Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

Rubutawa: Shehu Hirabri
08143533314
Amshi:
Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Idan ka ga nan a jahar Kabi,
Yara: Dr. Sama’ila ya aiko ×2
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: In Allah ya so ya yarda,
Kai za ka yi gwamnan jahar Kabi, ×2
Yara: Manya da yara suna addu’a,
Allah ya yarda da Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Jahar Kebi ba wargi ce ba,
Tana da ɗimbin al’umma,
Ku za’bi mutum cimcimtace×2
Irin Sama’ila Sambawa,
Dun kar ku yarda da jemage,
Yara: Ko yaushe kai na suke yake,
Ba za ya yarda da kowa ba.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Sake jikinki in don ‘yan ƙwaƙwa,
Wannan karon ba na su ba ne,
Yara: Dr. hana masu ‘ba’batu.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Sake jikinka in don APP,
Wannan karo ba nasu ba ne,
Yara: Dr. hana masu ‘ba’batu.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Dogo mijin Hajiya Baraka,
Ka ƙara matsawa don Allah,
Yara: Duk mai gaya ma shi wane ne,
Dr. gwada mishi hilinai.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Dogo mijin Hajiya A’i,
Ka ƙara matsawa don Allah,
Yara: Duk mai gaya ma shi wani ne,
Dr. gwada mishi hilinai.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Dogo mijin Hajiya Adama,
Ka ƙara matsawa don Allah,
Yara: Duk mai gaya ma shi wani ne,
Dr. Gwada mishi hilinai.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Yanzu duk mai gaya ma shi wani ne,
Yara: Dr gwada mishi hilinai.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: A jahar Kebbi kowa ya waye,
Ba su koma za’benka ‘barawo,
Ya kwashe kuɗin talakawanai×2
Ya je ƙasar waje ya ‘boye,
Yara: Har na ji mutane suna hwaɗin,
Olle raga muna nerori.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Mulkinka wane mulkin banza ne,
Mulkinka ba ya da tasiri,
Tun randa wane ya zam gamna,
A jahar Kebbi kowa na kuka,
Talakawa sun damu da kai,
Na ji har suna roƙon Allah,
Yara: Yada mun ka ga hwarkon mulkinka,
Ya Allah gwada muna ƙarshe nai.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Duk wanda yake ANPP,
A jahar Kebbi kowa ya katce×2
Yara: Don sun san ba su da majority,
In ga Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Duk yada aura ya kai ƙarhi,
Ba ya shiga ɗakin kura, ×2
Idan ba da bindiga ya zo ba,
Yara: Koda da bindiga ya zo ma,
Kare ba ya i mata wa a shi.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Nijeriya a bar ma Obasanjo,
Yara: Jihar Kebbi a bar maka Sambawa×2
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Wani ya ga alamun ya hwaɗi,
Can nis same shi Ɗanwarai,
Ya ɗauko shata babban mota×2
An shaƙe mai ita da albasa,
Yara: Ya ce a kai mai a Ibadan,
Can za a kai ta a saisam mai.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: APP kun ‘bata shirinku,
Kun kada girman sarakuna,
Ga wanda ya gadi sarauta,
Sai ɗai ku kar’be rawani nai,
Yara: Ku ɗauka ku ba maginin laka.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Wani ya ci tuwonsa na shinkahwa,
Ya ɗauki pure water ya sah,
Sai ya gano bawan Allah,
Mai cin tuwon dussa kullum,
Ya ce ya hana masa dussatai×2
Ku al’umma na tambaiku,
Shin wannan shi ne adalci?
Yara: Wannan ya yi babban zalunci,
Ko ba a ce masa komai ba.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: PDP babbar jam’iya,
Wanda yake yin PDP,
Ba ya kissa ba ya munahwuci,
Sai dai ya yi maka alheri,
Yara: Ka ci arziki ka ji daɗinka,
Don ba a yo ma mutun ƙeta.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: A Maiyama can lokal gwaman,
Ni Ɗanba’u na tambai ku,
Wa kuka son ya zame gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: A wa kuka shawar ya zame gwamna,
Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Na je a Jega can Lokal gwamman,
Ni Ɗanba’u na tambai ku,
Wa kuka shawa ya zame gwamna?
Yara: Sun ce Sam’ila Sambawa.
Jagora: Garin Gwandu can lokal Gwamman,
Na isko mutane sun taru,
Ni Ɗanba’u ni tambai su,
Wa kuka shawa ya zame gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Aleiro gari lokal gwamman,
Ni Ɗanba’u na tambai ku,
Wa kuka shawa ya zame gweamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Wa kuka shawa ya zame gwamna,
Sun ce Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Birnin Kebbi can lokal Gamman,
Ni Ɗanba’u taibaiku,
Wa kuka shawa ya zame gwamna,
Sun ce Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: A garin Kalgo can lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambai ku,
Wa kuka shawa ya zame gwamna,
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Birnin Bunza can lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Garin Kokoma lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Garin Bagudu logal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Garin Zuru can lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: A garin Argungu can lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: In garin Augi can lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Yelwa Yauwi lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: In garin Shanga ma lkal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Sai Ingaske lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Garin Zuru ma lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Birnin Fakai lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna? ×2
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: A Kangiwa lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Birnin Kamba ma lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Amshi: Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan takara gwamnan Kabi,
Dr. Sama’ila Sambawa.
Jagora: Danko Wasagu lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Birnin Ri’ba can lokal gamman,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Duka malammai na jihar Kabi,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: Sarakuna namu da a Kabi,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
Jagora: In talakawa na jihar Kabi,
Ni Ɗanba’u na tambaiku,
Wa kuka shawa ya zame Gwamna?
Yara: Sun ce Sama’ila Sambawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.