https://www.amsoshi.com/about-us/

 

 

 

 

NA
FATIMA ISAH RAHAMA


SAMIRA SHEHU HAMZA


LUBABATU ALIYU


 SASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA K’ERE-K’ERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA.


OKTOBA, 2017


https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

Babi na Biyu


2.01. Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.


Kamar yadda muka riga muka sani cewa waiwaye shi ne adon tafiya, to ko a wannan aiki waiwayen zai taimaka matuk’a, don haka za a waiwayi baya mu ga irin ayyukan da suka gabata wad’anda suke da dangantaka da wannan aikin..

Domin yi wa wannan aikin kwalliya za a binciki littattafai da kundaye da muk’alu da dai sauran wasu ayyuka da suka shafi wannan.

Sar’bi (2007), ya rubuta littafi mai suna “Nazarin Wak’ar Hausa” wannan marubuci ya rubuta littafin ne domin masu nazarin wak’ok’in Hausa musamman rubutattu. A cikin wannan littafi nasa ya yi magana a kan jigo, salo zubi da tsari, nau’o’in rubutacciyar wak’a da dai sauransu.

Wannan aiki na Sar’bi yana da alak’a da namu aikin saboda ya yitsokaci a kan wak’ar zamani yayin da muma namu aikin yana magana a kan wak’ok’in zamani. Inda kuma muka sha bamban da shi shi ne, shi Sar’bi ya mayar da hankali ne a kan muhimman hanyoyin da ake bi wajen nazarin wak’a. Mu kuma wad’annan hanyoyin su muka bi muka zak’ulo adon harshe a cikin wak’ar K’alubale.

Bunza (2009), ya rubuta wani littafi mai suna “Narambad’a” wannan littafi da wannan masani Al’dar Hausa ya rubuta littafi ne wanda ya tsara shi bisa ga tsari na babi-babi har babi goma sha biyu. A babi na d’aya masanin ya kawo jigogin wak’ok’in Narambad’a, a k’ark’ashi wannan babin ya fara da gabatarwa da da asalin kalmar jogo da rabe-raben jigo da babban jigo da k’aramin jigo da yadda ake neman sarauta da yadda sarauta take da nad’in sarauta.

A cikin babi na biyu akwai masarauta a wak’ok’in Narambad’a, a babi na uku ya kawo sarki a wak’ok’in Narambad’a, a babin na hud’u ya kawo fada a wak’ok’in Narambad’a, a babi na biyar kuwa ya kawo k’ananan jigogin wak’ok’in Sarauta. A babi da shidda akwai ke’ba’b’bun k’ananan jigogin sarauta, a babi na bakwai nan ne ya kawo salon wak’ok’in Ibrahim Narambad’a, a babi na takwas ya ba da falsafar wak’ok’in Ibrahim Narambad’a, a babi na tara ya zo da Tussan wak’ok’in Narambad’a, a babi na goma ya yi bayanin fashin bak’in Bakamdamiya, a babi na gaba sai ya rufe da kammalawa.

Wannan littafi da wannan masani ya rubuta ya haskaka sosai wajen samu dubarar da za a gina wannan aikin ya k’ayatar. Alak’arsa da wannan aikin ita ce, shi yana kallon wak’ok’in Narambad’a yana nazarinsu mu kuma muna nazarin wak’ar K’alubale kuma za mu fito da salon amfani da adon harshe.

Bungud’u da Maikwari (2014) sun rubuta wata muk’ala mai taken “Birgima Cikin Wak’ar Mu’azu Had’eja: Nazarin Jigon Wak’ar Yabon Ubangiji” malaman sun ta’bo ma’anar jigo da nau’o’isa da yadda ake gane jigo da kuma yadda ake warware shi a cikin wak’a.

Wannan aiki na su Bungud’u ya taimaka ainun wajen samun damar gudanar da wannan aiki. Haka kuma idan aka duba za a ga cewa aikin yana da allak’a da namu aiki saboda dukkansu suna nazari na wak’a. Inda kuma aka sha bamban shi ne su su Bungud’u sun tak’aita nazarinsu ne a kan jigo, yayin da ni kuma ina kallo dukkan sassan nazarin wak’a gwargwado hali.

2.0.2 Salon Nazari Da Zubi Da Tsarinsa.


Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin mutum. Salo muhimmin abu ne a cikin labari ko jawabi, haka kuma duk aikin da aka gudanar ba cikin tsari ba to, ba zai cimma nasara ba. Don haka domin samun nasarar gudanar da wannan aikin cikin sauk’i, an yi amfani da salo mai sauk’i, mai jan hankalin mai karatu. An kuma yi amfani da za’ba’b’bun kalmomi masu sauk’in ma’ana saboda mai karatu ya ji sauk’in karantawa.

Haka kuma an yi amfani da gajeru da matsakaitan jimloli, sannan aka gudanar da bayanan d’aya bayan d’aya a cikin sakin layi mai sauk’in fahimta.

Aikin kamar yadda aka sani an zuba shi ne a kan babi-babi har zuwa babi biyar saboda a samar wa mai karatu sauk’i wajen nazari.

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

https://www.amsoshi.com/about-us/

 

 

 

Babi Na Uku.


3.0.1 Ma’anar Wak’a.


Masana da yawa sun ba da gudunmuwa wajen samar da ma’anar wak’a,. Ga wasu daga cikinsu:

Yahya ya ba da tasa ma’anar wak’a da cewa:

“Magana ce da ake shisshirya kalmominta cikin azanci, ta yadda wajen furta su ana iya amfani da kayan kid’a”. Yahya (1997).

Shi kuma ‘Dangambo (2007:) cewa ya yi:

“Muna iya cewa, wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti, d’ango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (k’afiya), da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

A wani aikin kuma Gusau cewa ya yi:

“Wak’ar baka fage ce wadda ake shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre, wad’anda za su zaburar da al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwa da za su ba da damar a cim ma ganga mai inganci. Wak’a bisa jimla, takan zama fitila wadda take haskaka rayuwar jama’a kuma take kare rayuwar al’umma daga sallacewa”  Gusau (2011).

Bungud’u (2014) kuma ya bayar da ma’anar wak’a kamar haka:

“Wak’a ta k’unshi wasu jerin hikimomi ne da a kan tsara domin su dad’ad’a zukatan masu saurare, inda a kan yi amfani da wata za’ba’b’biyar murya don rerawa, ana kuma yin amfani da za’ba’b’bun kalmomi domin fizgar hankalin jama’a ya dawo gare su da zimmar bin diddigin ma’anoni da manufofinsu.

3.0.2 Muhimman Sassan Nazarin Wak’a


Nazarin wak’a wani ‘bangare ne da ya k’unshi wasu abubuwa da suka k’unshi Jigo, salo da zubi da tsari. Yanzu dai ga bayanan wasu daga cikinsu.

3.0.2.1 Jigo

Dangane da ma’anar jigo kuwa masana da manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu ga dai abin da wasu suke cewa.

‘Dangambo (2007:12) Abin da ake nufi da jigo shi ne sak’o, manufa ko abinda wak’a ta k’unsa, wato abin da take magana a kai.

Jigo a fagen adabi yana nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa Jigo shi ne irin sak’on da marubuci ke son sadarwa ga jama’a kuma duk wani salo da tsari ko wata dabara da marubuci zai yi amfani da su, zai yi hakan ne da nufin isar da sak’onsa ga jama’a. Sar’bi, (2007:71).

3.0.2.2 Nau’o’in Jigo.

             Masana da manazarta da dama sun bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, kamar dai yadda Bunza (2009) da sar’bi (2007) suka bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, wato ‘Babban jigo’ da ‘k’aramin jigo’. Yanzu bari mu zo da su d’aya bayan d’aya don ganin yadda abin yake.

3.02.2.1 Babban Jigo.

Babban jigo shi ne abin da mawak’i ko marubuci ya sa gaba gadan- gadan domin ya fed’e shi a gane shi sosai. Bunza (2009: 63).

Galibi shi babban jigo mawak’i ko marubuci ya kan fad’a a cikin wak’arsa ko kuma tun a sunan wak’ar ya zan yana tafiya da sak’on wannan wak’ar, idan kuma mawak’i ko marubuci bai fad’a a wak’arsa ba kuma ba a gane a sunan wak’ar ba, to sai mai nazari ya yi k’ok’arin yin anfani da kalmomin fannu da aka gina wak’ar da su wad’anda za ka samu k’ananan jigogin.

Marubuta wak’ok’in Hausa wani lokaci a wasu baitoci suna fad’in jigogin wak’ok’insu. Wannan ko shakka babu haka abin yake, idan muka dubi wak’ar K’alubale Ta Ak’ilu Aliyu, inda a baiti na tara ya ce:

3.0.2.2.2 K’aramin Jigo.

K’aramin jigo ya sa’ba wa babban jigo ta kowace fuska. Na farko dai abin da ya kyautu a kula shi ne, k’armin jigo d’a ne ga babban jigo, domin babban jigo ke haifar da shi. Haka kuma ba don k’ananan jigogi ba da babban jigo bai fito fili sosai aka ganshi ba. Duk wata wak’a da aka gina wani babban jigo d’aya, za a samu wasu k’ananan da yawa da za su mara wa babban jigon baya, domin K’awata shi da k’ara fayyace shi sosai. Bunza (2009:64)

Idan aka ce k’ananan jigogi dai to, anan nufin tuballan da suka gina babban jigo, su wad’annan tuballan sun danganta daga wak’a zuwa wak’a, ma’ana dai kowace wak’a da irin nata tuballai da suka samar da jigonta. A wasu wak’ok’i za ka ji an samar da yabo, kirari, siyasa,aminci shaida, sha’awa rok’o, tuba, ilimi da dai sauransu. Misali idan muka d’auki wak’ar Mu’azu Had’ejia ta Yabon Ubangiji za mu ga cewa k’ananan Jigogin sune suka had’u suka samar da Babban jigo. Ga kad’an daga cikin k’ananan jigogin don ganin yadda abin yake.

 

 

 

3.0.3 Wasu Daga Cikin Jigogin Rubutacciyar Wak’a.


Daga cikin ire-iren jigogin da aka rubuta wak’ok’i a kansu musamman a cikin k’arni na ashiri da kuma wannan k’arni da muke ciki wato k’arni na ashirin da d’aya, sun had’a da:

 • Jigon yabo.

 • Jigon fad’akarwa.

 • Jigon gargad’i.

 • Jigon ilimi.

 • Jigon sha’awa.

 • Jigon soyayya.

 • Jigon siyasa.

 • Da dai sauransu.


Wad’annan ba su kad’ai ba ne amma saboda tsabar yawan da ke gare su ba za a samu damar kawosu da yawa ba saboda yawansu ya wuce tsammani. Amma dai ga wannan jigon don ya zama  misali domin k’awata wannan nazari.

Misali: Jigon Addini

A wannan jigo marubuta da dama suna rubutu a kansa tu ma kafin zuwan su Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Danfodiyo, kuma har a yau wasu suna rubutu a kansa. Marubuta na wannan k’arnin su ma sun bada tasu gudunmuwa wajen rubuta wak’ok’i na addina. Malam Zainu Zubairu Bungud’u wani fasihin sha’iri ya rubuta wak’a mai suna “Bisimillahi Farkon Zance” ga dai wasu daga cikin baitocinta.

 1. 1. Ga kaya muna Tarawa,


Ga karfi shina k’arewa.

 1.           Ga kaya kwarai sun nauyaya,


Ba gammo da zamu azawa.

 1. Ga mu cikin duhu ba haske,


Babu abin da zan ya dawa.

 1. Ga mu cikin ruwa ga kaya,


Ga gulbi shina kawo wa.

 1. Kowa ga mu kai yai zafi,


Kana ba wurin hutawa.

 1. Gulbi ya cike yai baye,


Amma ba ruwan kur’bawa.

 1. Kowa sai shina masha’a,


Babu hani bare horawa.

 1. Don ga zamani ya canza,


Ga k’arfinmu bai k’arawa.

 1.   Banna ta yawaita a fili,


Sai ‘yan k’alla ke ‘boyewa.

 1. Kunya ta k’aranta ga kowa,


Manya yara ba runtsewa.

 

3.0.4 Salo


Masana da manazarta da yawa sun yi tsokaci dangane da salo ga dai abin da wasu masana suke cewa:

Shaihin malami Yahya(2005:1) ya bayyana muna cewa, salo a cikin nazarin wak’a ko adabi gaba d’aya wani kandami ne da ba a ganin k’arshensa. Gwanin iyo shi kansa sai dai ya nutso har Allah ya gajiyar da shi, amma ba don ya k’ure ba to balle wanda yake shi bami ne.

Malamai da masana sun bayar da ma’anar salo ta hanyoyi daban – daban duk da yake abu d’aya suka fuskanta.

Sa’idu Muh’d Gusau a tashi fahimtar ya ce:

“Salo shi ne hanyar da aka bi aka nuna gwaninta da dabaru a cikin furuci ko rubutu. Kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da za’bar abubuwa da suka dace game da abin da yake son bayyanawa. Daga nan ne za a fahimci salon mai sauk’i ne ko tsauri, mai tsauri ko mai dad’i ne da armashi ko mai kashe jiki maras karsashi da sauransu” Gusau (1993).

Akwai nau’o’in salo da yawa kuma ba za iya kawo su ba a cikin wannan kundin binciken sai dai za a d’an yi bayanin wasu da bincike ya ci karo da su a cikin nazarin wannan wak’ar.

3.0.5 Salon Nassi


Salon nassi salo ne in da mawak’i ko marubuci kan yi amfani da wani sashe da ke cikin Alk’ur’ani ko Hadisin Manzon Allah (SWA), a cikin wak’arsa domin ya yi wa wak’arsa kwalliya ko ya ja hankalin mai saurare. A nan mai wak’ar zai iya ya kawo wani bayani wanda Allah (SWA) ya fad’a a cikin Alk’ur’ani ko kuma ya kawo wani bayani wanda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce. Waton abin da Hadisi ya zo da shi.

Misali: Mu’azu Had’ejia a wak’arsa ta yabon Ubangiji yana cewa:

 

Rayin da babu uwa gare shi bare uba,

Shi ba shi d’a balle a san jikanshi.

Shi ba a cewa wance ce mata tasa,

Balle ta je ta yi kwalkwasa a gaban shi.

Ba ya buk’atar k’wark’wara da makulliya,

Balle a samu Jakadiya a gidan shi.

Can suratul Ihilasi ga ayarsa nan,

Shi Wahidun K’aharu ba na biyun shi.

(Mu’azu Had’ejia: Wak’ar Yabon Ubangiji)

Wad’annan baitocin sun bayyana a cikin Alk’ur’ani Maigirma Allah ya fad’a muna da kansa cewa shi kad’ai yake baya da abokin tarayya bai da uwa, bai da uba, bai da d’a, ko d’iya, ko jika, ko mata. Kamar dai yadda ya zo a cikin (Suratul Ikhlas).

Ita wannan wak’a ba wak’a ce da aka yi ta don sha’awa ba balle a ga wasu salailai da suka danganci Siffance da kamance da sauransu. A wannan bincike ya zama dole mu yi taka tsantsan kar mu shiga hurumin da zai keta haddi.

3.0.6 Adon Harshe


Adon harshe na nufin karkatar da wani zance daga sifarsa ta asali zuwa wata sifa ta daban amma yin hakan ya kasance ta hanyar amfani da kwalliya ko tamka ko mutuntarwa ko k’arangiya ko almci ko kuma jirwaye. (Shiply: 1970).

Ga dukkan alamu dai Adon Harshe ya k’unshi dukkan salailan da muke da su. Kasancewar salo a matsayin gishirin kowane rubutu da kuma zantutuka ya sa muka kalle shi a matsayin adon. Adon Harshe dai kamar yadda L.M. Amin (2014) ya ruwaito daga Shiply (1970) cewa karkatar da wani zance daga sifarsa ta asali zuwa wata sifa ta daban amma yin hakan ya kasance ta hanyar amfani da kwalliya ko tamka ko mutuntarwa ko k’arangiya ko almci ko kuma jirwaye. Wannan ya fito k’arara cewa kenan adon harshe shi ne salo.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

https://www.amsoshi.com/2018/06/15/harshe-da-adabi-adon-harshe-a-cikin-wakar-kalubale-ta-alhaji-akilu-aliyu-2/