Rubutawa: Shehu Hirabri
08143533314
Amshi:
Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: A jahar Sakwkato,
Nake magana,
Ciyamominmu na PDP,
Su goma sha biyar daidai,
Mai gaskiya Obasanjo,
Zance da kai yi yai daidai,
Ka gaya ma ciyamomi,
Su riƙe mai kiɗansu ‘Danba’u,
Na zare Ido ina dubi,
Yara: Ni hay yanzu ban ga komai ba.
Jagora: Na zare ido ina dubi,
Yara: Ni hay yanzu ban ga komai ba.
Jagora: Jama’a kun shige inwa,
Yara: Mai waƙarku na cikin rana.
Jagora: Im jama’a kun shige cikin lemat,
Yara: Mai waƙarku na cikin rana.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Yau duk ‘yan uwanmu sun yi sharaf,
Yara: Ni ko an ƙi yin su garkata.
Jagora: An ce mani an yi rabon kuɗi,
Manya da yara sun samu,
Amma an ƙi ba su ‘Danba’u,
In dai na yi hanƙurin rowa,
Yara: Ka sani ba ni hanƙurin ƙarya.
Jagora: In na yi hanƙurin cizo,
Yara: Ka sani ba ni hanƙurin yaga.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Wani ya sha karo da ɗa Musa,
Ado na ji Bala ya kasai,
Can nig gane shi Dagawa ×2
Wawa ya ɗau buhuhunan lalle,
Yara: Ya ce za ya kasuwa Muza.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Yale mai mota,
Ka kai ɗa,
Na san ka fi zuciya sauri,
Ƙarhe bakwai da sassahe,
Daga Sakkwato birni ka tashi,
Ka je cikin garin Legas,
Ka dawo Kaduna ka sha mai,
Sai ka wuce Kanon Dabo,
Yale ka gangaro garin Yabo,
Yara: Yadda na ɗau agogo nid duba,
Ƙarhe goma sha biyu rana.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Yale mai mota,
Ka kai ɗa,
Na san ka fi zuciya sauri,
Ƙarfe bakwai da sassahe,
Daga Sakkwato birni ka tashi,
Sai ka wuce garin Legas,
Ka je Abuja ka huta,
Ka dawo Kaduna ka sha mai,
Ka gangaro Kanon Dabo,
Yale ga sunta’ba gari Yabo,
Yara: Yadda ni ɗau agogo na duba,
Ƙarhe goma sha biyun rana.
Jagora: Wani ciyaman na duba,
Ƙazami ne ku mun san shi,
Taro munka je da shi Legas,
Kwana uku bai yi wanka ba,
Yara: Yada ya mammatso ni sai nic ce,
Tahi da nan kana yi min wari.
Jagora: Ƙazamin ciyaman mun san shi,
Taro mun ka je da shi Legas,
Kwana uku bai yi wanka ba,
Yara: Yada ya mammatso ni sai nic ce,
Tahi da nan kana yi man wari.
Jagora: Wawa!
Yara: Tahi da nan kana yi man
wari,
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Saga!
Yara: Tahi da nan kana yi man
wari.
Jagora: Kansiloli daban-daban Audu,
Kasiloli daban-daban Ada,
Ga kowane yana ta ƙiba,
Ɗan tsuntsun tsorolo tsomodo,
Yara: Shi har yanzu bai yi
gwa’bi ba.
Jagora: Kansiloli daban-daban Ada,
Kowansu na ga na ta ƙiba,
Ɗan tsuntsu tsorolo tsumodo,
Yara: Shi hay yanzu bai yi gwa’bi ba.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: A na Rabi mijin Amina,
Yara: Ƙara shirin duniya ga shi
ya hi.
Jagora: Haji Sabo Madawaki na gode,
Ban rena da ƙoƙarinai ba,
Haji Sabo Madawaki can Yabo,
Ban rena da ƙoƙarinai ba.
Jagora: Uban jam’iyyar nan sanata,
Ban rena ƙoƙarinai ba.
Jagora: A na gode mai Ali mai goro,
Yara: Ban rena da ƙoƙarinai ba.
Jagora: A dole in gode Ali maigoro,
Yara: Ban rena ƙoƙari nai ba.
Jagora: A Baba injiniya a gaishe ka,
Yara: Ban rena ƙoƙari nai ba.
Jagora: A Bala ɗan Audu Sifawa,
Yara: Ban rena ƙoƙari nai ba.
Jagora: Baba Bala ɗan Audu Sifawa
Yara: Ban rena ƙoƙarinai ba.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Na ji mutane suna ta gode ma,
Yara: Sun ce ka yi ƙoƙari Yabo×2
Jagora: Baba injiniya ubangari zaki,
Ban rena ƙoƙarinai ba.
Jagora: In dai na je garin Yabo,
Yaya zan barin garin Yabo,
Ni kam ban ga maigidana ba.
Jagora: Yale mai mota na gode ma,
Yara: Ban rena ƙoƙarinai
ba.
Jagora: In Yale mai mota mutumina ne,
Yara: Ban raina ƙoƙarinai
ba.
Jagora: Sanata Aliyu ɗan Garba,
Yara: Ban rena ƙoƙarinai
ba.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Jagora: Kun ji uban jam’iyya,
Dattijo senata,
Aliyu ɗan Garba,
Yara: Ban rena ƙoƙarinai
ba.
Jagora: A na gode wa Sabo na gode,
Yara: Ban rena ƙoƙari nai ba.
Jagora: A Madawakin Yabo ina Sabo?
Yara: Ban rena ƙoƙarinai ba.
Jagora: A Sani Ɗanmaliki,
Yara: Ban rena ƙoƙarinai ba.
Jagora: Sani Ɗanbaba na gode,
Yara: Ban rena ƙoƙari nai
ba.
Jagora: A Sani Ɗanbaba mutumena ne,
Yara: Ban rena ƙoƙarinai
ba.
Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Yaro: Amadu mai ɗamaray yaƙi,
Ware hannunka tunda ka yi kisa,
Wancan ne wanda ka koɗa,
Kwana nai biyat yana zawo,
Kuma ‘ya’yan Yabo sun ka faɗi.
Jagora/Yara: Wai har yanzu bai yi wanka ba.
Yaro: Amadu mai ɗammaray yaƙi,
Ware hannunka tun da ka yi kisa,
Wance ne wanda ka koɗe,
Kwananai biyaf yana zawo,
Mutan Yabo sun ka shaida mini,
Yara: Wai hay yanzu bai yi wanka ba.
Jagora: Ciyaman bugun ciyamomi,
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
Yara: Ciyaman bugun ciyamomi,
Bala ba a jan ka ɗan Musa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.