Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Jam’iyar DPN (Alhaji Musa Danba’u Gigan Buwai)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

www.amsoshi.com

Rubutawa: Shehu Hirabri 
08143533314

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Muna nan bisa gaskiya,

Kar mu katce ‘yan uwa,

Yara:    Kowa ya tsare gaskiya,

Ba ya kunya duniya,

Ba ya kunya lahira.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Tana da nuhin,

Gayra birni da ƙauye mun sani,

Yara:    Ta ha’baka noma da ilmi,

A zauna lahiya.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Mu ba duba mukai ba,

Kuma ba tsafi mukai ba,

Roƙon Allah muke,

DPN dai ta hau,

Yara:    Mazanmu da matanmu,

Kowa ya zauna lahiya.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Ni mamaki nake,

Mai duba shi da boka siyasa guda akai,

Mai duba ya buga ya ce su za su ci,

Boka ya yi tsahi da ‘yan kaji bakwai,

Kuma Allah yai hani tona siri nai a ji,

Yara:    To du a gama ta sai sun yi kunya duniya.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Ina mai hwara gaba,

In siyasa ta zaka,

Wane sai ka katanta ne,

Ka ce kai ɗai za a bi,

Talakawan sun gaji,

Yara:    Yanzu ba su biyarka,

Sun gane sheri ɗai kake.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Ina horon wane,

Kullun ya kauce ya ƙiya,

Wane ka bar neman shiga inda ‘yan taron daba,

Yara:    Siyasar ‘yan gurguzu,

Ai siyasar ƙeta ce.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Ina jin tsoron mutum,

Mai buƙatar gardama,

Ban son haka nan ba,

Wallahi Allah ya sani,

Ina kallon wane ya kama daji,

Yaro:   Wane dawo ga hanya,

Inda kowa ka murna ya hi kyau.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Baƙin kwaɗayin wane,

Ya kai shi ɗaukar arkane,

Yara:    Ga jirgin Makka,

Ya taka motar Ɗandume.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Na san kissa kare,

Ɗauke ƙahwa da ya yi,

Ba ciwo ne takai ba,

Yara:    Tsoron ya ka yi,

A korai da manyan dutsuna.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Salamu alaikum,

Mugunta mutum na nan ciki,

Sai in ka ba da hannuka,

Mugu ya riƙe,

Yara:    Kana neman ka zage hannu,

Ya dwage ma ido.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Mutane ku yi hankali,

Da sarkin ‘bannan kare,

Yana iya canye awakinku,

In ta zaburu,

Yara:    Ya ko runtce ido,

Ya dawo ya ce ba shi ba ne.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: In tafiya tai tsawo,

Kai amali ka tsarsuwa,

Jaki sarkin kuɗa,

Yara:    Duk yada ka so yakai,

Inda zango bai zuwa.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Ni na san ungulu,

Kolo rage taƙama,

Taƙamar banza shi kai,

Yara:    Yana iya tahiya,

Da ya iske mushe yai ta ci.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Sarkin ƙarya ga,

Don Allah wane a hankali,

Yara:    Don ko maibogaza,

Na shi time ya wuce.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Na gane bagamniyarka,

Ɗan tashin hankali,

Duk wada ka so ka kwaso ta,

Allah ya hana.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Komi kuɗin mutum,

In ba jama’a gare shi,

Aikin banza yakai,

Ni ko yau nim mace,

Buƙata ta biya,

Tunda mai kuri da nerag ga,

An ƙare da shi,

Yara:    Ba ya da kowa,

An bar shi yawo ɗai yake.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Ni na san maitatsine,

Wuyal lamari garai,

Don Allah dai mutane,

Ku bar yarda da shi,

Yara:    Ko an yi shiri da shi,

Watce tsarin nan yakai.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Yaro:    Don Allah masu ganga ku shasshafa min,

Kai Adamu mai kalangu ku dage ya hi kyau,

To ni dai na ji tsoro ga harka duniya,

Ga wani ɗan takara ya yi gunki ya aje,

Tun da ya shiga takara.

Jagora:  Yara: Ha da salla ya bari.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Yaro:    Don Allah ku mutane,

Ku bar ‘barnash shiri,

Don Allah ku mutane,

Ku bar ‘barnash shiri,

Shi gurja gunda ‘barna siyasa tai yakai,

Ga hanyar gaskiya sai ku kauce.

Jagora/Yara:   Wa zai za’be shi?

Jagora: Tunda canye ‘yan kaji shikai.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Sarkin yaƙin jaha.

Ina Ɗan’asali a gaishe ka,

Alhaji Arzika,

Uban Nasiru baba,

Kai ka watce Ameriaka,

Babu shakka mun sani.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Yaro:    Mi ar ranar kilinge,

Ga harkad duniya,

Ko ga shi cikin gida,

Kyalla shurewa takai.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Yanzu ko ga shi cikin gida,

Yara:    Kyalla shurewa takai.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Adamu Bakane,

Uban Inuwa zakin duniya,

Yara:    Uban Shehu maza suna son su motsa ka hana.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Bari dai in tada Babanmu,

Aiki ya hi kyau,

Bari dai in wasa babanmu,

Harka ta hi kyau,

Haji Ila Gada na Jumai,

Mutum mai hankali,

Haji Ila Gada na Laraba,

Baban Nasiru,

Yara:    Mijin Lantana,

Maganin mai sheɗana.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Haji Ila Gada,

Datijo ne mai hankali,

Mutanenmu na Sakkwato,

Ga jirgin gaskiya,

Yara:    Wanda ya ƙi shiga shi,

Dun nashi ‘yanci ya ‘bace.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Alhaji Bawa na Araba,

Bawa muzakari,

Yara:    Mazajen Araba,

Komai ka ciyo ya bari.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Sahabi na Amamata,

Sahabi Dattijo,

Maimaganin taron kawai,

Gabas bakin wauro,

Kawatce ‘yan banda ƙasa.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Umaru Garu Goronyo,

Sarkin yaƙi kake,

Ka kara Shirawa,

Ƙwarai tunda yaƙi ya zaka.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Ƙasar Sabon Birni,

Zan je mu iske salihu,

Haji Salihu Ɗanbakwai,

Ko da ɗai Gambo kake,

Yara:    Ruhe masu gada-gada,

Gas su ‘bata ma shiri.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Alhaji Umar Kalanjeni,

Mutum mai ƙorƙari,

Yara:    Yamma ba a barazana,

Tun da Umar ya hana.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Yaro:    Siyasa ba faɗa,

Tun da ba gaba ba ne,

Siyasa ba faɗa,

Tunda ba gaba ba ne,

Jagora/Yara:   Amma jiya wane,

Ya fara ɗwaɗin adduna.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: A na gani jiya wane,

Yara:    Ya fara ɗwaɗin adduna.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Yaro:   Sai na faɗi wagga,

Ka zo a murɗe min wuya,

Sai na faɗi wagga,

Ka zo a murɗen min wuya,

Kir tahi su gwaguwa hagunan tahi karkace,

Siyasa ke ɗai kike.

Yara:    Kai ku ji ƙwagowa har da fusta ya buga.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Na gode Garkuwa,

Haji Bello Muzakari,

Yara:    Ban rena mai ba,

Ya ba mu hairan mun yaba.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Gwadabawa za ni na,

In ishe maigida Lumu ubanmu ne,

Yara:    Ban rena mai ba,

Ya ba mu hairan mun yaba.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Alhaji kiryo na yabo,

Na gode ƙwarai,

Yara:    Ban rena mai ba,

Ya ba mu hairan mun yaba.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagoras: Ina Haji Kiryo na Yabo,

Ubana ka yi ɗa.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Abdulkadir Sani

Na yaba,

Yara:    Ban rena mai ba,

Ya ba mu hairan mun yaba.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora: Haji Modi na yabo,

Dattijo ne mai ƙoƙari,

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Jagora:  Ina Sarkin albasa,

Haji Maidobo kka yi ɗa.

Amshi: DPN ta yi daidai da ‘yan Nijeriya,

Alheri yanzu kowa buƙatatai yakai.

Post a Comment

0 Comments