Ticker

6/recent/ticker-posts

Sassaka A Garin Dakin-Gari: Tasirin Zamani A Kan Gargajiya (2)

NA

ABUBAKAR ALIYU
1310106004

KUNDIN DIGIRI NA FARKO NA HAUSA (B. A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NAJERIYA. JAMI`AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO

www.amsoshi.com

BABI NA ‘DAYA


K’UDURIN BINCIKE


K’udurin wannan bincke shi ne gano yadda ake yin sana’ar sassak’a da kuma irin rawar da take takawa a cikin al’umma. Bugu da k’ari binciken zai kuma neman gano sauye-sauyen da ake samu na zamani a cikin wannan sana’ar. Kazalika binciken zai yi k’ok’arin binciko da gano irin kayan da ake amfani da su a wajen sana’ar take da kwatanta tsarin da da na yanzu domin fito da tasirin zamani da kuma irin sauye-sauyen da aka samu a cikin sana’ar yanzu.

Bayan haka aikin zai dubi irin matsalolin da sana’ar take fuskanta a inda aka fito da kuma halin yanzu wanda yakan iya zama sila sanadiyar mutuwar sana’ar a nan gaba muddin ba a d’au mataki ba a kan wannan abin.

Shimfid’a


Daga farkon babin za a yi k’udurin bincike a akan wanann aikin na sassak’a a garin Dakin-Gari: Tasiirn Zmani a Kan Gargajiya. Sa’an nan kuma za a yi bitar ayyukan da suka gabata. Wato rubuce-rubucen da aka yi a kan wannan sana’ar wad’anda suka gabata. Bayan ga haka akwai hanyoyin gudanar da bincike. Daga nan kuma sai dalilin gudanar da bincike wanda za a nuna dalilin yin wannan bincike. Haka kuma za akawo wasu ayyukan manazarta amma sun sha bamban da wannan aikin bincike.

Bayan haka za a kawo muhimmancin bincike. A nan za a nuna muhimmancin da ke ga wannan bincike domin al’ummar D’akin-Gari da ma sauran al’umma baki d’aya. Wato ta yadda bayani zai biyo baya. Daga nan kuma sai farfajiyar bincike wato wurin da ake gudanar da wanann bincike domin samun bayanai. Daga k’arshe kuma za a nad’e wannan babi a tak’aice.

Bitar Ayyukan da Suka Gabata


Manazarta da masana al’adun Hausawa a cikin tasu gudummuwa sun yi rubuce-rubuce a kan sana’ar sassak’a. Ita wannan sana’ar tana d’aya daga cikin sana’o’in samar da kayan aikin da Hausawa ke amfani da su wajen ayyukan yau da kullum. Masana da suka ba da tasu gudummuwa sun had’a da Habibu Alhassan da wasu (1988) Zaman Hausawa bugu na d’aya da kuma bugu na biyu. Sun kawo ma’anar sassak’a sun kuma yi bayani dangane da yadda ake yin ta da kuma kayan aikinta da kuma kayan da ake samarwa. Amma duk a tak’aice.

Haka ma a cikin littafin Labarun da da Na Yanzu (1968) shi ma an ba da ma’anar sassak’a da yadda ake yin ta duk a tak’aice. haka ma a cikin littafin E. M. Rimmer da wasu Zaman Mutum da Sana’arsa (1948) shi ma an yi bayanin sana’ar sassak’a da yadda ake yin ta da kuma kayan da ake samarwa a tak’aaice.

Haka ma daga cikin ayyukan da aka gabatar a kan sana’o’in Hausawa a wannan sashe na koyar da harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato duk irin ayyukan da na duba babu wanda ya kawo bayani gamsasshe a kan wannan sana’ar. Misali: Bilyaminu Abdullahi (2010)  mai taken: “Sana’o’in gargajiya masu alak’a da maita.” Shi ma ya kawo bayani a kan sana’o’in gargajiyar Bahaushe ba tare da ya fad’ad’a kan sana’ar sassak’a ba.

Bayan haka a cikin kundin bincike da Sani Musa (2009) ya rubuta a kan cud’e-ni-in-cud’e-ka tsakanin sana’o’in Hausawa na gargajiya” ya kawo bayani ne kawia na cud’anyar da ke tsakanin noma da sassak’a amma bai yi bayanin sana’ar ba bai d’ayanta.

Haka shi ma Alhaji Rabi’u a cikin nasa kundin bincike wanda ya gabatar a kan sana’ar koli da sak’a (2002). Shi ma ya kawo jerin sana’o’in Hausawa ciki har da sassak’a. Shi ma ya yi kamar yadda sauran suka yi.

Shu’aibu Abdullahi Jangebe (1996) wanda ya yi aiki kan nazari a kan sana’ar koli da jauro wanda daga cikin aikinsa da ya yi tsokaci a wad’an nan sana’o’in na koli da jauro ya yi bayani kan sana’ar sassak’a sai dai bai zurfafa bayani gamsasshe kan wannans ana’ar ba illa dai ya yi tsakure ne kawai.

Haka ma a cikin kundin bincike na sana’o’in Hausawa “Sana’ar Koli da Awo” na Ibrahim Abbas Bashar (1989) shi ma ya kawo bayanin sana’o’in Hausawa ciki har da sana’ar sassak’a amma bai yi bayanin sana’ar sosai ba. shi ma ya yi tsakure ne kawai.

Garba C. Y. (1991) sana’o’in gargajiya a k’asar Hasua. Wannan littafi ya bayyana yadda sana’o’in gargajiya suke a k’asar Hausa. Inda ya d’auki ire-iren sana’o’in gargajiya a k’alla guda ishirin da uku (23) kuma ya bayyana yadda suke ta ‘bangarori da dama.

Daga cikin sana’o’in da wannan littafi ya yi bayani a kansu akwai kiwo da moman damina da noman rani da jima da rini da sassak’a da dillanci da tsubbu da talla da fatauci da kid’a da rok’o da bokanci da wanzanci da farauta da fawa da kuma sana’ar su (kamun kifi). Dukkan wad’annan sana’o’in ya yi k’ok’arin bayyana ma’anarsu da aydda suke a al’ada da kuma dalilin da ya haifar da su da amfaninsu da yanayinsu da masu aiwatar da su da yadda ake aiwatar da  kuma yadda ake koyar da su da kuma ire-irensu.

Bayanan cikin wannan littafin suna da dangantaka d aikin da zan gudanar dominkuwa an yi bayani ne a kan sana’o’in gargajiya na Hausawa a k’sar Hausa. Wanda ni ma nawa aikin zai yi bayani ne a kan sana’ar gargajiya na Bahaushe amma ni nawa zai tak’aita ne a kan sana’a d’d’aya tilo wato sana’ar sassak’a. Kuma a garin D’akn-gari kawai wadda mawallafin ya kawo bayanin ta a cikin littafin amma a tak’aice-inda ni kuma zan yi bayaninta tun daga yadda asalinta yake da kuma yadda ake aiwatar da ita.

Zaruk’, R. M. da wasu (1982) wannan littafi ya yi bayani a kan Hausawa ne dangane da abubuwa kamar haka: k’asar Hasua da yanayin k’asar da albarkarta da yadda suke fatauci da almajiranci da ci rani da bayani a kansu kan su Hausawan da al’adunsu. Bayan wannan ya bayyana yadda aure yake da haihuwa da tarbiya daga nan ne kuma ya fad’a kan sana’o’in wanda bayan su ya ta’bo sarautu da muk’amai. Wanda a ‘bangaren sana’o’I ya raba su gida biyar inda suka had’a da:

Sana’o’in samo abinci kai tsaye. Su ne kamar farauta da su da noma da kiwo da fawa. Kuma akwai sana’o’in da ke bayar da sutura da mafaka da kayan hutawa. Misalansu su ne kad’i da sak’a da d’inki da rini da jima da dukanci da  gini da bugu da dai sauransu. sai kuma sana’o’in da ake samun kayan aiki ta hanyarsu. Misali, sassak’a da k’ira. Sannan akwai sana’o’in sarrafawa da ciniki. Su ne kamar fatauci da koli da dillanci da awo da makamantansu.

Bayan haka sai ya kawo sana’o’in yi wa mutane hidima ko gyara kamar wanzanci da kitso da k’wadago da dai sauransu. wannan littafi yana da dangantaka da aikin da zan gudanar domin ya ta’bo ‘bangaren sana’o’i kuma ni ma nawa binciken a kan sana’a ne. amma shi ya ta’bo sana’o’i ne na Hausawa gaba d’aya wanda ya d’auki wasu daga ciki ya yi bayani a kansu. Amma ni kuwa nawa binciken zai gudana ne a kan sana’ar sassak’a kuma a garin D’akin-Gari kawai.

Yakasai S. A. (1979): A san mutum a san cinikinsa. Wannan littafi an rubuta shi ne a kan manyan sana’o’in malam Bahaushe da ire-iren kayan sana’o’in malam ahaushe wad’anda ake gudanar da su. Sannan ya kalli sunayen da ake kiran masu sana’o’in da shi kamar sak’a a ce masak’i da dai sauransu. sannan ya kalli yadda suke ci gaba ta harakar tattalin arzikin k’asa da zamantakewar yau da kullum a cikin al’umma.

Wannan littafi yana da alak’a da aikin da za a gudanar domin ya ta’bo ‘bangaren sana’o’in ne na malam Bahaushe wanda ya yi bayani a kan su da kuma yadda suke. Haka wannan binciike zai gudana ne a kan sana’ar Bahaushe wato sana’ar sassak’a. Amma ni zan yi nazarin sana’ar ne a cikin garin D’akin-gari kawai. Batare da yin k’asa a guiwa ba a cikin littafin an bayyana yadda sana’o’in gargajiya suke a k’asar Hausa. Inda ya d’auki ire-iren sana’o’in gargajiya yana mai bayar da ma’anarsu da kuma yadda ake aiwatar da su. Sannan da irin ci gaban da suka kawo a cikin al’umma. A cikin littafin marubucin ya d’auki rie-iren sana’o’in gargajiya a k’alla guda ishirin da biyu (22).

Daga cikin sana’o’in da wannan littafi ya yi bayani a kansu akwai k’ira da jima da dukanci da kasuwanci da fatauci da farauta da noma da sassak’a da gini da kitso da d’akin haya da jinka da rini da shuni da baba da fawa da aski da d’ibbo da bokanci da bori da d’inki da suhuri da lambu da yak’i da su (kamun kifi).

Duk wad’annan sana’o’in an yi k’ok’arin bayyana ma’anarsu da yadda suke a al’ada da kuma dalilin da ya haifar da su da amfaninsu da yanayinsu da kuma masu aiwatar da su da kuma yadda ake koyar da su. Bayanan da ke cikin wannan littafi suna da dangantaka da aikin wannan bincike da zan yi domin kuwa an yi bayani ne a kan sana’o’in gargajiya na Hausawa a k’asar Hausa. Wanda ni ma nawa zai yi bayani ne a kan d’aya daga cikin sana’o’in ne na gargfajiya wanda mawallafin ya ambata wato sana’ar sassak’a. Wanda binciken zai tak’aita ne garin D’akin-gari.

Argungu S. A. (2012): Bayani a kan cud’e-ni-in-cud’e-ka tsakanin sana’ar  k’ira da sauran sana’o’in Hausa: Ke’bantaccen anzari a garin Argungu.” Wannan kundin ya yi bayani ne a kan sana’ar k’ira wadda d’aya ce daga cikin sana’o’in Hausa. Wajen gudanar da wannan bayani ya ta’bo tun daga ma’anar sana’ar k’ira da kuma ma’anar sauran sana’o’in da ya danganta ta da su da tarihin sana’ar da kashe-kashenta da wurin da ake sana’ar da kayan da ake amfani da su wurin yin sana’ar da kayan da ake samarwa da irin magungunan da ake samu da irin kirarin da ake yi mata da kuma irin rawar da take takawa a cikin al’umma. A tak’aice dai ya d’auki wannan sana’ar ya bayyana yadda take a al’ummar Hausawa da kuma irin cud’anyar da ta yi da sauran sana’o’in Hausawa. Wannan kundi da aikin da nake bayani a kansa suna da alak’a. Domin kuwa sana’a ce da sauran sana’o’in Hausawa yake bayanai a kansu wanda wasu daga cikin hanyoyin da ya bi domin yin bayanin yadda sana’ar take da sauran sana’o’in na Hausawa ni ma na fito da su. Misali ma’ana ta sana’ar da yake bayanin a kan kanta da irin kayan da ake amfani da su wajen sana’ar da kayan da ake samarwa da magunguna da suke bayarwa ga jama’a da kumka irin magungunan da suke sarrafawa a lokacin sana’ar sai dai shi yana bayani ne a kan yadda ake yin sana’ar ne da sauran sana’o’in a ko’ina a k’asar Hasua. Ni kuma ina bayani a kan yadda ake aiwatar da sana’ar sassak’a a garin D’akin-gari.

Ibrahim D. (1986): wannan kundin ya bayyana yadda ake aiwatar da sak’a tufafi a k’asar Katagum a cikin jihar Bauchi. Wanda a k’ark’ashin haka ya bayyana tarihin sak’ar a Katagum. Sannan kuma ya nuna dangantakar masak’a da wasu na’o’i bayan haka ya kawo kayan sak’o da nuna yadda ake sak’a da kuma ire-iren kayan da ake sakawa. Haka kuma kundin ya nuna yadda sak’a take da harkokin kasuwanci da matsalolin sak’ar da gargajiya ke fuskanta da shawarwari don magance matsalolin da nuna yadda aka sami sauye-sayen zamani a cikin sana’ar sak’a.

Wannan aiki da aikin da nake gudanarwa suna da alak’a ta wasu ‘bangarori. Domin yayi bayani a kan d’aya daga cikin sana’o’in Hausawa na gargajiya wato sak’a. Alak’ar aikinsa da nawa shi ne ya bayar da tarihin sak’a a Katagum. Ya kawo irin kayan da ake sak’awa da irin matsalolin da take fuskanta da shawarwari a kan magance matsalolin. Wanda ni ma binciken nawa zai gudana ne a kan hakan.

Umar, M. B. (1983) Wannan takarda ta yi bayanin abubuwa da yawa daga ciki ya ta’bo ma’ana ta tattalin arziki da dangoginsa. Bayan wannan kuma ya yi magana a kan sana’o’I wanda a k’ark’ashin haka ne ya zayyano sana’o’n Hausawa har da sassak’a wanda ya nuna cewa noma shi ne wanda gidan kowa akwai shi. Daga cikin sana’o’in. a k’ark’ashin haka kuma ya kawo sana’o’i da maza ke yi da kuma wad’anda mata ke yi da dai sauransu.

Bayan wannan kuma akwai nau’o’in aikin da ya kawo da kuma yadda ya bayyana jari da sana’o’in da suke buk’atar jari kafin a yi su. Da yadda haraji yake da ire-irensa. Wannan takarda ta shafo abubuwa da yawa. Kasancewar ana magana kan tatalin arziki tsarinsa a k’asar Hausa. Haka kuma wannan takarda ta ta’bo sana’o’in da yadda aka zayyana su daga ciki har da sana’ar da nake aikin bincike a kanta. Amma ni ina gudanar da binciken nawa cikin garin D’akin gari.

Wad’annan su ne kad’an kenan daga cikin ayyukan da magabata suka gudanar a ‘bangaren sana’a musamman ma sana’o’in Hausa na gargajiya. Wanda kuma na nazarce su a wajen gudanar da wannan bincike da nake  yi a kan sana’ar Hausawa ta gargajiya wato sassak’a a cikin garin D’akin-gari.

Hanyoyin Gudanar Da Bincike


Da yake bincike a kan abin da ya shafi al’ada ne kuma abin yana faruwa ne a bikin al’umma, hanyoyin da ake ganin za su dace don k’udurin binciken sun had’a da tattara bayanai daga littattafai da aka wallafa wad’anda akan samu a d’akunan karatu daban-daban. Haka kuma za a tattara bayanai daga kundayen bincike da aka gudanar a jami’o’i da makarantu da kuma cibiyoyin ilimi daban-daban da mak’alun da aka gabatar a tarukan k’ara wa juna sani daban-daban. Da kuma wad’anda aka wallafa a mujallu da jaridu. Sannan da ta hanyar yanar gizo (internet) duk wad’anda suka danganci sana’ar sassak’a. Wani mataki kuma da za a bi domin kai ga kammala aikin shi ne neman bayanai ko hira da mutanen da ake ganin binciken zai amfana da su. Kamar sakkarawa (masu yin sassak’ar). Bin wad’annan hanyoyi zai sa ayi adalci wurin tace sahihan bayanai da za su zama madogara ga aikin binciken.

Bugu da k’ari Hausawa na cea, gani ya kori ji, kuma zuwa da kai ya fi sak’o. Wata hanya da za a bi domin yin binciken ita ce ta kusanta da ziyartar wuraren da ake gudanar da sana’ar sassak’a a garin D’akin-gari don fahimtar k’arin wasu abubuwa daga sakkarawan (masassak’an). A k’arshe samun nasara bin wad’annan hanyoyi zai sa a sami hujjoji masu k’arfi da za su taimaka wajen fito da wannan bincike na gano yadda sana’ar sassak’a ta zame nasara ga msau aiwatar da ita.

Dalilin Gudanar da Bincike


Ko shakka babu akwai dalili a kan kowane irin lamari wanda za a yi. Haka ma wannan aikin yana da dalilin aiwatar da shi daga cikinsu kuwa sun had’a da:

Da farko dalilin wanna aikin domin ganin cewa sana’o’in Hausawa na gargajiya suna da matuk’ar yawa da fad’i da kuma muhimmanci musamman sana’ar sassak’a wadda sana’a ce da kamar tana a ‘boye mutane ba su ba ta muhimmanci da ya kamata su a ta ba. Bugu da k’arfi yana d’aya daga cikin sharud’d’an kammala karatun digi na farko wani dalili kuma shi ne ganin masu bincike da suka gabata ba su cika sha’awar yin bincike a wannan fanni ba. Shi ya sanya na yi sha’awar yin nazari a wannan fanni mai matuk’ar muhimmanci ga al’umma.

Haka kuma wannan aiki zai zama d’an tudun dafawa musamman ga masu sha’awar fad’ad’a bincike a fannin. Ma’ana ana iya samun wani haske ko k’arin bayani dangane da abin da ya shafi wannan bincike ga manazarta nan gaba

Muhimmancin Bincike


Kamar yadda kowane aikin bincike ke da muhimmanci haka ma wannan aikin. Wannan aikin nazari a nemo irin wannan sana’ar ne da mutanenn da ke yi a garin D’akin –gari ko a al’umma baki d’aya. Domin zai ba sauran mutane da ba su yi wannan sana’ar damar su san ta sani na hak’ik’a.

Haka kuma za su san yadda ake yin ta da irin itatuwan da ake amfani da su wajen yin ta a garin D’akin-gari. Wannan ba don komai ba sai don k’ara ha’bakar da wannan sana’ar. Haka zalika da kuma nuna irin amfanin da al’umma ke samu ta hanyar sassak’a ta wajen amfani da itatuwa. Da kuma nuna irin illar sare itatuwa (in gusowar hamada). Wannan aikin zai zama abu na farko da na fara rubutawa da hannuna wanda yake abun alfahari ne gare ni haka kuma wannan aikin zai taimaka gare ni matuk’a wajen sa min k’aimi ga ayyukan bincike nan gaba. Haka kuma zai zama wani abin tuntu’ba musamman ga d’alibai masu sha’awar wannan fanni wannan bai tsaya ga d’alibai ba har ma da duk wani mai sha’awar wannan sana’a ta sassak’a a cikin al’ummar k’asar D’akin-gari.

Farfajiyar Bincike


A duk inda aka yi magana kan farfajiya to dole ne sai an ta’bo abin da ya shafi yanayin wannan k’asa. Saboda haka dangane da yanayin farfajiyar wurin bincike wuri ne mai yawan al’umma wad’anda mafi yawansu Fulani ne. amma akwai k’abilu ‘yan kad’an daga cikinsu kamar k’abilar Hausawa da Yarabawa da Igbo da Kengawa da Kabawa da sauransu.

Haka kuma k’asar tana da ‘bangare d’aya wato tudu haka kuma farfajiyar binciken ta cikin k’asa ce shimfid’ad’d’a ba tudu da rafi ba kamar sauran wurare ba. a ‘bangaren yawa kuwa, wuri ne mai yawan gaske domin ta yi iyaka da Bunza a Yamma a gabas kuwa ta yi iyaka da Mai’yama a kudu kuma ta yi iyaka da Zagga a arewa kuwa ta yi iyaka da Fana da Ilo da sauransu.

Haka ta ‘bangaren noma ba a bar ta a baya ba domin farfajiyar k’asar mai albarka domin tana da dausayi kma tana da yawan wuraren noma. Kuma k’asa ce wadda ke bunk’asa ko da yaushe. Kuma tana d’aya daga cikin k’asashen da Allah ya albarkata a sanadiyyar noma. Kai ba a wannan yanki ba har ma a wurare da dama. Bayan haka farfajiya ce mai yawan tsaunuka kuma wadda take da wadatattun itatuwa gwargwado ba wuri ne da ke da sahara ba.

Nad’ewa


K’arshe kamar dai yadda ak gani tun daga farkon wannan babin an kawo bayani kan yadda aikin zai kasance ta hanyar amfani da babi-babi. An kawo bayani kan bitar ayyukan da suka gabata da dalilan wannan binceke da farfajiyar bincike. Haka kuma an kawo muhimmancin binciken da muhallin bincike. Daga k’arshe kuma aka rufe babin da nad’ewa.

 

 

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

Post a Comment

0 Comments