Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummuwar Kasuwar Tsaye, Wajen Samar Wa Matasa Aikin Yi A Garin Tsafe

NA
MARYAM MUHAMMAD
SAMIRA LAWAL                 
ASMA’U RABI’U                  

SASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA K’ERE-K’ERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA.

www.amsoshi.com

SHEDANTARWA


Wannan aiki ya samu dubawa da tabbatarwa tare da kar’buwa gami da amincewar wad’annan malamai.

MAI DUBA AIKI NA CIKI (Project Supervisor)


Mal. Habibu Lawal K’aura

Sa-hannun…………………………………….

Kwanan wata…………………………………

SADAUKARWA


Mun sadaukar da wannan aiki ga mahaifanmu da kuma mazajen mu, Kamar Rabi’u Abdullah Dan Gido da Alh. Lawal Jibril Jangebe da Malam Muhammad Nahuce sai mai gidana Doctor Bashir Isah Tsafe sai malam Ibrahim nahuce, da Abdurrasheed (Tsoho) Allah ya saka masu da Alheri tare da yi masu sakayya da gidan Aljanna Ameen.

 

 

GODIYA


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.

Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun farko har ya zuwa ranar k’arshe.

Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka muna domin ganin hak’armu ta cimma ruwa, musamman ga iyayenmu da suka jure da yin hak’uri da mu har muka cimma wannan lokaci, haka kuma muna mik’a godiyarmu zuwa ga mazajenmu da suka bamu goyon baya har Allah ya nufemu da gama wannan karatu tare yin wannan kundin. Iyayen da mazajen sun had’a da: Malam Rabi’u Abdullah ‘Dan gido da Alh. Lawal Jangebe, da malam Muhammad Nahuce. Haka kuma muna mik’a godiya ga sauran ‘yan’uwa da iyayenmu kamar Abdullkarim Abdullah, Sani Abdullahi, Dangalima da malam Nasiru Ishaka da Akilu Ishaqa da Hassan Rabi’u Husaini Rabi’u Abdulrahman Rabi’u, Hanasa’u Sani, A’ishatu, Hussaini, Sadiya, Nusaiba, Aliyu, Habiba, Hairatu, da Hafsat da Sadiya da Ibrahim Shamaki, da Sulaiman (‘Dan’uwa) Dama wad’anda da Allah bai bamu ikon fad’iba duk Allah ya sa mugama da duniya lafiya Ameen.

Suma dai ‘yanuwa da abokan arziki ba za mu bar su a baya ba sai mun yi godiya a gare su Allah ya saka masu da alherinSa amin

Haka kuma muna mik’a kyakyawar  godiyarmu ta musamman ga malamanmu Na wannan sashe kamarsu; Malama Habibu Lawal K’aura wanda ya d’auki tsawon lokacinsa yana kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo k’arshe Allah ya saka masa da mafificin alherinSa amin. sai Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Malam Haruna Umar Bungud’u, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba, Mal. Habibu Lawali K’aura, Mal. Aminu Saleh, Mal. Husaaini Aliyu da Mal Isah Bala Homawa da Mal. Salihu Jangebe da Mal. Bashir tsafe da dai sauran su.

 

 

JINJINA


Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu jinjina ma malaman mu musamman Mal. Habibu lawal K’aura da ma wasu daga cikin mutanen da suka taimake muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan d’alibai da ma duk masu neman k’arin haske dangane da aikinmu. Muna masu rok’on Allah ya saka masu da maifificin alheri. Amin.

 

K’UNSHIYA


Shaidantarwa -      -        -        -        -        -        -        -        ii

Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        -        -        iii

Godiya        -        -        -        -        -        -        -        -        iv

Jinjina         -        -        -        -        -        -        -        -        vi

K’unshiya    -        -        -        -        -        -        -        -        vii

BABI NA ‘DAYA


1.0 Gabatarwa       -        -        -        -        -        -        -        1

1.0.1 Yanayin Bincike    -        -        -        -        -        -        2

1.0.2 Muhallin Bincike   -        -        -        -        -        -        3

1.0.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike    -        -        -        -        3

1.0.4 Manufar Bincike     -        -        -        -        -        -        4

1.0.5 Matsalolin Da Suka Taso  -        -        -        -        -        5

1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta      -        -        -        -        6

BABI NA BIYU


2.0.1  Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata   -        -        8

2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -        -        -        -        -        14

Babi Na Uku


3.0.1 Ma’anar Sana’a

3.0.2 Tak’aitaccen Tarihin Samuwar K’agaggen Labari-  -        18

3.0.2.1 Tsokaci A Kan Littafin Ruwan Bagaja        -        -        21

3.0.3 Muhimmancin Bid’a        -        -        -        -        -        22

3.0.4 Illolin Bid’a A Cikin Labarai      -        -        -        -        23

3.0.5 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        24

Babi Na Hud’u


4.0 Gabatarwa       -        -        -        -        -        -        -        25

4.0.1 Tasirin Bid’a A Cikin K’agaggen Labari        -        -        -        25

4.0.2 Bid’a A Littafin Ruwan Bagaja  -        -        -        -        28

4.0.3 Had’uwar Imam Da Zurk’e        -        -        -        -        -        29

4.0.4 Naman Ruwan Bagaja      -        -        -        -        -        30

4.0.5 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        31

Babi Na Biyar


5.0 Jawabin Kammalawa -        -        -        -        -        -        32

5.0.1 Shawarwari  -        -        -        -        -        -        -        34

Manazarta         -        -          -        -        -        -        -        -        35

 

 

 

 

BABI NA ‘DAYA




  • Gabatarwa




Wannan bincike zai gudana ta hanyar nuna muhimmacin kasuwanci musamman a wannan yanki. Bincike na haskakawa mai nazari hanya don fahimtar abin da bai sani ba ko wanda ya shige masa duhu. Haka kuma za mu yi tsokaci a kan muhimmancin kasuwar tsaye.

Domin samun sauk’in gudanar da wannan aiki za mu kasa wannan aiki namu zuwa babi-babi har babi biyar kamar yadda dokar rubuta kundi ta tanada.

A babi na farko zamu yi Gabatarwa da Yanayin Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da Aka Fuskanta.

A babi na biyu kuma zamu yi tsokaci dangane da Waiwaye a kan Ayyukan Da Suka Gabata da Salon Nazari Zubi da Tsarinsa.

Babi na uku kuwa zamu kawoMma’anar Kasuwa. Takaitaccen Tarihin garin Tsafe, Ma’anar Sana’a da Ire-Iren Sana’a da Dalilin Yin Sana’a Cigaban da aka samu a fagen kasuwanci a garin Tsafe.

A babi na hud’u nan ne  za mu yi tsokaci a kan kasuwar tsaye, da kuma Asalin Kasuwar Tsaye da Nau’oin  kasuwunne da kuma Asalin kasuwar tsaye da kayyayakin da ake tu’ammali dasu a kasuwar tsaye, da kuma lokacin kasuwar tsaye.

A babin k’arshe, wato babi na bayar zamu nuna yadda zamu kammala wannan bincike ne kuma zamu ba da shawarwari ga masu bincike daga nan sai mu kawo ta’arifin wasu kalmomi.


  • Yanayin Bincike




Hak’ik’a mutanen da suka kafa kasuwar tsaye sun yi k’ok’ari domin kafa hanyoyin kasuwanci masu sauk’i ga matasa marassa aiki yi, ta yadda zasu samu su yi kasuwanci mai sak’i domin su nema wa kansu halal. A wata fad’a ta Hausawa suna cewa “ Neman Halak da Wuya” .

Wannan bincike na da yanayi na dubawa, saboda matsayinsa na ilimi, kuma wannan aiki na bincike ya sha bam-bam da sauran bincike da ake yi. Dalili shi ne, wannan fanni na sana’a an gudanar da ayyuka a cikinsa sai dai bai samu wasu ayyuka masu yawa da suka had’a da nazarin Kasuwar Tsaye ba musamman wadda ta shafi garin Tsafe

Wannan ma ya sa a yunk’urinmu na gudanar da wannan aikin Binciken mun sha wahala sosai saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi magana a kan wannan aiki namu. Haka kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala matuk’a.


  • Muhallin Bincike




Hausawa kan ce kowane Allazi da nasa Amanu, amma wasu kuma sun ce ai wani Allazi Kafaru yake da shi. Abin nufi dai shi ne, a duk lokacin da wani ko wasu za su yi aiki irin wannan na bincike to wajibi ne ya samu wani muhalli da zai ke’bance aikinsa gare shi saboda samun sauk’i.

Wannan bincike mun gudanar da shi ne a ‘bangaren abin da ya shafi sana’a, kuma kasuwar tsaye ita ce muhallin da muka ke’bance wannan aikin namu gareta.

 Hanyoyin Gudanar Da Bincike


Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka wad’anda suka gabata domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi daban-daban don k’arin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.

Kamar yadda bayani ya gabata mun  lura da cewa, dukkan mai aikin bincike dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar da wannan bincike namu domin kuwa mun ziyarci mutane da dama da suka danganci tsofaffi masu masanniya a kan yadda sana’o’i musamman na gargajiya da kuma wasu wad’anda suka samu amfana da sana’o’i ta hanyar wannan cibiyar da muke bayani a kanta.


  • Manufar Bincike




Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano cikakkiyar k’warewar d’alibai da fahimtarsu da hazak’arsu. Ta wannan hanyar karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya k’ara tabbatar da abin da aka riga aka sani a fagen ilimi.

Binciken yana fitar da bayanai domin amfani al’umma, wani babban muhimancin bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.

Manufar wannan binciken ita ce, domin mu fito da bayanai da suka danganci kasuwar tsaye  da kuma irin gudummuwar da ta bayar wajen samar da sauk’i ma su saye da sayarwa tare da samar da aikin yi ga wad’anda ba su da aikin yi a garin Tsafe. Ba nan kad’ai ba sai har mun gano irin wad’annan mutane da suka amfana da wannan kasuwa.


  • Matsalolin Da Suka Taso




Wannan bincike namu mun gudanar da shi ne a kan hanyoyin da suka dace, na irin hanyoyin da ake bi wajen samun bayanan da suka dace ta hanyoyi da dama. Mun ci karo da matsaloli da dama wajen binciken mu kamar haka.

Rashin isassun kud’in mota, da matsalar iske wad’ansu masana ko wad’anda za a tattauna da su, da muke son mu tuntu’ba wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kud’in mota domin zuwa wajen  wad’ansu mutane da abin ya shafa, sai mu iske ba su nan. Haka ma kowa ya san irin halin da ake ciki a k’asar nan na rashin tsaro, a inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole sai da taka tsantsan.

Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu d’alibai mata masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama  sun sha kanmu. Daga cikinsu akwai:

Matsalar kar’bar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji da ta k’arshen zangon karatu.

Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka had’a da girke-girken abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk wad’annan matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo  da su .

Akwai matsalar tuntu’bar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu ba su da wani isashen lokaci da za su tsaya su yi muna bayani, don haka wasu sai ka d’an rik’a masu wani abu kafin ka je wurinsu.

Haka ma akwai matsalar yawan d’aukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta d’auke. Kad’an kenan  daga irin matsalolin da muka ci karo da su.

 


  • Matsalolin da aka Fuskanta




Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka, wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kud’i da za mu buga wannan aiki namu. Haka kuma akwai matsalar had’uwarmu idan mun yi alk’awali, kuma idan za mu tafi wajen  ganawa da wad’anda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne a same su ba.

Haka akwai sha’anin rashin lafiya yakan kama magidanci , ko kuma halin tafiya wajen k’aro ilimi wato a bangaren su masana.

Ba nan kad’ai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar karancin lokaci. Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a cikin shekara d’aya.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

BABI NA BIYU


2.0 Waiwaye A Kan Ayyukan Da suka Gabata


Anan za muyi waiwaye ne a kan wasu daga cikin ayyukan da suka yi kama da namu in da zamu duba wasu kundayen bincike da suka gabata masu alak’a da wannan bincike da zamu gudanar.

Wannan tunani namu ne tare da taimakon malami mai duba aikinmu. Don haka zamu iya bayani wasu daga cikinsu da suka gabata kamar haka:

Zarruk da wasu, (1982) sun rubuta littafi mai suna, “Zaman Hausawa” a cikin wannan littafi nasu sun raba sana’o’in Hausawa zuwa gida biyu, wato tsofaffin sana’o’i a yayin da sana’ar kad’i, sak’a, d’inki duk suna cikin tsofaffin san’o’in Hausawan. Kuma sun yi cikakken bayanin sana’o’in gaba d’aya.

Da wannan ne muka ga cewa nasu aikin yana da dangantaka da namu kundin da muke gudanarwa, saboda suna bayani a kan sana’o’in Hausawa mu kuma muna bayani a kan kasuwar tsaye ta garin Tsafe.

Bashir da wasu(1982), su ma sun rubuta wani littafi mai suna “zaman Hausawa” a cikin littafin sun bayyana yadda Hausawa suke zaune ciki kuwa har da sana’o’in Hausawa da yadda sana’o’in suke gudana. Malaman sun bayyana sana’o’in Hausawa. Wannan littafin ya haska muna fitila wajen samun wasu hujjoji da za mu gabatar wajen gudanar da wannan kundin namu.

R.M Zarruk da wasu (1987) mai suna “Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa” Don k’ananan makarantu. Wannan littafi ya dubi wasu abubuwa ne da suka shafi adabi da sana’oin gargajiya da noma da kiyo, littafin zai taimaka mana gaya domin mun samu bayanai da suka fad’ad’a aikinmu.

Aikin nan na su Zarruk yana da alak’a da namu aikin saboda sun yi tsokaci a kan abin da ya shafi sana’a yayin da namu aikin ma yana da bayanai da zai tattaro a kan sana’a, don bayanin kasuwa ba zai cika ba sai da sana’a. Haka kuma inda gizo ke sak’a shi ne ayyukan suna da bambanci saboda su aikinsu ya game duk adabi da al’ada yayin da namu kuma kasuwa ce ya k’unsa ko kasuwa na tsaye kuma ta garin Gusau.

Garba, (1991), a littafinsa mai suna, “sana’o’in Gargajiya a K’asar Hausa” inda ya kawo sana’o’in Hausawa bisa ga rukuninsu. Ya kawo masu aiwatar da irin su kiyo, noman damina, noman rani, inda har ya kawo, wasu dabbobi da ake mu’amula da su kamar su rak’umi a cikin rukunin masu sauk’in sarrafawa. Ya kuma yi bayanin shanu da ragona da awaki, sai ya kuma yi tsokaci dangane da sana’ar fawa.

Wannan aiki na Garba yana da alak’a da namu saboda shi yana magana a kan sana’ar gargajiya, inda har ya kawo sana’ar fawa a ciki da irin dabbobin da ake yankawa a cikin wannan sana’ar. Ta wannan ‘bangare ne muka samu dangantaka da shi, amma kuma inda muka sha bamban shi ne mu aikinmu ba a kan sana’ar fawa muke yinsa ba sai dai muna magana ne a a kan kasuwar tsaye a garin Tsafe.

S.A Sadi (1994) ya rubuta wani littafi mai suna “Tsafe Garin “Yandoto” wannan littafin an kawo Tarihin Garin Tsafe da Sarakunansu da Yananyin Mulkinsu. Haka kuma ya ta’bo yanayin kasuwanci na garin da makamantasu. Don haka wannan  litafi zai taimaka ga aikinmu gaya duk da cewar namu zai ya karkata ne a kan kasuwar tsaye a garin Tsafe.

Asiya B. Da wasu (2002), a kundinta mai taken “Sana’ar Rini A K’asar Hausa A Garin Zariya” don samun nasarar kammala karatunta na N.C.E a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau, Jihar Zamfara. A kundin sun yi bayanin sana’a da muhimmancinta ga rayuwar al’umma, wannan kundin yana da nasaba da namu dalili kuwa shi ne sun ta’bo muhimmancin sana’a ga al’umma sai dai sun bambanta saboda ita tana dubin sana’ar rini mu kuma mun mayar da hankali ne ga kasuwar tsaye ta garin Tsafe.

Umma, (2003), ta rubuta kundi mai taken “Sana’ar K’ira A Garin Katsina” don samun takardar shedar kammala karatun N.C.E a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau, Jihar Zamfara. Wannan kundin ya haskaka muna hanya sosai wajen samu wasu ayyuka da suka danganci namu. Umma dai tana nazarin sana’ar K’ira ne inda ta kawo ma’anar sana’a kuma ta yi bayanin sana’ar k’ira ta kawo muhimmancinta ga rayuwar al’umma. Kasancewar wannan kundin namu yana bayanin ne na abin da yake da alak’a da sana’a ya sa muke ganin aikin Umma yana da alak’a da namu aikin, sai dai mu ba wai sana’a ce kawai muka mayar da hankali ba sai dai hankalinmu ya karkata ne ga kasuwar tsaye ta garin Tsafe

Nafisa (2003), ta rubuta kundin bincike mai taken “Sana’ar Jima a Garin Gusau”, ” don samun takardar shedar kammala karatun N.C.E a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau, Jihar Zamfara.

Kundin ya yi tsokaci dangane da ma’anar sana’a da yadda ake gudanar da ita kana ta bayyana matsayin masu sana’ar a idon jama’a. Wannan kundin ya yi kama da namu aikin ta fusakar kawo ma’ana da asali da muhimmanci na sana’a, sai inda bambancin yake ita tana nazarin sana’ar Jima ne mu kuma muna nazarin kasuwar tsaye ta garin Tsafe.

Hassana (2003), wannan d’alibar ta rubuta kundin mai taken “Sana’ar Fawa A Garin Gusau” wannan kundin ya yi muna amfani matuk’a saboda ta hanyarsa ne muka k’ara samun wasu ayyuka da suka gabata. Manazarciyar ta yi bayanin sana’ar fawa da yadda ake yinta da muhimmancin ta ga rayuwar al’umma tare da yadda take gudana a cikin garin Gusau a halin yanzu.         Wannan kundin yana da alak’a da namu sai dai mu namu yana kallon kasuwar tsaye ta garin Tsafe. Ta rubuta wannan kundin ne domin samun takardar shedar kammala karatu a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau, Jihar Zamfara.

Zainab da wasu (2012), sun rubuta kundin domin samun takarda shedar kammala karatun N.C.E. a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya, Da Ke Garin Gusau. Kundin mai taken “Nazari A Kan Sana’ar Kad’i Da Yadda Ake Yinta A Da, Da Yanzu”. Sana’ar kad’i dai ita ce wadda ake sarrafa auduga ta koma zare, shi kuma zare ana iya samunsa a kasuwar tsaye ta garin Tsafe. Da wannan ne muke ganin aikin yana da alak’a da namu aikin saboda an yi bayanin wani abu daga cikin abubuwan da ake iya samu a cikin wannan kasuwar ta tsaye.

Salamatu  da wata (2013) a kundin su mai taken: “Nazari a Kan Kasuwar Kanawa da ke Garin Gusau” a wannan kundin sun yi k’ok’arin bayani  a kan tarihin samuwar kasuwar Kanawa da Asalinta da Tak’aitacen Tarihin Garin Gusau, haka kuma sun yi bayani a kan irin Rawar da Kasuwar ke Takawa wato ta hanyar samar da abubuwan masarufi da kuma yanayin kud’in shiga da take samarwa. Marubutan sun kawo muhimmancin kasuwar ga al-umma garin. Wannan aikin zai taimaka mana domin yana da alak’a da namu, don haka aikin zai haskaka ma wanda zamu yi nazari a kansa. Ayyukan suna da bambanci saboda su Salamatu sun mayar da hankali a ne a kan kasuwar Kanawa da ke garin Gusau, yayin da mu kuma aikinmu yana bayani ne a kan kasuwar tsaye a garin Tsafe.

2.0.2. Salon Nazari Da Zubi Da Tsarin Bincike


Salo shi ne hanyar da marubuci ke bi domin samun nasarar isar da sak’onsa ga masu karatu ko sauraro.

Idan aka ce salo to, ana nufin duk wata dubara da marubuci ko mai magana ya bi wajen isar da sak’onsa a cikin sauk’i.

Gusau (1993: 5), cewa ya yi. “salo shi ne hanyar da ake bi a nuna gwaninta da dubara a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da za’bar abubuwan da suka dace game da abin da yake son bayyanawa.

A duk lokacin da aka yi maganar salo ana magana ne a kan irin k’warewar manazarci, wajen aikin bincike da kuma yadda yake jawo hankalin mai karatu a kan aikin da marubucin ya yi a kowane lokaci.

A wannan kundin dai za mu yi amfani da salo mai burgewa wajen aiwatar da wannan kundin ta yadda duk wani ya d’aga shi sai ya amfana matuk’a. Wannan ba ya rasa nasaba da irin ziyarar da za mu yi a wuraren da ake gudanar da wannan sana’ar wato kasuwar tsaye ta garin Tsafe. Don haka muka yarda cewa dukkanmu za mu ziyarci wannan kasuwa don mu ga irin kayan da ake sayarwa a wannan kasuwar domin samun ingantacciyar hujja.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

BABI NA UKU


3.0.1 Ma’anar Sana’a


Sana’a ita ce samuwar hanya ta neman abinci da d’an Adam zai yi domin neman halaliyarsa. Sana’a kan iya zama ta aikin k’arfi, wato neman halaliya ta yin aikin mai wahala kamar su noma, gini, k’ira, jima, kad’i, d’inki da sauran su. Ta kan iya zama ta hanyar jiya, wato biyar ta koma goma wato aikin gwamnati a tak’aice dai duk wani aikin da d’an Adam zai yi ta zama sanadiyar samuwar kud’i a gare shi. Duk abin da mutum zai yi ya samu wani abin da zai gudanar da rayuwarsa da ta iyalinsa kuma jama’a suka san shi da ita wannan shi ake kira sana’a.

Sana’a dai ita ce saye da sayarwa ko aikata wani akin da zai samar wa mutum riba da zai iya ya kore wa bakinsa k’uda. Idan mutum ya samu wata hanya ta samun kud’i ko samun abinci ko biyan wasu buk’atu kuma jama’ar da ke kusa da shi suka sani cewa wannan abu da wane yake yi yana samar masa da abin da zai iya yin lalurorinsa wannan shi ne sana’a.

Sana’a hanya ce ta sarrafa albarkatun k’asa da sauran ni’imomi da Allah ya yiwa d’an’Adam kamar amfanin gona da dabbobi da tsirrai da kuma wasu albarkatu wad’anda suke k’ark’ashin k’asa, ya Allah dutse ko kuma ruwa domin samun abin masarufi. Haka nan kuma za mu iya cewa sana’a hanya ce wadda ta danganci tono albarkatun k’asa da sarrafa su ta hanyoyin kimiyya da ni’imomi da suke tattare da d’an’Adam da sha’anin kasuwanci na saye sa syarwa. Sana’a ita ce mafi girman matsayi da Hausawa suke amfani da sunan don dogaro da kai.

Wasu masana sun bayana sana’a da  cewa wata abu ce wadda mutum yake koyo ya  iya, wadda kuma sai da ita ce mutum yake iya zaman duniya mai amfani. Kowace sana’a tana da amfani ga al’umma, kuma kowane mutum da sana’ar da ya iya yake ci yake sha.

3.0.2 Ire-Iren Sana’a


Nau’o’in sana’a wasu abu ne masu muhimmanci domin sukan fitar da irin ressan da sana’a take d’auke da su. Bisa ga irin abubuwan da ake amfani da su a lokacin da ake aiwatar da ita muna iya cewa, sana’a tana da ressa masu tarin yawa da suka had’a da: Noma, k’ira, Jima, kad’i, d’inki, sak’a, sassak’a, fawa, sarkanci, wanzanci, da dai sauransu. Ba za a iya cewa ga iya adadin nau’o’in sana’a ba. Wasu suna saye da sayarwa, wasu bankwai suke yi wasu tireda, wasu dako, wasu lodi da saukale, wasu lebaranci sukai wasu kanikanci suke yi, kai abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa.

Wannan bincike ba bayanin su za a yi ba, sai dai kamar yadda aka gani wad’annan su ne ake kira sana’o’in Hausawa. haka kuma ana iya samun wasu sana’o’i da ba na gargajiya ba kuma ba na gado ba, kamar saye da sayarwa na wasu kayan amfanin jama’a. kamar dai kayan aikin gona da kayan aikin gini, da kayan aikin girke-girke da kayan masarufi da kayan ci da na sha da kayan miya da kayan gyaran abinci da k’walama kamar kayan tand’e-tand’e da lashe-lashe.

Akwai kuma wasu kayan buk’ata na rayuwa da al’umma ke sayarwa masu buk’ata suma duk suna cikin sana’o’in da ake yi a k’asar Hausa.

3.0.3 Sana’o’in Da Suka Shafi Jinsin Mata


Akwai sana’o’i da dama da suka shafi jinsin mata wad’anda mata ne kawai ke yinsu ba da maza ba. Wasu kuma idan ka ga maza na yinsu to lallai sai dai ‘yan daudu ko kuma wasu d’ai-d’aiku. Wad’annan sana’o’in sun had’a da: Sana’ar Kitso, Sana’ar Koda, Sana’ar Dafe-Dafe, Sana’ar Dawo da dai makamantansu.

Misali, Sana’ar Kitso wannan sana’a ce da mata ke yi suna samun wani abu. Sukan tanadi wasu kayan aikin sana’ar su kamar mashaci, da  tsinke wanda suke yi tsagar gashi da shi yayin da suke yin kitso.(Tcinke). Matar da take buk’atar a yi mata kitso takan kwance/banye gashin kanta ta wanke ta saka mai irin wanda ta fi son ta yi buk’ata da shi sai ta sa a kanta sai ta nufi inda wadda take yin kitso take domin a yi mata wannan kitson irin wanda take buk’ata, wasu suka ce a yi masu zanen yawo, wasu kuma sukan yi wibin ko kalaba ko shuku ko kwando, ko dai wani nau’in na daban.

 

 

3.0.4 Sana’o’in Da Suka Shafi Jinsin Maza


Kamar dai abin da muka ambata cewa, akwai sana’o’in da suka shafi jinsin mata to, haka kuma akwai wasu sana’o’i da jinsin maza ne suka fi aiwatar da su. Ba wai lallai sai maza ne kawai keyinsu ba amma mafi yawan sana’o’in maza ne suka fi yinsu. Irin wad’annan sana’o’i sun had’a da: K’ira, Rini, Jima, Farauta, Noma, Dukanci, Tauri, Dambe, Kokawa, Wanzanci, Sarkanci, K’wadago, Sassak’a, Sodori, Bashirwanci, da dai makamantansu.

Sana’ar Fawa: Sana’ar Fawa dai sana’a ce ta mahauta, wadda mafi yawan masu yin ta sun gada ne, wad’ansu kuma ba su gada ba. (Calvic Y. Garba 1991)

Sana’ar fawa wata sana’a ce ta Hausawa, ta gargajiya wadda ake sayen dabba a yanka ta a sayar da namanta, domin miya ko wata buk’ata. Ana sarrafa naman ne ta yin balangu, ko a soye ko a yi kilishi ko a dafawa ko a yi tsirai ko langa’bu ga jama’a masu buk’ata.

Don haka fawa sana’a ce ta rundanci, wadda ake yanka dabba don a sayar da namanta ga jama’a, haka kuma sana’ar fawa ta k’unshi tun daga kawo dabbab zuwa mahauta, kayar da ita, yankawa da fed’ewa da rarrabawar k’ashi da tsoka da sayar da naman d’anye ko balangu don sayarwa tare da zimmar cin riba.

3.0.5 Sana’o’in Da Aka Yi Tarayya Tsakanin Maza Da Mata.


Su wad’annan sana’o’i dai kamar yadda aka ce na tarayya ne to dukkan jinsin biyu suna iya yinsu kuma ba ya zama wani abu. A al’adar Hausawa wasu sana’o’i da suke na mata ne idan aka ga namiji ya shiga yinsu to, sai a kama kallonsa da wani abu daban marar kyau, saboda a ganin su ya sa’bawa al’adun malam Bahaushe. A wasu lokuta kuma har da tsarguwa tana shiga a ciki har ta kai a a la’anci mai yin sana’ar ba don sana’ar ba ta yuwuwa ba. Haka abin yake ga sana’o’in da suke na maza ne idan mace ta shiga dumu-dumu a ciki sai ka ga mutane suna kyamarta ko ma su la’ance ta.

Duk da cewa sana’a da ake yi tana da gurbin da ya dace ta fad’a dangane da jinsin al’umma. Wato kamar sana’o’in da suka danganci jinsin maza da kuma wad’anda suka danganci jinsin mata. Akwai kuma wasu sana’o’in da suke an yi tarayya a wajen yinsu wato maza na yi kuma mata na yi. Irin wad’annan sana’o’in sun had’a da: Malanta, Kad’i, ‘Dinki, Sak’a, Kiyo, Dillanci da dai sauransu.

Domin mu samun d’aure akuyarmu a kan magarya za mu d’auki d’aya daga cikin wad’annan mu d’an yi tsokaci a kai.

3.0.6 Muhimmanci Sana’a Ga Al’umma.


        Sana’a dai kamar yadda aka sani tana da matuk’ar muhimmanci ga al’umma amma yanzu bari mu kawo wasu bayanai da za su tabbatar da haka.

  • Sana’a tana samar da aikin yi ga al’umma. Idan kana da sana’a to lallai ya zama wajibi kai ka k’aru su kuma al’ummar da suka saya su samu biyan buk’atarsu.

  • Sana’a tana rage sace-sace ga al’umma.

  • Sana’a tana rage zaman Banza ga al’umma.

  • Sana’a tana rage dogaro ga gwamnati, da wasu ‘yan siyasa.

  • Sana’a tana tare da albaka saboda annabi Muhammad (SAW) ya bayyana cewa, albarka tana cikin sana’a.

  • Sana’a tana samar wa mai ita kud’i da suna da girma.


Idan muka yi la’akari da wad’annan muhimman abubuwa da muka zayyana za mu ga cewa, suna daga cikin muhimman abubuwan da rayuwa ta k’unsa. Kuma dukkansu sana’a ce take samar da su.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

BABI NA HU’DU


4.0.1 Tak’aitaccen Tarihin Garin Tsafe


Tarihi dai shi ne  adananun al’amuran  da suka riga suka shud’e. Haka kuma tarihi ya bayar da k’arfi ne kawai ga abin da  ya riga ya shud’e ko kuma abun da gashi ama ana son gano asalin tarihinsa. Tarihi  ya shafi kowane fannin ilmi da kuma rayuwar d’an’Adam da kuma bayar da bayani filla-filla da suka  haifar da wasu al’amura ko kuma shud’ewarsu.

Bala Usman yace “A gaskiya mafi yawan tarihin Tsafe sai do ko ka dogara da hira da datijai” to wannan kusan haka ne domin cikin tuwasan tarihin uku na tarihin yammacin afrika kafin zuwan turawa guda biyu ne kawai ake d’an samun tarihin Tsafe a ciki wato tushen marubuta ‘yan gida na afrika cikinsu akwai 1905 to sanan tarihi akhabari wato tarihin Hausa wanda matan Isyaku Tsafe ya rubuta a 1911.

Asalin sunan Tsafe babbar matsalar a nan ta sh’anin tarhin Tsafe ita ce, ta had’a da abubuwa guda uku su ne (a) asalin sunan Tsafe (b) farkon zama ko kafa garin Tsafe ko zuwa wad’anda suka kafa garin (c) farkon fara shiga, bancin garin inda muka samu zantawa da wani ya fad’a mana wasu abubuwa game da garin inda yace “yankin k’asar Tsafe gunduma ce kuma yanzu Tsafe hedikwata ce ta k’aramar hukumar Tsafe kusan kilomita 48 gabas daga garin Gusau a kan hanyar Zariya zuwa Gusau. A 1911, mataimakin D.O (wato A.D.O) tawi Bature cikin Turawan Mulkin Mallaka wai shi Kyaftin Blake ya zaga yawon tantance yankin gundumar Tsafe a inda ya nuna cewa k’asar Tsafe tana da iyakoki samammu na yanayi.

Bisa k’iyasin turawa, k’asar Tsafe tana  kan fad’in k’asa 110 inci  da 57  arewa da tsawon k’asar 60 55 daga gabas. Wato ta yi iayaka da gulbin Gagare daga gabas (in ban da wajen su hayin Alhaji da ‘yar Talata da U/sarki da sauransu. Wad’anda ke gabas da shi kad’an). Wato daga wannan gefen ta yi iyaka da yankin ‘Dank’ara. Kudu maso gabas kuma ta yi iyaka da k’oramar Jauri, daga kudu sosai kuma  ta yi iyaka da k’oramar Bilbis wato yankin Faskari da ‘Yankara ( rabin mil kenan Kudu daga ‘Danwuri). Daga Yamma kuwa ta yi iyaka da gulbin Sakkwato da k’oramar Marra, wato mil uku Arewa da Rakya’bu ko kuma mil guda Kudu da garin ‘Yandoto. Bisa wad’annan iyakokin Eric Saxon ya ce, “K’asar Tsafe tana da murabba’in fad’in k’asa na mil 400.

Ko kuma a ce ka d’auki duk (Taswirar) k’aramar hukumar Tsafe amma ka d’ebe duk abin da yake bayan gulbin Sakkwato daga Yamma da shi; Sannan Arewa ka yi k’asa mil guda Kudu daga garin ‘Yandoton Daji, Kudu kuwa har Bilbis da Wanzamai; Gabas kuwa har ‘Dauki da hayin Alhaji da ‘Yanwarin Daji, wannan yankin shi ne k’asar Tsafe. Wato kenan ya had’e kusan duk fad’in k’aramar hukumar Tsafe ta yau.

Wasu kan so su nuna cewa, “K’asa Tsafe ta fi wannan fad’in da aka ambata. Misali ana cewa, ‘Yandoto Usman ya sara garin Guga na k’asar Bakori. Amma a hak’ik’a, ba tabbatacciyar alamar cewa akwai huld’a ta mulkin Tsafe k’etaren wannan farfajiya da aka ambata a sama. (S. A Sadi. 1998;14)

Tsafe tana da unguwanni da dama kamar haka:

  1. Unguwar Shantali

  2. Unguwar ‘Dan umma

  3. Unguwar ‘Dan Bawa

  4. Unguwar Madawaki

  5. Shiyar Sauri

  6. Shiyar ‘Dan Malam

  7. Sabon Gari


Wadanan duk cikin garin suke a wajen kewayen Tsafe kuwa akwai unguwanni da dama kamar haka:

  1. Makera

  2. Kanya

  3. Unguwar Anna

  4. Babban K’auye

  5. Tsaferu

  6. Rak’ya’bu

  7. ‘Dan fatu

  8. Unguwar mafad’i damo

  9. Bazza

  10. Bayan ‘Dna Ali

  11. Mangawa

  12. Unguwar Kare

  13. Unguwar Sarkin Filani

  14. Unguwar Hashimu


4.0.2 Ma’anar Kasuwa


Ita dai kasuwa wuri ne da al’umma kan samu su ke’be suna gudanar da kasuwancinsu wato suna siyar da sana’a don cigaban al’ummar gari da kuma mutane gabaki d’aya. Haka kuma kasuwa wuri ne da al-umma da dama kan hadu don musayar wani abu kuma kasuwa wurine da al’umma kan taru su yi cinikayyarsu. Haka kuma ana iya cewa kasuwa wuri ne da al’umma kan had’u don sayar da sana’arsu da kuma sada zumunci domin idan ka shiga kasuwa zaka sami al’umma daban-daban cikinta suna harkar kasuwanci don haka kasauwa wuri ne da ke da matukar muhimmanci ga al’umma baki d’aya domin ba lalle ba ne a sayi sana’ar mutum ba ranar kasuwa ba, don haka ranar kasuwa sai ka ga mutane sun dade wannan wurin da aka ke’be masu suna kasa sana’arsu domin su sami ciniki daga al-umma da ke zuwa suna sayar wa ba ‘yan kasuwa kawai ke zuwan ta ba harma da mutanen gari.

Don haka zamuce kasuwa wuri ne da aka kebe don harkokin kasuwanci na saye da sayarwa.

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

4.0.3 Tsokaci A kan Kasuwar Tsafe


Ita dai kasuwar garin Tsafe kasuwa ce da aka jima ana moriyarta. Al’ummar da suke a wannan k’aramar hukuma musamman wad’anda suka fito da k’auyuka da ma wad’anda ba daga kauyuka suka fito ba. Mutane daga ko’ina fad’in k’asar Zamfara da ma mak’wabta kamar Katsinawa da mutanen Kaduna da Zariya da Neja duk sukan amfana da wannan Kasuwa ta garin Tsafe.

Kasuwar garin Tsafe kamar sauran kasuwanni na k’asar Hausa tana da kayayyakin da a ake sayarwa wad’anda  da ba lallai ba ne mutum ya iya k’ayyade su.

Domin samun tudun dafawa saboda mu ba ‘yan kasuwa ba ne, mun tuntu’bi wani daga cikin masu kula da sha’anin kasuwar wato Mansur Abdullahi ya bayyana muna cewa, “ Wannan kasuwa dai kamar sauran kasuwanni na k’asar Hausa suna da tsari da suke bi wanda ya yi daidai da tsarin wasu kasuwanni na wannan k’asar, kuma wannan tsari ni ko da na tashi na tarar da wannan tsari. Ita wannan kasuwa ta garin Tsafe duk abin da ka nema na buk’atar al’umma wanda bai sa’ba ma doka ba za ka same shi a ciki, kuma kowane irin abu kake buk’ata da akwai inda za ka neme shi”.

Da muka k’ara tambayarsa ko za mu san adadin abin da ake sayarwa a kasuwar? Sai ya ce, “Babu adadi wai mutuwa ta shiga kasuwa. Sai dai mutum a fad’i kashi d’aya bisa d’ari na abin da ake sayarwa a kasuwar. Misali idan muka dubi fannin abin da ya shafi sutura kamar shadda, atanfa, leshi, hijab, kallabi, hula, takalmi, yadudduka da dai sauransu. Sai mu koma fanni kayan ado, kamar sark’a, ‘yan kunne, zobe, awarwaro da tsakiya da murjani da kandu da dai makamantansu. Sai abubuwan da suka shafi kayan aikin gona kamar kalme, kwasa, lauje, adda, wuk’a, matcamaki da dai makamantansu. Sai fannin kayan aikin girke-girke kamar tukunya murhu, mucciya, kato (luddan miya) kwanna da dai sauransu. Idan ka d’auki fannin kayan abinci shi ma za ka samu shinkafa gero, dawa, masara, maiwa, wake, dankali, rogo, doya da dai makamantansu. Idan kuma ka d’auki kayan k’walama shi ma ba a ma san da – me- da – me za a fad’a ba, ga taliya ka d’an bushini ga tsirai, ganda, tani, ligidi, da dai sauransu. Haka idan ka koma fannin tireda ga kaya nan barjak kamar jamfa a jos. Idan ka d’auki fannin kayan amfanin gida suma ba ma za ka iya lisafa su duka ba. Idan kuma ka d’auki kayan da suka k’unshi na wutar lantaki suma suna nan da yawa. Haka abin yake ga kayan wayar salula da baturai da memori da duk sauran kayan amfani na wannan fanni. Haka kayan amfani na layi da katin waya da dai sauransu”.

Malam Mansur Abdullahi ya bayyana muna cewa ba za a iya lissafa abubuwa da ake sayarwa a wannan kasuwa ba.

Kasuwar Tsafe ta kasu kasha-kashi dangane abin da ake sayarwa. Akwai wasu ‘bangarori na kasuwanci wad’anda aka ware daban ana kuma gudanar da kasuwanci ga dai misalin wad’annan kasuwunni da ake da su a garin Tsafe:

  1. Kasuwar Tsafe ta ‘Yan kaji

  2. Kasuwar Tsafe ta Kayan gona

  3. Kasuwar Tsafe ta Dabbobi da sauransu.


Wad’annan kasuwanni da suka ware daga cikin ainihin kasuwar garin an yi shi ne duk domin a samu sauk’i ga masu huld’ar kasuwanci, kuma saboda a rage cinkoson al’umma tare da samar da sauk’i ga masu huld’a ta kasuwanci.

4.0.4 Lokacin Cin Kasuwar Tsafe


Kamar yadda aka riga aka sani kowace kasuwa tana da lokacin da ake gudanar da huld’ar cinikayya, haka ma wannan kasuwar tana da wani fitaccen lokaci wato ranar kasuwar garin na Tsafe. Wannan lokaci dai shi ne ranar lahadi kuma ita ce ranar kasuwar garin, a wannan rana ne kasuwar take cika. Duk da cewa ko yaushe za ka iya samun duk abin da kake buk’ata a wannan gari a kasuwar Tsaye da ma sauran wuraren da aka ware domin kasuwanci, bai hana aka samu wani lokaci aka ware ba, domin a k’ara samar da sauk’i da kuma samun wadatar kayan buk’ata da al’umma ke muradi. A irin wannan yanayi ‘yan kasuwar ba su da wani lokacin da ake neman su a rasa, ama dai ranar lahadi shi ne ranar kasuwar.

Akwai ke’ba’b’ben lokacin da aka ware domin wannan rana, la’akari da cewa ba mutanen da ke zaune a garin kad’ai ke kawo kayan sayarwa ba, ya sa aka tanadi lokaci da zai zama mafi sauk’i ga masu gudanar da kasuwanci na kusa da na nesa. Wannan lokacin kuwa yana farawa ne daga safe karfe takwas (8:00am) na safe zuwa k’arfe shida dai dai (6:00pm) na yamma, wannan shine lokacin da kasuwar take d’auka kuma takan cika da ‘yan ksauwa da masu huld’ar saye da sayarwa.

 

 

4.0.5 Samar Da Kud’in Shiga Ga Gwamnati Daga Kasuwar Tsafe.


Kasuwar Tasfe gwamnati na al’fahari da ita don tana samar da kud’in shiga ga gwamnati mun tanbayi wani ma’aikacin k’aramar hukumar ya ce sunansa Shehu kuma yana aiki ne a Sashen kula da haraji na k’aramar hukumar ta Tsafe (revenue Deparment) wato masu kar’bar kud’in shiga na k’aramar hukumar (Tsafe) ya tabbatar muna da cewa suna samun kud’in shiga ak’alla dubu uku duk sati a wannan kasuwa. A yayin da wani Abubakar ya ce shi ne ma’ajin wannan k’ungiya a’bangaren shuwagabanin wannan kungiya muna samun ak’alla dubu hud’u a matsayin kud’in shiga duk sati amma fa wannan ya yi muna samun dubu d’aya da d’ari biyar zuwa dubu biyu ne kawai amma Al’hamdullilahi a cewar shi.

4.0.6 Kayayyakin Da Ake Samu Da Su A Kasuwar Tsaye Ta Tsafe


Ita dai wannan kasuwa ba wasu kayane da yawa ake tu’ammali da suba domin kuwa duk kayan da ake tu’ammali dasu abin da ya shafi waya ne, ita kanta wayar da sauran tarkacenta domin kuwa wuri babu abinda ake tu’ammali dashi bayan wayar (salula) to sai kuma abinci, ko shi musan dan masu zuwa wurin su saya su ci ne kawai ake kai shi amma da abin da ake tu’ammali da shi na gaske  a wannan kasuwa shi ne waya da kuma abin da ya shafi wayar kamar baturin waya (Batttery)  da kuma katin daukar bayanai (memory card) layin waya wato (sim card) da kuma tura wak’a, ko wa’azi ko ko totuna masu motsi da maras motsi (Pictures and Videos) da yima waya leda ko canza ma waya kwaba (Re-casing) ko sayar da wayar ita kanta ko kuma sayo wayar ko dai abin da ya shafi wayar tun daga wayar har caza (charger) zuwa dai sauran abin duk da ya shafi wayoyi na salula (Phones) wad’annan abubuwa da muka fad’i duk su ne ake tu’ammali da su a wannan kasuwar ta tsaye da ke garin Tsafe.

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

4.0.7 Cigaban Da ka Samu na Kasuwanci A Garin Tsafe


An samu cigaban da baya misaltuwa a kasuwar Tsafe dake garin Tsafe. Na d’aya daga ciki kasuwar ta bunk’asa fiyada yadda take a baya, kasuwar ta samu bunk’asa musamman lokacin da ta taso daga tsohon wurinta zuwa sabon wurin da take yanzu.  A wata hira da muka yi da sakataren kasuwar Mansur Abdullahi ya tabbatar mamu da cewa wannan kasuwa tana samar da kud’in shiga ga k’aramar hukumar mulki ta Tsafe. Haka kuma ya shaida muna cewa a dalilin wannan kasuwa matasa da dama sun samu aikin yi tunda ga gyaran waya da kuma sayar da waya, da sayarda baturin waya da kuma tura kad’e-kad’e da wak’e-wak’e da wa’azi harma da sayar da memori na waya da kuma yima waya leda da saka mata wasu kayan kwalliya da dai makamantansu.

Domin yin maganin zaman banza ga matasa marasa aikin yi don yanzu da wuya ka shiga garin Tsafe ka ga matashi ba ya da sana’a ko k’ak’a take yakan rik’a yana aiwatarwa.

4.0.8 Gudummuwar Da Kasuwar Tsaye Take Yi Ga Matasa


Wannan kasuwa ta tsaye da ke garin Tsafe, kasuwa ce da ta d’auki hankalin samari da dama na garin Tsafe. Irin wannan kasuwanci da ake gudanarwa a duk fad’in k’asar Hausa yana da saurin shiga cikin zuciyar samari, ba don komai ba saboda mafi yawan abubuwan da aka tu’ammali da su a sha’anin kasuwancin bak’in abubuwa ne, kuma galibi sai mai ilimi yake gudanar da su. Mai ilimin zamani shi ne ya fi kowa cin gajiyar wannan sana’a da ta fi yawa a kasuwar tsaye da ke garin Tsafe.

Mun bayyana cewa, wannan kasuwa mafi yawan abubuwan da ake a cikinta abubuwa ne da suka shafi kayan wayar salula, kama daga baturi, da kwaba da suturce waya, da saka mata leda don gudun saurin lalacewa ko gogewa da sayar da makarai na waya da katin waya don masu saye su saka su kira da sayar da layin waya da abin adana bayanai da lasifikar kunne da saka wak’ok’i da hotuna da fina-finai da tashoshin wasanni da wasu tashoshin sarrafa bayanai kamar apilikashin (Application da gyaran wayar da dai makamantansu.

Wad’annan abubuwa da muka zayyano ba kowa ne zai iya su ba sai wanda yake da ilimin zamani wanda ya had’a da yadda za a sarrafa na’ura mai k’wak’walwa da kuma ita kanta wayar. Wannan ya bayarda dama ga mafi yawan samari/matasa da ke wannan garin suka tsunduma a cikin harakar kasuwanci na hannu wasu da jari duk a wannan sashe na kayan waya da gyaranta suna samun d’an abin lalurorinsu na yau da kullum.

A wannan sana’a da matasa suke gudanarwa wasu daga cikinsu da ita ce suke gudanar da karatunsu a makarantun sakandare da kuma wasu makarantu na gaba da sakandare. Wasu kuma a nan suke ci suke sha a cikin sana’ar, wasu kuma suna amafana da sana’ar wajen samun biyan buk’atunsu na rayuwa, wasu sukan mori gyara ko kuma samun wani bayani ko wasu ajiyayyun bayanai daga masu gudanar da wannan sana’a. Abubuwan gudummuwa da wannan kasuwa ta bayar ga matasa sun had’a da:

  • Samarda kayan buk’ata na rayuwa

  • Samar da aikin yi ga matasa

  • Yawaitar kayan wayar salula

  • Samar da kaya gyaran waya

  • Samar da kayan watar lantarki

  • Samar da wasu ajiyayyun bayanai ko kayan tarihi ko na tuna baya ya hanyar wayar salula

  • Samar da kud’ad’en shiga ga hukumar garin

  • Rage zaman banza

  • Rage karancin kayan buk’ata na amfanin rayuwa

  • Ha’baka tattalin arziki na bi’ba ta Matasa

  • Samar da ilimi na na’ura mai k’wak’walwa

  • Zaburar da matasa wajen neman ilimin sarrafa na’ura mai k’wak’walwa

  • Himmatuwa wajen koyon sana’a don samun abin yi da dai sauransu


Wad’annan abubuwa da muka zayyanosu ne gudummuwar da wannan kasuwa ta tsaye ta garin Tsafe take bayarwa ga matasa na wannan gari.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

BABI NA BIYAR


5.0.1 Jawabin Kammalawa


        Babu shakka wannan bincike ya kawo k’arshe kuma a cikin wannan babi ne za mu gabatar da jawabinmu domin kammala wannan bincike. Wannan aiki, aiki ne da muka ba taken “Gudummuwar Kasuwar Tsaye Wajen Samar Wa Matasa Aikin Yi A Garin Tsafe” Kuma mun kasa wannan kundin bisa ga tsari na babi-babi in muka zuba shi bisa ga babi biyar.

Baya ga babi na d’aya da babi na biyu wad’anda suke su abin da ake gudanarwa a ciki bai shafi gundarin aiki ba.

A cikin babi na uku ne muka kawo ma’anar sana’a inda har muka ce sana’a na nufin amfani da wasu hanyoyi ko dabaru domin neman ma kai abin buk’ata na yau da kullum. Haka kuma mun kawo nau’o’in sana’a da suka k’unshi sana’o’in maza zalla da na mata zalla da kuma wad’anda aka yi tarayya wato maza na yi mata na yi. Mun kuma kawo muhimmancin sana’a ga rayuwar al’umma.

Shi kuwa babi na hud’u a nan ne muka yi bayani a kan kasuwa inda har muka ce wani ke’ba’b’ben wuri ne da aka ware don gudanar da kasuwanci, kuma a nan ne muka kawo d’an tak’aitaccen garin tsafe domin shi ne farfajiyar bincikenmu. Mun yi tsokaci a kan kasuwa da kayayyakin da ake tu’ammali da su a kasuwa. Haka kuma mun bayyana irin kayan da ake samu a kasuwar tsaye ta garin Tsafe da kuma irin gudummuwar da wannan kasuwa take bayarwa ga matasa yayin da muka ce ta samar da aikin yi ga matasa da kayan more rayuwa.

        Bincike ya gano cewa wannan kasuwa tana samar da kud’ad’en shiga ga k’aramar hukumar Tsafe, haka kuma bincike ya gano cewa, matasa suna amfana matuk’a da wannan kasuwa, domin sanadinta an samu abubuwa da adama da suke ba ma matasa kad’ai ba hatta ma da wad’anda suke tsofaffi ne da k’ananan yara suna amfana da wannan kasuwa ta tsaye.

 

 

5.0.2 Shawarwari


A matsayinmu na d’alibai masu nazarin harshen Hausa muna ba duk wanda zai yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da kundin mu kuma in har binciken nasu yana da alak’a da namu da su yi k’ok’arin d’orawa daga inda muka tsaya kar su kwashe d’ai, domin yin hakan ba ya taimaka wa nazari. Kamar yadda muka za’bo taken da wani bai ta’ba yi ba muka yi shige –shige har muka tattaro bayanan da suka gina muna wannan kundin ya zama abin karatu ga wasu to lallai suma ya zama wajibi su dage don su samar da wani abu mai amfani, ba wai su kwashe abin da wasu suka yi ba.

Baya ga shawara ga d’alibbai muna kuma ba da shawara ga duk wanda yake da sha’awar yin wata sana’a da ya tuntu’bi masu ilimi a kan sana’ar kafin ya tsunduma a ciki har ya kai ga yin hasara.

Haka kuma muna bayar da shawara ga dukkan wad’anda ba su da aikin yi da su yi k’ok’ari su samu sana’a domin zaman banza ba na al’umma ba musamman Hausawa.

 

Manazarta.


https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Post a Comment

0 Comments