https://www.amsoshi.com/about-us/

 

NA
FATIMA ISAH RAHAMA


SAMIRA SHEHU HAMZA


LUBABATU ALIYUSASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA K’ERE-K’ERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA.
OKTOBA, 2017


https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Babi Na ‘Daya


1.0.1Gabatarwa


Wannan aiki mai taken “Harshe da Adabi: Amfani da Salon Adon Harshe a Wak’ar ‘K’alubale’ Ta Ak’ilu Aliyu” za a gudanar da shi ne a matsayin aikin bincike da za a gudanar domin samun takardar shaidar malanta wato (N.C.E).

Domin samun damar gudanar da wannan aikin za a karkasa wannan kundin kamar yadda tsarin gudanar da bincike na wannan sashe da ke wannan makaranta ya tanada wato bisa ga tsari na babi-babi.

A babi na farko dai za a kawo bayanai ne bayan mun yi gabatarwa ta gaba d’aya, a kan Yanayin Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar da Bincike tare da Matsalolin Da Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta,

Yayin da a babi na biyu kuwa, kamar yadda aka saba za mu waiwayi baya don ganin ayyukan magabata tare da yin tsokaci a kan wad’anda suka samu. Salo da Zubi da Tsarin wannan bincike zai biyo baya duk a cikin wannan babin.

Babi na uku zai k’unshi, ma’anar Wak’a, Muhimmancin Wak’a, rabe-raben wak’ok’in zamani, ma’anar jigo, kashe-kashensa, ma’anar salo, wasu daga cikin kashe-kashen salon.

A babi na hud’u kuwa nan ne za a yi nazarin wak’ar tare da fito da salon adon harshe da wak’ar ta k’unsa da jigonta babba da k’ananan jigogin tare da warwarar jigon wak’ar, da kuma kawo wasu baitoci domin kafa hujja.

Babi na biyar kamar yadda aka sani a nan ne za a kammala wannan bincike ta hanyar yin jawabin kammalawa da kuma bayar da wasu shawarwari.

1.02. Yanayin Bincike


Wannan aikin yana da zimmar yi wa wak’ar “K’alubale” Ta Ak’ilu Aliyu kallon garau da bitar tsaf-tsaf da nazarin k’wak’waf domin fito da wasu muhimman abubuwa da wak’ar ta k’unsa, wad’anda ba kasafai mutum zai yi farat ya fito ya ce ga su ba.

Haka kuma aikin yana da manufar zak’ulo wasu bayanai sahihai dangane da ita kanta wak’ar.

A sabili da haka ne muke ganin ya kamata a matsayi mu na masu nazarin harshen Hausa muka ga ya dace mu tuntu’bi masu ilimi a wannan fanni domin samun makamar wannan aiki.

1.0.3. Muhallin Bincike


Wannan aikin za a gudanar da shi a kan adabin zamani na Hausa. Sannan kuma za a tak’aita shi a kan wak’ar nan ta “K’alubale” wadda Ak’ilu Aliyu ya rubuta, kuma za a ke’bance aikin a kan “Amfani da Salon Adon Harshe a cikin wak’ar” saboda haka muhallin wannan bincike zai ke’banta ne kawai a kan wak’ar kuma ita ce muhallin.

1.0.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike.


        Domin samun nasarar gudanar da wannan aiki a cikin sauk’i za a bi hanyoyi da dama da suka had’a da:

Karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da muk’alu da Mujallu domin zak’ulo wasu bayanai masu nasaba da aikin. Za a kai ziyara a d’akunan karatu da suka had’a da nan cikin makarantarmu wato Kwalejin Ilimi da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya da ke Garin Gusau, (FCET) , da Kwalejin Fasaha da Kimiyya (ZACAS) Gusau, da Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara da ke Maru (C.O.E.) Maru, da sauransu domin tattara bayanai masu nasaba da wannan aiki.

Haka kuma za a yi amfani da tuntu’bar malami masana da manazarta wak’ok’in Hausa domin samun sauk’in gudanar da wannan aiki.

1.05. Matsalolin Da Suka Taso.


        A wannan bincike mun fahimci cewa akwai wani gi’bi da aka manta ba a cika ba a cikin fannonin da ake bincike a kansu. A  akwai abubuwa da yawa wad’anda suka shafi al’amurran jama’a na wannan zamani amma sai aka yi fatali da su ba wanda ya kula. Tuni wasu mashahuran malamai suka yi iya k’ok’arin su don ganin cewa sun samar wa jama’a abin karatu da kuma abinda za su nazarta. Wannan ya nuna kenan har ko yaushe ba a rasa wasu da suka yi k’ok’ari wajen samar da abin da za a iya dogaro da shi na abin da ake nazari.

Saboda a d’an ilimin da ke akwai a wannan fanni da aka d’auka, na nazarin wak’ar ba a yi wani aiki mai yawa ba a wannan fanni. Wannan na d’aya daga cikin manyan dalilan da suka ja hankalinmu har muka fantsama cikin yin nazari a kan wannan fanni.

Wasu da suka taso a wannan lokaci ba su san, wak’a tana da matuk’ar rawar da take takawa ba wajen jan hankalin mai sauararo ba. Haka kuma muna iya cewa wasu wak’ok’i da ake yi a wancan zamani suna d’auke da karantarwa da ilimantarwa musamman abin da ya shafi addini. Wannan yasa muke ganin ya dace mu mayar da hankali a kan adon harshe da wasu salalai da Ak’ilu Aliyu ya yi amfani da su a cikin wak’arsa ta “K’alubale”.

1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta


Kamar yadda ma’anar ke nuni “matsala” wato irin cikas d’in da aka ci karo da shi a yayin da ake gudanar da wannan bincike. A duk lokacin da mutum ya samu kansa a cikin irin wannan aiki na bincike to lallai wajibi ne ya ci karo da wasu matsaloli da za su iya kawo tarnak’i ga aikinsa na bincike kafin ya kai ga cin nasara. A lokacin gudanar da wannan kundi mun samu barazana ta wasu matsaloli da suka had’a da:

Matsalar littafan karatu. Wannan matsala matsala ce babba saboda wannan makaranta ba ta da isassun littafai da za a duba, wannan ya sa sai da na lek’a wasu makarantu don samun wasu bayanai da za su taimaka a gina wannan kundin. Wannan walaha ta ziyarce-ziyarcen wasu makarantu ta kawo tafiyar hawainiya ga gudanar da wannan bincike.

Matsalar kud’i: wannan matsala tana d’aya daga cikin manyan matsaloli da suke tauye komai da ake yunk’urin yi har dai in ya zama abu ne mai buk’atar a inganta shi. Matsalar kud’i babbar matsala ce har dai garemu mata da yake d’auke ake da nauyinmu kuma ba kasafai za mu nemi a bamu kud’i a gidajenmu a bamu ba, sai an samo kuma sai an gani in babu wani abu da ya fi buk’atarmu muhimmanci sannan a bamu, idan kuwa aka samu wani abu da ya fi tamu buk’atar muhimmanci to, lallai mu ba zamu samu ba sai har an samu wasu gaba sannan wata kila mu samu. Rashin kud’in dai ya kawo matsala, amma yanzu an shawo kan matsalar.

Matsalar wutar lantarki: wannan matsala ta taka rawa sosai wajen yi wa wannan aiki tarnak’i wato matsalar ta kawo tafiyar hawainiya wajen gudanar da wannan binciken. Ana kuma iya gane cewa wannan zancen namu na matsalar wutar lantarki gaskiya ne idan aka dubi yanayin garin na Gusau za a ga cewa babu isasshiyar wutar lantarki wadda da ita ne kawai za a iya buga muna rubutunmu a cikin Kwamfuta (Computer). Wannan ya sa aka saka wannan matsala ta rashin wuta a cikin matsalolin da suka taso suka dabaibaye gudanar wannan Bincike.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

https://www.amsoshi.com/2018/06/15/harshe-da-adabi-adon-harshe-a-cikin-wakar-kalubale-ta-alhaji-akilu-aliyu-1/