Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Wakar Daddadan Dadin Saniya Ta Alhaji Ak’ilu Aliyu

NA

HINDU YUSUF H                   10698

UMMA ABUBAKAR             10705

SAMIRA SULEIMAN             10749

SASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA K’ERE-K’ERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA

www.amsoshi.com

SADAUKARWA


Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta k’asa (NCE) a Sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere da ke Gusau a jihar Zamfara ga mahaimafanmu wato Alhaji Aminu da Alhaji Yusuf Maifata da Malam Abubakar. Da fatar Allah ya saka masu da alhairinsa amin.

 

 

GODIYA


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.

Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun farko har ya zuwa ranar k’arshe.

Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka muna domin ganin hak’armu ta cimma ruwa, musamman ga iyayenmu kamar su Alhaji Aminu da Alhaji Yusuf Maifata da Malam Abubakar da suka jure da yin hak’uri da mu har muka cimma wannan lokaci, haka kuma muna mik’a godiyarmu zuwa ga iyayenmu mata da suka bamu goyon baya har Allah ya nufe mu da gama wannan karatu tare da yin wannan kundin. Suma dai ‘yan’uwa da abokan arziki ba za mu bar su a baya ba Allah ya saka masu da alherinSa amin

Haka kuma muna mik’a kyakyawar  godiyarmu ta musamman ga malamanmu Na wannan sashe kamarsu; Dr. Sani Aliyu Soba da Haruna Umar Maikwari wad’anda ya d’auki tsawon lokaci suna kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo k’arshe. Allah ya saka masu da mafificin alherinSa amin. Sai godiya ta musammam ga Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Dr. Haruna Umar Bungud’u, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba, , Mal. Aminu Saleh, Mal. ‘Dahiru Sankalawa da mal. Bashir Tsafe da Mal. Ibrahim ‘Dan’amarya da Malam Habibu Lawal K’aura

 

 

JINJINA


Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu jinjina ma malaman mu musamman Dr. Sani Aliyu Soba da Mal. Haruna Maikwari da ma wasu daga cikin mutanen da suka taimake muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan d’alibai da ma duk masu neman k’arin haske dangane da aikinmu. Muna masu rok’on Allah ya saka masu da maifificin alheri. Amin.

 

K’UNSHIYA


Shaidantarwa -      -        -        -        -        -        -        -        ii

Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        -        -        iii

Godiya        -        -        -        -        -        -        -        -        iv

Jinjina         -        -        -        -        -        -        -        -        vi

K’unshiya    -        -        -        -        -        -        -        -        vii

BABI NA ‘DAYA


1.0 Gabatarwa       -        -        -        -        -        -        -        1

1.0.1 Yanayin Bincike    -        -        -        -        -        -        2

1.0.2 Muhallin Bincike   -        -        -        -        -        -        3

1.0.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike    -        -        -        -        3

1.0.4 Matsalolin Da Suka Taso  -        -        -        -        -        4

1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta      -        -        -        -        5

1.0.6 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        7

BABI NA BIYU


2.0 Gabatarwar Babi       -        -        -        -        -        -        8

2.0.1  Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata   -        -        8

2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -        -        -        -        -        14

2.0.3 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        14

Babi Na Uku


3.0 Gabatarwar Babi       -        -        -        -        -        -        16

3.0.1 Ma’anar Wak’a      -        -        -        -        -        -        16

3.0.2 Rubutacciyar Wak’a         -        -        -        -        -        -        17

3.0.3 Tak’aitaccen Tarihin Rubutacciyar Wak’a.    -        -        19

3.0.4 Wak’ok’in K’arni Na Goma Sha Takwas (K’18).    -        20

3.0.5 Wak’ok’in K’arni Na Goma Sha Tara. (K’19).        -        -        21

3.0.6 Wak’ok’in K’arni Na Ashirin (K’20).  -        -        -        24

3.0.7 Wak’ok’in K’arni Na Ashirin Da ‘Daya (K’21)       -        -        26

3.0.8 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        28

Babi Na Hud’u


4.0.1  4.0. Gabatarwa      -        -        -        -        -        -        29

4.0.1 Bayanan Share Fage         -        -        -        -        -        29

4.0.1.1 Tsokaci a kan Marubucin Wak’ar Daddad’an Dad’i

Saniya         -        -        -        -        -        -        -        29

4.0.2 Muhimman Sassan Nazarin Wak’a       -        -        -        31

4.0.2.1 Jigo -        -        -        -        -        -        -        -        31

4.0.2.2 Nau’o’in Jigo.     -        -        -        -        -        -        32

4.0.2.2.1 Babban Jigo.    -        -        -        -        -        -        32

4.0.2.2.2 K’aramin Jigo.  -        -        -        -        -        -        33

4.0.3 Wasu Daga Cikin Jigogin Rubutacciyar Wak’a.       -        34

4.0.4 Salo    -        -        -        -        -        -        -        -        34

4.0.5 Nazarin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya      -        -        -        36

4.0.5.1 Jigon Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya       -        -        -        36

4.0.5.2 Gajerta Jigon Daddad’an Dad’i Saniya        -        -        -        37

4.0.5.3 Warwarar Jigon Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya -        38

4.0.6 Salo Da Sarrafa Harshe a Wak’a Daddad’an Dad’i Saniya 41

4.0.7 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        43

Babi Na Biyar


5.0 Jawabin Kammalawa -        -        -        -        -        -        44

5.0 Jawabin Kammalawa -        -        -        -        -        -        44

5.0.1 Shawarwari  -        -        -        -        -        -        -        45 Manazarta         -        -          -        -        -        -        -        -        47

Ratayen Wak’ar Yabon Ubangiji Ta Mu’azu Had’ejia    -       48

 

Babi Na ‘Daya

Wannan aikin mai take “Nazarin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya ta Alhaji Ak’ilu Aliyu” Mun gudanar da shi ne domin cika wani gurbi daga cikin sharud’d’an wannan makaranta. Haka kuma aikin zai taimaka mana wajen gani mun samu kar’bar takardunmu na shaidar kammala wannan karatu na wannan makaranta (N.C.E).

Domin samu sauk’in gudanarwa mun kasa wannan aikin namu a kan tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko za mu kawo bayani ne a kan Gabatarwa, da Manufar Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike sannan mu biyo baya da kammalawar Babin.

A babi na biyu kuwa nan ne za mu yi tsoakci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata da kuma Salo Da Tsarinsa.

Babi na uku za mu kawo Ma’anar Wak’a da Ma’anar Rubutacciyar Wak’a da Tak’aitaccen Tarihin Rubutacciyar Wak’a da Rabe-raben Rubutacciyar Wak’a da Muhimmancin Rubutacciyar Wak’a.

Shi kuwa babi na hud’u nan ne za mu d’an yi Tsokaci a kan Marubucin Wak’ar da Nazarin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya da Bayanan Share Fage da Jigon Wak’ai da Zubi da Tsarin Wak’ar da Salo da Sarrafa Harshe da ke cikin wak’a, kana mu biyo da Kimar jimilla.

Haka kuma a babi na biyar nan ne za mu yi Kamalawa ta gaba d’aya ta wannan kundin sai Shawarwari su biyo baya. Manazarta da Ratayen Wak’ar da aka nazarta za ta kasance a k’arshe cikin wannan kundi.

1.0.2 Manufar Bincike


Wannan aikin yana da manufar yi wa wak’ar Alhaji Ak’ilu Aliyu ta “Daddad’an Dad’i Saniya” kallon garau da bitar tsaf-tsaf da nazarin k’wak’waf domin fito da wasu muhimman abubuwa da wak’ar ta k’unsa, wad’anda ba kasafai mutum zai yi farat ya fito ya ce ga su ba.

Haka kuma aikin namu yana da manufar zak’ulo wasu bayanai sahihai dangane da jigon wak’ar da kuma abubuwan da shi marubucin ya fad’a da wasu abubuwa masu amfani da ke tattare da ita kanta saniya. Manufar wannan binciken ba za ta kammala ba har sai mun d’an warwari jigon wannan wak’a mai nazari ya ga yadda ake sharhi ko nazarin wak’a musamman rubutacciya.

1.0.3 Muhallin Bincike.


        Wannan aikin mun gudanar da shi a kan adabi kuma rubutacce na Hausa. Sannan muka tak’aita shi a kan wak’ar “Daddad’an Dad’i Saniya ta Alhaji Ak’ilu Aliyu”, kuma muka ke’bance aikin namu a kan “ga Nazarin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya” saboda haka muhallin wannan bincike zai ke’banta ne kawai a kan wak’ar.

1.0.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike


Domin samun nasarar gudanar da wannan aiki namu cikin sauk’i mun bi hanyoyi da dama da suka had’a da:

Karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da muk’alu da Mujallu domin zak’ulo wasu bayanai masu nasaba da aikinmu. Mun kai ziyara a d’akunan karatu da suka had’a da nan cikin makarantarmu wato Kwalejin Ilimi da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya da ke Garin Gusau, (FCET) Gusau, da Kwalejin Fasaha da Kimiyya (ZACAS) Gusau, da Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara da ke Maru (C.O.E.) Maru, da sauransu domin tattara bayanai masu nasaba da aikinmu.

Haka kuma mun yi amfani da tuntu’bar malami masana da manazarta wak’ok’in Hausa.

Wata hanya da muka bi ita ce, hanyar tuntu’bar wasu daga cikin malamanmu da muka san sun k’ware wajen sharhin wak’a suka bamu tasu gudummuwa domin mu ga wannan aikin bincike ya kammala.

1.05. Matsalolin Da Suka Taso.


        A wannan bincike mun fahimci cewa akwai wani gi’bi da aka manta ba a cika ba a cikin fannonin da ake bincike a kansu. A  akwai abubuwa da yawa wad’anda suka shafi al’amurran jama’a na wannan zamani amma sai aka yi fatali da su ba wanda ya kula. Tuni wasu mashahuran malamai suka yi iya k’ok’arin su don ganin cewa sun samar wa jama’a abin karatu da kuma abinda za su nazarta. Wannan ya nuna kenan har ko yaushe ba a rasa wasu da suka yi k’ok’ari wajen samar da abin da za a iya dogaro da shi na abin da ake nazari.

Saboda a d’an ilmin da ke akwai a wannan fanni da aka d’auka, na nazarin wak’ar ba a yi wani aiki mai yawa ba a wannan fanni. Wannan na d’aya daga cikin manyan dalilan da suka ja hankalinmu har muka fantsama cikin yin nazari a kan wannan fanni.

Wasu da suka taso a wannan lokaci ba su san, wak’a tana da matuk’ar rawar da take takawa ba wajen jan hankalin mai sauararo ba. Haka kuma muna iya cewa wasu wak’ok’i da ake yi a wancan zamani suna d’auke da karantarwa da ilimantarwa musamman abin da ya shafi addini. Wannan yasa muke ganin ya dace mu mayar da hankali a kan wasu salalai da Alhaji Ak’ilu Aliyu ya yi amfani da su a cikin wak’arsa ta “Daddad’an Dad’i Saniya”.

1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta


Kamar yadda ma’anar ke nuni “matsala” na nufin irin cikas d’in da aka ci karo da shi a yayin da ake gudanar da wannan bincike. A duk lokacin da mutum ya samu kansa a cikin irin wannan aiki na bincike to lallai wajibi ne ya ci karo da wasu matsaloli da za su iya kawo tarnak’i ga aikinsa na bincike kafin ya kai ga cin nasara. A lokacin gudanar da wannan kundi mun samu barazana ta wasu matsaloli da suka had’a da:

Matsalar littafan karatu. Wannan matsalar,  matsala ce babba saboda wannan makaranta ba ta da isassun littafai da za a duba, wannan ya sa sai da muka lek’a wasu makarantu don samun wasu bayanai da za su taimaka a gina wannan kundin. Wannan walaha ta ziyarce-ziyarcen wasu makarantu ta kawo tafiyar hawainiya ga gudanar da wannan bincike.

Matsalar kud’i: wannan matsala tana d’aya daga cikin manyan matsaloli da suke tauye komai da ake yunk’urin yi har dai in ya zama abu ne mai buk’atar a inganta shi. Matsalar kud’i babbar matsala ce har dai garemu mata da yake d’auke ake da nauyinmu kuma ba kasafai za mu nemi a bamu kud’i a gidajenmu a bamu ba, sai an samo kuma sai an gani in babu wani abu da ya fi buk’atarmu muhimmanci sannan a bamu, idan kuwa aka samu wani abu da ya fi tamu buk’atar muhimmanci to, lallai mu ba zamu samu ba sai har an samu wasu gaba sannan wata kila mu samu. Rashin kud’in dai ya kawo matsala, amma yanzu an shawo kan matsalar.

Matsalar wutar lantarki: wannan matsala ta taka rawa sosai wajen yi wa wannan aiki tarnak’i wato matsalar ta kawo tafiyar hawainiya wajen gudanar da wannan binciken. Ana kuma iya gane cewa wannan zancen namu na matsalar wutar lantarki gaskiya ne idan aka dubi yanayin garin na Gusau za a ga cewa babu isasshiyar wutar lantarki wadda da ita ne kawai za a iya buga muna rubutunmu a cikin Kwamfuta (Computer). Wannan ya sa aka saka wannan matsala ta rashin wuta a cikin matsalolin da suka taso suka dabaibaye gudanar wannan Bincike.

 

1.0.7 Kammalawar Babi.


A wannan babin mun yi gabatarwa, muka biyo da manufar bincike inda muka ce, za mu yi nazara k’wak’waf ga wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya ta Alhaji Ak’ilu Aliyu. Mun kuma bayyana muhallin da za mu gudanar da wannan bincike inda har muka ce, za mu tak’aita wannan bincike a fagen adabi kuma na zamani. Binciken ya bayyana hanyoyin da zai bi wajen tattaro bayanai da za su taimaka domin gudanar da wannan aikin. Sai kuma Matsalolin da suka taso da kuma wad’anda aka fuskanta.

 

Babi na Biyu

A wannan babi na biyu nan ne za mu yi bitar ayyukan da suka gabata, wannan kuma shi ne ake kira waiwaye. Wato ana nufin mai nazari ya yi binciken ayyukan da suka gabata kama daga littattafai da kundaye da mujallu da muk’alu da ma jaridu in akwai wani abu da yake da dangantaka da nasa. Bayan waiwaye kuwa za mu yi tsokaci dangane da salon nazari da zubi da tsarinsa.

2.01. Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.


Kamar yadda muka riga muka sani cewa waiwaye shi ne adon tafiya, to ko a wannan aiki waiwayen zai taimaka matuk’a, don haka za a waiwayi baya don ganin irin ayyukan da suka gabata wad’anda suke da dangantaka da wannan aikin..

Domin yi wa wannan aikin kwalliya za a binciki littattafai da kundaye da muk’alu da dai sauran wasu ayyuka da suka shafi wannan. Mai nazari ya dace ya bincike wasu ayyuka da aka gudanar a wannan fanni da yake bincike a kansa don ya ga inda aka tsaya shi kuma ya san inda zai d’ora nasa. Wanna ya ba mu damar mu zak’ulo wasu ayyuka don mu san inda ya dace mu kama. Ga dai wasu daga cikin ayyukan da kuma samu da za su yi muna jagora ga gudanar da namu aikin.

Gusau S.M (1996), a wani littafinsa mai suna “Makad’a da Mawak’an Hausa”  a wannan karon masanin ya zuba littafansa ne a tsarin kashi-kashi kamar haka: Kashi na d’aya ya kawo makad’an yak’i, a kashi na biyu kuma ya kawo makad’an sarakuna rukuni na I, a kashi na uku kuwa ya kawo makad’an sarakuna runi na II. Kashi na hud’u makad’an jama’a kashi na biyar kuma makad’an sana’a, daga nan sai ya kammala.

Wannan kundin yana da alak’a da namu aikin yayin da shi Gusau ya kalli wak’ok’in ya karkasa su kuma ta’allak’a aikinsa ga wak’ok’in baka, mu kuma muka d’auki rubutacciyar wak’a muka nazarta.

Gusau S.M (2008), a wani littafi nasa mai suna “Wak’ok’in Baka A K’asar Hausa, Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu” har wa yau dai masanin ya zuba littafinsa a tsarin babi-babi, inda a babi na d’aya ya kawo tarihin k’asar Hausa da yanaye-yanayenta, a babi na biyu kuwa ya kawo kid’a da kayan yinsa. Sai a babi na uku inda ya kawo makad’an baka na Hausa. A babi na hud’u kuwa ya kawo halayya da nau’o’in wak’ok’in baka, daga nan dai sai ya shiga babin kammalawa inda ya gudanar da jawabinsa na kammalawa.

Wannan littafi yana da rawar da zai taka matuk’a wajen gudanar da namu aikin domin kuwa ya nazarci wasu wak’ok’i kuma mun ga yadda ake nazarin wak’a. Don haka za mu bi wannan salo da ya yi amfani da shi mu tsara namu kundin a kan nazarin wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya.

Shi kuwa Mustapha Abba da Balarabe Zulyadaini (2000) a cikin wani aiki da suka yi mai suna “Nazari Kan Wak’ar Baka Ta Hausa” wad’annan masana sun gudanar da aikinsu ne a kan tsarin na babi-babi, inda suka kawo tarihin samuwar wak’ar baka a k’asar Hausa da rabe-raben makad’an baka a k’asar Hausa, dangane da rukunoninsu da jigogin wak’ok’in baka na Hausa.

Wad’annan masana sun gudanar da aikin su a fannin adabin baka kuma wak’a mu kuma daman aikin da muke da k’uduri yi na adabi ne sai dai yana da bambanci saboda namu aikin wak’a ce ta zamani. Wannan ya nuna cewa aikinmu yana da alak’a da nasu sai da su suna kallon dukkannin makad’a na k’asar Hausa ne yayin da mu kuma rubutacciyar wak’a d’aya ce muka za’ba don yin sharhi a kai.

Sar’bi (2007), ya rubuta littafi mai suna “Nazarin Wak’ar Hausa” wannan marubuci ya rubuta littafin ne domin masu nazarin wak’ok’in Hausa musamman rubutattu. A cikin wannan littafi nasa ya yi magana a kan jigo, salo zubi da tsari, nau’o’in rubutacciyar wak’a da dai sauransu.

Wannan aiki na Sar’bi yana da alak’a da namu aikin saboda ya yitsokaci a kan wak’ar zamani yayin da muma namu aikin yana magana a kan wak’ok’in zamani. Inda kuma muka sha bamban da shi shi ne, shi Sar’bi wak’ok’in zamani ya yi tsokaci a kansu amma ba mu ga wak’ar da muke nazari ba a ciki.

Bunza (2009), ya rubuta wani littafi mai suna “Narambad’a” wannan littafi da wannan masani Al’dar Hausa ya rubuta littafi ne wanda ya tsara shi bisa ga tsari na babi-babi har babi goma sha biyu. A babi na d’aya masanin ya kawo jigogin wak’ok’in Narambad’a, a k’ark’ashi wannan babin ya fara da gabatarwa da da asalin kalmar jogo da rabe-raben jigo da babban jigo da k’aramin jigo da yadda ake neman sarauta da yadda sarauta take da nad’in sarauta.

A cikin babi na biyu akwai masarauta da a wak’ok’in Narambad’a, a babi na uku ya kawo sarki a wak’ok’in Narambad’a, a babin na hud’u ya kawo fada a wak’ok’in Narambad’a, a babi na biyar kuwa ya kawo k’ananan jigogin wak’ok’in Sarauta. A babi da shidda akwai ke’ba’b’bun k’ananan jigogin sarauta, a babi na bakwai nan ne ya kawo salon wak’ok’in Ibrahim Narambad’a, a babi na takwas ya ba da falsafar wak’ok’in Ibrahim Narambad’a, a babi na tara ya zo da Tussan wak’ok’in Narambad’a, a babi na goma ya yi bayanin fashin bak’in Bakamdamiya, a babi na gaba sai ya rufe da kammalawa.

Wannan littafi da wannan masani ya rubuta ya haskaka sosai wajen samun dubarar da za a gina wannan aikin ya k’ayatar. Alak’arsa da wannan aikin ita ce, shi yana kallon wak’ok’in Narambad’a yana nazarinsu mu kuma muna nazarin wak’ar “Daddad’an Dad’i saniya ta Alhaji Ak’ilu Aliyu”.

Bungud’u da Maikwari (2014) sun rubuta wata muk’ala mai taken “Birgima Cikin Wak’ar Mu’azu Had’eja: Nazarin Jigon Wak’ar Yabon Ubangiji” malaman sun ta’bo ma’anar jigo da nau’o’isa da yadda ake gane jigo da kuma yadda ake warware shi a cikin wak’a.

Wannan aiki na su Bungud’u ya taimaka ainun wajen samun damar gudanar da wannan aiki. Haka kuma idan aka duba za a ga cewa aikin yana da allak’a da namu aiki saboda dukkansu suna nazarin wak’ok’in k’arni na 21 ne. Inda kuma aka sha bamban shi ne, su Bungud’u sun tak’aita nazarinsu ne a kan jigo a cikin wak’ar “Yabon Ubangiji” ta Mu’azu Had’ejia, yayin da ni kuma ina kallo dukkan sassan nazarin wak’a gwargwado hali.

Bungud’u da Maikwari (2016) sun rubuta littafi mai taken “Wak’a Zancen Hikima” malaman sun kasa wannan littafi gida shida bisa ga tsari na babi-babi. A babi na d’aya sun yi shimfid’a game da ma’anar wak’a da rabe-raben wak’a. sai a babi na biyu inda suka d’auki wak’ar baka suka yi lugudenta tun daga asalinta da sigoginta da nau’o’inta tare da misalai don ganin yadda abin yake gudana. A babi na uku kuwa sun mayar da hankali ga Rubutacciyar wak’a yayin da suka yi mata radan-radan a ciki ita ma sun kawo tarihinta asalinta samuwarta da nau’o’inta da sigoginta, sun kuma kawo misalai a ciki. Sai a babi na hud’u inda suka yi bayani a kan Amsa – Amo tare da misalai. Sai a babi na biyar inda suka ta’bo bayanai game da jigo, kuma sun ‘barje guminsu a ciki game da jigo tare da misakai masu k’ayatarwa. A babi na shida wanda shi ne na k’arshe kuwa sun yi tsokaci a kan Salo.

Wannan littafi na su Bungud’a zai ya taimaka ainun wajen sanin makamar namu aikin.

2.0.2 Salon Nazari Da Zubi Da Tsarinsa.


Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin mutum. Salo muhimmin abu ne a cikin labari ko jawabi, haka kuma duk aikin da aka gudanar ba cikin tsari ba to, ba zai cimma nasara ba. Don haka domin samun nasarar gudanar da wannan aikin cikin sauk’i, an yi amfani da salo mai sauk’i, mai jan hankalin mai karatu. An kuma yi amfani da za’ba’b’bun kalmomi masu sauk’in ma’ana saboda mai karatu ya ji sauk’in karantawa.

Haka kuma an yi amfani da gajeru da matsakaitan jimloli, sannan aka gudanar da bayanan d’aya bayan d’aya a cikin sakin layi mai sauk’in fahimta.

Aikin kamar yadda aka sani an zuba shi ne a kan babi-babi har zuwa babi biyar saboda a samar wa mai karatu sauk’i wajen nazari.

2.0.3 Kammalawar Babi


Kamar dai yadda aka gani a wannan babi mun yi gabatarwa inda muka fad’i cewa a ciki ne za mu yi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, sai muka kawo wasu ayyuka da magabata suka rubuta, masu alak’a da namu kuma muka fad’i inda suka samu bambanci da aikinmu. Mun kuma kawo salo da zubi da tsarin wannan kundin inda har muka fad’a cewa za mu zuba wannan aikin bisa ga tsari na babi-babi kuma zai k’unshi babi biyar.

 

Babi Na Uku.

A wannan babin za mu yi bayani a kan Ma’anar wak’a da Rubutacciyar wak’a da Tak’aitaccen Tarihin Samuwar Rubutacciyar Wak’a da yad’uwar wak’a tun daga k’arni na 18 har zuwa wannan k’arni da muke ciki na 21. Sannan mu biyo da muhimmancin Wak’a ga al’umma.

3.0.1 Ma’anar Wak’a.


Masana da yawa sun ba da gudunmuwa wajen samar da ma’anar wak’a,. Ga wasu daga cikinsu:

Yahya ya ba da tasa ma’anar wak’a da cewa:

“Magana ce da ake shisshirya kalmominta cikin azanci, ta yadda wajen furta su ana iya amfani da kayan kid’a”. Yahya (1997).

Shi kuma ‘Dangambo (2007:) cewa ya yi:

“Muna iya cewa, wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti, d’ango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (k’afiya), da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

A wani aikin kuma Gusau cewa ya yi:

“Wak’ar baka fage ce wadda ake shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre, wad’anda za su zaburar da al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwa da za su ba da damar a cim ma ganga mai inganci. Wak’a bisa jimla, takan zama fitila wadda take haskaka rayuwar jama’a kuma take kare rayuwar al’umma daga sallacewa”  Gusau (2011).

Bungud’u (2014) kuma ya bayar da ma’anar wak’a kamar haka:

“Wak’a ta k’unshi wasu jerin hikimomi ne da a kan tsara domin su dad’ad’a zukatan masu saurare, inda a kan yi amfani da wata za’ba’b’biyar murya don rerawa, ana kuma yin amfani da za’ba’b’bun kalmomi domin fizgar hankalin jama’a ya dawo gare su da zimmar bin diddigin ma’anoni da manufofinsu.

3.0.2 Rubutacciyar Wak’a.


        Rubutaccen adabi shi ne ya haifar da rubutacciyar wak’a, kuma ita rubutacciyar wak’a ba kamar wak’ar baka ba ce ko da yake wak’ar baka ta riga rubutacciya, amma suna da bambanci tsakaninsu. A lokacin da ake yunk’urin yin wak’ar baka za a gaya wa duk wad’anda ake wak’ar da su yadda za ta kasance kuma za su je su koya su hardace kamar yadda take, ba wani zancen su rubuta ta ko su samar mata da wata k’a’ida wadda rubutacciya ta kunsa. Amma a rubutacciyar wak’a duk wanda zai rubuta sai ya bi wata tsararriyar k’a’ida da ta k’unsa. Wannan ya sa aka samar wa wak’ar wasu tsararrun k’a’idoji da ake bi wajen gudanar da ita. Misali idan muka dubi k’a’ida ta aruli wadda ba a samu a wak’ar baka. Akwai kuma sigogi na rubutacciyar wak’a wad’anda wak’ar baka ba ta k’unshe su ba, kamar dai amsa-amo, kari, daidaiton d’angaye da kuma baitoci da sauransu.

Rubutacciyar wak’a wani sak’o ne da ake gina shi a kan tsararriyar k’a’ida ta baiti da d’ango da kari da amsa amo da sauran k’a’idojin da suka danganci daidaita kalmomi, da za’bar su, tare da yin amfani da su, a rubuce sannan a rera lokacin da ake buk’ata.

Haka kuma ana iya cewa; rubutacciyar wak’a hanya ce ta isarwa, ko gabatar da wani sak’o cikin k’ayyadaddun, kuma daidaitattun kalmomi da akan rubuta kuma a rera lokacin buk’ata.

Rubuta wak’a dama ce da ta shafi ke’ba’b’biyar basira. Zurfin ilimi, ko da kuwa na sani k’a’idojin rubuta wak’a ne, ba ya bayar da tabbacin iya rubuta wak’a. Abin nufi a nan shi ne, rubuta wak’a ba shi da wata dangantaka da zurfin ilimi. Allah (SWT), Shi ne kad’ai ke ba wa mutum basira irin ta rubuta wak’a. Saboda haka ana iya samun shaihun malami a fagen nazarin wak’a,  kuma ya kasance bai iya rubuta wak’a ba. Sai dai akan yi sa’a manazarcin wak’a ya zama marubucinta.

3.0.3 Tak’aitaccen Tarihin Rubutacciyar Wak’a.


Abu ne mai wuya a ce ga lokacin da aka fara rubuta wak’a a k’asar nan. Da yawa daga cikin masu binciken rubutattun wak’ok’in Hausa sun yi imani cewa an fara rubuta wak’ok’in Hausa a lokacin jihadin Shehu Usmanu. I, ba shakka a wannan lokacin ne aka fi rubuta wak’ok’in domin watsa manufar jihadi da dalilan yi sa, amma a k’ashin gaskiya tun kafin jihadi ana rubuta wak’ok’i a wannan k’asar. A yanzu haka wasu masana sun gano wata wak’a da wani malami mai suna Shitu d’an Abdurra’uf ya rubuta tun kafin bayyanar Shehu Usmanu ‘Danfodiyo, ana kiran wannan wak’ar da “Jiddul-Ajizi”. Wannan wak’a dai tana magana ne a kan  fik’ifu. Wannan ya nuna cewa akwai irin wad’annan tsofaffin wak’ok’i wad’anda ba a samu kaiwa garesu ba.

Ana iya karkasa rubutattun wak’ok’in Hausa zuwa; Wak’ok’in k’arni na sha takwas da na sha tara da na ashirin kai har ma da na k’arni na ashirin da d’aya, (K’18, K’19, K’20, K’21). Bungud’a da Maikwari (2016)

3.0.4 Wak’ok’in K’arni Na Goma Sha Takwas (K’18).


Muna iya cewa , kamar yadda watak’ila aka sani, tun kafin zuwan Larabawa da Turawa a k’asar Hausa, Hausawa na da wasu wak’ok’i da suke tsarawa su  rik’e a ka, kuma su rera lokacin da suke buk’ata, irin wad’annan wak’ok’i ana rera su ne a lokuta daban-daban. Kuma wad’annan wak’ok’i sun had’a da wak’ok’in da ake rerawa a cikin tatsuniya da na gad’a da na da’be da na farauta da na bara da na aikin gayya da sauransu.

Amma idan aka ce rubutattun wak’ok’i, wato wad’anda ake auna su, a daidaita su bisa wani salo da tsari na musamman, sannan a rubuta su, wannan ya fara ne a k’arni na sha takwas (K’18). A wannan k’arni ne aka samu wasu malamai da suka yi rubuce-rubuce, ciki har da rubutattun wak’ok’i. Wad’annan malaman sun had’a da ; Malam Muhammadu Al-katsinawi, da malam Muhammadu Na birnin Gwari, da malam Shitu d’an abdurra’uf, wanda ya rubuta wak’ok’i masu yawa. Daga ciki akwai wak’ar Tuba da kuma wak’ar Wawiya. (Yahaya 1988: 38-39).

Da yake a wannan k’arnin ba kasafai ake samun wad’anda suka mayar da hankali a fannin nazarin wak’ok’i ba, wannan ya sa ba a samu wasu wak’ok’i ba da yawa kuma iya wad’anda masana suka bayyana muna kenan na abinda aka samu a wancan zamanin wato k’arni na sha takwas (K’18).

Ko da yake ba a samu wasu wak’ok’i da yawa ba a wannan k’arni ba zai hana a d’an samu wadda za a kawo ba don ganin irin yadda wak’ok’in wannan zamani suke. Bungud’u da Maikwari (2016)

3.0.5 Wak’ok’in K’arni Na Goma Sha Tara. (K’19).


         Ko da yake an fara samun rubutattun wak’ok’i tun a k’arni na sha takwas (K’18), ko shakka babu, ba a fara samun ingantaccen tsarin rubuta wak’ok’i, da kuma ha’bakar wak’ok’in ba sai a k’arni na sha tara (K’19). Shehu Usmanu ‘Danfodiyo shi ne jagoran masu jihadin 1804, wanda aka k’addamar sakamakon ta’bar’barewa, da kuma gur’bacewar halaye da d’abi’un Musulmi a wancan lokaci. An yi yak’e-yak’e domin a kyautata tarbiyar musulmi da ta riga ta gur’bata da tsafe-tsafe da camfe-camfe da kuma watsi da ibada. Shi ne ma ya sa wasu marubuta ke kiran yak’e-yak’en da suna jihadin jaddada musulunci.

Daga nan ne ma masu jihadi, k’ark’ashin jagorancin Shehu Usmanu ‘Danfodiyo suka yi tunanin rubuta wak’ok’i a kan fannoni daban-daban a musulunci. Musamman ganin cewa wak’a na daga cikin nau’o’in salo masu jawo hankalin mutane zuwa ga wata manufa. Sun rubuta wak’ok’in da suka shafi wa’azi da shari’ar musulunci, da siyasar musulunci, da fik’ihu da ilimi da sauransu.

Daga cikin wak’ok’in k’arni na goma sha tara (K’19), akwai wad’anda aka rubuta su da Hausa. wasu kuwa an rubuta su ne a cikin harshen Larabci da Filatanci. To amma dai an fassara wad’ansu daga cikinsu a cikin harshen Hausa.

Daga cikin masu jihadi wad’anda suka rubuta wak’ok’i a (K’arni na 19) sun had’a da Shehu Usmanu ‘Danfodiyo da k’aninsa Shehu Abdullahin Gwandu da d’ansa Muhammadu Bello, da ‘yarsa Nana Asma’u da Maryam ‘yar Shehu da kuma Khalil d’an abdullahi da sauran sun had’a da Sa’idu d’an Bello da Dikko d’an Bagine da waziri Bukhari, da sauran almajiransa irin su Isan Kware da Mamman Tukur da Mallam Dambo da Salihu ‘Dan Zama da kuma Abdullahi Mai Bod’inga.

A wannan k’arnin (K’19), kamar yadda aka fad’a cewa an samu wani yunk’uri na bunk’asa ilimi da yad’a addinin musulunci, da kau da jahilci da al’adu, da camfe-camfe a k’asar Hausa. shugabannin jihadi sun yi wallafe-wallafe masu yawa a fannin ilimi daban-daban  da Larabci, kamar su Tauhidi da Fik’ihu da Hukuknce-hukuncen shari’a da tsarin mulki da dai sauransu. Daga nan suka ga cewa hanyar da ta fi sauk’i ga isar da sak’onsu ga jama’a ita ce ta hanyar harshensu. Suka ga cewa kuma wak’a ita ce ta fi saurin shiga kai. Sai suka shiga bayyana musu manufofin nasu a wak’e cikin Fillanci da kuma Hausa, suna tsamo wad’annan manufofin nasu daga cikin talifan nasu da suka yi da Larabci.

Shehu Usmanu da Abdullahi k’anensa da Asma’u da Isa ‘ya’yansa duka sun rubuta wak’ok’i masu yawa da Hausa, amma na fillaci sun fi yawa, sai daga baya ne aka yi ta fassara wasu zuwa Hausa, har ma an fassara wad’ansu rubuce-rubucen daga Larabci zuwa Hausa. Mafi yawan fassarar da aka yi asma’u da Isa da Sa’idu d’an Bello ne suka yi ta.

Yawancin wak’ok’in k’arni na sha tara an rubuta su ne kan yabon Ubangiji (Allah) da yabon Annabi Muhammad (SAW), da wa’azi da Fik’ihu da Shari’a  da sha’anin mulki. Wato dai sun fi ba da k’arfi ga addinin musulunci.

Wannan salo ya ci gaba har zuwa k’arshen wannan k’arnin bai canza ba. Za a kuma samu kowace wak’a tana da mabud’i da marufi, wato a fara ta da godiyar Allah da salatin Annabi, a kuma rufe da su. Duk kuma tsarinsu da ma’aunansu da k’afiyoyinsu, wato amsa-amo duk irin na wak’ok’in Larabawa ne.

Abin lura a nan shi ne su wad’annan wak’ok’i na k’arni na goma sha tara don mutuk’ar amfaninsu da muhimmancinsu ga al’ummar musulmi, har gobe ba a daina cin moriyarsu ba. Hasali ma har gobe ta hanyar su ne mutane da yawa ke koyon addininsu da wasu hukunce-hukunce da tarihin jihadi. Bungud’a da Maikwari (2016)

3.0.6 Wak’ok’in K’arni Na Ashirin (K’20).


A k’arni na ashirin an samu wani sabon salo na rubuta wak’a a k’asar Hausa. sarkin Zazzau Aliyu d’an Sidi shi ne ya fara bud’e wannan k’arni da wak’arsa ta habaici, wadda kuma ba a fara ambaton sunan Allah ba sai da k’arshe aka rufe da Shi. Mun fad’a a baya cewa wak’ok’in k’arni na sha tara kusan sun k’unshi addini ne kawai, kuma suna da mabud’i da marufi, sa’annan kuma malamai ne suka yi su. To amma a k’arni na ashirin, sai ga shi bayan addini, har wasu masu ilimin zamani suna rubuta wak’a. Cikin su akwai ma’aikatan gwamnati, akwai En’e, akwai malaman makaranta. A wannan lokaci mutane irin su marigayi Sa’adu Zungur da Mu’azu had’ejia suka fi shahara. Sa’annan ga su Alhaji Aminu Kano, da alhaji Na’ibi Sulaiman wali da Alhaji Mudi sipikin da Alhaji Ak’ilu Aliyu da Yusuf Kantu da Gambo Hawaja da Tujjani Tukur Yola da malam Bello Sakkwato. Wad’annan mutane ban da rubuta wak’ok’i a kan addini har ma suna rubutawa  kan abubuwan da suka shafi rayuwar d’an Adam ta yau da kullum, kamar su ilimi da siyasa da yabo da dai sauransu.

Idan aka dubi tsari da ma’aunin wak’ok’in k’arni na ashirin za a tarar an samu cigaba a kan wak’ok’in k’arni na sha tara. Ban da koyi da tsarin wak’ok’in Larabawa, sun fito da wani sabon salo a d’aukar ma’aunin wak’ok’in baka su rubuta wak’a da shi, ba tare da ya hau kowane irin ma’aunin wak’ar Larabawa ba, ko kuma su kwaikwayi muryar wak’ok’in Indiya. Wani lokaci sukan aro wasu kalmomin Turanci su saka, maimakon na Larabci da aka saba da shi. Wasu mawak’an kuma ba su cika kula da mabud’in wak’a ko marufinta ba, wato ambaton sunan Allah a farko ko a k’arshe.

Rubutattun wak’ok’in Hausa sun k’ara bunk’asa a k’arni na ashirin. Wannan ya auku ne saboda canje-canjen zamani da k’arnin  ya zo da su. Bungud’u da Maikwari (2016)

3.0.7 Wak’ok’in K’arni Na Ashirin Da ‘Daya (K’21)


Masu iya magana sun ce “ zamani bak’o ne” don haka sai mu duba mu gani shin ko mutanen da suka yi wallafe-wallafe a wancan zamani su ne ke yi har yau koko akwai wasu da ke yi a yanzu haka? Tambayar kenan da za a amsa a wannan sashe.

Amsar ita ce a’a, a yau ma muna da marubuta da suke yi mana rubutun wak’ok’inmu dai dai da zamaninmu na yau. Babu shakka wannan lokaci shi ne k’arni na ashirin da d’aya (K’21), kuma akwai marubuta da yawa da suke rubuta wak’a a cikinsa. Ko da yake ba a iya cewa ga yawansu amma mun san da akwai: shaihin Malami Aliyu Muhammadu Bunza, Kaftin Suru Ummaru ‘Da (RTD), Shaihin Malami Haruna Abdullahi Birniwa, Shaihin Malami Abdullahi Bayero Yahya, malam Musa Maidawa (Surus), Malam Bello Sa’id, Malam Umar Balarabe da malam Zainu Zubairu Bungud’u da dai sauransu. Su wad’annan malamai marubuta wak’ok’in Hausa ne kuma sukan samu jigo na musamman su rubuta wak’a don shi, sukan rubuta wak’ok’insu ne tare da yin amfani da salon da wad’anda suka gabace su suka yi da shi. Wannan ya nuna cewa dai ko da yake rubutacciyar wak’a ta samo asali daga wak’ok’in Larabawa kuma ana amfani da ma’auni a wak’ok’in na Larabawa da ma wasu na Hausawa da aka yi koyi da na Larabawan, sai ga shi tun a k’arni na ashirin an fara fatali da wad’annan k’a’idoji sai dai a tsara wak’a ta fato daidai da yadda ake buk’ata kuma ta isar da sak’o ga al’umma. An fad’a a baya cikin k’arni na ashirin cewa mawallafan wannan k’arnin suna amfani da Bahaushe kari ko ma wani lokaci su kwaikwayi muryar Indiya su yi wak’a da ita kuma wak’ar ta yi dad’i. A wannan k’arnin ma akan yi haka kuma kwalliyar ta biya kud’in sabulu. Da yake zamanin ya canza wasu mutane da suka d’auki wak’ar sana’a suma sukan rubuta kuma har su yi amfani da kayan kid’a na zamani su rera. Amma fa galibin wad’annan mawak’an sun fi yin wak’ok’in ga jigon siyasa da aure da yabo da soyayya da dai sauran wasu abub uwa da suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum.

Galibi su wad’annan mutane da muka zayyana sunayensu a sama ba sukan yi wak’ok’i don siyasa ba ko yabon wani don sana’a. A’a sai dai sukan yi wak’ok’i ne a kan wani jigo da suka ga ya kamata su yi wak’a don su isar da sak’onsu ga jama’a. Misali idan muka dubi wak’ok’in Aliyu Muhammad Bunza za mu ga cewa akwai na ilimi, wasik’u, marsiyya addini, gargad’i fad’akarwa da sauransu. Bungud’a da Maikwari (2016)

3.0.8 Kammalawar Babi


A wannan babi mun kawo ma’anar wak’a da bayani a kan Rubutacciyar wak’a yayin da har muka kawo ma’anoni daban-daban daga masana da manazarta wak’ok’in Hausa. mun kuma yitsokaci a kan tarihin rubutacciyar wak’a yayin da muka ce ta samu tun a k’arni na 18 kuma tana samun bunk’asa har wannan k’arni na 21.

 

 

 

 

 

Babi Na Hud’u


4.0. Gabatarwa


Wannan babin ya k’unshi, Tak’aitaccen Tarihin Marubucin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya wato Alhaji Ak’ilu Aliyu. Kuma a cikinsa ne za a d’an yi bayanin muhimman sassan nazarin wak’a kamar su Jigo, Salo da dai makamantansu. nazarin wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya zai biyo baya da bayanan share fage da jigon wak’ar da zubi da tsari na wak’ar da salo da sarrafa harshe, sai mu biyo da Kimar Jimilla.

4.0.1 Bayanan Share Fage


A nan bincike zai yi k’ok’arin fito da tarihin rayuwar marubuci da kuma na wak’ar da ake nazari a kai kamar dai yadda za a gani a yanzu.

4.0.1.1 Tsokaci a kan Marubucin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya


Wak’ar Daddad’an dad’i saniya dai Ak’ilu Aliyu ne ya rubuta ta, kuma shi Ak’ilu Aliyu sananne ne, kuma shi asalinsa mutumin k’asar Kabi ne a k’aramar hukumar Jega ta jihar Kebbi. An haife shi a Unguwar K’aurar Lailai a Jega ta jihar Kebbi a cikin watan Muharram, a shekarar 1918. Ya fara karatun Alk’ura’ani a wajen Mahaifinsa wanda aka fi sani da malam Aliyu Madaha saboda shi ma’abucin Ishiriniya ne. bayan rasuwarsa a lokacin Ak’ilu yana d’an shekara kamar sha biyu, sai ya ci gaba da d’aukar karatu a wajen su Alhaji Mukhtar Tsoho da Mal. Muhammad d’an Takusa da Mal. Ban-Allah da kuma mal. Abdulmumini, inda ya fara karatun ilimi yana da kamar shekara sha biyar, ya fara zuwa Kano. Yana zuwa neman ilimi da sana’a yana komawa, har dai ya k’ware da zama sosai a Kano d’in, Babban malaminsa na ilimi shi ne Mal. Mahmuda da malam Salga shaihinsu na d’arik’ar Tujjaniyya kuwa shi ne malam Salga. A zaman Ak’ilu a Borno inda ya yi shekara ashirin da uku, ya yi siyasa da k’arfinsa da hazak’arsa. Haka kuma ya ci gaba da neman ilimi da yad’a shi har ya rasu.

Ta fannin wak’a kuwa Ak’ilu tun yana yaro ya fara tsara ta, kusan ko yaushe kuwa a cikin halin k’ulla ta yake shi kansa bai san iyakar wak’ok’in da ya shirya ba, saboda yawa sun ‘bace amma ba su kasa dubu.

Bayanin da kuma samu a cikin littafinsa na Fasaha Ak’iliyya ya nuna muna cewa, Alhaji Ak’ilu Aliyu ya shahara wajen shirya wak’a, haka kuma an dad’e da sanin wak’ok’insa, daga na addini  da na gargad’i har zuwa na siyasa don kuwa an buga wasu a littafi, wad’ansu kuma a jaridu. Sau da yawa a kan ji shi a gidajen rediyo wasu wak’ok’in kuma akan ji su a fayafan garmaho. A lokacin da yana raye yakan shira wak’a musamman idan an gayyace shi a wani babban taro. Ak’ilu ba ‘boyayye ba ne a wajen ma’abuta karatun wak’ok’i na zamani wato rubutattu.

Ita kuma wannan wak’ar ta Daddad’an Dad’i Saniya tana daga cikin wak’ok’insa na sha’awa, kuma ya yi ta ne saboda lura da irin d’imbin amfanin da ke tattare da saniya.

4.0.2 Muhimman Sassan Nazarin Wak’a


Nazarin wak’a wani ‘bangare ne da ya k’unshi wasu abubuwa da suka k’unshi Jigo, salo da zubi da tsari. Yanzu dai ga bayanan wasu daga cikinsu.

4.0.2.1 Jigo


Dangane da ma’anar jigo kuwa masana da manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu ga dai abin da wasu suke cewa.

‘Dangambo (2007:12) Abin da ake nufi da jigo shi ne sak’o, manufa ko abinda wak’a ta k’unsa, wato abin da take magana a kai.

Jigo a fagen adabi yana nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa Jigo shi ne irin sak’on da marubuci ke son sadarwa ga jama’a kuma duk wani salo da tsari ko wata dabara da marubuci zai yi amfani da su, zai yi hakan ne da nufin isar da sak’onsa ga jama’a. Sar’bi, (2007:71).

4.0.2.2 Nau’o’in Jigo.


             Masana da manazarta da dama sun bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, kamar dai yadda Bunza (2009) da sar’bi (2007) suka bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, wato ‘Babban jigo’ da ‘k’aramin jigo’. Yanzu bari mu zo da su d’aya bayan d’aya don ganin yadda abin yake.

4.0.2.2.1 Babban Jigo.


Babban jigo shi ne abin da mawak’i ko marubuci ya sa gaba gadan- gadan domin ya fed’e shi a gane shi sosai. Bunza (2009: 63).

Galibi shi babban jigo mawak’i ko marubuci ya kan fad’a a cikin wak’arsa ko kuma tun a sunan wak’ar ya zan yana tafiya da sak’on wannan wak’ar, idan kuma mawak’i ko marubuci bai fad’a a wak’arsa ba kuma ba a gane a sunan wak’ar ba, to sai mai nazari ya yi k’ok’arin yin anfani da kalmomin fannu da aka gina wak’ar da su wad’anda za ka samu k’ananan jigogin.

Marubuta wak’ok’in Hausa wani lokaci a wasu baitoci suna fad’in jigogin wak’ok’insu. Wannan ko shakka babu haka abin yake, idan muka dubi wak’ar K’alubale Ta Ak’ilu Aliyu, inda a baiti na tara ya ce:

Ina magana kan ilmu ne,

                   A nan k’unshinsa na walwale.

4.0.2.2.2 K’aramin Jigo.


K’aramin jigo ya sa’ba wa babban jigo ta kowace fuska. Na farko dai abin da ya kyautu a kula shi ne, k’armin jigo d’a ne ga babban jigo, domin babban jigo ke haifar da shi. Haka kuma ba don k’ananan jigogi ba da babban jigo bai fito fili sosai aka ganshi ba. Duk wata wak’a da aka gina wani babban jigo d’aya, za a samu wasu k’ananan da yawa da za su mara wa babban jigon baya, domin K’awata shi da k’ara fayyace shi sosai. Bunza (2009:64)

Idan aka ce k’ananan jigogi dai to, anan nufin tuballan da suka gina babban jigo, su wad’annan tuballan sun danganta daga wak’a zuwa wak’a, ma’ana dai kowace wak’a da irin nata tuballai da suka samar da jigonta. A wasu wak’ok’i za ka ji an samar da yabo, kirari, siyasa,aminci shaida, sha’awa rok’o, tuba, ilimi da dai sauransu. Misali idan muka d’auki wak’ar Mu’azu Had’ejia ta Yabon Ubangiji za mu ga cewa k’ananan Jigogin sune suka had’u suka samar da Babban jigo.

 

 

4.0.3 Wasu Daga Cikin Jigogin Rubutacciyar Wak’a.


Daga cikin ire-iren jigogin da aka rubuta wak’ok’i a kansu musamman a cikin k’arni na ashiri da kuma wannan k’arni da muke ciki wato k’arni na ashirin da d’aya, sun had’a da:

 • Jigon yabo.

 • Jigon fad’akarwa.

 • Jigon gargad’i.

 • Jigon ilimi.

 • Jigon sha’awa.

 • Jigon soyayya.

 • Jigon siyasa.

 • Da dai sauransu.


Wad’annan ba su kad’ai ba ne amma saboda tsabar yawan da ke gare su ba za a samu damar kawosu da yawa ba saboda yawansu ya wuce tsammani.

4.0.4 Salo


Masana da manazarta da yawa sun yi tsokaci dangane da salo ga dai abin da wasu masana suke cewa:

Shaihin malami Yahya(2005:1) ya bayyana muna cewa, salo a cikin nazarin wak’a ko adabi gaba d’aya wani kandami ne da ba a ganin k’arshensa. Gwanin iyo shi kansa sai dai ya nutso har Allah ya gajiyar da shi, amma ba don ya k’ure ba to balle wanda yake shi bami ne.

Malamai da masana sun bayar da ma’anar salo ta hanyoyi daban – daban duk da yake abu d’aya suka fuskanta.

Sa’idu Muh’d Gusau a tashi fahimtar ya ce:

“Salo shi ne hanyar da aka bi aka nuna gwaninta da dabaru a cikin furuci ko rubutu. Kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da za’bar abubuwa da suka dace game da abin da yake son bayyanawa. Daga nan ne za a fahimci salon mai sauk’i ne ko tsauri, mai tsauri ko mai dad’i ne da armashi ko mai kashe jiki maras karsashi da sauransu” Gusau (1993).

Akwai nau’o’in salo da yawa kuma ba za iya kawo su ba a cikin wannan kundin binciken sai dai za a d’an yi bayanin wasu da bincike ya ci karo da su a cikin nazarin wannan wak’ar.

 

4.0.5 Nazarin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya


Wak’ar daddad’an dad’i saniya wak’a ce da Alhaji Ak’ilu Aliyu ya rubuta. Wannan bincike zai yi k’ok’arin fito da abubuwan nazari ta hanyar yin taken wannan wak’a. Abubuwan da za a nazarta sun had’a da: Bayanan share fage da jigon wak’ar da k’unshiyarsa da zubi da tsarin wak’ar da kuma salo da sarrafa harshen wak’ar da kimar jimilla.

4.0.5.1 Jigon Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya


A fagen nazari jigon wak’a na nufin sak’o ko manufar da wak’a take d’auke da ita wadda ta rasta ta daga farko har zuwa k’arshe.

Babban sak’on wannan wak’a shi ne bayani a kan muhimmanci da amfanin da ke tattare da saniya. Kuma muhallin wannan jigo ya fito k’arara ne a baiti na hud’u na wak’ar, inda mawak’in ke cewa:

Amma a tak’aice a dan mu san,

                   ‘Dinbin amfanin saniya.”

Wannan baitin ya bayyana jigon wak’ar k’arara inda yake cewa a san d’imbin amfanin saniya wannan ko shakka babu abin da marubucin ya mayar da hankali shi ne “Amfanin Saniya”. Sau da yawa Hausawa na fad’in “nagge dad’i goma” amma shi Alhaji Ak’ilu ganin yake yi dad’in ya fi goma. Amma za mu gani a gaba.

4.0.5.2 Gajerta Jigon Daddad’an Dad’i Saniya


Ta fuskar gajerta jigon wak’ar kuwa ana iya cewa wannan wak’a tana bisa ga tartibinta Shaihin malami ‘Dangambo (2007:15) ya ce, “A nan wurin za a bi wak’a a tak’aice baiti bayan baiti ana tak’aita abin da mawak’i yake fad’a. Za a yi haka ba tare da yin sharhi, bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Misali ana iya cewa a baiti na 1-3 ya k’unshi yabon farawa, baiti na 4-7 ya k’unshi gabatar da Jigo.

Idan aka yi la’akari da abin da magabata suka fad’a dangane da Gajerce Jigo za a ga cewa, wannan wurin yana buk’atar a fito da hoton bayanin wak’ar a tak’aice ana iya d’aukar d’iya ko baitoci na wak’ar rukuni-rukuni a fito da muhimman abubuwan da take magana a kai.

        Anan wurin za a bi wak’a a tak’aice baiti bayan baiti ana tak’aita abin da marubucin wak’ar ya rubuta/fad’a. Za a yi haka ba tare da yin sharhi ko bayyana ra’ayi ko wani dogon bayani ba. Ga dai yadda abin yake a wannan wak’ar ta Daddad’an Dad’i Saniya:

Baiti na 1-3 – Ambaton Ubangiji

Baiti na 4 -      Furucin k’wayar jigon wak’ar

Baiti na 5-9 – Muhawara a kan cewa nagge dad’i goma ce kawai

Baiti na 10-27 – lissafo abubuwan amfani daga jikin saniya

Baiti na 29-31 – Tunani a kan wani abu maras amfani daga saniya.

Baiti na 32-39 – Amfani da tambaya da amsa a kan saniya

Baiti na 40 -     Sunan wak’a

Baiti na 41- 57 – Yabo da nuna fifikon saniya a kan sauran dabbobi ta fuskar daraja

Baiti na 58-65 – Nubayi’ar sauran dabbobi zuwa ga saniya

Baiti na 66-67 – jawabin dakatawa da ambaton sunan wanda ya yi wak’a.

4.0.5.3 Warwarar Jigon Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya


Anan za a yi sharhi ne kan Jigo gaba d’ayansa. Za a duba shi dangane da jawaban jigo, da kuma abin da wak’ar ta fad’a a tak’aice. To amma muhimmin abin shi ne za a duba lungu-lungu na wak’ar dangane da jigo tare da k’arin bayani daga dukkannin abin da za a iya danganta wak’ar da shi. Misali ana iya kawo k’arin bayani don kafa hujja da misalai daga Alk’ur’ani, Hadisi, littattafai, muk’alu, da ra’ayoyi iri daban-daban da dai sauran bayanai da za su taimaka wajen gane abin da wak’ar ta k’unsa da inda aka dosa. ‘Dangambo, (2007:16)

Mabud’in Wak’ar Daddad’an dad’i saniya

Marubucin ya yi amfani da salon bud’e wak’a na rubutacciyar wak’a wato, farawa da sunan Allah ko yabo ga Mafificin halitta ko rok’o ga Allah (SWA). Ga dai abin da yake cewa:

Ya Mai ni’ima Mayawaicia,

          Ya Mai K’udura Makad’aiciya.

“Haske da basira naKa ne,

          Ya Rabbu ka bud’an zuciya.

Bayan da marubucin ya bud’e wak’arsa da ambaton allah ya kuma cigaba da furucin k’wayar jigonsa a baiti na hud’u. Ga dai abin da yake cewa:

Amma a tak’aice a dan mu san,

                   ‘Dinbin amfanin saniya.”

Sai a gaba kuma ya kawo muhawara a kan cewar da Hausawa ke yi Wai “Nagge dad’i goma” shi a nasa gani wannan zancen ba haka yake ba. Yana ganin cewa dad’in nagge ya ma fi a k’irga kuma koda an k’irga ba za a kasa d’ari biyu ba. Ga dai abin da yake fad’a a cikin baiti na biyar zuwa tara. (5-9) misali:

Amma a tak’aice a dan mu san,

                   ‘Dinbin amfanin saniya.”

          sun ce mata dad’i goma wai,

                   Wannan magana na dai jiya.”

          Wato maganar na ji ta ne,

                   Kar’ba ta ta sai na waiwaya.

          A’a kar’bar ta da lokaci,

                   Sai na juya na waiwaya.

          Ba goma ba ma, wane d’ari,

                   Metin suke har da guda d’aya.

          Wa za shi iya shi k’ididdige?

                   Daddad’an dad’in saniya.

Da jin wannan ka san Alhaji Ak’ilu yana son ya jefa muhawara cikin al’umma ne.

Domin marubucin ya kafa hujja a kan maganarsa da ya yi kan cewa amfani saniya ko dad’in saniya ya fi gaban yadda Hausawa ke adon harshe da cewa wai “Nagge dad’i goma” sai ya ya shiga lisafo kad’an daga cikin abubuwan amfanin jama’a da ke tattare da saniya. Wad’annan baitoci za su zame muna hujja a kan abin da marubucin wak’ar ke fad’a:

          Kin d’au kaya, kin d’au mutum,

                   Da abinci mutum ya rataya.

          Kallonta shi sanya farinciki,

          ...........................................

Madara, kindirm, dak’k’ashi,

                   Kangar da cikui daga saniya.

          Kassanta ana alli da su,

                   Ya kyautu a nan in waiwaya.

          Kashinta ana shafe da shi,

                   Lasonmu na da Nijeriya.

4.0.6 Salo Da Sarrafa Harshe a Wak’a Daddad’an Dad’i Saniya


Kamar da yadda Gusau (1993). ya fad’a cewa salo shi ne hanyar da aka bi aka nuna gwaninta da dabaru a cikin furuci ko rubutu. Kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da za’bar abubuwa da suka dace game da abin da yake son bayyanawa. Daga nan ne za a fahimci salon mai sauk’i ne ko tsauri, mai tsauri ko mai dad’i ne da armashi ko mai kashe jiki maras karsashi da sauransu”

Salon Mutuntarwa:

Wannan naiin salo ya k’unshi a d’auki wani abu da ba mutum ba a ba shi sifa ta mutum a cikin wak’a misali:

Taure ya ce a sanar da ke,

                   Sak’on akuya da na tunkiya.

          Sun mik’a wuya sun sallama,

                   Cewa a nad’a ki sarauniya.

          Sun sa hannu da guda-guda,

                   Sun lamunce daga zuciya.

          Rago tuni shi ya sallama,

                   ‘Dauke shi jakada saniya.

Salon Kambama:

Wannan salo nau’in salo ne dake kambama abu ana kururuta shi ana kai shi inda bai kai ba. Ak’ilu ya yi amfani da wannan nau’in salo inda yake cewa:

Dabbar da ja gaba da ke,

                   Ta d’au wahala matsananciya.

          Gurbin riba sai fad’uwa,

                   Sai rarraba hajar mujiya.

4.0.7 Kammalawar Babi


A wannan babin mun yi bayanin Jigo, Salo, Warwarar Jigo da Gajerce shi. Mun kuma kawo tak’aitaccen tarihin mawallafi inda muka ce an haife shi a watan Al’umaharram 1918. Baya ga ma’anonin jigo da salo da muka kawo mun kuma nazarci wak’ar da su kuma mun kawo wasu baitoci don kafa hujja.

 

 

Babi Na Biyar.


5.0 Jawabin Kammalawa


Muna godiya ga Allah Subhanahu Wata’ala da ya nuna muna k’arshen wannan aikin mai taken “Nazarin Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya ta Alhaji Ak’ilu Aliyu”

Kamar yadda aka sani a babi na d’aya mun yi gabatarwa, muka biyo da manufar bincike inda muka ce, za mu yi nazara k’wak’waf ga wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya ta Alhaji Ak’ilu Aliyu. Mun kuma bayyana muhallin da za mu gudanar da wannan bincike inda har muka ce, za mu tak’aita wannan bincike a fagen adabi kuma na zamani. Binciken ya bayyana hanyoyin da zai bi wajen tattaro bayanai da za su taimaka domin gudanar da wannan aikin. Sai kuma Matsalolin da suka taso da kuma wad’anda aka fuskanta.

Mun waiwayi baya don ganin ayyukan da suka gabata a babi na biyu inda muka hango wasu ayyuka na magabata da suke da alak’a da namu aikin mun d’auki na d’auka kuma mun aje wad’anda ba su da alak’a da namu aikin. Mun kawo zubi da tsarin wannan bincike duk a cikin wannan babi na biyu.

A babi na uku kuwa mun kawo ma’anar wak’a da bayani a kan Rubutacciyar wak’a yayin da har muka kawo ma’anoni daban-daban daga masana da manazarta wak’ok’in Hausa. mun kuma yitsokaci a kan tarihin rubutacciyar wak’a yayin da muka ce ta samu tun a k’arni na 18 kuma tana samun bunk’asa har wannan k’arni na 21.

A babi na hud’u mun yi bayanin Jigo, Salo, Warwarar Jigo da Gajerce shi. Mun kuma kawo tak’aitaccen tarihin mawallafi inda muka ce an haife shi a watan Al’umaharram 1918. Baya ga ma’anonin jigo da salo da muka kawo mun kuma nazarci wak’ar da su kuma mun kawo wasu baitoci don kafa hujja.

Babi na biyar kuwa nan ne muke nad’e tabarmar wannan bincike kuma za mu bayar da shawarwari ga mutane daban-daban da musamman wad’anda suka samu karanta wannan aiki namu.

5.0.1 Shawarwari


Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu d’alibai shawara su mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin k’ok’ari gwargwadon hali, su kasance masu gwazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to su yi k’ok’ari su d’ora daga inda muka tsaya na wannan bincike.


Manazarta.


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Ratayen Wak’ar Daddad’an Dad’i Saniya


Ya Mai ni’ima Mayawaicia,

Ya Mai K’udura Makad’aiciya.

“Haske da basira naKa ne,

Ya Rabbu ka bud’an zuciya.

Domin in yi wak’a, ‘yar kad’an,

Mai ‘yar magana mashahuriya.   

sun ce mata dad’i goma wai,

Wannan magana na dai jiya.”

Wato maganar na ji ta ne,

Kar’ba ta ta sai na waiwaya.

A’a kar’bar ta da lokaci,

Sai na juya na waiwaya.

Ba goma ba ma, wane d’ari,

Metin suke har da guda d’aya.

Wa za shi iya shi k’ididdige?

Daddad’an dad’in saniya.

Nan dai a tak’aice guda d’arin,

Zan zo muku d’aid’aya.

To sai mu yi tsit domin mu ji,

Zan fara bayanin saniya.

Mamaki ne ta tu’ajjibi,

A cikin sha’anonin saniya.

Tirk’ashi! O’Oi wane mutum,

Sambarka d’au duka saniya.

Kin d’au kaya, kin d’au mutum,

Da abinci mutum ya rataya.

Kallonta shi sanya farinciki,

Kukanta shi sanyaya zuciya.

Shafarta shi sa maka walwala,

Dubanta idonka shi sanyaya.

Ba a samu guda ba, na yasuwa,

Daga kowane sashen saniya.

Madara, kindirm, dak’k’ashi,

Kangar da cikui daga saniya.

Kassanta ana alli da su,

Ya kyautu a nan in waiwaya.

Kashinta ana shafe da shi,

Lasonmu na da Nijeriya.

K’irginta ana wasaki da shi,

Mun san haka duk Nijeriya.

Har gobe ana kiri da shi,

Da gare shi ake bulaliya.

Na lura ana waga da shi,

Da gare ake yin tsirkiya.

Shi ke d’aure karaga da shi,

Tsani, barho da takubiya.

Shi ke yin takalma da shi,

‘Dwak’k’wara k’irgin saniya.

Na lura da shi ke yin kube,

Na wuk’a, barho da takobiya.

Ka tuna fa da shi janjami,

Sai mai girma kan rataya.

Ba za na yawaita magangannu,

Ga ‘yar sa’at magajarciya.

Ba nuna gadara ko isa,

Ko k’asaita matsananciya.

Daga nan ya zuwa can ko’ina,

A cikin duka sassan saniya.

Na hanga zaune a hanlaki,

Kuma na maka duba natsaya.

Wai ko zan gano na yasuwa,

Wani d’an gutsure daga saniya.

Anya! Kuwa a same shi dai?

Amsa na ke so na tambaya.

Shin ko ko akwai abu ne daban?

Marashin fa’ida daga saniya.

In dai da akwai a fad’a mu ji,

Daga sa ya zuwa kan saniya.

Guzuma ta zamo ko dagwali?

Ko karsana ce ma sauraya.

Amsa: a’a ai babu shi,

Abu yasasshe daga saniya.

Wannan kuwa ta gamsar da ni,

Amsa ke nan matak’aiciya.

Mai haske ga ta wartsake,

Har yau mai dad’ad’a zuciya.

Wak’ar sunan da na bata shi,

Daddad’an dad’i saniya.

Wannan jin dad’i ya isa,

Daga kowane sashen duniya.

Kar wai ku cire gefe guda,

Daga kowane ‘barin saniya.

Me za mu kwatanta ne da shi?

Ga misali sai dai lafiya.

Wannan ita ce duk kan gaba,

Daga duk jin dad’in duniya.

Amma a wadata kowace,

Daga kowane fannin duniya

Jama’u-jama’u duk an had’u,

Cewa dai babu ya saniya.

Fifiko nata yana gaba,

Ga na dabbobi duka saniya.

Yai nisa babu tara da shi,

Ko sun yi gudu sun garzaya.

Ba za fa su shawo kansa ba,

Ko sun zaga sun kewaya.

Kai ban zaci sa riske shi ba,

Ko sun tafiya matsananciya.

Abu ne mawuyaci dank’ari!

Har yanzu wayar mawuyaciya.

Gaba dai, gaba dai, gaba dai, gaba,

Gaba nagge da aiki saniya.

Ja al’amarinki mad’aukaki,

Gaba dai dai ba baya ba saniya.

Ja dai sha’aninki na arziki,

Ke ba ki shiga sha’anin tsiya.

Madalla-madalla da ke,

Tsarinki da kyawo saniya.

Sannunki na ce na gai da ke,

Ni na yabi aikin saniya.

Girman daraja, girman isa,

Sannan darajar mayawaiciya.

Taure ya ce a sanar da ke,

Sak’on akuya da na tunkiya.

Sun mik’a wuya sun sallama,

Cewa a nad’a ki sarauniya.

Sun sa hannu da guda-guda,

Sun lamunce daga zuciya.

Rago tuni shi ya sallama,

‘Dauke shi jakada saniya.

Dabbar da ja gaba da ke,

Ta d’au wahala matsananciya.

Gurbin riba sai fad’uwa,

Sai rarraba hajar mujiya.

Tsini aka je nema gaba,

Tun da ta gagara tun jiya.

Wannan magana ba ta fad’i ba,

Wa za ya gaya mini kai tsaye?

Jama’a daga nan zan dakata,

In sanya alama in tsaya.

Ni naku Ak’ilu Aliyu ne,

Amsa a wajen mai tambaya.

 

Post a Comment

1 Comments

 1. A gaskiya na ji dadin wannan kundi sosai domin kuwa ya zo min a dai-dai lokacin da nake cikin da muradin sa. Allah ubangiji ya kara lafiya da albarka ameen ya Allah

  ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.