Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Karin Magana A Cikin Littafin Zamanin Nan Namu

NA

A’ISHA ALIYU S. KAYA                   

HUSSAINA MUHAMMAD HARUNA            

HASSANA MUHAMMAD HARUNA             

SAHEN  HAUSA TSANGAYAR HARSUNA KWALEJIN ILIMI DA K’ERE-K’ERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU,JIHAR ZAMFARA 

www.amsoshi.com

SHEDANTARWA


Wannan aiki ya samu dubawa da tabbatarwa tare da karbuwa gami da amincewar wad’annan malamai.

MAI DUBA AIKI NA CIKI (Project Supervisor)

Mal. Habibu Lawal K’aura

Sa-hannun…………………………………….

Kwanan wata…………………………………

 

SADAUKARWA


Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta k’asa (NCE) a sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere da ke Gusau a jihar Zamfara ga Kananninmu da kuma iyayenmu mahaimafanmu bisa ga kyakkyawar tarbiyyar da suka bamu tun daga farko rayuwar mu har zuwa yau. Iyayen da kakannin sun had’a da: Maimartaba Ibrahim Maigandi Maradun da Kuma Malam Haruna  Liman Bedi. Sai iyayaen namu su kuma ga su kamar haka: Marigari Aliyu Sarkin Yak’in Maradun da kuma Alhaji Muhammad Haruna Bedi.  Allah ya saka masu da alheri amin.

 

 

GODIYA


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.

Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun farko har ya zuwa ranar k’arshe.

Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka muna domin ganin hak’armu ta cimma ruwa, musamman ga iyayenmu kamar su da kakanni kamar su: Maimartaba Ibrahim Maigandi Maradun da Kuma Malam Haruna  Liman Bedi. Sai iyayen namu su kuma ga su kamar haka: Marigari Aliyu Sarkin Yak’in Maradun da kuma Alhaji Muhammad Haruna Bedi da Alh. Sulaiman Ibrahim Tabotaki, da Kamaluddin Abdulmumin Zabarma, da Abubakar Isah da Muhammadu Sani Rilwanu Kano da Abdurrahman lamid’o Muhammad. Suma dai ‘yanuwa da abokan arziki ba za mu bar su a baya ba, Allah ya saka masu da alherinSa amin

Haka kuma muna mik’a kyakyawar  godiyarmu ta musamman ga malamanmu na wannan sashe kamarsu; Malam Habibu Lawal K’aura wanda ya d’auki tsawon lokacinsa yana kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo k’arshe Allah ya saka masa da mafificin alherinSa amin. sai Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Malam Haruna Umar Bungud’u, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba, Mal. Habibu Lawali K’aura, Mal. Aminu Saleh, Mal. Sani Aliyu Soba da Mal. Ibrahim Ahmadu ‘Dan’amarya da sauran su.

 

JINJINA


Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu jinjina ma malaman mu musamman Mal. Habibu Lawal K’aura da ma wasu daga cikin mutanen da suka taimka muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan dalibai da ma duk masu neman k’arin haske dangane da nazari da muka gudanar a kai muna masu rok’on Allah ya saka masa da maifificin alheri. Amin.

 

K’UNSHIYA


Shaidantarwa -      -        -        -        -        -        -        -        ii

Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        -        -        iii

Godiya        -        -        -        -        -        -        -        -        iv

Jinjina         -        -        -        -        -        -        -        -        vi

K’unshiya    -        -        -        -        -        -        -        -        vii

BABI NA ‘DAYA


1.0    Gabatarwa    -        -        -        -        -        -        1

  • Yanayin Bincike - - -        -        -        -        2

  • Muhallin Bincike -        -        -        -        -        3

  • Hanyoyin Gudanar da Bincike -        -        -        3

  • Manufar Bincike -        -        -        -        -        5

  • Matsalolin Da Suka Taso -       -        -        -        5

  • Matsalolin Da Aka Fusakanta - - -        -        6


BABI NA BIYU


2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata    -        -        8

2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -        -        -        -        -        13

BABI NA UKU


3.0.1 Tak’aitaccen Tarihin Marubucin Littafin Zamanin Nan

Namu         -        -        -        -        -        -        -        16

3.0.2 Ma’anar Karin Magana    -        -        -        -        -        19

3.0.3 Kashe-Kashen Karin Magana     -        -        -        -        20

3.0.3.1 Karin Maganar Jiya (Na Gargajiya)   -        -        -        21

3.0.3.2 Karin Maganar Yau (Na Zamani)      -        -        -        22

3.0.4 Tasirin Karin Magana a Rayuwar Bahaushe   -        -        23

3.0.5 Illolin Karin magana        -        -        -        -        -        27

BABI NA H U’DU


4.0.1 Karin Magana a Littafin zamanin Nan Namu -        -        28

4.0.2 Wasu Karuruwan Magangannu Da Littafin Ya K’unsa      29

4.0.2.1 Karin Maganar Cikin Wasa Ta Farko

(Malam Mai Dala’ilu)     -        -        -        -        -        29

4.0.2.2 Karin Maganar Cikin Wasa Ta Biyu (‘Yar Masu Gida    31

4.0.3 Bayanin Wasu Karuruwan Magangannu na Cikin

Littafin        -        -        -        -        -        -        -        33

4.0.3.1 Karin Magana Mai Nuni ga Gargad’i a Cikin Littafin

Zamani Nan Namu -        -        -        -        -        -        34

4.0.3.2 Karin Magana Mai Nuni ga Shawara -        -        -        35

4.0.3.3 Karin Magana Mai Nuni ga Raddi     -        -        -        35

BABI NA BIYAR


5.0.1 Jawabi Kammalawa         -        -        -        -        -        37

  • Shawarwari - -        -        -        -        -        -        39


Manazarta        -        -        -        -        -        -        -        40

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/about-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Babi Na ‘Daya


Gabatarwa


Wannan bincike mun yi shi ne domin mu bayar da tamu gudunmuwa wajen bunk’asa sashen Hausa, don haka mun rututa wannan bincike ne mai taken “Nazarin Karin Magana a Cikin Littafin Zamanin Nan Namu” don amfani ga masu nazarin harshen Hausa.

Domin samu sauk’in gudanarwa mun kasa wannan aikin namu a kan tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko za mu kawo bayani ne a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike da Manufar Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Da Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.

A babi na biyu kuwa nan ne za mu yi tsokaci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata da kuma Salon Nazari Da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa nan ne za mu kawo Tak’aitaccen Tarihin Marubucin Littafin Zamanin Nan Namu, da Ma’anar Marin Magna, Da Asalin Karin Magana da Ire-Iren Karin Magana.

A babi na hud’u kuwa nan ne muka yi tsokaci a kan littafin Zamanin Nan Namu da kuma a ciki ne muka zak’ulo wasu akrin magangannu da Hausawa ke amfani da su, da muhimmancin wad’annan karuruwan magana da illolinsu ga Hausawa.

A babi na biyar kuwa nan ne za mu yi bayani a kan Jawabin Kammalawa da Shawarwari sai Ta’arifin Wasu Kalmomi.

Yanayin Bincike


Kamar yadda aka sani mun gano cewar akwai buk’atar mu yi nazari a kan wasu bayyanai da marubuta suka yi a kan wannan binciken  kuma mun gano cewa, mu yi Nazarin wannan Littafi na “Zamanin Nan Namu” , don haka muka ga ya kamata mu gudanar da wannan binciken domin  zuwa  gaba, ko kuma mu ce domin masu tasowa yanzu da su san cewa wannan littafi yana da rawar da yake takawa a cikin adabin Hausa, musamman ta fannin karin magana.

Haka kuma a yunk’urinmu na gudanar da wannan aikin Binciken mun sha wahala sosai saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi Magana a kan wannan aiki namu. Haka kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala matuk’a.

Muhallin Bincike


Wannan bincike mun gudanar da shi ne a ‘bangaren adabin Hausawa, sai dai domin samun sauk’in gudannarwa mun ke’bance aikin namu a kan littafin “Zamanin Nan Namu” wanda Shu’aibu Mak’arfi ya rubuta, kuma karin magana ce kawai za mu mayar da hankali a kai.

Hanyoyin Gudanar da Bincike


Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka wad’anda suka gabata domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi daban-daban don k’arin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.

Kamar yadda bayani ya gabata mun  lura da cewa, dukkan mai aikin bincike dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar da wannan bincike namu domin kuwa har d’akunan  karatun wasu manyan makarantu mun lek’a. Mun kuma ziyarci d’ukunan karatu, don yin bincike ga kad’an daga cikinsu: ZACASS inda muka shiga d’akunan karatunsu wato (library).

Binciken namu bai  tsaya a wannan makaranta ba kurum. Domin kuwa ziyarar binciken ta kai mu ga tuntu’bar wasu malamai da muke da su domin mu samu abin da muke nema. Mun kuma tattauna da wasu masu k’ok’arin karatun littatafan wasannin kwaikwayo domin su k’ara wayar muna da kammu. Yayin da muka tattaro bayanai game da adabin Hausa ta fannin karin magana domin mu samu abin da muke buk’ata.

Manufar Bincike


Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano cikakkiyar k’warewar d’alibai da fahimtarsu da hazak’arsu. Ta wannan hanyar karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya k’ara tabbatar da abin da aka riga aka sani a fagen ilimi, ko abin da ba sani ba sai a fahimce shi.

Binciken yana fitar da bayanai domin amfani al’umma, wani babban muhimancin bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.

Manufar wannan binciken shi ne mu fito da wasu abubuwa musamman abin da ya k’unshi karin magana da wannan littafi na Zamanin Nan Namu ya k’unsa. Muna kuma fatar wannan nazari namu ya zama abin dogaro ga masu nazarin harshen Hausa.

Matsalolin Da Suka Taso


Kasancewar masana da manazarta harshen Hausa sun baje kolinsu a fagen adabi kuma sun yi aikace-aikace masu yawa a ‘bangaren adabi, kuma sun lek’a warare da dama, ya sa ka ga sun lak’ume ko’ina amma da muka lek’a fannin karin magana wadda ake yi a cikin wasannin kwaikwayo sai muka ga ashe sun bar wani wuri da ba su game ba gaba d’aya, kuma wannan ya sa  mu kuma muka ga kamar sun bar wata kafa sai muka ga ya dace mu bayar da tamu gudummuwa a wannan fanni.

Matsalolin da aka Fuskanta


Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka, wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun fuskanci matsaloli da dama kamar:

        Rashin isassun kud’in mota, da matsalar iske wad’ansu masana da muke tuntu’ba wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kud’in mota domin zuwa wajen  wad’ansu mutane da abin ya shafa, sai mu iske ba su nan. Haka ma kowa ya san irin halin da ake ciki a k’asar nan na rashin tsaro, a inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole sai da taka tsantsan.

Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu d’alibai mata masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama  sun sha kanmu. Daga cikinsu akwai

Matsalar kar’bar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji da ta k’arshen zangon karatu.

Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka had’a da girke-girken abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk wad’annan matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo  da su .

Haka ma akwai matsalar yawan d’aukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta d’auke. Kad’an kenan  daga irin matsalolin da muka ci karo da su.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/about-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

Babi Na Biyu


2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.


An gabatar da ayyuka da dama a kan wannan fanni na adabin baka, saboda haka ya zama wajibi a gare mu da mu waiwayi wasu ayyuka da aka riga aka gabatar a wannan fanni, domin sanin alak’arsu da namu aikin tare da ganin bambancin da ke tsakaninsu.

A cikin jerin ayyukan da suka gabata a wannan fage akwai bugaggun littattafai da masana suka rubuta, da kundayen bincike da manazarta suka rubuta da mujallu da muk’alu da masana da manazarta daban-daban suka rubuta a kan fannoni daban-daban na adabin Hausa. Ga dai wasu daga cikinsu kamar haka:

Madauci I. Da Wasu (1968), A littafinsu mai suna “Hausa Custom” sun yi tsokaci a kan haihuwa zuwa mutuwa da addini da sana’o’i da Chamfi da karin maganar Hausawa.

Wannan gagarumin aiki da wad’annan maruta suka yi yana da alak’a da namu, idan aka duba za a ga cewa sun yi tsokaci a kan karin magana, wanda a namu kundin mu ma muna za mu yi tsokaci a kan karin magana. Duk da cewa wannan littafi yana da alak’a da aikinmu, sai ga shi kuma a wani gefen yana da bambanci da kundin nan da muke da k’udurin yi, saboda su marubutan suna bayani ne a kan karin magana gaba d’ayanta tare da wasu abubuwa da suka shafi al’ada wato haihuwa da mutuwa da addini da sana’a da Chamfi. Yayin da mu namu aikin ba sai mun yi tsokaci a kan wad’annan ba.

Skinner N. (1980), a Littafinsa mai suna “Anthology Of Hausa Literature). Marubucin ya yi bayanin nau’o’in adabi da suka had’a da take da kirari da labaru da wasanni da karin magana da wak’ok’i da littattafan hira da zube da tatsuniyoyi da kacici- kacici.

Wannan aiki na Skinner yana da alak’a da namu ta wani fanni musamman idan aka duba inda ya yi bayani a kan karin magana, wannan ya sa muke da alak’a saboda karin maganar da ya yi tsokaci a kai. Bambancinmu da shi kuwa shi ne ya yi bayanin wasu abubuwa da mu ba sai mun yi bayani a kan su ba. Mu namu aikin ya fi mayar da hankali ne a kan karin magana da ke cikin littafin Zamanin Nan Namu ne kawai.

Zarruk R. M. da Wasu (1988), a nasu littafin mai suna “Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa; Don K’ananan Makarantun Sakandare, littafi na I da na II da na III, a cikin littafan sun yi bayani a kan harshe da adabi da al’ada, to a cikin abin da ya shafi adabi sun yi magana a kan karin magana wannan ya sa aikinsu yake da akak’a da namu, inda aikinsu ya samu bambanci da namu kuma shi ne su suna Kallon harshe da al’ada da adabi duka a cikin aikinsu, mu kuma namu aikin yana bayani ne a kan karin maganar da aka yi a cikin littafin Zamanin Nan Namu ne kawai.

Junaidu I. Da Wasu (2007), sun rubuta littafi mai suna “Harshe da Adabin Hausa A Kammale; Don Manyan Makarantu Sakandare”  Marubutan sun rubuta littafin ta fuskoki guda biyu, sun kuma yi shi a kan tsarin babi-babi har babi biyu, inda babi na farko ya k’unshi harshe, yayin da babi na biyu ya k’unshi Adabi. A rabo na biyu kashi na farko ya kawo hanyoyin gwanintar sarrafa harshe kamar su Zaurance, Karin Magana Kirari da dai sauransu.

Wannan aiki yana da alak’a da namu aikin saboda ya ta’bo karin magana a cikin aikinsa yayin da mu ma a namu aikin mun ta’bo karin magana. Sai dai inda muka bambanta da nasa aikin shi ne mu mun ke’bance aikin namu a kan karin karin magana da ke cikin littafin Zamanin Nan Namu, wato ba karin magana gabad’ayanta za mu nazarta ba.

‘Dangambo A (2008), a nasa littafi mai suna “Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari)”. Masani ya yi tsokaci a kan yadda adabin Hausa ya rabu dalla-dalla, a cikin aikinsa ya kawo magangannu irin na hikima wad’anda suka had’a da Ba’a Sara, da Karin magana da Zaurance da dai sauransu. Wannan aikin nasa yana da alak’a da namu aikin saboda ya yi bayanin karin magana wanda yake daman muma namu aikin yana magana ne a kan karin magana, sai da inda suka bambanta shi yana bayanin wasu sassa da dama daga cikin adabin Hausa.

Gusau S. M. (2008), ya rubuta littafi mai suna, “Dabarun Nazarin Adabin Hausa” inda ya yi tsokaci a kan makarantu da makarantun nazarin adabin Larabci da na Ingilishi. Marubucin ya k’ara da kawo tarihi da ginuwar nazarin da fed’e adabin Hausa ciki kuwa har da magangannun hikima da suka had’a da take, kirari, karin magana da salon magana da bak’ar magana.

Wannan aiki na Gusau yana da alak’a da namu aikin saboda ya ta’bo karin magana, wanda muma namu aikin yana da alak’a da karin magana sai da inda muka samu bambanci da nasa aikin shi ne mu mun tak’aita namu aikin a kan karin maganar da ke cikin littafin Zamanin Nan Namu da tasirinsa ga Hausawa.

‘Dan Hausa E.M (2012) A Littafinsa mai suna “Hausa Mai Dubun Hikima” Marubucin ya tsara littafinsa ne a kan tsarin babi-babi, inda a babi na d’aya ya yi bayani a ne a kan Hausawa da hikimominsu na zantuta. A babi na biyu kuwa ya yi tsokaci a kan karin magana da kirari, a babi na uku ya yi bayanin habaici a wajen Hausawa.

Idan muka lura da wannan aikin za mu ga cewa yana da alak’a da namu aikin wannan kuwa haka yake musamman idan muka duba a babi na biyu inda ya yi bayanin karin magana. Wannan yasa namu aikin yake da alak’a da nasa. Inda kuma suka bambanta shi ne shi marubucin yana bayani ne a kan karin magana gaba d’ayanta inda mu kuma mun ke’bance aikin namu a kan karin maganar Hausa da ke cikin littafin wasan kwaikwayon nan na Zamanin Nan Namu.

K’aura (2012), ya rubuta wata muk’ala mai taken “Bak’o A Karin Maganar Bahaushe” K’aura ya kawo ma’anar Bak’o da Ma’anar karin magana da wasu kare-karen magangannu da suke da alak’a da bak’o tare da yin bayani kowanne daga cikinsu.

Idan aka lura za a ga cewa wannan aiki da K’aura ya yi yana da alak’a da aikinmu ta fuskar karin magana da ya yi bayani a kai. Inda kuma ayyukan suke da bambanci shi ne, shi K’aura yana kallon bak’o ne a cikin karin magana, mu kuma duk karin maganar da ya fito a cikin littafin Zamanin Nan Namu shi ne muka mayar da hankali a kai.

Dukkan wad’annan ayyuka da muka duba suna da alak’a da wannan aiki namu da muke da k’udurin yi ta wasu fuskokin sai da kuma idan muka dubi wasu fuskokin kuma za mu ga cewa ayyukan suna da bambanci da namu.

2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa        


Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin mutum.

Salon nazari wata hanya ce ta isar da sak’o da bayyana tunanin mutum. Haka kuma salo ya na nufin hanyoyin da marubuci ko mawallafi kan bi domin yi wa harshe kwalliya ko kuma yi wa rubutun sa ado, haka kuma wata dabara ce da marubuci kan yi amfani da ita domin samun sauk’in isar da sak’onsa a cikin rubutunsa. A dalilin haka ne mu ka yi amfani da hanyoyin guda uku na nazarin salo.

Na farko dai irin kalmomin da muka yi amfani da su, kalmomi masu sauk’i ne. Sai kuma muka saka su a inda ya dace.

To anan za mu yi amfani da salo mai jan hankali, domin  mu ja hankalin mai karatu ya karanci wannan kundi, ba tare da wata wahala ba ko ya k’agara da karatun wannan bincike ba.

Idan mai karatun wannan aiki ya kwantar da hankalinsa ya biyo mu cikin natsuwa to zai ga irin matakan salon da muka yi amfani da shi wajen rubata wannan kundi saboda mun yi amfani da littatafai masu saukin fahimta.

An kuma yi amfani da nuna k’warewar harshe sosai a cikin wannan kundi saboda anyi amfani da kalmomi masu burgewa da kuma armashi wad’anda ke sa mai karatu ya ji dad’i a zuciyarsa, wannan shi zai sa binciken namu ya yi kwarjini da farin jinni ga makaranta.

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/about-us/

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

Babi Na Uku


3.0.1 Tak’aitaccen Tarihin Marubucin Littafin Zamanin Nan Namu


Alhaji Shu’aibu Mak’arfi d’an shekara 79, kuma marubuci ne, a kafafen yad’a labarai ya rubuta wasannin kwaikwayo a gidajen rediyo wad’anda aka watsa, wad’ansu kuma aka buga su, a matsayin littafin wasannin kwaikwayo da aka yi nazarinsu a makarantun sakandare inda manyan makarantun gaba da sakandare da sauransu.

Alhaji Shu’aibu Mak’arfi ya soma karatun firamare d’insa a Zariya. Sannan ya halarci sananniyar makarantan nan ta midil da ke Zariya. Daga bisani ya wuce kwalejin horanda malamai da ke Katsina da Bauchi. A matsayin shi na malamin makaranta ya koyar a d’an k’ank’anin lokaci a makarantar midil da ke Zariya kamai ya shiga aikin soja a (1941-9143) a matsayin malami mai koyar da harshen Turanci.

Bayan aikin soja sai ya shiga aikin hukumar kula da adabi ta arewacin Nijeriya, a tak’aice ana kiranta da suna (NORLA) daga baya wadda ta kasance hukumar adabi, sanna ya yi aiki da hukumar aikawa da wasik’u da sadarwa (P&T) na tsawo shekaru biyar a 1948. Haka kuma ya yi aiki da hukumar ‘yad’a labarai ta k’asa wato (NBC) ya yi rubuce-rubuce da yawa a ‘bangaren wasannin kwaikwayo, wasu daga cikin su sun had’a da; Jatau Na K’yallu, Zamanin Nan Namu da kamfanin gaskiya ya buga a (1970). A halin yanzu yana zaune a garin Kaduna. Marubucin ya yi fice wajen yin gwagwarmaya da fito da ra’ayoyinsa ta haujin k’irk’irar adabi da bunk’asa shi da al’ada da kuma jagoranci wanda shi ne k’ashin bayan tattaunawarmu.

Alhaji Mak’arfi ya soma a matsayin marubuci kuma d’an jarida, ya rubuta fitattun littafan wasannin kwaikwayo guda biyu da suka had’a da Jatau Na K’yallu da Zamanin Nan Namu, wad’anda suka yi fice a k’asar Hausa. An ji Mak’arfi bai da k’udurin kansa a marubuci amma daga baya ya samu kan sa a matsayin mai rubuta wasannin kwaikwayo a gidan rediyo.

Haka kuma Mak’arfi yana d’aya daga cikin wad’anda suka assasa aikin jaridanci a 1948, wato shekara hud’u bayan kafawar jaridar Gaskiya ta Fi Kwabo. A nan ma ya baje baiwar da Allah ya hore masa, kamar lokacin da yake matsayin ma’aikacin gidan rediyo. Ya rik’a muk’amai daban-daban, a lokacin da yake aiki a hukumar yad’a labari ta Nijeriya. ya kuma aje aiki a watan Augusta a shekarar 1974.

Mak’arfi ya ta’ba zana daractan labarai a jaridar New Nigeria News Paper Limited daga 1974-1980. Kuma ya ta’ba zama wakili a hukumar yad’a labarai ta arewacin Nijeriya, wadda yanzu haka ake kira da Gidan Rediyon Nijeriya ta Kaduna wato (FRCN).

Alhaji Mak’arfi ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya guda. Da kuma jikoki da dama, ya bar gagarumin tarihi a lokacin da yake aiki a gwamnati tare da nuna kyawawan d’abi’u abin koyi ga na baya. Duk da cewa, ya rik’a muk’amai da dama a cikin aikin jaridanci.

Mun yi sa’a a shekarun da suka wuce an yi hira da marigayi Alhaji Shu’abu Mak’arfi a kan ayyukansa na adabi, wanda Dr. Ahmed K. Babajo Tsohon malami a sashen koyar da harshen Turanci na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Malam Babajo ya same shi a wani lokaci a cikin watan Febareru 1997 a kamfanin New Nigeria, inda ya nemi buk’atar a buga tattaunawar da ya yi da Shu’aibu Mak’arfi.

 

3.0.1 Ma’anar Karin Magana


Masana da manazarta da dama sun ba da gudunmuwarsu dangane da abin da ya shafi karin magana. Ga dai wasu daga cikinsu.

Zarruk da Wasu (1986), sun bayyana cewa “Karin magana gajeren zance ne wanda yake k’unshe da hikima”

Yahaya I. Y. Da Wasu (2003) sun ce, “Karin magna tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajerce na hikima da zalak’a tare da bayar da ma’ana gamsasshiya mai fad’i mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi daki-daki.

Junaidu I. Da wani (2007) sun bayyana karin magana da cewa, “Karin magana shi ne wata ‘yar jimla gajeriya da mai magana zai fad’a ta hikima wadda ta k’unshi magana mai yawa idan an tashi yin sharhinta”.

Umar, (1980) cewa ya yi, “ Karin magana dunk’ulalliyar jimla ce mai sassa biyu, da ta k’unshi zunzurutun ma’ana lokacin da ake yin bayani. Idan har karin magana ya amsa sunansa karin magana da an ambaci sashensa d’aya za ka ji abokin magana ko wani daban ya cika d’ayan sashen

Shi kuma ‘Dangambo (1984), ya bayyana karin magana da cewa, dabara ce ta dunk’ule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kad’an cikin hikima.

Bisa ga la’akari da wad’annan ma’anoni da masana da manazarta suka bayar za mu iya cewa, “Karin magana wani gajeren zance ne wanda aka shirya shi domin wa wakilci zance mai yawa tare da ma’ana.

Idan muka dubi wad’annan ma’anonin za mu ga cewa kusan duk suna da makusanciyar dangantaka, saboda duk sun yarda cewa zance ne kuma gajere mai k’unshe da hikima. Wato a karin magana za a ga cewa in har zancen yana buk’atar ciko to tilas ne ya k’unshi ‘bangare biyu. Shi dai ‘bangare na farko yana k’unshe ne da jimlataccen bayani na furuci da aka yi wato manufa. Shi kuma ‘bangare na biyu yana k’unshe da k’arin bayani a kan ‘bangare na farko.

3.0.2 Kashe-Kashen Karin Maganar Hausa


Masana da manazarta daban-daban sun yi ruwa sun yi tsaki wajen karkasa karin magana. Misali

Umar (1980), a littafinsa mai suna “Adabin Baka” ya karkasa karin magana zuwa rukuni-rukuni. A cikin “Hausa Ba Dabo Ba Ne”, Kirk Greene (1996) ya bi salon tsara k’amus ne ya karkasa karin magana dangane da haruffa na farko, wato ya jefa su a tsarin abajada tun daga ‘a’ zuwa ‘z’. Shi kuwa Ibrahim Yaro Yahaya a Littafinsa mai suna “Labarun Gargajiya” sai ya yi amfani da hikimomin da ke cikin lamarin ya ware karin magana, ma’ana, hak’uri da arziki.

Haka kuma akwai wata hanya ta rarraba karin magana wato ta bin tsarin gininsu. Ana iya yin la’akari da sigar jimlolin karin magana. Wannan ya nuna cewa kenan abu ne mawuyaci a iya cewa ga iya kashe-kashen da karin magana ya kasu.

A wannan kundin a d’an namu nazari dangane da wannan batu za mu karkasa karin magana zuwa gida biyu, wato za mu dube ta ta fuska biyu, ma’ana karin magana jiya da kuma yau.

3.0.2.1 Karin Maganar Jiya (Na Gargajiya)


A wannan kashi na karin magana wato karin maganar jiya, kamar yadda sunan ya nuna cewa jiya wato lokacin da ya riga ya shud’e ko tsintsar gargajiya to yana nuna duk wani rukuni na karin magana da ya kasance gargajiya ne zalla shi zai shiga a wannan rukuni. misali

  1. Za mu hau inji baran mai doki.

  2. Na duk’e Tsohon Ciniki.


iii. Ba ni na kashe ba, rataya aka bani

  1. Allah suturubuk’ui, inji kishiyar mai doro.

  2. Sai bango ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga.


Da sauran su.

Idan muka kwantar da hankali muka dubi wad’annan karuruwan magangannun za mu ga cewa, dukkannin su suna d’auke ne da lafuzza irin na dauri, wato babu wata kalma da ta danganci zamani a cikinsu.

 3.0.2.2 Karin Maganar Yau (Na Zamani)


Shi kuma wannan kashi na karin maganar yau, akasi ne na karin maganar gargajitya wato shi kamar yadda kalmar nan ta yau ke nuna cewa, abin da bai dad’ad’d’e ba ne yana daidai lokacin da ake gudanar da shi wato dai a tak’aice na zamani ne.

A wannan rukuni nan ne duk wani karin magana da ke da lafuzza da suka danganci zamani zai shiga, muna iya lura da cewa, wasu karuruwan magangannu suna d’auke da lafuzza da suke da ka ji su za ka gano cewa na zamani ne. Misali

  1. Rigakafi ya fi magani.

  2. In mutum ya ce zai baka riga, dubi ta wuyansa


iii. Mai kaza a aljihu, ba ya jimirin as

  1. Ban sa a ka ba, inji ‘barawon hula


Idan muka lura da wad’annan karuruwan magana da muka kawo a sama za mu ga cewa, wasu daga cikin lafuzzan da aka yi amfani da su aka gina karin maganar na zamani ne. Misali kalmomi kamar Rigakafi, riga, aljihu, da kuma hula.

Wannan aiki namu zai fi mayar da hankali ainun dangane da abin da ya shafi tasirin Bak’o a cikin karin maganar Hausawa.

3.0.3 Tasirin Karin Magana A Rayuwar Bahaushe.


Kasancewar karin magana dad’ad’d’iyar magana ce ta hikima wadda take d’auke da sak’o, ta yi tasiri sosai a rayuwar Bahaushe ta fuskoki da dama. Ga dai wasu daga cikin su.

  1. Adon Harshe


Karin magana ado ne na harshe da Bahaushe ke amfani da shi a cikin zancensa na yau da kullum, domin k’awata maganarsa da burgewa ga mai sauraro. Misali.

“zancen kuke so an ce da gwauro ya iyali?”

“Sai ka yi, wai karuwa ta ji mai wa’azi”

“Duk dai ga Baba, inji agola”

  1. Tak’aita Zance Da Saurin Isar Da Sak’o.


Ana amfani da karin magana wajen isar da sak’o a cikin sauk’i ba tare da an yi wani dogon sharhi ba, wato a cikin tak’aitattun kalmomi. Misali.

“Komai nisan jifa, k’asa za ta.”

“Komai nisan dare, gari zai waye”

“Ko an ci goro, an sha barci”

“Kwac ce ya iya wuri aka ba shi”

 

 

 

  1. Yin Sirri A Cikin Zance


Kasancewar ba kowane Bahaushe ne ya san karin magana ba, don haka yakan yi amfani da karin magana don ya ‘boye sirrinsa. Misali

“Na san a rina, an sace wa mahaukaciya zane”

“Laifin ba na bara ba ne, an daki biri ga rani”

“A dai ci gaba da gashi, suya sai ran salla”

“Da ruwan ciki, akan ja na rijiya”

  1. Gargad’i


Ana amfani da karin magana wajen yi wa wani mutum ko wasu mutane don su guji aikata wasu abubuwa mara sa kyau. Misali

“In zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere”

“Zuwa da kai, ya fi sak’o”

  1. Shawara


Shawara tana da muhimmaci a rayuwar Bahaushe, wannan ya sa ya ke amfanai da karin magana wajen ba d’an’uwansa shawara a kan gyara kayanka ko ko aikata wani abu mai muhimmanci. Misali

“Zomo ba ya kamuwa daga kwance”

“In an bi ta ‘barawo, a bi ta mai kaya”

“Fakon kaya ya fi ban cigiya”

  1. Mayar Da Martani


Bahaushe yana amfani da karin magana wajen mayar da martani a kan wani abu da aka aikata masa da ba daidai ba. Misali

“Kowa ya yi zagi a kasuwa ya san ko da wa yake”

“Kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha”

“Ko ba a gwada ba, linzami ya fi k’arfin bakin kaza”

Tasiran na karin magana da yawa suke ba wad’annan kad’ai ba ne, amma mun d’an bayar da wad’annan ne domin mu d’aure akuyarmu a kan magarya, ma’ana mu bayyana wa mai nazari cewa karin magana yana da tasiri ga rayuwar Bahaushe.

 

 

3.0.4. Illolin Karin Magana


Duk da cewa karin magana ya yi tasiri a rayuwar malam Bahaushe to kuma yana da illoli a tattare da shi. Ga dai wasu daga cikin illolin da karin magana ya k’unsa.

  • Karin magana na karya k’a’idar nahawu.

  • Karin magana tana kawo gaba da d’an’uwa.

  • Karin magana tana juyar da ma’anar harshe.

  • Karin magana tana hardasa rashin fahimtar harshe ga bami.

  • Karin magana tana wahalar da mai koyon harshe.

  • A kam yi amfani da karin magana a cutar da wanda ba ya jin harshen sosai.

  • Karin magana wani makami ne na fad’a tsakanin mazauna wuri d’aya.

  • Ana tafka sa’bo wani lokaci a cikin amfani da karin magana.


Wad’annan su ne illolin da karin magana take tattare da su. Ba wai su kad’ai ba ne sai dai su kawai muke iya bayarwa kar mu wuce gona da iri.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/about-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Babbi Na Hud’u


4.0.1 Karin Magan A Littafin Zamanin Nan Namu


Wannan littafi dai kasancewar littafi ne na Hausa kuma an rubuta shi daidai da al’adun Hausawa, don haka yana k’unshe da karuruwan magangannu na Hausa da yawa.

Idan muka tuna da abin da muka fad’a a baya cewa, karin magana wani zance ne gajere mai d’auke da sak’wanni da yawa, za mu ga yana da matuk’ar amfani da jan hankali tare da armashi saboda sarrafa harshen da aka yi aka fitar da shi ya yi daidai da tunanin mai karatu ko sauraro.

Marubucin wannan littafi ya yi amfani a irin wannan salo domin ya ja hankalin ma’abuta karatun rubutunsa, kuma wannan nau’in salo na sarrafa harshe da ya yi amfani da shi yana da armashi, tare da jan hankalin mai karatu. Ba sai an je nesa ba mu ma shi ne ya ja hankalinmu har muka lura da cewa, akwai wani abu da ya dace mu yi nazari akai. Ga dai wasu karuruwan magangannu da muka samu a cikin wannan littafi.

 

4.0.2 Wasu Karuruwan Magangannu Da Littafin Ya K’unsa


Daga cikin karuruwan magangannu da wannan littafin na Zamanin Nan Namu ya k’unsa sun had’a da Karin Magana domin mayar da martani, domin shawara, gargad’i, da dai sauransu. Ga dai bayanan wasu karuruwan magangannun da aka samu a cikin littafin.

4.0.2.1 Karin Maganar Cikin Wasa ta Farko (Malam Mai Dala’ilu)


Wannan wasa ta farko dai wasa ce da aka ba suna “Malam Mai Dala’ilu” wannan wasa dai an yi amfani da karuruwan magangannu a cikin ta, kuma wasu an yi su ne domin ‘boye sirri wasu kuma domin gargad’i wasu kuwa domin bayar da shawara. Ga dai wasu karuruwan Magangannu.

Karin Magana na Cikin Fotowa ta ‘Daya

  • Har abin kunya ne in huda cikina kuma in dawo ina kirari

  • Gwanin iya ruwa shi ne wanda ya fidda kansa kuma ya fidda wani nasa

  • Duniya ita kan ta makaranta ce, ta yaye marasa jin maganar iyaye.

  • Mutum baya huda cikinsa ya koma yana kirari.


Karin maganar Fitowa ta Biyu

  • Me kake ci na baka na zuba

  • Ana baka kana cewa in kawo k’warya

  • Kai dai kifin rijiya ne

  • Kowa ya k’i gaskiya ya ‘bata

  • Ai kin sami zare, sai walwala kike yi a hankali


Karin Maganar Fitowa ta Uku

  • Kowa ya iya allonsa, ai wankewa za ya yi

  • Da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne

  • Mu gudu tare, mu tsira tare

  • Ikon Allah k’urji ya fito ga bakin zabaya

  • Duban shawagin karya


Karin Maganar Fitowa ta Hud’u

  • Wadda nike yaba wa salla, ita ce ta kasa alwala

  • Wargi wuri yake yi

  • Hawainiyar ki ta kiyayi rama ta

  • Ban ci kayan Nani ba, Nani kuwa kada ya dameni

  • Kowa ya iya allonsa ya wanke

  • Anya abin da ya gagari baki, sankace na iya maganinsa


Karin Maganar Fitowa ta Biyar kuma fitowa ta K’arshe ga wasan Malam Mai Dala’ilu

  • In k’osar da doki in ya yi k’iba ya harban

  • Zumunta a k’afa take

  • Ai in dukiya ta ‘bace, bai kamata hankali ya ‘bace ba.

  • Itace tun yana k’arami ake iya lank’wasa shi

  • Tsakanin harshe da hak’ori ma ana sa’bawa


A wannan wasa ta Malam Mai Dala’ilu, mun shiga mun tsamo wasu karuruwan magangannu da aka yi amfani da su domin a k’ara wa rubutun armashi. Wasu karuruwan magana da aka yi a cikin wannan littafi suna yin hannunka mai sanda ga wasu mutane. Duk da cewa, taurarin da suke cikin wannan wasa su ne suke aiwatar da wannan karin magana.

Idan muka duba karin magangannun nan za mu ga cewa duk suna da dalilin da aka yi su. wasu ana yin su domin sirri wasu kuma domin shawara, wasu ko domin gargad’i.

4.0.3 Karin Magana na Cikin Wasa ta Biyu (‘Yar Masu Gida)


Ita ma wannan wasa an yi amfani da salon sarrafa harshe a ciki. Kuma wannan wasar tana d’auke da wannan salo da yawa a ciki. Kamar dai waccan wasa da ta gabata, mafi yawan wad’annan karuruwan magana ana yin su ne domin a tak’aita zance cikin hikima a ba wani ko wasu shawara, ko a yi gargad’i ko mayar da martani da dai sauransu. Ga dai wasu karuruwan magangannu da muka samu a tattare da karatun wannan wasa.

Karin Magana a Fitowa ta ‘Daya

  • Wani ma ya yi rawa, balle d’an makad’i

  • Mai uwa a murhu, ai baya cin tuwo gaya

  • Some-somen hauka tofar da yawu

  • Kowa da kiyon da ya k’ar’be shi

  • Zaki zama kurar ‘yammata a garin nan

  • Jaka sha tik’a

  • Zama da mad’aukin kanwa, shi ke kawo farin kai


Karin Magana a Fitowa Ta Biyu

  • Asshe ba ki da ta ido

  • Duk wanda ya yi watsi da kayansa sai iska ta watsar a jeji

  • Kowa ya iya allonsa ya wanke

  • Rak’umi da akala ka zama mik’oonnin shi

  • Gajin hak’uri shi ke kawo me aka dafa


Karin Magana ta fitowa ta uku

  • Kin zama mujiya cin ‘yan mata

  • Ban da akuyar d’aure ta samu saki

  • Masoyinka annabin ka

  • Ana dara ga dare ya yi

  • Zamani bancin mun yi alk’awari da kai haka ba


Karin Magana ta Fitowa ta Hud’u

  • Karen bana shi ke maganin zomon bana

  • Sakaran uba mai gara da man kad’anya

  • Tsuntsun da ya sha ruwa shi ruwa kan doka

  • Zamani ban gaji da rok’onka ba

  • An aike ni gurin samari ya fi bak’in goyo yawa


Karin Magana ta Fitowa ta biyar

  • Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah

  • Mu gani a ak’asa an ba kare tuwo a kwano

  • To ba gyaran-gyaran ba to dai ta yi mai

  • To ba ka ji an ce, “Ciniki goma maganin mai gasa ba”

  • Babbar magana, abu namu d’an kura da kallabin tsire

  • Shirwa mai idon zalunci

  • Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi birgima


Karin Magana ta Fitowa ta Shida

  • Banza ba ta kai zomo kasuwa


Karin Magana ta Fitowa ta Goma

  • Ina ruwan arziki da mugun gashi


Karin Magana ta Fitowa ta Goma Sha ‘Daya

  • Kowane gauta ja ne..

  • Kud’i ba ku da abokin gaba,

  • Kud’i masu gida rana, masu mai da tsoho saurayi


Karin Magana ta Fitowa ta Goma Sha Hud’u

  • Me gara za ta yi da dutse in banda lasa

  • An dad’e ana ruwa k’asa na shanyewa


Wad’annan su ne karuruwan magangannun da aka yi a cikin wasan ‘Yar Masu Gida”. Da yake karin magana ne muka mayar da hankali a kai kuma wasu suna da kama da kirari, amma wannan ba sa muka aje su ba. Saboda mun yi la’akari da wasu karuruwan magangannu da suke da alak’a da raddi ko mayar da martani da kuma wasu wad’anda su ke yanayi da gargad’i da jan kunne da kuma wad’anda su ke da yanayi da habaici da salon magana da adon magana.

4.0.4 Bayanin Wasu Karuruwan Magangannu na Cikin Littafin


Kamar yadda muka fad’a a baya cewa akwai wasu karuruwan magangannu da suke ishara ga gargad’i da shawara da martani. Yanzu ya dace mu tsamo su domin mu ga yadda suke.

4.0.4.1 Karin Magana Mai Nuni ga Gargad’i a cikin Littafin Zamanin Nan Namu.


Gargad’i dai a koyaushe yana tafiya da hani da horo da kira ga wani al’amari. A littafin Zamanin Nan Namu wasu karuruwan magangannu da suna ya yanayi na gargad’i musamman idan taurarin suna gudanar da zance a tsakaninsu, kuma idan za a yi gargad’i sai ka ji bayan zantukan da ake jerawa har da karin magana da zai k’ara sa wanda ake yi wa gargad’i ya mayar da hankali. Ga dai misalan wad’annan karuruwan magangannu:

  • Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah

  • Tsuntsun da ya sha ruwa shi ruwa kan doka

  • Asshe ba ki da ta ido

  • Duk wanda ya yi watsi da kayansa sai iska ta watsar a jeji

  • Kowa ya iya allonsa ya wanke

  • Zaki zama kurar ‘yammata a garin nan

  • Jaka sha tik’a

  • Zama da mad’aukin kanwa, shi ke kawo farin kai

  • Har abin kunya ne in huda cikina kuma in dawo ina kirari

  • Gwanin iya ruwa shi ne wanda ya fidda kansa kuma ya fidda wani nasa

  • Duniya ita kan ta makaranta ce, ta yaye marasa jin maganar iyaye.

  • Mutum baya huda cikinsa ya koma yana kirari.


4.0.4.2 Karin Magana Mai Nuni ga Shawara a Cikin Littafin


Shawara dai ta k’unshi wasu zantuka da wani zai yi ga wani domin samar da mafita. Alal misali idan wani abu ya taso kuma ya raba hankalin wanda ya taso ma, yakan tuntu’bi wasu ko wani da ke kusa da shi. Su kuma za su kawo masa bayanai da za su samar masa da mafita. Wasu sukan kawo shawarar k’warai yayin da wasu kuma sukan bayar da shawarar banza.

A cikin littafin nan na Zamanin Nan Namu, marubucin ya yi amfani da wasu karuruwan magangannu da suke nuni ga bayar da shawara. Wad’annan karuruwan magangannu dai sun had’a da:

  • Wadda nike yaba wa salla, ita ce ta kasa alwala

  • Wargi wuri yake yi

  • In k’osar da doki in ya yi k’iba ya harban

  • Zumunta a k’afa take

  • Ai in dukiya ta ‘bace, bai kamata hankali ya ‘bace ba.

  • Itace tun yana k’arami ake iya lank’wasa shi

  • Tsakanin harshe da hak’ori ma ana sa’bawa


4.0.4.3 Karin Magana Mai Nuni ga Raddi a Cikin Littafin


Raddi dai ga Hausawa daidai yake da d’aukar fansa. ‘Daukar fansa kuwa daidai take da rama abin da aka yi wa mutum. Da yawan mutane idan aka yi masu wani abu da bai yi masu dad’i ba sukan fusata su kuma nemi hak’k’insu. Wasu kuma sukan rana har ya wuce kimanin abin da aka aikata musu. Akan yi wa mutumba daidai ba, kuma yana iya d’aukar fansar abin da aka yi masa ku da baki ko da wasu sassa na jiki.

Marubucin wannan littafi ya yi amfani da salon sarrafa harshe, ta hanyar yin karin magana da yake nuna raddi ga wanda ya aikata wani abu da aka samu sa’banin ra’ayi. Ga dai irin wad’annan karuruwan magangannu da suke d’auke da raddi a cikinsu.

  • Karen bana shi ke maganin zomon bana

  • Me gara za ta yi da dutse in banda lasa

  • An dad’e ana ruwa k’asa na shanyewa

  • Ban da akuyar d’aure ta samu saki


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/about-us/

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Babi Na Biyar


5.0.1 Jawabin Kammalawa.


Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah Mad’aukakin Sarki Mai Kowa Mai komai, Mahaliccin sammai da k’assai da ya bamu ikon kammala wannan aikin Bincike. Yabo da jinjina ga AnnabinSa Muhammadu (SAW) Imamin Manzanni Cika makin Annabawa Muhammadu d’an Abdullah, da iyalan gidansa da Sahabbansa da magoya bayansa tun daga farko har k’arshe.

Kamar yadda aka gani a baya mun raba aikin nan namu gida biyar bisa ga tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko ya k’unshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da aka fuskanta.

A babi na biyu kuwa kamar yadda doka ta tanadar mun kawo  Waiwaye A Kan Ayyukan da Suka Gabata inda har muka kawo wasu littattafai da kundaye wad’anda suke da alk’a da namu aiki mun kawo bambancinsu da namu aikin. kana muka yi byanin Salon Nazari da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa mun kawo bayanai a kan tak’aitaccen tarihin marubucin littafin Zamanin Nan Namu, da ma’anar karin magana ida muka ce, “wani zance ne gajere mai ma’ana. Haka kuma mun kawo kashe-kashen karin magana, yayin da muka kawo karin maganar jiya da ta yau kuma muka kawo muhimmancinta ga rayuwar Hausawa da kuma dalilan da ke hardasa a yi karin magana.

A babi na hud’u kuma nan ne muka yi tsokaci Nazarin karin Magana a littafin Zamanin Nan Namu, yayin da muka kawo wasu karuruwan magangannu da daga cikin littafin, kuma mun bi shi tun daga wasa ta farko har ta biyu. Mun kuma fito da karuruwan magangannun da ke ciki don mu ji sauk’in nazarinsu. A cikin babin ne muka fito da wasu karuruwan magangannu da irin rawar da suke takawa wajen gargad’i ko shawara ko raddi.

Shi kuwa wannan babi na biyar shi ne muka kammala aikinmu a cikinsa kamar yadda aka gani yana k’unshe da Jawabin Kammalawa da Shawarwari.

 

 

5.0.2 Shawarwari

Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu d’alibai shawara su mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin k’ok’ari gwargwadon hali, su kasance masu k’wazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to su yi k’ok’ari su d’ora daga inda muka tsaya na wannan bincike.

Muna kira ga wasu wad’anda ba nazarin wannan kundi suke yi ba da su yi k’ok’ari su koyi darussan da ke cikin wannan kundi kar su yi k’asa a guiwa su kasance masu kyautatawa ga al’ummar su ta Hausa. Kuma su saka wayon da yadace da hankalin wad’anda za su yi wa wayon kar su kasance sun tafka kuskure a cikin tsarinsu.

 

Manazarta.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments