Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi (Alhaji Musa Danba’u Gigan Buwai)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

www.amsoshi.com

Rubutawa: Shehu Hirabri 
08143533314
 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Hamma’ali mukai mu kwan biyu,

Yara:    Malami Maigandi na biɗata.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Abin da kai man hamdullahi,

Malami Maigandi ba mu ramma.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Malami ka ima shirya dambe,

Malami ka ima shirya dambe,

In ka bugi baki da zuciya,

Ka tabbata k’ato ya suma,

Yara:   Sai ka yi wajen wuya ka isai.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Kada ka ce ni ina gama ni,

Kada ka ce ni ina gama ni,

Kowa na gaya maka da zahi,

Yara:   To kai ma gaya masa da zahi.

 

Jagora: In kowa na gaya maka da zahi,

Yara:   To kai ma gaya masa da zahi.

 

Jagora: Don zaki in ya kai k’arhi,

Yara:    Bai jin tsoron karo da giwa

Jagora: A ɗan sarki in ya gawurta,

Yara:    Bai jin tsoron karo da sarki.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: A Hamma’ali na tafi yawo,

Ga wani nai muna kurin banza,

Ya ce shi aka wa Sardauna,

Sai nac ce kauce da nesa,

Yara:   Kusun kusumi ba ya kyau da sarki.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

Jagora: Cikin ‘yan sarki na Hamma’ali,

Akwai wani sata yakai da rana,

Shi wannan ya zame muzuru×2

Yara:   ‘Yan kaji bai bari su girma.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna

 

Jagora: Na sauka Kware don in ga ciyaman,

Na tahi ofis sai nig gaisai,

Sai ya ce ba ni kuɗɗin mai,

Da ya ce a ba ni kuɗin mai,

Ni yi jira ba a mik’a min ba,

Ni mamaki ya kama ni,

Ga rijiya ta ba da ruwanta,

Yara:   Sai guga ta hana a ɗebo.

 

Amshi: Sardaunan Hamma’ali zaki,

Malami Maigandi bi da arna.

 

 

Jagora: A Ɗanmaliki na Kware dwatijo,

Haji Hayatu na gode mai,

Yara:   Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: Ɗanmaliki na Kware mai nera,

Ka ga ta kowa ɗan dattijo,

Sun kauce maka ko don dole,

Im Haji Hayatu na gode ma,

Yara:   Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A Alhaji Arziki Ɗankwangila,

Yara:   Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A Ɗannayintin ban rena mai ba,

Yara:    Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: Alhaji Aminu gaida Ɗankabo,

Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A ni Ɗankabo Alhaji Aminu,

Yara:    Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A ni Bello tihwa ba rana mai ba,

Yara:    Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A ga Bushiya mai naman rago,

Yara:    Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: A Bagobiran nan ta Ɗantasakku,

Ɗanba’u ya yaba da girma×2

 

Jagora: A ni shugaba Raha na gode,

Yara:   Ɗanba’u ya yaba da girma.

 

Jagora: Rai ya daɗewa mai tayoyi,

Mai kamfanin taya na gode.

Yara:   Ɗanba’u ya yaba da girma.

Post a Comment

0 Comments