Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'anar Waka Cikin Waka


(Alkali Haliru Wurno)
Waƙa ɗumi ne hira ko labari,
Zargi yabo zagi da kiznin sharri,
Koko kwaɗai ga mutum ya ba ka ka amsa.

Labar ɗumi na wanda kay yi ga tsari,
Wani dunƙulalle kay yi jeri-jeri,
A cikin nashaɗi ko ganin ka ƙosa.

Waƙe bayani na kaɗan na da tari,
Wani bi ka sa gishiri ka yo mishi ƙari,
Haɗari na waƙe mai faɗin damassa.


Waƙa da waƙe Hausa sun ɗauke su,
Sunansu waƙa ko’ina an san su,
Ka biɗo bayani babu sai dai kansa.

Waƙa fasaha ne da yac cuɗe ka,
Kuma ba karatuna ba in an ba ka,
Ilimi dubu sai ka biɗo wani nasa.

A cikin ɗumi waƙe kamar rana ne,
Koko ya zam hadarin ruwan bazara ne,
Shi taho da sanyinai na ma’aunin nesa.

Post a Comment

0 Comments