Kundin Bincike Wanda Aka Gabatar A Sahen Hausa Na Tsangayar Harsuna A Kwalegin Ilmi Da Ƙere-Ƙere Ta Garin Gusau, Jihar Zamfara
NA
RUƘAYYA SANI
AMINA SANI
KHADIJAH M. SANI
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan
bincike ga iyayenmu da suka haɗa da: Malama Khadijatu Abdullahi Abdu Show da
Malama Saratu Abdullahi Mai Shuɗiya da Malama Maimunatu Umar Sani da dukkan waɗanda
suka bamu gudummuwa wajen gudanar da wannan karatu namu Allah ya saka masu da
alheri. Amin.
Jinjina
Muna masu jinjinawa babban malaminmu kuma jagoran wannan bincike wanda ya kula
da mu wato malam Habibu Lawal Ƙaura na tsangayar harsuna sashen Hausa. Saboda
nuna ƙwazonsa wajen duba wannan kundi tare da mayar da hankalinsa wajen wannan
aiki tun farkon lokacin da aka fara har Allah ya kawo mu a wannan lokaci. Allah
ya saka masa da mafificin alheri. Amin.
Godiya
Muna godiya ga tabbataccen Sarkin wanda bai haifa ba, ba a haife Shi ba. Kuma
tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittu annabi Muhammad (SAW).
Haka kuma muna miƙa kyakkyawar godiyarmu zuwa ga iyayenmu, maza da mata da
sauran ‘yan’uwana da suka taimaka a cikin wannan karatu namu Allah ya saka masu
da alhairi.
Haka kuma muna miƙa kyakkyawar godiyarmu zuwa ga Malam Habibu Lawal Ƙaura wanda
ya ɗauki tsawon lokaci yana duba aikinmu da Dr. Haruna Umar Bunguɗu(
H.O.D) na sashen Hausa a Tsangayar Harsuna Kwalejin Ilimi Da Ƙere-Ƙere Ta
Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau Jihar Zamfara, kuma ina miƙa godiyata ga
dukkan malaman wannan sashe, kamar su Malam Salisu Sadi Tsafe da malam Sani
Aliyu Soba da Malam A.D ‘Dan’amarya da Malam Habibu Lawal Ƙaura da Malam M.A
saleh da Mal. Muhammad Abubakar da Mal. Bashir Tsafe da Mal. ‘Dahiru Sankalawa
da mal. Haruna Maikwari, na gode ga baki ɗaya Allah ya bar zumunci ya sa ma
karatun da muka yi albarka ya sa abin da za a taimaki wannan jiha da ƙasa baki ɗaya
ne.
Ƙumshiya
1. Shedantarwa
-
-
-
-
- -
ii
2. Sadaukarwa
-
-
-
-
- -
iii
- Jinjina
-
-
-
-
- -
- iv
1. Godiya
-
-
-
-
- -
- v
2. Ƙumshiya
-
-
-
-
- -
vi
- Babi Na ‘Daya
1.0. Gabatarwa
-
-
-
- -
-
- 1
1.0.1 Yanayin Bincike
-
-
-
-
-
- 2
1.0.2 Manufar Bincike
-
-
-
-
-
- 3
1.0.3 Muhallin Bincike -
-
-
-
-
- 3
1.0.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike
-
-
-
- 4
1.0.5 Matsalolin Da Suka
Taso
-
-
-
- 5
1.0.6 Matsalolin Da Aka
Fuskanta
-
-
- 6
2.0 Babi Na Biyu
2.0.1 Waiwaye (Ayyukan Da suka Gabata)
-
-
- 9
2.0.2 Salo, Zubi Da Tsarin Bincike
-
-
-
- 15
3.0 Babi Na Uku
3.0.1 Ma’anar Kalma
-
-
-
- -
- 17
3.0.2 Azuzuwan Kalmomi
-
-
-
- -
18
3.0.3 Ƙa’idojin Rubuta
Kalmomi
-
-
- 25
3.0.4 Saiwa/Tushen Kalma
-
-
-
- -
28
Babi Na Huɗu
4.0.1 Haɗa kalmomi A Rubutu -
-
-
-
- 31
4.0.2 Kalmomin Ishara/Manuni -
-
-
-
- 37
4.0.3 Kalmomin Tambaya
-
-
-
- -
39
4.0.4 Kalmomin Jam’u
-
-
-
-
-
- 41
4.0.5 Raba kalmomi A Hausa
- -
-
-
- 44
4.0.6 Kalmomin Sharaɗi -
-
-
-
- -
47
4.0.7 Kalmomi Masu Zaman Kansu
-
-
-
- 50
4.0.8 Gaɓoɓin Kalmomin Hausa
-
- -
- 51
4.0.8.1 Rabe-Raben Kalmomin Hausa -
-
-
- 51
4.0.8.2 Tsarin Gaɓa
-
-
-
- -
- 52
4.0.8.3 Yawan Gaɓoɓin Hausa
-
-
-
- -
55
Babi Na Biyar
5.01 Jawabin Kammalawa
-
-
-
- -
56
5.0.2 Shawarwari -
-
-
-
- -
- 57
Manazarta -
-
-
-
- -
-
- 59
Babi Na ‘Daya.
1.0 Gabatarwa
Wannan aiki mai taken “Nazarin Kalmomi Masu Ma’ana Da Matsayinsu A Rubutun
Hausa” mun gudanar da shi ne wannan mataki na wannan makaranta, da manufar cika
wani ɓangare na karatunmu domin samun takardar shaidar Malanta ta ƙasa wato
(N.C.E).
Wannan bincike ya ƙunshi sassa guda biyar, babi na ɗaya ya ƙunshi, Gabatarwa,
Yanayin Bincike, Muhallan Bincike, Hanyoyin Gudanar da Bincike, Matsalolin Da
Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.
Babi na biyu kuwa ya ƙunshi Waiwaye ga Ayyukan Da Suka Gabata, sannan da irin
Salo Da Zubi Da Tsarin Marubutan suka yi amfani da shi.
Shi kuwa babi na uku ya ƙunshi Ma’anar kalma da Azuzuwan Kalmomi da Ƙa’idojin
Rubutu da Sassan Kalma.
Babi na huɗu nan ne muka yi bayani a kan Haɗa Kalmomi A Cikin Rubutu, da
Kalmomin Ishara/Manuni, da Kalmomin Tambaya da Kalmomin Jam’u da Raba Kalmomi
da kalmomin Sharaɗi da Kalmomi masu Zaman Kansu da Gaɓoɓin Kalmomin Hausa da
Tsarin Gaɓoɓin Kalmomin Hausa da Yawan Gaboɓin Hausa Kamar Masu Gaɓa ‘Daya, da
Masu gaɓa biyu da gaɓa uku da gaɓa huɗu da gaɓa biyar da gaɓa shida.
Babi na biyar nan ne muka ƙulle zare wannan bincike, wato nan ne muka kammala
wannan aiki. A babin dai mun kawo: Jawabin Kammalawa da Shawarwari ga mai
nazarin aikinmu.
Yanayin Bincike
Wannan aikin yana da zimmar yi wa kalmomin Hausa nazarin ta natsu. Ma’ana dai
za a kalli kalmomi da matsayinsu tare da nuna yadda ya dace a rubuta su, kana a
yi bayani mai gamsarwa ga masu karatun wannan fage na nazarin harshen Hausa.
Haka kuma aikin yana da manufar zaƙulo wasu bayanai sahihai dangane da yadda
kalmomi suka kasu tun daga gaɓa ta ɗaya har zuwa gaɓa ta shida.
A sabili da haka ne muke ganin ya kamata a matsayi mu na masu nazarin harshen
Hausa muka ga ya dace mu tuntuɓi masu ilimi a wannan fanni domin samun makamar
wannan aiki.
1.0.2 Manufar Bincike
Wannan aiki namu yana da manufar samar da sahihan bayanai da suka danganci
samar da inganci ga haryar rubutun Hausa, da nuna yadda ya dace a yi shi, tare
da bayyana azuzuwan kalmomin na Hausa.
Har wa yau aikin zai bamu damar karɓar takardarmu ta shaidar malanta ta ƙasa
wato (N.C.E) Sannan ya kuma shedi zamanmu a wannan makaranta.
Muhallin Bincike
Babu shakka mun yanke shawarar yin wannan bincike ta ɓangaren Nahawun Hausa a
Nahawun ma mun ke ɓance a wani muhimmin rukuni na
Nahawu guda wato ilimi Ma’ana wato (Semantic). Haka kuma a cikin aikin akwai
wani ɓangare da zai ƙunshi Ginin Kalma/Tasrifi wato (Morphology). Saboda haka
binciken namu zai ta’allaƙa ne a waɗannan ɓangarori na Nahawu. Wannan bincike
zai taimaka wa manazarta da masu sha’awar karatun wani rubutu domin samun wani
darasi a kan rubutun Hausa.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
1.0.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Kamar dai yadda aka sani cewa kowane bincike da za a gabatar to ya zama wajibi
a san hanyoyin da za a bi wajen yin sa. Wannan ya sa muka fito da wasu
hanyoyi guda uku saboda manufar wannan binciken ta kammala.
Hanya ta farko da muka bi domin cimma nasara wajen gudanar da wannan bincike
ita ce, ta tattara bayanai daga littatafan da aka wallafa masu dangantaka da
wannan aiki, da mujallu da kundaye da muƙalu da dai makamantansu waɗanda suka
shafi Nahawu. Wannan zai bamu dama mu bi waɗansu hanyoyi da suka haɗa da:
Karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da muƙalu da Mujallu domin zaƙulo
wasu bayanai masu nasaba da aikin. Za a kai ziyara a ɗakunan karatu da suka haɗa
da nan cikin makarantarmu wato Kwalejin Ilimi da Ƙere-Ƙere Ta Gwamnatin Tarayya
da ke Garin Gusau, (FCET) , da Kwalejin Fasaha da Kimiyya (ZACAS) Gusau, da
Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara da ke Maru (C.O.E.) Maru, da sauransu domin
tattara bayanai masu nasaba da wannan aiki.
Hanya ta gaba kuwa ita ce hanyar zantawa da wasu mutane da suke da masanniya a
kan abin da yake gudana a ɓangaren Nazarin Harshen Hausa.
Matsalolin Da Suka Taso.
A nazarce – nazarce da faɗi-tashi da malamai da ɗalibai suka yi domin faɗaɗa
wannan fanni na harshe, sai ya yi ƙamari sosai. Amma har yanzu wannan fanni buƙace
yake da a kaimasa ɗauki. Domin akwai abubuwa ko mu ce sassa da dama a ɓangaren
harshe da ke fuskantar rashin kulawa musamman wannan batu da muke magana wato
Nazarin kalmomi masu ma’ana da matsayinsu a rubutun Hausa.
Bisa ga wannan muka ga cewa ya dace mu ɗauki wannan batu domin mu shiga cikin
irin waɗancan ɗalibai da suka yi rubuce-rubuce a wannan fanni, don mu bayar da
tamu gudummuwa bisa ga wannan matsala da ta taso wa wannan fanni na rashin samu
yawaitar manazarta.
Haka kuma akwai matsalar rashinsamun isassun littattafai da kuma isassun
kundayen bincike. Wannan matsala ce wadda ta kawo muna farmaki a lokacin da
muke cikin karatu sai muka yanke shawarar cewa, duk lokacin Allah ya kai mu
lokacin da za mu rubuta kundin bincike za mu tallafa wa wannan fanni da tamu
gudummuwa domin a kawar da wannan matsala.
Matsalolin Da Aka Fuskanta
Bisa ga al’adar bincike irin wannan , duk lokacin da aka ce za a yi wani
bincike to lallai ba za a rasa wasu ‘yan matsaloli da suke yin barazana ba.
Wannan ya tabbatar muna da cewa, lallai ya dace mu yi la’akari da matsaloli da
za mu fuskanta. Tabbas a cikin wannan aiki na gudanar da wannan kundin mun haɗu
da matsaloli daban-daban da suka haɗa da:
- Matsalar rashin samun
isassun littatafan da za mu nazarta don gudanar da wannan bincike.
- Matsalar ganawa da wasu daga
cikin waɗanda muke buƙatar zantawa da su.
- Matsalar “masu gida rana”
wato kuɗi kenan waɗanda suke su ne abokan tafiya a cikin wannan aiki namu.
- Matsalar wutar lantarki na
daga cikin matsalolin da muke fuskanta saboda sanin jama’a ne cewa a ƙasar
ma baki ɗaya babu wadatacciyar wutar lantarki yanzu-yanzu duk an ɗauke
wutar wannan ya kawo ma wannan aiki tafiyar hawainiya.
- Wata matsala da muke
fuskanta ita ce, a lokacin da muke gudanar da wannan binciken muna da buƙatar
tattaunawa da wasu malamai da ɗalibai dangane da wannan aiki da muke da ƙudurin
yi.
- Matsalolin ƙarancin lokaci
saboda abin ya zame muna biyu ga bincike ga karatun jarabawa da yake ana
gudanar da wannan bincike tare da karatun zango na farko da na biyu a ƙarshen
kammalawa.
To, Alhamdulillahi duk da irin wannan barazana da muke fukanta ta waɗannan
matsaloli Allah Maɗaukakin Sarki Gagara Misali bai sa muka yi ƙasa a guiwa ba
sai da muka ga gurinmu ya cika na aiwatar da wannan kundin.
Babi Na Biyu
2.0.1 Waiwaye A Kan Abubuwan Da Suka
Gabata.
Wajibi ne ga duk wanda ke son aiwatar da bincike irin wannan ya waiwayi baya
don ganin irin ayyukan da suka gabata, wannan zai ba shi damar sani inda aka
kwana da inda za a tashi.
Shi wannan waiwaye ya zama tilas domin ta wannan ne mai nazari zai san inda ya
dosa, wato yana da masanniya game da wasu ayyuka da suka shafi binciken da zai
aiwatar, don haka, sai ya ɗora a kan su ko ya rushe su ya gina nasa tsarin ko
ya ɗauki waɗansu abubuwa ya watsar da wasu, gwargwadon yadda ya fahimta ko ya ɗora
daga inda aka tsaya.
A wannan binciken mun yi ƙoƙaƙarin bincika ayyukan da suka gabata na masana da
manazarta daba-daban da suka haɗa da bugaggun littattafai da kundaye waɗanda
suke da alaƙa da namu aikin. Ga dai wasu daga cikin ayyukan da suka gabata na
wasu masana da manazarta da muka ci karo da su yayin gudanar da wannan bincike.
Garba C.Y (1984) a littafinsa mai suna “Nazarin Hausa a Ƙananin Makarantun
Sakandare Littafi na Farko”. Marubucin ya tsara wannan littafin nasa a kan
kanun batutuwa, ta hanyar amfan i da sautukan A,B,C,D,. Da farko ya fara bayani
ne a kan harshe da sadarwa da adabi da furuci da adabin gargajiya da furuci na
biyu da al’adu da furuci na uku da Hausa a fakaice da jimlar Hausa. Aikin na
Garba yana da nasaba da wannan aikin da muke gudanarwa domin kan batun “A” yayi
tsokacinsa ne a kan harshe. Haka kuma ya bambanta da namu aiki domin bai ce
komai ba a kan azuzuwan kalmomi da matsayinsu a cikin rubutu.
Bagari (1986), “Bayanin Hausa Jagora Ga Mai Koyon Ilimin Bayanin Harshe.”
Marubucin ya yi bayani mai gamsarwa a kan abin da ya shafi harshe, inda ya kawo
ɓangarori daban-daban, yayin da a wani ɓangare na littafinsa ya taɓobayani a
kan azuzuwan kalmomi, wanda cikin wannan ɓanagare, akwai ƙarin haske ga abin da
muke buƙata. Sai dai na namu aikin ya karkatu ne a kan ma’anar kalmomi da kuma
matsayinsu a rubutu.
Zurruk R.M da Wasu (1986) a littafinsu mai suna “Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa,
Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na I,II,III”. A wannan littafi
marubutan sun tsara aikin nasu a kan kashi-kashi kuma a ƙarƙashin kowane kashi
ana samun babi-babi, a cikin littafi na ɗaya kashi na huɗu babi na takwas, sun
yi tsokaci a kan harshe da sifofin harshe da amfanin harshen.
Wannan aiki da su Zarruk suka yi ya taimaka ainun wajen gina namu aiki. Da
wannan ne muke ganin cewa, aikin nasu yana da alaƙa da namu aiki saboda sun yi
magana a kan harshe yayin da muma namu aikin abin da yake magana kenan. Haka
kuma aikinmu yana da bambanci da nasu saboda su ba su yi maganar komai ba game
da Azuzuwan kalmomi da kashe-kashensu.
Yahaya I.Y. (1988), ya rubuta littafi mai suna “Hausa A Rubuce” a cikin wannan
littafi masanin ya yi bayanin rubutu, tarihin samuwar rubutu yadda aka samu
rubutun zube, wasu daga cikin littafan da aka samu na zube, gasar da aka shirya
don samun littattafan zube tarihin wasu hukumomi na gudanar da ayyukan rubutu
musamman na boko da na Arabiyya.
Wannan aikin na shaihin malami Yahaya I. Y. Yana da alaƙa da aikinmu saboda ya
yi tsokaci a kan wasu manyan harshen Hausa kuma ya kawo wasu ayyuka da aka
gudanar musamman a wasu manyan cibiyoyi na wallafa ayyukan Hausa, kuma su waɗannan
cibiyoyi suna da matuƙar muhimmanci idan za a kula da tsarin rubutun Hausa da
tarihin Rubutu da dai sauransu. Aikin yana kuma da bambanci da namu saboda shi
yana magana ne a kan adabi da harshe da al’adun Hausawa da zubensu da tarihinsu
yayin da mu namu aikin ya ta’allaƙa ga harshe kawai kuma ko harshen mun
mayar da hankali ga Nahawu da kuma ginin kalma.
Bunza (2002) “Rubutun Hausa Tadda Yake Da Yadda Ake Yinsa” a wannan littafin
marubucin ya yi ƙoƙari inda ya zaƙulo abubuwa da dama a cikin littafin kamar
abin da ya shafi asalin rubutu musamman rubutun boko, haka kuma ya kawo bayanai
a kan yadda ake samar da kalmomi da wani ɗan haske a kan yadda ake rubutun
Hausa da Ƙa’idojin Rubutu da haɗewa da rabewa a cikin rubutu.
Wannan aiki na Bunza yana da alaƙa da namu aikin saboda shi Bunza yana bayani
ne a kan rubutun Hausa, da yadda yake da yadda ake yinsa. Mu kuma muna bayani
ne a kan kalmomin Hausa masu ma’ana da matsayi a cikin rubutu. Inda gizo ke saƙa
kuwa shi ne ayyukan suna da bambanci ta fuskar yadda aka tsara su. Shi Bunza ya
a nasa aiki ya mayar da hankali ne ga rubutun Hausa da ƙa’idojinsa. Mu kuma mun
fi mayar da hankali ne ga kalmomin Hausa da kuma matsayinsu a cikin rubutu.
Muhammad Y.M (2009) “Rubutun Hausa Da Ƙa’idojinsa” wannan marubuci ya fito da
bayanai a cikin littafinsa waɗanda suka haɗa da rabe-raben kalmomi da da amsu
karan ɗori na Hausa.
Wannan aikin nasa yana da alaƙa da namu, domin duk a fannin harshe mu ke
bayani, sai dai ya sha bamban da namu aikin, saboda ma’anar kalmomi muke yi
tare da nuna matsayinsu a cikin rubutu.
Mukhtar A.B. (2010) “Nazarin Harshen Hausa: Sigar Hatsin Bara” a cikin littafin
ya kawo bayanai da suka haɗa da gaɓar kalma da sauransu duk da cewa wannan
marubuci yana bayani a kan harshe sai dai kuma mun samu ƙarin haske a kan
ma’anar kalmomi.
Wannan aikin yana da alaƙa da namu aikin, saboda ya yi magana a kan gaɓar
kalmomi, yayin da mu ma za mu yi bayani a kansu. Inda muka sha bamban kuwa shi
ne wannan aiki na Mukhtar ya mayar da hankali ne a kan gaɓobi kalma. Yayin da
mu kuma muke kallon kalmomi da ma’anar su da matsayinsu.
Yakasai S.A. (2012) “Ilimin Walwalar Harshe” wannan masani ya yi ƙoƙari ƙwarai
a cikin wannan aiki. Saboda ya kawo bayanai da suka haɗa da kalmomin Ishara da
kalmomin malamai da kalmomin mata da sauransu. Masanin ya yi bayanin yadda
harshe yake da yadda ake amfani da shi a al’ummar Hausa. ya kawo yadda ake
walwalar harshe da kuma irin mutanen da ke amfani da shi a cikin al’ummar
Hausawa.
Wannan littafi na Yakasai yana da alaƙa da aikinmu saboda ya yi tsokaci a kan
wasu kalmomi yayin da namu aikin yana bayani ne a kan kalmomin Hausa. inda kuma
muka sha bambanci da shi, shi ne Yasakai yana kallon gabaɗayan harshen Hausa ne
da kuma walwalar shi tare da wasu kalmomi da wasu rukuni ko jinsi ke amfani da
su. Yayin da mu kuma muna kallon kalmomin Hausa ne tare da yadda ma’anarsu da
matsayinsu a cikin rubutun Hausa.
2.0.2 Salo/ Zubi Da Tsarin Aiki
Salo shi ne hanyar da marubuci ke bi domin samun nasarar isar da saƙonsa ga
masu karatu ko sauraro.
Idan aka ce salo to, ana nufin duk wata dubara da marubuci ko mai magana ya bi
wajen isar da saƙonsa a cikin sauƙi.
Gusau (1993: 5), cewa ya yi. “salo shi ne hanyar da ake bi a nuna gwaninta da
dubara a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu
ta bin yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace game da abin da yake
son bayyanawa.
A duk lokacin da aka yi maganar salo ana magana ne a kan irin ƙwarewar
manazarci, wajen aikin bincike da kuma yadda yake jawo hankalin mai karatu a
kan aikin da marubucin ya yi a kowane lokaci.
A wannan kundin dai za mu yi amfani da salo mai burgewa wajen aiwatar da wannan
kundin ta yadda duk wani ya ɗaga shi sai ya amfana matuƙa. Wannan ba ya rasa
nasaba da irin yawo da za mu riƙa yi saboda tattara bayanai da suka shafi
wannan kundin. Don haka muka yarda cewa dukkanmu za mu ziyarci ɗakunan karatun ɗalibai
don ganin yadda abin ke gudana.
Babi Na Uku
3.0.1 Ma’anar Kalma
Mukhtar A.B. (2010) ya bayyana ma’anar kalma da cewa, “Kalma ita ce inda ake
samun haɗuwar gaɓoɓi wuri guda domin su ba da kalma mai ma’ana. A Hausa kalma
tana iya kasancewa gaɓa ɗaya tak, ko biyu ko fiye da haka kamar yadda za a ga
wasu misalai kamar haka:
Kalma Gaɓoɓi
Rai
Gaɓa ɗaya Misali- Rai
Dawa
Gaɓa Biyu Misali- Da+Wa
Masara
Gaɓa Uku Misali- Ma+sa+ra
Makaranta
Gaɓa Huɗu Misali- Ma+ka+ran+ta
Yarjejeniya
Gaɓa Biyar Misali- Yar+je+je+ni+ya
Nuƙurƙusasshiya Gaɓa
shida- Misali- Nu+ƙur+ƙu+sas+shi+ya
Yakasai S.A. (2012) ya bayyana kalma da cewa, “Kalma sautuka ne ake haɗawa wuri
guda a cikin ƙayyadajjen tsari a gina zantuka masu ma’ana.
Idan aka yi la’akari da bayanan da masanan nan suka bayar game da ma’anar kalma
za a ga cewa, “Kalma dai ita ce haɗuwar gaɓoɓin furucin magana bisa ga wani
tsari wanda zai bayar da sunan wani abu ko aiki ko umurni da ko sifa ko bayanau
ko wani abu makamancin su.
3.0.2 Azuzuwan Kalmomi
A Hausa akwai azuzuwan kalmomi waɗanda kowace kalma da inda ta faɗa. ga dai
wasu azuzuwan kalmomi da muke da su a harshen Hausa:
1. Suna
2. Wakiln Suna
3. Sifa
4. Aikatau
5. Bayanau
6. Nunau
7. Mafayyaciya
8. Ma’auni
Domin ɗaure akuyarmu a kan magarya, ma’ana kafa hujja yanzu za mu ɗan yi
bayanin kowane daga cikinsu a taƙaice.
1. Ajin Suna: Kamar yadda
sunan ya nuna kalma ce da ke nuna sunan abu, mai rai ko maras rai, wanda ake
iya taɓawa ko wanda ba a iya taɓawa, wanda ake gani ko wanda ba a iya gani.
Misali matum, zakara, ruwa, iska, haske, duhu, murmushi yunwa da dai sauransu.
Suna dai ya kasu kashi-kashi kamar yadda za a gani. Misali:
1. Sunan Yanka
2. Suna Gama-gari
3. Suna Tattarau
4. Gagara-Ƙirga
Yanzu bari mu ɗan yi tsokaci kaɗan dangane da su:
1. Sunan Yanka: Sunan yanka dai
suna ne wanda ake kiran mutum kodabba ko ƙasa ko gari ko wani abu da shi wanda
kowa ya san shi da shi. Misali Mutum: Muhammadu, Abubakar, Umar, Haruna da
sauransu. Sunan Gari: Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Zariya, Kano. Da sauransu.
Sunan Ƙasa: Nijeriya, Kamaru, Saudiyya Nijar, da sauransu.
2. Suna gama-gari: Wannan nau’in
suna, suna ne wanda baya rarrabe abu ɗaya. Kuma shi wannan suna idan aka ambace
shi to duk wani abu da yake jinsi ko dangi ko mai asali ɗaya da shi ake.
Misali: Mutum, Mota, Sutura, Tuwo, da dai sauransu.
3. Suna Tattarau: Wannan nau’in
suna, suna ne da ake amfani da shi yayin da ake son a kira wasu da suke da yawa
da shi. Misali: Gungu, Ƙungiya, Ayari, Runduna da sauransu.
4. Suna Gagara-Ƙirga: Kamar
dai yadda sunan ya nuna wannan ya shafi abubuwa waɗanda ba a iya ƙirgawa.
Misali: Gishiri, Mai, Ruwa, Gero Dawa, Suga, da dai sauransu.
5. Wakilin Suna:Wakilin suna dai
kalma ce mai wakiltar suna a cikin jimla, ma’ana aka iya yin amfani da shi a
maimakon jimla. Misali: Ni, Kai, Ke, Shi, Ku, Mu, Su, Ita, da sauransu.
Ana iya mafani na kalmar Ni, shi, kai a maimakon Haruna, Musa,
Habibu da sauransu. Kuma ana iya amfani da ke, a maimako
A’isha, ko Binta ko Hadiza da sauransu. Haka kuma ana iya amfani da waɗannan
duka a maimakon kalmomin nan ma su nuna sunayen jam’i. Misali: mu, su,
ku,.
Wakilin suna ya kasu kashi-kashi kamar haka: wato ɓoyayye, Katsattse,
Gama-Duniya, Tamabayau. Ga dai su kamar yadda za a gani:
ɓoyayye: Wannan nau’i na wakilin suna shi kamar haka: Wane, wance
su wane, da su wance.
Katsattse: shi kuma wannan shi ne kamar: Ni, mu, su, ku, kai, shi,
ke, ita da dai sauransu.
Gama-Duniya: Wannan nau’o’in wakilin suna sun haɗa da: Kowane,
kowace, ko waɗannan.
Tambayau: Wannan nau’in wakilin suna kamar yadda sunan ya nuna,
wannan nau’i ne da ya danganci tambaya. Misali: Wa?, Me, wacce?, wanne? da
sauransu.
1. Ajin Aikatau: Aikatau kalma
ce dake ɗauke da aiki a cikin jilma. Ma’ana duk wani abin da aikata a cikin
jimla, dunƙule yake a cikin aikatau. Misali.
- Audu ya Share ɗaki.
- Bala ya ƙare rubutu
- Binta ta dafa abinci
- Hauwa ta ɗumama ruwa
A waɗannan jimloli guda huɗu kalmomin Share, da Ƙare da Dafa, da Ƙumama dukan
su aikatau ne domin su suke ɗauke da abin da aka aikata.
Dangane da shiga jimla aikatau iri biyu ne. ga shi kamar haka:
1. So-Karɓau
2. Ƙi-Karɓau
Ga dai bayanan su kamar haka:
So-Karɓau: Wannan shi ne wanda aiki ya faɗawa. Abin nufi
anan shi ne a cikin jimla akan faɗi aiki kuma aikin ya faɗa wa wani abu, wannan
shi ne so karɓau. Misali:
- Audu Ya Tara kuɗi
- Binta ta girka abinci
- Musa ya wanke mota
- A’isha ta yi bacci
A waɗannan jimloli za a fahimci cewa kalmomi kamar: Kuɗi, Girka, Wanke, bacci
dukkan su aki ne kuma sun faɗa wani abu.
Ƙi-Karɓau: Wannan aikatau akasin wancan ne saboda aikin da
aka yi yana komawa ne ga wanda ya yi aikin. Misali:
- Tulu ya cika
- Yaro ya ɓace
- Riga ta wanku
- Kaza ta dahu
Idana aka lura kalmomi irin su cika da ɓace da wanku da dahu dukkan su sun faɗa
ne a kan waɗannan abubuwa da aka amfata cewa sun aikata wannan aiki.
1. Mafayyaci: Wannan kamar
yadda sunan ya nuna kalma ce mai fayyace abu. Misali Wani yaro, wata, yarinya,
waɗansu mutane. Da sauransu. Wannan ya nuna kalmar wani da wata da waɗansu suna
fayyacewa ne. a misali na farko yaro ne jinsin namiji, a misali na biyu kuwa
wata yarinya ake son a fayyace jinsin mace a misali na ƙarshe kuma waɗansu,
mutane ne wannan yana ƙoƙarin fayyace wa ne cewa jam’i mutane ake son a
fayyace.
2. Ajin Sifa: Sifa kalma ce da take
ƙarin bayani ga suna. Misali: Baƙi, fari, Dogo, gajere da sauransu. Sifa ta
kasu kashi-kashi kamar haka:
3. Sassauƙa
4. Aiwatau
5. Nanatau
Sassauƙa:Wannan ta ƙunshi kalmomi irin su baƙi, Fari, dogo,
gajere da dai sauransu.
Aiwatau: wannan nau’in sifa ya ƙunshi kalmomi kamar: Maguji,
Magujiya, Maguda, Maƙaryaci Maƙaryaciya, Maƙaryata, Malalaci, malalaciya,
Malalata da sauransu
Nanatau: Sifa nanatau dai ita ce nau’in sifar da ake ambaton kalmar
da ake nanatawa a yayin faɗinta. Ga dai misalin wannan nau’in sifa: Baƙi-baƙi,
Fari-fari, dogo-dogo, gajere-gajere. Da sauransu
1. Ajin Ma’auni: shi kuma wannan kamar
yadda sunan ya nuna, “Ma’auni” kalma ce da danganci yawa ko adadin abu. Misali:
2. Doki ɗaya
3. Mutane bakwai
4. ‘Dalibai tuli
5. Littafai kaɗan
Kamar yadda aka gani a sama kalmar ɗaya, da bakwai da tuli, da kaɗan. Dukkan su
suna nuna adadi ko ma’aunin kimanin yawan yawan abubuwan da aka lissafa. Wannan
shi ake nufi da mau’ni.
3.0.3 Ƙa’idojin Rubuta
Kalmomi
Ƙa’idojin rubutu na nufin daidaitattun hanyoyi na rubutu, waɗanda kan fara ƙarfafa
sadarwa ta fuskar ƙara fito da ma’anar saƙo. Su ƙa’idojin rubutu abubuwa ne
kamar harshe; wato sukan samu karɓuwa su game jama’a ta hanyoyi sanannu.
Manyan matsalolin ɗalibai ta fuskar ƙa’idojin rubutu sun haɗa da, rashin amfani
da daidaitacciyar Hausa da rashin rubutu mai kyau da rashin sanin wuraren
amfani da manyan baƙaƙe da da rashin fahimtar rabawa da haɗawar kalmomi da
rashin gane amfanin alamomin rubutu.
Ga dai bayanan wasu abubuwa daga cikin ƙa’idojin rubutu musamman waɗanda suke
shige wa ɗalibai cikin duhu.
Amfani Da Manyan Baƙaƙe
Yana daga cikin kura-kurai da sakaci da ɗalibai ke yi a cikin rubutunsu,
musamman abin da ya shafi bincike sai a ga sun yi amfani da ƙaramin baƙi a muhallin
babba ko kuma akasin haka. Ga dai muhimman wuraren da ya dace ɗalibai su kiyaye
domin amfani da manyan baƙaƙe:
Sunayen Yanka Ko Laƙabi
1. Sunayen Allah da
lamiransa
2. Mala’ikku - Azara’ilu
iii. Mutane
- Garba Buba Makau Ta Sallah.
Sunayen Harsuna
Hausa Ingilishi/Turanci, Larabci, Yarbanci da sauransu
Sunayen Garuruwa
Gusau Sakkwato
Tsafe
Ƙaura
Zariya
Sunayen Fannonin Ilimi/Darussa
Ilimin Ƙasa, Lissafi, Tarihi da Sauransu.
Sunayen Gulabe/Kogona, Duwatsu/tsaunuka:
Kwara, Benuwe, Chadi, Dala, Kufena da sauarnsu
Sunayen Ƙasashe. Nijeriya, Masar Chana, Pakistan, Platsine.
Sunayen Iskoki: Ifiritu, “Yar Fulani, da sauransu
1. farkon kwace jimla
2. bayan kowace aya ko
alamar yambaya ko ta motsinrai
3. farkon kowane sakin
layi
4. Wata matashiya ko kan
labari
5. Harafi na farkon
bayan alamar zancen wani.
6. Farkon jawabin
motsinrai
Rabawa Da Haɗa kalmomi
Wani abu da yake da gagarumin muhimmanci da kuma taka rawa wajen kyautatawa ko
lalata ma’ana da manufar rubutun Hausa, shi ne rabawa da haɗa kalmomin Hausa.
Dalili kuwa, rabawa da haɗa kalmomi yana hardasa abubuwa masu yawa da suka haɗa
da lalata ma’ana da inganta ma’ana da canzawa ko faɗaɗa ma’ana. Duba waɗannan
misalai na jimlolin da ke biye irin na su Zarruk:
- Akuya ta fi kiyo
- Akuya tafi kiyo
- Aku ya ta fi kiyo
Haka kuma ga wasu misalai da za a gani.
- Sa mata kai biyu
- Sama ta kai biyu
- Sa matakai biyu
Wani misalain shi ne:
- Abarshiyajekaratu
- Abarshi ya je karatu
- A bar shi ya je karatu
3.0.4 Saiwar/Tushen Kalma
Saiwa ko tushen ƙare-ƙaren kalma muhimmin abu ne. a lura dai cewa waɗannan ƙare-ƙaren
ma’ana ne ake gina kalmomi daga saiwoyi. Ma’anonin kalmomi kuwa ko da saiwar su
ɗaya ce suna bambanta sosai. Bayan haka yana yiwuwa saiwa ta zama kalma
cikakkiya. Amma idan an ƙara mata ƙare-ƙaren ma’ana sai a sami wasu kalmomi
daban. Misali idan an ƙara wa kalmar karanta “ma” a baya, zai zama Makaranta
wato kalmar ta tashi daga aikatau ta koma suna.
Saiwar Kalma/Tushen Kalma: Wannan dai ita ce ainihin farko ko tushen da kalma
ta samo asali. Saiwa dai kamar yadda sunan ya nuna, ta samo asali ne daga
ainihin abin da ake kira saiwa/saye/tushe/farko na wani abu, kamar
icce/bushiya. Amma a wannan fage ba bushiya ake nufi ba, Kalma ake nufi. Ga dai
misalin wasu kalmomi da saiwoyin su:
Kalma Saiwa/Tushen
Kalma
Sama
Sam
Ƙasa
Ƙas
Yaro
Yar
Gona
Gon
Karatu
Kar
Masara
Mas
Gada
Gad
Jarunta
Jar
Kwalabe
Kwal
Gulbi
Gul
Katifa
Kat
Da dai sauransu.
Irin waɗannan suna nan da yawa a kuma kowace saiwa aka ɗauka ana iya yi mata ƙarin
ka kwayar ma’ana da samar da ainihin kalamar da za a gina daga cikinta.
Babi Na Huɗu
Haɗe Kalmomi a Rubutu
Masana da manazarta harshen Hausa sun zauna sun tsara yadda ya dace rubutun
Hausa ya kasance saboda samar da sauƙi da fitar da ma’anar abin da yake a
rubuce a cikin takar da ga mai karatu. Wannan ya ba da dama ga masanan suka
shata wasu dokoki da suke gani su, suka fi cancanta mai karatu ya bi domin
samun sauƙi wajen farautar ma’ana.
Kasancewar haɗe rubutu da raba shi suna taka muhimmiyar rawa ya sa masanan suka
ga ya dace su rarrabe tsakanin inda ya dace a raba da inda ya dace a haɗa
rubutu. Ga dai misalan wuraren da ya dace a haɗe rubutu. Misali
Mallaka: A harshen Hausa idan aka ce mallaka ana nufin abin da aka
fi ƙarfinsa aka rinjaye shi, aka mallake shi so da ƙi. Ai don haka aka ce ma
Turawan da suka yaƙi ƙasar nan suka shugabance ta “Turawan Mulkin Mallaka”. Ta ɓangaren
masana Nahawu kuwa, mallaka ita ce wasu alamomi da ake rubutawa a masu nuna an
mallaki wani abu ga abin da aka danganta shi da shi, ko abin da ake magana a
kai. Masana Nahawu sun bayyana cewa wannan mallaka iri biyu ce. Akwai Doguwar
Mallaka da kuma Gajeruwar Mallaka.
Doguwar Mallaka: A wajen masana Nahawu doguwar mallaka takan kasance
tilo ko jam’u, namiji ko mace. Kalmomin da ke nuni ga irin wannan mallaka ba a
ware ake rubuta su ba, a haɗe ake rubuta su a jikin kalmar da aka mallaka ta.
Wata kila shi ya sa masana Nahawu suke kiran ta doguwar mallaka. Dubi wannan
fasali sosai ka rarrabe yadda ake rubuta doguwar mallaka da rabe-rabenta.
Namiji Mace
Naka
Naki
Nasa
Nata
Nashi
Tilo Jam’u
Nawa
Namu
Tawa
Tamu
Naka
Naku
Nasa
Nasu
Naki
Naku
Nashi
Nasu
Da sauransu.
Waɗannan kalmomi da aka gani a sama ana haɗe “Na” da “Wa” don ya zama “Nawa”
wato mallaki na. Ko “Na” da “Mu” wato “Namu” abin da yake mallakin mu. Haka
abin yake ga sauran kalmomi da muka zayyano a sama.
Ga dai su a cikin jimla don a ga yadda ake rubuta su.
- Ki daina hanzari ni na karɓi naki
- Saurayinta ya hana a karɓi nata
- Ki daina wasa da namu kar
ya mutu
- In an haɗo da namu a
bamu
- Ibrahim ya san nasu ba
ya da yawa
- An baka naka littafin?
Idan aka lura da wasu kalmomi da aka ja ma layi a cikin waɗannan jimlilo da
muka kawo, za a ga cewa, waɗannan kalmomi su ne muka bayar da misalai a kan su
sama, kuma su ne muka ce ake kira doguwar mallaka. Idana aka lura ko yaushe a
haɗe ake rubuta kalmomin ba a kuma haɗe su da kowace kalma. Bugu da ƙari za a
lura da cewa, ita doguwar mallaka gaɓa biyu ce. Kuma in ba mallaka ba ce ba a
haɗe kowace gaɓa da wata, amma idan doguwar mallaka ce ana haɗe waɗannan gaɓoɓi.
Gajeruwar Mallaka
Gajeruwar mallaka, mallaka ce amma duk ma’anar su ɗaya. Tsarin gajeruwar
mallaka ya saɓa wa doguwar mallaka tun siffar su har i zuwa hukuncinsu. Ga
alamomi biyu da ke iya rarrabe gajeruwar mallaka da doguwar mallaka. Misali:
Jinsi
Yawa
R – Mace
Tilo
N – Namiji
Jam’i/Tilo
Bayyanar waɗannan haruffa a gaɓar harshe ta suna yana iya bayyana a matsayin
mallaka. Wato a mallaka wani abu ga wani mutum ko dabba, ko wani abu daban.
Misali
Jinsin Mace (r)
Jinsin Namiji (n)
Motarsa
wandonsa
Matarsa
takalminsa
Rigarsa
hannunsa
Ijiyarsa
littafinsa/mu
Babarsa
babansa/su/mu
Jakarta
zaninta
Haɓarta
ɗakinta
ɗiyarta
ɗiyanta/ɗansa
Butarshi
garinmu
Idana aka lura da kyau za a fahimci cewa waɗannan misalai da aka bayar a sama
harafin (r) yana nuna cewa wannan abin da aka mallaka ga wani ko wasu ta hanyar
amfani da wakilin suna jinsin mace ne. shi kuwa harafin (n) ana dangata shi ne
ga wani suna wanda yake daga cikin jinsin namiji.
Dubi yadda haɗuwar suna mai (r) da (n) zai kasance da wakilin suna mai gaɓa ɗaya.
Ga tsarin kamar haka:
Suna mai ɗauke da wakilin
suna mai gaɓa ɗaya /r/
Rigarka
Matarsa
Hularka
Motarsa
Jigidarta
Gyaɗarsu
Matsalarku
Masarautarmu
Ƙungiyarku Maƙabartarsu
‘Dariƙarku Masheƙarmu
Siyasarku
Mashigarmu
Manufarsa
gangarka
Abokiyarsa
amaryarka
Budurwarsa darajarka
Haɓarsa
jakarka
Ijiyarsa
bindigarka.
Suna Mai Ƙauke da wakilin suna mai /n/
Halinta
kayansu
‘Dakinta
garinsu
Zanenta
gidansu
Gidanta
buƙatunsu
Gidanku
yaranmu
ɗakinku
kayanmu
Garinku
kuɗinmu
Filinku
abokanmu
Abin lura anan shi ne, kowane wakilin suna da ya zo cikin misali mai gaɓa ɗaya
ne. haka kuma kowane ɗaya daga cikin wakilan sunan an liƙa su ga suna da ya
gabace su. Ga ɗan misalin yadda suke bayyana a cikin jimlilon Hausa, kamar
haka:
Misalan /r/
- Cikin gonar ta ya mutu
- Ƙofar gidansu ya kwanta
- Masarautarmu tana yamma da
tasu
- Budurwarsa ta musulunta jiya
- Bindigarka ko ɓera ba ta
kashe ba
Masalan /n/
- Sun rinjayi yaranmu da
hujjoji
- Naira dubu goma ya sayo
jakinsa
- Akuyar Ali ta zubar masa da
kununsa
- Kai ɗai ka riƙa bayar da
kalihun kayanka
- Kar ka yarda su gane halinka
Ko yaushe za ka rubuta gajeruwar mallaka ka kula a liƙa da sunan da ke ɗauke da
wannan mallaka suna bayyana a kowane bagire. Abin da ya kamata a kula anan shi
ne, wasu kalmimon doguwar mallaka sun fi kusa ga wasu karuruwan harshe. Abin
nufi anan doguwar mallaka: nasa, nashi, tasu, sun fi kusa da Sakkwatanci
Kalmomin Ishara/Manuni
A ƙa’idar rubutun Hausa, kalmomin ishara ko manuni a haɗe ake rubuta su. Abin
da ake nufi da ishara ko manuni, kalmomi ne masu nuna abin da mai magana ke
magana a kai. Anan ba sai ya nuna abin da hannunsa ba, matuƙar an ga bayyanar
kalmomin ana iya fahimtarsa a gane abin da yake nufi. Ga tsarin kalmomin kamar
haka:
- Wancan,
- Waccan
- Waɗannan,
- Waɗancan
- Waɗanga
- wannan
a ko’ina, waɗannan suna bayyana dokar rubutun Hausa ta ce, a haɗe ake rubuta
su. Huɗu daga cikinsu an fi amfani da su a daidaitacciyar Hausa. yayin da biyu
kuma an fi yin amfani da su a karin harshen Sakkwatanci, amma duk da haka dokar
rubuta su ɗaya ce, a haɗe ba a rabawa. Dubi yadda ake son su bayyana a cikin
jimla kamar haka:
- wancan yaron Bakane ne
- waɗancan matan sakkwatawa ne
- waɗannan littaffan na malama ne
- wannan gida na kakana ne
- wane yaro ne wancan?
- Na haɗa su da waɗancan
- Manta da zancen wannan
- Ku yi hattara wancan zai
ruga
- Jaye wannan waɗancan nake
nufi
- An fi samun waɗannan a
kasuwa
- Gajeren ya fi wannan ƙwazo
da naci
A tsarin Nahawu wannan fasalin za a lura da cewa, kalmomin: “Wannan da Waɗannan”
suna nuni ga abin da yake kusa sosai, haka kuma “wannan” tilo ne amma “Waɗannan”
jam’i ne a tsarin nahawu. Su kuwa “wancan da waɗancan” suna nuni ga abin da
yake nesa ko yake da ‘yar tazara. “wancan” tilo ne amma “waɗancan” jam’i ne ga
tsarin nahawu. Tattare da waɗannan bambance-bambancensu na nahawu duka, idan an
zo a rubutu a haɗe ake rubuta su.
Bayan haka, idana aka dubi waɗannan kalmomi wato kalmomin ishara kalmomi ne
masu nuna abin da ake magana a kanshi. Haka kuma mun kawo misalai daban-daban
masu ma’ana waɗanda ke da dangantaka da wannan aikin kamar yadda aka jera su a
cikin jimla domin su ƙara bayar da ma’ana, saboda haka kalmomin ishara/manuni
suna nuna abin da ake magana a kansa ko mai nisa ko kuma wanda yake kusa.
Kalmomin Tambaya
A kowane lokaci mai rubutu ke son ya yi tambaya, ko kawo wata tambayar da wani
ya yi, zai yi amfani da wasu kalmomi, kalmomin da yake yin amfani da su, masu
nuna tambaya su ne kalmomin tambaya. Ba ainihin kalmomin ne tambaya ba, amma su
ke bayyana domin su ƙara fito da tambayar a fili a fahimceta. Ga tsarin
kalmomin tambaya kamar haka:
Jinsi
Adadi
- Wane? Namiji tilo
- Wace? Mace tilo
- Mene? Mace/namiji Jam’i/tilo
- Waɗanne? Mace/Namiji Jam’i.
Da yawa sabon ɗan koya ke ruɗewa, idan waɗannan kalmomin tambaya sun haɗu
dirka, wani lokaci sai a kwaɓe su taru a rasa gane bakin zaren. Ga yadda tsarin
yake idan suka haɗu da dirka:
- Wane ne wancan?
- Wace ce wannan?
- Mene ne bayanin malam
- Waɗanne ne yaran sarki
Waɗannan kalmomi haɗuwar su a kalmomin dirka na “ne” ko “ce” kar ya ruɗa ka,
kalmomin tambaya haɗe ake rubuta su, su kuwa “ce” da “ne” a rubuta su daban.
- Ya ɗaga kai ya ce wane?
- Bayan wannan wace?
- Don ya hana ka mene?
- Ko kun san wane ne wannan?
- In ka san ta wace ce a
cikinsu?
Dalilin yi musu sunan kalmomin tambaya ke nan. A kowane hali suka zo, akwai
sigar tambaya a jimlar da suke. Kalmomin ba su da wata doka, a tsarin
nahawun jimla ko ma’ana domin a kowane bagire suna bayyana ga jimla su ba da
ma’ana. Misalai da suka gabata suna bayyana a farkon jimla, da ƙarshen jimla da
kuma tsakiyar jimla.
Haka kuma kalmomin tambaya suna nuni ne a kan tambayar wani abu kamar yadda
sunan ya nuna. Mun kawo misalai da dama waɗanda mai karatu ko mai rubutu da ya
duba zai ga alamun tambaya kuma zai fahimta ya gane abin da ake ce ma kalmomin
tambaya. Haka kuma waɗannan kalmomi na tambaya suna da dangantaka da wannan
aikin namu wato” kalmomi masu ma’ana” da kuma wasu sauran kalmomi da za mu dubu
a can gaba. Domin samun bayanai masu inganci.
Kalmomin Jam’u
A tsarin nahawun rubutun Hausa, Kalmomin da ke nuni zuwa ga tarsashin abu
dukkanninsu a haɗe ake rubuta su. Kalmomin wannan rukuni sukan kasance na
jinsin namiji ko na mace, tilo ko jam’i duk hukuncin rubuta su ɗaya ne. a haɗe
ba a ware su ba. Dubi tsarin waɗannan kalmomi. Misali:
Rukuni na ɗaya:
- Kowa
- Komai
- kowane
Rukuni na biyu:
- Kowace
- Ko yaushe
Rukuni na uku
- Ko’ina
A tsarin wannan rukuni, rukuni na farko kalmomin jam’u ne wanda ya haɗe komai
da komai. Kalmar “kowa” ana yin ta ga dukkan jisunan biyu wato na namiji da
mace duka. Kalmar “komai” kuwa ana danganta da da kowane irin abu. Sai kalmar
“kowane wadda ake danganta ta da jinsin namiji kuma jam’i. Sai kalmar “kowace
wadda ake dangantawa da jinsin mace, kuma jam’i. Ita kuma kalmar “Koyaushe” ana
danganta ta da lokaci. Kalmar “Ko’ina” kuwa ana dangantata da bagire. Don haka
ne ake ce ma waɗannan kalmomi “Kalmomin jam’u”. Idan mai rubutu ya ci karo da
su ana rubuta su a haɗ ba a ware ba.
A cikin wannan fasali akwai wasu kalmomi masu kama da kalmomin jam’u kuma suma
idan mai rubutu ya ci karo da su a haɗe ake rubuta su ba a rabe ba. Ga tsarin
kalmomin kamar haka:
- Waɗansu
- Sauransu
- irinsu
waɗannan kalmomi duk lokacin da suka bayyana a rubutu a haɗe ake rubuta su ba a
rabe ba. Ga dai sigar yadda waɗannan kalmomi su ke a cikin jimla:
- kowa ya zo nan kusa
- ba ni son a ce komai
- na fahimci kowane daga
cikinsu
- kowace rana da irin ƙaddarar
da ke ciki
- a riƙa tunawa da
makoma koyaushe
- ko’ina kake ba ka tsere wa
ajalinka
- bayan ta’asar waɗansu ɓarayi
suka shigo
- da tsinkayarsu na
gangame sauransu
- irinsu ne ke girma su hinjire
wa malamansu
Kamar yadda muka ga misalai a sama na waɗannan kalmomi wato “Kalmomin Jam’u”.
Kalmar Jam’u kalma ce da ke haɗa jimillar wani abu domin samun sauƙi ga mai
magana. Idan aka ce kowa ba sai an ce da ke da ke ba ko da kai da shi ba, wato
kowa ta game ku duka. Haka idan aka ce komai ba sai an ce da wannan da wancan
ba wato iata ma kalmar ta komai ta game su duka. Haka idan aka ce, ko yaushe,
ba sai an ce da rana ko dare da safe ba, wannan kalma duk ta haɗe su. Haka abin
yake ga sauran kalmomin kamar, ko’ina, waɗansu, sauransu, irinsu.
Raba Kalmomi A Rubutu
dukokin raba kalmomi na daga cikin manyan babuka cikin babukan rubutun Hausa.
Raba kalma shi ne a bai wa kowace mai cin gashin kanta damar a rubuta ta ita kaɗai
ba tare da an liƙa ta da wata ba. Dokokin raba kalmomi a rubutun Hausa sun fi
dokoin haɗe kalmomi yawa, kuma sun fi su rikitarwa da wuyar ganewa ga ɗan koyo.
Wannan shi ne dalilin da ya sa muka fara gabatar da dokokin haɗa kalmomi. A ƙa’idar
raba kalmomi dole a kiyaye da hukunce-hukuncen nahawu sosai. Domin da su ake
kafa hujja wajen raba kalmomin. Haƙiƙa zumuntar raba kalmomi da nahawun Hausa
irin ta jini da tsoka ce. Don haka da nahawu za mu dinga tafiya wajen yin
bayanin waɗansu matsaloli da yadda ake warware su.
Dokar Wakilin Suna Da Aikatau
Haɗuwar wakilin suna da
aikaltau wata matsala ce babba mai rikitarwa. Kasancewar wakilin wata kalma mai
wakilta kalmar suna ya sa ake kiran wannan kalmar da wakilin suna. Ita kuma
kalmar aikatau kalma ce da ke ɗauke da aiki a cikin jimla.
Doka ta farko dai ita ce ba a haɗe wakilin suna da aikatau. Wakilin suna dai
shi ne: Ni, Kai, Shi, Ita, Ku, Su, Mu, Ke da sauransu. Aikatau
kuwa yana da kalmomi da suka danganci: ci sha, yi, kama, kashe, zo,
tafi, guga, goge, ranke, sa, zuba, share, da dai sauransu. Ga dai
yadda waɗannan kalmomi suke a cikin jimla:
- Musa ya tafi kasuwa
- Ali ya je makaranta
- Sani ya kama akuya
- Binta ta ɗora girki
- Musa ya yanka rago
- Aminu ya saye mota
- Ladi ta share ɗaki
Idan aka yi la’akari da waɗannan jimloli da aka kawo daga sama za a lura cewa,
za a ga an ja ma wasu kalmomi layi a ƙasa. Waɗannan kalmomi dai akwai wakilin
suna a cikinsu kuma akwai aikatau. Kalmomi kamar: ya, ta, dukkan su wakilan
suna ne. kuma kalmomi kamar: share, yanka, tafi, je, zo, ɗora, kama. Dukkan su
aikatau ne.
Haka kuma za a lura cewa, dukkan su an rubuta su a rabe ba a haɗe ba. Wannan ke
nuna cewa, haka ake rubuta su. Ga dai yadda a dace a rubuta su idan sun zo a
cikin rubutu.
Wakilin suna na
Farko Aikatau
Naa
zo
Naa
tafi
Naa
share
Naa
je
Wakilin suna na
Biyu Aikatau
Kaa
zo
Kaa
tafi
Kaa
kama
Kaa
share
Kaa
tafi
Ke
zo
Ku
zo
Wakilin suna na
Uku
Aikatau
Shi
je
Ta
je
su
zo
Ana raba waɗannan kalmomi a duk inda aka gan su a cikin rubutu saboda dukkan su
malmomi ne masu zaman kansu. Saboda haka kalmomin wakilin suna da na aikatau ba
a haɗe su a cikin rubutu.
4.0.6 Kalmomin Sharaɗi
Sharaɗi wani abu ne da za a aza a kan aukuwar wani abu. Wani lokaci yakan
kasance ba da zaɓi. A wani lokaci kuma yana kasancewa ba da shawara a kan abu ɗaya.
A cikin kalmomin sharaɗi akwai:
- In
- Idan
- Sai
Fagen rubutu a wasu wurare kalmomin sharaɗi sukan sukan rikitar da mai rubutu,
idan sun haɗu da wakilin suna ko aikatau mai gaɓa ɗaya. Ƙa’idar rubutun Hausa
cewa ta yi ba a haɗe kalmomin sharaɗi da aikatau balle wakilin suna ko wata
kalma can daban. Dubi waɗannan misalai kamar haka:
- Kira shi in ya shiga ciki
- Hana ta in ta ce sai ta yi
- Bi shi sai ya aminta da kai
- Buge shi sai ya mutu
- Kara mata in ta yi godiya
- Gaya masa idan na fita waje
- In an ce sai ya yi, ya yi
- A kore su idan sun ƙi yarda
- In sai ya yi, idan ba a yi
ba, ya yi
Ashe kalmomin sharaɗi na aukuwa sau ɗaya ko biyu ko uku a jimla ɗaya. Haka kuma
duk lokacin da suka haɗu da wakilin suna ba a haɗe su, rubuta su ake yi a haɗe.
Idan kuwa da aikatau suka haɗu anan ma raba su ake yi, ba haɗe su ake yi ba.
Dubi misalan aikatau da suka fi sa kuskure a rubutu: Ci, Bi, Yi, Ba. Ga wasu
misalai a cikin jimla.
An ce sai ya tabbatar, in ce a ba shi kuɗin
Sharaɗin salla musulunci, in ba shi ba salla
In ka ba ni izini, sai in yi magana da ita
Idan an ba shi sarautar, sai in yi hijira kawai
Ba a haɗe kalmar sharaɗi da aikatau da wakilin sun. Za a ba kowanen su damar ya
ci gashin kansa ne a rubutu.
A wannan kuwa wato kalmomin sharaɗi shi ma nau’i ne na raba kalmomi. Wato
bayanin yadda za a rubuta kalmomi ba tare da an game wata kalma a cikin wata
ba. Ko kuma su samu cinkoso. A nan kalmomin sharaɗi kamar yadda sunan ya nuna
kalmomi ne da ke ba da sharaɗin wani umurni, ko shawara a kan wani abu wanda za
ace ka aikata ko kuma a ce kada ka aikata. Misali:
- Idan ka tafi kasuwa, ka dawo
da wuri
- In an baka kaya ka kawo mini
- Ka aje kuɗin a cikin jaka,
kada su ɓace.
Wannan ƙarin bayani ne a kan waɗannan kalmomi na sharaɗi, su ma waɗannan
kalmomi su na da dangantaka da wannan aikin namu na bincike.
4.0.7 Kalmomi Masu Zaman Kansu
Abubuwan da muka tattauna a baya sun isa su baka damar sanin duk kalmar da ke
cin gashin kanta. Kuma ita kalmar da ke cin gashin kanta daban ake rubuta ta.
Duba waɗannan kalmomi da kyau. Misali:
- In ka zo da shi, ka ce da
su, su baka shi.
- Ya sa na ƙi bin su, don ya
fi su
- Da shi, ya fi, ba da shi ba.
- In an san da kai, ka san da
su, da ni da kai
- Ni na san da so da ƙi, ya fi
ku
- In so, in ƙi, in bi, in fi,
ya fi, da, yi, ba da shi ba
- Kun sa ya fi ni, su ke da ƙi
ba ni ba.
Abin lura anan duk cinkoson kalmomi masu gaɓa ɗaya a jimloli bai sa aka haɗa
wata gaɓa da wata ba. Idan aka lura da jimla ta farko ta ƙunshi kalmomi-kalmomi
har goma sha uku babu wadda aka haɗa da wata. A dubu jimla da bakwai za aga
tana da kalmomi masu gaɓa ɗaya-ɗaya har gaɓa sha shida, kuma kowanen su gashin
kansa yake ci ba a haɗa ta da wata ba. Haka kuma komai yawan kalma in dai ƙa’ida
ta ce a rubuta ta a wuri ɗaya to babu zaɓi, wuri ɗaya za a rubuta ta.
Gaɓoɓin Kalmomin Hausa
Ma’anar Gaɓa
Gaɓa: yanki ne na fadar kalma mai tsarin baki da wasali a jere wato
baki da wasali ne tubalin gina kalma. Misali: Ka-ra-tu
4.0.8.1 Rabe-Raben Kalmomin Hausa
A gaba daya dai gaɓa irin biyu ce ta fuskar tsari. Akwai Buɗaɗɗiya da
Rufaffiya.
Buɗaɗɗiyar Gaɓa: ta kunshi baƙi ne sai wasali,
wanda zai iya kasancewa Dogo Ko Gajere, ko Tagwan wasali a Hausa. Ana
nuna ta haka BW/BWW.
Ruffaffiya Gaɓa: kuwa ta ƙunshi baƙi ne da Gajeren wasali,
sannan wani baƙin. Ana nuna ta haka BWB.
4.0.8.2 Tsarin Gaɓa
Gaɓoɓin Hausa na da tsari na Musamman da ake iya rarrabe su da shi. A irin
binciken da masana Hausa suka yi, Tsarin gaɓoɓin Hausa yana da matakai guda
shida. Adadin gaɓa na kalma ya danganta da tsawon wannan kalmar. Akwai kalma
mai gaɓa ɗaya tak da mai gaɓa biyu da mai uku da mai huɗu ko fiye da haka. Duba
wannan misalai:
- Mu
- Gida
- Littafi
- Makaranta
- Masana’anta
- Almubazzaranci
Yanzu abin tambaya mutum bambancin da zai fi saurin lura dashi tsakanin
kalmominnan shida, ba shakka cewa zai yi kalma ta farko ta fita biyu
gajerta, ta biyu tafi ta uku, ta uku tafi ta hudu, da dai sauransu. Amma
kuma tawace hanya za a iya bayyana wannan bammanci na tsayi? Hakika za a
iya yi ta hanyoyi biyu: (a) ta hanyar tattashiya da kuma (b) hanyar
kasha rauji. Dangane da (a) yayin da kalma ta farko ta kunshi haruffa biyu ‘M’
da ‘U’ ta biyu hudu ta kunsa, ‘G,I,D da ‘A” da suaransu. Dangane da (b) kuma
Yayin da kalma ta biyu gareta “GI da “DA”. Fadi sauran kalmomin huɗu da kanka
tare da bugun kashin raujin kowacce. Za ka lura da cewa ta uku na da kanshi
rauji na kalma, shi ake nufi da “Gaɓa”. Saboda haka, kowane kashin rauji na waɗannan
misalai yana zaman “Gaɓa” ne.
A dukkanin gaɓoɓin nan iri biyu, ana kiran baƙin farko gashi, wasali da ke biye
cibiya, sannan a wasalin ƙarshe dangane da rufaffiyar baɓa sai a dubi waɗannan
misalan na ƙasa
(a) Cibiya gajeren wasali
Ci |
“BW’ |
Eat |
Ji |
ƁW” |
Hear |
Wa-ni |
ƁW-BW’ |
Samobody |
Wa-je |
ƁW-BW’ |
Outside |
Sa-la-la |
“BW-BW-BW |
Thin gruel |
(b) Cibiya dogon Wasali
Cii |
ƁWW’ |
Eating |
Jii |
ƁWW’ |
Hearing |
Kii-fii |
ƁWW-BWW’ |
Fish |
Goo-naa |
ƁWW-BWW |
Farm |
Buu-laa-laa |
ƁWW-BWW-BWW’ |
Whip |
(c ) Cibiya tagwan wasali
Yau |
ƁWW’ |
Today |
Kai |
ƁWW’ |
Head |
Tuu-rai |
ƁWW-BWW’ |
Europe |
Sau-ruu |
ƁWW-BWW’ |
Mosquito |
Rufaffiyar Gaɓa
Nan |
ƁWW’ |
Here |
Can |
ƁWW’ |
There |
Kum-fa |
ƁWW-BWW’ |
Form |
Bi-yar |
ƁWW-BWW’ |
Five |
Kan-ka-naa |
ƁWW-BW-BWW’ |
Water-melon |
Ya kyautu mu jawo hankalin a kan cibiyar rufaffiya Gaɓa
Ko yaushe gajeren wasali ne. A nan watakila za a yi
tambaya a ce yaya lamarin yake. Misali, idan an zo ƙara dafa ƙeya
–nl-r Ga Buɗaɗɗiyar Gaɓa wadda
cibiyarta dogon wasali ne ko tagwan wasali yadda ƙarshen za ta komo
rufaffiyar ‘Gaɓa. Shi wannan dogon wasali ko tagwan ba zai zauna yadda yake ba?
A zahirin gaskiya ko da a irin wannan hali, dogon wasali nan
ko tagwai sai an mayar da shi gajeren wasali, kamar yadda za mu misalta
nan ƙasa:
‘Daa (son) + ɗafa-ƙeya –n ɗan (the Son), ba ɗaan ba
‘Yaa (daughter) + ɗafa-ƙeya –r ‘yar ( the daughter) ba ’ yaar ‘ ba.
Mai (oil) + ɗafa-ƙeya –n Man (the Oil) ba main ba
4.0.8.3 Yawan Gaɓoɓin Hausa
Adadin gaba na kalma ya dangata ne da tsawon wannan kalma
Akwai mai gaba daya, Misali
Mu, Ku, Su, Zo, Je, shi , ci, yi, ni, ki, kai, sha, yi, da sauransu.
Akwai mai gaba biyu Misali:
Tafi, Waje, Wani, Wawa, kusu, mari, zagi, taya, kare, kaza, rago, tasa, mota,
kwano, kwakwa, mara, fari, jika, zani, ido, da dai sauransu.
Akwai mai gaba uku
Karatu, Rubutu, Kujera, Taburi, akuya, agwagwa, alewa, akwati, da sauransu.
Akwai mai Gaɓa Huɗu:
Misali:
Makaranta, Massalaci, Mahaukaci, malalaci, mahanƙurci, marowaci, marowata,
sakatare, madakata, mazambata, makarkata, maƙaryaci, da dai sauransu.
Akwai mai gaba Biyar
Masana’anta, Marubuciya, Bagidajiya. Taɓarɓarewa, damalmalawa,
sakankancewa, Cumuimuyewa, Duƙunƙulewa da dai sauransu.
Akwai mai gaba shida
Damokuradiya, Al-mubazzaranci, da sauransu.
Babi Na Biyar
5.0.1 Jawabin Kammalawa
Babu shakka wannan
bincike ya kawo ƙarshe kuma a cikin wannan babi ne za mu gabatar da jawabinmu
domin kammala wannan bincike. Wannan aiki, aiki ne da muka ba taken “ Nazarin
kalmomi Masu Ma’ana da Matsayinsu A Rubutun Hausa” Kuma mun kasa wannan kundin
bisa ga tsari na babi-babi inda muka zuba shi bisa ga babi biyar.
Baya ga babi na ɗaya da babi na biyu waɗanda suke su abin da ake gudanarwa a
cikinsu bai wuce abin da aka tsara ba a ƙa’idar gudanar da aiki irin
wannan.
A babi na uku dai nan ne muka kawo bayanai a kan ma’anar kalma da azuzuwan
kalmomi inda har muka yi tsokaci a kan azuzuwan kalmomin kamar suna da wakilin
suna da aikatau da bayanau da dai makamantansu. Kuma duk a ciki ne muka kawo
yadda ake rubutun kalmomi da sassan jimla.
A babi na huɗu kuma nan ne muka yi tsokaci a kan Dokokin rubutu na haɗe kalma
da rabata, kuma mun kawo wasu wurare da suke buƙatar a haɗe kalmomi da kuma
inda ya dace a haɗe su. Mun bayyana cewa dokar rubutu ba ta aminta da haɗe
wakilin suna ba da aikatau ko suna, haka kuma bata yarda a haɗe suna da aikatau
ba. Mun kawo wasu misalai domin kafa hujja. Kuma duk a wannan babi ne muka yi
bayanin gaɓa da yadda take tare da kawo wasu kalmomi da za su taimaka wajen
fito da manufar wannan aiki namu.
A babi na biyar kuwa nan ne muka kwashe kayanmu da muka baza a yayin da muke
gudanar da wannan bincike. Kuma nan ne muka kawo ƙarshe a wannan bincike don
haka muke kammala wannan bincike a nan. Kamar yadda aka gani a Jawabinmu na
kammalawa sai ko shawarwari da za a gani a nan ƙasa kaɗan.
5.0.2. Shawarwari
A matsayinmu na masu nazarin harshen Hausa muna ba duk wanda zai yi nazari a
wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da kundin mu kuma in har binciken
nasu yana da alaƙa da namu da su yi ƙoƙarin ɗorawa daga inda muka tsaya kar su
kwashe ɗai wannan ba ya taimaka wa nazari. Kamar yadda muka zaɓo taken da wani
bai taɓa yi ba muka yi shige –shige har muka tattaro bayanan da suka gina muna
wannan kundin ya zama abin karatu ga wasu to lallai suma ya zama wajebi su dage
don su samar da wani abu mai amfani, ba wai su kwashe abin da wasu suka yi ba.
1 Comments
munji dadin Karo da wannan bincike NAIA a internet muna godiya visa jajircewarku wurin karfafa wannan yare namu mai fading gaske
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.