Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Rubutawa: Shehu Hirabri08143533314
Amshi:
Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Ga ɗan Galadima Horo,
Jikan Galadiman Horo×2
Sai kai Galadima,
Yara: In ɗau iyalinmu in koma Horo.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: A sai kai Galadima,
In ɗau iyalinmu in koma Horo.
Jagora: Ka gama da tsohon kolo,
Wane ya bar gida nai, ×3
Yara: An ce yanzu kullun yana loja kwance.
Jagora: Na yi marmari Haji Ɗanba’u,
In je in ƙara waƙa Shagari.
Jagora: Na san karo da kai,
Ba ya da daɗi,
Kai ji wane ya sha kaye,
Don na gane shi can malisa,
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi.
Jagora: Don na gane shi can malisa,
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi.
Jagora: Wawa!
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi.
Jagora: Saga!
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Yanda kai mani na gode ma,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: A in dai kana nan Shagari,
In maida waƙa Shagari.
Jagora: Yau da gobe kyauta sai Allah,
Yara: Sai kai ciyaman Shagari. ×2
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Ga ɗan Galadiman Horo,
Jikan Galadiman Horo,
Sai kai Galadima,
Yara: In ɗau iyalinmu in kuma Hora,
Jagora: A in kai galadima,
Yara: In ɗau iyalinmu in koma Hora.
Jagora: A kwana a tashi dattijo,
Sai kai Galadima Horo.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Na ji har mutane suna hwaɗi,
Ko yau siyasa ta dawo,
Yara: Kai za a za’ba Shagari.
Jagora: Ka gyara birnin Shagari,
Ka gyara birnin Shagari,
Yanzu ga wuta kuma ga famfo,
Da ƙauyukka ka gyara su,
Ha na ji mutane suna yabo,
Ko yau siyasa ta dawo,
Yara: Kai za a za’be Shagari.
Jagora: Ko yau siyasa ta juyo,
Yara: Kai za a za’be shagari.
Jagora: Tun da sun yi dai sun has wahala,
In kuma siyasa ta dawo,
Yara: To ba za su za’ben mai cuta.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Rabbana ya ƙara kiyaye ka,
Allah ya ƙara tsare man kai,
Rabbana ya ja zamanin Mamman,
Kullun inai ma addu’a,
Yara: Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Kullun inai ma addu’a,
Yara: Mamman ciyaman Shagari.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Gai da Mai’akwa Jareɗi,
Yara: Tunda hairan ya ban ya amfanan×2
Jagora: Ma’akwai ƙanen Modi sadauki,
Yara: Hairan ya kai ya amfanan.
Jagora: Kansi Bashar na gode ma,
Hairan ya kai ya amfanan.
Jagora: Ɗan Muhammadu na Lambara,
Yara: Hairan ya kai ya amfanan.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Yaro: Wani ciyaman na nan mai rowa,
Da du ya gane ni ya sha toka, ×2
Wani mai idanun ‘yabin,
Yara: Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Ina mai idanun mussoshi,
Yara: Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.
Jagora: Mudun ka ga ne ni a Shagari,
Yara: Mamman yake murna in je×2
Jagora: Na gode ciyaman na Yabo,
Bala Musa ɗan Ahmadu,
Yara: Hairan yakai ya unhwanan.
Jagora: Na gode ciyamanmu na Yabo,
Bala Musa ɗan Amadu,
Hairan ya kai ya unhwanan.
Jagora: Godiya ni kan Sani sanata,
Hairan yakai ya unhwanan×2
Jagora: Godiya nikai Haji Bello ciyaman,
Birnin Boɗinga,
Yara: Hairan yakai ya unhwanan.
Amshi: Dogo kana halin kyauta,
Alhaji Ɗan’ige ɗan dattijo,
Mamman ciyaman Shagari.
Jagora: Wani ciyaman ne,
Sarki rowa,
Sai son a zo a yi mai waƙa,
To ba ni yin aikin banza,
Yara: Na daina yin waƙa kyauta.
Jagora: Wawa!
Yara: Na daina yin waƙa kyauta.
Jagora: Saga!
Yara: Na daina yin waƙa kyauta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.