https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

NA


ABUBAKAR ALIYU
1310106004


 


KUNDIN DIGIRI NA FARKO NA HAUSA (B. A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NAJERIYA. JAMI`AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO


https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

BABI NA UKU


SASSAK’AR GARGAJIYA


Shimfid’a


A wannan babi na uku mai taken sassak’ar gargajiya na da k’ananan sassa kamar dai yadda bayani zai biyo. A sashe mai magana a kan ma’anar sassak’a sashen zai kawo ma’anar sassak’a ne watau daga masana daban-daban sai kuma kayan aikin sassak’a. Haka kuma za a dubi hanyoyin samun itace wanda shi ma bayani ne a akan hanyoyin samun itace. Daga nan kuma sai bayanin Hanyoyin sarrafa itacen wanda shi ma bayani ne akan yadda ake sarrafa itacen. Baya ga haka sai amsassak’a a garin D’akin-gari. A nan za a kawo jerin masassak’a ne a garin D’akin-gari wato masu yin wannan sana’a. sai kuma bayani kawo muna ire-iren itatuwan da ake amfani da su a wajen sassak’a. Haka kuma sai bayanin yadda ake samun magungunan da ake samu ga masu sana’ar sassak’a. A k’arshe sai bayanin kammala abin baki d’aya.

Ma’anar Sassak’a


Sanin ma’anar sassak’a na da muhimmanci domin ta haka ne kad’ai za a iya gane matsayinta ga al’umma. Saboda haka za a ga irin gudummuwar da take bayarwa wajen ci gaban al’umma  baki d’aya. Haka kuma wasu na danganta sassak’a da cewa, sana’a ce ta gargajiya wadda ake aiwatarwa da hannu ta hanyar amfani da wad’ansu kayan aiki wurin yin ta kamar su gatari da gizago da guru da k’umbula da sauransu. da kuma samun icce mai kamar da ake so. Amfani da shi a yi turmi ko kujera da ta’barya da alluna da mucciya da ‘botoci da sauransu.

To kamar yadda aka gani a cikin wad’annan bayanai na sama dangane da ma’anar sassak’a ni a nawa gani sana’a ce ta gargajiya wadda ake aiwatarwa da hannu ta hanyar amfani da itatuwa daban-daban tare da wad’ansu kayan aiki wajen aiwatar da ita. a kuma mayar da wannan iccen wani abun amfani kamar kujera ko turmi ko ta’barya ko mucciya ko ‘botoci da dai sauransu.

Kayan Aikin Sassak’a


Duk sana’ar da aka ce sana’a ce da ake aiwatarwa da hannu to sai an sami kayan da ake amfani da su wajen aiwatar da ita. saboda haka sana’ar sassak’a sana’a ce da ake yin ta da wad’ansu kayayyakin aikin kamar haka:

 1. Gatari

 2. Guru

 3. Kumbula

 4. Mahuri

 5. Gizago

 6. Mazari

 7. Makwashi

  • Gatari
Shi ne abu na farko wanda ake amfani da shi wajen yin wannan sana’ar kuma aikinsa shi ne sare icce da shi ya fad’i kafin duk a soma wani aiki. Haka kuma gatari wani k’arfe ne da mak’era kan k’era wanda akan sanya shi a wata kussawa ta ‘bota domin dad’in rik’awa.

 

3.2.2 Guru

Amfanin wannan abin aikin shi kuma ya ke’banta ne kawai yayin da za a yi turmi wnda da shi ne ake amfani a yi wa turmi wannan ramin da ake zuba abin daka. Haka kuma guru wak’ni k’arfe ne da mak’erakan k’era wanda ke da wata ‘yar tank’wara. Kuma yana da fad’in baki sai dai bai kai girman kwasa ba. amma ya yi kama da kwasa.

 • Kumbula


Tana d’aya daga cikin kayan da ake amfani da su wajen aiwatar da wannan sana’ar kuma ‘bota ce ta guru. Haka kuma ita kumbula tana da tank’wara a samanta kuma ta fi sauran ‘botoci girma. Ana amfani da ita wajen sassak’a babban turmi da kuma kwashe saman icce da sauransu.

 • Gizago


D’aya ne daga cikin kayan aikin wannan sana’a kuma wannan wata ‘yar k’aramar hanya ce mai ‘yan ‘bota wadda kamar da ita ce ake saisaye duk wani abu da suka yi wanda ya danganci wannan sana’a tasu. Hausawa suna masa kirari da gizago ba ka da sabo.

 • Mazani


Wannan wani k’arfe ne marar kauri kuma bai wuce tak’ar hannu biyu a. wanda ake amfani da shi a sanya shi wuta, idan ya yi zafi sai a yi wa turmi zane, amma ko turmin k’aramin turmi domin ba a yi wa baban turmi zane kana kuma suna amfani da shi su zane kujera.

 

 • Makwashi


Wannan shi ne kuma masassak’a (Sakkarawa) suna amfani da shi wajen kwashe abubuwa da ke cikin aikin da suka yi na sassak’ar. Domin abin ya zama ya k’ayatar kuma yana ban sha’awa tare da nuna ya yi sul’bi kuma yana k’ara haskaka a idon mutane masu san sayen kayan da suka sassak’a. Kamar irin su turmin daka na mata da kujerar zama sannan kuma da k’otar kalme ta noma.

 

 • Magagari


Wannan wan k’arfe ne mai kama da wuk’a mai gorje-gorje mai kauri yana da abin rik’o kamar wuk’a amfanin wannan magagari shi ne d’ad’i ake yi da shi da sauran ayyuka.

 • Wuta


A wannan sana’a ta sassak’a na amfani da wuta wajen k’wane iccen ta’barya wanda idan an sare iccen ta’barya sai a sa masa wuta sai samansa ya k’one sai a kashe wutana d’auka a kankare a jera.

A k’arshe wad’annans u ne kayan da ake amfani da su a sana’ar sassak’a.

 • Hanyoyin Samun Itace


Hanyoyin da ake samun itace kusan banyoyin biyu ne wato ta hanyar gargajiya da kuma ta zamani.

Gargajiya


Ta hanyar gargajiya shi ne inda basakkare (masassak’i) yake d’aukar gatarinsa ya je daji domin ya sare itacen da zai yi amfani da su a wurin sana’arsa kamar yadda na yi hira da sakkarawan garin D’akin-gari kamar haka:

Saddo Muhammadu shugaban sakkarawan garin D’akin-gari ya fad’a cewa hanya mafi sauk’i da basakkare ke samun itace zai d’auki gatarinsa ya je daji mai nisan gaske nda ake samun manyan itatuwa wad’anda yake ba na gwamnati ne ba kuma ba kowa ne ke da su ba sai ya sari icce wanda yake so. Haka kuma ya k’ara da cewa a lokacin da basakkare yake saran iccen wani iccen yakan nuna waibuwar bai saruwa a duk lokacin da aka sare shi sai ya had’e saran ko kuma sai mutum ya yi ta sara har ya kusan sarewa sai ya had’iye saran (wato ya dawo kamar yadda yake). A duk lokacin da basakke ya ga icce yana yi masa hakan to wad’ansu sakkarawan sukan yi wasu ‘yan siddabaru ga iccen domin nuna wa iccen tasu waibuwa wadda suka gada kaka da kakanni a inda wad’ansu sakkarawan sukan bar icen sai su kama  ma wani wasu ko sukan bar dajin gaba d’aya domin sun san ranar nan babu nasara ga wannan aiki. Sai kuma sakke Babbari Umaru wanda kuma shi ne shugaban sakkarawan shiyar fada. Shi ma ya cewa hanyoyin samun itace ga sakkarawa hanya mafi sauk’i ita ce wadda suka gada kaka da kakanni wato mutum ya je daji ya saro itace irin wanda yake buk’atar aiki da shi ko kuma ya ga wani ice godanar wani yakan iya rok’a a ba shi ko a sayar masa domin ya yi amfani da shi ya sarrafa zuwa wani abu. Abu Magi yana cewa a wasu lokuta idan basakke yana saran ice wasu itacen sukan nuna irin tasu waibuwa ta cewa ba su saruwa ko kumasu fad’awa wanda ke saransu su ka she shi ko su raunana shi ko kuma su fad’a masa wata k’addara tashi wadda yake da a gida. A yayin da wasu masassak’an suka ga hakan, wad’anda suke ‘yan gado ga sana’ar wato ba hawanta ne suka yi ba daga baya sukan yi wasu ‘yan tsafe-tsafe domin su nuna wa iccen tasu buwaya.

Haka kuma sakke Babiyo Riniya a yayin da nake tattaunawa da shi kan hanyoyin da suke bi wajen samun itacen da suke amfani da su na sana’ar tasu. Shi ma ya gaya min cewa sukan je daji su saro icce ko su yi jinga a saro musu. Ya k’ara da cewa sukan saro itace irin su aduwa da mad’aci da gawo da dalbejiya (lim) da k’irya da hanoda d’anya da sauransu.

A k’ok’arin tattaunawar da na yi da wad’annan mutanen a kan hanyoyin da suke bi wajen samun itacen da suke amfani da su wajen sana’ar sun gaya min da cewa suna amfani da itace daban-daban a lokacin da suke aiwatar da sana’arsu. Wad’annan itatuwa sun had’a da:

 1. Dogon yaro (dalbejiyalim)

 2. Kad’e

 3. Loda

 4. Danya

 5. Gamji

 6. Gawo

 7. Kaiwa

 8. Geza

 9. Kalgo

 10. Malga

 11. K’ok’iya

 12. Alillibo

 13. Gora

 14. Wuyan damo

 15. Mad’aci

 16. Molo

 17. Ced’iya

 18. Aduwa

 19. Dashe

 20. Marke

 21. Tsiriri

 22. Faru

 23. Maje

 24. K’irya

 25. Katsari

 26. Kurya

 27. Kawo

 28. Turare

 29. Madobiya


Hanyoyin Zamani


Hanyoyin samun itace na zamani wad’annan hanyoyin ne wad’anda zamani ya zo da su wad’anda ba a san su ba a gargajiyance. A binciken da na yi ta hanyar yanar gizo (internet), jaridar Aminiya ta tabatar muna da cewa ba k’asar Hausa kawai ake sana’ar sassak’a ba domin kuwa ta binciko muna labarin wani mutum mai suna Sa’idu inda yake cewa Burina in bud’e kamfanin sassak’ar turami na zamani Sa’idu mai Turmi.

Duk wanda ake ce masa akwai  masu sana’ar sassak’ar turmi a tsakiyar k’asar makka da ke k’asar Saudiya zai yi mamaki. Aminiya ta gano wani wuri da ake kira ‘yan turmi a unguwar yubalash da ke yankin shara mansur birnin makka inda Hausawan Nijeriya da Nijer suke sassak’ar turame iri-iri. Alhaji Sa’idu Sani Borno d’an Nijeriya ne da ya yi shekaru masu yawa yana sassak’ar turame a wurin.

Ya bayyana dalilin da ya sa yake sassak’a turame a Saudiya da irin nasarori da kuma matsalolin da yake fuskanta.

 • Hanyoyin Sarrafa Itace


Idan masassak’i yana son ya sarrafa wani abu kamar turmi da ta’barya ko kuma wani abu na daban wanda ba wad’sannan ba yakan je daji ya saro icce ya kawo gidansa ko wurin sana’arsa wani lokaci a dajin zai bar iccen sai ya yi aikin sa a can. Bayan ya sami iccen da ya ga ya dace da yin turmi kamar iccen mark’e ko loda ko k’irya ko dalbejiya ko gawo ko dai wani icce mai k’arfi sai ya yanke inda yake so daga nan sai ya kawo kayan aikin da zai yi amfani da su irin su gatari da gizago da wuk’a da mahuji da dai sauransu daga nan sai ya shiga aiki.

Yakan sanya mahuri ya rik’a hure iccen watua ya rarage shi sannan sai ya kwashe tukar da ke cikin turmin sai ya zubar yayin da masassak’i ya ga ya soma zama irin abin da yake so sai ya gyara shi ya sanya abin lauyewa kad’an-kad’an cikinsa da waje sannan daga baya sai ya shafa wa kan turmin wani makk’o wani abu makamancinsa wanda zai sanya turmin ya kama yin walk’iya yana haskakawa domin ya jawo hankalin masu saye.

Har ila yau sakkarawa sukan saro iccen aduwa ta amfani da gatarinsu inda za su sare reffen icce domin su yi ‘botar/k’otar fatanya (kwasa) ko ta kalme ko allon karatu ko kuma k’otar sungumi. Inda za su sassak’e itacen har su zama irin abin da suke buk’ata.

 • Masassak’a a Garin D’akin-gari


Kowace irin sana’ar da ake yi a k’asar nan ba ma k’asar D’akin-gari kad’ai ba za a tasras da cewa akwai jinsi ko k’abilar da ta ke’banta da ita. saboda haka sana’ar sassak’a sana’a ce wadda mutanen da ke yin ta a garin D’akin-gari Hausaw ne kuma su mutanen da ke wannan sana’a suna yinta ne bayan ga cewa suna da wata hanyar cin abincinsu wato sana’ar noma. Duk da haka ita wannan sana’ar yawancin wad’anda ke yin ta sun gade ta ne ga iyayaen ba sun yi mata hawan k’awara ba ne. amma duk da haka akan sami wad’anda ba su gada ba. sun koya kuma sun iya ta ta kuma zama ita ce sana’arsu.

Haka zalika masu aiwatar da wannan sana’ar ana kiran su da suna sakkarawa idan dai jam’insu ne amma idan mutum d’aya ne ana kiran sa da suna sakke. Bayan haka su wad’annan mutane suna rik’e da wannan sana’ar ce domin k’ara hanyar cin abinci da kuma suturarsu da sauran lalurorinsu na yau da kullum. Bugu da k’ari ita wannan sana’a sana’a ce da maza kawa ke yin ta kuma mazan manya na yi matasa na yi. Amma mata ba su yin wannan sana’ar a garin D’akin-gari. Dangane da haka ashe ke nan wannans ana’a ce da ta ke’banta ga jinsin maza kawai ko sun gada ko ba su gada ba.

 • Ire-iren Itatuwan Da Ake Amfani da Su a Wajen Sassak’a


Da yake wannan sana’a ce da ake amfani da itatuwa ana sarrafa su domin mayar da su wani abin amfani ta fuskoki daban-daban domin inganta wasu ‘bangarori na bunk’asa tattalin arzikin al’umma. Dangane da haka ga jerin itatuwan da aka fi amfani da su a sana’o’in sassak’a:

 1. Iccen kolo

 2. Iccen k’irya

 3. Iccen dogon yaro

 4. Iccen kanya

 5. Iccen mak’arho

 6. Iccen kamdare

 7. Iccen katsitsi

 8. Iccen d’orowa

 9. Iccen katsari

 10. Iccen malga

 11. Iccen gwabsa

 12. Iccen faru

 13. Iccen kawo

 14. Iccen wandama

 15. Iccen taramniya

 16. Iccen gyayya

 17. Iccen hono

 18. Iccen aduwa

 19. Iccen tsirri

 20. Iccen mad’aci

 21. Iccen maje

 22. Iccen doka

 23. Iccen kad’e

 24. Iccen taura


Magungunan da Ake Samu Ga Masu Sana’ar Sassak’k’a


Kamar yadda an yi hira da sakke Nura dogo da Faruk’u Sani da D’angaye da Babiyo da Sanda da Babbari duk wad’annan sakkarawa ne sun tabbatar min da cewa ana samun magugunguna daban-daban a sana;arsu ta sassak’a. Amma kuma galibi an fi samun magungunan ne ga ‘yan gado wato wad’anda suka gade ta kaka da kakanni ba wad’anda suka d’auke ta daga sama ba. ga jerin magungunan da suke bayarwa kamar haka:

 1. Maganin makero

 2. Maganin k’yasfi

 3. Maganin gizo-gizo

 4. Maganin karjayen icce

 5. Maganin sard’en icce (taho mu gama)

 6. Maganin dukkanin wani icce ko k’ayar icce

 7. Maganin shawara


Nad’ewa


A wannan babi an yi bayanin dukkan k’umshiyar wannan babi daga farkonsa har zuwa k’arshensa a tak’aice. Sai kuma ma’anar sassak’a inda aka kawo ma’anoni daban-daban dangane da sassak’a. Daga nan kuma sai kayan aikin sassak’a wanda a wannan sashe an yi k’ok’arin kawo kayan aikin sassak’a a tak’aice. daga haka kuma sai hanyoyin samun itace inda aka nuna yadda masu wannan sana’ar ke samun itatuwa su mayar da su wani abun amfani ga al’umma. Sai kuma hakayoyin sarrafa itace domin mai da abin amfani ga al’umma. Sai kuma masassak’a a garin D’akin-gari inda ake k’ok’arin kawo bayanin irin nau’o’in da jinsin mutanen da ke yin wannan sana’ar a garin D’akin-gari. Daga nan sai ire-iren itatuwan da ake amfani da su a wajen sassak’a. Inda ake amfani da hanyoyi daban-daban wajen samunitatuwan da ake amfani da su a sana’ar sassak’a. Daga nan sai magungunan da ake samu ga masu sana’ar sassak’a inda aka yi bayanin yadda suke samar da magunguna a cikin wannan sana’ar ta sassak’a a k’arshe sai kuma nad’ewa wanda shi wannan sashe bayanin nad’e babin ne a tak’aice.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/