Ticker

6/recent/ticker-posts

Munin Ƙarya Ga Taɓarɓarewar Tarbiyyar Al’umma

NA

AISHA JAMILU          

HADIZA ISAH            

HASSANA SULE        

SAHEN  HAUSA TSANGAYAR HARSUNA KWALEJIN ILIMI DA ƘERE-ƘERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU,JIHAR ZAMFARA 

SHEDANTARWA


Wannan aiki ya samu dubawa da tabbatarwa tare da karbuwa gami da amincewar waɗannan malamai.

SADAUKARWA


Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta ƙasa (NCE) a sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da Ƙere-Ƙere da ke Gusau a jihar Zamfara ga mahaimafanmu kamar malma Samon Bala da Malam Ibarhim Gambo da Alh. Jamilu Salisu da kuma iyayenmu mata wato Cicilia Samon da da Malama A’ishatu Ibrahim da Hajiya Suwaiba Lawali haka kuma mun sadaukar ga mijin abikiyar aikinmu wato Malam Lawal Abubakar da yannai da ƙannai da fatar Allah ya saka masu da alheri amin.
GODIYA


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.

Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka muna domin ganin haƙarmu ta cimma ruwa, musamman ga iyayenmu kamar su malma Samon Bala da Malam Ibarhim Gambo da Alh. Jamilu Salisu da kuma iyayenmu mata wato Cicilia Samon da da Malama A’ishatu Ibrahim da Hajiya Suwaiba Lawali haka kuma mun sadaukar ga mijin abikiyar aikinmu wato Malam Lawal Abubakar da yannai da ƙannai, da suka jure da yin haƙuri da mu har muka cimma wannan lokaci, haka kuma muna miƙa godiyarmu zuwa ga iyayenmu mata da suka bamu goyon baya har Allah ya nufemu da gama wannan karatu tare da yin wannan kundin. Suma dai ‘yanuwa da abokan arziki ba za mu bar su a baya ba, Allah ya saka masu da alherinSa amin

Haka kuma muna miƙa kyakyawar  godiyarmu ta musamman ga malamanmu na wannan sashe kamarsu; Malama Haruna Umar Maikwari wanda ya ɗauki tsawon lokacinsa yana kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo ƙarshe Allah ya saka masa da mafificin alherinSa amin. sai Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Malam Haruna Umar Bunguɗu, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba, Mal. Habibu Lawali Ƙaura, Mal. Aminu Saleh, Mal. Sani Aliyu Soba da Mal. Ibrahim Ahmadu ɗan’amarya da sauran su.




JINJINA


Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu jinjina ma malaman mu musamman Mal. Haruna Umar Maikwari da ma wasu daga cikin mutanen da suka taimka muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan dalibai da ma duk masu neman ƙarin haske dangane da nazari da muka gudanar a kan “Munin Ƙarya Ga Taɓarɓarewar Tarbiyyar Al’umma” muna masu roƙon Allah ya saka masa da maifificin alheri. Amin.

 

ƘUNSHIYA


Shaidantarwa -      -        -        -        -        -        -        -        ii

Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        -        -        iii

Godiya        -        -        -        -        -        -        -        -        iv

Jinjina         -        -        -        -        -        -        -        -        vi

Ƙunshiya    -        -        -        -        -        -        -        -        vii

BABI NA ɗAYA


1.0    Gabatarwa    -        -        -        -        -        -        1

 

  • Yanayin Bincike - - -        -        -        -        2

 

  • Muhallin Bincike -        -        -        -        -        3

 

  • Hanyoyin Gudanar da Bincike -        -        -        3

 

  • Manufar Bincike -        -        -        -        -        4

 

  • Matsalolin Da Suka Taso -       -        -        -        5

 

  • Matsalolin Da Aka Fusakanta - - -        -        6

 



BABI NA BIYU


2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata    -        -        8

2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -        -        -        -        -        12

BABI NA UKU



 

  • Tsokaci a Kan Ƙarya - -        -        -        -        15

 

  • Mace ce Ƙarya? -        -        -        -        -        16

 

  • Ƙimar Ƙarya da Maƙaryata a Al’adance -        -        19

 

  • Kashe-Kashen Ƙarya - -        -        -        -        20

 


3.0.4.1 Ƙaryar Furuci -        -        -        -        -        -        21

3.0.4.2 Ƙaryar Aiki   -        -        -        -        -        -        23

 

  • Adawar Al’ada da Ƙarya -        -        -        -        24

 

  • Ƙarya da zamaninmu - -        -        -        -        25

 



BABI NA H UɗU


4.0.1Gudummuwar Ƙarya ga Durƙusar da Al’umma da

Ruguza ta    -        -        -        -        -        -        -        27

4.0.2 Ƙarya a Cikin Zamantakewa     -        -        -        -        28

4.0.2.1 Ƙarya a Neman Aure    -        -        -        -        -        30

4.0.2.2 Ƙarya Bayan Aure       -        -        -        -        -        33

4.0.3. Ƙarya a Tsarin Siyasarmu        -        -        -        -        35

4.0.4. Ƙarya a Gidan Jaridu      -        -        -        -        -        36

4.0.5 Hanyoyin Magance Ƙarya        -        -        -        -        -        39

BABI NA BIYAR


5.0.1 Jawabi Kammalawa         -        -        -        -        -        42

 

  • Shawarwari - -        -        -        -        -        -        43

 


Manazarta        -        -        -        -        -        -        -        45

 

 

 

Babi Na ɗaya



Gabatarwa


Wannan bincike mai taken “Munin Ƙarya Wajen Taɓarɓarewar Tarbiyyar Al’umma”. Za mu gudanar da shi ne domin cika sharudɗ’an ƙare wannan kartu namu da kuma samu damar karɓar takardarmu ta ƙare karatu a wannan makaranta wato N.C.E.

Sanin kowa ne cewa, ƙarya ba abu ce mai kyau ba, kuma duk wanda ya lizimci ƙarya rabonsa bai wuce kunya ba.

Domin samar da sauƙi ga masu nazari, mun tsara aikinmu bisa ga tsari na babi-babi har babi biyar.

Babi na farko za mu kawo bayani ne a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike da Manufar Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Da Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.

A babi na biyu kuwa nan ne za mu yi tsokaci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata da kuma Salon Nazari Da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa nan ne za mu yi bayani a kan Tsokaci a Kan Ƙarya, Ma’anar Ƙarya, Kashe Kashen Ƙarya, Ƙarya ta Furuci da Ƙarya a Aikace da Ƙarya da Al’ada, Taho mu Gaman Ƙarya da Al’ada da Ƙarya a Zamaninmu.

A babi na huɗu za mu biyo da bayani Gudummuwar Ƙarya Wajen Durƙusar da Tarbiyyar Al’umma da Ƙarya a cikin Zamantakewa da Ƙarya a cikin Neman Aure da Ƙarya a cikin Zaman Aure da Ƙarya a cikin Siyasarmu da Ƙarya a cikin Gidajen Jaridunmu da Hanyoyin da za a bi a Magance Barazanar Ƙarya.

Shi kuwa wannan babi na biyar a nan ne za mu naɗe tabarmar wannan bincike namu ta hanyar yin Jawabin Kammalawa da Shawarwari.

Yanayin Bincike


Wannan bincike na da yanayi na dubawa, saboda matsayinsa na ilimi, kuma wannan aiki na bincike ya sha bam-bam da sauran bincike da ake yi. Dalili shi ne, wannan fanni na al’ada an gudanar da ayyuka a cikinsa sai dai bai samu wasu ayyuka masu yawa da suka haɗa da ƙarya ba kuma wadda take zama sanadin taɓarɓarewar tarbiyyar al’umma ba.

Wannan ma ya sa a yunƙurinmu na gudanar da wannan aikin binciken mun sha wahala sosai saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi Magana a kan wannan aiki namu. Haka kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala matuƙa.

Muhallin Bincike


Da yake aikin yana da alaƙa da abin da ya shafi al’ada duk da cewa ƙarya ba ta cikin al’adun Hausawa, amma kuma wasu daga cikin Hausawa sukan iya aiwatar da ita a cikin neman aure ko a zama na aure. Wannan ya sa muka keɓance wannan aiki namu ga abin da ya shafi ƙarya da yadda take zama sanadi na taɓarɓarewar tarbiyyar al’umma. Ba kuma zamu fita daga cikin jihar Zamfara ba saboda wuraren da ake yin ƙarya suna da yawa ko nan Gusau kaɗai muka tsaya haƙar za ta cimma ruwa sai mun ije.

Hanyoyin Gudanar da Bincike


Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka waɗanda suka gabata domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi daban-daban don ƙarin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.

Kamar yadda bayani ya gabata mun  lura da cewa, dukkan mai aikin bincike dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar da wannan bincike namu domin kuwa mun ziyarci mutane da dama da suka danganci tsofaffi masu masanniya a kan yadda ake yin ƙarya da kuma yadda ƙarya take taka rawar gani wajen taɓarɓarewar tarbiyyar al’umma musamman a nan jihar Zamfara.

Manufar Bincike


Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano cikakkiyar ƙwarewar ɗalibai da fahimtarsu da hazaƙarsu. Ta wannan hanyar karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya ƙara tabbatar da abin da aka riga aka sani a fagen ilimi.

Binciken yana fitar da bayanai domin amfanin al’umma, wani babban muhimancin bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.

Manufar wannan binciken ita ce, domin mu ga irin yadda ƙarya take zama illa ga rayuwar al’umma musamman a nan jihar Zamfara

Matsalolin Da Suka Taso


Akwai wasu matsa da suka taso suka zamo ƙalu-bale ga al’umma kuma waɗannan matsaloli akwai hanyoyi da ake iya bi a warware su, sai mutane suka yi fatali da su, suka watsar. Ba mu sani ba ko dai akwai wani abu da ya sa suka zaɓi wannan matsala ta riƙa ci masu tuwo a ƙwarya.

Mun lura da cewa, ƙarya tana kawo ɓaraka a cikin al’umma, amma al’umma sun yi mindinƙis sun watsar da gaskiya sun zaɓi su yi ƙarya don samun wani abu daban. Wannan matsala ce babba da take addabar mutane, saboda idan mutum ya duba zai lura cewa, ita dai ƙarya ko da yaushe ƙarshenta ba mai kyau ba ne. idan kuma mutum ya lizimce ta to zantukansa ba za su yi tsari ba a idon al’umma.

Haka kuma a wannan ɓangare na nazari harshen Hausa ba a yi wasu ayyuka da yawa da suke da alaƙa da wannan fanni ba. A ɗan binciken da muka yi ba mu ci karo da aiki mai kama da wannan ba shi ya sa muka yanke shawarar mu bayar da tamu gudummuwa a wannan fanni.

Matsalolin da aka Fuskanta


Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka, wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kuɗi da za mu buga wannan aiki namu. Haka kuma akwai matsalar haɗuwarmu idan mun yi alƙawali, kuma idan za mu tafi wajen  ganawa da waɗanda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne a same su ba.

Ba nan kaɗai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar karancin lokaci. Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a cikin shekara ɗaya ba tare da an haɗa  shi da wani darasi ba.

Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu ɗalibai mata masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama  sun sha kanmu. Daga cikinsu akwai:

Matsalar karɓar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji da ta ƙarshen zangon karatu.

Akwai matsalar tuntuɓar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu suna ganin kamar za mu raina masu da al’adu ne saboda mu ‘yan boko ne su kuma ba su yi bokon ba.

Haka ma akwai matsalar yawan ɗaukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta ɗauke. Kaɗan kenan  daga irin matsalolin da muka ci karo da su.

 
Babi Na Biyu

2.01. Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.


Babu shakka ga duk wanda ya ke son ya aiwatar da aikin bincike dole ne a gare shi ya waiwayi baya domin ganin irin ayyukan da magabata suka yi masu dangantaka da nashi daga nan shima sai ya san inda suka tsaya ga bincike, ya kuma san inda zai ɗora nasa aikin.

Hausawa kan ce “waiwaye adon tafiya” wannan ko shakka babu gaskiya ne domin ta hanyar waiwaye ne kaɗai mutum zai iya gane irin ayyukan da magabata suka yi, sannan ya san ta wace hanya zai bi wajen gudanar da nashi aikin na bincike. A cikin wannan binciken ne manazarci zai samu wasu ayyuka da dama waɗanda zai ɗauki wasu, kuma ya watsar da wasu.

A wannan bincike mun aiwatar da haka domin kuwa mun nemi inda za mu samu ayyukan magabata da za mu waiwaya, mu ga abin da suka nazarta da kuma yadda za mu gudanar da namu. Ga dai wasu daga cikin ayyukan da muka samu yayin da muke nazarin wannan bincike.

CNHN, Jami’ar Bayero Kano (1981) sun buga wani littafi mai taken “Rayuwar Hausawa” an tsara wannan littafi bisa ga tsari na kashi-kashi inda suka fito da kashi shidda. Kashe na ɗaya dai ya ƙunshi tarihin ƙasar Hausawa, kashi na biyu kuwa yana bayani a kan aure, a kashi na uku bayanai ne game da haihuwa, yayin da kashi na huɗu yake ƙunshe da bayanai a kan mutuwa. Kashi na biyar kuwa bayanai ne a kan tasirin bukin al’adu a kan al’adun Hausawa, sai kashi na shida wanda yake shi ne na ƙarshe kuma a cikinsa ne suka kammala littafin.

Wannan littafi yana da alaƙa da aikinmu ta wani ɓangare musamman a kashi na biyar saboda ya yi tsokaci a kan tasirin baƙin al’adu duk da cewa ba nan kaɗai ya tsaya ba. Wannan bayani a kan baƙin al’adu, shi ne kaɗai yake da alaƙa da aikinmu, kuma zai taimaka ainun wajen gudanar da namu aikin. Inda gizo ke saƙa kuma shi ne aikin yana da bambanci mai yawa tsakanin namu da nasu. Dalili kuwa shi ne ba su ce komai ba game da ƙarya da yadda take taka rawa wajen taɓarɓarewar tarbiyyar al’umma.

Alhassan da wasu (1982), sun rubuta wani littafi a kan Al’adun Hausawa, waɗanda suka haɗa da aure haihuwa da mutuwa, a cikin wannan littafin na su Alhassan sun yi bayanin auren Hausawa kuma sun kawo ire-iren auren Hausawa da kuma yadda ake yin aure da lokacin da ake yin aure na Hausawa.

Wannan littafi na su Alhassan yana da alaƙa da namu aikin saboda sun taɓo al’adun Hausawa daga ciki kuwa har da aure. Wannan shi ne muke ganin aikin su yana da alaƙa da namu, sai dai inda ayyukan suka bambanta shi ne duk da cewa aikinsu yana da alaƙa da namu kuma akwai inda muka sha bamban da su. Saboda su suna magana ne a kan al’adun Hausawa gaba ɗaya mu kuma muna magana ne a kan ƙarya da yadda take gurɓata tarbiyyar al’umma.

Zarruk da wasu (1986) sun rubuta wani littafi mai taken “Sihili Uku” a cikin wannan littafi an yi bayani a kan al’adun Hausawa da yadda suke aure da yadda suke bukukuwan aure. Wannan aiki nasu yana da alaƙa da namu aikin saboda sun yi bayani a kan al’adun Hausawa da yadda suke gudanar da bukukuwan aurensu. Ganin ba yadda za mu bi mu sanar da al’umma aibin ƙarya sai mun warware masu al’adunsu na gargajiya da aka yi masu tarbiyya a kai, ya sa muka ta’allaƙa aikin ga al’adu na Hausawa.

Adamu M. I. (1998), “Aure a Ƙasar Hausa” adamu ya tsara aikin nasa ne a kan tsarin babi-babi har zuwa babi huɗu. Yayin da a babi na ɗaya ya yi bayani a kan aure a ƙasar Hausa. A babi na biyu kuwa bayanai ne da suka danganci neman aure a ƙasar Hausa. Sai a babi na uku inda marubucin ya yi tsokaci a kan baiko da ɗaurin aure. A babi na huɗu ya kawo bayanai a kan biƙi.

Duk da cewa wannan aiki na Adamu yana ɗauke da bayanai masu yawa bai hana a ga inda aikinmu yake da alaƙa da nasa ba, kamar yadda aka ga ya yi magana a kan neman aure. Wannan ko shakka babu a namu aikin za a ga cewa akwai ƙarya a cikin neman aure. Sai dai inda bambanci yake shi Adamu bai yi magana a kan yadda ƙarya ke take yin illa ga rayuwar al’umma ba.

Garba U.G (2012) ya rubuta littafi mai suna “Bukukuwan Hausawa” a cikin wannan littafin, Garba ya kawo bukin naɗin sarauta da bukin salla da bukin aure da na haihuwa.

Wannan aiki na Garba yana da alaƙa da namu aikin saboda ya taɓo bayanai a kan bukukuwa, namu aikin kuwa, ya zama wajibi mu yi magana a kan ƙaryar da ake yi cikin bukukuwan Hausawa. Wannan ne ya sa ayyukan suke da alaƙa da juna. Inda kuma suka bambanta shi ne aikin Garba yana bayani ne a kan bukukuwa, amma mu namu aikin ba wai a bukukuwa ne kawai ya keɓanta ba hatta da gano yadda ƙarya take a cikin lamari na sha’anin rayuwa.

Shi kuwa Musa I (2013) ya rubuta kundinsa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin samun digiri na farko a sashen Hausa, a cikin kundinsa mai taken “Nazarin Aure A Jahiliyya” ya yi bayanin a kan aure a zamanin jahiliyya da kuma aure a wannan zamani na ilimi, ya kawo irin yadda ake gudanar da auren a wancan zamani na jahiliyya ya kuma kawo yadda ake gudanar da shi a wannan zamani. Musa ya kalli aure a addinance kana ya kalle shi a zamanin dauri.

Wannan aiki na Musa yana da alaƙa da aikinmu saboda shi Musa yana bayanin ne a kan wata al’ada daga cikin al’adun Hausawa, yayin da muma muna nazarin da ya shafi al’adun. Inda kuma muka sha bamban da shi shi ne, shi ya kalli abin a jiya da yau, mu kuma aikinmu ya ta’allaƙa ne a kan gano illar ƙarya ga rayuwar al’umma.

2.0.2 Salo, Zubi Da Tsarin Bincike


Salo da zubi suna nufin irin dabarun da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike. Tsarinsa na nufin yadda aka tsara wannan bincike.

Salo shi ne hanyar da marubuci ke bi domin samun nasarar isar da saƙonsa ga masu karatu ko sauraro.

Idan aka ce salo to, ana nufin duk wata dubara da marubuci ko mai magana ya bi wajen isar da saƙonsa a cikin sauƙi.

Gusau (1993: 5), cewa ya yi. “salo shi ne hanyar da ake bi a nuna gwaninta da dubara a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace game da abin da yake son bayyanawa.

A duk lokacin da aka yi maganar salo ana magana ne a kan irin ƙwarewar manazarci, wajen aikin bincike da kuma yadda yake jawo hankalin mai karatu a kan aikin da marubucin ya yi a kowane lokaci.

A wannan kundin dai za mu yi amfani da salo mai burgewa wajen aiwatar da wannan kundin ta yadda duk wani ya ɗaga shi sai ya amfana matuƙa. Wannan ba ya rasa nasaba da irin yawo da za mu riƙa yi gida-gida saboda tattara bayanai da suka shafi wannan kundin. Don haka muka yarda cewa dukkanmu za mu ziyarci masu ilimi a kan wannan lamari na aure don samun ingantacciyar hujja.

Babi Na Uku

3.0.1 Tsokaci a Kan Ƙarya


A kodayaushe magabata da masana da ɗaliban bincike da masu kai da kawo cikin al’ummarmu sukan koka sosai a kan tavarvarewar al’adunmu. Wasu su zargi zamani gaba ɗaya, bisa ga fahimtar zamani mai yayi. Wasu su zargi kasawar mahaifa ga ba da nagartacciyar tarbiyya, a kan fahimtar cewa ; kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. Har yanzu, wasu na zargin mulkin mallaka da Turawan Ingilishi suka yi wa ƙasashenmu, domin zama da maɗaukin kanwa shi kan kawo farin kai. A hangen wasu, cuɗeɗeniyar al’adun mutanen duniya da ke bazuwa a duniya ta fuskan kafofi yaɗa labarai da sadarwa da cuɗanya da masu gurvatacciyar tarbiya ita ce sandar da ta yi na tarbiyyarmu bugu ɗiyan kaɗe. Cikin waɗannan abubuwa, idan muka nazarce su, za mu ga kowane baki wuta da irin nasa hayaƙi. A ɗan nama tunani,  babban abin da ya rusa muna al’adu da tarbiyya da zubar  muna da girma, duk bai wuce ‘ƙarya’ ba.

  
3.0.2 Mece ce Ƙarya?


A zahiri, za a ce kowa ya san ƙarya, kuma kowa na iya cewa, wannan abu ƙarya ce, ko wane/wance maƙaryaci ne ko maƙaryaciya ce, ko maƙaryata ne. A haƙiƙanin bincike, ƙarya ta fi bayyana a harshe a ji ta da kunne. Haka kuma, ƙarya na bayyana ga ayyuka a gan ta ƙuru-ƙuru ko da an kasa tava ta, ko a yi mata magana ta ji. Ƙarya ta fuskar bayar da labari, da mai da jawabi da shaida, tana da ma’anar :

 

1.     Faɗar abin da ba a gani ba.

 

2.     Faɗar abin da ba a ji ba.

 

3.     Faɗar abin da ba a yi ba.

 

4.     Faɗar abin da ba a tabbatar ba.

 

5.     Faɗar abin da ba ka ji an yi ba.

 

6.     Faɗar abin da ba ka sani ba.

 

7.     Faɗar abin da ba a sanar da kai ba.

 

8.     Faɗar abin da ba haka yake ba.

 

9.     Faɗar abin da ba haka nan aka san shi ba.

 

10. Faɗar abin da ba haka nan ake yin sa ba.

 

11. Faɗar abin da ba haka ake faɗar sa ba.

 

12. A faɗi abu yadda ake so.

 

13. A faɗi abu yadda yake a rage wani abu.

 

14. A yi ragi, a yi ƙari.

 

15. Giɗaɗawa ko kururutawa.

 

16. Nuna ba a sani ba an sani.

 

17. Gyara abin da ba ya da gyara ko ba ya gyaruwa.

 


Kowane ɗaya daga cikin waɗannan bubuwa goma sha bakwai suka bayyana gaban Bahaushe zai zaci ‘ƙarya’ kuma daga nan ƙimar abin ta rage daga gare shi. Wannan ya sa tilas ne ga mai fuskantar al’umma ya yi jawabi irin shugabanni da malamai da iyaye da `yan siyasa da `yan jarida, su tabbata ba su yi taho-mu-gama da ƙarya ba a zantukansu da ayyukansu. (Bunza 2017)

Ƙarya ita ce bayar da labarin abin da bai faru ba sam-sam, kuma da gan-gan. (Hira da wani malamin Islamiyya mai suna Malam Musa)

Ƙarya ita ce faɗin abin da ba a yi ba ko bai faru ba ko kuma yin ƙari wajen bayar da labari ga abin da ya faru, ko kuma rage wani abu daga ciki da gangan don cimma wata manufa.

Bahaushe ya ɗauki gaski a matsayin wani makami na kare martabarsa. Gaskiya bar so ce, da ƙauna, mai ƙarya abin tsoro ne da gujewa. Haka kuma malam Bahaushe yana kiran gaskiya cewa, “Gaskiya takobin yaro” idan muka yi la’akari wa wannan karin magana za mu gaskata abin da aka ambata a sama cewa wani makami ce, wato dai tunda takobi ce, kuma da takobi makami ce shi kuma makami da shi ne ake kare duk wani abu da zai cetar ta hanyar yin rauni ga wani.

A al’adar malam Bahaushe idan mutum ta yi ƙarya kuma aka gane gaskiya yakan ji kunya da shi da wanda suke tare suna aikata ƙaryar a gaban jama’a. Da wannan ne Bahaushe yake yin wasu karin magangannu da salon magana a kan ƙarya. Ga dai wasu misalai da za a tabbatar da haka:

 

1.     Kowa ya yi ƙarya, ana samun ɗan garinsu

 

2.     Ƙarya mugun guzuri

 

3.     Yau da gobe ke ƙaryata boka

 

4.     Ba a ƙarya a tayar da kai zama

 

5.     Ramin ƙarya gajere ne

 

6.     Ƙarya fure takai ba ta ‘ya’ya

 


Idan Bahaushe ya yi ƙarya kuma aka gane gaskiya to kunya za ta baibaye shi. Kuma ba ya ƙara samun girma ga waɗanda ya yi wa ƙaryar.

Wannan ko shakka babu haka abin yake. Kuma idan aka lura da waɗannan abubuwa da Bunza ya zayyano a sama su ne ake kira ƙarya. Da abu ɗaya daga waɗannan ya shiga to ƙarya ta tabbata.

3.0.3 Ƙimar Ƙarya da Maƙaryata a Al’adance:


Har ila wa yau Shaihin Malami Bunza yana cewa, “Babu wata al’umma daga cikin al’ummomin duniya da ba su muzanta ƙarya da maƙaryata ba. Babu tarbiyar da ƙarya ba ta vatawa, babu ci gaban da ƙarya ba ta rusawa, babu fitinar da ƙarya ba ta jawowa. A Bahaushen tunani, da an shaidi mutum da ƙarya za a ce:

 

  • Ba a shiga ɗaki da maganar wane.

 

  • Maganar wane rabi kuɗi rabi bashi ce.

 

  • Maganganun wane a bar shi da abinsa.

 

  • Bar ta inda ka ji ta.

 

  • In ka ƙara gaba gare ka aka jiya.

 


Waɗannan kalamai na zargi ne da zubar da ƙima da girma ga mutum ko waye shi. Babu wani mai magana ko mai ba da labari ko mai ba da shaida da zai ji daɗin a jefe shi da waɗannan munannan kalamai. Tilas kowa ya kama mutuncinsa da zarar an shiga shafin wannan baƙin littafe duniya ta gama da mai shi.”

Abin lura a nan shi ne ita ƙarya da su maƙaryata al’ummar da suke bisa ga tsari na al’adunsu na asali waɗanda suka ƙyamaci ƙarya ba su kallon duk wani zance da ba na gaskiya ba da ƙima, haka kuma duk wanda ya furta wani zance wanda ba na gaskiya ba to shi ma baya da wata ƙima a idon su. A wani lokaci ma maƙaryaci yana iya funkantar hukunci idan abin da ya faɗa ƙarya ne.

3.0.4 Kashe-Kashen Ƙarya.


Babu wani abu na duniya da ba a iya tsintuwar ƙarya a ciki. A ko’ina aka tsince ta bayyane take domin da an hangi matakai (18) da muka lissafa ana lalubo wurin da ta voye. A ganin Bahaushe, zango biyu ke ga ƙarya. Akwai ƙaryar da:

(i) Ake furtawa.

(ii) Ake aikatawa.

3.0.4.1 Ƙaryar Furuci


Duk abin da baki ke furtawa wanda ba a yi ba, ko ya yi ƙari daga abin da ya faru na gaskiya, ko kuma a yi ragi na ganin dama da sauya ma’anar abin da ya faru na zahiri domin biyan buƙatar mai maganar ko voye wani abu don gudun wani abu daban, duk a cikin furuci wannan ƙarya ce.

Shi kuwa shaihin malami Bunza yana cewa, “Duk abin da baki ke furtuwa ko a rubuta shi, kuma ya yi canjaras da ɗaya daga cikin abubuwa nan wato:

1.     Faɗar abin da ba a gani ba.

2.     Faɗar abin da ba a ji ba.

3.     Faɗar abin da ba a yi ba.

4.     Faɗar abin da ba a tabbatar ba.

5.     Faɗar abin da ba ka ji an yi ba.

6.     Faɗar abin da ba ka sani ba.

7.     Faɗar abin da ba a sanar da kai ba.

8.     Faɗar abin da ba haka yake ba.

9.     Faɗar abin da ba haka nan aka san shi ba.

10. Faɗar abin da ba haka nan ake yin sa ba.

11. Faɗar abin da ba haka ake faɗar sa ba.

12. A faɗi abu yadda ake so.

13. A faɗi abu yadda yake a rage wani abu.

14. A yi ragi, a yi ƙari.

15. Giɗaɗawa ko kururutawa.

16. Nuna ba a sani ba an sani.

17. Gyara abin da ba ya da gyara ko ba ya gyaruwa da ake ambata to ƙaryace. Narambaɗa ya fuskanci irin wannan zance da yi masa suna da “batutuwa”: Da Bahaushe y ace “batutuwa” an san cewa zantukan da ba su da tushe ne.

Jagora: Ya waste batutuwa na Jekada

                   : Ya taho gida

Yara:   Kunya ga ta nan gare ku mutanen banza.

          Gindi: Gwauron Shamaki na Malam toron giwa

                   : Baban Dodo ba a tammai da batun banza.”

 

Shi kuwa Kabiru Yahaya ‘Classic’ a wata waƙa da ya yi wa Chiroman Wamakko Alhaji Aliyu Oroji, ya bayyana nasa baitin kamar haka:

Jagora:        Ga wani ya so yai mani ƙarya, ya aza na ɗauka,

          ‘Y/rakiya:    Ashe sara kaka kallonai ka voye asirinka,

          Jagora:        Muna ta wayonwayo da wane ka gani na ganka,

          ‘Y/rakiya:    In ba don ba don ba Classic kai ka san bai ragama.

3.0.4.2 Ƙaryar Aiki


Da ganin wata tafiya ta samarin zamaninmu ka san ƙarya ce, domin ba haka ake ba, ba kuma haka aka saba yi ba. Ina laifin Bamaguje da ya shiga birnin (Kano) ya ga ba rumbu, ba masussuki, ya ce: “Ana zaman ƙarya”. Da asuba, ya ga motoci da babura da kekuna da masu tafiya ƙasa kowa urzurce zuwa wuri-aikinsa, sai ya ce: “Na san tana haka, ina zama ga wurin da babu abin zama?”

Kai da ganin saka kayan wani ka san ƙarya ce zalla, wani kuma tafiya, wani kuma mu’amula ta rayuwa wani kuma hidima kamar bukukuwa ko sha’anin aure ko sarauta ko neman suna ko burge wata mata ko wasu ko tsoratar da wasu duk ka san ƙarya ce. Ga dai abin da Makaɗa Walga Bunza ya hangi wata ƙarya ta aiki ga wani jahili da bai iya karatun salla ba ya rinƙa gunaguni sai makaɗa ya ce:

Jagora: Gunguni ba salla ba

          : Ba a iya na ba

          : Tun da maganriba ta yi

          : Ba ni son ƙarya

          : Wanda ya iya salla ya fissuwa hili.

3.0.5 Adawar Al’ada da Ƙarya


Al’adar Hausawa an shiya ta bisa ga wata tarbiyya wadda ba duk mutum na duniya ne zai iya rarrabe ta da addini ba. Don haka daga cikin abubuwa na rashin gaskiya babu ɗaya da al’adar ta yi na’am da shi.

Al’adar Bahaushe ba ta rage wa ƙarya hakin susa ba. A koyaushe, ƙarya da mutanenta cikin muzanta suke da zolaya da gwalo. Ba a tava bijiro da wata tatsuniya ko karin magana da tarihi ko tarihihi da ƙarya ta samu wurin miƙe ƙafafunta ba, sai dai ta yi fitar kutsu. Maƙaryaci ba ya da mataimaki in ji makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo:

Jagora: Mai kurin biɗan faɗa

          :Bana an ba shi kashi,

Yara  :Han na zaburo rabo sai-

          :Nij ja da baya nat tuna

          :Ƙaryar da yay yi min

          :Gyara a ba shi ka shi

Gindi: Bai ɗau wargi ba Audu

          :Mu zo mu ga Madawaki

 

A tsarin tunanin Bahaushe, maƙaryaci ba ya da hutawa koyaushe cikin jewaɗi yake da shan ranar kare abin da ba ya karuwa. Makaɗa Narambaɗa ya tabbatar da haka a faɗarsa:

Jagora: Taro na tambaye ku

                   :Shin ko wag ga wuta

                   :An ka ce a ɗebo wa ka zuwa?

Yara: Wanda yag gani ka zuwa,

                   :Ko was shaida shi ka shan rana,

                   :In bai tai ba yai batun banza.

                   :Ko can yanzu shi batun banza daɗi hwaɗi garai.

Gindi: Ya ci maza ya kwan shina shire

                   Gamda’aren sarkin Tudu Alu

Daga cikin gawurtattun sunayen ƙarya akwai “batun banza” 

3.0.6 Ƙarya da Zamaninmu:


Shaihin malami Aliyu Muhammadu Bunza yana faɗa a cikin wata muƙala da ya gabatar a zauren taro na ma’akatan ƙananan hukumomin jihar Zamfara mai taken “Ƙarya Hure Takai” yana cewa “Ban yarda al’adu na tavarvarewa ba sai dai waɗanda ke riƙe da al’adu su tavarvare. Ina shakkar zargin zamani ga tavarvarewar al’amurran mutanansa, domin da rana da wata da taurari da sararin samaniya da ƙassai da iska da ake shaƙe ko ɗai bai fasa aiki ba kamar yadda yake yi a da. Mutanen da ke ciki dai suka sassauya abubuwa gwargwadon son ransu suka gayyato ƙarya ta yi ka-in-da-na-in ciki sai abubuwa suka kasance kamar yadda muka gan su. A ko’ina aka ga wani abu ya lalace ƙarya aka sa a ciki. Matuƙar ana ba ƙarya sarari ta kutsa kai cikin kowane irin sha’ani da wuya a gama lafiya domin ba ta da abokiyar adawa sai “gaskiya”. Ƙyalƙyalinta na yaudara ke sa ana muzanta gaskiya da mutanenta domin su ji tsoranta su voye a ba ta wuri ta baje kolinta. Huɗubar da Narambaɗa ya yi wa gaskiya a kan ƙarya abar kulawa ce:

Jagora: Na hore ki gaskiya bari tsoron ƙarya

Yara: Mai ƙarya munahuki Allah su Yaƙ ƙi

Jagora: Har yau ba mu ga in da an ka yi mai ƙarya ba

Yara :  Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi.

Gindi: Gwarzon shamaki na malam toron giwa

          :Baban Dodo ba a tarma da batun banza.”

 Don haka ya dace a duk inda mutum ya samu kansa ya kasance yana mai haƙuri da gaskiya komai ɗacinta, kuma komai tsufanta. Idan lamari ya zo na furuci to ya furta gaskiya, in kuma na aiki ne to ya aikata gaskiya ko da ba zai samu wanin abu ba.

Babi na Huɗu

4.0.1 Gudummuwar Ƙarya Ga Durƙusar Da Al’umma Da Ruguzata


Sanin jama’a ne cewa, ƙarya ta yi kaka gida a dukkan lamurran mu da yau da kullum, don haka yana da kyau mu sake shirin farfaɗo da tsarin ilmin ƙasarmu mu ɗeve ƙarya a ciki. Yau takardun shaidar karatu tun na firamare har zuwa na digirin ƙarshe ba su kuvuta ga maguɗi ba. Yau masu takardun ƙarya ke zama likitocin kiwon lafiyarmu su kashe mu da `ya’yanmu. Su ne injiniyoyin gina muhalli, a yi bene ya rusga kowa ya mutu. Su ke cikin jami’an tsaronmu (na kayan sarki da farin-kaya) shirin tsaron ƙasa ya gagara. Su suka mamaye gidajen shari’o’inmu shari’un sun ƙi ci sun ƙi cinyewa. Sun mamaye siyasar ƙasarmu, ɗan majalisa ya gama shekarunsa babu wanda ya ji muryarsa a ƙauyensu. Sun cika jami’o’inmu, ba a kore su ba, sun kasa kammala karatu. A wasu sassa na ƙasarmu har gadon takardun karatu ake yi. Taruwar waɗannan abubuwa shi ya sa yawaitar ma’aikatan ƙarya a ko’ina cikin ma’aikatunmu da ƙananan hukumomi, da jiha da tarayya. Da gwamnati za ta kafa wani kwamiti na adilai, a tantance masu takardun ƙarya na shaidar karatu da ma’aikatan ƙarya, a ƙalla kashi sitti (60%) na matasanmu marasa aiki za su samu guraben aiki kai tsaye ba tare da ka-ce-na-ce ba. Bunza (2017)

A ɗan namu nazari da muka yi mun fahimci cewa, yin ƙarya a kowane fanni yana kawo cikas na gurvata da tavarvarewar tarbiyya da durƙusar da al’umma. Gurin kowace al’umma ta samu tattalin arzikinta ya havaka kuma, su kasance sahun farko na masu kyawawan halayya. Idan kuma suka bijire wa gaskiya to babu shakka suna iya haɗuwa da wani sakamako marar kyau.

4.0.2 Ƙarya a Cikin Zamantakewa:


A zamantakewa aurenmu, ƙarya ta yi muna katutu wanda shi ne musabbabin yawaitar mutuwar aure a yau. Da aure ya tavarvare, sai zina ta yawaita. Yawaitar zina ke haifar da yara marasa tarbiyya da ba su san iyayensu maza ba. Wanda bai san tsohonsa ba tsohon kowa ba ya tausai. A tsarin kasuwancinmu mai kaya rantsuwa, mai saya rantsuwa, dillali rantsuwa, kuma duk sun sava wa juna, wane ne maƙaryaci a ciki? A mu’amala ta yau da kullum ana kallo wanda ba yada wata sana’a, ya mallaki dukiyar da zai saye kayan masu sana’a, a taru gidansa ana fadanci. Wane ne maƙaryaci a cikinsu? Shi attajirin girshi ko ni, da kai, da ku, da muka taru gidansa jiran a ba mu? A rayuwarmu ta addini ƙarya ba ta ƙyale mu ba. Shigan burtun da jahilai ke yi cikin rigar addini da sunan malamai kuma ƙungiyoyinsu da ɗariƙoƙinsu da mazhabobinsu da aƙidojinsu su aza su a karagogin wa’azi suna shara ƙarya ana kabbarori. Abin ban tausai, kowane vangare rantsuwa yake yi cewa, sai an bi shi za a shiga aljannan. To, wa za a gaskanta? Wa za a ƙaryata? Abin mamaki kuma, duk vangarorin sun taru gaban hukumar da ba ta yarda da kalmar shahada a matsayin tsarin tafiyar da dokointa ba, kuma duk su yi mata ɗa’a bayan sun wargaza kanun mabiya. A gai da Sambo Wali Giɗaɗawa da ke cewa,

Mik kai mallamai gidan gwamnati ban da wauta

          Niyyattai guda ta ya sami kafa ta cuta

          Babu kira ga ƙyafatowa ga tavasgarta

          Tsorci Ubangiji mallami an kama bauta,

                    Bari sa kanka hanyar da ba fita ƙasag ga.

Ga wani mallami can da malfatai da sanda

Ya shawo naɗi ka ji tsohon ɗan baranda,

Ofis za shina wurin manya `yan ta’adda,

Don ya matsa su ba shi mamba koko takarda-

‘Tenda’ don ya toye kuɗɗin jama’ar ƙasag ga,

 

(Sambo Wali : Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana, baiti 41-42)

Ba mun ce a raba siyasa da addini ba, amma amfani da siyasa a yaudari addini ƙarya ce. Haka kuma, amfani da addini don a yi cuwa-cuwar siyasa ƙarya ce. Anya! Ba irin wannan ƙaryar ta haddasa muna rikice-rikicen addini ba?  Bunza (2017)

4.0.2.1 Ƙarya a Neman Aure


Ƙarya na taimakawa wajen kashe aure a ƙasar Hausa a yayinda “zani ta tarar da muje” watau maƙaryaci ya haɗu da maƙaryaci a wurin neman aure, amma duk kansu ba su tantance junansu sosai ba har sai bayan sun kasance mata da miji wanda anan ne gaskiya za ta yi halinta ta hanyar ƙure ramin. Duk wani albishir da suka wa junansu kafin aurensu.

Bayan haka ƙarya na kasancewa sanadiyar mutuwar aure sakamakon rashin gudanar da bincike na asali a kan manemin aure, saɓanin abin da ya gabatar ko ta gabatar a lokacin neman aure.

Wannan na nufin wasu manema aure (maza ko mata) da ake neman aure na ba da jawabi wanda ba gaskiya ba ne a game dasu amma sai ayi kunnen uwar shegu har sai an kai ga ƙarshe sai a dinga samun matsala har a samu nasarar mutuwar auren.

Saurayi ya yima mace ƙarya cewa yana da kuɗi zai yi mata kaza kamar ya ce zai saya mata mota idan sunyi aure zai ba ta duk abunda take buƙata idan takai miliyan zai yi mata sai ta yarda ta aure shi sai bayan an yi aure sai ta gane cewa ƙarya yake yi mata ka ga tanan za a fahimci cewa ba gaskiya yake faɗa mata ba, nan take sai aure ya samu matsala har ya kai ga mutuwa.

Akwai wasu ƙaryayyaki da suke gudana a wannan yanayi na neman aure ga su kamar haka:

Ƙarya: A halin yanzu kusan ita ce mafi kusan abin da ‘yammata da samari ke yin amfani da ita domin neman wani matsayi wanda ba su kai shi ba. Suna yin wannan ne ba don komai ba sai don su samu shiga a wurin wanda suke son su mallaki zuciyarsa. Ƙarya a cikin neman aure ta kasu kashi-kashi kamar haka:

 

1.     Yin ƙaryar gida

 

2.     Yin ƙaryar Mota

 



 

  • Yin ƙaryar dangi

 



 

1.     Yin ƙaryar wurin aiki

 

2.     Yin ƙaryar sutura

 



 

1.     Yin ƙaryar gida: wannan ya ƙunshi abin da muka faɗi a baya yaro zai yi ƙaryar cewa, ai yana da gidaje, saboda ya san sai wanda ya mallaki gida ne zai zo da maganar aure. Yana kuma iya dubin yanayin yadda yarinyar ke buƙatar gida ya gaya mata fiye da tunaninta. Haka zai tsara wa yarinya yawan gidajensa domin kawai ya mallake zuciyarta da ta iyayenta.

 

2.     Yin ƙaryar Mota: wannan ma kamar wancan ne, zai iya aron motoci kala-kala yana zuwa wurin yarinyar da yake nema da su, ba zai yarda ya zo wurinta da irin motar da yazo da ita ba jiya. Kullum sai ya aro wata kala domin kawai ya samu yarinyar ta amince da shi a zuciyarta.

 

3.     Yin ƙaryar dangi: Saurayi kan yi ƙaryar dangi idan yana son ya mallaki zuciyar budurwa, haka kuma itama takan yi ƙaryar dangi domin ta samu galaba ga zuciyar saurayi. Amma an fi samun ƙaryar dangi a wurin maza. Za su ce ai su ‘yan dangin wani mai kuɗi ko mai mulki ne saboda su samu karɓuwa ga zuciyar wadda suke nema aure da iyayenta.

 

4.     Ƙaryar Wurin Aiki: Ita wannan ƙaryar samari ne suka fi yinta, sukan yi ta ne don su samu shiga ga budurwa, zai nemi wurin aikin da yasan ‘yan’uwan yarinyar ba su da alaƙa da wurin kuma ya san wurin babbar ma’aikata ce, sai ya yi ƙaryar cewa, shi a can yake aiki. Kuma ya gaya masu cewa, yana da babban muƙami a ma’aikatar.

 

5.     Yin Ƙaryar sutura: Wannan ma shi ne mafi sauƙin ƙarya daga cikin ƙaryaryakin da samari da ‘yanmata ke yi a yau. ‘Yanmata sukan yi aron sutura a wurin ‘yan wanki da ƙawayensu da yayyensu da dai sauran wurare. Haka kuma suna iya yin tariyar kuɗi su ɗunka kaya masu tsada duk don samarinta su ɗauka cewa ita wata ce, ko ɗiyar wani ce. Haka kuma su ma samari sukan yi ƙaryar kaya kamar su matan sai su je neman auren matan don dai su mallake zuciyar ‘yanmatan.

4.0.2.2 Ƙarya Bayan Aure


        Ita wannan ƙarya ba sai an buɗa baki an yi furuci ba, aikin da maigida ke yi shi ke nuna ta. Abin da muke nufi a nan shi ne, miji bai kai ƙarfin lalura ba sai ya dage sai ya matsa wa kansa domin kada matarsa ta ga kasawarsa. Wannan yana iya sa mijin ya faɗa kowace irin rayuwa, idan abin da yake samu bai kai abin da kashewa sai matsala ta shiga. Kuma zai iya cin bashi ma don ya faranta wa matarsa rai.

        Miji ne zai riƙa anso bashi don ya faranta ma matarsa rai idan an anso bashin sai ya kawo su ci mai kyau su sha mai kyau, su saka mai tsada a yi ta bushasha daga ƙarshe idan kuɗin sun ƙare sai a yi ta ganin laifin juna. Kuma a riƙa zuwa masa biyar bashi daga ƙarshe sai yaga duk fa a kan wannan ake yima kaza to bari in rabu da ita in huta tunda yanzu bama ganin mutuncina take yi ba.

Haka kuma miji ko mata suna iya yin ƙarya a cikin lafuzzan su na yau da kullum. Wannan ma yana taimakawa wajen lalata aure. Idan miji zai riƙa yi wa mata ƙarya kullum to za wayi gari wata rana gaskiya ta bayyana, daga nan kuma sai rashi yarda ya shaga tsakani. In kuma mata ce ke yi wa miji ƙarya to wata rana ita ma gaskiya za ta bayyana asiri ya tonu, daga wannan ranar zai kasance bai yarda da abin da ta faɗa.

Rashin faɗar gaskiya yana hardasa rashin aminci tsakanin mata da miji, rashin aminci kuma yana hardasa zubewar mutunci, rashin mutunci kuma yana hardasa rashin jittuwa, rashin jittuwa kuma yana hardasa sakin aure. Wannan duk ƙarya ce sanadi.

4.0.3 Ƙarya a Tsarin Siyasarmu:


Yahudawa da suka ƙirƙiro demokraɗiyya da gangan suka yi domin a ba ƙarya damar ta lalata makomar mutanen ƙwarai. Ku dubi irin halin da ƙasashenmu suka shiga na bushewar tattalin arziki. Masu jagorantar hukumominmu da ake bai wa albashi cikin arzikin ƙasarmu sun fi ƙasarmu arziki. Daga su sai `ya’yansu da matansu da `yan korensu ke more wa arzikin ƙasa, me ya haifar da BOKO HARAM? Me ya zaburar da NIGER DELTA MILITANTS? Me ya zuzuguta farfaɗo da tatsuniyar BIAFARA? Mene ne musabbabin ƙiyayyar yunƙurin raba ƙasa? Waɗanda suka yi ɗunɗu bisa taskar arzikin ƙasa ne ke son ko a ba, su ɗana, ko a mutu har liman; domin sun san wuraren da suka voye `ya’yansu da matansu. Waɗannan maƙaryata da suka tara dukiyar ƙarya, su talaka zai je ya yi musu banga, a kashe ya kashe. Wai su ne ake yi wa addu’ar samun galaba a Masallatai da Coci. To, kowane azzalumi maƙaryaci ne, ɗan ta’adda maƙaryaci ne, mai tallan maƙaryata don a so su, maƙaryaci ne. Matuƙar a kwai maƙaryata cikin masu jagorancin hukuma, babu sauran zaman lafiya. Mai musun wannan batu ya je Tubali ya tambayi abin da Malamin kiɗi Narambaɗa ya ce :

Jagora:     Sarki ka ga mutum shidda

Yara:       Babu mai zaunawa lafiya da su

                :Wanga azuji wanga butulu

                :Guda ashararu guda mavannaci

                :Wanga guda tsohon munafuki

Yara/uba : Akwai wani na nan mai ƙure mutum

Gindi :      Ya ci maza ya kwan yana shire

                :Gamda’aren sarki Tudu Ali.

Narambaɗa “Azuji” ya fara ambato wato maƙaryaci kuma mai ƙiren ƙarya. Yau duk waɗannan miyagun shida su ne `yan gaban goshin gwamnatocin da muke zave. Me ya sa komai akai muna ba mu da kaico! Shugabanni na kallon ana yi muna yankan rago sai ƙara sawo motocin alfarma suke, da fafitikar ƙara wa kansu albashi da alawus alawus, mu ko ga mu nan ga `yan ta’adda a yi tayi! Anya!

Ka gaje mu an yi ma dagaci mai takarda,

          Ko kuma Emiya cikakke Cif had da sanda,

          Kuma kun sa ido tsakaninmu da `yan ta’adda,

          Sai ku shige kuna ta shan farfesu da ganda

                   Ai gadonku kare dukkan jama’ar ƙasag ga.

(Sambo Wali: Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana, baiti 35)

4.0.4 Ƙarya a Gidajen Jaridu:


Aikin jarida daɗaɗɗen aiki ne, Mahdi mai dogon zamani. `Yan jarida su ne idon hukuma ga abin da ba ta hango ba. Su ne wakilan talakawa, ga abin da hukuma ke gudanarwa. Su ne kunnen jama’a ga abubuwa da ke faruwa ciki da wajen ƙasarsu. Babban burin `Yan jarida a kan kowane irin al’amari a yi shi filin wuri dabon Ɗankama, komai ya zama twa-da-twa wankin ɗan kanoma mashaya. Su ke gyara wa shugaba zama idan ya yi wawan walle ko ya yi tunƙa da walwala. Ga saninmu, suke yayyafa wa ƙurar yaƙe-yaƙe da tarzoma da zanga-zanga, da rikice-rikicen addini da ƙabilanci da siyasa ruwa, sai ƙurar ta lafa a fahimci juna, a share jinni , a koma wasa.

Bai kamata a samu ƙarya ko ƙiris cikin riwayar `yan jarida ba. Bai kyautu a ce, `yan jarida ke tallar `yan siyasa ba, ƙiri-ƙiri a mayar da fari baƙi, baƙi ya koma fari fes. Ba dole sai sun yi takin saƙa da hukuma ba, amma ka da su yarda a sa su ƙarya. Duk wani labari da za su yaɗa su tabbata babu mai ƙaryata shi domin su ganau ne ba jiyau ba. Zuguguta kanun labarai don jawo hankalin masu sauraro ko masu sayen jarida yaudara ce da ƙarya. Ya kamata `yan jarida su sani cewa, wata magana sarakkuwar baki ce. Me ya haddasa rikicin sarautar Musulunci wato tsakanin Dasuƙi da Macciɗo? Me ya haddasa turnuƙun hayaƙin zaven June, 12? Me ya harzuƙa wutar tawayen Ojuku? Idan za mu lura, yaƙin basasan Nijeriya da `yan jarida aka yi amfani. Mun san, babu makawa, babu duniyar da ba a yi da `yan jarida. Idan suka yi wa gaskiya riƙon kwabon makaho, suka yi wa ƙarya hurjin mussa dole a tabbata Borno gabar take. Ga wani saƙo na wani ɗan jarida zuwa ga `yan uwansa `yan jarida yana cewa:

Yau bari dud da `yan jarida nika son tavawa,

          Masu biyar muhimmai su sami abin tavawa,

          Niyyar kowane dai ya samu kuɗin kashewa,

          Sambo Wali ga yau ko gidanai bai ragawa,

                   Don na san da dama suna sabga hakan ga.

          Yau kuma dud da `yan jaridar waje ban bari ba,

          Na san masu aibu na in kai ba ka sani na,

          Zwazwafa yamutsi sukai kowa bai kula ba,

                   Kowace nahiya suna tabka irin hakan ga,

          Tambaye-tambayanku na firgita masu lura,

          Wasu don tambayenku sun tabka tulin kurarra,

          Magana ta fi dag ga zagar bunu ku lura,

          In har ta fito da zafi a buga a barra,

                   Komawatta ba shi yi sai an kwava darga

 

(Sambo Wali: Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana, baiti 16-18)

Haka kuma, ya kamata a ce, masu wasannin kwaikwayo da finafinai sun yi tsayin daka na ganin an hana wa ƙarya wurin sake jiki a ƙasarmu. Duk mai hulɗa da kafofin sadarwa na zamani ya san da cewa, maganganun da ke bayyana a ciki ba a tantance su. Magana ɗaya za a yi mata launi arba’in cikin dare ɗaya. An mayar da wuraren kamar dandalin kece raini, kowa ya faɗi abin da yake so, kan wanda yake so, ga abin da bai ji ba, bai ga ni ba. Me ya sa jama’a suka fi kulawa da kafofin yaɗa labarai na waje irin su BBC, CNN, VOA, FRANCE da makanatansu? An san ba su cika kintaci-faɗi ba, ba su zaƙewa ga yin fadanci, a gaban kowa suna tsage gaskiya. Ban ce, babu laifi gare su ba, kamar yadda Sambo Wali ya hango, sai dai suna sara suna duban bakin gatari. Mutane irinmu bai kamata a ce, sun yi mutunci da ba mu iyawa ba. Bunza (2017)

4.0.4 Hanyoyin Magance Ƙarya
Hanyoyin magance ƙarya masu sauƙi ne ba kamar hanyoyin da za a bi wajen yinta ba. Domin duk mai tsoron Allah ba zai yi ƙarya ba domin Allah ya faɗi abunda zai yi wa masu ƙarya a ranar alƙiyama. Acikin Alƙur’ani Mai Tsarki sura ta ta ɗari da bakwai aya ta ɗaya (107;1)  Allah yana cewa, “ko kaga masu ƙarya ranar sakamako”. Haka kuma a sura ta tamanin da uku (83) aya ta goma (10) Allah yana cewa, “kwaren azaba ya tabbata ga maƙaryata”.

Wannan tsoratarwa ce daga Allah a kan masu yin ƙarya don haka duk mai tsoron Allah da azabarSa, ba zai yi ƙarya ba sakamakon ƙarya kunya, to me zai sa mutum ya yi abunda zai kunyatar da shi? Ƙarya ba ta da amfani Hausawa na cewa, “ramin ƙarya ƙurare ne” ma’ana idan mutum na ƙarya nan take yaji kunya.

Allah ya hana ƙarna domin ba ta da fa’ida sai ƙasƙanci duniya da lahira. Cikin Alƙur’ani sura ta sha ɗaya (11) aya ta goma sha takwas (18) Allah yana cewa, “wane ne ya fi zalunci wanda ya ƙirƙiroma Allah ƙarya waɗannan su ne za a zo da su ga Ubangijinsu sai masu shaida su ce waɗannan su ne suka ƙirƙiro ƙarya ga Ubangijin su sai Allah Maɗaukakin Sarki ya ce la’antar Allah ta tabbata ga maƙaryata. Kaga idan mutum yana so ranar ƙiyama ya tashi cikin tsalkaka to, ya daina ƙarya. Allah ya fitar damu dayin ƙarya.

A cikin Hadisin Manzon Allah (S.A.W) yana cewa; “alamomin munafuki uku ne, idan ya yi magana ya yi ƙarya, idan aka ba shi amana ya ci, idan ya yi alƙawari ya saɓa, yana iya zama munafuki to Allah ya tsare mu da shiga cikin waɗannan halaye.

Babbar hanyar da za kuɓuta daga wannan ita ne, barin ƙaryar. Idan mutum ya tsalkake kansa ya bar ƙarya ya ɗauke ta abin ƙyama, sai ya zauna lafiya. Idan aka shaide shi cewa baya ƙarya to komai ɗabi’unsa sai ka tarar yana da sauƙin al’amari. Haka ita ma mace, idan ta kasance ba ta ƙarya, mijin ya shaide ta ba ta ƙarya to duk yarda da kyautatawa yana yi mata.

Babi Na Biyar

5.0.1 Jawabin Kammalawa
Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai Kowa Mai komai, Mahaliccin sammai da ƙassai da ya bamu ikon kammala wannan aikin Bincike. Don haka a nan ne za mu naɗe tabarmar wannan bincike. Kamar yadda aka gani a baya mun raba aikin nan gida biyar bisa ga tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko ya ƙunshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da aka fuskanta.

A babi na biyu kuwa kamar yadda doka ta tanadar mun kawo Waiwaye A Kan Ayyukan da Suka Gabata kana muka yi bayanin Salon Nazari da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa a nan ne muka yi Tsokaci a kan ƙarya, da Ma’anar ƙarya da bayani a kan Ƙarya da Al’ada inda har muka ce ba su haɗu, babu jittuwa a tsakaninsu mun bayar da kashe-kashen ƙarya yayin da muka ce ta kasu kashi biyu wato Ƙarya ta Furuci da kuma Ƙarya a Aikace. Mun kawo bayani da kowannen su domin mu bayyana yadda suke.

A babi na huɗu kuma nan ne muka yi bayanin yadda Ƙarya take taka rawar gani wajen durƙusar da tarbiyyar al’umma, yayin da muka kawo ƙarya cikin zamantakewa inda muka dubi neman aure da zaman aure da siyasa da ayyukanmu kamar na jarida da yadda abubuwan suke gudana a yau. Haka kuma mun kawo hanyoyin magance barazanar ƙarya wanda duk ya bi su kuma zai kuɓuta daga barazanarta.

Sai a wannan babi na biyar inda muka yi yunƙurin naɗe tabarmar wannan bincike namu, ga shi kamar yadda aka tanada muka yin jawabin kammalawa daga shi kuma sai shawarwari da za mu bayar ga mai karatu.

5.0.2 Shawarwari


Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu ɗalibai shawara su mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin ƙoƙari gwargwadon hali. Su kasance masu ƙwazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to su yi ƙoƙari su ɗora daga inda muka tsaya na wannan bincike.

Muna kira ga wasu waɗanda ba nazarin wannan kundi sukai ba da su yi ƙoƙari su koyi darussan da ke cikin wannan kundi kar su yi ƙasa a guiwa su kasance masu kyautatawa da neman ilimi da kauce wa abin duk da za ya sa a yi masu kallon da bai dace ba.

Manazarata


Post a Comment

0 Comments