Ticker

6/recent/ticker-posts

Sassaka A Garin Dakin-Gari: Tasirin Zamani A Kan Gargajiya (7)

NA

ABUBAKAR ALIYU
1310106004

KUNDIN DIGIRI NA FARKO NA HAUSA (B. A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NAJERIYA. JAMI`AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO

www.amsoshi.com

BABI NA BIYU

TARIHIN SASSAK’A A GARIN D’AKIN-GARI


Shimfid’a


A wannan babi na biyu mai taken tarihin sassak’a a garin D’akin-gari na da k’ananan sassa kamar dai yadda ayani zai biyo. A sashe na biyu mai taken tarihin garin D’akin-gari sashen zai kawo tarihin garin D’akin-gari ne watau yadda ya kahu har ya zuwa inda yake a yanzu. Sai kuma ma’anar sassak’a wanda shi ma a wannan sashe za a yi bayanin ma’anar take a tak’aice.

Haka kuma za ayi bayanin tarihin sana’ar sassak’a a grin D’akin-gari wanda shi ma bayanin ne a kan sana’ar sassak’a a garin D’akin-gari. Daga nan kuma sai yanayin tattalin arzikin mutanen garin D’akin-gari wanda shi ma bayani ne a kan tattalin arzikin garin. K’ari ga haka sai yanayin k’asar D’akin-gari. A nan za a kawo bayanai ne na yadda yanayin k’asar take. A k’arshe sai bayanin kammalawar babin baki d’aya.

Tarihin Garin D’akin-gari


An kafa garin D’akin-gari a shekarar 1810 wanda suka kafa ta wasu Kabawa ne ko kyangawa maharba. Sunan babbansu Hodi Jan K’osai su wad’annan mutane sun fito ne daga Birnin Kebbi. Bayan an ci Birnin Kebbi da yak’i cikin 1805, sai shi Hodi Jan K’osai ya gudo da shi da d’iyansa da sauran wad’anda suka biyo shi suka taho kyangakwai suka zauna ‘yan shekaru . daga baya ya taso ya taho ya kafa D’akin-gari a 1810.

Sana’arsu ga lokacin ita ce harbin namun daji da kuma noma. Nan babu ruwa sai sun yi tafiyar mai d’an nisa su d’ibo ruwa a gulbi.

Yanda Sunan D’akin-gari Ya Samu


Bayan Jan K’osai da iyalinsa sun zauna sai suka gina d’akunan kwana kuma Jan K’osai ya gidan wani d’aki babba inda shi ke aje gari da namunsa na harbi. Idan wani mutum ya biyo nan wajensu sai su ce a kai shi can d’akin gari shi sha ruwa in sun ba shi abinci ya ci ya sha ruwa. Idan ya tafi gaba sai ya ce daga wurin su Jan K’osai nake sai a ce suna ina sai ya ce suna can wani wuri can da ake kira wai d’akin-gari. Da haka sunan garin D’akin-gari ya samu.

Sun Gane Inda Ruwa Suke


Bayan Hodi Jan K’osai sun zauna nan D’akin-gari sai wasu Fulani masu kiyon shanu suka zo suna kiwo. Sunan babbansu Ja’oji. Shi Ja’o’ji wurin yawonsa na kiyo sai ya ga wani sa daga cikin shanunsa ya shiga wani gulbi ko da ya duba ciki sai ya ga wani d’an tabkin ruwa daga nan sai ya koma  ma sarkinsa. Da ya koma sai ya fad’a wa mutane suka tafi suka sare gulbin suka rik’a d’aukar ruwa a nan.

Da wannan tafki ya k’afe sai suka gina rijiya a nan. Sunan rijiyar rijiyar Argida amma yanzu ta mutu. Wurin da take shi ne na nan susa da marina ta bakin kasuwar garin D’akin-gari.

Sun Tafi Zagga Sun Samo Malami


A lokacin da Jan K’osai ya ga mutane na taurwa garinsa saboda hatsin da suke nomawa ga namun daji da sauk’in samu ya tuna irin cin da aka yi masu can da suna Birnin Kabi saboda rashin addini sai ya tafi Zagga ya rok’o malami sunan Malamin Bosu. Ya ce shi taho nan D’akin-gari shi zauna shi koya ma yaransa addini. Bosu ya yarda ya komo D’akin-gari da zama ya ci gaba da karantarwa.

Bosu ya Zama Shugabansu Na Addini


Lokacin da Bosu ya komo D’akin-gari a 1815 ya zama limaminsu kuma malimsu mai koyar musu addini. Daga nan sai mutane suna zuwa wurinsa don neman ilimi.

Hodi Jan K’osai


Hodi da jama’arsa suna zaman gari bai dame su ba saboda mafi yawan sana’arsu a wannan lokaci noma da kiyo da harbi ne. zaman gari bai dame su ba don haka in zai yi tafiya sai ya bar ma Bosu gari ya rik’a masa ya zama wakilin gari kenan har Hodi ya dawo. Dan haka in an yi bak’o can za a kai shi ko wasu batutuwa suka faru ana yin su a garkar liman Bosu. Saboda shi kullum yana gida zaune dan mutane na zuwa wurinsa dan d’aukar karatu. Don haka ya zan kamar shi ne shugaban amma ba a ta’ba kiran sa da  sunan sarki ba sai dai malaminsu ko liman. Hodi shi ne sarkin Bosu kuwa shi neliman. Ana cikin hakas ai Allah da ikonsa ya yi ma Bosu rasuwa. Ya rasu ya bar d’ansa Boyi sai aka bashi Limanci don shi gadi limancin mahaifinsa Bosu.

Ana cikin haka sai Hodi Jan K’osai ya rasu. Hodi ya rasu ya bar ‘ya’aynsa shi ba su isa rik’a sarauta ba. Saboda yara k’anana ne k’warai ba su isa rik’on muk’amin ba.

Za’ben Sarki


Wa za a ba sarauta kafin d’iyan Hodi su girma sai aka rasa saboda ga wannan lokacin akwai jahilci ga jama’a suna gudun jihadi na Shehu Usmanu D’anfodiyoga shi sun tba amma akwai saura kuma suna ganin sarauta ba tabari su tafi gona kullumdon haka suka yi shawara su ba Boyi d’an Bosu matsayin liman saboda su kabawa wanda duk aka ba sai ya k’i dan haka aka ce a ba oyi shi rik’a har zuwa gaba in yaran Hodi Jan K’osai sun girma.

Aka taru aka a Boyi rik’o aka tafi da shi Gwandu wurin sarki suka ce ga wanda suka ba garin su rik’o sai aka nad’a shi aka dawo da shi garin D’akin-gari daga nan rik’o ya fita daga Kabawa ya fad’a hannun Fillani. An nad’a Boyi ya zama sarkin D’akin-gari a shekarar 1820.

Bayan rasuwar Hodi Jan K’osai Boyi d’an Bosu malaminsu limaminsu amma shi Bosu shi bai yi sarauta ba. da Boyi ya rasu sai aka ba d’ansa Mamman Boyi. Daga nan wannan ya rasu a nad’a wanan a fid da wannan a nad’a wancan har rik’on ya zago Sambo Sni shi ne sarki. Daga sambo Sani sai Torankawa. Sambo Sani ya fid da malaminsa Ahmadu Hussaini saboda rikicin kud’i sai ya aika Gwandu yana san a aiko masa da Malami aka ciko masa malami Batoranke. Malamin sarki ya zo bai zo da mata ba sai ya shawarce shi cewa ga d’iyata nan ta fito gwauruwa ce in yana sonta aure. In yana so ya je ya gana da ita ya gan ta ya ce yana so sai aka had’a su aure. An d’aura musu aure da d’iyarsa Sambo Sani daga suna zaune tare sai rashin lafiya ya kama Sambo Sani. Sai ya yi wasicci zuwa ga sarkin Gwandu cewa ko bayan ransa a ba surikinsa mai auren d’iyarsa shi ne Haliru Sarki Allah cikin Ikonsa ya yi wa Sambo Sani rasuwa ya rasu a shekarar 1919.

Bayan rasuwarsa aka nad’a Haliru sarki ya zama sarkin kudun D’akin-gari. Ya yi sarauta 1941. Shi ma malamin sarki ya rasu 1943. Sai su ma Torankawa wannan ya hau ya sauka wannan ya sauka har rik’o ya kawo ga sarkin kudu Abdullahi Malam Abdullahi ya zamo sarkin Kudu 1961. Ya yi shekara 33 yana  sarauta ya rasu 1994. Alla ya yi masa gafara. Sai d’anshi Malam Aminu ya gade shi (1994) ya soma sarauta har bayan da Allah ya yi masa rasuwa. Yayi shekara (17) watan ya rasu a 2011. Bayan rasuwar Aminu a 2011 sarauta ta koma ga hannun  Fulani inda aka ba Jafaru Haliru sarautan garin D’akin-gari a 2011 har zuwa yau. to ga dai yadda sarautar D’akin-gari ta kasau gida uku (3) Kabawa da Fulani da Torankawa.

  1. Farkon sarautar Hodi Jan K’osai 1810-1820 shekara 10

  2. Sai Fulani Boyi D’an Bosu 1820 – 1919 shekara 99

  3. Torankawa 1961 – 1994 zuwa 2011

  4. Sai kuma Fulani 2011 zuwa yau.


A tak’aice garin D’akin-gari ya yi shekara 199 da kafuwa.

Ma’anar Sassak’a


Sassak’a na nufin gyara itace da gizago ko sarrafa shi don yin amfani da shi da misali irin su turmi daga itacen k’irya. Bayan haka kuma na iya cewa sassak’a abin da aka sarrafa daga itace kamar allo ko turmi ko mutum mutumi. Sana’ar sassak’a itace don samar da surori da sauransu.

Wannan ma’anar an samo ta ne daga k’amusun Hausa wanda aka rubuta daga Jami’ar Bayero da ke Kano.

Alhassan da wasu (1982) sun bayyana cewa sassak’a itace irin hure icce da aiwatar da shi da san a mai da shi wani abin amfani kamar su jirgin ruwa da kyaure (gambu) da kujerar zama ta mata ko kwalliyar sirdi ko d’angarafai ko k’otar garma ko fartanya (hauya) ko gatari da alluna na karatu ko mutum mutumi. Wata ma’anar kuma akan sana’ar sassak’a daga cikin littattafai karatu kamar su:

Labarun da da na yanzu: An bayyana sassak’a da cewa akwai masassak’a turame da k’ujeru irin na mata da akussa da itacen k’irya. Amma a k’auye an fi yin wad’annan ‘botoci kuma a kan sannak’a su ne a birni da k’auye galibi an fi yi da iccen aduwa.

Hamma da Bagudu (2004: 10) cewa sunka yi sassak’a ita ce aikin da ake yi domin samar da kayan amfani musamman kayan noma da suka had’a da k’otar kalma da kuma kayan aikin gida da suka had’a da kujerar zama ta mata da akusi da dai sauransu.

Tarihin Samuwar Sassak’a a Garin D’akin-gari


Duk irin abin da mutum ya gani a duniya yana da tarihi ko asalinsa haka ma sana’ar sassak’a a garin D’akin-gari.

Amma duk da k’ok’arin da na yi na in samu hak’ik’ianin ko tabacin faruwar wannan sana’ar ta asali abin ya faskara domin duk wanda na tunkara dangane da tarihin wannan sana’ar ta sassak’a a garin D’akin-gari sai ya nuna mini cewa shi kam dai bai iya cewa ga lokacin da aka fara ta. Amma dai ya san cewa sana’a ce mai d’imbin tarihi a duniya ba a garin D’akin-gari kawai ba.

Saboda ita wannan sana’ar an fara ta tun lokacin da Annabi Nuhu ya sassak’a jirgin ruwa. Wanda mutanensa suka rink’a yin kashi a cikinsa. Haka kuma kamar yadda sakke Nura dogo d’an kimanin shekara (35) ya ce shi kam dai ya tashi a gidansu ya iske mahaifinsu yana yin wannan sana’ar tun yana k’arami har ya girma sai aka rink’a koya masa daga nan sai ya iya amma shi ba zai san lokacin da aka fara wannan sana’ar ba a garin D’akin-gari.

Haka zalika akamr yadda na nazarto da Gura Muhammadu ya ce shi ma wannan sana’ar ya san ana yin ta a gidansu tun tashinsa amma ba zai iya kawso ko kimanin shekaru nawa aka fara ita wannan sana’ar ba. sai dai ya san ya tashi ya ga kakansa na yi da kuma ubansa na yi har ya kawo shi ma yana yi da kuma ‘ya’yansa su ma suna yi.

Malam Abu Magi a lokacin da na ke hira da shi ya tabbatar da cewa sana’ar sassak’a a garin D’akin-gari ta samu ne tun kaka da kakanni domin ita ce sana’ar gidansu. Ya gade ta ne ga mahaifinsa shi ko mahaifinsa ya gade ta ga mahaifinsa. Ya k’ara da cewa sana’ar sassak’a a garin D’akin-gari ta samu tun lokacin da aka samu sana’ar noma. Wanda yake noma shi ne ya haifar da sana’ar k’ira da sassak’a wad’anda su ne k’ashin bayan sana’ar da kayan aikin ga manoma. A inda mak’era su ne ke samar da kayan aikin irin su ruwa wato k’arfe. Kamar tsabar kwasa (fartanya) da tsabar kalme da ta sungumi da lauje da dai sauransu. A inda sana’ar sassak’a wato sakkarawa (masassak’a) ske samar da kaan aiki ga manoma irin su k’otar kwasa (fartanya) da k’otar kalme da ta sungumi. Haka kuma suna samar da kayan aikin ga mata a cikin gida tun a wancan lokaci har zuwa yau. kamar irin su turmi da ta’barya da muciya da kujerar zama ta mata da sauransu. kazalika samar da kayan fita ga masunta kamar jirgin ruwa da hirahiri.

Yanyin Tattalin Arzikin Mutanen Garin D’akin-gari


A duk inda aka samu al’umma suke  zaune to tabas sai an sami hanyoyin da suke gudnar da rayuwarsu ta yau da kullum dangane da abin da ya shafi tattalin arizkinsu. Saboda haka dangane da yanayin tattalin arzikin mutanen k’asar D’akin-gari k’asa ce mai yawan sana’o’in akwai na maza akwai kuma wad’anda mata da maza duk suna yi. Amma duk da wad’annan sana’o’I da suke yi, babbar sana’arsu ita ce noma kuma noma ya had’a da na damini da rani. Ga jerin sana’o’in da maza kawai ke yi kamarhaka:

  1. Sana’ar sassak’a

  2. Sana’ar k’ira

  3. Sana’ar farauta

  4. Sana’ar tauri

  5. Sana’ar gina

  6. Sana’ar kafinta

  7. Sana’ar fawa

  8. Sana’ar su (kamun kifi)


Haka kuma ga jerin sana’o’in da mata ke yi wad’anda suka had’a da:

  1. Dawa-dawa

  2. Hoce

  3. ‘Bula

  4. Koda

  5. Kitso

  6. K’osai

  7. K’uli-k’uli

  8. Kad’i

  9. Suyan kifi

  10. Shinkafa

  11. Tuwo

  12. Awo

  13. Dillancin kayan mata

  14. Sak’ar kaba

  15. Waina

  16. Sayar da ruwan pure watar

  17. Nik’an gari da k’ananan injuna da sauransu.


Ta ‘bangaren sana’o’in maza da mata kuwa sun had’a da:

  1. Sana’ar kiwo

  2. Sana’ar noma

  3. Sana’ar fatauci

  4. Sana’ar sak’a

  5. Sana’ar d’inki

  6. Sana’ar fawa

  7. Sana’ar sa kai

  8. Sana’ar dillanci

  9. Sana’ar k’ira

  10. Sana’ar sassak’a


Duk wannan bai tsaya a nan ba domin daga cikin hanyoyin tattalin arzikin wad’annan mutane akwai noma k’warya da kuma kasuwancinta. Haka zalika wad’annan sana’o’in da wad’annan mutane ke yi suna yin su ne rani da damina. Amma duk da haka wad’ansuidan damina ta sauka suna ajiye sana’ar da suke yidomin su koma gona. Wad’ansu kuwa ba su ajewa domin ba su da wata hanyar cin abinci sai nan. Bisa ga wannan kuma za mu ga cewa k’asr D’akin-gari k’asa ce da Allah ya albarkata da hanyoyi da dama na bunk’asar tattalin arzikinta. Wannan kuwa ba zai rasa alak’a da yadda al’ummar D’akin-gari suka tashi haik’an wurin koyo da d’aukar sana’o’insu da muhimmanci a kicin al’umma.

Yanayin K’asar D’akin-gari


A duk inda aka yi magana kan k’asa to dole ne sai an ta’bo abin da ya shafi yanayinta saboda haka dangane da yanayin k’asar D’akin-gari k’asa ce mai yawan al’umma wad’anda mafi yawansu Fulani ne. amma akwai k’abilu ‘yan kad’an daga cikin su kamar Hausawa da kabawa da Zabarmawa da Yarabawa da Igbo da Kyanyawa da Torankawa da sauransu.

Haka kuma k’asar tana da ‘bangarori guda biyu wato fadama da tudu. Haka kuma k’asar ba ta cikin rafuka da yawa. A ‘bangaren yawan k’asa kuwa k’asa ce mai yawan gaske domin ta yi iyaka da Bududo a kudu a gabas kuwa ta yi iyaka da Maiyama a yamma ta yi ta yi iyaka da Dandi (Kamba) a arewa kuma t ayi iyaka da Bunza.

Haka zalika ta ‘bangaren noma ba a bar ta a baya ba domin k’asar k’asa ce mai albarka domin k’asar tana da dausayi kuma tana da yawan wuraren noma kuma k’asar ce wadda ke bunk’asa ko da yaushe. Kuma tana d’aya daga cikin k’asashen da Allah ya albarkata a sanadiyar noma a jahar Kebbi. Ba a jahar Kebbi kad’ai ba har ma a jahohin arwa baki d’aya. Bayan haka k’asar D’akin-gari k’asa ce mai tsaunuka kuma k’asa ce wadda ke da wadataccen itatuwa gwargwado ba k’asa ce da ke da sahara ba.

Nad’ewa


A wannanbabi na biyu mai taken tarihin sassak’a a garin D’akin-gari an kawo tarihin garin D’akin-gari da ma’anar sassak’a da kuma tarihin sassak’a a garin D’akin-gari da kuma yanayin tattalin arzikin mutanen garin D’akin-gari da yanayin k’asar. A k’arshe shi ne nad’ewa ya biyo baya.

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments