https://www.amsoshi.com/contact-us/
Rubutawa: Shehu Hirabri
08143533314
https://www.amsoshi.com/game-da-mu/
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Wanda Allah ya ba,
A bi shi shi ad daidai,
Wad’anda ba su buk’atakka,
Ga su nan sun muzanta,
Yara: Tunda ba su da komai,
K’asa kuma ba su da kowa.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Baba d’an Audu,
Na Audu mai gidan Haji ‘Danba’u,
Na Alhaji Mani mai yi ma yak’i tahiyayya,
Yara: Mai buga ga mak’oshi,
Dambe da kai ba ya da dad’i.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Adamu Bakane,
Ka yi dangali bana ka huta,
Adamu Bakane,
Mai gida baban Shehu da Inuwa,
Yi zamaninka ka huta,
K’attan banzan ga masu kuri Illela,
Yara: K’yale su da yara suka ruga musu kashi.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Duk bak’o ya shigo a birnin Illela,
Sai ka ji ya ce,
Garin ga maye ni ka shakku,
Bak’in angulu,
Ka yi hurhura ka gama aski,
Yara: Kai ka shafa mana lahiya,
A bar ce muna mayu.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Ar! Ga wani ya yi takarab bayis,
Ta ruhe da shi ya hwasa kuka,
Yanzu swata yaka nema,
Bak’in dutse kakai ka iske,
Yara: Tun da d’an asali ba ya kasuwanci da k’azami.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Buhun lalle yay kama buhu bai yi buhu ba,
Shi buhun lalle ya yi kama buhu ba ya da nauyi,
Da ina tsoron wane yanzu na bar tsoronshi,
Yara: Tunda bakin garkassu munka watce masa kaya.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Shi buhun lalle ya yi kamar buhu ba ya da nauyi,
Shi buhun lalle yai kamar buhu bai yi buhu ba,
Da ina tsoron wane yanzu na bar tsoranshi,
Yara: Wanga lokaci ba ka da k’arhi.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Bambad’awan lokal,
Su wane sank’ira,
Kada ka hwad’a ‘Danba’u,
Yara: Wanga lokaci ba ka da k’arhi.
Jagora: Da kai nike kai wane,
Rak’umi d’an atalolo bana ina za ka da kaya?
Yara: Za ya je ‘bantalagindi,
Inda mata suke banza.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Godiya Haji Hadi,
Yara: Tunda hairan yaka yo man.
Jagora: Godiya Haji Hadi,
Yara: Saboda hairan yaka yo man.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Mijin Hajiya Maryama Sadauki,
Yara: Dattijo baba Allad dad’a girma. ×2
Jagora: Mijin Asma’u,
Yara: Dattijo Allad dad’a girma ×3
Jagora: Mijin su Umaima,
Yara: Dattijo Allad dad’a girma×2
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Sanusi d’an Wali,
Yara: Yadda yay yi min,
Ban iya ramma.
Jagora: Sanusi na gode,
Yara: Yadda yay yi mini,
Ban iya rammai,
Jagora: Sanusi d’an Wali,
Yara: Yadda yay yi man,
Ban iya rammai.
Jagora: Sarkin dawaki na gode,
Yara: Yanda yay yi man,
Ban iya rammai.
Jagora: Modi bakanike Modi,
Yara: Yanda yay yi man
Ban iya rammai,
Jagora: Bakanike Modi,
Yara: Yanda yai yiman,
Ban iya rammai.
Jagora: Godiya sarkin Shanu,
Wanda yai mani,
Yara: Yanda yay yi man,
Ban iya rammai.
Jagora: Godiya ga sarkin noma,
Yara: Tunda ya kyauta.
Jagora: Ina Sanusi d’an Wali?
Ubangidan ‘Danba’u abin ka yi mani,
Yara: Yanda yay yi min,
Ban iya rammai.
Jagora: Gaishe ka sarkin darabto,
Yara: Yanda yay yi min,
Ban iya rammai.
Jagora: Sarkin alaru na gode,
Yara: Yanda yay yi min,
Ban iya rammai.
Jagora: Magaji Darma ka kyauta,
Yara: Yanda yay yi min,
Ban iya rammai.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Godiya wajen Mustapha,
Ina alkali Alhaji ya gode,
Yanda yai man,
Ban iya rammai.
Jagora: Haji Mamman mai mota baba na gode,
Yara: Yanda yay yi min,
Ban iya rammai.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Koma ganin bushiya a birnin Illela,
K’ila ko ta tahiyat ta?
Tana nan Illela,
Yara: Don ku jiya mun ganat,
Ga ‘yan yara ga hannu.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Baba Salihu ya yi d’a,
Alhaji na gode,
Yanda yai man,
Ban iya rammai.
Amshi: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
Jagora: Wanda Allah ya ba,
A bi shi shi ad daidai,
Wad’anda ba su buk’atakka,
Ga su nan sun muzanta,
Yara: Tunda ba su da komai,
K’asa kuma ba su da kowa.
Jagora: Rik’a bari wargi,
Karo da kai ba ya da dad’i,
Isuhu Musa ciyaman,
Kai ne suka sauna.
https://www.amsoshi.com/contact-us/
- Home
- _Game Da Mu
- _About Us
- _Publish
- _Services
- _Advertise
- _Contact Us
- AL'ADA
- _Maguzawa
- _Zamantakewa
- _Abinci
- _Magunguna
- _Bukukuwa
- _Sana'o'i
- _Gine-Gine
- ADABI
- _Azanci
- __Karin Magana
- __Kacici-Kacici
- _Waƙoƙi
- __Waƙoƙin Baka
- ___Na Gargajiya
- ___Na Mawaƙa
- __Rubutattun Waƙoƙi
- __Waƙoƙin Zamani
- __Poems
- _Zube
- __Almara
- _Wasan Kwaikwayo
- __Finafinai
- HARSHE
- _Ƙirar Sauti
- _Tsarin Sauti
- _Ƙirar Kalma
- _Ginin Jumla
- _Ilimin Ma'ana
- _Walwalar Harshe
- _Fassara
- EDUCATION
- KIMIYYA
- KWASA-KWASAI
- BIDIYOYI
0 Comments
Rubuta tsokaci.