayi na shan ƙwayoyi ko
wani sinadari da zai kawar da hankali na ɗan wani lokaci. Wannan yanayi na shan
kayan maye domin kawar da hankali da aikata wani abu galibi matasa ne ke yinsa
kuma sukan sha kayan mayen ne idan za su aikata wani lamari na ta’addanci kamar
sare-sare ko zage-zage ko tashin hankalin jama’a ko dai wani abu daban. Matasan
kan sha kayan maye da suka haɗa da: giya, sholisho, kodin, Fetur, ƙwaya, babba
juji, tabar wiwi, hodar ibilis, roce, da dai sauransu. Duk waɗannan kaya da
muka zano kaya ne da mashaya ke amfani da su kuma kayan suna kawar da hankalin
duk wanda ya sha su.
4.0.2.3 Lalacewar Hukuma
Hukuma ita kanta tana daga cikin manyan dalilan da suka sanya matasa
ta’addanci. Hukuma dai ta bayar da gagarumar gudummuwa wajen samar wa
ta’addanci gindin zama a cikin jama’a, saboda gazawa wajen samar wa matasa
aikin yi da kuma yi masu hukuncin da ya dace a lokacin da suka aikata aikin
ta’addanci.
Rashin adalcin da hukuma ke yi wajen hukunta wanda ya aikata ta’addanci shi ne,
wani lokaci ko sun kama wanda ya aikata ta’addancin sai su sake shi da an basu
kuɗi. Ko kuma wani lokaci sai a gaya ma jami’an tsaron da suka kama cewa, yaron
wane kaza ne ko a nuna masu cewa, idan suka hukunta yaran ko yaron su ma za a
iya raba su da aikinsu. Wannan duk sakacin da hukuma take da shi ne wajen
hukunta mai laifi. Kuma wannan yana ƙara wa yaran ƙwarin guiwar sake aikata
ta’addanci.
4.0.2.4 Munanan Abokai
Munanan abokai suna daga cikin dalilan da ke hardasa ta’addanci, wannan kuwa
yana faruwa ne a lokacin da mutum bai dace da abokai na gari ba, wato ya samu
abokai masu cuɗanya da irin halin da bai dace ba. ‘Yan ta’adda dai suna nan
cikin jama’a sawƙe, kuma sau dayawa sukan nemi su mayar da duk wanda ya kusance
su daga cikinsu. Idan matashi ya haɗu da matashi ɗan uwansa kuma aka yi sa’a ba
su da aikin yi sai suka fara tunanin yadda za su yi su biya wata buƙata da ke
gabansu in ba a yi sa’a ba komai suna iya shiryawa kuma su aikata.
Irin wannan lamari ko mutum yana da karatu indai ba mai zurfi ba ne ko mai
amfani sosai sai ka ga ya samu kansa a cikin ta’addanci sakamakon haɗuwarsa da
abokin da ke aikata ta’addanci. Sau da yawa za ka ga mutum ya yi karatu amma ya
kasance a cikin wannan lamari, ko dai a yi shaye-shaye da shi ko a nemi matan
banza, ko a dinga zuwa gidan wani ɗan siyasa yana ba da kuɗi ana shaye-shaye
ana cin zarafin duk wanda ake buƙatar a ci zarafinsa.
4.0.3 Nau’o’in Ta’addanci
Sanin jama’a ne wannan lamari na ta’addanci ya kasu kashi-kashi akwai wasu
nau’o’i da muka ci karo da su waɗanda suka haɗa da:
4.0.3.1 Fashi Da Makami
Kamar dai yadda ma’anar ta nuna ta ta’addanci cewa, wata mummunar ɗabi’a ce
wadda ake aikata wa da makami wani lokaci. Wannan ma haka za a ga cewa, fashi
da makami shi ma da makami ne ake yinsa wannan ma ya isa a gano cewa, shi na ɗaya
dga cikin nau’o’in ta’addanci. Ko bayan haka za a ga cewa, ta’addanci ba wani
abin abin da ake so ba ne, wato ma ba ɗabi’a mai kyau ba ce haka shi ma Fashi
da makami ba ɗabi’a mai kyau ba ce.
Fashi da makami wani lamari ne da wasu ɓata gari ke yi su tanadi makamai da
suka haɗa da bindiga, da takobi da adduna da dai sauran makamai, wani lokaci
suka shiga daji su tare hanya duk wanda ya zo sai a tare shi a anshe abin da ya
samo ko ya zo da shi. Haka kuma suna iya zuwa gida-gida su yi amfani da makamai
su ƙwace duk abin da mai gida ya mallaka ko kuɗi ko wasu kadarori.
4.0.3 2 Sata
Sata dai ita ma wata muguwar sana’a ce da wasu masu busasshiya zuciya ke
aikatawa. Sata ita ce wani ko wata ko wasu mutane da suke da wannan mummunan ɗabi’a
su ko ya ko ta ɗauke kayan wani ko wata ko wasu ba tare da sanin su ba ko
ba tare da sun gani ba. Ita sata akan yi ta ne ba tare da mai kaya ya gani ba.
Kamar dai yadda aka riga aka sani cewa, sata mummunar ɗabi’a ce kuma ana iya a
aikata ta da makami ko da kuwa ba a sari kowa ba ko ba a harbi kowa ba. ɓarawo
ko ɓarayi ko ɓarauniya galibi idan za su yi sata suka je da wani makami domin
su kare kansu in aka rutsa su ko kuma su yi barazana da shi su karɓe kuɗin
wanda suka yi wa barazanar ko kaya masu amfani da wannan makami.
Wannan lamari na sata mummunar ɗabi’a ne kuma yana daga cikin nau’o’in
ta’addanci saboda ita sata ba ɗabi’ar ƙwarai ba ce kamar yadda ta’addanci ba ɗabi’ar
ƙwarai ba ce, haka kuma dukkansu ana yin su ne da makamai.
4.0.3.3 Ƙungiyar Sara-Suka
Ita wannan ƙungiya ba ƙungiyar kirki ba ce, kuma tana daga cikin haramtattun ƙungiyoyi
saboda ita babban aikinta shi ne ta’addanci. Idan mutum ɗan ta’adda ne za ka ga
ko yaushe yana yawo da makamai da zai yi ta’addanci da su. Sau da yawa samari
ko matasa waɗanda suke cuɗanya da wannan lamari za ka gan su da makamai a cikin
jikinsu kamar wuƙa
ko adda ko gariyo ko wani tsini ko dai wani abu da zai iya yin illa da shi.
4.0.3.4 Bangar Siyasa
Bangar siyasa dai wani al’amari ne da matasa suka sa kansu na ɗaukar makamai da
shaye-shaye a lokacin siyasa domin su ci ma mutane da abokan adawa mutunci, ko
zarafi a lokacin kamfe ko zaɓe. Mafi yawan waɗannan halaye sun samu asali ne
daga abin da ‘yan siyasa suke taimaka wa matasan da shi ne kamar makamai da kuɗin
shaye-shaye.
Bangar siyasa “wata ɗabi’a ce da ‘yan siyasa suka ƙirƙiro a cikin wannan ƙarni
na ba matasa makamai da kuɗi su yi shaye-shaye na kayan maye domin su ci
mutunci abokan hamayyarsu.
Wannan al’amari na da ban tsoro ƙwaran gaske, ganin cewa al’amarin sai daɗa ƙaruwa
yake yi, kuma matasa na daɗa tsunduma a cikin waɗannan miyagun halaye na
shaye-shaye.
Bisa ga jin ra’ayoyin waɗannan mutane da muka yi, mun gano cewa, bangar siyasa
ba wani abu ba ce illa, ‘yunƙurin da matasa ke yi na zuga ɗan takara da kuma
kururuta shi da tallata shi ba ta hanyar waƙa ba, haka kuma akwai suka ga
abokan adawa, tare da yin ɓatanci a gare su domin dushe tauraronsu’.
Wannan yanayi na banga a wannan lokaci ba abu ne mai kyau ba saboda ya surka da
cin zarafin jama’a, shaye-shaye, sata, rashin kunya, ta’addanci da dai wasu
haramtattun abubuwa da doka ba ta yarda da su ba.
4.0.4 Dalilan Da Ke Haifar Da Bangar Siyasa
Akwai dalilai da yawa da suke haifar da bangar siyasa da suka haɗa da:
1.
Rashin ilimi ga matasa:
Da yawa matasa da suke wannan lamari ba su da ilimin zamani kuma babu na
addini. Rashin ilimi na daga cikin manyan dalilan da suka rardasa wannan
bala’i.
2.
Rashin tarbiyya ga
matasa: Da yawan matasan da suke wannan sana’a ta bangar siyasa ba su da
tarbiyya, wannan daga iyaye ne su suka kasance masu rauni da rashin tsawatawa
har yaran suka samu kansu a cikin wannan sana’a.
- Talauci: Talauci yana daga cikin manyan dalilan da suka
saka matasa cikin wannan yanayi na bangar siyasa. Idan matashi yana da
wadata to lallai ba zai so ya zama a cikin wannan yanayi ba.
1.
Rashin aikin yi ga
matasa:A wannan lokaci sanin jama’a ne cewa, dayawa za ka ga matasa ba su da
aikin yi sai zaman banza zaman kashe wando. Wannan yanayi na rashin aikin yi ga
matasa ya taimaka sosai wajen bunƙasa wannan lamari.
2.
Son kai ga shuwagabanni
da neman duniya ko ta wane hali: Mafi yawan ‘yan siyasa sukan bayar da kuɗi ga
matasa su kuma umurce su da su je su cutar da wani abokin adawa, kuma su ko
matasan ba za su iya zuwa haka kawai kai tsaye su aikata wannan ɗanyen aiki ba,
wannan ya sa suke amfani da kuɗin su saye muyagun ƙwayoyi da za su kawar da
hankalinsu sai su aikata duk abin da aka umurce su.
4.0.5 Masu Yin Bangar Siyasa
Mafi yawan masu yin bangar siyasa matasa ne kuma da yawa a cikinsu ba su da
aikin yi ba su da wata takamaimiyar sana’a, tare da rashin samun tarbiyya ta
gari.
Matasa sukan je gidan ɗan siyasa su zubar da mutunci shi kuma ya basu kuɗi ya
kuma ba su makamai. Su kuma su yi amfani da kuɗin su sayi kayan maye wato ƙwayoyin
da za su haukata su ko su kawar da hankalinsu domin su ji daɗin yin ta’addanci.
Akwai wasu da ake ganin cewa, suna bangar siyasa amma su ba su shaye-shaye da
ta’addanci, sai dai suna yin duk wata magana da ke iya hardasa jidali. Irin waɗannan
‘yan bangar siyasa sun fi yin bangar su a fili ko a kafafen yaɗa labarai da
suka haɗa da rediyo da talabijin da jarida da dai makamantansu.
4.0.6 Yadda Ake Yin Bangar Siyasa
Galibi bangar siyasa takan samu ne a lokacin da ake gudanar da wani taro na
‘yan siyasa, kamar kamfe ko ranar zaɓe ko wajen wani ɗaurin aure, ko zanen suna
ko bukin sarauta ko dai wani taro da za a iya samu wani ɗan siyasa ya halarta.
Matasa waɗanda suke cikin wannan sha’ani suke zuwa su yo shaye-shaye su riƙo
makamai suna tayar da hankalin jama’a, wani lokaci ma har suna iya saran wani
da makami, ko su buga ma wani sanda ko dai su samu wani aibu su yi wa wani.
Matasan sukan fara wannan ta’addacin tare da kuwace-kuwace da zage-zage da faɗin
“sai wane ko ba a wa Allah” suna kuma iya yin amfani da lafazi kamar haka, “sai
wane ko ran dubu zai ɓaci” ko su ce, “Sai wane ko a sha adda” wato gwaninsu (ɗan
takara).
Matasan za su riƙa yin rawa suna jujjuyawa suna faɗin sai wane, tare da jujjuya
makamai ana tayar da hankali da nuna ƙin jinin wanda ake adawa da shi.
4.0.7 Nazarin Ta’addanci A Littafin Zaɓi Naka
Littafin Zaɓi Naka
littafi ne da Munnir Mamman Katsina ya rubuta tun a shekarar 1982, wannan
littafi dai marubucin ya gina labarinsa da wani tauraro mai suna Na-muduka kuma
ya kawo irin wahalhalun da shi Na-mudukan ya sha da irin halin da Na-mudukan ya
samu kansa a ciki. Ga dai yadda abin yake a cikin littafin.
4.0.7.1 Na-muduka A Matsayin Ɗan Ta’adda.
Ta’addancin Na-muduka ya fara bayyana ne tun a shafi na 13, inda ya fara da
cewa, “Muma yaran gidan ganin ba wanda ya kula da mu da an ce gari ya waye sai
mu fita yawon banza. Ba mu dawowa iskancinmmu ya ishe mu, ko mun dawo ko ba mu
dawo ba ba wanda ya damu da inda muka je. Cikin ɗan lokaci kaɗan ni kuma
na zama ɗan iska tun ina ƙarami na, saboda cuɗanya da waɗannan yaran”.
Idan aka dubi abin da Na-muduka ya faɗa a cikin wannan littafi za a ga cewa, ya
yi daidai da abin da muka faɗa da cewa rashin kula da yara yana hardasa shiga
cikin lamarin ta’addanci. Wannan nauyi ne da ya rataya ga iyaye kuma shi
Na-muduka haka ya faru da shi sai ya samu kansa a cikin duba za a ga
cewa, haɗuwa da miyagun abokai yana daga cikin abin da ke hardasa shiga lamarin
ta’addanci, wannan ko shakka babu saboda ga Na-muduka ya haɗu da wasu da suka
fita yawon iskancinsu tare.
Haka kuma a shafi na 15 Na-muduka ya ƙara da cewa, “Ni dai ba abin da ya fi
burgeni da ba ni sha’awa kuma ya fi ɗaukemin hankali irin halayen ‘yan giya.
Sai ka ga mutum ya sha ya bugu har ya buge yana wata irin tafiya a makaifa, ya
tangaɗa nan ya tangaɗa can yana faɗain duk abin da ya fito a bakinsa....” .
Wannan bayani da Na-muduka ke yi yana nuna cewa a shirye yake da shiga lamarin
shaye-shaye wanda kamar yadda muka faɗa a baya cewa, yana daga cikin dalilan da
suke hardasa ta’addanci. Galibi idan mashayi ya yi shaye-shaye yakan iya yin
duk wani abu na ɓarna ko ta’addanci tunda dai ga shi Na-muduka ya faɗa cewa,
idan mutum ya sha ya bugu sai ya kama faɗin duk abin da ya fito ga bakinsa.
Idan kuma mutum ya kama faɗin duk abin da ya fito ga bakin sa kuma yana iya
zama sanadiyya ɓarkewar wata rigima a kama ta’addanci.
4.0.7.2 Na-muduka A Gidan Yari
Wannnan lamari na ta’addanci ya sa yaro Na-muduka ya shiga gidan yari. Amma
abin da yarage mu sani shi ne shin ko Na-muduka ya yi ladabi ko kuma lamarin ƙara
haɓaka ya yi. Yanzu dai ga abin da yake cewa, a shafi na 27. a cikin wannan
shafi Na-muduka ya faɗa da bakinsa cewa, “Da jama’ar da ke wurin suka ga haka
sai suka kirawo ɗan sanda ya kamani. Da aka kai ni ga alƙali sai ya yanke mani
hukuncin ɗauri shekara shidda a gidan yari, saboda na yi faɗa da mutane har na
yi masu rauni a kan haƙƙinsu”.
Ya ci gba da cewa, “Wannan ɗauri da alƙali ya yanke mani sai na ji daɗi domin a
nan gidan yarin sai na haɗu da wasu ƙasaitattun ɓarayi waɗanda aka ɗaure rai da
rai. Na koyi darussa na sata bayan fitowa na zama hamshaƙi kuma gawurtaccen ɓarawo”
Na-muduka dai ya gawurta dalilin shigarsa a gidan yari. Wannan na nuna cewa, da
yawa wani lokaci idan aka kai mutum a gidan kaso ko dai ya koyi darasi mai kyau
ko kuma ya koyi maras kyau. Wasu daga cikin matasa na wannan zamani sukan
aikata makamanci wannan lamari. Idan hukuma ta kama su a madadin a kaisu inda
ya dace sai a ajeyesu a inda bai dace ba, wannan na iya ƙara gurɓata su.
4.0.7.3 Namuduka Ya Shiga Soja.
A cikin littafin Zaɓi Naka kuma a shafi na 29, Na-muduka ya bayyana da kansa cewa,
“...Kafin a ɗauke ni sai da aka auna faɗin ƙirjina, da tsawona da ƙarfin idona
aka ga komai lafiya lau yake, saboda haka sai aka ɗauke ni” wannan jawabi da ya
yi ya nuna cewa an ɗauke shi aikin soja kuma ya yi aiki soja. Wannan ɗauka da
aka yi ma su Na-muduka ta yi amfani ko da yake baya da karatu amma kuma yana da
ƙarfin da zai yi aikin soja. Da haka hukuma ta yi ta rage zaman banza ga matasa
da an ji sauƙin wannan musiba da ke faruwa da ta’addancin marasa aikin yi.
4.0.7.4 Na-muduka Da Ƙungiyar ɓarayi
Bayan Na-muduka da abokan aikinsa sun gama aikin soja sai suka yanke shawarar
su kafa ƙungiyar ɓarayi mai zaman kanta, saboda dauri da suke a soja biyansu
ake yi amma yanzu ba a biya kuma babu wani wuri na samun wannan kuɗin da suka
saba ansa a matsayin albashi. A shafi na 40, dai Na-muduka yana cewa, “..saboda
haka sai na kawo shawarar cewa, ni a ganina ba sana’ar da ta dace da mu sai
fashi. Tun da daman mun riga mun san yadda ake amfani da makamai, kuma gashi
muna da kuɗi kamata ya yi tun kafin mu kashe su, mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu sayi
makamai da su.
Ya kuma ci gaba da cewa, “mu samu wani ruƙumin daji muka yi gidan ƙasa a ciki
yadda da wuya wani mutum na daban komai bincikensa ya gane mu. Kafin ka ce haka
duk mun fitini gari da sace-sace da kashe-kashe, kullum da dare ya yi sai mu
saka Mask mu ɗauki makamai mu tasar ma gidajen masu hannu da shuni, mu kashe su
mu kwashe dukiyarsu duka. Kai da muka buwaya har da rana tsaka muke
ta’addancinmu”
Wannan bayani da Na-muduka ya yi yana nuna cewa duk lokacin da hukuma ta kori
jami’an tsaro aiki ko ta dakatar da su ko ta taushe masu haƙƙinsu to wannan
lamari kan iya faruwa. A yau dai matasa ne suke cin karensu babu babbaka kuma
wannan ta’addanci da ake yi galibi duk su ne sai dai rashin aikin yi shi ne
sanadi da kuma rashin ilimi.
4.0.8 Hanyoyin Magance Ta’addanci
Ya kamata hukuma ta bi hanyoyi nagartattu wajen magance wannan lamari na
ta’addanci, waɗannan hanyiyi dai sun haɗa da:
- Samar wa matasa aikin yi
- Bayar da ilimi mai amfani ga matasa
- Kawar da cin hanci da rashawa
- Samar da tsaro na gaskiya
- Bin doka da oda
Waɗannan abubuwa idan aka samu aka kawar da rashin aikin yi da samar da aikin
yi ga matasan da ba su ilimi da kawar da cin hanci da rashawa, wato idan
mutum ya aikata laifi a hukunta shi ko ɗan wane ne, kar a karɓi kiɗi a sake
shi. Wannan zai taimaka sosai wajen magance wannan matsala saboda idan aka
hukunta wani daidai da abin da ya aikata wani zai ji tsoron ya aikata wani abu
mai kama da wannan ɓarnar ko ta’addanci.
4.0.9 Kammalawar Babi
A wannan babi mun yi bayani a kan ta’addanci da nau’o’insa inda har muka kawo
fashi da makami da sara-suka da bangar siyasa kuma duk mun tofa albarkacin
bakinmu a ciki. Mun kuma yi nazarin littafin Zaɓi Naka kana muka danganta
wannan abin da muka nazarta da abin da muke batu wato ta’addanci. A cikin nazarin
mun ga yadda Na-muduka ya kasance a cikin rayuwarsa, kuma mun ga yadda yaruwar
matasa take a wannan lokaci musamman waɗannan da suke cikin ta’addanci
sakamakon siyasa.
Babi Na Biyar
- Jawabin Kammalawa
Kamar yadda a ka gani a baya, wannan bincike namu yana a matsayin share fage ne
kan muhimmin ɓangaren adabi wanda ya shafi zube da rayuwar da matasanmu ke ciki
a yau.
Kamar dai yadda aka saba mun kasa wannan kundin bisa ga tsarin babi-babi, kuma
kowane babi da abin da yaƙunsa daban tun farko har ya zuwa babi na ƙarshe.
A babi na ɗaya mun yi tsokaci a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin
Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin Da Suka Taso da Matsalolin Da
Aka Fuskanta.
A babi na biyu kuwa, mun yi Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata kana muka biyo
da Salon Nazari da Tsarinsa.
Babi na uku Wannan babin ya ƙunshi ma’anar rubutu da ma’anar rubutun zube da
Gasar ƙagaggun labarai na Hausa da kuma samuwar ƙagaggun labaran Hausa, a cikin
mun yi bayanin ƙagaggun labarai na Hausa waɗanda muka ce sun samo asali ne tu
zamanin Turawan mulkin mallaka, kuma wannan lokaci ne ya yi daidai da shekarar
1933, sai dai kuma ko bayan wannan lokaci an yi ta yin gasa makamanciyar wannan
kuma ana samar da littattafai, misali idan aka duba shekarar 1982, ai an samar
da wasu litattafai da da suka haɗa da ma littafin da za mu yi nazari a cikinsa.
Shi kuwa babi na Huɗu A wannan babi mun yi bayani a kan ta’addanci da
nau’o’insa inda har muka kawo fashi da makami da sara-suka da bangar siyasa
kuma duk mun tofa albarkacin bakinmu a ciki. Mun kuma yi nazarin littafin Zaɓi
Naka kana muka danganta wannan abin da muka nazarta da abin da muke batu wato
ta’addanci. A cikin nazarin mun ga yadda Na-muduka ya kasance a cikin
rayuwarsa, kuma mun ga yadda yaruwar matasa take a wannan lokaci musamman waɗannan
da suke cikin ta’addanci sakamakon siyasa.
A babi na biyar nan ne muka naɗe tabarmar wannan Bincike da Jawabinmu na
Kammalawa tare da yin bayar da shawrori ga jama’a.
5.0.1 Shawarwari
A nan muna kira ga masu sha’awar labaran zube da su hankalta da cewa yanzu fa
lokaci ya canza an kuma samu cigaba wajen karatun labarai da aka shirya su
domin isar da wani saƙo.
Idan aka duba ta furskar addinin Musulunci za a ga, ya kawo babban sauyi kan
yadda Hausawa suke tafiyar da al’amurransu na rayuwa, wanda wannan sauyi ya
shafi har yadda ake gudannar da wannan sha’ani na Ƙagaggun Labarai.
Dangane da shigowar turawan mulkin mallaka sun kawo wata hallayar rayuwa saɓanin
wadda mazauna ƙasar Hausa ke bi kafin zuwansu. A nan sun kawo tsarin ilimin
zamani da sabon tsarin kiwon lafiya na zamani wanda ya ƙunshi rubuce-rubucen da
suka isar da wani saƙo daban, saɓanin namu.
Bugu da ƙari, wasu Hausawa masu ilimin zamani na ƙyamar wannan wannan sashe na
nazarin Hausa. Saboda haka ya kamata iyayen su himmantu wajen sanya ‘ya’yansu
makarantun zamani da na addini domin samun ilimin wanda zai zamana domin samun
cigaba.
Manazarta
Tuntuɓi Amsoshi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.