Ticker

6/recent/ticker-posts

Sassaƙa A Garin Ɗakin-Gari: Tasirin Zamani A Kan Gargajiya (3)

... sana’a ce ta gargajiya wadda ake aiwatarwa da hannu ta hanyar amfani da waɗansu kayan aiki wurin yin ta kamar su gatari da gizago da guru da ƙumbula da sauransu.

ABUBAKAR ALIYU

1310106004

www.amsoshi.com

BABI NA UKU

SASSAƘAR GARGAJIYA


Shimfiɗa

A wannan babi na uku mai taken sassaƙar gargajiya na da ƙananan sassa kamar dai yadda bayani zai biyo. A sashe mai magana a kan ma’anar sassaƙa sashen zai kawo ma’anar sassaƙa ne watau daga masana daban-daban sai kuma kayan aikin sassaƙa. Haka kuma za a dubi hanyoyin samun itace wanda shi ma bayani ne a akan hanyoyin samun itace. Daga nan kuma sai bayanin Hanyoyin sarrafa itacen wanda shi ma bayani ne akan yadda ake sarrafa itacen. Baya ga haka sai amsassaƙa a garin Ɗakin-gari. A nan za a kawo jerin masassaƙa ne a garin Ɗakin-gari wato masu yin wannan sana’a. sai kuma bayani kawo muna ire-iren itatuwan da ake amfani da su a wajen sassaƙa. Haka kuma sai bayanin yadda ake samun magungunan da ake samu ga masu sana’ar sassaƙa. A ƙarshe sai bayanin kammala abin baki ɗaya.

Ma’anar Sassaƙa


Sanin ma’anar sassaƙa na da muhimmanci domin ta haka ne kaɗai za a iya gane matsayinta ga al’umma. Saboda haka za a ga irin gudummuwar da take bayarwa wajen ci gaban al’umma  baki ɗaya. Haka kuma wasu na danganta sassaƙa da cewa, sana’a ce ta gargajiya wadda ake aiwatarwa da hannu ta hanyar amfani da waɗansu kayan aiki wurin yin ta kamar su gatari da gizago da guru da ƙumbula da sauransu. da kuma samun icce mai kamar da ake so. Amfani da shi a yi turmi ko kujera da taɓarya da alluna da mucciya da ɓotoci da sauransu.


To kamar yadda aka gani a cikin waɗannan bayanai na sama dangane da ma’anar sassaƙa ni a nawa gani sana’a ce ta gargajiya wadda ake aiwatarwa da hannu ta hanyar amfani da itatuwa daban-daban tare da waɗansu kayan aiki wajen aiwatar da ita. a kuma mayar da wannan iccen wani abun amfani kamar kujera ko turmi ko taɓarya ko mucciya ko ɓotoci da dai sauransu.

 

Kayan Aikin Sassaƙa


Duk sana’ar da aka ce sana’a ce da ake aiwatarwa da hannu to sai an sami kayan da ake amfani da su wajen aiwatar da ita. saboda haka sana’ar sassaƙa sana’a ce da ake yin ta da waɗansu kayayyakin aikin kamar haka:

1.     Gatari

2.     Guru

3.     Kumbula

4.     Mahuri

5.     Gizago

6.     Mazari

7.     Makwashi

 

o    Gatari

Shi ne abu na farko wanda ake amfani da shi wajen yin wannan sana’ar kuma aikinsa shi ne sare icce da shi ya faɗi kafin duk a soma wani aiki. Haka kuma gatari wani ƙarfe ne da maƙera kan ƙera wanda akan sanya shi a wata kussawa ta ɓota domin daɗin riƙawa.

3.2.2 Guru

Amfanin wannan abin aikin shi kuma ya keɓanta ne kawai yayin da za a yi turmi wnda da shi ne ake amfani a yi wa turmi wannan ramin da ake zuba abin daka. Haka kuma guru waƙni ƙarfe ne da maƙerakan ƙera wanda ke da wata ‘yar tanƙwara. Kuma yana da faɗin baki sai dai bai kai girman kwasa ba. amma ya yi kama da kwasa.

  • Kumbula

 

Tana ɗaya daga cikin kayan da ake amfani da su wajen aiwatar da wannan sana’ar kuma ɓota ce ta guru. Haka kuma ita kumbula tana da tanƙwara a samanta kuma ta fi sauran ɓotoci girma. Ana amfani da ita wajen sassaƙa babban turmi da kuma kwashe saman icce da sauransu.

  • Gizago

Ɗaya ne daga cikin kayan aikin wannan sana’a kuma wannan wata ‘yar ƙaramar hanya ce mai ‘yan ɓota wadda kamar da ita ce ake saisaye duk wani abu da suka yi wanda ya danganci wannan sana’a tasu. Hausawa suna masa kirari da gizago ba ka da sabo.

  • Mazani

 

Wannan wani ƙarfe ne marar kauri kuma bai wuce taƙar hannu biyu a. wanda ake amfani da shi a sanya shi wuta, idan ya yi zafi sai a yi wa turmi zane, amma ko turmin ƙaramin turmi domin ba a yi wa baban turmi zane kana kuma suna amfani da shi su zane kujera.

  • Makwashi

Wannan shi ne kuma masassaƙa (Sakkarawa) suna amfani da shi wajen kwashe abubuwa da ke cikin aikin da suka yi na sassaƙar. Domin abin ya zama ya ƙayatar kuma yana ban sha’awa tare da nuna ya yi sulɓi kuma yana ƙara haskaka a idon mutane masu san sayen kayan da suka sassaƙa. Kamar irin su turmin daka na mata da kujerar zama sannan kuma da ƙotar kalme ta noma.

 

  • Magagari

Wannan wan ƙarfe ne mai kama da wuƙa mai gorje-gorje mai kauri yana da abin riƙo kamar wuƙa amfanin wannan magagari shi ne ɗaɗi ake yi da shi da sauran ayyuka.

  • Wuta

A wannan sana’a ta sassaƙa na amfani da wuta wajen ƙwane iccen taɓarya wanda idan an sare iccen taɓarya sai a sa masa wuta sai samansa ya ƙone sai a kashe wutana ɗauka a kankare a jera.

A ƙarshe waɗannans u ne kayan da ake amfani da su a sana’ar sassaƙa.

  • Hanyoyin Samun Itace

Hanyoyin da ake samun itace kusan banyoyin biyu ne wato ta hanyar gargajiya da kuma ta zamani.

Gargajiya


Ta hanyar gargajiya shi ne inda basakkare (masassaƙi) yake ɗaukar gatarinsa ya je daji domin ya sare itacen da zai yi amfani da su a wurin sana’arsa kamar yadda na yi hira da sakkarawan garin Ɗakin-gari kamar haka:

Saddo Muhammadu shugaban sakkarawan garin Ɗakin-gari ya faɗa cewa hanya mafi sauƙi da basakkare ke samun itace zai ɗauki gatarinsa ya je daji mai nisan gaske nda ake samun manyan itatuwa waɗanda yake ba na gwamnati ne ba kuma ba kowa ne ke da su ba sai ya sari icce wanda yake so. Haka kuma ya ƙara da cewa a lokacin da basakkare yake saran iccen wani iccen yakan nuna waibuwar bai saruwa a duk lokacin da aka sare shi sai ya haɗe saran ko kuma sai mutum ya yi ta sara har ya kusan sarewa sai ya haɗiye saran (wato ya dawo kamar yadda yake). A duk lokacin da basakke ya ga icce yana yi masa hakan to waɗansu sakkarawan sukan yi wasu ‘yan siddabaru ga iccen domin nuna wa iccen tasu waibuwa wadda suka gada kaka da kakanni a inda waɗansu sakkarawan sukan bar icen sai su kama  ma wani wasu ko sukan bar dajin gaba ɗaya domin sun san ranar nan babu nasara ga wannan aiki. Sai kuma sakke Babbari Umaru wanda kuma shi ne shugaban sakkarawan shiyar fada. Shi ma ya cewa hanyoyin samun itace ga sakkarawa hanya mafi sauƙi ita ce wadda suka gada kaka da kakanni wato mutum ya je daji ya saro itace irin wanda yake buƙatar aiki da shi ko kuma ya ga wani ice godanar wani yakan iya roƙa a ba shi ko a sayar masa domin ya yi amfani da shi ya sarrafa zuwa wani abu. Abu Magi yana cewa a wasu lokuta idan basakke yana saran ice wasu itacen sukan nuna irin tasu waibuwa ta cewa ba su saruwa ko kumasu faɗawa wanda ke saransu su ka she shi ko su raunana shi ko kuma su faɗa masa wata ƙaddara tashi wadda yake da a gida. A yayin da wasu masassaƙan suka ga hakan, waɗanda suke ‘yan gado ga sana’ar wato ba hawanta ne suka yi ba daga baya sukan yi wasu ‘yan tsafe-tsafe domin su nuna wa iccen tasu buwaya.

Haka kuma sakke Babiyo Riniya a yayin da nake tattaunawa da shi kan hanyoyin da suke bi wajen samun itacen da suke amfani da su na sana’ar tasu. Shi ma ya gaya min cewa sukan je daji su saro icce ko su yi jinga a saro musu. Ya ƙara da cewa sukan saro itace irin su aduwa da maɗaci da gawo da dalbejiya (lim) da ƙirya da hanoda ɗanya da sauransu.

A ƙoƙarin tattaunawar da na yi da waɗannan mutanen a kan hanyoyin da suke bi wajen samun itacen da suke amfani da su wajen sana’ar sun gaya min da cewa suna amfani da itace daban-daban a lokacin da suke aiwatar da sana’arsu. Waɗannan itatuwa sun haɗa da:

1.     Dogon yaro (dalbejiyalim)

2.     Kaɗe

3.     Loda

4.     Danya

5.     Gamji

6.     Gawo

7.     Kaiwa

8.     Geza

9.     Kalgo

10. Malga

11. Ƙoƙiya

12. Alillibo

13. Gora

14. Wuyan damo

15. Maɗaci

16. Molo

17. Ceɗiya

18. Aduwa

19. Dashe

20. Marke

21. Tsiriri

22. Faru

23. Maje

24. Ƙirya

25. Katsari

26. Kurya

27. Kawo

28. Turare

29. Madobiya

Hanyoyin Zamani


Hanyoyin samun itace na zamani waɗannan hanyoyin ne waɗanda zamani ya zo da su waɗanda ba a san su ba a gargajiyance. A binciken da na yi ta hanyar yanar gizo (internet), jaridar Aminiya ta tabatar muna da cewa ba ƙasar Hausa kawai ake sana’ar sassaƙa ba domin kuwa ta binciko muna labarin wani mutum mai suna Sa’idu inda yake cewa Burina in buɗe kamfanin sassaƙar turami na zamani Sa’idu mai Turmi.

Duk wanda ake ce masa akwai  masu sana’ar sassaƙar turmi a tsakiyar ƙasar makka da ke ƙasar Saudiya zai yi mamaki. Aminiya ta gano wani wuri da ake kira ‘yan turmi a unguwar yubalash da ke yankin shara mansur birnin makka inda Hausawan Nijeriya da Nijer suke sassaƙar turame iri-iri. Alhaji Sa’idu Sani Borno ɗan Nijeriya ne da ya yi shekaru masu yawa yana sassaƙar turame a wurin.

Ya bayyana dalilin da ya sa yake sassaƙa turame a Saudiya da irin nasarori da kuma matsalolin da yake fuskanta.

  • Hanyoyin Sarrafa Itace

Idan masassaƙi yana son ya sarrafa wani abu kamar turmi da taɓarya ko kuma wani abu na daban wanda ba waɗsannan ba yakan je daji ya saro icce ya kawo gidansa ko wurin sana’arsa wani lokaci a dajin zai bar iccen sai ya yi aikin sa a can. Bayan ya sami iccen da ya ga ya dace da yin turmi kamar iccen marƙe ko loda ko ƙirya ko dalbejiya ko gawo ko dai wani icce mai ƙarfi sai ya yanke inda yake so daga nan sai ya kawo kayan aikin da zai yi amfani da su irin su gatari da gizago da wuƙa da mahuji da dai sauransu daga nan sai ya shiga aiki.

Yakan sanya mahuri ya riƙa hure iccen watua ya rarage shi sannan sai ya kwashe tukar da ke cikin turmin sai ya zubar yayin da masassaƙi ya ga ya soma zama irin abin da yake so sai ya gyara shi ya sanya abin lauyewa kaɗan-kaɗan cikinsa da waje sannan daga baya sai ya shafa wa kan turmin wani makƙo wani abu makamancinsa wanda zai sanya turmin ya kama yin walƙiya yana haskakawa domin ya jawo hankalin masu saye.

Har ila yau sakkarawa sukan saro iccen aduwa ta amfani da gatarinsu inda za su sare reffen icce domin su yi ɓotar/ƙotar fatanya (kwasa) ko ta kalme ko allon karatu ko kuma ƙotar sungumi. Inda za su sassaƙe itacen har su zama irin abin da suke buƙata.

  • Masassaƙa a Garin Ɗakin-gari

Kowace irin sana’ar da ake yi a ƙasar nan ba ma ƙasar Ɗakin-gari kaɗai ba za a tasras da cewa akwai jinsi ko ƙabilar da ta keɓanta da ita. saboda haka sana’ar sassaƙa sana’a ce wadda mutanen da ke yin ta a garin Ɗakin-gari Hausaw ne kuma su mutanen da ke wannan sana’a suna yinta ne bayan ga cewa suna da wata hanyar cin abincinsu wato sana’ar noma. Duk da haka ita wannan sana’ar yawancin waɗanda ke yin ta sun gade ta ne ga iyayaen ba sun yi mata hawan ƙawara ba ne. amma duk da haka akan sami waɗanda ba su gada ba. sun koya kuma sun iya ta ta kuma zama ita ce sana’arsu.

Haka zalika masu aiwatar da wannan sana’ar ana kiran su da suna sakkarawa idan dai jam’insu ne amma idan mutum ɗaya ne ana kiran sa da suna sakke. Bayan haka su waɗannan mutane suna riƙe da wannan sana’ar ce domin ƙara hanyar cin abinci da kuma suturarsu da sauran lalurorinsu na yau da kullum. Bugu da ƙari ita wannan sana’a sana’a ce da maza kawa ke yin ta kuma mazan manya na yi matasa na yi. Amma mata ba su yin wannan sana’ar a garin Ɗakin-gari. Dangane da haka ashe ke nan wannans ana’a ce da ta keɓanta ga jinsin maza kawai ko sun gada ko ba su gada ba.

 

  • Ire-iren Itatuwan Da Ake Amfani da Su a Wajen Sassaƙa

 


Da yake wannan sana’a ce da ake amfani da itatuwa ana sarrafa su domin mayar da su wani abin amfani ta fuskoki daban-daban domin inganta wasu ɓangarori na bunƙasa tattalin arzikin al’umma. Dangane da haka ga jerin itatuwan da aka fi amfani da su a sana’o’in sassaƙa:

 

1.     Iccen kolo

2.     Iccen ƙirya

3.     Iccen dogon yaro

4.     Iccen kanya

5.     Iccen maƙarho

6.     Iccen kamdare

7.     Iccen katsitsi

8.     Iccen ɗorowa

9.     Iccen katsari

10. Iccen malga

11. Iccen gwabsa

12. Iccen faru

13. Iccen kawo

14. Iccen wandama

15. Iccen taramniya

16. Iccen gyayya

17. Iccen hono

18. Iccen aduwa

19. Iccen tsirri

20. Iccen maɗaci

21. Iccen maje

22. Iccen doka

23. Iccen kaɗe

24. Iccen taura

Magungunan da Ake Samu Ga Masu Sana’ar Sassaƙƙa


Kamar yadda an yi hira da sakke Nura dogo da Faruƙu Sani da Ɗangaye da Babiyo da Sanda da Babbari duk waɗannan sakkarawa ne sun tabbatar min da cewa ana samun magugunguna daban-daban a sana;arsu ta sassaƙa. Amma kuma galibi an fi samun magungunan ne ga ‘yan gado wato waɗanda suka gade ta kaka da kakanni ba waɗanda suka ɗauke ta daga sama ba. ga jerin magungunan da suke bayarwa kamar haka:

 

1.     Maganin makero

2.     Maganin ƙyasfi

3.     Maganin gizo-gizo

4.     Maganin karjayen icce

5.     Maganin sarɗen icce (taho mu gama)

6.     Maganin dukkanin wani icce ko ƙayar icce

7.     Maganin shawara

Naɗewa


A wannan babi an yi bayanin dukkan ƙumshiyar wannan babi daga farkonsa har zuwa ƙarshensa a taƙaice. Sai kuma ma’anar sassaƙa inda aka kawo ma’anoni daban-daban dangane da sassaƙa. Daga nan kuma sai kayan aikin sassaƙa wanda a wannan sashe an yi ƙoƙarin kawo kayan aikin sassaƙa a taƙaice. daga haka kuma sai hanyoyin samun itace inda aka nuna yadda masu wannan sana’ar ke samun itatuwa su mayar da su wani abun amfani ga al’umma. Sai kuma hakayoyin sarrafa itace domin mai da abin amfani ga al’umma. Sai kuma masassaƙa a garin Ɗakin-gari inda ake ƙoƙarin kawo bayanin irin nau’o’in da jinsin mutanen da ke yin wannan sana’ar a garin Ɗakin-gari. Daga nan sai ire-iren itatuwan da ake amfani da su a wajen sassaƙa. Inda ake amfani da hanyoyi daban-daban wajen samunitatuwan da ake amfani da su a sana’ar sassaƙa. Daga nan sai magungunan da ake samu ga masu sana’ar sassaƙa inda aka yi bayanin yadda suke samar da magunguna a cikin wannan sana’ar ta sassaƙa a ƙarshe sai kuma naɗewa wanda shi wannan sashe bayanin naɗe babin ne a taƙaice.


Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.