Ticker

6/recent/ticker-posts

Harshe Da Adabi: Adon Harshe A Cikin Waƙar Ƙalubale Ta Alhaji AƙIlu Aliyu (5)

NA

FATIMA ISAH RAHAMA

SAMIRA SHEHU HAMZA

LUBABATU ALIYU

SASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA ƘERE-ƘERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA.

OKTOBA, 2017

Babi na Huɗu

4.0.1 Tsokaci a kan Marubucin Waƙar Ƙalubale


Waƙar Ƙalibale dai Aƙilu Aliyu ne ya rubuta ta, kuma shi Aƙilu Aliyu sananne ne, kuma shi asalinsa mutumin ƙasar Kabi ne a ƙaramar hukumar Jega ta jihar Kebbi. An haife shi a Unguwar Ƙaurar Lailai a Jega ta jihar Kebbi a cikin watn Muharram, a shekarar 1918. Ya fara karatun Alƙura’ani a wajen Mahaifinsa wanda aka fi sani da malam Aliyu Madaha saboda shi ma’abucin Ishiriniya ne. bayan rasuwarsa a lokacin Aƙilu yana ɗan shekara kamar sha biyu, sai ya ci gaba da ɗaukar karatu a wajen su Alhaji Mukhtar Tsoho da Mal. Muhammad ɗan Takusa da Mal. Ban-Allah da kuma mal. Abdulmumini, inda ya fara karatun ilimi yana da kamar shekara sha biyar, ya fara Kano. Yana zuwa neman ilimi da sana’a yana komawa, har dai ya ƙware da zama sosai a Kano ɗin, Babban malaminsa na ilimi shi ne Mal. Mahmuda da malam Salga shaihinsu na ɗariƙar Tujjaniyya kuwa shi ne malam Salga. A zaman Aƙilu a Borno inda ya yi shekara ashirin da uku, ya yi siyasa da ƙarfinsa da hazaƙarsa. Jaka kuma ya ci gaba da neman ilimi da yaɗa shi har ya rasu.

Ta fannin waƙa kuwa Aƙilu tun yana yaro ya fara tsara ta, kusan ko yaushe kuwa a cikin halin ƙulla ta yake shi kansa bai san iyakar waƙoƙin da ya shirya ba, saboda yawa sun ɓace amma ba su kasa dubu.

Bayanin da kuma samu a cikin littafinsa na Fasaha Aƙiliyya ya nuna muna cewa, Alhaji Aƙilu Aliyu ya shahara wajen shirya waƙa, haka kuma an daɗe da sanin waƙoƙinsa, daga na addini  da na gargaɗi har zuwa na siyasa don kuwa an buga wasu a littafi, waɗansu kuma a jaridu. Sau da yawa a kan ji shi a gidajen rediyo wasu waƙoƙin kuma akan ji su a fayafan garmaho. A lokacin da yana raye yakan shira waƙa musamman idan an gayyace shi a wani babban taro. Aƙilu ba ɓoyayye ba ne a wajen ma’abuta karatun waƙoƙi na zamani wato rubutattu.

4.0.2 Nazarin Waƙar Ƙalubale ta Aƙilu Aliyu


Kamar dai yadda aka riga aka sani wajibi ne ga dukkan mai nazarin waƙa kowace iri ce ya kamata ya dubi waɗannan abubuwa da suke yin jagora wajen gudanar da nazarin kamar dai jigo da salo da sauran abubuwan da waƙar take da su. Wannan ma haka za a yi har sai kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

4.0.3 Jigon Waƙar Ƙalubale


A waƙar Aƙilu Aliyu ta Ƙalubale da muka nazarta mun gano cewa Jigon wannan waƙar dai shi ne “Ilimi”.

Galibi idan mai rubutu bai fito a fili ya faɗi jigon waƙarsa ba to mai nazari yakan yi la’akari da wasu muhimman kalmomin fannu da waƙa ta ƙunsa don ya gane inda aka dosa. Wannan ya ba mu damar zaƙulo babban jigon wannan waƙar ta amfani da wannan hanyar. Ga kuma hujjar daga waƙar:

Baiti na (9)  “Ina magana kan ilmu ne

A nan ƙunshin sa na walwale?”

          Ko shakka babu idan mutum ya kalli baitocin waƙar zai ga cewa duk ILIMI take magana a kai, kamar dai yadda za a gani a gaba cikin warwarar jigo da zai biyo baya.

4.0.4 Warwarar Jigon Waƙar .


                  Anan za a yi sharhi ne kan Jigo gaba ɗayansa. Za a duba shi dangane da jawaban jigo, da kuma abin da waƙar ta faɗa a taƙaice. To amma muhimmin abin shi ne za a duba lungu-lungu na waƙar dangane da jigo tare da ƙarin bayani daga dukkannin abin da za a iya danganta waƙar da shi. Misali ana iya kawo ƙarin bayani don kafa hujja da misalai daga Alƙur’ani, Hadisi, littattafai, muƙalu, da ra’ayoyi iri daban-daban da dai sauran bayanai da za su taimaka wajen gane abin da waƙar ta ƙunsa da inda aka dosa. ɗangambo, (2007:16)

A ɗan tunaninmu a nan mai nazari yake da babban aiki kuma ja! Domin ana son ya tsattsafe bayanan da waƙar ta ƙunsa ya fito da su daki-daki. Sannan kuma yana da kyau a kalli waƙar ɗaka da waje wato dangantakar waƙar da Alƙur’ani Mai Tsarki ko Hadissai ko wani tarihi na musamman ko ambaton ayyukan ci gaba, ko wata magana mai matuƙar muhimmanci, da dai duk abin da mai sharhi zai iya gano asalinsa ta fuskar waƙa. Ashe ke nan ana son a yi nazarin ƙwaƙwab ga waƙar. Wannan fili ne na faɗin fahimtar mai nazari dangane da abin da ya gano game da waƙar da yake sharhi a kai.

A nan za a yi sharhi na gaba ɗaya tare da fitowa da saƙwannin wannan waƙa daki-daki domin ganin yadda abin yake wakana.

Saboda muhimmanci ilimi da marubucin yake gani da irin riƙon sakainiyar kashin da mutane suke yi masa shi ya zaburar da marubucin ya shirya wannan waƙa don ya ankarar da mutane da su tashi tsaye don su mayar da hankali ga nemansa. Ga dai yadda abin yake a wannan waƙar ta Ƙalubale.

Yanzu bari mu mayar da homa ruwa don ganin iya abin da za mu kamo na wannan sharhin da ya ƙunshi Jigo da Gajerce shi da Warware shi. Ga yadda abin yake.

A baiti na 1-3 Aƙilu ya jefa tambaya ga mutane ta tatsuniyar kacici-kacici, ko zai samu mai iya amsa masa tambayarsa. Ga dai misalin yadda abin yake:

 

1.     Ƙulun ƙulufit abu dunƙule,

 


Ƙalau na ƙale ƙalubale.

 

2.     Kacinci-kacinci: Meye abin,

 


Dake yaɗo kuma dunƙule.

 

3.     ya watsu ya barbazu tattare,

 


da ressa ga shi a mulmule.

Waɗannan baitukan ko shakka babu suna ɗauke da tambayoyi irin na cikin tatsuniyar kacici-kacici. Kuma su waɗannan tambayoyi da Aƙilu ya jefa, ya sani sarai ba wanda zai iya amsa masa su don haka sai ya ƙulla zaren waƙarsa ta hanya bayar da amsar da kansa.

A baiti na 4-8 kuwa marubucin ya ci gaba da nuna wa mutane abin da ya kyautu su yi a kan neman ilimi. Ga dai yadda abin yake a cikin waƙar.

Kadan ka ture zuciya,

                   Da ilmu ake ƙalubale.

Abin da ya kyautu da mu mu yi,

                   Mu himmatu kar mu kashangale,

Mu ƙyale bukata kowace,

                   Cikin ilmi mu shugulgule.

          A Ofis ko a cikin sito,

                   A kowane gu ya maƙalƙale.

          Mu je mu tsaya mu fito da shi,

                   Mu jajjawo shi mu ƙwaƙwale.

A nan Alhaji Aƙilu ya nuna wa mutane abin da ya kyautu su himmatu ga nema wato ilimi.

A baiti na tara kuwa nan ne ya fito da jigon waƙar ƙarara. Ga dai abin da yake faɗa:

Baiti na (9)  “Ina magana kan ilmu ne

A nan ƙunshin sa na walwale?”

          Ko shakka babu idan mutum ya kalli wannan baiti waƙar zai ga cewa ILIMI take magana a kai.

Baiti na 10 -17 marubucin yana ya ci gaba da bayyana wa mutane illar rashin ilimi da makomar marar ilimi. Ga dai abin da yake cewa:

 

10. Kadam ba ilmu gare ka ba,

 


                   Ba ka cure ba, ka dunƙule.

 

11. Ba ka Shafa ba ka lailaye,

 


                   Ba za ka naɗa ba, ka mulmule.

 

12. Kadam ba ilmu gare ka ba,

 


                   Cikin sha’ani kai ne bale.

 

13. Kana kallo a yi ban da kai,

 


                   Ganinka da ji ka dabalbale.

          14 Baƙar magana a yi ma ka ji,

                   A dole ya zan ka daƙile.

 

15. Rashin ilimi in yai duƙu,

 


                   Ba a ga fara ba a dunƙule.

          ............................................................

                   ..........................................................

          Da jin waɗannan baitoci mutum zai fahimci illar rashin ilimi. Kuma duk abin da marubucin ya faɗa yana faruwa ga maras ilim..

Haka kuma a baiti na 18-45 marubucin ya ci gaba da kiran mutane da su hankalto su mayar da hankali wajen neman ilimi kada su yi ƙasa a guiwa. In da yake cewa:

Kiran mu nake jama’a mu ji,

                   Mu amsa kar fa mu daƙile.

          Mu tashi mu miƙe kyam tsaye,

                   Mu nemi sani mu fi’ittile.

          Ina wani in ba ilmu ba,

                   Da in lamari ya dagule.

          Ya kwakkwaɓe ya dabalbale,

                   Yana nema ya jagwalgwale.

          Wa zai tsamo shi ya fidda shi,

                   Irin rikicinsa ya walwale?

          Marar ilimi dattijo ne,

                   Irin na biri mai ɗankwale.

          Cikin zarafin assha da tir,

                   Marar ilimi ya zaƙalƙale.

          Akwai zaƙin baki garai,

Marar ma’ana da yawa tule.

Da jin waɗannan baitukan mutum zai gane cewa, ana kiransa ne ga ya dage ya nemi ilimi. Tunda marubucin ya kawo fa’idoji na ilimi kuma ya kawo illoli na rashinsa.

A ƙarshen baitocinsa ya zo da marufin waƙa duk da cewa bai yi amfani da mabuɗi ba. Ga dai abin da yake cewa a baiti na 47-48:

A wannan garnannan buki,

                   Na waƙoƙi ƙalubale.

          Salamu aikum sai baɗi,

                   Aƙilu Aliyu ya hamdale.

A waɗannan baituka kuwa, da ji za a gane cewa waƙar ta zo ƙarshe. Tun da marubucin ya faɗa cewa sai baɗi kuma ya ce ya hamdale.

4.0.5 Gajerce Jigon Waƙar Ƙalubale


        ɗangambo (2007:15) ya ce, “A nan wurin za a bi waƙa a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da mawaƙi yake faɗa. Za a yi haka ba tare da yin sharhi, bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Misali ana iya cewa a baiti na 1-3 ya ƙunshi yabon farawa, baiti na 4-9 ya ƙunshi gabatar da Jigo.

Idan aka yi la’akari da abin da magabata suka faɗa dangane da Gajerce Jigo za a ga cewa, wannan wurin yana buƙatar a fito da hoton bayanin waƙar a taƙaice ana iya ɗaukar ɗiya ko baitoci na waƙar rukuni-rukuni a fito da muhimman abubuwan da take magana a kai.

        Anan wurin za a bi waƙa a taƙaice baiti bayan baiti ana taƙaita abin da marubucin waƙar ya rubuta/faɗa. Za a yi haka ba tare da yin sharhi ko bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Ga dai yadda abin yake a waƙar Ƙalubale.

 

1.     A baiti na 1-3 marubucin ya jefa tambaya ga masu sauraro ta fuskar tatsuniyar kacici-kacici.

 

2.     A baiti na 4-8 kuwa marubucin ya shiga kira da tunatarwa ga al’umma da su dage wajen neman ilimi.

 

3.     Shi kuwa baiti na 9 a cikinsa ne marubucin ya bayyana jigo waƙarsa.

4.     A baiti na 10-17 marubucin ya ri bayanin makomar marsa ilimi.

5.     A baiti na 18 zuwa 46, marubucin ya mayar da hankali ga bayanin alfanun ilimi da kuma alfanu samun sa. Haka kuma duk a cikinsu ya zu da bayanai na illar rashin ilimi.

6.     A baiti na 47-48 ya rufe waƙarsa. Duk da cewa marubucin mai bi hanyar da aka sani ba wajen buɗe waƙarsa, amma a ƙarshe ya zo da salon rufe waƙar.

4.0.6 Amfani da Adon Harshe.


kafin mu shiga cikin bayanin ya dace mu san mene ne “Ado” sannan Mene ne “Harshe”?

        Mene ne Ado: Ado dai kamar yadda muka sani ana danganta shi da kwalliya, ko wani abu maikyau.

Shi kuwa Harshe: Baiwar da Allah ba ɗan Adam ta amfani da harshe ita ce ta bambanta shi da sauran halittu. Allah ya halicci ɗan Adam ya kuma ba shi harshe ya riƙa yin sadarwa. Da harshe ne mutum ko mutane suke sadarwa a cikin sauƙi. Babu wata hanya wadda dabba yake amfani da harshe yayin da yake sadarwa. Wannan ya sa ɗan Adam ya yi wa sauran halittun duniya zarra.

Idan aka ce mutum ya san harshe to ana nufin yana iya yin magana da harshen jama’a su fahimce shi, su kuma idan suka yi magana ya fahimce su. Wato dai mutum ya bayyana tunaninsa da ke cikin rayuwarsa a fili ta hanyar amfani da sautukan magana har mutane su gane abin da yake ƙoƙarin bayyanawa, ke nan za a ce ya san harshe.

Akwai abubuwa da dama da ke tattare ga sanin harshe, waɗanda idan aka ce mutum ya san harshe to ana nufin ya san dukkan abubuwanan. Su dai waɗannan abubuwan sun haɗa da:

 

1.     Sanin kowane harshe ya ƙunshi sanin sautukan wannan harshe. Wato mai magana ya san sautuka mallakar wannan harshe da yake magana da shi.

 

2.     Sani yadda za a furta sautukan wannan harshe.

 

3.     Sanin tsarin sautukan wannan harshe.

 


Sanin yadda za a danganta sautukan wannan harshe da ma’ana.

Kamar dai yadda muka faɗa a baya cewa Adon Harshe shi ne, “karkatar da wani zance daga sifarsa ta asali zuwa wata sifa ta daban amma yin hakan ya kasance ta hanyar amfani da kwalliya ko tamka ko mutuntarwa ko ƙarangiya ko almci ko kuma jirwaye. (Shiply: 1970)”.

A wannan waƙa ta ƙalubale Alhaji Aƙilu Aliyu ya yi ƙoƙari sosai don kuwa babu wani baiti da bai ɗauke da adon harshe tun daga baiti na farko har zuwa baiti na ƙarshe. Ga dai yadda abin yake.

4.0.6.1 Salon Adon Harshe a waƙar Ƙalubale.


Ga dukkan alamu dai Adon Harshe ya ƙunshi dukkan salailan da muke da su. Kasancewar salo a matsayin gishirin kowane rubutu da kuma zantutuka ya sa muka kalle shi a matsayin adon. Adon Harshe dai kamar yadda L.M. Amin (2014) ya ruwaito daga Shiply (1970) cewa karkatar da wani zance daga sifarsa ta asali zuwa wata sifa ta daban amma yin hakan ya kasance ta hanyar amfani da kwalliya ko tamka ko mutuntarwa ko ƙarangiya ko almci ko kuma jirwaye. Wannan ya fito ƙarara cewa kenan adon harshe shi ne salo”.

 

1.     Salon Ƙarangiya

 


A wannan waƙar ta Ƙalubale marubucin ya yi amfani da salon ƙarangiya. Ƙarangiya dai ita ce sassarƙa kalmomi bisa ga tsari mai ma’ana da ɗaukar hankali.

Aƙilu ya yi amfani da salon ƙarangiya a baiti na ɗaya (1) da kuma   baiti   na arba’in da shida (46). Misali.

 

1.     Ƙulun ƙulufit abu dunƙule,

 


          Ƙalau na ƙale ƙalubale.

 

46. Shaƙwab da laƙwab da na kammale,

 


          A yau za ai ta a daddale.

A waɗannan baitoci mutum zai iya fahimtar wasu karmomi da aka sassarƙa bisa ga tsari mai ma’ana aka tayar da baiti.

 

2.     Salon Siffantawa

 


Salon siffatawa dai kamar yadda malamai suka faɗa cewa shi ne siffanta wani abu da wani daban.

A wannan waƙa Aƙilu ya siffata mutum marar ilimi da dabba biri ga dai abin da yake faɗa:

 

1.     Marar ilimi dottijo ne,

 


Irin na biri mai ɗankwale.

Anan marubucin ya danganta mutum marar ilimi da dabba biri. Haka kuma marubucin da ƙara da siffanta ilimi da abin da ke yaɗo kuma ga shi a dunƙule, kuma ya watsuwa da ykuma bazu. Ga dai abin da yake faɗa:

 

1.     Kacici-kacici me ye abin?

 


                   Da ke yaɗo kuma dunƙule.

 

1.     Ya watsu, ya barbazu tattare,

 


Da ressa ga shi a mulmule.

A nan marubucin ya yi amfani da salon tatsuniyar kacici-kacici ya kuma danganta ilimi da wasu abubuwa masu dunƙulewa da masu watsuwa da masu yaɗuwa da bazuwa.

 

3.     Salon Abuntarwa

 


Salon abuntarwa dai salo ne da ake amfani da shi wajen siffatan mutum ko dabba da wani abu na daban wanda ba mutum ba kuma ba dabba ba.

A nan marubucin ilimi ne ya abuntar duk da cewa ilimi ba mutum ba ne kuma ba dabba ba. Ga dai yadda abin yake a misali.

 

10. Kadam ba ilmu gare ka ba,

 


                   Ba ka cure ba, ka dunƙule.

 

4.     Abuntar Abuntarwa.

 


Wannan nau’in salo shi kuma yana bayani ne a kan yadda mawaƙi ko marubuci ya ɗauki wani abu na daban ya sauya masa sifa zuwa wani abu wanda ba bagirensu ɗaya ba ko yanayinsu ɗaya ba. Misali

A ofis ko a cikin sito,

          A kowane gu ya maƙalƙale

A nan marubucin ya yi amfani da salon abuntar Abuntarwa ya mayar da ilimi wani abu da ake iya taɓawa kamar da yanar gizo, ko wani haki da ake iya gani a taɓa. kamar dai yadda aka gani a cikin baitin sama cewa wai a kowane gu ya maƙalƙale.

 

5.     Yin Tambaya a Ciki Waƙa

 


Marubucin ya yi amfani da salo mai jan hankali yayin da ya gwama tambaya a cikin waƙarsa duk da cewa ba wani yake jira ya amsa masa tambayar ba. Ga dai misalin yadda abin yake.

          Ina wani in ba ilmu ba,

                   Da in lamari ya dagule.

          Ya kwakkwaɓe ya dabalbale,

                   Yana nema ya jagwalgwale.

          Wa zai tsamo shi ya fidda shi,

                   Irin rikicinsa ya walwale?

A waɗannan baitukan marubucin ya yi amfani da salo mai jan hankali yayin da ya jefa tambaya ga masu karatun waƙarsa, duk kuwa da cewa ba jira yake a amsa masa ba.

 

6.     Salon Habarce/Bayar da Labari.

 


Wannan nau’in salo dai marubuta waƙoƙi suna amfani da shi domin su yi kwalliya ga waƙarsu, kuma su fizgi hankalin mai sauraro. A wannan waƙa ta ‘Ƙalubale’ Alhaji Aƙilu ya yi amfani da irin wannan nau’in salo. Misali

 

          Cikin zarafin assha da tir,

                   Marar ilimi ya zaƙalƙale.

          Akwai zaƙin baki garai,

Marar ma’ana da yawa tule.

A nan idan muka lura za mu ga cewa marubucin yana bayar da labari ne na marar ilmi. Inda yake faɗa cewa, duk wani lamari na ci gaba ba a ganin marar ilmi a ciki. Kuma shi marar ilmi yana da zaƙin murya, wato yana iya shirya wa mutum bayanin ƙarya ko ya yi ƙari a cikin bayaninsa.

Babi Na Biyar

5.0.1 Jawabin Kammalawa


Alhamdulillah wannan bincike da muka gudanar a nan ne za a kawo ƙarshensa saboda nan ne za mu biyo da jawabinmu na kammalawa tare da faɗin duk wani abu da ya gudanar a cikin wannan bincike. Kamar dai yadda za a gani.

Baya ga babi na ɗaya da babi na biyu waɗanda suke su abin da ake gudanarwa a ciki bai shafi gundarin aiki ba.

A babi na gaba kuwa an yi tsokaci a kan ma’anar waƙa kuma an kawo muhimman sassan nazarin waƙa kamar su jigo da nau’o’insa kamar babba da ƙarami wato ƙananan jigogi. Haka kuma an yi bayani a kan salo duk a cikin wannan babin na uku. Bayani a kan Marubucin waƙar wato Alhaji Aƙilu Aliyu shi ma yana a cikin wannan babi, yayin da muka faɗa cewa, shi Alhaji Aƙilu Aliyu asalinsa mutumen ƙasar Gwandu ne kuma shi an haife shi a wani gari da ke jihar Kebbi a yau wato Jega. Haka kuma ya tashi a garin Kano ya kuma yi karatunsa a can ya yi aure, ya kuma rubuta waƙoƙi masu yawa, daga ciki kuma har da wannan waƙa da muke nazari a kai.

A babi na huɗu kuwa nan ne muka yi bayani a kan nazarin waƙar wato kamar waɗannan muhimman sassa na nazarin waƙa sai muka yi amfani da su muka ɗan yi sharhi a kan waƙar. An gano babban jigon waƙar inda har aka ce babban jigon shi ne “Ilmi”. Kuma an yi warwarar jigon waƙar, yayin da aka bi ta dalla-dalla ana bayyana jigogin da take ɗauke da su. Haka kuma an gajarce jigonta ana bayyana shi baiti bayan baiti har inda waƙar ta ƙare. Duk a cikin wannan babi an kuma kalli saloda nau’o’insa kana aka duba yadda yake gudana acikin waƙar. An kuma yi hakan ne saboda ganin ita wannan waƙa dukkan salon da ke cikinta na “Adon Harshe” ne.

A babi na biyar kuma nan ne na tattara dukkan abin da aka yi aka zuba shi a cikin jawabin kammalawa sannan aka biyo da shawarwari, kamar dai yadda aka gani.

5.0.2. Shawarwari


A matsayinmu na masu nazarin harshen Hausa muna ba duk wanda zai yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da kundin nan kuma in har binciken nasu yana da alaƙa da namu da su yi ƙoƙarin ɗorawa daga inda muka tsaya kar su kwashe ɗai wannan ba ya taimaka wa nazari. Kamar yadda muka dage muka zaɓo taken da wani bai taɓa yi ba muka yi shige –shige har muka tattaro bayanan da suka gina wannan kundin ya zama abin karatu ga wasu to lallai suma ya zama wajebi su dage don su samar da wani abu mai amfani, ba wai su kwashe abin da wasu suka yi ba.

 

 

 

MANAZARTA


https://www.amsoshi.com/contact-us/

Ratayen Waƙar “Ƙalubale” Ta Alhaji Aƙilu Aliyu.


Waƙar “Ƙalubale”

Ƙulun ƙulufit abu dunƙule,

Ƙalau na ƙale ƙalubale.

Kacinci-kacinci: Meye abin,

Dake yaɗo kuma dunƙule.

ya watsu ya barbazu tattare,

da ressa ga shi a mulmule.

Kadan ka ture zuciya,

Da ilmu ake ƙalubale.

Abin da ya kyautu da mu mu yi,

Mu himmatu kar mu kashangale,

Mu ƙyale bukata kowace,

Cikin ilmi mu shugulgule.

A Ofis ko a cikin sito,

A kowane gu ya maƙalƙale.

Mu je mu tsaya mu fito da shi,

Mu jajjawo shi mu ƙwaƙwale.

Ina magana kan ilmu ne

A nan ƙunshin sa na walwale?”

Kadam ba ilmu gare ka ba,

Ba ka cure ba, ka dunƙule.

Ba ka Shafa ba ka lailaye,

Ba za ka naɗa ba, ka mulmule.

Kadam ba ilmu gare ka ba,

Cikin sha’ani kai ne bale.

Kana kallo a yi ban da kai,

Ganinka da ji ka dabalbale.

Baƙar magana a yi ma ka ji,

A dole ya zan ka daƙile.

Rashin ilimi in yai duƙu,

Ba a ga fara ba a dunƙule.

Kiran mu nake jama’a mu ji,

Mu amsa kar fa mu daƙile.

Mu tashi mu miƙe kyam tsaye,

Mu nemi sani mu fi’ittile.

Ina wani in ba ilmu ba,

Da in lamari ya dagule.

Ya kwakkwaɓe ya dabalbale,

Yana nema ya jagwalgwale.

Wa zai tsamo shi ya fidda shi,

Irin rikicinsa ya walwale?

Marar ilimi dattijo ne,

Irin na biri mai ɗankwale.

Cikin zarafin assha da tir,

Marar ilimi ya zaƙalƙale.

Akwai zaƙin baki garai,

Marar ma’ana da yawa tule.

A wannan garnannan buki,

Na waƙoƙi ƙalubale.

Shaƙwab da laƙwab da na kammale,

A yau za ai ta a daddale.

Salamu aikum sai baɗi,

Aƙilu Aliyu ya hamdale.


Post a Comment

0 Comments