https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

NA


 


MUSA SULEIMAN


08061256096


Musasuleiman424@gmail.com


 


 


KUNDIN BINCIKE NA SHAIDAR KAMMALA KARATUN DIGIRIN FARKO (B.A HAUSA), DA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO SAKKWATO.


 


https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

BABI NA ‘DAYA: GABATARWA


Shimfid’a


Harshe wata halitta ce da Allah Ya yi wa bani Adama,wadda yake amfani da ita domin sadarwa. Shi kuma nazarin kimiyyar harshe fage ne da yake da alak’a da sadarwa. Sanin wasu abubuwa da harshe ya k’unsa sai dai Allah (S.W.T.). Duk da haka, masana da manazarta kimiyyar harshe, sun duk’ufa domin fito da abubuwan da harshe ya k’unsa. Masana da dama suna gudanar da bincikensu a kan wasu ‘bangarorin  harshe da suka had’a da:

 • Ilmin furuci.

 • Ilmin tsarin sauti.

 • Ilmin k’irar kalma.

 • Ilmin ginin jimla.

 • Ilmin ma’ana.


A tak’aice dai, wannan nazari ya fad’o a k’ark’ashin ilmin k’irar kalma, wanda yake da take: “Sigogin Kumbura a K’irar Kalmomin Hausa”. Wannan bincike yana d’auke da babi guda hud’u. Babi na d’aya ya k’unshi shimfid’a, bitar ayyukan da suka gabata, hanyoyin gudanar da bincike, manufar bincike da kuma nad’ewa.

Babi na biyu ya k’unshi nazarin k’irar kalma, rassan nazarin k’irar kalma da alak’arsu da kumbura, hanyoyin nazarin k’irar kalma, fasalin k’irar kalma jiya da yau da kuma nad’ewa.

Babi na uku yana d’auke da sigogin kumbura wanda ya had’a da ma’anar kumbura, nau’o’in kumbura da kuma nad’ewa.

Babi na hud’u ya k’unshi tak’aitawa, kammalawa gami da manazarta.

Amma a nan, wannan babin ya k’unshi: Bitar ayyukan da suka gabata, hanyoyin gudanar da bincike, manufar bincike da kuma nad’ewa.

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


Kafin a shiga tsundum! Ga gudanar da wannan bincike akwai buk’atar a waiwayi baya,a ga irin gudummawar da wad’ansu manazarta da d’aliban kimiyyar harshe suka bayar. Musamman wad’anda suka gudanar da binciken da ya shafi kimiyyar harshe. A yi amfani da wad’anda suke da kusanci da wannan binciken.

Daga cikin ayyukan da za a duba,a kuma yi bita tare da yin amfani da su sun had’a da: Bugaggun littatafan da suka shafi kimiyyar harshe, musamman ma k’irar kalma, da k’undaye da mujallu da k’asidu da kuma yanar-gizo wanda aka fi sani da “internet” domin tattara bayanai da binciken masana musamman wad’anda suka kusanci wannan binciken.

Junju M.H. (1980):A cikin littafinsa  mai suna “Rayayyen Nahawun Hausa” ya yi bayani a kan sassan kalma da k’arin ma’ana gabanin saiwar tushe da tushen kalma. Inda ya nuna yadda ake samun saiwar kalma. Haka kuma, ya yi bayani a kan yadda ake samun k’ari a gaban saiwar kalma kamar haka: Katshina – Bakatsine, Kano – Bakano.

Duk da haka ya k’ara bayanin yadda ake samun k’ari,a gaban saiwar kalma ta hanyar d’afi. Misali:

Danne – dann – danniya

Goce – goc- gociya

Skinner, N (1977): A cikin littafinsa mai suna “A Grammar of Hausa for Secondary Schools and collages”, ya nuna yadda wasu k’wayoyin ma’ana suke gudana a tsakanin wasu kalmomi. Idan ya d’auki kalma, misali: “d’aki” yana nuna d’afin da aka k’ara a saiwar Kalmar domin sifarta ta canza kamar haka:

‘Dak- + [-una], d’ak-+ [-i], d’ak-  + [-a].

A nan nake ganin Junju (1980) ya tak’aita aikinsa ne kawai a kan yadda ake samun k’ari a gaban kalma ko bayyana ta kawai. Shi kuwa wannan bincike zai d’ora a kai domin fito da sigogin kumbura.

Duk irin wad’annan k’wayoyin ma’anar ya bayyana a tak’aice. Wannan bincike nasa ba zai hana gudanar da wannan bincike ba. Domin wannan bincike zai fi mai da hankali ne a kan kumbura da sigoginta a k’irar kalmomin Hausa.

Bagari (1986): A cikin littafinsa mai suna “Bayanin Hausa: Jagora ga Mai Koyon Ilmin Bayanin Haushe”. Littafin yana d’auke da manyan babuka guda uku. Babi na d’aya yana d’auke da fasali guda takwas. Inda babin ya yi bayani a akan sautuka. Babi na biyu yana d’auke da fasali guda bakwai, wanda ya yi Magana a kan k’irar harshe da nahawun harshe. Babi na uku yana d’auke da fasali guda d’aya wanda ya k’unshi kalmomi. A cikin babi na uku ya yi bayani a kan ‘yantattun k’wayoyin kalmomi da turkakkun k’wayoyin kalma. Ya bayyana cewa: “k’wayoyin kalma iri-iri ne, wasu za su iya zama su kad’ai a matsayin kalma. Wasu kuma sai sun had’u da k’wayoyin kalma sannan su ta da kalma. Misaali: sha, ci, d’aya, zauna, duk wad’annan ‘yantattu ne (free morphemes)su kuma wad’anda suke dogara da wasu sun had’a da: [-anta], [-waa], [-ee], [-e] su ake kira da (bound morphemes). Haka kuma ya yi bayani a kan d’ofane da k’wayar kalma. Amma bai yi bayani a kan kumbura ba. Ina ganin cewa wannan ba zai dakatar da wannan binciken ba, wanda yake k’ok’arin fito da sigogin kumbura a k’irar Kalmar Hausa.

 Booij (1993):A cikin mujallar Year Book of Morphology.A ta sa gudummawar mai taken”Inherent ‘bersus conted’tual inflection and the split morphology hypothesis”.Ya yi bayani a kan k’irar kalma, musamman ma kumbura inda ya kalle ta,ta fuskoki guda biyu wato k’aramar kumbura da babbar kumbura da take nuna jituwa ta zahiri da ta bad’ini da kuma wanda ke nuna jagoranci. Duk wannan aikin ya gabatar da shi cikin harshen Ingilishi. Ganin haka ya tabbatar da wannan binciken ya zo daidai da lokacin da ake buk’atar shi a cikin harshen Hausa.

Abubakar (2001): A cikin wannan littafi nasa mai suna “Introductory Hausa Morphology”, ya yi bayani mai yawa, kuma mai gamsarwa a kan k’irar kalma a Hausa bisa tsari na nazarin k’irar kalma da kuma k’wayoyin ma’ana. Sai dai ya fi mai da hankalinsa a kan k’irar kalmomin Hausa wato tsira da kumbura da kuma hard’antawa. Sai dai bai yi sharhi sosai a kan kumbura ba. Tunaninsa ya fi raja’a a kan yadda ake k’era kalmomi kawai. Shi kuma wannan bincike ya fi damuwa da kumbura da kuma sigoginta a k’irar Kalmar Hausa.

Sani (2002): A cikin alfiyarsa mai taken “Tsarin Sauti Da Tasarifin Hausa A Wak’e”. Littafin yana d’auke da babuka guda biyu. Babi na d’aya ya yi bayani a kan tsarin sauti. Babi na biyu ya yi bayani a kan k’irar kalma. A cikin babin na biyu, malamin ya yi bayani a kan kumbura da yadda take nuna jinsi da adadi, inda ya bayar da misalansa a cikin baituka kamar haka:

845 – Misalanmu nan ta wajen kumburi,

Kawo su za mui yi a jinsi,ka ji.

 

846 – Har adadi nan fa tare dad’a,

Da iko na Allah a wannan wuri

848 – Saiwa ta {gunt-} daga guntu a nan,

Ka k’ara d’afa-k’eya {-uwa}, ka ji.

849 – In ka yi hakan guntuwa za ka ga,

Wato macen ai a wannan wuri.

Dangane da wannan bayanin da ya yi ya fi mai da hankalli ne a kan kumburar kalma ta nuna jinsi da kuma adadi kamar yadda ya bayyana a cikin baitocin wak’arsa.Amma wannan bincike zai yi k’ok’arin fito da sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Daura (2002): A cikin mujalla mai suna Algaita, a gudummuwarsa mai taken “Morphological and Phonological Adaptation of Arabic Loan Words into Hausa”. Ta yi k’ok’arin bayyana kalmomin Arabic da na Hausa da yadda k’irar kalmominsu ke gudana da kuma alak’arsu. Haka kuma ta bayyana hanyoyin da Hausa take aro kalmomi daga Larabci ta wad’annan hanyoyi:

 • Mayewar bak’ak’e.

 • Mayewar wasulla.

 • Sharewar bak’ak’e.


Haka kuma ta bayyana misalan kamar haka:

Hausa

Karya                                                  Kakkarya

(to break)                                             (to break into several pieces)

Arabic

Kasara                                                 Kassara

(to break)                                             (to break into several pieces)

Dangane da wannan bincike nata ba ta fito da sigogin kumbura ba, ta fi mai da hankalinta a kan kwatancin yadda harsunan suke k’era kalmomisu. Wanda shi kuma wannan bincike ya fi mai da hankali a kan sigogin kumbura.

Ummulkhairi (2002/2003): A cikin mujallar Harsunan Nijeriya Volume number 1 wanda ta rubuta a cikin harshen Ingilishi. A gudummawarta mai taken “Similerities and Differencies Between Inflectional and Drivational Affid’es in Hausa”. A cikinta ta kawo bayanai da ke nuna yadda k’wayar kalma da ake d’afa ta a kalmar da cewa, ba ta sauya ma’anar kalma. Sai dai ta nuna jinsi da kuma adadi. Haka kuma, ta kawo bayanai da ke nuna yadda k’wayar kalmar da aka d’afa wa tushen kalma da ta tsira ke sauya ma’anar kalma nan take. Haka kuma ta kawo irin bambance-bambancen da ake samu tsakanin tsira da kumbura. Misali tana cewa:

Kumbura: Tana kak’o ‘boyayyar ma,ana.

Tsira: Tana kawo ma’ana ta sarari.

Sai dai malamar ta fi damuwa da kamanninsu da kuma bambancinsu , wanda kuma ba shi muke buk’ata ba. Mun fi damuwa da sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Sani (2003):A cikin mujallar Harsunan Nijeriya ‘Bolume d’d’. A tasa gudummawar mai taken “Hausa Agentivebe Nominalization”. A ciki ya kawo bayanai masu yawa da yake nuna yadda ake d’afa-goshi da k’wayar kalma ta [-ma] ga tushen kalmomin aikatau, ta sauya musu aji su koma kalmomin suna. Kamar yadda ya kawo, ana amfani da wannan k’wayar kalma ne wajen sauya ajin kalma daga wani rukuni zuwa wani, musamman daga ajin aikatau zuwa ajin suna. Duk wannan aikin da ya yi ya tak’aice shi ne kawai a iya tsira da kumbura. Don haka wannan nazarin ke ganin aikin Sani (2003) ba zai hana shi gudana ba. Domin wannan nazari zai tunkari yadda sigogin kumbura suke a k’irar kalmomin Hausa.

Fagge (2004): A cikin littafinsa mai suna “An Introduction to Hausa Morphology”. Littafin wanda ya rubuta da Ingilishi yana k’unshe da babuka guda hud’u. A cikin babi na hud’u ya yi bayani a kan kumbura, inda ya bayyana yadda k’wayar kalma ke canza ma’anar kalma ta hanyar sauya d’afi. Misali:

 • Murz- + [a] = murza.

 • Murz- + [ee] = murzee.

 • Murz- + [oo] = murzoo.

 • Murz- + [u] = murzu.


Haka kuma, ya nuna yadda kalma take kumbura ta nuna jinsi da adadi. Misali:

 • Kafir + a

 • Kafir + i

 • D’alib + i


A nan ya tak’aita aikin a kan wad’annan misalan wanda ya fi mai da hankali a kan kumbura wadda ke nuna jinsi da adadi. Wannan ba zai dakatar da wannan binciken ba domin ya fi mai da hankali ne a kan fito da sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Marial and Gil (2006): A cikin littafinsa mai suna “Linguistics and Universal”. Malamin ya kawo bayanai na yadda za a fasalta nazarin kimiyyar harshe da irin sauyin da ake iya samu a harshe. Haka kuma ya kawo bayanai da suka shafi ginin jimla da kuma yadda za a yi nazarin k’irar kalma a harshe .Haka shi ma, yafi maida hankalinsa a tsirar kalmomi da kumburarsu.Duk wannan ba zai hana gudanar da wannan binciken ba.Domin wannan binciken zai fi maida hankali ga sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Amfani (2007): A cikin littafinsa mai suna: ‘Basic linguistics for Nigerian languages Teachers’ wanda masana kimiyyar harshe suka wallafa, duk da cewa an wallafa shi ne musamman domin samar da hanyar da ta dace malaman harshe su bi wajen koyar da harsunan Najeriya. A tasa gudumawar ya kawo bayanai da suka shafi nahawun harshen Hausa da suka had’a da: ginin jimla, tsarin sauti, k’irar kalma da kuma k’wayar kalma. Malamin ya nuna cewa; kalma ko da suna ce ko aikatau ko sifa za ta iya zama k’wayar kalma. Inda ya ba da misali da Kalmar ‘wata’. Ya ce: idan aka d’auki saiwar wato [wat-] aka yi mata d’afi na d’afa-k’eya na [-a] za ta nuna jinsi da adadi. Misali

 • Gida (House) = gidaje  (Houses)

 • Jaki (male donkey) =          jaka (female donkey)

 • Fari (white) =          farare (whites)

 • Shege (male bastard) =          shegiya (female bastard)


A nan ya tak’aita bayanin nasa ne kan wad’annan misalai. Don haka wannan nazarin ke ganin aikin ba zai hana shi gudana ba. Domin wannan nazarin ya raja’a ne a kan sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Abdulkarim (2008): A cikin k’undin digirinsa na farko (B.A. Linguestics) wanda ya yi a sashen koyar da Harsunan Turai da Ilmin Kimiyyar Harshe, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sokkwato. A bimcikensa da ya yi a cikin harshe Ingilishi mai taken “Affid’ation in Hausa”, ya yi bayananin k’irar kalam, d’afi da kuma nau’o’in d’afi. Haka kuma ya yi bayani a kan kumbura da tsira da k’wayar kalma tare da nau’o’inta. A cikin aikin nasa ya k’ara bayani a kan kumbura ta nuna jinsi da adadi kamar yadda ya bayyana. Misali:

 • Waw + a = wawa

 • Waw + anya = wawanya


Idan aka dubi wannan aiki da ya gudanar ba zai hana gudanuwar wannan bincike ba, domin wannan binciken zai fi mai da hankalinsa a kan sigogin kumbura a fagen nazarin k’irar kalmomin Hausa.

Yusuf  (2011): A cikin littafinsa mai suna “Hausa Grammar an Introduction”. Littafin ya k’unshi babi bakwai. A cikin babi na d’aya ya yi bayani a kan kumbura wadda take nuna jinsi da adadi. Ya nuna yadda saiwar kalma ke kumbura ta nuna jinsi da adadi.

Misali:

 • Abok- + [-i] = aboki

 • Abok- + [-iya] = abokiya

 • Bak’- + [-i] = bak’i

 • Bak’- + [-a] = bak’a


Amma bai yi wani bayani sosai a kan kumbura ba. Sai dai ya d’an tsakuro abin da hannunsa ya kai gare su. Ganin wannan aikin da ya yi, yana buk’atar a k’ara fad’ad’a bincike domin shi wannan nazari zai k’ara fito da sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Muhammad (2011): A cikin k’undin digirinsa na biyu (M.A. Hausa Studies). A Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo, Sakkwato. A cikin wannan gagarumin aikin da ya yi bayani a kan k’irar kalma, tak’aitaccen tarihin k’irar kalma da samuwar k’irar kalma. Haka kuma ya yi bayani mai gamsarwa a kan rassan nazarin k’irar kalma, wanda suka had’a da kumbura da kuma tsira. Haka kuma malamin ya daddagi k’wayar Kalmar Hausa yadda ya kamata. A cikin wannan gagarumin bincike ya nuna yadda kumbura take nuna jinsi da adadi da giredi daga na d’aya har zuwa na bakwai. Sai dai ya yi bayani a kan kumbura a tak’aice, domin bai fad’ad’a kumbura yadda ya kamata ba, ya nuna yadda kalma take kumbura ta nuna jinsi da adadi. Wannan muhimmin aiki nasa ba zai hana ci gaba da wannan bincike ba, domin wannan bincike zai fi mai da hankali ya fito da sigogin kumbura a k’irar kalmomin Hausa.

Sani  (2011): A cikin littafinsa mai suna “Gamayyar Tasarifi da Tsarin Sauti.” Littafin ya rubuta shi ne domin ya fito da irin alak’ar da ke tsakanin k’irar kalma da tsarin sautin Hausa. Malamin ya yi k’ok’arin ya fito da fitattun wurare wad’anda tsarin sauti yake da tasiri a kan k’irar kalma, kamar k’wayoyin kalma na madanganci da na nasaba da kuma mahad’i. Haka kuma ya kawo fitattun wuraren da k’irar kalma ke da tasiri a kan tsarin sauti kamar k’wayar sautin gand’a da kuma le’bantawa, daga k’arshe sai ya kawo bayani a kan yadda haushen Hausa ke samar da sababbin kalmominsa. Sai dai bai fito da bayani ba a kan abin da ya shafi kumbura tsura ba, kuma wannan bincike ya fi mai da hankali a kan sigogin kumbura.

Halliru (2013): A cikin mujallar D’und’aye. A tasa gudummawar mai taken “Aspects of Hausa Morphological Process”. Malamin ya yi bayani a kan k’irar kalma, d’afi da tsira da kumbura da kuma k’wayar kalma. Sai dai bai yi wani cikakken bayani a kan kumbura ba, wanda kuma wannan bincike kai zai fi mai da hankali.

1.2     HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


Ana gudanar da wannan bincike ne ta hanyar shiga d’akunan karatu, domin karanta wasu daga cikin ayyukan da aka gabatar musamman na kimiyyar harshe, wad’anda ke da dangantaka da wannan bincike.

Ganawa da malamai da manazarta da d’alibai, domin samun k’arin haske dangane da wannan bincike.

Shiga hanyar sadarwa ta zamani wato ‘internet’ domin samun k’arin bayanai wad’anda suka shafi wannan bincike.

1.3     MANUFAR BINCIKE


Domin samun takardar kamala karatun digiri na farko (B.A. Hausa).

Domin ba da tawa gaggarumar gudummawa ga bunk’asa harshen Hausa, saboda ‘yan baya da za su zo su samu abin dubawa da zai taimaka musu wajen fahimtar inda aka dosa.

 

 

1.4     NA’DEWA


Cikin wannan babi an ga yadda muka kawo bayanai na ayyukan masana da manazarta da d’alibai musamman ma na kimiyyar  harshe wad’anda suka gudanar da bincike ta fuskoki daban-daban. Wasu daga cikinsu kai tsaye suke da alak’a da wannan bincike da ake buk’atar gudanarwa. Wasu kuma sun k’yallaro wani ‘bangare daga cikinsa.

Haka kuma,an gabatar da bayanai a kan hanyoyin gudanar da wannan bincike tare da bayyana manufar wannan bincike da kuma nad’ewa a tak’aice.

 

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/