MUSA SULEIMAN
08061256096
KUNDIN BINCIKE NA SHAIDAR KAMMALA KARATUN DIGIRIN FARKO (B.A HAUSA), DA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO SAKKWATO.
TABBATARWA
Na tabbatar da wannan k’undin ya cika sharrud’a da kuma k’a’idojin shi, domin samun shaidar digirin farko a sashen Harsunan Najeriya (B.A. Hausa) a Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato 2015.
__________________________ _______________
Isah Abdullahi Muhammad Kwanan wata
(Mai dubawa na farko)
________________________ _______________
Prof. A.M. D’antumbishi kwanan wata
(Shugaban Sashen Harsunan Nijeriya)
_________________________ _______________
Mai dubawa na biyu Kwanan wata
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan bincike ga dukkan iyalan marigayi Suleiman Mayanchi da iyalan gidan marigayi Alhaji Ahmadu Sufi K’ofar Mazugal, musamman mahaifina marigayi Halilu Lawal K’ofar Mazugal, da mahaifiyata Hajiya Umma Ahmad Sufi da dukkan wad’anda suka tallafa wajen d’aukar d’awainiyar karatuna tun daga farkonsa har zuwa wannan mataki.
Ina rok’on Allah Ya kyautata rayuwarsu, ya kuma biya musu dukkan buk’atunsu na alkairi, ya kuma ba su lafiya da zaman lafiya a tsakaninsu, Amin.
GODIYA
Dukan godiya ta tabbata ga Allah mad’aukakin sarki mai kowa mai komai, wanda ya sanar da mutum abin da bai sani ba. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, cikamakin Annabawa , Annabi Muhammad (S.A.W), da iyalan gidansa da sahabbansa da dukkan wad’anda suka yi rik’o da sak’onsa, suka bishi da gaskiya har ranar tashin Alk’iyama.
Bayan godiya ga Ubangiji wanda ya ba ni lafiya da ikon kammala wannan bincike. Da farko, ina mik’a godiya ta musamman wadda ba ta da iyaka ga malamina, Malam Isah Abdullahi Muhammad, Na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya (Hausa). Wanda ya sadaukar da lokacinsa wajen duba wannan bincike. Wanda ba don da taimakonsa ba, da wannan bincike ba zai karantu ba. Ina k’ara mik’a godiya ta musamman ga irin taimakon da ya yi a gare ni da dukan abin da na nema da kuma ba ni shawarwari a kowane lokaci tun daga farkon wannan binciken har zuwa k’arshe. Allah Ya saka masa da alkhairinsa, ya kuma kara masa lafiya da rufin asiri da basira ya kuma tsare shi da dukan iyalansa, ya kuma tsare shi daga dukan sharri na rayuwa.
Ina mik’a godiya ga dukan malamaina na wannan sashe domin da bazarku ce nake rawa har na kai matakin da nake a yau na yin wannan bincike. Allah Ya saka muku da alkhairinsa Ya kuma kare ku a duk inda ku ka sami kanku, amin.
Bugu da k’ari, ina mik’a godiya da jinjina ga iyayena, Marigayi Halilu Lawan Kofar Mazugal da mahaifiyata Hajiya Umma Ahmad Sufi, wad’anda suka tarbiyantar da ni, kuma suka d’ora ni akan hanya madaidaiciya, musamman ta neman ilimi tare da azan i bisa ga hanya managarciya. Ina rokon Allah mai kowa mai komai Ya gafarta masu Ya kyautata makwancinsu Ya kuma sa Aljanna ta zamo sakamakonsu na k’arshe, amin.
Haka zalika ina mik’a godiya ga yayye na da k’annena wad’anda bazan ta’ba mantawa da su ba a rayuwa ta, domin kuwa a kodayaushe fatansu a gare ni na zanto mutum na gari mai ilimi da kuma aiki da shi. Haka kuma ina mai godiya da farin ciki da addu’ar da ku ke yi mini a kodayaushe da irin goyon baya da ku ke ba ni a kowane lokaci. Ina rok’on Allah Ya saka muku da alkhairi Ya kuma k’ara had’a kanmu Ya tsare mu da sharrin rayuwa.Amin.
Haka kuma,ba zan ta’ba mantawa da abokai na da ‘yan ajinmu bisa ga irin goyon baya da gudunmawar da na samu a gare ku. Na san babu wata kalma da zan yi amfani da ita ya zam na gamsar da ku,ba domin kuwa ban san iyakar gatan da ku ka yi mini ba wajen karatu. Sai dai kawai in ce Allah Ya biya muku bukatun ku, kuma ya sa aljanna ce makomarku.Amin.
Haka kuma ina mik’a godiya ta musamman ga dukkan dangina da duk wanda Ya taimaka koda da mene ne wajen gudanar da wannan bincike da karatu na baki d’aya. Allah Ya saka wa kowa da alkhairi. Amin.
ABUBUWAN DA KE CIKI
Taken Bincike…..……………………………………………………i
Tabbatarwa…………………………………………………………..ii
Sadaukarwa…………………………………………………………iii
Godiya………………………………………………………………’bi
BABI NA 'DAYA: Gabatarwa
1.0 Shimfid’a…………………………………………………...1
1.1 Bitar ayyukan da suka gabata……………………………...2
1.2 Hanyoyin gudanar da bincike…………………………….13
1.3 Manufar bincike…………………………………….…….13
1.4 Nad’ewa…………………………………………………...13
BABI NA BIYU: Nazaarin k’irar kalma
- Shimfid’a…………………………………………………15
2.1 Ma’anar k’irar kalma…………………………………….15
2.2 Rassan nazarin k’irar kalma: Alak’arsu da kumbura…….16
2.3 Hanyoyin nazarin k’irar kalma………………….……….26
2.4 Fasalin nazarin k’irar kalma. A jiya da yau…….……….29
2.5 Nad’ewa………………………………………………….32
BABAI NA UKU: Sigogin Kumbura
3.0 Shimfid’a…………………………………………………33
3.1 Ma’anar Kumbura……………………………………….33
3.2 Nau’o’in kumbura……………………………………….35
3.2.1- K’aramar Kumbura (inherent inflection)………………...35
3.2.1.1- Jinsi (Gender)………………………………………….36
3.2.1.2- Giredi………………………………………………….39
3.2.1.3 Suna d’an aikatau……………………………………….44
3.2.1.4 Adadi (Number)……………………………………….45
3.2.2 Babbar Kumbura (comted’tual inflection)………………47
3.2.2.1- Jituwa (Agreement)………………………………….48
3.2.2.1.1- Jituwa ta zahiri ……………………………………49
3.2.2.1.2- Jituwa ta bad’ini…………………………………...50
3.2.2.2- Jagoranci (go’berning)………………………………51
3.4- Nad’ewa………………………………………………….52
BABI NA HU'DU:
4.0 Kammalawa:……………………………………………..53
4.1 Manazarta:……………………………………………….54
https://www.amsoshi.com/contact-us/
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.